da nashi. Zuciyarta ta yi rauni.
"Allah Ya jiƙanka Abbana." Ta furta a fili gami da amsawa da amin. Ƙarar wayarta dake nufowa ɗakin ya katse tunaninta, Ummi ce a guje rike da wayar sai Ansar a bayanta da alama so yake ya kwace wayar.
"Mommy an kiraki! Ansar ne ya dau wayar."
Ta karɓa tana bugamishi harara ya shiga ƙaryata Ummin.
"Kul! Kar ka ƙara. Duk ku fice daga dakin toh." Sum sun suka fita, har wayar ta katse, kafin ta kai ga duba sunan mai kiran an ƙara kira. Ƙurawa fuskar wayar ido ta yi, Hilal? Ta dauka da s🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
02)
"Haba Ƙanwata, sai an ga dama za'a amsamin kenan? Sarautar ta motsa."
Ya yi maganar cikin shaƙiyanci, ta yi dariya.
"Wane mutum. Kawai dai bana kusa kafin na ƙaraso ta katse. Ina wuni Yaya Hilal."
Ya amsa cike da fara'a kafin ya ce.
"Zan amsa amma fa har yanzu ke mai laifi ce a wurina, kaf gidanku an zo ganin Babyna banda ke, ga shi har gobe suna. Anya kin kyauta Ramla?"
Ta rufe fuska da hannu daya tana murmushi kamar a gabansa.
"Ban kyauta ba, amma In Sha Allah zan wanke laifina, zan zo washegarin suna."
Da dariya ya amsa.
"Toh Alhamdulillah, haka nake son ji. Ya su Hajiya?"
"Sunanan lafiya."
"Ki gaidamin su sosai."
Ta amsa da toh sannan suka yi sallama. Ba ta zurfafa tunani ba ta mike ta fita dakin gudun matsawa kwakwalwar da tunani.
***
Ranar Lahadi, misalin ƙarfe biyar na yamma, ita kadai ce a gidan, Hajiya ta je babban gida, gidan iyayenta ita kuwa A'isha ta wuce da yara gidan Anti Zulaihat za'ayi birthday din ƴan biyunta, daga can za ta biya ɗaukarsu.
Ta fito tsaf cikin atamfarta V.I.P Holland kalar coffee da ratsin ja, an mishi ɗigo ɗigon milk. Dinkin riga three-quarter akai mata sai straight skirt. Ta yafa jan mayafinta madaidaici, ba wani kwalliya ta yi ba, gida kadai ta shafa da man leɓe marar kala. Takalminta mai ja da baƙi, flat. Daga haka ta dau jakarta mai kalar takalmin sai kuwa mukullin mota ta fito.
Motarta sai sheƙi take an wanke mata tas. Murmushi ta yi sa'ilin da ta shiga ta ga hatta da komai an na ciki an goge.
"Wani aikin sai Nasiru." Ta furta cike da jin wani dadi. Hakanan ta tashi da wani irin farin ciki a yau, bai wuce nasaba da zuwan Yayanta Munir da kuma irin rahar da suka yi wanda an dade rabon da ayi din har take ce mishi za ta sunan Hilal ya yi murmushi.
Wannan ya sanya a hanya ta kunna waƙar Hamisu Breaker mai taken So dangin mutuwa. Kalamansa suna ratsata, ga sanyin Ac na shiga dukkan wata ƙofa ta ilahirin fatar jikinta. Gaba daya waƙar na shigarta har tana jin kamar ta zubar da hawaye. Abubuwa da dama sun tsayamata a rai, ta kasa ciresu. Har dai ta tsaya a katafaren shagon Yayansu Munir a yanzu, Alheri Store, ba ta bar tunani ba. Shiga ta yi ta siya kayan jarirai komai pink bayan sun gaisa da mutan shagon sannan ta ja motarta. Har ta iso unguwar Lamiɗo Crescent waƙar take ji, daga ta ƙare sai ta tariyota. Ba ta ji faduwar gaba ba sai da ta ganta a ƙofar gidan Hilal Maigadi ya budemata ƙaton ƙyauren ta shiga. Duk wani sauye-sauye da gidan ya samu, hakan ba zai sa ya ɓacemata ba. Ta ya za ta mance ranar da komai ya samo asali? Dakyar ta samu nutsuwar saita tunaninta, ta faka motar a inda ya dace, ba ta san tarbar da za ta samu daga matar gidan ba. Abu daya ta sani, saboda Hilal ta zo. Ba kuma za ta fasa shiga ba koda hakan na nufin rusa farin cikinta.
