Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fadin. "Gobe da safe ka zo muje gidan su yaronnan. Ina rantsuwa da Allah, muddin ina numfashi Ramlatu sai ta auri zaɓinta. Sai ta auri wanda ta ke so." Daga haka ya katse kiran, ya zauna ɗabas gefen gado. Bai san ya akai ya soma gani bibbiyu ba, sai ji ya yi ya kife zuwa ƙasa. *** Hajiya tana kuka ta ke magana a falon. "Kaicon mai taurin kai da bauɗaɗɗen hali irin naki. Kaicon ƴa da ba za ta yi biyayya da iyayenta ba. Ina jiyemaki makomar rayuwarki Ramlatu." Kowannensu kuka yake, Hajiya ta mike har hakan ya zaburar da Ramlat don a zatonta duka za ta sha, sai dai ta ga ta shige daki ta bar ta nan zaune. Ita kuwa Hajiya ba ta ga dalilin dukan ba, wanda ke jin magana kuma ya ke da gatan a fada ya ji ko a tursasa ya bi, shi ne suke da ikon idan bai ba su daga hannu su daka. Banda Ramlatu, ta nuna musu iyakarsu. Mijinta ta hango kwance a ƙasa rub da ciki. Hannu ta sanya a kai cike da matukar gigicewa ta buga salati iyaka ƙarfinta. A zabure Ramlat ta shigo, Hajiya tana jijjiga Abban tana kiran sunansa. "Kar ka mutu Khalid! Ba ita kadai ka haifa ba! Kar ta kashemana kai!" A can falo kuwa jin salatin Hajiya ya shigo da mata da ƴan samari (baƙin Daura) ƴan biki cikin falon Alhajin. Sai dai ba wanda ke da ikon ƙarasawa dakin Abban sai Zulaihat da ta nufi ciki da sauri. Idanun Rafee'ah ya wacce ta zauna dalilin jin wani murɗi da cikinta ke yi ya kai saman takardar da ke kan kujera, ta dauka tana karantawa, sai ta ji kamar an karawa tsohon cikinnata ƙaimi wurin murɗawar. Ta matse takardar da karfi tana rike cikin da salati. Daidai sadda aka fito da Abba, samarin suka tari Hajiya da Zulaihat suka rikeshi aka fita. "Ku dube ni!" Cewar Rafee'ah da ke murkususu  riƙe cikinta ɗan wata bakwai, ga hawaye caɓe-caɓe saman fuskarta. Ai tuni wasu cikin iyaye aka yi kanta aka taimaka ta mike, ga ciwo a jikinta, ga tunanin Abbansu da kuma wannan tashin hankali da bakin ciki da Ramlat ta jawomusu a wannan rana. Motar Abba har ta yi gaba, har lokacin ruwa ake ba ƙaƙƙautawa. Itama Rafee'ah motar kai yara makaranta aka ciro, daya daga cikin baƙin Daura ne, Dauda, direban tasi. Shi ya tuƙasu cike a Bus zuwa asibitin. Tana gefe tana kuka kamar ranta zai fita, ba wanda ya kara kallonta, duk wanda ma ya kalla ya tambayeta meke faruwa ba ta ko kallonsa balle ta amsa. Amrah ce ta nufi inda take ta ja hannunta suka shiga daki ta kulle kofar. Ta dubeta a gigice, idanun sun yi ja. Kasancewar Amrah farar fata ya sanya hatta da fuskar ta dauki ja na wacce ta ci kuka. "Me kika aikata?" Ramlat ga ɗago ta dubeta cikin sheshsheƙa. "Me ake zaton zan aikata don Allah Amrah? Me ake zaton zai faru da aure irin nawa? Ya sakeni. Ya sakeni saki ..." Bata kai ga ƙarasawa ba Amrah ta fidda hannu ta dauketa da lafiyayyan mari. Marin da ya hargitsata ya kuma sa ta cika da dumbin mamaki. Amrah ƙawa kuma Aminiya ita ta fidda hannu ta mareta? Abinda koda wasa ba ta zata ba, ya zo mata a hagunce. Kafin ta farfaɗo daga tunanin da ta faɗa na tuna ƙarfin alaƙarsu da Amrah din. Ta ji kaifafan