abinda ke ba shi tsoro sai yanda zai yi ya biya kuɗaɗen da ya ci na Chairman. Ƙananun filaye har biyu ya siya ba tare da sanin ƴan uwannasa ba. Wannan tashin hankalin ya sa ya kara magantuwa.
"Haba Yaya, ka mance da auren Ramlatu na baya? Ka mance irin tijarar da ta yi mana? Yanzu Rabi ke har kin mance kina ɗauremata gindi?"
Hajiya wacce ta ke jin ya zamemata dole ta koma wajen Malam Mu'azzam ƙanin babansu na Daura ta yi shiru ba ta ce masa uffan ba. Suka ci gaba da ja in ja, daga ita har Kawu Usman ba wanda ya ƙara tankawa. Kawu Jamilu ya kafe lallai a mayar da kudi yayinda Bello da Haruna suka ce sam ba zai yiwu ba. Wannan ne karon farko da suka yi mishi musu a rayuwa. Ko ba komai shima Haruna ya ci rabonsa. A karshe dai Hajiya ta mike ta wuce sashin Hajja ina ta tarar da Zulaihat zaune su na tattauna maganar.
"Aa, kenan dagaske dai Uwani ta ke za ki zo?"
Hajiya ta harari Zulaihat wacce ita kuma yanda idanun Hajiyar ya yi ja ya ɗaga hankalinta. Ta koramusu duk yanda aka yi. Hajja ta yi salati.
"Ke Rabi! Ban ce ki bari zan je na same su da kaina ba?"
Hajiya ta girgiza kai.
"Ki bar ni kawai Hajja, ni yanzu gobe ma Daura na nufa zan je na sami Baba Mu'azzam da kaina mu tattauna."
"Hakan ya kamata ki yi tun farko ba yanzu da muka dawo ba. Meyasa tun acan shi ba ki mishi bayani ba sai yanzu da ki ka je kike kokarin rushe zumuntarku da ƴan uwanki."
Hajiya ta kalli Mahaifiyarta da mamakin furucinta, ga dai Hajja girma ya ja amma kyawun jikinta yasa ta ke nan ƙyam da ita tubarakAllah.
"Ƙarya na yi kike kallona Rabi? Meyasa za ki tunkare su, ni ban isa ki zo ki fara shawarta ta ba shi ne za ki yi gaban kanki. Yanzu idan wannan ya haɗaku rikici fa? Mun cika alƙawarin da muka ɗaukarwa Babanku kafin rasuwarsa na ganin zumuncinku ya kara ɗanko?"
Hajja ta karashe gami da fashewa da kuka. Hankalin Hajiya da Zulaihatnya tashi, suka shiga ba ta hakuri da neman gafara, dakyar ta sauko ta kuma yi mata fada sosai.
"Idan irin haka ta faru ba'a yanke hukunci cikin fushi. Hakuri ake yi da kuma kai zuciya nesa."
Ta amsa da toh tana sharar kwalla.
***
Zufa sosai ya shiga ketowa Halima, kirjinta na dukan tara-tara. Da gaskiyar ƴar uwarta da ta taɓa gargaɗinta akan son abin duniya.
_*"Watarana idan ba ki yi hankali ba Halima, son kudinki zai kai ki ya baro. Kuɗi sheggun abu ne da idan har ka sa a ranka za ka aikata komai don ka same su, toh ina mai tabbatar maki cewa wataran za su yi sanadin rushe rayuwarka."*_
"Kin yi shiru Halima."
Hajiya Batool ta faɗi tana murmushi yayinda Hajiya Zeenatu ke kallonta cike da nazari tana shakkun ko za ta yi musu abinda suke so.
"Ba fa a kyauta za ki yi wannan aika-aikar ba. Hajiya Zeenatu za ta dauki nauyinki ki je duk ƙasar da kike so ki rayu cikin aminci da walwala. Za kuma ta ba ki gida da mota mallakinki. Ke ba wannan ba, duk abinda kike so za ta yi maki. Kawai ke dai ki aikata abinda muke sonki da shi."
