Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shirin da ake yi ya fi komai ɗagamata hankali. Zuwa lokacin Hajiya ta gama fahimtar har sannan ba son Hilal take ba, ba kuma ta ɓoyewa Anti Zulaihat da Rafee'ah ba. Aikuwa ranar da suka zo gidan suka tararmata.   "Kar ma ki fara wannan iskancin! Wallahi kika bari ya je kunnen Abba sai kin gane shayi ruwa ne. Ke ba abin kunya bane ba ma ace kin yaudari Hilal? Ya yi rayuwa a ƙasar waje, ya ga wacce ta fi ki komai da komai bai sa ya ji zai sauya sheƙa ba, sai ke da amana ta miki ƙaranci ko?" Ta turo baki gami da tsuke gira, kalaman Rafee'ah ba karamin zafi da suka suke yiwa zuciyarta ba. Kai tsaye ta ba ta amsa babu shakkar komai. "Ai ba ni na sanyawa zuciyata son Aliyu ba, Allah ne Ya haɗamu. Kuma da yardarSa, shi zan aura. Hilal ni na kawoshi na ce ina so yanzu kuma nace bana so bana ra'ayinsa, yanda ba'a yiwa wani cikinku dole ba nima..." Marin da Anti Zulaihat ta watsamata ya sanya ta yin shiru da dafe kuncinta. Ta mance rabon da fuskarta ta ji mari, jin zafin zuciya da na marin na neman haɗemata ya sa a haukace tana kuka ta ci gaba da magana murya a sama. "Eh! Eh! Ba zan daina son Aliyu ba! Zan iya kashe kaina muddin ku ka aurar da ni ga Hilal! Bana sonsa! Bana sonsa ko za'a yimin dole?" Tana gama magana ta fice a guje daga dakin Hajiyar zuwa ɗakinta ta rufe kofar gami da sanya muƙulli ta zube kasa tana kuka. Sa'arta guda Hajiyar na sashin Abba. Zulaihat da Rafee'ah suka shiga kallon kallo tsakaninsu da tsananin mamaki da kuma sanyin jiki. "Cabɗi! Akwai aiki!" Fadin Rafee'ah bayan ta farfaɗo daga suman zaunen da ta yi. Ita kuwa Zulaihat salati ta yi ta shiga safa da marwa a tsakar ɗakin kafin ta tsaya ta dubi Rafee'ah mai fama da karamin ciki. "Wallahi aikin asiri ne. Maza-maza Hajiya ta zo a san abin yi."    "Kamar kin shiga zuciyata wallahi. Ko waye shi kin san bai barta a banza. "    "Meke faruwa? Hayaniyar me ku ke yi?" Kusan a razane suka juya, Abba ne a gaba sai Hajiya a gefensa. Shakka babu muryar Ramlat ce ta fiddosu. "Bakomai Abba." Fadin Zulaihat cikin son kwantar da hankalin Uban nasu. Itama Hajiya shiru ta yi sanin abinda ke gudana, ranta na ɓaci don har wani huci take fitarwa, tuni ta gane hayaniyar Ramlat ce, kuma ba akan komai ba sai akan Aliyu. Tana jin Abba na fada akan kar su ƙara. "Ku mata ne, bai dace a dinga jin muryarku a ɗage haka ba, bana so kar a kara." Suka amsa da toh kafin ya fice Hajiya ta dubesu kamar ta yi magana sai ta fasa ta bi bayansa.   Ita kuwa Ramlat sai da ta ci kuka mai isarta kafin ta fito, kusan hakan ya zamemata jiki, duk sadda abu ya ɓata ranta, ta fi kaunar ta kulle ɗaki ta yi kuka har ta huce a karon kanta kafin ta fito. A falon ta iskesu gaba daya har Abba, a gefe ga Yaya Munir shima ya zo. Kusan ma a kanta suke tattaunawa, ta ɗan ja burki ganin ba su ganta ba ta dan koma baya. Batun furnitures ake yi sai kayan kicin da za'a damƙa ragamarsu a hannun Zulaihat.   "Komai na Ramlatu ina so ya zama na musamman, kamun kan yarinyar ya fi komai burgeni, ba ta biyewa samarin zamanin nan ba, ba kuma ta tarasu ba barkatai. Hakan ya fi komai kyau, kuma shi ya fi dacewa da dukkan wata ɗiya mace da ta san ciwon kanta. Allah Ya yi mata albarka da ku gaba daya." Idan ka cire Yaya Munir da ya amsa fuska a sake, su Hajiya kam sun amsa cike da tausayin Abban wanda bai da masaniyar abinda ɗiyarsa ke shukawa. "Ni kaina Ramlat ta burgeni ta kuma shayar da ni mamaki Abba. Allah Yasa ayi komai lafiya a gama. Ya basu zaman lafiya."    Aka amsa addu'ar Munir da Amin. Ta juya a hankali ta koma dakin, wani sabon kukan ta shiga yi. Ji take inama za ta iya ture dukkan komai ta mika zuciyarta ga Hilal, inama za ta iya wannan kawaicin ta auri Hilal ko don wannan kyakkyawar shaidar Abba da Munir gareta ya bibiyi rayuwarta. Sai dai kuma daga sadda dare ya raba, duniya ta dauki shiru sai kukan karnuka, kunnuwanta suka shiga sauraron kalaman Aliyu masu tsumata da ƙaramata dukkanin kwarin gwuiwa, daga sannan ta sanya ƙafa ta shure tunanin kalaman mahaifinnata da Yaya Munir.  Ta ƙara rudewa susucewa akan Aliyu. Ta kuma kudurce da kara daukar mishi alkawarin yanda ya rabu da Muhibbat dominta, haka za ta rabu da Hilal ta aureshi.     Ta shagala iyakar shagala wurin fayyace mishi abinda ya wakana a yau da kuma irin tijarar da ta yi duk a kanss, ba zato ta ji an yaye bargon rufarta gaba daya. A gigice ta mike duk a zatonta A'isha ce, sai dai ganin Hajiya tsaye a kanta ya sanya cikinta ɗurar ruwa. Kafin Hajiya ta ce komai sai da ta ɗaga wayar ta haɗa da jikin bango ai kuwa ya fadi anan ya tarwatse,Ramlat jiki na rawa ta bude baki da zummar magana ta dauketa da mari hagu da dama.   "Waya?! Wayar dare?!! Har wuyanki ya kai wannan kaurin? Ramlatu wace irin jaraba ce wai! Wane irin jahilin so kike yiwa Aliyu? Anya ba asiri ya yi miki ba? Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" "Waye shi? Meke faruwa?" Ba Ramlat ba, hatta da Hajiyar sai da ta ji hantar cikinta ta kaɗa. Abba ne ke tambayar tsaye bakin ƙofa sanye da doguwar jallabiya, basu san adadin lokacin da yake a tsayen ba, sai dai ya ji komai. Ba wani abu da bai shiga kunnensa ba. Jikinsa har rawa, kallo ɗaya za ka ga tsananin ɓacin rai da mamaki shimfiɗe saman fuskarsa, yake ya ƙaraso cikin dakin. Ya ji sunan Aliyu a bakin Hajiya sai dai ya fi kaunar ya gasƙata don tsoro yake ya zamana kunnuwansa ne suka sami matsala. Ya dubi Hajiya ya kuma kai duba ga Ramlat kafin ya dubi wayar dake a tarwatse a ƙasa.   "Dare ya yi, ko mene a bari zuwa safe." Abinda ya iya kokarin furtawa kenan kafin ya fice. Hajiya ta kwashi wayar da ta tarwatse ta dubi diyarta. Ramlat ta kaɗu da ganin hawaye a fuskar Mahaifiyarta, har ta fice ta ja kofar ba ta iya cewa uffan ba. Ta hada kai da gwuiwa ta shiga kuka, kuka iyakar ƙarfinta. Ba za su gane ba, ba kuma zasu fahimta ba, son Aliyu kawai take. So marar algus. Wannan daren ta rasa inda za ta sanya kanta, ta rasa kwanciyar hankali da nutsuwarta, a hankali wani bangare na zuciyar ya shiga yi mata tuni da addu'a ko ta samu mafita. Ko za ta samu Abba ya tausayamata ya bar ta da auren zaɓin ranta.   