Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fuskansa na dauke da damuwa sosai yana kallon motan yaga wacce ke ciki ba yar gidansu bane cus motan Mami ba tinted bane, while Ziora har lokacin jikinta ke rawa, calmly yakarasa wajen kofan baiyi knocking ba direct yabude kofan inda take dasauri tajuyo ta kallesa jikinta na rawa hakama bakinta sai kawai yayi shiru ya tsareta dawasu irin idanu da tunda take aduniya bata taba ganin wani yamata kalan kallon ba kamshin turaren dataji rannan na ratsa hancinta mai bala’in dadi, dauke kanta tayi da sauri gabanta na fadi ahankali da muryanta mai shegen zaki nan that looks like na baby tace “Ma….Mami is at home with your brother Imam” jin shiru baice komiba saita dago idanunta karaf suka hada idanu still kallonta yake, maida kanta kasa tayi takai hannu taja gyalenta daya sauka a bayanta tarufe kanta, ahankali Ziora tace “she asked me to go with this car and bring it back tommorow” shiru har lokacin baiyi motsi ba, sake kallonsa tayi zata kauda idanu for the first time tunda yazo wajen cikin wani husky voice that’s not that loud and it’s very calm yace “which hospital did you take Mami to?” Idanunsa kaman wuta haka yake mata ajiki ga muryansa dadi kuma a natse yake mata magana unlike dayan Imam dakeyi kaman mahaukaci, ahankali tace “Evercare Hospital” anatse yace “me suka mata a hospital”? Kallonsa tayi wai yadauka ita Dr ce yake mata magana haka, da yar mitsilan voice tace “it’s my brothers hospital, he’s a Doctor, his name is Dr Muhammad Chidi, he was trying to wake her up bata tashi ba before I see cancer card in her bag da drugs nata and went to tell him, he told me good job and he did something she wakes up tace she doesn’t want anything, Ya Chidi did not do anything to Mami and she got better” yadade yana kallonta tunda tafara magana kaman mai reading wani abu kafin anutse yace “thank you!” Sai kawai yajuya tabisa da kallo jin yace mata thank you, motan taga yashiga yayi reverse back sai yawuce yashiga layin da mugun gudu tabi motan da kallo har lokacin gabanta na fadi sannan ta kunna motan jin ya kunnu kawai taja bata damu da damage dayama motar ba ai ta gidansu ce. Budemai gate akayi ya shiga gidan da gudu wani wawan parking yayi yafito yayi cikin gidan, bude kofan flat nasu yayi, falo ne mai bala’in kyau ga gefe daya hospital bed ne dayake a gyare, ga wheel chair ga cart da drugs da abubuwa da dama na hospital ke kai, ga wata nurse dake sanye da uniform tana ganinsa tace “welcome Dr” ko kallonta baiyiba direct yawuce wani daki dake nan kasa yabude kofan kai tsaye Mami yagani harta chanza kaya ta kwanta Imam na rufamata bargo duk juyowa sukayi suka kallesa sai yataho wajen gadon muryansa yanuna bacinrai sosai yace “mesa ka barta ta fita Imam? Why didn’t you call me?” Imam zaiyi magana Mami tace “baruwan Maheer shima baisan nafita ba, ni nahana ma’aikatan su kiraka I wanted naje nai lalli” kallonta yayi idanunsa sunyi wani iri yace “we could’ve called mai lalle har nan gida Mami, what if something happened to you” shiru Mami tayi tana kallonsa saitai murmushi takalli Imam tace “Maheer ka gayama yayanka Aliyu I can’t escape death, ko da ban fita daga gidan nan ba, nagaji da zama waje daya, I’m not happy, da ragowan karfi na akan mene bazan fita ba saidai komi azo amini agida eh, nagaji, ku barni naji dadin rayuwana ko yayane kafin mutuwan tazo duk ita muke jira duk kuhuta” dasauri Imam yaduka yace “Mami, Mami why are you talking like this?” Cikeda fada Mami tace “why won’t I talk like this? Kaima nadawo gidan nan yarinyar data taimakeni baka mata godiya ba sai cimata mutunci kana mata tijara daban daban kake agabana sabida kaga bani da karfin fada dakai sai yanda kukai dani dakai da yayanka, me kuke nufi dani? Ku kyaleni naje nakama haya nayi zamana mana, baku bani kwanciyan hankali, bata