Halima da jikinta ke kakkarwa ta sharce gumin da sanyin Ac bai sa sun fasa zuba ba. Duban Hajiya Zeenatu da Batool take kamar wasu zakuna wanda kwakkwarar numfashi idan ta fitar bai musu ba za su tashe ta daga aiki yanzun. Ta yi shiru tana nazarin kudaden da kuma sauyin rayuwar da za ta samu.
_*"Abu ne da kika jima kina nema, kullum kina cikin kallon hotunan ƴan film da yaran masu hannu da shuni kina kwaɗayin ki samu fiye da haka. Lokaci ne ya yi Halima, mene don ki kashe rai ɗaya tilo kin gudu? Nawa aka yi?"*_
Nan da nan ta samu wani irin sukuni a ranta. Da murmushi ta ɗago ta dube su wannan karon. Wannan ya sa suka dubi juna su ma suka murmusa.
"Hakan na nufin kin amince?" Cewar Zeenatu.
Ta gyada kai tana dariya.
"Ɗari bisa ɗari na amince Hajiya, na tsani Ramlatu sai dai ban zaci zan iya kasheta ba, amma yanzu yanda nake ji zan mata duk abinda ya kama idan har hakan na nufin samun ɗaukaka ta a duniya. Na dai so ace tana raye za ta ga yanda Halima za ta zama, amma ba komai, yaranta za su gane mata."
Ta ba su dariya sosai har da cafkewa. Sai kuma aka shiga tattauna yanda za'a yi komai kuma a darennan. Ta yi shiru tama sauraronsu tana gyada kai. A karshe ta ce.
"Na amince. Duk yanda ku ka ce zan bi na yi."
Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi.
"Yauwa ƴar gari, yanzu bani lambar ita Ramlat din. Ki tabbata kin isa wurin kafin ta je."
"An gama ranki ya daɗe." Tana kai wa aya ta ciro waya ta ba ta duka lambobin Ramlatu guda biyu sannan suka Hajiya Zeenatu ta ba ta kudi har dubu ɗari wai ta ɗan taɓa. Wannan ma ya ƙara zuzuta Halima. Ta fice da murnarta da kuma ɗaukar ALWASHI.
***
Hajiya da Zulaihat suka zauna saman kujera, Ramlat ta fito daga ɗaki da sauri. A farko ta yi zatom shiriritar Ansar ne da ya ke batun dawowarsu. Lokacin ƙarfe shida na yamma, don haka ba su yi wani dogon zance ba sai da aka idar da Magriba.
Zama suka yi Hajiya ta ba Ramlat labarin duk yanda aka yi.
"Ai yau ba gobe ba, ki je ki fiddo kuɗaɗen nan ki kawo su kwana a hannuna. Da kaina zan koma na kai wa Yaya Jamilu."
Ramlat kamar ta rungume Hajiyarta don dadi, ta dinga godiya da addu'a. Murmushi kawai Hajiya ta yi.
"Shikenan ma kinga sai ki ragemin hanya."
"Kai Maman Twins, nan da nan ba mota zan ɗauka ba."
"Haba ƴar Hajiya ƴar gatanta, daure don Allah muje da mota kinga ko yaya kika ɗan ragemin zai min sauƙi."
Ramlat ta yi murmushi.
"Baƙonmu ya zo?" Hajiya ta tambaya.
"Eh tun ɗazu, yanzu ma nake shirin zuwa na kirashi mu yi magana. Wallahi duk ya matsu."
"Wa kenan?" Zulaihat ta nemi ba'asi.
Nan Hajiya ta labarta mata, sosai ta ji ya ba ta tausayi.
Ramlat ta mike ta yiwa AlHassan iso, suka gaisa da Hajiya da kuma Zulaihat, a karshe suka yi mishi addu'ar Allah Yasa a dace da abinda ake nema ya yi ta jin dadi da godiya. Bayan fitarsa Ramlat ta bi bayansa gami da ba Zulaihat hakuri kan yanzun za ta dawo. A harabar gidan suka zauna saman kujera. Ya gyara zaman gilashinsa yana dubanta.
"Nema ne da muka jima mu na yiwa Hussein, yanzu sai abin kusan muke tunanin ya zo ƙarshe idan har yana raye kuma yana hannun matarnan."
Ya ba ta labarin duk yanda suka yi da Rasheed abokin Hussein, ya ƙara da fadin.
