Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya daure fuska kamar bai taɓa dariya ba. "Malam kar ka kara yimin zancen banza! Shege ne da za ka ce kar na bari ya fito duniya? Kai ka fi kowa sanin duk iskancina bai wuce zuƙe-zuƙe da ƴar romance ba, amma bana babbar harka balle a samu akasi. Toh don me za'a haifarmin ɗan sunnah ka nemi ka kashen gwuiwa. Ba dan iskan da zai sa na zubar da cikin Baby." Ya ƙarashe gami da watsawa G Baba harara. Shi kuwa G Baba ya kara yarda da irin son da Aliyu ke yiwa Ramlat. Ya tabbata shi ya shafi abinda ke cikinta. Aliyu kaifi daya ne idan ya ga dama, idan har ya yi irin tsaurinnan to ba mai juyamishi ra'ayi wannan ta sanya ya ja bakinsa ya wayance da yi mishi kirari hadi da fadin. "Ko ba komai ai ma zo mu ƙarawa sama ado." Suka cafke gami da wata irin dariya. ***   Ramlat zamanta ta yi a dakin bayan ta idar da sallar La'asar da ba ta yi kam lokaci ba. Tana jin yunwa, sai dai ba ta kaunar ganinsu. Kwantar da kai ta yi a saman hannunta jikin gado tana daga zaune saman darduma, tunani mai zurfi ta faɗa gami da riƙe cikinta. Har sannan tana kara jinjina lamarin, wai ciki ne da ita.  'Cikin mashayi.' Wani bangare na zuciyarta ya ayyana mata, ta jima anan zaune har wahalallen baccin da ba ta samu yinsa da safe ba ya soma fisgarta sai dai cikinta na ta ƙara saboda yunwa. A hankali ta ji hannu saman fatar cikinta. Firgigit ta bude idanu, Aliyu ne durkushe ya daga rigar yana shafa cikin. Suka hada ido, murmushi ya sakarmata. Ita kuwa warin sigari ke tayarmata da zuciya don haka ta mike da sauri ya riko hannunta gami da miƙewar shima. "Baby lafiya?" Ta rufe baki da hancinta da hannu ta shiga tureshi tana girgiza kai. "Don Allah ka fita, warin taba, zan yi amai wal..." Yunkurin aman ya katseta, da sauri ta faɗa banɗaki shi kuwa ya fita daga dakin. Ba wani abin kirki ta amayar ba, ta wanke baki ta fito, ganin baya dakin yasa ta daukar turare mai sanyin kamshi a bakin madubi ta ɗan fesa a jikin wani dan handkerchief ta toshe hancin sannan ta bude winduna  dakin. Kiraye kirayen sallar Magriba ne ya sa ta mike ta zura hijabinta. Sai da ta yi sallah sannan ta mike ta nufi falon don Aliyun ya shigo har sau biyu kafin ta idar. Maimakon ƙamshin sigari, sai ta ji ƙamshin turaren wuta. Ba kowa a falon hakan ya bata tabbacin Aliyun ne ya kunna. Ta saba duk sadda ya gama busa hayaƙinsa za ta yi azamar daukar kaskonta ta kunna gawayi ta saka turare. Sai ta ji hakan da ya yi ya burgeta, kaso hamsin na damuwarta ya yaye. Sai a sannan ta ci dora abinci mai saukin dahuwa ta ci, ta shiga karatu. *** Washegari da ɗokinta ta fita daga gidan. Aliyu ne ya kai ta saman mashin dinsa.    Koda ta shiga Malami ya shigo basu sami damar gaisawa da Amrah ba sai dai wannan karon sun samu zama wuri guda. Ana tashi, kowa ya fice daga ajin suka yi zamansu. "Mai ciki ba za ki ci komai ba? Rana fa ta yi." Fadin Amrah cikin murmushi. Harararta ta yi sannan ta ja guntun tsaki.   "Ni har tsoron haihuwar ma nake." "A gidan Aliyun ko kuwa me?" Tasan Amrah da biyu ta yi tambayar, ba kuma ta so ta bada kofa yanzu Amrah ta san sirrin gidanta. Ta fi kaunar Amrah ta dawo da tausayi da kaunarta a zuciya kamar dai a baya. "A'a, kada na mutu wurin haihuwa." Dariya Amrah ta yi. "Sai kuma aka fadamaki haihuwar ƙarar kwana ce? Addu'a za ki yi, In sha Allah za ki haihu lafiya. Af, ga saƙon Umma ma. Ta cemin ki dinga shan kayan marmari da abinci lafiyayye. Kar kuma ki yawaita daukar abu mai nauyi. Kuma wai ko nan gaba za ta aikomaki mene? Oho na manta. Ta ce dai na miki albishir tana nan zuwa." Dadi, farin ciki da annashuwa suka cika zuciya da fuskar Ramlat. Daga washe haƙora tana dariya sai ga hawaye na fita. Hawayen tana da wata uwa da ba ita ta haifeta ba, amman ta tuna da ita. Tana kokarin ba ta kulawa irin ta uwa. "Meye abin kukan?" Fadin Amrah da ke jin zuciyarta itama na neman karyewa. Ta daure ta tattaro dauriyar wuri guda, ta shiga zolayarta. "Oh, wa ya ga Ramsy da ɗa? Naga yanda za ki yi raino. Wai har ki shayar." Ta ƙarashe gami da sanya dariya, itama ba ta san sadda ta dara ba ta hau share fuskarta.   "Kema ai kamar yau ne." Taɓe baki Ramlat ta yi. "Ni da aure sai na kammala karatu in Sha Allah." Murmushi Ramlat ta yi kafin su taɓa hira, so take Amrah ta jefomata tambayar da ta shafi gidanta ko dangin mijinta, sai dai ta lura kokarin kaucewa hakan ma Amrah ke yi. Don haka itama sai ta kara rufe cikinta ba ta kaunar su sami wata matsalar. ***    Bayan sati biyu hankalin Ramlat a kwance, za ta yi waya da Abbanta da kuma Hajiya wacce a sannan ta ɗan sassauta kadan. Umman Amrah kuwa kiranta take sosai su yi hira ta yi ta kwantar mata da hankali. Ta dauketa kamar ƴar da ta haifa a cikinta. Bangaren Aliyu, ya rage zuwa ya yi mata shaye-shaye a gida kamar yanda ya daina shigomata a buge. Hakan ya kara kwantar da hankalinta ba kaɗan ba. Abinda ke yawan bata mamaki ya daure mata kai, banda Abulle babu wani ko wata a dangin Aliyu dake zuwa gidanta, zargin ba sa kaunarta ya kara tabbata a kansu. Don haka ta ja jikinta ta kama kanta. Hakan bai hana ta kira mahaifin Aliyun ta gaidashi, shi kam lafiya sumul yake amsamata.      A yammacin juma'a ta fito falon bayan ta yi wanka ta shirya cikin riga da wando Pakistan. Tashinta daga bacci kenan bayan ta dawo daga makaranta. Kicin ta shiga ta hau kiciniyar yin tuwon semo da miyar kuka kasancewar hakanan ta ji tana sha'awarsa. Sai dai me? Babu gas. "Ya Salam." Ta furta a fili. Jiki a sanyaye ta fito falon tana jan tsaki, waya ta dauka ta lalubo lambar Aliyu ta kira.   "Kamar ya babu gas? Har gas din gidan ya ƙare?" Shi ne tambayar da ya jefomata bayan ya saurari bayaninta. Ta ciji leɓɓanta ta kasa cewa komai. Sai kuma ta ji ya ja tsaki kafin ya ce. "Nidai wallahi banda kudi, kema kin sani kuma. Yanzu haka ganinan wani banza dan gin..." Kiit, ta katse kiran, a duniya ta tsani ta ji yana ashariya. Abin na ƙona ranta. "Allah Ka shirya." Ta firta a fili, ita kam yunwa ta ke ji don haka ta mike. Ta tuna da lemun da ta gani Aliyu ya ajiye a fridge da safiyarnan, sadda aka kawo wuta. Ta soma shiga kicin ta dauko ragowar bireda ta fiddo lemun. Tun kafin ta ƙaraso ta bude ta shiga kwankwada. Sosai ya yi mata dadi. Tana zama ta hau tauna biredin, idanunta na kan wayarta dake ƙara kuma sanin Aliyun ne ta ƙi ɗagawa. A hankali kuma ganinta ya soma zama dishi-dishi. A kokarinta na  ajiye robar lemun saman Centretable sai ya zube a ƙasa. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Mene haka?" Ta fadi cike da karfin hali. Ita ta san me take ji. Jirin na kwasarta, yana kokarin fitar da ita daga hayyacinta. A hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta danna. Cikin muryar ƴan maye ta soma magana. "Aaaaaliiii." Ba ta ji me yake cewa ba ta wurgar da wayar, ta mike ta na tafe tana rangaji da zagaye falon, ba ta yi aune ba ta ci uban tuntuɓe da takalminta ta bugi gefen mararta da tv stand ta zube anan. Duk da ba'a hayyacinta take ba sai da ta saki ƙara. *** A hargitse ya banko kofar falon ya shigo. Kallo ɗaya ya yiwa robar lemun ya san abinda ke faruwa. Jijjigata ya soma. "Baby! Baby! Ramlat!" Ya rasa na kira, cak ya ɗagata ya fita. Ba kuma zai yiwu ya sanyata a mashin ba, dole ya dawo da ita ya fita ya taro ɗan sahu suka bar gidan zuwa asibiti. *** "Ka yi hakuri, cikinta ya riga da ya zube." Bayanin Dr Lamin kenan bayan ya gama faɗawa Aliyu cewa a jininta da aka auna an samu tabbacin ta sha kwaya mai ƙarfi, ya kuma yi faɗan meyasa ya bar ta yin shaye-shaye duk kuwa da sanin da ya yi tana da ciki. Ga mamakin shi kansa Aliyu ya kasa cewa komai, har Likitan ya yi faɗa ya kammala. Batun zubewar cikin ya fi komai ɗagamishi hankali. Idanunsa suka kaɗa. 'Ko mene laifinka ne ai! Da ba ka ajiye a gidan ba, ta ina za ta gani ta dauka tunda ba halinta ba ne!' Faɗin wani sashi na zuciyarsa. *** Awanni kaɗan bayan farfaɗowarta ya shiga. Ta ɗago idanu ta dubeshi sai ta soma hawaye.   "Kaga abinda halinka ya jazamana ko?" Ya zaune gami da riko hannunta. "Laifinki ne, meyasa ba ki ɗaga wayata ba ina ta kira? Tunawa nayi na ajiye a fridge shiyasa na so na gargaɗeki." Ta kauda kanta kawai, cike da bakin ciki. Abin kunya sanadin shaye-shayen mijinta, cikinta ya zube.     "Kaicona." Ta furta a fili, sai kuka. Kewa, kewar iyayenta take. Don haka ta juyo ya dubeshi. "Bani wayarka." "Ki yi me?" "Abbana zan kira." Ya daure fuska. "Ki ce mishi kin sha abin maye cikinki ya zube? Asirinmu za ki tona? Dama ya lafiyar giwa ballantana an jefeshi da kashi? Toh ki je ki gwada tona asirin namu. Naki ne zai fi wari, ni dama ba ganina suke da gashi ba." Daga haka ya mike ya sa kai ya fice a zuciye. Ta bishi da kallo, wani malolon abu ta ji ya tsayamata a maƙogwaro. Tana jin haushin irin kalaman da Aliyu ke yi akan iyayenta. Ko ba komai iyayenta kuma su suka haifeta. Dole ta takawa abin burki. 