Falon farko ba ta tarar da kowa ba sa'ilin da ta yi sallama, sai kuma mai aikinta ta fito daga kicin tana amsawa. Bayan sun gaisa da fara'a take sanarmata ta ƙarasa falo na biyu, suna ciki. Ta yi godiya ta sanya kai. Tana tafe tana karewa gidan kallo, abubuwa da dama suna dawowa kwanyarta. Tashin muryoyin da ta ji ya bata tabbacin ba matar gidan kadai bace. Sallamarta ta dauki hankulansu. Wadanda ta gani zaune ya sa ta daukewar wucin gadi. Meyasa da ta fito daga gidansu da nishadinta, ba ta zarce kai tsaye gidan Yayarta Zulaihat ba? Meyasa ba ta ji shawarar A'isha ta ƙi zuwa ba? Sai dai kuma ta faru ta ƙare, an yiwa mai dami ɗaya sata.
"Toh fa, wata sabuwa inji ƴan caca. Ramlah, dama ana ganinki? Duniya mai yayi."
Maganar ta fito daga bakin wata kakkaurar mace dake zaune kusa da Anti Bilkisu Matar Munir.
Ta daure ta ƙaraso ciki tana yaƙe, sai da ta zauna ta gaishesu. Suka amsa ciki-ciki. Ta maida kai ga mai jego da tun ganinta ta sauya fuska.
"Sannu Fa'iza, Barka mun samu ƙaruwa, Allah Ya rayamana Amal."
Ba wanda ya amsa sai Anti Fareeda wacce ta soma magana, itama tana wata ƴar dariyar shaƙiyanci.
"Amma dai Munir bai san za ki zo ba?"
Tambayar da Bilkisu ta jefomata kenan. Ta yi mata duban rashin fahimta. Sai kuma ta fasa magana.
"Ramla, ya hakuri? Ashe kuma kin samu kanki dakyar. Naji ance har dukanki yake. Allah dai Ya gafartamasa."
Wannan karon Anti Murja ce. Su hudu ne a falon, da Fareeda sai Murja da Bilkisu sai kuwa Fa'iza mai jego.
Maganar Murja ta daki zuciyarta. Ta kasa hakuri, kafin ta tanka Anti Fareeda ta cafe.
"Kee Murja, idan dukan ne ma ai da sauki. Kedai kawai abar kaza cikin gashinta. Dama shi alhaki ai kwuiwuiyo ne, kadan kenan. Da sauran rina a kaba, yanzu ba gashinan ana girbar abinda aka shuka ba."
Dukkan zantukan suna shigarta, ta kuma san baƙar suke jefamata, dama ba mai hakurin bace, sai dai yanzun dole ta koyar da ita hakurin da kauda kai. Don haka a gaggauce ta miƙawa Fa'iza ledar.
"Gashinan ba yawa Fa'iza. Allah Ya rayamana ita. Ni zan tafi."
Ba wanda ya amsa wannan karon, tana dab da ficewa ta ji Bilkisu na fadin.
"Ki bi dai a hankali Fa'iza, don wallahi wannan karon daga ke har mijin za ta iya rabaku da numfashinku, don ga dukkan alama zawarcinsa take."
Ta tsaya cak gami da juyowa, idanunta kadai idan ka kalla za ka fahimci ranta a mugun ɓace yake. Kamar ta tanka sai kuma ta haɗiye ta yi musu jam'in kallon su din banza da ido kafin ta fice ta bar Bilkisu na daga murya da fadin ta zo ta shaƙeta tunda ba ƙaramin aikinta bane.
A miliyan ta bar gidan, sai da ta ɗan yi tafiya mai nisa kafin ta faka a ƙasa wata bishiya kusa da wani mai katin waya, ta kusan awa a wurin tana jinyar kirjinta dake zafi, dakyar ta shiga ambaton Allah sannan ta samu karfin gwuiwar soma tafiya, har da taimakon Allah ta koma gida lafiya. Kai tsaye ɗakinta ta shige ta rufe gam da muƙulli. Zubewa ta yi saman gado ta shiga rera kuka. Sai da ta jiƙa rigar filonta jagaf sannan ta ɗago tana mai dafe kai da goshi. Kukan dai ba ta fasa ba.