kalamai na fitowa daga bakinta. "Wallahi ba ki da hali! Ba ki da hali! Na tsaneki! Haka kika zaɓarwa kanki? Haka kike da son kanki? To ki sani, tun kafin wani ya wulakantaki! Ke kika soma wulakanta kanki! Tun kafin wani ya ci zarafinki! Ke kika soma nuna ke din ba kowa bace ba ki da daraja da mutunci ko ƙanƙani! Ki yi kuka da kanki Ramla! Ki kuka da kanki bisa duk abinda zai biyo baya! Sai dai ki saka a ranki! Allah Madaukakin Sarki Shi ne Ya ce mu bi iyayenmu! Sun mana komai, sun kyautata mana. Ke kuma kin zaɓi ki saɓamusu saboda wani banzan Aliyu! Saboda wani shashasha da bai san ciwonki ba! Wallahi Aliyu ba ya sonki! Kema kuma ba sonsa kike ba! Hauka kike! Ni Amrah Abdullahi ki sani, a yau a wannan rana kuma, babu ni babu ke! Ba zan iya ƙawance da mai hali irinnaki ba. Ban yi sa'ar ƙawa ta gari ba mai daukar shawara. Yau idan Abba ya mutu saboda banzan son rai irinnaki, ki sani kina cikin masifa. Bani babu ke! Na tsaneki." Tana kaiwa nan ta bude kofar ta fice daga dakin a guje tana kuka. Ramlat ta zube a wurin tana kuka sosai har da sheshsheka. Sosai maganganun Amrah sun shigeta, kuka take kamar ranta zai fita. Mutuwar Abba da ta ambata shi ya fi komai tsayawa a ranta don haka ta mike a gigice ta fito. Matan da ke falo suna jimami suka dubeta. "Ke Ramla ina za ki?! Ke!" Fadin Yakumbo yar uwar Abba. Masu kwari suka bi bayanta dakyar ta yarda ta zauna ta jira su dawo gidan. Idan Abba ya mutu ba za ta yafewa kanta ba! Da gaskiyar Amrah, tana da son kanta da yawa. ***   Da gaggawa aka shigar da Abba ciki, itama Rafee'ah an miƙata Labour room don an tabbatar haihuwa ce ta tahomata kuma bakwaini.   Hajiya na zaune tana kuka har lokacin ba ta cewa kowa komai ba, Hajja ta zauna gefenta. Cikin fada take magana. "Wai menene ke faruwa Rabi? Bamu kai mu ji bane? Haba! Tun a mota nake tambaya an min shiru!" Baba Hajara diyar Hajja ta biyu ta caɓe. "Nima dai Hajja abinda ban gane ba kenan. Sai kuka ta ƙi magana. Ga Rafee'ah ma na naƙuda. Ki fadi meke faruwa ko hankulanmu zai kwanta." Zulaihat ta ƙaraso wurin rike da takardar sakin Ramlat da Rafee'ah ta damƙamata kafin a shige da ita daki. Ta dubesu tana kuka. "Sakin Ramlat fa aka yi. Ita ta sanya Hilal ya saketa. Wannan ne dalilin faduwar Abba, da kuma naƙudar Rafee'ah." "Wace Ramlatun aka saka?" Cewar Hajja, tambayar dake zuƙatan maza da matan gurin kenan saboda rudewa ma sun kasa gasƙata batun Zulaihat. To mene abin ɓoyon? Abinda komai ya riga ya bayyana, zubewar girma da bada kunyar da ake tsoro ya afku. Irin ABINDA AKE GUDU (Batool Mamman) ya riga ya faru. Don haka sai ta musu filla-filla yanda zasu gane. Sai ga mata na kuka da salati. "Ni dama na san ba inda dolen nan zai kaimu. Kamar na sani Rabi'atu na ce ki fadawa Khalid a fasa. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Wannan wane irin zamani muke ciki? Lokacin da aka mana auren bamu san mazajen ba ma, mu ce me?" Hajja ke wannan batun tana kuka. "Amm, don Allah Mama ku yi hakuri. Kun yi yawa a asibitin nan, ga marar lafiyarmu ba ya son hayaniya. Don Allah ku ragu, ko kuma ku yi shiru. Kuna damun sauran marasa lafiya su ma." Likita ke wannan jawabi a tausashe. Ya dubi Zulaihat don fuskarta kadaiya shaida sai ta Hajiyar. "Kina iya biyoni ofis." Ta amsa da toh tana share hawaye ta bishi a baya. Can kuwa Nos ta fito ta na fadan ba wanda ya tsaya wurin Rafee'ah gashinan ta haihu kuma ana bukatar kayan amfani. "Me ta haifa?" Har suna hada baki wurin tambaya. "An samu namiji. Itama kuma da sauki jikinnata." Suka sauke ajiyar zuciya, nan aka yiwa mijin Rafee'ah waya akan ya zo kuma ya taho da kaya da gaggawa, ta haihu. Abinda ya jefashi cikin ruɗu da mamaki kenan, an haifar masa bakwaini. *** Likita ya yi faɗa kwarai akan yanda aka bari jinin Abba ya hau sosai, ya kuma ce anan zai riƙe shi har sai ya warware. Zulaihat kuka kawai take. Ya kammala rubutun ya miƙa mata takarda. Har ta mike ta dawo. "Dr don Allah ko za ka kiramin Munir a waya." Likitansu ne, hakan yasa suka saba sosai da mutan gidan. Ya fiddo wayarsa ya dannawa Munir kira. Shi kuwa Munir dama tun sadda ya dinga kiran wayar Abban ya ji ba'a dauka, ya fito ya taho bai ko damu da ruwa ba. Kwanciyar hankalinsa daya, uayi tozali da Abban.   Ya na hanyar nufar gidan ne, kiran Dr Sunusi ya shigo. Da mamaki ya ɗaga, maimakon ya ji muryar Dr Sunusi sai ya ji ta Zulaihat. Ba shiri ya gangara gefen titi kirjinsa na bugu ya ɗaga. "Hello Baban Yasmin, Zulaihat ce." "Meke faruwa Zulaihat? Ina Abba? Ya kirani ya yimin wasu zantuka marasa dadin sauraro." Cikin kuka ta soma zayyane mishi dukkan abinda ke faruwa bayan fitar Dr daga dakin. Salati kawai ya ke, jiki na rawa ya katseta. "Ganinan zuwa Zulaihat, don Allah a ragu a asibitin. Ki ban Dr, kar ya bar kowa ya shiga wurin Abba yanzu." Ta amsa da to ta leka ta mikawa Dr Sunusi sannan ta yi gaba. Shi kuwa Munir ya jaddada wa Dr Sunusi cewa kar ya bar kowa ya shiga wurin Abba daga nan suka yi sallama ya sauya location zuwa asibitin. ***  _*Bayan Cudewar Awanni*_ Safiya ce, garin ya yi sanyi kuma ya yi luf-luf kamar a lokacin wani hadarin ne zai hadu ruwa ya ƙara sauka kamar yanda aka kwana ana yinsa. Kamar wacce laka ya fashewa a ciki, haka ta shiga taka barandar asibitin. Idan yaro zai yi mata kallo ɗaya, nan take zai ayyana a ransa cewa mahaukaciya ce. Ga duk mai hankali kuwa zai ga tsantsar tashin hankali da damuwa cike fal shimfide a saman fuskarta. "Mutuwa akai mata da alama." Ta tsinci muryar wasu mata a gefe, ba ta kallesu ba balle ta tofa. Ba kowa ta ke ganewa ba,ba kuma kowa take gani ba. Abbanta kawai take son sanyawa a idanu. Da shi ta kwana kuma ta tashi. Hijabin jikinta duk ya cukurkuɗe ya yi jirwaye na ruwan hawayen da ta dinga gogewa da shi. Silifas ne a kafarta na baƙin gidansu, ba ta san inda nata yake ba. Ta dai tuna da shi Hajja ta yi amfani wurin dukanta. Fuskarta yatsun Amrah ne kwance a samansu wadanda har yanzu basu baje ba.  