'Kin manta ke kika bada ƙofa.' Cewar wani bangare na zuciyarta, hakan sai ya karyarmata da gwuiwa. Ta yi shiru ta soma hawaye. Tana jin haushi da tsanar kanta akan duk abinda ya faru tsakaninta da yan uwanta, a gefe guda kuma don Aliyu ya zama kamar bugun numfashinta wanda ba ta jin za ta iya rayuwa babu shi. Sai dai kuma hakan ba zai hana ta janyo ƴan uwanta jiki ba, ta dinga ziyartarsu koda ba su zo mata ba. Ta kudurta sauya takunta tun kan abu ya yi nisa. ***   Sai da ta yi kwanaki uku aka sallameta daga asibiti. Shi ne lokaci na farko da ta ga matan mahaifin Aliyu a gidanta da sunan dubiya. Ba su kadai ba, har su Abulle da Mamar Muhibbat sun zo. Kana ganin fuskokin za ka san dole akai musu. "Ikon Allah, kema dai ina ce ba shi ya jawomaki ɓarewar cikin ba?" Cewar matar Malam (mahaifin Aliyu) ta farko, Atine. "Wane zancen banza ne haka ke Atine? Wa kike nufi da ɓarar da ciki? Au dama sharrin da za ku yiwa Zakina kenan?" Fadin Abulle cikin masifa. Wannan yasa Atine fadin "Allah Ya ba ki hakuri Baba." Abulle ta yi kwafa. Ramlat dai tana zaune ta dukar da kai a saman kujera don Abulle ta hanata zama ƙasa.    Sun jima a gidan don har sai da Abulle ta saka yanmatan jikokinta su yiwa Ramlat girki a risho. Haka suka shiga suna kunkuni. Har gobe ba sa kallonta da gashi, Muhibbat ce tasu. A karshe kowa ya watse aka bar ta ita daya ta yi ta godiya kuwa. Komawa ciki ta yi ta ga yanda suka yi kaca-kaca da kicin din, ta kuma sani da biyu suka yi hakan. Haka ta daure ta kimtsa ko'ina. Tana jin sadda Abulle ke cewa Zalihat diyar Atine ta zauna ta kwana biyu yarinyar ta yi kememe uwarta na turata ta fice ta shige mota. Murmushi ta yi mai ciwo. Ta dauki waya cike da so da kewar iyayenta ta dannawa Hajiya kira. Ringing uku ta ɗaga da sallama. "Hajiya." Ta fadi a raunane zuciyarta a karye. Daga dayan bangaren Hajiya ta ji gabanta ya fadi, ta daure. Kwanakinnan da tunanin Ramlat take kwana da tashi. Tun sadda aka ce ta yi ɓari ta kira Zulaihat da Rafee'ah akan su shirya su je. Yanzu kam sun amince zasu je bisa umarninta. "Ramlatu, ya gida? Ya jikinnaki?" Wani sanyin dadi ya saukarmata a zuciya. Yau ne karon farko da Hajiyar ta kira sunanta ta kuma bata kulawar da ta dace. "Jikina da sauki Hajiya. Hajiya yaushe za ki zo? Ki yafemin don Allah Hajiyata." Kukan da take riƙewa ta shiga yi. "Hajiya kin yi shiru. Hajiya ki yafemin." "Na yafemaki Ramlatu, na yafemaki duniya da lahira. Ki kwantar da hankalinki. Ki bi mijinki, Allah Ya yi maki albarka. Gobe yayyanki zasu zo." Rasa kalar farin cikin da za ta yi ma ta yi. Sai ga ta nan tana dariya. Suka yi sallama da Hajiyar ranta fari sol. Ta ɗago kai kenan ta hada ido da Aliyu. Yana jingina kansa cikin bangon falon yana zuƙar taba da fesarwa. Ganin ta kammala wayar ya tako ya zauna gefenta. "Su waye zasu zo?" Ta mance da batun wani sigari ko warinsa, rungumeshi ta yi sosai cike da farin ciki ta amsa. "Tayani murna, Hajiya ta yafemin, ga Anti Zulaihat da Anti Rafee'ah zasu kawomin ziyara gobe." Ga mamakinta sai ta ji ya ja tsaki. Ta ɗago tana kallonsa. "Da yake ba ki da zuciya ko? Duk irin rashin kaunar da suka nunamana akan wani banzan Hilal bai ishemu ba? Wane irin kalamai ne ita Zulai din ba ta ce a kaina ba? Ita kuwa Rafee'ah wato tsabar tsana har.." "Ya isheka! Ya isheka!!" Ta tsinci muryarta da fada, bakinta da kakkarwa, jikinta da rawa. Ta miƙe tsaye kyam da ƙafafunta. Idanunta a rufe cike da masifa!  Kallonta kawai yake yana zuƙa da fesarwa, maimakon ɓacin rai, murmushi yake, murmushi sosai har da dora ƙafa daga saman Centre Table. "Ƙarya nayi?" Shi ne abinda ya furta.  