Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Yaushe sabo mai karfi ya shigeku har haka?" Ta turo baki kadan. "Dan uwana ne fa Hajiya." Abba dake karanta jarida ya ɗago kai yana dariya. "To kinji amsarki ai. Kwana nawa ne za ta tattara ta bar miki gidan ke da autarki? Ki bar ta ta sada zumunci, ta samu lada biyu. Na juma'a da kuma zumuncin." Ramlat ta sauke ajiyar zuciya, dama tana sane ta tambaya a gaban Abban don tasan zai goyi bayanta. Tun safe Hajiyar ke cin magani tana mitar wai ta sauya daga Ramlatun da ta sani akan ta shigo tana waya ta yi shiru har ta fita daga dakin. Wannan ne kuma ya tabbatar da zargin Hajiyar cewa akwai saurayin da ke huremata kunne a yanzu. Koda Hilal bai ce komai ba, ita ta lura ɗiyar ta bar rawar kafa a kansa da komai ma. "Ban wayarki. Idan kin dawo kya karɓa." Maganar Hajiyar ya daskarar da ruwan jikinta, ta bude baki za ta yi magana sai dai tuni miyan bakinta ya daskare jin muryar Abba na magana cikin nuni da goyon baya. "Ba ta idan har za ki tafin. Tunda gidan Yayanki ne ai ba damuwa. Zuwan dai ake kokarin hanaki." Ba haka ta so ba don dama da biyu take son fitar, Aliyu na son ganinta ko ta wane hali don su tattauna su samarwa kansu mafita sai dai kuma da alama karyarsu ta kare muddin wayarta ta shiga hannun Hajiya. Ba ta da zaɓin da ya wuce ta fiddo wayar daga jaka ta miƙa wa Hajiyar. _Idan lokacin bayyana soyayyarmu bai yi ba har yanzu, sai yaushe? Sai yaushe ne za'a san abinda muke ta ɓoyansa? A soyayya ba'a shakka balle tsoro. Idan aka yi hakan ba'a yi mata adalci ba, ba'a fitar da hakkinta ba._ Wadannan kalaman Aliyu ne, nan take ta ji wani kwarin gwuiwa. Ƙarƙari Hajiya ta bincika wayarta ta kuma bibiya shiga da ficen kiranta. To me ta aikata? Ai ba haramtacciyar soyayya ba ce. 'Nema cikin nema?' Ta ture tunanin ta hanyar yi musu sallama ta fita, Abba ya bita da kyakkyawar addu'a yayinda hankalin Hajiya ya koma ga wayar ta yi mishi ƙuri kamar mai jiran amsa daga cikinta. "Menene wai Rabi'atul Adawiyya? Meke damarmin ke da zuciyarki? Kwanakin nan ina lura da tsaurin da kike ƙara yi game da yarinyar nan. Ta yi wani abu ne?" Hajiya ta yi shiru tana dan kallonsa, ta fi kowa sanin halin mijinta, yana da sauki amma idan ranshi ya ɓaci babu kyau. Bai fiye zargi ba kamar yanda bai fiye daukar magana ba idan har ba shi ya ganewa idanunsa ba ko kuma yana da hujja. Tasan idan ta furta wani abin bisa zargin zai iya yiwuwa nata ne zai yi wari don haka ta ɗan murmusa. "Ba komai Abban yara, tunaninka ne kawai ya ba ka hakan. Ramar da take yi ne kawai bana so, a kanta aka fara aure?" Ya riko hannun Hajiya yana murmushi. "Kar ki damu, ko kin manta ban da auren shirin zana jarrabawa ta ke? Na dan lokaci ne In Sha Allah. Ko kin manta kalar naki zullumin dab da aurenmu?" Da sigar wasa ta harareshi suka yi dariya gami da yiwa Ramlat din kyakkyawar addu'a. *** Cike da fara'a Anti Bilkisu ta tarbeta. "Lale marhabin da Amaryarmu. Yau an tuna da ni?" Ramlat ta kama hannun Maama babbar ƴar Yaya Munir suka zauna saman kujera. Tana dariya "Kai