Tana fashin sallah, wannan yasa ba ta kalli gabas ba balle fuskar ta ci darajar wanki. Ta dai tsarkake inda ya zamemata dole saboda kyankyami irin nata, ko ba komai kula da lafiyar jikinta ne. Ta shanye komai a awannin da suka biyo baya. Zagi, tsinuwa da ma duka, duk ta dauka daga dukkan wadanda acewarta sun kai su yi mata su. Ta ji ta dau komai idan har za'a bar ta ta ji da abinda ke cin ranta. Har ta iso dakin da Abba ke kwance tana tunani mai zurfi, ta gane dakin a dalilin hango Mijin Rafee'ah, Isma'il da ta yi zaune a saman kujera, gefensa Yaya Munir ne su na magana. Yaya Munir na kallonta tana kallonsa. _"Ban yarda ɗayanku ya taɓa lafiyarta ba, kar wanda ya tuhumeta akan abinda ta yi, ni da kaina zan auramata wanda take so. Na dauki laifina na yi mata auren dole kamar yanda ta ce."_ Ya tuna kalaman Abbannasu a jiya ga Hajiya, Zulaihat da kuma shi Yaya Munir din. Sai dai ya yiwa kansa alkawarin babu shi babu Ramlat. Don haka ya kauda kai kamar bai ganta ba. Isma'il ne ya tsayar da ita suka gaisa yana mata fadan ba ta kyauta ba, tsam Yaya Munir ya mike. "Muje ga Rafee'ah ko?" Ya katse Isma'il. Hakan yasa shima ya mike suka tafi. Ta bisu da kallo idanun taf da kwalla sannan ta murda kofa ta shiga dakin Abban da sallama. Babu kowa a ciki sai Abban dake kwance ya yi shiru idanunsa biyu. Ya juyo ya dubeta, ga mamakinta murmushi ya yi mata. Ta sunkuyar da kai ta ji saukar hawayen da take riƙewa a saman kuncinta. Hannu ya miko. "Zo nan Ramlatu." Tana tafiya kamar a iska tsabar ramar da ta yi ta zauna saman kujerar gefensa ta rike hannun sai kuka. "Abba don Allah ka yafemin. Abba na tsani kaina, na kasa rankwafar da zuciyata na yi maku biyayya. Abba ka yafemin na tuba. Na shirya zama da Hilal kamar yanda ku ke so. Ku ce ya maidani. Wallahi zan zauna." Murmushi Abba ya yi, ya shiga girgiza kai. "Kin ji nace ba zan ba ki Aliyu ba? Ko wani ne ya ce hakan? Ki yi shiru ki daina kuka, ni na yi laifi da na dage wurin yi miki aure da wanda bakya so. Ki yi hakuri ki yafemin kinji? Zan aura maki Aliyu cikin satinnan in sha Allahu. Yau zan koma gida ba zan ƙara kwana a asibitin nan ba. Idan har Khalid na raye, sai kin auri zaɓinki. Ki daina kukan. Na yafemaki duniya da lahira. Allah Ya yi maki albarka." Ya ƙarashe da rarrashi, ta kasa gane zantukan Abban suka dosa. Ta kasa gane dagaske yake maganar ko kuwa mai harshen damo ne? Don haka ta bi umarninsa ta share hawayen. Ya dinga jan ta da hira har ta yi dariya. Hankalinta ya ɗan kwanta. Amman maganar Abban ta shiga yawo a kwanyarta cike da rashin gamsuwa. Maimakon ma ta yi murna, sai ta shiga firgici da kuma faduwar gaba. Daga nan ta karasa dakin Rafee'ah, ba ta shiga ba, ta hango baby mai kyau dai, ta yi murmushi sannan ta koma ga Abban. *** Kwana biyu da sallamar Abba, ya sallami dukkan baƙi ƴan Daura, ya basu hakuri akan abinda Ramlatu ta yi. Daga nan ya tara iyalinsa ya tsawatar akan bai yarda ko maganar banza wani ya yiwa Ramlat ba. Abba da mahaifin Amrah, da ma wasu a ƴan uwa, suka dunguma har gidan su Hilal. Suka ba iyalinsa hakuri cike da nadamar abinda Ramlatun ta aikata don tuni sun ji abinda ta yi har ya saketa. Bai ɓoye wannan ba. Wannan ya ɗan sassauta ran iyayen Hilal, ko ba komai iyayen Ramlat sun nuna ba hannunsu. Basu nemi sulhun kome ba, koda