I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/xcmnTANK99 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 18) "Nace ƙarya na yi?" Ya kara maimaita tambayarsa ganin ga tsaya cak tana kallonsa. Sai sannan ta kauda idanunta daga kansa. "Ya isheka! Aliyu ya isheka! Ban raina iyayenka ba, ban taɓa faɗar kalma marar dadi a kansu ba, kar ka fara da nawa. Kar ka koyamin. Ba zan dauka ba. Ko ba komai sun haifamaka ni." Wata dariya ya yi kafin ya kashe sigarin a karamin farantin tasar Ramlat din da ya mayar na kashe taba. Miƙewa ya rungumeta tana kaucewa. "Sorry Baby, Allah Ya ba ki hakuri. Ba zan ƙara ba." Ta zame jikinta kawai ta nufi daki. Dakyar ta sauko ta bar fushin ganin yanda ya ke lallaɓata kuma ta san kwanan zancen sai dai dole ya hakura don ba dama. *** WASHEGARI Tun zamansu a falon suke kallon ko'ina gami da taɓe baki.  Can kuma Zulaihat ta dubeta. "Matar Aliyu, ya jikin?" Ba ta son suna kiranta da wannan sunan, ta fi kaunar Ramlat din da aka yankamata rago da shi, sai dai furta hakan tasan wata baƙar maganar za ta ƙara tofamata, don haka ta haɗiye ɓacin ran ta yi yaƙe tana ɓarewa Khalifa ledar alewa. "Jiki da sauki. Na warware. Yau dai Allah Ya yi kun zo min." "Yanzun ma don kin haɗamu da uwarmu ne, gudun ɓacin ranta ne ya kawomu gidanki. Kinsan ba duka aka taru aka zama ɗaya ba." Fadin Rafee'ah kenan wacce dama tun ɗazun take ba Daddy nono tana wani jijjiga ƙafa. Murmushi Ramlat ta yi. "Kowa dai da irin kaddararsa." Tsaki Rafee'ah ta ja, ita kuwa Zulaihat ta yi dariyar rainin wayon Ramlat. "Allah Ya kyauta, Ramlat baki abin magana." Ta yi murmushin da bai kai ko'ina ba. Duk a zatonta zuwan yini suka yi mata, ashe ba haka ba. Duka-duka basu fi mintuna talatin ba suka miƙe. Baki sake ta ke dubansu. "Wai ba dai tafiya ba?" "Ah, me zamu zauna mu yi? Ko an fadamaki namu mazan ba sa sonmu suka bari muka zo?" Zulaihat ke fadi sa'ilin da take gyara zaman mayafinta. Idanunta suka cicciko da kwalla. "Don Allah ku tsaya ku ci abinci, wallahi na yi girki kuma idan ba ku ci ba zai iya lalacewa." Tausayinta ya ɗan tsirga Zulaihat, ko ba komai kanwa ce garesu, ta lura babu wani ƙiba na amarci da Ramlat ta yi face rama. Hasken fatar ma ta tabbatar ma cuta ne. "Ke kika san wannan, nikam muje Sis. Baban Khalid bai ce na jima ba, kuma kinsan zai dawo daga Gusau." Zulaihat ta koma ta zauna. "Mintinan kadan zamu ƙara Rafee'ah, yi hakuri mu ci abincin. Yunwa nake ji dama." Ta fadi ne kawai don Ramlat din ta ɗan ji sanyi ganin har ta soma hawaye. Guntun tsaki Rafee'ah ta ja don ita ba ta son ma tuna cewar a gidan Aliyu da Ramlat take. Ganin haka da sauri Ramlat ta faɗa kicin ta shiryo musu lafiyayyan jellof din shinkafa da taliya da ta girka musamman domin su, ya ji alayyahu da kifi. Cima ce da ta san suna masifar so musamman idan Hajiyarsu ce ta girka da busasshen kifi. Tun kafin ta ƙaraso ƙamshin ya bugesu. Rafee'ah na zaune tana buga game  wayarta, Zulaihat kuwa ta kwashi gara suna hira. Ana cikin haka, sai ga Amrah ta kira. Daga makaranta takanas ta