_'Wace irin ƴa na haifa? Rabi'atu wace irin ƴa kika haifamin?! Anya ba'a yimin musanye a asibiti ba?! Don ina mamakin kasancewar Ramlatu jinina!'_
Ta kara fashewa da kuka tunano kalaman mahaifinta ranar da ta koma gida bayan iyaye da yan uwan da suka miƙata gidan miji basu jima da watsewa daga gidannasu ba.
Kiran da ya shigo wayarta ne ya dauki hankalinta. Ta kai duba, Hilal ne. Ta yiwa sunansa ƙuri kamar yau ta soma gani. Lambar ba baƙuwa ce a wurinta ba don kusan tun sadda suke tare ta sanshi da ita. Ina za ta mance soyayyar da suka yi wanda a karshe lamura suka sauya? Ba ta kai ga amsa wayar ba har ta katse zuciyarta ta tafi ga tunanin farkon haɗuwarta da shi.
***
Katafaren hall din na Aseem Event Centre ya cika da mata da maza har ma da yara tsiraru kasancewar ranar ake dinner party na Munir Khalid Mu'azzam da Bilkisu Tijjani Dutse.
Anko kam an yi shi na wani French lace kalar blue mai kyau. Kannen Ango su huɗu cif sun fito a nasu ankon na daban. A lokacin Zulaihat kadai ce ta yi aure a cikinsu sai Rafee'ah dake da sanya rana a kanta. Kwalliyar wani arnen lace peach suka yi, karshen kyau ƴaƴan Hajiya kam sun yi shi. Duka-duka A'isha ba ta wuce shekaru goma sha biyu ba sannan sai dai ƴar lukuta suke kiranta tsabar ƙiba tubarakAllah. Duk cikinsu Ramla ce baƙa, ita ta dauko kamannin mahaifiyarsu sak, don kaf dinsu mahaifinsu suka biyo. Baƙar fata ce ita, tana da matsakaicin tsawo. Surarta abin a kalla hakanan kyakkyawar halittar fuskarta. Duk da kasancewarta baƙa, sai a ɗauketa da gudu ba'a ɗauki ɗayansu ba. Fuskarta kadai ka kalla za ka tabbatar tana cike da farin cikin wannan rana.
Ta dage sai rawa take tana zubawa Amarya da Ango kari, ta yi baya da zummar fita daga gurin za ta kaiwa Rafee'ah gulmar hararar da Munir ya jefamata sanin da ya yi murnar auren da biyu take, ba zato ta ji ta yi karo da mutum har yana kiran wayyo. Ta yi saurin juyawa ganin kansa a ƙasa ya riƙe yatsansa na hagu da ya sha taku a wurinta. Tsinin takalminta ya ji mishi ciwo a ƙafa.
A gigice ta durkusa itama tana ganin yanda fatar wurin ta ɗan ɗago. Idanunta suka yi rau, ta dubeshi.
"Don Allah ka yi hakuri." Da rawar murya ta ƙarasa zancen sakamakon faɗuwar gaban da ta ji lokaci guda ganin irin kallon da yake mata kamar zai cinyeta. Ya mike tsaye itama ta mike, fita ta ga ya yi daga tsakiyar filin zuwa kujera, kafar ya daga yana duba. Ta karasa sadda wani a gefensa ke mishi magana don ba ta san me yace ba dalilin ƙarar kiɗa da ta cika wurin.
"Don Allah ka yi hakuri wallahi ban lura ba."
Jin muryar a saitin kunnensa ya sa shi ɗago kai ya dubeta, ganin kusancin ya yi yawa sai ta ɗaga kai, ta yi da niyyar ya ji abinda ta ce saboda kiɗan kan iya hanawa ya ji din. Murmushi ya sakarmata wanda ya kara fiddomata da kyawunsa. Fari ƙal, ga dukkan alamu dai bai saba da wata aba wahala ba.
"Kar ki damu, amma sai kin biyani."
Ta zaro ido sai kuma ta karyar da wuya gami da marairaicewa.
"Ta yaya? Don Allah ka yi hakuri."
Wayarsa ƙirar Motorolla ya zaro ya miƙamata.