"Don Allah my sis idan har da wani abu sa kika sani game da matarnan kar ki ɓoyemin. Jikina yana bani ɗan uwana yana raye."
Tausayi sosai ya bata don har idanunta suka cicciko da kwalla. Ta sharesu.
"Ka kwantar da hankalinka, labari ne mai tsawo kamar yanda na faɗamaka. Shakka babu nasan inda Hajiya Zeenatu ta ke kamar yanda na sani cewa Hussein yana tare da ita tsawon shekarun da ku ke nemansa."
Ai wata irin zabura da Alhassan ya yi ya mike tsaye sai da ya razanata.
"Dagaske kike?! Hussein na hannunta?! Ya akai kika san Hussein din?! Tashi muje ki kai ni wurinsa don Allah."
Jikinsa har rawa yake yi, ga mamakinta ma hawaye ya soma. Dakyar ta kwantar da hankalinsa.
"Don Allah ka zauna mu yi magana. Idan har daga jin wannan ka shiga ruɗani, ta ya za ka iya amsar dukkan labarin da zan ba ka?"
Hakan da ta faɗi sai ya koma mazauninsa yana jero hamdala ga UbangijinSa. Lallai kukansu ya zo ƙarshe. Hawayen Dada zai daina zuba.
"Mami! Mami!!"
Suka dubi yaran, AlHassan na ji kamar ya zanesu don sun katsemishi hanzari. Wayarta ce su ke kokarin miƙo mata. Ta karɓa tana fadin mene.
"Kira aka yi kuma an miki saƙo."
Fadin Ummi, ta karba ta basu umarnin su koma ciki. Har za ta ajiye wayar saman cinyarta, ta hangi suna kamar ma Hussein a karshen saƙon da aka turo wacce lamba ce.
"Yi hakuri don Allah." Ta faɗi a gaggauce, hannu na rawa ta buɗe.
_*"Za su kashe ni. Ramlat ke kaɗai za ki iya taimakamin. Ki zo ki cece ni. Hussein."*_
Ta karanta ya fi sau uku, hannunta na rawa, wani saƙon ya ƙara faɗowa. Adireshin wurin da yake ne kawai.
"Wai meye haka? Innalillahi." Ta furta tana mai mikewa da fashewa da kuka. Da sauri AlHassan ya karɓi wayar don dama ba a nutse ya ke ba. Yana karantawa ya dubeta.
"Hussein ɗina zaa kashe?! Su waye? Taho mu je!!"
Duk a hargitse ya yi wannan kalamin, ya nufi motarsa amma mukullin na ɗaki, don haka a guje ya koma ciki har yana mance ɓangarensa a gidan yana faɗawa falon Hajiya, ganinsa a rude yasa Hajiya miƙewa tare da Zulaihat.
"Lafiya?" Suka nemi sani. Maimakon ya amsa sai ya kasa don haka ya fice, Allah Ya taimaka ya gane dakin, ya shige ya dauki mukullinsa a aljihun kayan da ya fidda. Su Hajiya tuni sun fito harabar gidan inda Ramlat ke safa da marwa cike da tashin hankali tana kuka kamar ranta zai fice.
"Meke faruwa?" Tuni AlHassan ya tayar da mota yana mata horn. Ta dubi su Hajiya.
"Za su kashe Hussein."
"Ki taho mu je ko?!"
Tsawarsa ta sa duk suka dubeshi, su Hajiya na ta salati gami da fadin.
"Kai Hassan kar ka yi tuƙi a wannan yanayi! Ka tsaya!"
Amma ina! Ramlat ba ta ƙarasa rude ƙofar ba ya ja, Baba Maigadi tunda ya ga an tayar da mota ya tsaya bakin gate, ganin ya taho kawai sai ya buɗe masa.
Ita ce ta dinga yi mishi kwatance, sai dai kafin su kai wurin saƙo ya ƙara faɗowa.
"Dakata!" Ta faɗi da babbar murya. Ya ci wawan burki yana jin wani irin mutuwar jiki, idanunsa da yake gani dishi-dishi a dalilin faɗuwar gilashinsa a ƙasan ƙafafunsa, ya ƙuramata su.