Anti, ko wata fa ban yi ba rabona da gidannan." Taɓe baki Anti Bilkisu ta yi tana dan murmushi. "Ai shikenan, nasan da mutuniyata ce har da kayan kwananta zan ganta. Kin dai wanke kanki tunda kin zo. Yau na huta da shiga kicin." Dariya ta yi kawai sanin halinta, wato dai tana nufin A'isha don sun fi ɗasawa, dama murnar da take na zuwannata kusan da biyu ne. Wata irin mace ce mai son jiki da ba ta son aiki, burinta kawai a yi mata, wasu lokutan akwai ta da shan ƙamshi da kuma sakarwa mutum hidima duk sadda ya kai mata ziyara, wannan ta sa ba ta fiye zuwan ba. Da ace ta san ma dalilin zuwannata da sai ta ji kamar ta shaƙeta. "Mutuminki kuwa jiya kusan wuni ya yi a gidannan, kinsan fa ni ya damƙawa haɗa lefe don haka ki min biyayya idan kina son ganin tsala-tsalan kaya." Tsaki ta yi wanda ba ta san ma ya fito fili ba, da mamaki Bilkisu ta dubeta. "Tsaki ki ka yi?" Sai ta ɗan basar. "Wayata na tuna na bari a gida, kuma ina son yin waya. Don Allah ban aron ta ki." "Au, toh ki gama wayar a karshe ki ce ya turon kati don nasan ƙararwa za ku yi." Ta ƙarashe tana mai sanya kai ta fice daga falon zuwa ɗaki. Da sauri Ramlat ta mike ta nufi kicin, lambobin da suka riga suka zama tamkar lazimi a wurinta shi ta shiga rubutawa kafin ta danna kira. Sai safa da marwa take yi a kicin din har kiran ya shiga. "Assalamu alaikum." Ta tsinci muryar mace, muryar da ba ta yi kama da ta Muhibbat ba don akwai sadda ta taɓa kiran Aliyun, ta daga ta ce ba ya kusa. Ranar ta tabbatar sun kusa yin kaca-kaca da Aliyu don har rantsuwa ya yi mata a kan idan tana so ma zai sauwakewa Muhibbat duk a dalilin kishin da ta motsamata. "Hello." Aka kara fada daga can bangaren sai dai ta kasa magana. Tana shirin katse kiran cike da faduwar gaba ta tsinci muryar macen. "Kanwarsa ce Habiba, Yaya Aliyun yana ciki wurin likita su na magana." Da wani irin matsanancin tsoro ta watsamata tambaya kamar a tsawance. "Meya sameshi?! Wane asibitin ne?" Habiba sai da ta ɗan yi shiru kafin ta yi magana cikin rashin wayo. "Anti Muhibbat ce ta yi ɓari, ya bar wayar a dakin ne, idan ya dawo zan fadamasa kin kira." Da sauri ta katse kiran ta kuma goge lambar daga wayar. Tasan ba ta son Muhibbat, ba kuma tsana ba, a'a, kishinta take. Sai dai fitar cikin ya zo mata a bazata, ba ta san sadda ta shiga fitar da hawaye ba, ta ajiye wayar a gefe ta hau fiddo kayan girki jikinta a sanyaye. Ba ta taɓa jin tausayin Muhibbat din ba sai a wannan rana.   Tana cikin gyara kayan miya ta tuna ba ta ma tambayi Antin abinda za'a dora ba, tana niyyar fita ne kuma ta ji wayar ta dauki ƙara, jiki a sanyaye ta karasa ta daga, lambar Aliyun ne. "Ki yi hakuri, waccan ƴar rawar kan ce ta ɗaga. Ta fadamaki muna asibiti ko? Kar ki damu fa zan zo din. A ina za mu hadu?" Ita kuwa wane irin rashin adalci ne wannan da zai sa ta nemi ganinsa a yau duk da tashin hankalin da matarsa ke ciki yanzu? Ko ba komai a yau Muhibbat ta cancanci duk wata alfarma. Don haka ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta shiga girgiza kai kamar yana