"Sanyamin lambarki." Ta saci kallonsa tana murmushi ƙasa-ƙasa. Shima tuni ya mance da zafin da yake ji a ƙafar ya shagala da kallonta.
"Sai dai ta Landline din gidanmu."
"Ba matsala a sakamin."
Murmushi bai bar saman fuskarta ba ta karɓa ta sanyamishi.
Ya karɓi wayarsa fuska a sake.
"Ya yi kyau, wane suna zan sanya?"
"Ramlat." Ta furta kai tsaye, ya maimaita yana murmushi za ta bar wurin ya dakatar da ita.
"Ba ki tambayi sunana ba."
Ta waigo tana dubansa. Ya ƙuramata ido kamar ya cinyeta.
"Hilal, Hilal Aminu Dutse, amma zan so ki raɗamin My Future Husband."
Tana murmushi ta bar wurin da saurinta har tana tuntuɓe sakamakon kunyar da ta kamata. Haka ta koma mazauninsu. Duka ta ji an kai mata a baya, ta kalli mai shi, aminiyarta wacce suka taso tun firamare tare har zuwa yanzu da suke Sakandire aji na hudu, Amrah Abdullahi. Ɗaga gira ta yi tana dariya.
"Na fa ganki da wani haɗaɗɗen guy. Wato dai su Kb kika rainawa wayo da kike hanasu lambar waya."
Ta harareta da murmushi dauke saman fuskar, Kb wani yayan wata ƴar ajinsu ce, a makaranta ya ganta yake so, sai dai ta ce sam bai yi mata ba.
"Ke kam wa ya fadamaki soyayya muke? Shikenan ba dama ku gaisa da mutum sai cibi ya zama ƙari?"
Harararta Amrah ta yi.
"Aikin ɓurr, faɗawa wanda bai sanki ba. Matar da gaisuwar ma ba ki damu ki yi da wani namijin ba. Lallai ma, an gaisheki toh. Idan ta yi wari na ji."
Ganin yanda take neman yin fushi ne ya sanyata riko hannunta tana dariya.
"Haba tawan, ai kema kinsan ya wuce ace sai ta yi wari kya ji. Ba fa wani abu bane."
Nan ta bata labarin Hilal, suka dinga dariya ta ɗora da fadin.
"Amma wallahi ya kwantamin, ko ba komai yana da kyau kuma da alama dangin Amarya yake. Nidai ina sonsa."
"Saboda shi son ba shi da wuya ko Ramsy?"
Ta kirata da sunan da suke fadamata a makaranta. Ta zubamata dara-daran idanunta, kafin ta kara satar kallon Hilal wanda ga mamakinta wajen da take ya ke kallo. Murmushi ya sakarmata ta yi saurin juyar da kai numfashinta na harbawa da sauri. Amrah na lura da su, banda murmushin itama ba abinda take zabgawa.
"Na yarda Ramsy kin harbu. Allah Yasa ya zamemaki alheri. Farin cikinki, shi ne nawa."
Ta ɗago ta dubeta duba na kaunar ƴan uwantaka da amincin dake tsakaninsu.
"Ameen tawan. Kina son abinda nake so, shiyasa nima nake ji da ke."
Suka murmusa sannan suka ci gaba da shagalinsu.
A daren bayan komawarsu gida ta shiga wanka.
"Ramsy! Tun dazu fa wani wai shi Hilal ya kira yana nemanki, yanzun ma ina tunanin shi ne."
Ai da sauri ta watsa ruwa ta ja zani ta fito gudun kada wani a sashin Hajiyarta ya dauka. Suka dubeta suna dariya ganin kumfa a kafaɗarta ta dama da kuma ƙeyarta. Ta fisge kan waya a hannun ƴar uwarta da suka zo daga Daura, Naja'atu. Sai dai ganin fisgewar ta janyo kan wayar gaba daya daga saman tebur. Ta ja guntun tsaki.
"Ke Ramla, wai hala sabon kamu kika yi?". Fadin Najaatu.
Harara ta bugamata.
"Yo ke Naja sai an hwaɗi maki? Ai gahi kina gani."
Cewar Sa'adah. Itama dai daga Daura ta zo.
Ita dai Ramla gaba ta yi zuwa banɗaki ta bar su suna mata shaƙiyanci, ba ta kai ga abinda ta yi niyya ba, wayar ta ƙara ringing, da sauri ta fito suna mata dariya ta ɗaga.