"Sun kashe shi?" Yanda ya yi maganar a sanyaye yasa ta dubansa da nata idanun da suka yi kaca-kaca da hawaye.
I just published "BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ffa2oRRGKcb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
47)
"Aa, ba kisa ba ne."
Ta miƙa masa ya shiga karanta saƙon.
"_*Muddin ki ka sake ki ka zo da wani ki tabbatar babu abinda zai hana mu katse numfashin Hussein a doron ƙasa."*_
"Ka bar ni na je ni kaɗai kar su kashe shi."
Ta faɗi da gaggawa, da sauri ya ja motar ya gangara gefe.
"Kinsan me za'a yi? Sauka ki shiga adaidaita sai na bi bayanki."
Ta gyada kai sai kuma ta dube shi.
"Toh kuɗin.." Ba ta karasa ba ya hau laluben aljihu, ya zaro kudin da bai san nawa ba ne ya miƙamata. Har ta sa kai ta fita, ta leƙo.
"Ka kira Hisham ka sanarmasa, ka kuma ba shi kwatance."
Daga haka ta wuce da sauri, Allah Ya taimaka ta samu abin hawa da wuri. Tana shiga yana biye da ita, lokaci guda kuma ya kira Hisham ya sanarmasa komai. Hisham wanda dama hankalinsu ke a tashe sanadiyyar kiran da Hajiya ta yi mishi kan Ramlatun da Hassan. Da gaggawa ya amsa da cewar yana nan tafe da hukuma. Daga haka AlHassan ya kashe kiran.
***
Hisham ya gwada kiran wayar Hussein sai dai duk wayoyinsa a kashe. Wannan ne ya sanya shi ruɗewa, ya kuma gasƙata maganar Ramlat haka yake. Da sauri ya mike ya zari mukulli. Aisha ta tare shi tana kuka.
"Don Allah kada ka je kai kaɗai"
Ya kama gefen fuskarta.
"Please ki kwantar da hankalinki, in sha Allah ba abinda zai faru. Ba ni kadai zan je ba, zan biya wurin ƴan sanda." Daga haka ya samu ta gyada kai gami da yi mishi fatan nasara. Hisham koda ya fito bai tsaya ko'ina ba sai babban hedikwatar ƴan sanda na Bompai. Shiga ya yi kai tsaye ya yi report. Kallonsa sosai Sajan ya yi.
"Me ce ce shaidarka?"
Ya riƙe goshi.
"Saƙo suka yi mata, kuma ƙanwata ce."
"Ina saƙon?"
Hisham kamar ya shaƙe shi ya amsa.
"Na faɗamaka ba ni suka aikawa ba, ita da aka aika wa tana can ta kama hanyar zuwa ita kadai ba tare da wani ba. Don Allah ku taimakamin."
Har Sajan zai magana sai ga D.P.O ya shigo.
"Meke faruwa ne?" Hisham ya dubeshi, baki sake D.P.O ke dubansa.
"Aa, Hisham Muhammad, me ka ke yi anan? Lafiya kuwa?"
Hisham wanda mamakin ganin yayan marigayin abokinsa, Safwan ya kamashi, a gefe guda wani farin ciki marar misaltuwa ya shige shi. Nan ya ba shi labari a gaggauce. D.P.O Musa ya yi salati.
"In sha Allahu za ta kuɓuta, amma na fi tunanin it is just a trap. Gwada kiranta ka ce ta dakata kar ta ƙarasa."
Jin haka Hisham ya shiga kiran Ramlat amma ina! Ba ta ɗaga ba. Wannan yasa D.P.O ya ba sajan umarnin maza a ɗauki mota a je. Ba shiri suka dunguma suka fita Hisham na mishi godiya.
***
Fili ne sosai na makarantar Gwamnati, unguwa ce mai masifar shiru, sai a kwashi tsawon mintuna talatin ba ka ga abin hawa ko ɗaya a wurin ba. Mai Adaidaita na ƙorafi da tambayarta abinda ya kawo ta irin wannan wuri sai dai ba ta tanka masa ba. Kiran Hajiya har da su Hisham da Yaya Munir yana ta shigowa sai dai ba wanda ta amsawa. Text ya faɗo ta yi saurin dubawa hannunta har rawa yake sai dai ba ta fasa addu'a ba,ba ta fasa maimaita addu'a a zuciyarta ba.