farin cikina kuke ba, kulleni kawai kuke adaki kullum” Maheer zaiyi magana Mami tace “duk ku tashi kufitan mini daga daki, kufita I don’t want to talk to any one acikin ku” juyawa ahankali Babban yayi yafita, shima Maheer yatashi yafita Mami tai shiru saitakai hannu ta goge fuskanta, she knows mesa suke all this abubuwan nan but tagaji bataso, ko mutuwa zata risketa tafiso mutuwan ya risketa tana cikin farin ciki da annashuwa, yes tafita tafadi ta suma and sai me? Farin cikin tafita taga jama’a taga mutane ta shaki fresh air outweighs sumewan datayi da sauransu, and she also met a beautiful young girl Amrah. Imam na fitowa yaga yayan nasa yawuce staircase yayi sama, Ya Haidar akwai bakan zuciya, yadan jima tsaye a wajen saiya kalli kofar dakin Mami sai ya kadakai yawuce benen yayi sama direct yayi dakin dake karshe chan lungu a saman, knocking yayi yana tsaye kusan 5secinds sannan daga ciki yace “come in” bude kofan yayi yashiga ciki yana tsaye yabama kofan baya yana cire kayan jikinsa anatse Imam yace “can we talk Ya Aliyu”? Labcoat din ya yazare ya ijiye kan gado yace “uhm’hmm” ma’ana yana jinsa, ahankali Imam yace “please kadan rangwanta wasu abubuwan akan Mami, if you look at it since tana stage din da there’s really nothing we can do why don’t we let her have her way eh Ya Haidar? But right now she feel caged, she feels suffocated, please Yaya let her be kaji, tadinga fita anytime takes……” wani kallo daya juyo yama Imam yasa yakasa karasa maganan, cikin kakkausan murya yace “do you think tana fita fainting everywhere dataje is good for her? Do you think sabida she has just few more days or weeks or months to live who knows na barta taita yanda takeso tana decreasing quality na life dinta? Do you think i should just give up on her? Do you have any idea the way i spend day and night making research for any miracle that can cure Mami looking for trials here and there”? Lumshe idanunsa yayi kadan trying so hard to control temper nashi sannan yabude su yace “kome Mami takeso i mean komenene she knows me, I will provide it for her ko a bangon duniya ne I can go and bring it to her reach, but tadinga fita I will never let that happen, she was lucky today Imam what if she fainted while driving on a her way?” Yayi shiru yace “sabida she’s dying I should just let her die? I can’t, I can’t and this conversation ends here please” yana maganan yawuce yashiga bayi, Imam yadade tsaye awajen all maganan da Ya Haidar yayi is true sabida ance zaka mutu doesn’t mean abarka kayi acting reckless ka kashe kanka, banda hakaba it bothers Ya Haidar ciwon Mami sama da kowa, ahankali yajuya yafita yabar dakin he will talk to Mami dake fushi anjima when she is calm. 💫KAUNA DA SO💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 1️⃣1️⃣ Wanka yayi yafito daure da towel, shiryawa yayi cikin wani simple 3quater ash color da white vneck t-shirt sai uban kamshi yake, yafito sanye da slippers yakaraso falon daidai nurse na fitowa daga dakin takallesa tace “she refuse to take her drugs Dr” Imam dake zaune a dinning kallon nurse din yayi jin abinda tace, anatse Haidar yakalli agogon dakin yace “it’s almost time you can leave, I’m not going anywhere” dasauri Nurse din tace “thank you Dr” tawuce wajen kujera tadauki wani leda ta warware abayanta tasaka tasaba handbag tafice while shikuma yawuce kitchen, da kansa Imam yataso yabiyosa yace “mezaka dafa mana Dr Yaya Aliyu Haidar”? Wani kallo Haidar yamai baiyi magana ba, Imam yayi dariya yazo ya tsaya kusada shi, kadakai kawai Haidar yayi yabude freezer yana ciro chicken Imam ya karba yawuce wajen tap yana wankewa, yaciro frozen peppers yasa a food processor yayi chopping nasu, cikin 40min yahada chicken soup sannan yayi smoothie na apples da cucumber, yabude wani powder magani na magnesium da Calcium yazuba