gabanta. "Ka yi hakuri, nima ce maka zan yi Hajiya ta karɓi wayata har sai na koma gida sannan za ta maidomin. Yanzu haka ina gidan Yaya Munir, wannan wayar Anti Bilkisu ce." "Kenan ba zamu hadu ba?" "Ka yi hakuri don Allah Sweet Aliy, a yau Muhibbat na bukatar kulawarka. Ka ce ina mata sannu. Zuwa gobe zan san yanda za'a yi mu hadu ko bayan tashi daga makaranta ne." "Yau ita ta samu wannan alfarmar a wurin sarauniyar masu kishi?" Ya fadi cike da zolaya yana ƴar dariya. Murmushi kawai ta yi mai sauti. "Ai ina tunanin gida zasu wuce da ita har sai ta samu lafiya. Naga yayyunnata sai wani kallo suke watsamin kamar ni na janyo zubewar cikin. Mtsw, ita kanta In-law ba don darajar Granny ba sai na fadamata maganar da za ta hanata bacci." Ta gane In Law din da yake nufi, wato Mama mahaifiyar Muhibbat, a duniya ya sha fadamata ya tsani matar saboda ko kallo bai isheta ba har gobe. Idan ma ya gaidata amsawar kamar mai taunar maɗaci haka ake yinta.      "Allah Ya bata lafiya." Ta furta cike da tausayi. "Ke na yi wani karambanin. Wayarki na soma kira kafin wannan. Har kuma saƙo na aika da ban ji kin ɗauka ba." Ta fiddo ido waje game da riƙe kirji. "Dagaske?" "Yes, amma ya naji kamar kin razana? Mene a ciki? Mene don Hajiya ta san da zamana? Ko kina tunanin lokaci bai ba da zamu bayyana abinda ke zukatanmu? Saboda Allah na gaji da wannan ɓoyon!" Ta ɗan sauke ajiyar zuciya. "Me ka rubuta a sauƙon toh?" "Idan kin koma gidan kya gani. Sai anjima." Ya katse kiran, nan da nan hankalinta ya tashi har garin saurin ta kirashi, kiran Yaya Munir ya shigo ta katse. Sai da ya kusan katsewa sannan ya daga. "Me za ki cemin kuma?" Ta marairaice. "Ka yi hakuri. Wallahi nima yanzu bana tsoron kwan ya fashe kowa ya ji. Kawai dai na tambaya don na sani, amma ka yi hakuri." Sai da ta kwashi mintuna uku tana bada hakuri, karshe ya hakura ya shiga karfafamata gwuiwa akan kar ta kusa ta ji shakkar komai akan abinda yake ƴancinta. Ya na kara nunamata muddin ta bari ta auri mijin da ba ta so za ta tafka kuskure. Ita kuwa ƙara hawa take gami da hango gaskiyar hakan. Tana ji kira na faman shigowa ta ƙi maida hankali a kai, sai da aka soma warning na karewar kati sannan ta tuna ita ta kira suka yi sallama bayan ya dorata kan hanyar da za ta bi ta fidda abinda ke ranta idan Hajiya ta mata zancensa. Ba tare da ɓata lokaci ba ta goge dukkan shiga da fitar da lambarsa ta yi a wayar. Hamdala ta yi kafin ta fita ta kaiwa Antin wayar. "Me zan dafa?" Ta katse Anti Bilkisun dake kokarin daga wayar mijinta, cikin maida hankali ga wayar a gaggauce ta amsamata. "Duk abinda kike so ki dafa kawai. Hello." Ta ƙarashe da daga wayar Munir. Cikin sauri Ramlat ta yi gaba tana ji Anti Bilkin na ba shi hakuri da cewa ba ita ke amfani da wayar ba, can kuma ta ji tsakinta da masifa. Taɓe baki Ramlat ta yi don ta san kaɗan daga aikinta kenan. Ko a jikinta don tana da tabbacin zai wahala Yaya Munir ya isketa cikin gidan. Ai kuwa ta ci sa'a don tana kammala girka shinkafa da miya, suka ci. Ba ta ko biyewa mitar Anti Bilkin ba na