sun nema iyayen Hilal sun yanke wannan alaƙar. Hatta Alhaji Aminu mahaifin Hilal wannan karon ya yi Allah wadai da irin Ramlatu. Toh Abban ma bai da ra'ayin komawarta. Washegari kuwa kamar yanda suka nemi iyayen Aliyu, sai gasunan sun zo. Ba ɓata lokaci Abba ya karbi sadakin ƴarsa. Nan aka daura auren Aliyu da Ramlat don duk wani bincike an yi ta hanyar Yaya Munir an kuma tabbatar daga Hilal har ita Ramlatun babu idda a kanta. "Ga sadakin aurenki Ramlatu, na auramaki Aliyu. Ina fatan wannan zai faranta ranki. Zai sa ki dawo da walwalarki. Ki kuma maido soyayyarmu a zuciyarki?" Ta ɗago ta dubi Abba tana hawaye. Abban murmushi yake har hakoransa tana hangowa. Ita ya kamata ta yi irin wannan kalar fara'ar, sai ya kasance ita ce mai kuka, Abban da mutan gidan na dariya. Hajiya ma sosai ta sakarmata fuska. "Ramlatu matar Aliyu. Allah Ya baku zaman lafiya." Wannan ne kalaman Hajiyar kafin ta fita zuwa asibiti wurin Rafee'ah duba lafiyarta. Ramlat ta shiga daki ta zauna, ta yiwa kudin da Abba ya damƙamata kuri da idanu, abin mamaki su dinma jiƙasu ta soma da hawayenta. Ranar da ya kyautu ta yi rawa da juyi, ranar da ya kyautu ta fi kowa farin ciki. Abin mamaki kuma ya sanyata, kukan ta shiga yi kuwa iyakar ƙarfinta, koda za'a shaƙeta ba za ta ce ga dalili ba. Ba ta da masaniyar cewa Mafarin kenan!!! ***   https://my.w.tt/iRW2CA35T9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 15) Kallo ɗaya za ka yi mishi ka hango farin ciki tsantsa da walwala marar misaltuwa a saman fuskarsa. Sigari ya sanya a bakinsa yana zuƙa lokaci daya yana fesarwa. Ihu da kurantawa shi kawai ke tashi daga bakin maza da matan wurin. "Cau cau Aliyu Angon Ramlat!" Fadin G Baba. Hakan sai ya kara tunzura Aliyu har sai da ya zuƙe kara biyu cikin ƙanƙanin lokaci kafin ya kwantar da kai yana kallonsu ƙasa-ƙasa yana doka murmushi. Ko ba komai yau burinsa ya cika. Ko ba komai ya mallaki abinda ya jima yana dakonsa. Ya na a jingine da kujera cikin club ɗin, yana kallon yanda ake rawa da rausaya mata da maza. Duk ana yi don tayashi farin cikin  samun cikar burinsa. Hannu ya zura a aljihu ya ciro bandir din dubu daya ya bude ya watsamusu. Aka hau kwasa ana ihu da kara korantashi. Abin na mishi dadi. Wayarsa dake saman tebur ya duba, kira ke shigowa ba kuma na kowa ba sai na Granny. Ya mike tsaye ya yi musu bankwana ya fice. Yau bai sha abin maye ba don ya fi son a yi komai cikin hayyacinsa ya gani. Bai daga kiran ba har sai da ya bude sabuwar karamar motarsa Honda wanda Abulle ta sanya aka siyamishi ya shiga. Ya soma tuki a nutse kafin ya dauki waya ya kira Granny. "Ina ka shiga wai? Ka zo mu tattauna game da lefen." Ya yi murmushi gami da kara  lumshe lumsassun idanunsa. "Ina hanya Kakus, gani nan tafe." Ya kashe kiran bayan ta mishi addu'ar zuwa lafiya. Ya kai duba ga agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa. Karfe tara da mintoci na dare. Buga sitayari ya yi gami da sakin ƴar ƙara da furta. "Yes!!" Cike da nishadi ya kara gudun motar gami da ware kiɗa. Har ya isa gidan bai kashe  kidan ba duk kuwa