ciki yasa komi a tray yadauka yafice daga kitchen din, Imam kuma yazuba nasa soup din yafito yawuce yayi zamansa a dinning. Gently yabude kofan dakin Mami da sallama abakinsa yar karama, Mami na kwance kan gado tana ganinsa tadauke kai, maida kofan yayi yarufe yataho dakin yazo wajen gadon ya ijiye abincin a kan carpet yadawo bakin gadon yazauna yayi shiru yana kallonta kafin ahankali yakama kafafunta yadaura kan cinyansa ya matsa calmly da wannan muryan mai bala’in dadi ta lallashin iyaye yace “Hajiya Mami” shiru Mami tamai, ahankali cikeda lallashi yace “I am sorry Hajiya Mami, dan Allah kidena fushi dani” yayi maganan yayi shiru yana kallonta, yakai kusan minti daya ahaka yana kallonta sai Mami tajuyo takallesa sai kawai ta taso ta zauna kusadashi tace “I felt dizzy na sume and so what? A gida ma yanamin haka naga ko, inaso nai kunshi” tanuna hannayenta da akamata kunshi dayayi kyau sosai da kafafu tace “bazan iya fita ba? Aliyu mutuwan nan ko munaso ko bamu so saitazo then why should I restrict my self from living? Ka barni lemme make the few days I have left memorable, sanda ciwon zata kankama ma ko ance naje nan da chan bazan iyaba eh…..” dan shiru tayi sabida yanda taga yana kallonta idanunsa sun kada sunyi jaaa, saikuma taji zuciyanta yamata rauni, ya mugun bata tausayi, danma namiji ne, is not easy kaga mahaifiyarka right in front of you kuma kasan bazata dade a duniya ba, yanda yaga jikinta yayi sanyi tama daina fadan sai yaji komi ya tsaya masa, ataushashe yace “me da me kikeso Hajiya Mami?” Yanda kirjinta yamata sanyi na rashin kuzari yasa tama kasa magana, matsa kafanta yayi yayi murmushi yace “tell me” kallonsa tayi tai murmushi tace “inaso nadan dinga fita koda bazanyi nisa ba, kaman zuwa su chefane, da sauransu inaso nadinga zuwa” gyadamata kai yayi yace “okay zan dinga kaiki” dasauri tace “aikin ka fa”? Ahankali yace “my work can wait anytime kike bukatan wani abu Hajiya Mami, yanzu sauko kici abinci” abincin ta kalla saita kallesa tace “nagaji da cin irin wayan nan abinci Haidar, kubani dambu, fate, burabusko, farfesu, da abubuwa masu zaki sunake so” shiru yayi duk yana kallonta saiya gyadamata kai yace “okay let’s finish eating this i will get pen ki lissafa ko me kikeso i will get them tommorow, you haven’t eaten anything, come Hajiya Mami” yayi maganan yana kamata batai musu ba ta sauko carpet din ta zauna daidai ana bude kofan Imam ne yaci gayu yace “bari naje gida” Mami tace “ka gaidamin da Maman Samha” murmushi yayi yace “okay makesure kin cinye tasss, idan kinason wani abu call me zan taho miki dashi anjima” gyadamai kai tayi tace “banda gudu a mota” karban smoothie tayi tanasha, ahankali Haidar yace “what happened today Mami?” Dan kallonsa tayi kafin tabasa labarin from beginning to the end tace “nadade banga yarinya mai shigarai kaman itaba, she’s very very caring Aliyu” baice komi yadinga bata abincin tanaci she ate small yabata magungunan ta tasha na dare dan magrib yayi sannan yakamata yakaita bayi tai alwala yafito yasata a dadduma yabata hijabi lokacin an tada salla a masallaci bayinta yakoma yayi alwala sannan yafito yaje sama yasa jallabiya yana zuba kamshi yafito yawuce mosque. Saida akai isha’i yadawo yashigo gidan, dakin Mami yabude itama mikewanta dagakan sallaya kenan tamasa murmushi tace “bari na watsa ruwa” gyadamata kai yayi tabude bayi ahankali ta shiga shikuma yawuce wardrobe nata very comfortable abubuwa suke saya mata, rigan bacci yaciro mata doguwa har kasa pink mai bala’in taushi ya ijiye akan gado, skin dinta use to become so flecky so sheerbutter take shafawa ya ijiyemata dawani simple body spray dawasu safuna dawani man zafi saiya wuce yazauna kan wani kujera dake gaban study desk dake dakin yana facing bango, fitowa Mami tayi daure da towel idanunta akansa saita dauke tazo bakin