ta karar mata da kudin kira kuma ta hadata faɗa da miji, ta tattara ana la'asar ta yi gaggawar barin gidan cike da kwarin gwuiwa ta doshi gidansu don kuwa tana ji daga zuciya da gangar jikinta, yanzun tana da abin faɗa, tana kuma da abin kare kanta. Ta gaji da ɓuyar. ***    "Gida zan tafi da ita, ba zan bari ta koma gidansa a wannan halin ba. Ba kuma zan bari kakarku ta ci gaba da juyamin yarana ba son ranta. Dole wannan karon a yiwa abin tufka." Fadin Mama tana huci cike da takaicin halin da Muhibbat ke ciki. Duk wannan karfin ikon tana yi ne bayan tafiyar Abule gida don a farko Abule ta kasa ta tsare cewa kafarta kafar Muhibbat din, ita za ta kula da ita, acewarta ta ga jiya kuma ta ga yau, don haka sai dai ta koyar da wankan jego. Dakyar su Justice suka lallaɓata ta bar asibitin.   Ta zubawa mahaifiyarta idanu tana mai jin hawaye na sauka bisa kuncinta. Sosai ta goyi bayan hakan, ta ji ta kuma gani za ta koma gidan iyayenta. Komawar da za ta zama na har abada. Wannan na nufin alaƙarta da Aliyu ta ƙare. Lumshe ido ta yi bayan ta share hawaye ta yi shiru kamar mai bacci tana ci gaba da sauraron yanda yayyunta maza da kuma Mamar suke fadin albarkacin bakinsu. Don babu wanda bai taɓa ganin cin kashin da Aliyu ke mata ba, musamman mazan da suka fi kowa sanin har gobe bai bar shaye-shaye ba.    Ta tuno yanda komai ya faru har ya yi sanadin faduwarta da kuma suma.     _Tana zaune a falo ta zubawa talabijin ido sai dai rabin hankalin ya tafi ga tunani, cikin wannan halin ta ji bugun ƙofa kamar za'a ɓalla. Da hanzari ta mike ta fito tsakar gidan, shakka babu bugun ne. Wannan yasa ta tuna bai fita da mashin dinsa ba, asalima mashin din kwana biyu ta bar ganinsa, ta kuma ji yana waya yana kiran siyarwa zai yi ya siya wani._    _Hijab ta zura gami da daukar mukullin gidan jiki na rawa ta nufi kofar a ranta tana mamakin abinda ya hanashi daukar nasa mukullan. Kai tsaye ta bude gami da kaucewa ganin mutum ya shigo a hargitse kuma yana tangaɗi. Ji ta yi cikinta ya yi wani irin juyawa, tabbas yana sha, amman duk ranar da ya yi niyyar sha zai umarceta da fita daga dakinsa ya kulle, takan sa kunne ta ji yana tamɓelansa har bacci ya kwashe shi. Kusan rabin mayen a kiran sunan Ramlat ko kuma Baby zai ƙare sai kuwa zage-zage._   _"Ki rufe ƙofar kin tsaya kina kallona kamar farin wata."_ _Ya yi furucin da muryar ƴan maye. Jiki na rawa ta rufe suka koma ciki tana ambaton Allah a'a zuciya. Abinda kawai take tunani bai wuce na kasancewar mashayi uban ɗan cikinta ba, ta shafi cikin da tun da ya murda bai saki ba tana kuka sosai. A haka ta iskeshi ta zube a saman dinning table yana bude kulolin abinci gami da watsar da murafan a tsakar falon. Ba don plastic bane da ya fasamata._     _"Ke, ban hanaki yimin tuwo a gidannan ba?"_ _Ta share hawaye, ya za ta yi? Abinda ke cikinta shi yake da muradi, ta kasa cin komai tun safe. Ganin kuma sun jima ba su ci bane ya sanya ta girkawa._ _"Ka yi hakuri."