Shi kuwa Abba kasa bacci ya yi ya zauna gefen gado ya yi shiru. Koda Hajiya ta shigo, ya zaunar da ita a gefensa. "Rabi'atu kar ki ɓoyen komai, fadamin dukkan halin da diyarki ke ciki." Ta sunkuyar da kai cike da tsabar tausayinsa, duka-duka yaushe ne ya gama yabonta? Yau kunnuwansa zasu jiyemishi abinda ta san zai wahala idan bai yi mishi shamaki da bacci ba a wannan daren. Duk abinda ta sani game da Aliyu ba abinda ba ta sanarmishi ba.   "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Shi ne abinda Abban ya furta. ***    Ranar ta Asabar ce misalin ƙarfe tara da mintoci na safe, sai dai sakamakon hadarin da ya soma haduwa a sararin samaniya ya sanya garin yin luf-luf. Iska mai dadi na hurawa mai sanya annashuwa da walwala a zukatan bayin Allah idan ka cire zuƙatan iyalin Alhaji Khalid Mu'azzam da suke jin kamar sun yi rashin wani babban giɓi nasu.  A haka Yaya Munir ya shigo gidan ya tarar da su, ya zo adalilin daurin auren da zasu je na ɗan abokin kasuwancin Abban. Ya yi mamakin ganin rayukan iyayen nasa a ɓace, ya kuma yi mamakin ganin taron nasu akan Ramlat ne wacce ta ƙunshe can gefe guda kanta a ƙasa tana kuka, wannan ta sa ya yi shiru yana son jin daga inda matsalar take.   "Ki fadamin waye Aliyu? Tun yaushe ku ka soma mu'amala? A ina kuma ku ke haduwa?" Ta ɗago kai ta kalli Abban cike da firgici da kuma rashin abin fada don kwata kwata ba ta fahimci inda maganar ta dosa ba. Wace irin haduwa Abban ke nufi? Wace kuma irin mu'amala? "Aliyu?" Fadin Yaya Munir da mamaki. Abba ya ɗaga mishi hannu sannan ya dakamata tsawan da ya sa ta kara karfin kuka gami da soma magana.   "Ina rantsuwa da Ubangijin da Ya busa numfashina Abba, babu wani abu da ke tsakanina da Aliyu face soyayya mai tsafta. Wallahi Abba ina sonsa. Don Allah ka yi hakuri." Abba kusan kasa motsi ya yi a wurin, ya kuma rasa bakin magana don ganin komai yake kamar a mafarki. Hajiya kuwa ta yi shiru don ita lamarin ma ya fara bata tsoro, ta kuma kasa yarda da cewa asiri ne Aliyun ya yi mata kamar yanda su Zulaihat suka ce, ta riga ta san kafiyar diyarta. "Me kenan? Ke za ki fadamin waye Aliyu ko sai na tattaki yanzu?" Yaya Munir ke zancen cike da mamakin jin sabon lamarin da bai da masaniya a kai. A jiyan ne yake ji daga bakin Bilkisu batun hirar da ta yi da Hilal wanda yake tsoron sauyin da ya soma gani a wurin Ramlat din har yana goyon bayanta da ganin kawai yanayin karatu ne. Sai ga wata sabuwa inji ƴan caca.   Sanin halin Yaya Munir dagaske zai iya tattakatan yasa ba shiri ta basu labarin Aliyun a taƙaice da kuma tarihinsa. Don tsabar bakin ciki bai san sadda ya mike ya shiga kai mata duka ba ta duk inda ya samu, sai da  Abba ya dakatar da shi sannan ya koma mazauninsa yana huci. "Rabu da ita Muniru, kyale ta. Abinda kika manta Ramlatu, Khalid ba ya magana biyu. Ina miki rantsuwa da Allah ko za ki mutu sai dai ki mutu a dakin Hilal, ba kuma zan fasa daura aurenki a lokacin da muka sanya da magabatansa