gadon ta zauna tai amfani da karamin towel ta goge jikinta tadauki man ta shafa tadauki rigan tasaka ta zare towel ta ijiye gefenta sannan tazauna tadanyi gyaran murya, juyowa yayi yataso towel din yafara dauka ya maida bayi saiya dawo yaduka agabanta kafanta yadauka yasaka kan cinyarsa ya shafaman da kyau kafin yashafa man zafi yasa mata safa duk Mami na kallonsa, yasake daukan dayan kafan yamata haka saiya gutsuro kadan yazo ya shafa a lips dinta sai kallonsa take Haidar baida magana, baida hayaniya, amman yanada zurfin ciki sosai, banbancinsa da Imam kenan shi yanada magana da yanzu yacika dakin da hayaniya. Maida kayan shafa yayi yadawo ya gyara pillows din ya kwantar da ita yaja bargo ya rufamata yana rage remote na AC while Mami tahada hannu tana yan addu’a zama yayi abakin gadon yana kallonta, ahankali Mami takai hannunta takama nasa, kallonta yayi hakan yasa calmly Mami tace “taho” jawosa tayi sai kawai tadaura kansa saman cikinta zai tashi dasauri tace “I’m fine ba abinda kemin ciwo ka kwanta Aliyu” ijiyan zuciya ya sauke ya kwantar da kansa cikin nata, anatse Mami ta shafa kansa tai shiru kaman mai tunani kafin chan tace “you’ve dedicated your whole life to me, baka fita da frinds, baka zuwa shakatawa na samari irinka, baka zuwa buga su kwallo ko golf kaman su Imamu, you don’t do anything for yourself sai ni, amman natashi natasaka agaba da fitina, inata masifa kaman bana ganin abubuwan dakake tauye kanka akaina ko, I’m so inconsiderate” zaiyi magana tace “shiii I don’t want you to talk” shiru yayi saitadan jinkirto ta yanda zataga kansa da kyau akan cikinta shima yana ahaka ya kalleta all she sees is dan yaronta data haifa 35yrs ago, lumshe idanu tayi tabude cikin wani sanyin murya tace “I don’t think without you I would have survived all this years Aliyu, seeing how you’ve worked so hard everyday for me wants me to live more for you, banso natafi na barka, thank you Aliyu, Allah maka albarka” maida idanunsa yayi ya lumshe da sauri he hates when Mami tafara irin maganganun nan, har gwara ma tanamai masifa da fada ma da wannan emotional abubuwan, yayi shiru kawai ahaka, baitaba nunama Mami weakness nasaba bazatasa yakuma fara yauba, seeing him weak will be wat will kill her first kafinma ciwon, dago kansa kawai yayi yana bude idanuwansa yakama hannunta yakai bakinsa yayi kissing yace “enough of the talk, you had a busy day yau, now sleep” ijiyan zuciya ta sauke saitai murmushi ganin karfin halinsa da jarumtarsa cikin yar kankanuwan murya tace “gobe zakaga Amrah don’t be rude like your brother Maheer kaji”? Gyadamata kai kawai yayi saitai murmushi ta kwanta yasake gyaramata rufa ta lumshe idanu nan da nan bacci ya kwasheta yadade zaune awajen yana kallonta, juyawa tayi cikin bacci hulanta ya salube babu gashi akanta sai wasu yan kwarorin gashi farare Chemo ya cinye gashin tass, yadade yana kallonta ahaka kafin yatashi ya gyaramata hulan yasa mata da kyau, yaja drawer gefen gadon yaciro stethoscope yamakala a kunnenta yakai ya daura a kirjinta yayi shiru sannan ya cire ya ijiye yamata addu’a da kansa saiya mike yajuya yafita daga dakin yarufe kofan ahankali without making a sound ya kalli agogon bango is 9:30 tunda har yakai war haka bai dawo ba bazai kwana nan ba yau, kofa yawuce ya rufe dudda sunada ma’aikata he don’t trust aikinsu, immune system na mamansa is low, baison anything dazai sa tadauki wasu germs ko bacteria hakan yasa kawai yashiga kara gyara falon da dinning dan nanne wajen zamanta da gadonta na mara lafiya, yayi mopping ko ina ya goge ko’ina da duk inda hannunta zai iya tabawa da abubuwan dake kashe germs har tv kana ganin yanda yake aiki kasan yanada zafin jini, wuraren 10:30 yagama yatafi sama dakinsa yashiga direct yafada bayi sai wanka. Yafito daure da towel yana tafiya abubbude zai wuce wajen wardrobe yaji