_ _Miƙewa ya yi ya ƙaraso inda ta ke, ba zato ta ji ya ɗauketa da mari, abinda tun da take za ta iya cewa ba'a taɓa marinta ba da girmanta. Wannan ta sanya ta yin baya a gigice, ba kuma zato ta bugu da bangon dake gefen 3 steps na hawa dinning din wanda ya yi sanadin gocewarta ta fadi akan cikin da ko fitowa bai yi ba. Ba shiri ta saki wani mugun ƙara gami da ambaton Allah, a hankali ta daina motsi. Shi kuwa ya nuna ta da yatsa._ _Tsabar raini ya shiga tsakaninmu shi ne za ki kwanta bacci ina magana? To don uwar ubanki ki yi ta baccin mana! Aikin banza!"_ *** Ta ƙara runtse ido, tabbas ta ji wannan kalamin can tsakar kanta kuma kamar a mafarki, koda ta farka a gadon asibiti ta ganta Abulle a gefanta tana sharar hawaye da surutan kada Allah Ya sa ta mutu ba ta ga yaran Aliyu da Muhibbat din ba. Ta kudurta wannan buri na Abulle ba zai samu ba da yardar Allah, ta hakura da Aliyu koda sonsa zai zama ajalinta. Ta ba shi damar auren wacce duk yake so. Ita kam karatunta da yace ba ya so shi za ta koma yanzun. Bangaren iyaye sun dauka a karon kanta ta ce ba za ta koma makaranta ba, ita da Aliyun ne kaɗai suka san sirrin rashin komawarta. Duk don ya kuntata mata ya ce ba za ta koma ba.   Tana ji yayyunnata suka fita a dakin sakamakon sallamar su Amarya da sauran mutanen gidan.   *** Aliyu na tsaye a farfajiyar asibitin, shigowarsa kenan. Ko kallonsa ba su yi ba, shi kuwa ya bisu da banzan kallo da harara, yana tafe yana tunanin me ya yi mata? Daki-daki ya tuno dukkan yanda aka yi. _Yana tangaɗi ya kife saman kujera bacci ya yi awon gaba da shi bayan ya yi magaginsa ya gama. Bai farka ba sai da sanyin asuba ya ratso falon. Cikin mamaki ya tashi gami da dafe kansa dake ɗan sarawa. A hankali ya shiga tariyo abinda ya faru daki-daki, shi dai ya san sun siya kayan maye da abokansa. Anan motar abokinnasa suka sha banda G Baba wanda ke tuƙi yana musu dariyar rashin hakurinsu na ƙarasawa gida. Duk cikinsu shi ɗaya ne ya yi aure banda su da ke kokarin hada takardun Degree. Bai manta sadda suka kawo shi gida ba suka yi gaba, bai kuma yi kasa a gwuiwa ba wajen budurin da suka yi da Muhibbat. Da hanzari ya mike ya nufi hanyar ɗakinta, ba ta nan, banɗaki ma haka. Ya fito da niyyar nufar nashi dakin ya hango mutum kwance a hanyar wurin dinning table. Jiki na rawa ya karasa, ba karamin kaduwa ya yi na ganin jini ba. Kai tsaye ya kira family doctor din su Muhibbat din da ma jama'ar gidan. Ba ɓata lokaci ya mishi bayanin halin da take ciki, sanin tana da ciki ya sanya shi bada umarnin kawo ta asibiti. A gigice ya fita da zummar kwankwasawa makwafcinsa, ya ci sa'a ya fito don zuwa Masallaci. Lurwan ya dubeshi._ _"Lafiya kuwa Aliyu? Meyafaru?"_ _"Muhibbat ba lafiya, taimaka ka kaimu asibiti nan kusa ne don Allah."