ba. Idan ke din ɗiya ce ta halal, ba za ki watsamin ƙasa a ido ba. Na miki uzuri a wannan karon, na kuma dauki hakan da kika yi a wauta. Daga yau, yanzu a daidai wannan lokacin, kar ki kusa na kara jin wani tashin tashina game da Ali.." "Ka yi hakuri Abbana, don Allah ka yafemin. Wallahi ina sonsa, bana son Hilal, na tsaneshi! Abba kar ka yimin auren dole." Wannan karon Hajiya ce ta mike tana kuka tana mai rufeta da duka. "Kaicon ɗiya irinki! Haihuwarki ba ta ƙareni da komai ba! Wallahi gwara naga mutuwarki da ganin wannan rana." Babu wanda ya yi yunkurin kwatarta a hannun Hajiyar, ita kanta Ramlat ta gwammace ta mutu a hannunta. Ta gwammace koma mene ta tarar muddin za'a yarda da zaɓinta. Kuka da dukan Hajiyar bai kashe bakinta daga magana ba. "Ku yimin rai ku bar ni na auri Aliyu, wallahi shi kadai nake so. Ku yafemin don Allah. Yaya Munir ba'a yi maka dole ba! Kar ka bari a tauyemin rayuwa." Anan ne Abban ya dakatar da Hajiya, ya dubi Munir wanda idanunsa suka kaɗa, ji yake kamar ya shaƙe Ramlat ta mutu ko iyayensa zasu huta da bakin cikinnan. Mamakinsa bai wuce na yanda akai ta shaƙu da soyayyar gayen ba, yaushe aka fara da har ya zurfafa? "Idan wannan shi ake kira da so, na yi tirr da irin naki. Ina miki kallon yarinya mai biyayya ashe ba haka kike ba! Ke kuma Rabi'atu har yaushe ki ka bari yarinyarnan ta yi nisa da soyayya haka ba tare da kin sanarmin ba? Wane irin zama kike yi da ita? Ina tsoron ace mu ne ba mu kula da kiwon da Allah Ya bamu ba! Muniru yau ba gobe ba, duk inda Aliyu yake a gidan Justice Abdulrahman Buba, ka nemomin shi." Daga haka Abban ya bar falon a fusace har walkiyar da ake zubawa tana hasko falon ga kuma ruwa da ke zuba kamar da bakin kwarya. Yaya Munir ya shiga rarrashin Hajiya kafin ya nemi ta ba shi dukkan wayoyin na Ramla ya gani, hakan tasa suka mike zuwa dakin Hajiyar ba wanda ya kalleta fuskokin a haɗe. Ganin haka Ramlat ta mike da saurinta ta faɗa ɗaki ta kulle gudun kada ma Yaya Munirun ya fito ya hau ta da duka a karo na uku. Jikinta ko'ina tsami yake yi, fuskarta kuwa shatin hannun Hajiyar ce kwance a kai. Tausayin kanta da na Aliyu ya kamata, ta sani ko giyar wake Abban ya sha ba zai yarda da aurensu ba. Ba kuma zai kira Aliyun bane don magana ta nuna rarrashi ko tausayawa, tana da tabbacin gargadi ne zai yi mishi da kuma datse alaƙarsu. *** Komai sai ya sauya, tun daga ranar da Abba ya yiwa Aliyu cin mutuncin da ba ta taɓa zaton ya iya ba akan ya bar masa ɗiyarsa, komai sai ya sauya. Daga Aliyu, zuciya ya yi ba kuma da kowa ba sai Abban, ya kuma ci alwashin ko guduwa ne zai iya yi da Ramlat, son da yake mata ba zai tafi a banza ba. Hatta ita kanta Ramlat ji ta yi idanunta sun rufe ta bar ganin kowa da gashi akan abinda take so, kullum ganin da take auren dole zasu yi mata. Amrah yanzu ta bar bata goyon baya, hatta Umma mahaifiyar Amrah ta ji koken Hajiya ta kuma rantse kan bata da masaniyar fitar da Ramlat ke yi zance a gidanta. "Amma kuma ta ƙare! Ba za ta kara faruwa ba Hajiya Rabi, wallahi yarda da tarbiyyar yaran ce ta sanya duk muka saki jikinmu da su, ashe ba haka ba. Allah Ya kyauta." Cewar Hajiya Balki kenan uwa ga Amrah.   