wayansa na kara juyowa yayi yakalli wayan saiya bude wardrobe nasa yadauki kayan dazai saka yadawo yazo yazauna abakin gadon yakalli screen na wayan Dr B aka rubuta a screen din, saida wayan ya katse yayi dialing number yakai kunnensa ringing daya aka daga muryan mace ne daga bangaren cikin more like fada da masifa tace “how many miss calls kaga na maka Haidar?” Shiru yayi baice komiba sabida yanda tamai maganan da fada, kaman tagane meyake nufi tadan sassauta murya tace “how many miss calls kaga namaka fisabilillahi? I’ve called you more than 30times, you left the hospital without letting me know, inata kiranka tun kafin magrib har zuwa yanzu baka dagawa and ina tambayanka kamin banza wani irin miskilanci ne wannan”?. 💫KAUNA DA SO💫 ✍🏻M SHAKUR EPISODE 1️⃣2️⃣ Strictly da muryansa dake fita da kyar yace “they was an emergency at home I had to rush back home, I left my phone in my room while I’ve been with Mami all this while” sosai kirjinta ke tafarfasa when will this old winch die tasami kan Haidar dinta all to her self? Taki mutuwa? Yaro baida sukuni sabida ita, baida lokacin soyayya akan mene, mata kawai tazama annoba arayuwan danta ga yaronta haddden guy ga mahaukacin ilimi gasa dan baiwa, da kyar ta sassauta muryanta tace “how is she?” “Asleep” yafadi kai tsaye da yar karaman murya, dan sassauta muryanta tayi tace “I’ve missed us Haidar, I’ve missed you, I can’t remember the last time muka zauna and had a good conversation tare tun muna UK, you barely look at me ko a hospital, you are either with patients ko busy making research ko kana gida tareda Mami, in all this do you even know what I’m going through?” Dan shiru yayi he felt a little bit bad cus yasan how much Habiba ke sonsa, Beeba really loves him, ahankali yace “I thought kin bini siyama Mami drugs a mall the other day” dasauri tace “ko kallo na isheka ne, ba dadan mun hadu a hanya bama ai bazan ganka ba” shiru yayi feeling bad ahankali yace “I will check my schedules for next week, I will see you” murmushi tayi sosai tace “thank you, I love you Dr AH” anatse yace “me too” he’s always serious idan da sabo ta saba da halinsa zatai magana yace “good night” abu taji ya tsaya mata a wuya kaman tacemai durun uwarka da goodnight ta daure da kyar tace “sweet dreams Mijina” katse wayan yayi ya ijiye yatashi yasa kaya shi yanada wani irin mindset gani yake all those soyayya surutan nan bata lokaci ne, once yace wannan zai aura shine kawai, mena wani this and that kaman yara, dadduma ya shimfida yayi shafa’i da wuturi yadauki Al Qur’ani yakaranta wanda kullum duniya da daddare saiya karanta baya samun time na karantawa da safe sannan yamike yasauka yazo yabude dakin Mami wani blacket yadauka ya shimfida akasa yasa pillow kawai ya kwanta ko yace karya kwana dakinta baya iya bacci yadinga tunani yana saukowa up and down dubata kenan, saisa kwana tareda ita yafi mai alkhairi. ** Gaban wani babban gida kaman gari guda yayi horn nan da nan aka budemai gidan ya shiga, babban gidane na gani na fada ga flat manya manya guda biyu, wucewa yayi yay parking yasauko yana tafiya yawuce babban flat din yabude kofa yammata ne a dakin su uku suna hira suna ganinsa atare sukace Ya Imam sannu da zuwa, gyadamusu kai yayi yawuce sama gaban wani daki yayi knocking tareda budewa wata hamshakiyan mata ce zaune ga waya a kunnenta tana magana, tama Imam wani kallo amman ko ajikinsa saima karbe bowl na fruits dake jikinta dayayi ya zauna gefenta yana sha, matan tace “I will call you back Uwale” tana sauke wayan tawani dakamai duka abaya saida fork da fruits dake jikinsa yafadi akasa dasauri Imam ya kalleta yace “Mamaaaa” dakuwa tamai tace “kaci uwaka da Mama, kana ina tun jiya?” Tabe baki yayi yace “ina tareda Nabeel” wani kallo tamai tace “wani Nabeel din? Wanda yazo nemanka dazu shima? Ko wani Nabeel din