taho dubiya. Cike da farin ciki ta yi kwatance, ta leka ta tarbota a gate. Ita kanta ta yi mamakin ganin su Rafee'ah a gidan. Wannan shine taimakon da Ramlat ta samu, abincin ya ƙare tas sai wanda zasu ci ita da Aliyunta. Zuwan Amrah ya daukemusu hankali aka shiga hira sosai, sai dai Rafee'ah na kaucewa hirar da za ta haɗata da Ramlat din. *** Shaf ya mance da batun wasu baƙi, abu ne da ba'a saba ba. Ya saba ya wuni kasuwa ya dawo ya riski matarsa ita daya. Kusan ma a fusace yake, mashin dinsa a waje ya bar shi, wayar da abokin kasuwancinsa Nabil ya mishi ita ta ƙara fusatashi. Shikenan ba dama ka ranci kuɗaɗen mutane sai su takura maka a waya. Ya ci alwashin cika abinda ya yi niyya yau, ya tabbatar hakan zai ba shi ribar da zai maida bashin ya kuma kashe wata matsalar. "Dalla malam nace maka gobe zan ba ka kudinka! Dan ....uwarka ka rabu da ni!" Jin abinda ya ce, Nabil ya fusata shima ya shiga surfa mishi ashar. Shima bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya hau ramuwa har ga shigo cikin falon. Idanunsa sun rufe bai ko lura da mutanen da ke zaune ba. Gaba daya idanunsu yana kansa, Ramlat kirjinta ne ya shiga bugu da sauri.  Wani irin ashar yake ƙundumawa kamar tsohon ɗan tasha. Zulaihat ta dubi Rafee'ah kafin ta maida dubanta ga Ramlat wacce ke jin kamar ƙasa ta buɗe ta nutse a wurin. Ta saci kallonsa, ya gama wayar ya zaro lighter daga aljihunsa, sanin me hakan ke nufi ya sa Ramlat saurin miƙewa gami da ƙarasawa inda yake. "Sannu da zuwa. Muna da baƙi fa." Ta furta murya na ƴar rawa. Sai a lokacin ya san da ita a falon, ba ma ita din ba, ya ankara da mutanen da ke zaune. Mutanen da ya kira da maƙiyansa. Kallon da ya watsamusu kallo ne na raini, kafin ya maida duba ga Ramlat cikin halin ko'in kula. "Sai me? Inace ke suka zo dubawa? Me zan musu? Ai wanda ke yi da ni, da shi nake yi. Mtsw." Ya ƙarashe da tsaki ya yi ciki, ta daskare a tsaye, ta kasa koda juyowa ta dubesu. Rafee'ah a fusace ta mike tsaye ta ja zanin goyon Daddy ta saɓeshi. "Sai ku tashi mu bar gidan. Gobe idan an ƙara ganin ƙafarmu a yi mana fin haka. Dama wane mutunci ko karramawa za'a samu wurin wannan mutumin?" Rafee'ah ke maganar a fusace, ba ta jira komai ba ta fisgi gyalenta daga saman kujera ta ɗauki jakarta ta yi gaba. Ita kuwa Zulaihat jiki a sanyaye ta mike tana ƙara maimaita Allah Ya kyauta kamar wani karatu. Ita abin dauremata kai ya yi da kuma mamaki. Bangaren Amrah kuwa, itama miƙewa ta yi ta hau gyara zaman ɗankwalinta da ya sunce. Sannan suka kama hanya. Ramlat ta juyo tana dubansu, sai a sannan ta yi yunkurin magana ta karasa da sauri ta tsayar da su. "Don Allah ku yi hakuri. Wallahi ransa ne a ɓace. Ba haka yake ba, ku yi hakuri don Allah." Wani murmushi Zulaihat ta yi. "Ai ba ke kika yi mana ba, mijinki ne. Kuma ko ba komai gidansa muka zo, kinga ko shari'a ta kayar da mu. Koma ciki kawai, ma yi waya." Tana kuka kuma tana ji tana gani suka kama hanya. Ta riko hannun Amrah. "Sakarni don Allah Ramlat, ma haɗu a makaranta. Ko me ya faru ke kika ja. Ke ce silar komai. Ke kika bada ƙofa aka daina ganin naki da