Abba ya tara yaransa kaf meeting, ya Kuma rantse akan duk wanda ya bar Ramlat yin zance a gidansa bai yafe ba. Ba kuma ga Aliyun ba, hatta da Hilal. "Mutuncin hira a zo gidanku a sameki, don haka ban yarda ba. Ba kuma zan lamunta. Kar ki kuskura na ganki da yaronnan Ramlat, ko labari ya riskeni sai kin gayawa aya zaƙinta. Tunda ba ki da mutunci a yanzun ba kya ganinmu a mutanen da suka isa su fadamaki ki ji." Ta ɗago kai ta dubi Abban wanda tsakanin lokacin da aka soma maganar har ya rame. Ta dubi ƴan uwanta, sakon hararar da kowanne ke aikamata ya sanya ta sadda kai ƙasa. "Nikam Abba da za ka yimin iznin tafiya da ita gidana ina ganin kamar zai fi. Da kaina na kaita makaranta kuma na je na dawo da ita gidan. A ganina wannan hanya ce kawai zamu bi mu toshe duk wata kofar da zai sadata da wannan gayen." Rafee'ah ce ta cafe zancen Yaya Munir. "Wallahi nima hakan naga zai fi." Murmushi mai ciwo Abban ya yi. "Kayya, ku bar wannan maganar. Ko kun manta alaƙar ita Bilkin da Hilal? Bana son su fahimci komai. Hakan zai janyomata tsana daga dangin shi Hilal din. Ku barmin ita anan, amanarta a karkashinmu take, za kuma mu yi iyakar kokarinmu." Kukan da ta fasa ne ya sanya suka maida hankali gareta. Miƙewa ta yi ta zube saman gwuiwoyinta, duk a zatonsu kukan na nadama ne da kuma sauya ra'ayi, sai dai tun kan aje ko'ina ta basu haushi. "Ku yi hakuri don Allah Abba, ku yafemin. Da ace akwai yanda zan yi na cire Aliyu daga zuciyata da na yi. Abba idan aka yimin auren dole zan iya mutuwa!" Wannan karon Abban ne ya kai mata duka, bai fasa dukan ba yana fidda hawayen ganin wannan rana na bakin ciki, babu kuma wanda ya hanashi. "Ka yi hakuri Abba! Ka tausayamin ka auramin wanda nake so! Zan iya mutuwa wallahi!" Kalamanta suka kara harzuka zuciyarsa, yana cikin dukan sai gani akai ya zube. Da wani irin gigicewa iyalinsa suka yi kanshi. "Abba! Abba!!" Fadin Zulaihat, Rafee'ah har ma da A'isha wacce ke jin tsanar Yayarta har cikin ranta. Hajiya kuwa salati take tana karawa daidai sadda Yaya Munir ya daukeshi ya yi hanyar waje babu ko takalmi a kafafunsu. Babu wanda ya kara bin ta  Ramlat suka dunguma zuwa motar Munir dake shirin fita. A'isha ce ta dawo a guje ta dauki Hijabin Hajiya ta koma, ta dai ga Ramlat ko motsi haka ta fice. Bayan tafiyarsu ta dawo ciki, Indo sabuwar mai taya Hajiya aiki ta fito daga ɗakinta. "Auta meke faruwa?" Kuka kawai A'isha ke yi ta kasa amsawa. Ganin Ramlat shimfiɗe a ƙasa ya sanya Indo da matukar razana ta yo kanta. "Innalillahi! Ramlatu! Ramlatu!!" Sai dai ko kusa babu alamar za ta motsa. Ta miƙe da jiki na rawa ta shiga kicin ta dauko ruwa ta hau yayyafamata. Cikin sa'a kuwa ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta bude idanu gami da fadin. "Na shiga uku Abba kar ka mutu, kar ka auramin shi." Indo ta san inda zancen ya dosa, ko ba komai ta tsinkayi abinda ke faruwa a gidan kwanakinnan, ta taimaka mata ta kai ta daki. Sai sannan ta dawo hayyacinta sosai. A gigice ta mike tsaye har tana jiri.   "Abba, Abba, ina Abba?" Ganin ba amsa kwakkwara wurin Indo ya sanya ta maida akalar tambayar ga A'isha dake faman kuka. "Ai ke kika kashe mana shi idan ma ya mutu. Sun tafi asibiti." Kasa nutsuwa ta yi ta fito bayan ta zura hijabi, asibitinsu daya ne a duniya, ma'ana inda ya kasance na family dinsu. Zuwansa gidan kenan adalilin son ganinsa da Abban ke yi, da kansa ya kirashi a jiyan cewa ya zo yau din zasu yi wata magana. Hakan yasa shi zuwa cike da faduwar gaba don ko motarsa bai shigo da ita ciki ba. Kiciɓus ya yi da sanyin idaniyartasa, sai dai ruɗun da ya gani saman fuskarta ya sanya shi tareta a hargitse. "Meke faruwa Ramlat? Ina za ki je?" Ta tureshi kusan a gigice ta dakamasa tsawa. "Dalla Malam ka kyaleni! Nace bana sonka! Bana sonka! Ka rabani da farin cikina, ka rabani da iyaye da yan uwana! Yanzu kuma sanadinka Abba na can asibiti kwance! Ka fita a hanyata!" Ta yi maganar tana kuka kafin ta ja tsaki ta giftashi ta fice a gidan ta mika hanya. Hilal wanda ya kasa kwakkwarar motsi, idanunsa suka kaɗa. Sai kuma ya lura da hatsarin da ke cikin tafiyarta ita daya a wannan halin, komai zai iya faruwa. Da zafin nama ya shiga motar ya tayar, wani wawan ribas ya yi ya kuma sha gabanta gami da bude murfin motar. Ta dubeshi, ta san muddin ba ta hau ba babu yanda za ta yi, kusan ma titin ba ababen hawa sosai, cikin sauri ta shiga. Magana daya da ta shiga tsakaninsu bai wuce sunan asibiti ba, daga haka kowanne ya yi shiru zuciyar na tafasa. Hilal kam ya kasa gaskata abinda ya ji daga bakinta, mutuniyar da ya ke ji kamar ana kara mishi sonta a kowace daƙiƙa. Har suka isa asibitin, ba ta ko bari ya saita parking ba ta ɓalle murfin ta fice da gaggawa. Shima fitowar ya yi ya bi bayanta cikin sanyin gwuiwa.    I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/JS1CQzbtN9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem Ina mika gaisuwa ga duk wadanda aka yi wa rashi. Allah Ya musu rahama. Ya kyautata namu zuwan. Ameeen 12) Su Hajiya ta soma hangowa a tsaye a ƙofar wani daki wanda nan take jikinta ya bata Abba ne ciki. Kai tsaye ta doshi dakin, kafin ta kai ga murɗa kofar ta ji an fisgota har tana faduwa, dama jikinta ba wani kwari ba, ko'ina kuma ya mata tsami sai dai hakan bai sa ta yunkura ta mike ba tana kallon Yaya Munir dake tsaye yana mata banzan kallon da ba ta taɓa gani daga gareshi ba. "Kin zo ki karasamana shi? Kin ji labarin bai mutu ba shi ne kika biyoshi asibitin?" Ganin bai lura da Hilal dake tahowa ba ya sanya Rafee'ah saurin yin magana murya a dan bude kadan. "Hilal sannu da zuwa, tare kuke?" Hakan da ta yi sai ya ankarar da Yaya Munir, ya dubeshi, shima karasowa ya yi yana dubansa kafin kuma jiki a sanyaye ya dauke kai ya durkusa ya gaida Hajiya da tambayar mai jiki. Ramlat ta ja gefe ta zauna saman kujera a ɗarare, kanta a cikin cinya tana kuka. Bayan ya gaisa da Munir ne yake jin abinda likita suka ce. "Ba