'ALLAHUMMA ANTA 'ADHUDEE WA ANTA NAASIREE, WA BIKA UƘAATILU' (Ma'ana: Ya Allah Kai ne Majinginata, kuma Kai ne mai taimakona, kuma da Ƙarfinka ne zan yaƙesu).
_*"Mun hangoki, ki tabbatar da tafiyar mai napep ɗinnan, ki tako ki shigo makarantar ke kaɗai. Ki tabbata kin kashe wayarki."*_
"Tsaya! Ya isa. Anan zan sauka."
Yanda ta faɗa sai da ya tsorata mai napep din har ya juyo ya dubeta, hasken fitilar motar bai sa ha ga fuskar sosai ba. Ya ja ya tsaya ta sauka ta miƙamasa kuɗin.
"Chanji fa?"
"Na bar maka."
Ta faɗi ka tsaye, ya yi godiya ya kaɗa abin hawa ya juya ya tafi yana waigenta da mamaki.
Ta ci gaba da addu'a tana dosar cikin makarantar bayan ta kashe wayar gaba ɗaya. Mamaki da tsoro ta ke yi, me zai sa a kama Hussein a kuma kwo shi irin wannan wuri? Tafiya sosai ta yi har ta soma shiga wuraren ajujuwa.
***
AlHassan ya fito daga motarsa a hankali ya shiga takowa zuwa cikin filin da duhu ya mamaye sai kadan daga haskenfarin wata. A hankali ya ke tafe, madadin ya bi inda Ramlat ta bi sai ya zagaya. Wayarsa a mota ya bar ta gudun kada haskenta ya ankarar da su wanzuwarsa a wajen.
***
Halima wacce ta ci riga da wando baƙaƙe ta kuma sanya mask a gaba ɗaya fuskarta tana hango Ramlat. Yanda Ramlat ke ƙara takowa haka kirjinta ke bugu fat! fat! Ta kai duba ga mutumin da ta sanyawa baƙin kyalle ta rufewa fuska gaba ɗaya. Cikin raɗa-raɗa ta ce.
"Ta taho, ka soma acting."
Ya amsa da "An gama!"
Halima ta ƙara lalubo aljihunta ta fiddo bindiga. Ta nufi Ramlat.
***
Ramlatu dake cikin tafiya sai ji ta yi an rufe mata baki da ƙarfi, ta shiga kokarin kwatar kai sai jin bakin bindiga ta yi a saitin kanta.
"Ina Hussein yake? Na ji idan zai tsira ni ku kashe ni don Allah amma kar ku kashe Hussein."
Daga haka aka soma tafiya da ita har inda wani mutum da ta ga inuwarsa kadan sakamakon hasken farin wata, yana ta walainiya da kai alamar ya jigata sosai a hannunsu.
"Ramlat." Ya faɗi da wani irin sanyi kusan kalar muryar Hussein da ya yi haddarsa.
Kuka sosai Ramlat ta shiga yi. Za ta nufeshi Halima ta ƙara yo baya da ita.
Juyo da Ramlatun ta yi, Ramlat ba damar gudu. Hankalinta na kan Hussein yayinda idanun ke kallon masheƙin da ke tsaye a gabanta.
"Mene ribarku idan kun kashe Hussein? Me ku ke da buƙata?"
Wata dariya Halima ta yi kamar ta yara ƙanana, ta sauya murya.
"Ubanki za mu yi! Ai ke muke nema! Ke kuma aka ce mu kashe ba Hussein ba. Kai Gwaska!"
Tana fadin haka wanda ke zaune da ta yi zaton Hussein ne ya miƙe ya yakice kyallen. Nan ta ga wata sura marar kyan kallo don kamar babu ɗigon imani cikinsa. Ya ƙaraso, yanzun ne tunanin Ramlat ya ba ta cewar tarko ne aka yi mata kuma ya faɗa. Da wani irin sauri ta ja gefe ta yunkura za ta gudu, tuni Gwaska ya damƙe ta tana kokarin ihu ya rufemata baki.