mutunci." "Abu ba zai wuce ba Amrah?" Maimakon ta samu amsarta, sai Amrah ta kwace mayafinta ta ja hannun Khalifa suka bi bayan su. Rafee'ah tuni ta yi waje, tana tsaye tana jijjiga Daddy dake kuka, ita kanta hawayen take fitarwa, hawayen takaicin Ramlat. Tana ganin Zulaihat ta dubeta. "Me aka gujemata tun farko? Dama ai wanda bai ji bari ba zai ji hoho. Me dama za ta samu a wurin mashayi idan ba irin hakan ba?" Zulaihat ta mata ido ganin Amrah ta taho, sun dauki sirrin shan sigai da kayan mayen Aliyu matsayin sirri da ba kowa ne ya sani ba. Suna jin kunyar Amrah ta ji sai dai kuma basu da masaniya itama tana da labarin waye shi. Haka suka dunguma gwuiwa a sake su ka bar unguwar Rafee'ah ma faman mita. Zulaihat itama tana kiran sai ta faɗa wa Hajiya. "A'a Anti don Allah kar ku yi haka. Ko don Abba, kar fa ku manta har yau Abba na kan shan maganin hawan jini. Don Allah kar ku jefasu cikin damuwa. Ramlat ai ba ta je ta faɗa ba, kuma da alama mu din ne bai son gani a gidansa saboda ta riga ta nunamasa bama ganinsa da ƙima da mutunci. Shirun zai fi zama alheri ga su Hajiya." Amrah ke maganar a tausashe. Sun fahimci manufarta, don haka suka yi na'am da hakan. Sai dai kowa zuciyarsa ba dadi. ***   Kai tsaye ɗakin ta shiga da hawaye caɓe-caɓe saman fuskarta. Abinda idanunta ya gane mata ne ya sanya ta sakin baki ta haɗiye kalamanta. Sif din kayanta ya bude ya fiddo karamin akwatin sarƙoƙinta yana bincikawa. Wani dan gida wanda ta sanya auduga ta saka gwal dinta na wurin Abba a ciki shi ya fiddo. Sai wani set na gwal din da ya siyamata. Da sauri ta karasa ta fisgesu. "Mene haka? Me kake nufi?" Kallonta ya yi  fusace. "Me nake nufi kike tambaya? Siyarwa zan yi! Kudi nake so! Bashi ya min yawa, shagona kaya sun tasar ma ƙarewa, ko so kike ku rasa komai ne?" Zuciyarta na wani irin tuƙuƙi ta shiga girgiza kai. "Wallahi ba za ka siyarmin da zinaren da Abbana ya siyamin ba. Ko wanda ka siya  ai ya tashi daga naka, nawa ne. Don haka ba ka isa na ba ka ka siyar ba. Anya Aliyu kana cikin hayyacinka kuwa?" Hannu ya fidda ya ɗauke ta da mari Wanda ya yi sanadin zubewar gidan sarƙar, suka tarwatse a ƙasa. "Bayan laifin da kika yimin na kawomin tumakai cikin gida, hakan bai isheki ba sai kin kirani da mahaukaci?! Sarƙa kuma naga shegen da zai hana na siyar, idan kuma ubanki ne ya bani kudin na siyamaki sai ki faɗa!" Tana kuka ta shiga tattarawa ta dunkule a hannunta, ya shiga kokarin kwacewa. "Ba za ki saki ba? Wallahi zan miki dukan kawo wuƙa yanzu!" Ya ƙarashe gami da kai mata naushi a ciki. Ƙara ta saki, kafin ta ce. "Shikenan! Zan ba ka naka ka siyar amma wallahi banda na wajen Abba." Bai ko saurareta ba sai da ya kwace duka, zai fita ta rike ƙafarsa, wani harbin ya kai mata da ya samu bakinta, nan da nan ya kumbura ya soma fitar da jini. "Kar ka yimin haka! Ai Abbana ya siyamin shima! Ka bani na wajen Abba!" Ta miƙe a guje ta bi bayansa har harabar gidan, zai fice ta rike rigar gam tana kuka. Ya tureta, ganin ta ƙi sakinsa ya sanya a aljihun gaban rigarsa ya hau kai mata duka yana ashariya. Kira yake ita ce

Chapter 15 of 58