"Assalamu alaikum." Ta furta har muryar na ɗan rawa. Ya amsa mata sannan ya ce.
"Haba don Allah, wallahi ba ki ji yanda gabana ya shiga faɗuwa ba duk a zatona halinku na mata ki ka yimin. Wato dai na dauka wrong number kika ban."
Ta dan lumshe idanu sannan ta bude tana murmushi, su Najaatu sun tsuramata ido kuwa, ganin haka ta juyamusu baya.
"Kiyi magana ko hankalina zai kwanta don Allah."
"Ka yi hakuri, bana kusa ne."
Ta ji ya sauke numfashi.
"Alhamdulillah. Na kasa samun nutsuwa Ramlat, yanda nake jinki a raina tun daga haɗuwarmu zuwa yanzu, jikina yana bani kece mahaɗin rayuwata. Don Allah a amshi Hilal da hannu bibbiyu. Kinji?"
Ba karamin dadi kalamansa suka yi mata ba. Tana murmushi ta amsa.
"In Sha Allah."
"Hakan na nufin?"
Ya nemi sani. Ta gyada kai kamar yana kallonta.
"Na karɓa."
Hamdala ta ji ya yi yana zuba godiya har ya bata dariya.
Sai kuma hira ta ɓarke. Nan yake fadamata shi din cousin din Bilkisu ne. Mahaifinsa Alhaji Aminu, yaya ne ga Alhaji Tijjani mahaifin Bilkisu. Su mazaunan unguwar Goron Dutse ne. Ya hada Degree dinsa a fannin Accounting, yanzu haka kuma yana shirin zuwa Malaysia haɗo Masters. Ta nutsu tana jin jawabinsa, a karshe ya dora da fadin.
"Tsakani da Allah nake sonki, kuma da aure. Ba don karatun ya zama dole ba, da sai ince a dauran auren kawai na wuce da ke Malaysia. Toh na tabbatar kema ɗalibar ce kamar ni, ko kuwa?"
Suka dan dara, har cikin ranta take jin ya kwanta mata dari bisa dari.
"Toh yanzu dai nima sai ki biyani bashin labari. Fadamin tarihinki."
Ya buƙata. Ta fayyace mishi asalinsu da kuma matakin karatunta a yanzu.
"Nayi murna da samunki My Future, kuma ina ji a jikina kece matata da yardar Allah. Muyi fatan Allah Ya cikamana burinmu. Kafin na tafi zan iya kawomaki ziyara?"
Ta kasa cewa komai din farin ciki, sai dai kuma tana shakkar Yaya Munir ya ji labarin ta soma tsayawa hira da wani namiji yanzun. Don haka ta girgiza kai.
"Ka bari da kaina zan gayyaceka gidanmu. Ka ji?"
Yanda ta ƙarashe zancen a shagwaɓe ya haddasar mishi da wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ya yi gyaran murya kafin ya samu kwarin gwuiwar amsawa.
"Shikenan My Future, ni naki ne. A koyaushe kuma a kowane mataki na rayuwa da yardar Allah. Zan jiraki, ba kuma zan gaji da nayi ta jira har sadda Allah Ya so ba."
Murmushi take dagaske. Son Hilal na kara kewaya dukkan ilahirin jikinta. Sun shafe awanni suna hira sannan suka yi sallama. Ta kai duba ga masu yi mata ɗan baki, wasu sun yi bacci yayinda wasu ke waya. Miƙewa ta yi ta maida kan wayar ta ajiye sannan ta faɗa banɗaki don ci gaba da uzurinta.
***
Kamar da wasa, sabo mai tsanani ya shiga tsakaninta da Hilal, tun tana takatsantsan kada Hajiyarsu ta gane har dai wataran ta kama ta tana waya, Hilal ya kira lokacin Hajiya na kusa da wayar ta ɗaga. Kafin ta kai ga magana ta ji muryarta, ta yi mamakin jin kalaman soyayyar da ɗiyarta ke zabgawa. Karshe ta ajiye kan wayar ta leƙa ɗakin, tana tabbatar da ita ce din, kawai ta ja mata kofar. Idanun Ramla ya raina fata. Washegari da safe ta shiga kicin ta iske Rafee'ah na aiki. Tana ganinta ta yi kwafa gami da dariya.