da hango iyayensa maza da ya yi zaune a saman tabarma ƙasan ƴar rumfa a farfajiyar gidan. Duk sadda irin hakan ta kasance, tattaunawa suke game da wani abun mai muhimmanci. Kallonsa suke har ya kashe motar ya fito zai nufi cikin gida ba tare da tunanin gaishesu ba. Idan da sabo ya ci ma su saba. Malam Abdussalam cike da takaicin halin ɗannasa ya sunkuyar da kai. "Kai! Aliyu?!" Fadin Kawu AbdulRashid wanda ke bi wa Malam Abdussalam a haihuwa. Aliyu ya maido akalar tafiyar garesu. "Gani. Sannunku." Yanda ya gaishesu kerere ya fi komai baƙanta ransu. Daƙuwa Justice ya wurga mishi. "Ungo wannan! Yanzu kai tsabar iskanci da rashin kunya mu kake yiwa gaisuwa irin na ƴan iska?" Nan ya gane kurensa, sai ya durkusa yana shafar suma. Dama ya riga yasan har gobe dattijon haushin sakin da ya yiwa ɗiyarsa yake. Yana cikin farin ciki yau, don haka bai shirya wani abun ya ɓata ransa ba. "Ku yi hakuri." Ya ce kai tsaye cikin tausasa murya. Banda warin taba ba abinda ke tashi a jikinsa. Sun gaji da magana daya akansa. "Allah Ya shiryeka Aliyu, Yasa wataran ka sauya." Cewar Kawu AbdulRashid ransa na zafi. Nan Justice ya shiga magana. "Yarinyar nan mun ji labarin abinda ta aikata, kuma ta yi a bakin duniya duk don ta aureka. Ta yi laifi, ta yi kuskure. Mahaifinta ya damƙa amanarta gareka, da kunnenka ka ji kalamansa." Aliyu ya gyada kai cikin son tuna abinda Abban ya furta gareshi ranar da ya karbi sadakin Ramlat a hannun magabatansa. *"Ramlatu amana ce Allah Ya ba ni, yanzu kuma amanar za ta koma kanka. Ban ce lallai sai ka kyautata mata ba, ban kuma ce lallai sai ka yi mata adalci a rayuwa ba, duk wannan hakki ne da ya rataya a wuyanka ko ban faɗa ba. Ka ji tsoron Allah a lamuranka, kar ka manta zai tambayeka duk wani abu da ka aikata a rayuwa."* Bai mantawa a lokacin murmushi ya yi kawai. *'Ba dai haka ka so ba Abbanmu. Sai dai ba za ka hana abinda Allah Ya yi ba.'* Nan take ya ce a cikin ransa. "Don ubanka ina magana kake dariya? Wane raini kenan?" Kalaman Justice suka katse tunaninsa, ya ankara da murmushin da yake zabgawa har haƙoransa na bayyana. "Ayi hakuri." Ya kara fadi. Kowanne ya tofa albarkacin bakinsa kan ya riƙe amanar yarinya, daga nan ya yi musu godiya ya mike da uzurin Abulle na nemansa. Mahaifinsa ya bishi da kallo gami da addu'ar shiriya. Yaran ka haifa ba ka isa ka saita halayyarsu ba. Kiciɓus suka yi, ba haka ta so ba. So ta yi da sauri ta bar dakin Abulle kafin ya cimmata. Shigarta dakin Abulle don kai mata goron da ta dauko a dakin Daddynta. Jin Abulle na mitar Aliyun ya zaunar da ita zaman jiransa ya sa ta katse hirartasu ta yi mata sallama ta fito tana sauri ta bar bangarennata. Sai dai kuma ba yanda ta iya tunda gashinan gabanta. Ta daure ta haɗiye komai dake tasomata. "Ina wuni Yaya Aliyu." Bai san yana da kunya ba sai a yanzun, ya kauda kai daga kallonta. "Lafiya. Ya kike?" Ba tare da ta amsa ba ta wuce da sauri ta yi hanyar kofar sashinsu. Bayanta ya bi da kallo, Muhibbat kenan. Ya sa kai dakin Abulle. Salati ta shiga yi kafin ta hau yi mishi fadan sigari da ya sha. Taɓe