_ _Ba tare da ɓata lokaci ba suka je asibitin aka karɓeta suka wuce masallacin asibitin suka yi sallah, likita ya tabbatar da fitar cikinta._ "Sai kuma shikenan a dinga yi min kallon mai laifi? Mtsw" Ya ƙarashe da tsaki don shi dai yasan da ace a hayyacinsa ne ba zai yi wannan gangancin ba. To tunda ta faru ta ƙare kuma shikenan. A ranar aka sallameta bayan an tabbatar babu wata matsala, Mama ta tattara diyarta suka koma gida. Ita kanta ta ji dadi da ta ji Muhibbat na batun a raba aurensu da Aliyun. Ranar da take jira kenan. ***    Da sallama ta shiga gidan, ta yiwa Hajiya sannu da zuwa, ko arzikin kallo ba ta samu ba. Cikin sauri ta fice dakinsu, sai dai tana shiga ta ji an rufe kofar, da hanzari ta waiga. Hajiya ce tsaye da wayarta a hannu, ta ƙaraso tana dubanta. "Zauna magana zamu yi." Ba musu ta zauna a ƙasa ta sadda kai.   "Banda Hilal, akwai wani da kike kulawa ne?" Ta kalli uwar sai kuma ta sadda kai. Jin ba za ta yi magana ba yasa Hajiyar kara magana. "Na tambayeki ba don ban riga da na sani ba, a'a, ina so ne da bakinki inji kin fada. Idan akwai ya sunansa? Kuma tun yaushe ku ke tare?" Ta runtse ido tana mai jin ko'ina a jikinta na amsar kuwwar Aliyu, gwara kam a yi ta ta ƙare. "Sunansa Aliyu."I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/RjJi0Rs2J9 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! A madadina da ƴan rof. Ina kara mika sakon gaisuwata ga Husna Yarbaiwa bisa rasuwar mijinta. Allah Ya mishi Rahma, Yasa aljanna makomarsa. Allah Ya raya yaransu.😭😭👏🏿 11)   Wani murmushi na bakin ciki da takaici Hajiya ta yi. "Shi dai wanda ke karamaki ƙaimi wurin ganin kin bijiremana? Kin saɓa umarninmu? Kin ci amanar mutumin da ya yi dakon jiranki? Kina cikin hayyacinki kuwa?" Daga kalaman Hajiya ta fahimci cewa r bincike ta mata a wayar. Ta ɗan turɓune fuska yayinda idanunta suka cicciko da kwalla. "Wallahi Hajiya ina son shi. Kuma shi nake son au..." Buge bakin da Hajiyar ta mata ne ya dakatar da ita lokaci guda hawaye suka shiga kwaranyomata. "Kin isa?! Har kin isa kin kai ki bude baki a gabana ki ce wanin Hilal kike so?! Innalillahi wa inna ilaihir ra'ajiun! Na shiga uku ni Rabi'atu! Ashe zan ga wannan rana? Ke Ramlatu, ba ki isa ba! Nace ba ki isa ba don uwarki! Babu wanda zai hana aurennan! Wato kin raina mu? Kin raina mahaifinki! Uban wa ya ce ki ce kina son Hilal ki kuma amince da aurensa?!" Hajiya ta ci gaba da fada, yi take tana ƙarawa ita kuwa Ramlat sai kuka, duk abinda Hajiyar ke fadi ji take ba abinda zai sa ta fasa son Aliyu.  Tashin hankalinta kawai ɓacin ran Hajiyar, banda haka ba wani abu. Hajiya ta gama faɗan sai kuma ta hau nasiha da nunamata kuskuren yin nema cikin nema da kuma hanyar da ta dauko wanda ba zai ɓille ba. Ita kam shiru kawai ta yi ba don tana aminta ba. Ba don kuma za ta sauya ra'ayi ba, asalima ji take kamar ana bude zuciyarta ana ƙaramata soyayyar Aliyunta. "Kiyi hakuri Hajiya." Ta fadi tana riko zaninta ganin ta mike a fusace za ta fice kuma babu niyyar za ta ba ta wayar. Kallonta Hajiyar ta yi, ita ta haifi Ramlat don haka ta san kafiya da taurin kai irinnata zai yi wuya lokaci daya ta saduda. Wannan kaɗai ya tashi hankalinta ganin cewa dagaske yanzun ba ta son Hilal, kuma dole ta aureshi. "Hakuri daya ki cire yaron daga ranki. Don waya zan ba ki amman sai kin kammala jarrabawa. Ba abinda zai sa a fasa aurenki da Hilal, don haka ki bar ma mafarkin hakan." Daga nan