daban?” Shiru yayi baice komiba tasake haderai tace “kana gidan matan nan ko”? Wayansa yaciro batare dayace komiba yahau dannawa, rai abace Mama ta fizge wayan tace “I’m talking to you Maheer, me matan nan tabaka da ka kasa fita daga rayuwanta dana danta iyye? Wat are you doing in their house?” Dan kallonta yayi sabida yanda ta kwace wayansa, ahankali yace “Mama all this bitterness na menene? This woman nagadai tarabu da Abba ko? Mama fisabilillahi she’s sick, very sick da mutuwa kawai ake jira amman kullum fada kike akanta, menene aciki dannaje na dubata?” Cikin fushi Mama tace “akwai komi aciki ba babysitter na haifo ba danta na asibiti kai ka kashe wando kana watching over her kaki zuwa kampanin ubanka kai aiki, kwallo ma kaki zuwa kayi” cikin dan fushi yace “I’m not babysitting anybody Mama, Mami has everything, nurses, chef, her Son makes everything available for her Mama, I’m not babysitting kawai zuwa dubata nake, wai bakida tausayi ne Mama”? “Eh bandashi kuma banso kana rabansu” Mama tafada da zafi tana nunasa da yatsa tace “kuma ka kara zuwa ban yafe maka ba” shiru yayi yana wani irin kallonta tace “kajini ko” akufule yace “eh bani wayana toh zanje gidansu Nabeel dayazo nemana” cikin fushi tace “better ka kara zuwa kagani wlh ban yafe maka ba” karban wayan yayi yajuya fuuu yafice daga dakin Mama tabisa da harara, yana ficewa compound daidai ana bude gate wani arnen jeep na shigowa ga another car na securities yan sanda dolensa ya tsaya sabida mahaifinsa ne, parking akayi aka budemai baya wani magidanci yabude baya yafito zaiyi kusan 70yrs kawai yanada jiki mai kyau ne yasaka babban kaya, gawani tambarin Nigeria dake wajen aljihun babban rigan kaman mutumin yana rike dawani office a gwamnatin Nigeria, exactly bakin fatar mahaifinsa Aliyu yayo da yanayin jikin da kuma tsayin, yafara tafiya daidai yana tahowa dan dukawa gabansa Imam yayi yace “sannu da zuwa Abba” dakatawa mutumin yayi ya kallesa sosai wani irin mutum ne shi da Allah yamasa hikima da basiri kaman aljani, cikin muryan dattaku yace “yau kwana uku da wuni daya ban saka a idanuna ba Maheer kana ina?” Dan shiru yayi kaman bazai bada amsa ba yace “ina tareda Yaya Aliyu Abba” sake shiru Abba yayi sai kawai ya kadakai yawuce Imam yamike yabisa da kallo idan har shi yau kwana uku bai gansa ba, yafi wata daya rabon da Ya Aliyu yasa kafansa agidan nan cus he’s busy da Mami, kaman yamai magana yakamata yazo ya gaida Abba amman yashare maganan ya shige mota abinsa yabar gidan. ** Wuraren to 6 Ziora ta isa gidansu she knows Mami tadawo saloon mai saloon din zata gayamata takai wata wajen Ya Moh a hospital, she knows Mami will call Ya Chidi and confirm kafin tadawo gida, a compound taga Mommy tsaye tana magana da gardener dinsu tabi motan da kallo da Ziora tai parking, itama tamata wani kallo kafin tajuya tashiga flat nasu, waving step Mom dinta dayaga tafito daga flat nata Ziora tayi itama tai waving nata sannan ta shiga flat nasu Momy tace “na kaiki saloon sabida ki gyara kai and let go off this old braid amman kinje saloon kin dawo super woman, heroine and be taking people to the hospital ne cus you have a brother that’s a Dr” dan murmushi Ziora tayi kadan sai kawai tazo tai hugging Mommy, saikuma tafashe da kuka sosai dayasa duk wani masifa da Mommy keji ta hadiye tace “wat is it why are you crying eh? Matan tamiki wani abune”? Girgixama Momy kai tayi saita dago ta kalli Mommy ahankali tace “Mommy I love you so much” baki Mommy tasaki tana kallonta Ziora wannan yarinya ta iya drama, cikin sheshekan kuka dan she’s really emotional tace “I can’t imagine my life without you, Mommy idan kina malaria I use to cry kaman zan mutu balle kuma naji wani babban ciwo yakamaki, I can’t imagine my life without you in it, Mommy I will not survive idan banda ke, Mommy wlh

Chapter 6 of 26