baki ya yi, ya mance da hakan shaf bai jefa alawa bakinsa ba, bai kuma fesa turare ya tsaye a waje na mintoci ba kafin ya hau mota ya tuƙo. Ya mance rabon da ya shigo gidan yana warin taba. "Wai ni don Allah ki bar kunnena ya huta. Shikenan don kin ji warin abu a jikina sai ya kasance sha na yi? Ko a addini an hana irin wannan yanke hukuncin. Idan ina sha tsawon lokacin nan ba za ki sani ba sai yanzu? Mtsw, Abokina ne ya sha, shi na ziyarta shi ne ƙamshin ya biyoni." Hakan da ya faɗa sai kuma ta gyara zama ta hau jijjiga kai. "Kuma fa hakane. To ka kara kiyayewa dai. Raɓar abokai ɓata gari ba naka bane. Na soke abotar. Yanzu dai ya batun lefe? Mahaifinka cewa ya yi na farko an maka, na biyu kai za ka yi. Duk da haka Alƙali da sauran kawunnanka sun ɗan ba ka wani abin ka haɗa ka yi." Murmushi ya yi. "Lefen Baby ina son ya fi na kowa. Ina son a bude a kirashi da lefe. Masu yi mata habaici da zagi a kan aurena su daina. Don haka da kaina naji zan hada abina koda ace hakan na nufin karyewar jarina." Baki sakaka Abulle ta saki tana kallonsa kafin ta magantu. "Um um dai Zakina, ba za'a yi haka ba. Ƴar dangi ma ba ka ce hakan ba sai akan bare? Ina rabaka fa." Ya yi dariya. "Abulle tawa ni kadai,  Baby ai ta isa na yi mata komai. Koda kuwa komai nawan zai ƙare a kanta." Ta taɓe baki. "Fadi dai sunanta na zahiri, shi zan fi fahimta. Ramlatu ko? To naji, ungo nan." Ta daga filo ta fiddo damin kudi ta mikamasa. Ya karba ya zura a aljihu. "Wai nikam me zai hana ka mayar da yarinyarnan ɗakinta ne? Naga dai tsiraicinka yafi rigar aro ta mutane." Miƙewa ya yi tsam! "Sai da safe Kakus. Kwanta ki yi bacci abinki. Nima na tafi nawa lissafin." "Ai fa, ba dama a dauko magana sai ka kauce. Toh har gobe ban ga wata ɗiya da za ka kawo na ji ina sonta a raina ba irin Muhibba." Daga kafada ya yi alamar ke ta shafa ba kuma tare da ya komai ba ya fice daga dakin. Ko a ransa bai ƙara tada zancen Muhibbat din ba. ***   "Kai Allah Ya rayamana mai sunan Abba." Fadin Zulaihat kenan cikin waya tana murmushi ranta fari ƙal. Ramlat na daga kicin tana dahuwar indomie ta ji wannan kalamin. Anan ta fahimci sunan Abba ɗan Rafee'ah ya ci. Kwalla suka tarar mata, a yanzu ba ta rabo da hakan. Tunda aka daura aurenta da Aliyu, komai ya daina yi mata dadi. Ba kuma don ba ta sonsa ba, har gobe tana jinsa a ranta. Wuyarta ya kira wayarta ko kuma ta kirashi, za ka ganta cikin farin ciki da annashuwa. Kalamansa masu taushi da dadi, wanda ke nuni da nutsuwa da kuma cikar hankali, sun fi komai yi mata dadi a ranta. Sai dai ba ta nufin ta rabu da yan uwanta a dalilinsa, duk suna amsamata idan ta yi magana, sai dai irin amsawar da gwamma kar su yi. Babu fara'a babu sakin fuska. Sama-sama suke amsawa kamar ba sa so.  An kwaso kayanta kaf a gidan Hilal, a daren jiya ya zo har gidan ya riski Abba a falonsa. Sun jima suna magana sannan ya tafi. A hirar Zulaihat din da Hajiya ta ke jin cewa hakuri ya ba shi. Hakuri bisa sakin ƴarsa da ya yi. "Ke wane rashin hankali ne za ki kunna gas har abu ya ƙone haka? Gobara kike son

Chapter 12 of 58