"Kin ɓallowa kanki ruwa yarinya, Hajiya ta ji ki kina waya da Hilal. Za ki yi bayani dallah-dallah."
Ta ƙaraso gami da daga kafaɗarta idanu a waje. Rafee'ah ta ture hannun tana dariya.
"Wallahi kar ki cinyeni kina kallona da wannan manyan idanunnaki kamar mujiya."
Tsukke fuska Ramla ta yi, ba fada take nema ba, so take ta ji abinda Hajiya ta ce.
"Don Allah Sister ki bari, me Hajiya ta ce? Za ta fadawa Abba?"
Taɓe baki Rafee'ah ta yi tana tsamo dankali a cikin mai da cokalin girki.
"Oho, kya dai yi bayani, dama na lura ko karatun da kika saba duk karshen sati kin wani rage saboda soyayya, ke ga Laila ko? Toh ai idan ta fadawa Yaya Muniru ya lakaɗamaki duka kin huta."
Haushin Rafee'ah ne ya soma kamata, kawai ta juya bayan ta harareta ta fice daga kicin din. A falo suka yi kiciɓus da Hajiya tana taimakawa A'isha da tsifar kai tana mitar dama ita ba ta son kitso ya cika ƙanƙanta. Ganin Ramla sai ta daure fuska. Tun daga nan ta sha jinin jikinta. Ta karasa a sanyaye ta gaidata, maimakon ta amsa ta jefamata tambaya.
"Da wa kike waya haka karfe taran dare?"
Kirjinta na dukan tara-tara dakyar ta samu abin fada.
"Wani ne."
"Shi wanin bai da suna?"
Ta girgiza kai, kafin ta amsa mata, Abba ya yi sallama ya shigo, cikin Ramla ya bada wani sauti ƙululu. Ta san Hajiya ta fi Abba rashin fahimta sosai sai dai tana da saukin kai lokuta da dama, shi kuwa Abba akwai tsauri akan hukunci wasu lokutan. Idan ya ce a'a, zai yi wuya ya dawo ya ce eh. Wannan tasa ta tsoraci ya kwace wayarta ya kuma rabata da Hilal har abada.
Bayan an gaidashi, ya shiga yiwa Hajiya faɗan tsifa da safiyar Allah ko karyawa ba'ayi ba. Ta ba da hakuri sannan A'isha ta mike ta rufe kan ita kuwa ta fice wanko hannu.
"Zo nan Ramla, meke faruwa ne ke da Uwartaki?"
Ta mike ta ƙaraso ta zaune gefe sai dai ta kasa magana.
"Jiya ta sanarmin ta kama ki kina waya wuraren tara na dare. Fadamin, wanene shi? Kuma a ina yake?"
Da mamakin sauƙin kan da Abba ya nunamata ta sunkuyar da kai. Tiryan-tiryan ta shiga labartawa Abba wanene Hilal da kuma da niyyar da yake sonta.
Ɗan hade gira Abba ya yi.
"To shi haka ake neman aure? Meyasa ba zai soma yimin zancen ba? Sannan duka-duka a Ss1 kike yanzu Ramla. Kina zaton zan iya aurar dake yanzu? Ko kuwa kina ganin ya dace a cireki a makaranta ki yi aure yanzu ba tare da kin kammala ba? Inada burin naga kun yi karatu koda a gidajen mazajenku ne. Amma ban ce lallai ba, kuma a sanin da nayi maki kema kina da wannan ra'ayin. Me zai sa ki sauya?"
Ta ɗago kai sai a sannan ta kalli Abba idanunta rau rau kamar wacce aka ce kar ta ƙara shiga harkar Hilal.
"Abba dama ya ce yana son zuwa wajenka, ni ce ke tsoro. Kuma na fadamasa ni ba yanzu zan yi aure ba sai na kammala Sakandire."
Murmushin manya Abban ya yi, ya lura dai diyartasa da alama soyayya ta sauyata.
"Kin tabbata kina sonsa Ramlatu?"
Daga yanda ya kira sunan ta tabbatar ba wasa. Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya kara maimaita wa, ta gyada kai. Ya kara maimaitawa a karo na uku, sai kuma ta tsinci kirjinta da bugu da sauri-sauri. Ta ji wani gumi da ba ta san dalilinsa ba ya ketomata a goshi. Wani yanayi na sanyin jiki ya mamayeta. Ta daure ta yakice nauyin da bakinta ya yi a lokacin ta amsa da "Eh Abba." Sai ta ga ya yi murmushi har haƙoransa suka bayyana.