wani abu bane, kawai ƴar damuwa ce ta sanya hawan jininsa tashi, amma da sauki. Likitan na ciki shiyasa muka fito." "Ya Salam, dama yana da hawan jini? Allah Ya ba shi lafiya kuma Yasa kaffara ne." Suka amsa da Amin. Yaya Munir ya kasa bada amsa ta farko ga Hilal, su kansu basu san Abban da hawan jini ba sai dai sun yi amannar koma mene adalilin damuwar da ya saka a rai game da Ramlat ne. Basu jima sosai anan ba likita ya fito, ya dubesu. "Kun yiwa Abbanmu yawa fa, a yanzu bama son wata damuwa da za ta tashi hankalinsa. Ina rokonku idan ba damuwa a kyaleshi da mutum daya zuwa gobe idan ya samu ya ɗan huta sai ku dawo." Zancen likita ya yi matukar tasiri a zuƙatansu. Aka ba Hajiya damar ganinsa, ta shiga, yana kwance idanunsa a rufe. Ba ta so ta mishi zancen da zai tayar da hankalinsa karo na biyu hakan yasa ta fita. Yaya Munir ya ce zai zauna abinda zasu bukata a ba direba ya kawo don haka duk suka dunguma zuwa motar Hilal don tafiya gida, yayyun banda harara ba abinda suke watsawa Ramlat a fakaice. Tana ji tana gani ta ƙara hawa motar mutumin da ta kira a maƙiyinta karo na biyu. Har suka isa gida ba wanda ke magana. Godiya sosai su Hajiya suka yi mishi kafin su fita, har sun soma tafiya ya kira Ramlat. Kaifafan idanun Hajiyar ce kawai ya dakatar da ita, ta juya ta isa wurinsa yayinda suka shige cikin gida. "Kiyi hakuri, a karo na ba adadi ina kara ba ki hakuri. Ban san irin son da kike yiwa shi wanda kika samu har kike ganin ya fi ni ba Ramlat, sai dai kowane irin so kike mishi, bai yi zaton za ki mance da ni haka da sauri ba. Na dauka soyayyarmu soyayya ce mai tsafta da muka soma a karon farko da muka fara sanya juna a idanu. Bansan me na miki ba kika tsaneni har haka, sai dai inada yaƙinin muddin muka yi aure ni Hilal sai na mantar dake batun kowane namiji da yardar Allah. Ina kara jaddadamaki ina sonki, ina miki kaunar da ban san adadinsa ba. Ba irinki ake samu a kyale ba Ramlat. In Sha Allah komai zai wuce, zan jure." Bai tsaya jin amsarta ba don yasan masu zafi ne, bai tsaye kallon fuskarta ba (dama tun soma maganar bai kalla ba), yasan ba zai ci karo da murmushinta mai tafiyar da damuwarsa ba. Motarsa ya shiga sai dai ya kasa tashinta, kallonta yake tana tsaye a inda ya bar ta, bayanta yake iya hange ba fuskar ba. A hankali kuma ya ga ta soma takawa ta shiga gidan. "Me na yiwa Ramlat? Ina da wani aibun ne?" Ya samu kansa da yin tambayar da ta tafi a iska don babu mai amsawa, kifa kansa ya yi saman sitiyari. Tun babu wanda ya san damuwarsa, tun yana kokarin dannewa har ta soma fitowa fili. Kullum kamar ana ƙaramasa sonta, har yau bai yarda ba ta sonsa ba. Asiri ko tsafi ba abu ne da ya yi amannar su na tasiri ba a koyaushe, sai dai haka kawai yake zargin sauyawarta da cewa asiri ne. Yana sonta, ba ya jin kuma zai iya rabuwa da ita. Zai jure dukkan kunci da tsananin da zai fuskanta daga gareta. Yasan muddin ya tunkaro gidansu a haka, babu ɓata lokaci Mahaifiyarsa za ta gano damuwar dake kwance saman fuskarsa, don haka ya

Chapter 9 of 58