ta sanya kai ta fice. Kukan Ramlat abu biyu ne, kwace wayarta da kuma batun auren Hilal da Hajiyar ke jaddadamata duk kuwa da cewa ta san ba ta sonsa. Anan ta gane shirun ba zai mata amfani ba, kawaici da kauda kai ba zasu ƙareta da komai ba face tsananin bakin ciki da kuma nadama. Za ta cutar da kanta kamar yanda Aliyu ya faɗi muddin ba za ta fito fili ta nuna ta sauya ra'ayi ba. Ranar baccinta ya kasance rabi da rabi, duk juyi Aliyu take tunani, sanin da ta yi baccinsa ragagge ne idan bai ji muryarta ba. Sai kusan Asuba sannan bacci ya yi awon gaba da ita. ***   Ranakun da suka biyo bayan su za ta ce ba mai dadi bane sam a wurinta don kuwa Hajiya ta sanyamata takunkumi akan waya. Ba tare da sanin cewa tun a satin da hakan ta faru ta hadu da Aliyu a gidan su Amrah ya kuma cika alƙawarin kawomata karamar waya yanda za su dinga magana a ɓoye ba tare da ta bari a gida an san tana da wayar ba. Nutsuwa da maida hankali ga jarrabawarsu ta Waec da ta yi har suka kammala  ya sanya Hajiya ganin kamar ta fara mancewa da babin Aliyun.    Don ta Hilal suna hira a wayar Hajiyar bai kuma damu da jin cewa an kwace wayarta ba. Haka kawai hankalinsa ya kwanta da hakan. Ganin lokacin suna cikin shirin jarrabawar Neco ya sanyashi dauke kafa daga gidansu sai dai ta wayar, shi ɗin ma ba koyaushe ba dalilin yana dan jin nauyin Hajiyar.    ***    A gefen Aliyu har sannan Muhibbat ba ta dawo ba don kuwa sosai ta tayar da bore akan ta gama zama da Aliyun. Iyayenta ba wanda bai ba ta goyon baya ba, Abulle ce ta yi tsalle ta dire akan babu mai raba auren. Sai da Muhibbat ta yi wata biyu cif a gida sannan Abulle ta taka har bangaren Justice da zummar maidata. Ta kuwa ce sai dai takardarta. "Ke Hibbatu, kar fa kiga ina lallaɓaki don ina sonki, ba ki isa ki kashe sunnar ma'aiki ba. Aure abin wasa ne? Ko kin manta yanda kike kwana kina kuka akan son Zakina?" Hawaye ta share tana kallon Abulle. "Bana sonsa, yanzu bana kaunarsa, ba zan koma gidansa ba. Ki yi hakuri nidai kawai ya ban takardata." Nan fa Abulle ta sanya kuka wai Maryama ta zuge ɗiyarta. A karshe ta tara meeting don ganawa da kowa. Anan ma Muhibbat ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba ta ce ita kam ba za ta koma ba. Da yake Allah bai ƙaddara nisan zama tsakani ba, duk son Abulle da auren hakanan ta hakura aka rabasu. Kowa ya budi baki shaidar Muhibbat yake da hakuri, kunya da kawaici. A ganin iyayen tunda har ta iya karya bille ta furta kalmar saki, akwai dalili babba wanda kuma aka bar shi a sirrinsu tunda ba ta ce uffan ba.   Sakin ya fiye mata duk da irin son da zuciyarta ke yiwa Aliyu, so wanda ta girma da shi kuma ta raineshi. Sai dai an zo gaɓar da ta hakura, ba kuma za ta iya ci gaba da tafiyar ba.  A bangaren Aliyu sai da jikinsa ya yi sanyi amman kuma bai wani damu ba ko ba komai zai auri zaɓinsa kuma abar sonsa.    *** Jarrabawar NECO kadai ya ragewa su Ramlat wanda tuni aka soma. Ta rame koyaushe ba ta da aiki sai kuka da tunani. Hankalinta ya gaza kwanciya, matsowar auren da irin

Chapter 8 of 58