"Shikenan, ki ce ina son ganinsa gobe."
Da toh ta amsa sannan ta mike ta yi daki tana jin muryar Rafee'ah dake jera kwanuka saman ledar cin abinci na mata dariya. Jikin kofar dakinnasu ta jingina, wasu hawaye ta shiga fitarwa da ba ta san asalinsu ba. Damuwa ce ko akasinsa? Murna ce ko bakin ciki? Babu daya da kwakwalwarta ta buɗamata. Wayar ta nufa ta kirashi, ya kuwa dauka ta sanar mishi abinda Abba ya ce sannan ta ajiye wayar ta koma falon. Ana cin abincin amma jikinta a sanyaye yake, abin mamaki sai sannan ta ga sakin fuskar Hajiyar, ba ta san dalilin fushinta a farko ba. Amma ta san dalilin sakin fuskar yanzu na murnar hukuncin Abban ne don har Rafee'ah na tsokanarta bayan fitar Abba akan za ta yi kewarmu. Tana fadin Autarhttps://my.w.tt/ub8deMQ0g9
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
03)
"A farko nayi tsammanin irin samarin zamanin nan ne masu hurewa ƴanmata kunne da zantukan banza da dare. Sai kuma da naji ko waye, naga ashe na gida ne. Toh Allah Ya tabbatarmana da alheri."
Hajiya ke koro wannan bayanin sa'ilin da Ramla ke gyaramata gado ita kuwa tana gaban madubi tana goge jiki ta fito daga wanka. Murmushi Ramla ta yi ta kara maida kai ga aikinta.
"Allah kuwa Hajiya ba ruwansa. Kuma fa yace zan karasa karatuna."
Abin ya sanya Hajiya dariya.
"Ai shikenan ƴar nema, Allah Ya sanya alheri."
Ta amsa a zuci tana dariyar itama.
Hilal ya zo suka yi magana da Abba, sosai yaron ya shiga ransa. Karshe ya ba shi iznin zuwa hira sai dai ya ce ya kasance jifa-jifa saboda ɗaliba ce. Ya kara da mishi iznin turo magabata a tsaida ranar biki. Wannan magana ta fi kowacce yiwa Hilal dadi. Ya dinga godiya. Karshe suka dan taɓa hira da Abba cikin barkwanci, koda zai wuce Abba ya hanashi akan lallai ya tsaya ya ci abinci. A kunyace ya ƙaraso cikin falon.
Tana zaune tare da Rafee'ah a falo, sai ganinsa suka yi. A guje ta mike ta nufi daki don sanya hijabi, ita kuwa Rafee'ah me za ta yi banda dariya.
Ya zauna suka gaisa tana fadin.
"Masha Allah Angon ƙanwata. Allah Ya sanya alheri."
Cike da jin dadin wannan maganar ta Rafee'ah ya amsa yana shafa keyarsa. Abba ya shigo tare da Hajiya sanye da mayafi. Cikin girmamawa Hilal ya kwashi gaisuwa sannan suka dunguma saman ledar da tuni Rafee'ah ta haɗa komai na abincin dare. Abba ya shiga wulga idanu.
"Ina ita Ramlar? Auta kiramin ita maza."
A'isha ta mike da sauri ta nufi hanyar dakinsu. Daidai nan Yaya Munir ya yi sallama, a bayansa Amaryarsa Bilkisu. Hangame baki Yaya Munir ya yi ganin Hilal, shi kuwa sunkuyar da kai ya kara yana dariya ƙasa-ƙasa. Bai mancewa gidansa ya soma zuwa suna ƙusƙus da yar uwarsa Bilkisu game da zuwa ganin Abba. Koda ya tambayi wane Abban, sai ya bagarar yana fadin idan ta yi wari zai sanarmishi. Wannan ta sanya Munir kallon Bilkisu, ta yi mishi dariya cike da kunya ganin idon surukan a kansu. Ya dauke kai bai ce komai ba suka ƙarasa. A wurin cin abincin yake jin abinda ke wakana tsakanin kannennasa. Murmushi kawai ya yi gami da fatan alheri. Ajiyar zuciya Ramlat
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 58