"Ki kashe ta! Me kike jira?!" Ya yi maganar a tsawance ganin Halima ta kasa sarrafa bindigar kamar yanda ya koyamata. Ta runtse idanu ta harba ba tare da saiti ba. Wata ƙara Gwaska ya saki sakamakon samunshi da ta yi a cinya. Ramlat ganin hakan ta ture shi za ta gudu, Halima ta damƙota.
"Ki kashe ta nace!" Gwaska ya fadi iyakar karfinsa yana dafe da cinyarsa. Jin haka AlHassan ya fito daga maɓoyarsa sai dai kafin ya karasa tuni Halima ta ƙara sakin bindigar wanda cikin sa'a ta samu Ramlat a kafaɗa.
"You are under arrest!"
Muryar mutum suka ji. Gaba daya suka juya, fitilun motocin da ke shigowa gurin ya haskewa Halima fuskar AlHassan. Ta zaro ido ta cikin mask din fuskarta. Hussein ne?! Hajiya dama karya ta yi da ta ce ta saka shi bacci?
Ganin haka ta yunkura za ta gudu sai dai da wani irin zafin nama na ɗaya daga cikin ƴan sandan, ya cafketa tana kiran wayyo Allah. Ramlat dake zube anan tana gani dishi-dishi hannunta na dafe da kafaɗarta da Gwaska ya samu. Ba shiri ta zube a ƙasa. Wani irin sunguma da AlHassan ya yi mata a gigice yana ambaton sunanta, amma ko motsi.
"Kai ta mota mu je asibiti!" Hisham daga bayansa ya faɗi a gaggauce. Kafin ka ce me, sun isa mota tuni rigar AlHassan ta ɓaci da jini. Hisham ya bada umarnin tafiya da su Gwaska da nufin zai je station din daga baya. Suka tafi da ɗan sanda saboda ba da shaida.
Munir wanda ya taho, suka yi waya ya ke sanarmasa halin da ake ciki, hankali a tashe ya juya kan abin hawa ya nufi asibitin da Hisham ya kwatantamasa.
Kafin su je ya riga su isa, don haka suna zuwa ya tarbesu. Shi ya karɓi Ramlat ya ƙarasa ciki da ita. Sai dai aka kammala dukkan wani sa hannu aka hau ceton rai da gaggawa.
Munir ya kira gida ya faɗawa Zulaihat wacce ke faman kiransa a waya. Jin abinda ya faru daga ita har Hajiya suka kasa zama gidan suka nufo asibitin.
"Laifina ne, meyasa na bar ta ta je ita kaɗai ban maramata baya ba?"
"Ka daina faɗin haka Hassan, rai da ajali duk a hannun Ubangijin al'arshi su ke, kaddararmu ce haka. Mu yi fatan samun saukinta." Hajiya ta faɗi tana mai sharce hawayen saman kuncinta.
AlHassan hankalinsa sam bai kwanta ba, ga tsananin son ganin Hussein da ya ke yi. Yanzun da ya san inda yake sai ya ke jin kewarsa ta ƙaru. Fitowar Likita ne yasa suka dubeshi.
"Alhamdulillah an cire harsashin, ba dai ta farfaɗo ba. Amma muna sa ran komai zai zo da sauƙi. Dafin bai shiga jikinta sosai ba."
"Alhamdulillah." Suka furta kusan a tare. Hajiya ta dubi Zulaihat bayan sun gama addu'a da godiya ga Allah.
"Uwani maza ki wuce Muniru ya sauke ki gida, dare ya yi. Ni zan tsaya anan da ita."
"Aa Hajiya, ba za'a yi haka ba. Su Ummi da aka bari a gida fa?" Cewar Zulaihat.
"Ina ce Ladidi na nan? Zan ƙarasa na nemi alfarma ta kwana yau dai ɗaya. Daga nan zan haɗaku a waya idan da abinda ki ke buƙata sai na dawo na kawomaki. " Faɗin Munir yana mai ƙarashewa da mayar da akalar zancen ga Hajiya.
Suka yi na'am, Hajiya ta ƙara duban AlHassan.
"Hassan sai hakuri ka ji? A kara godewa Allah tunda a baya ma ba'a san inda yake ba. Yanzun kuma da Allah Ya nuna in sha Allahu komai zai zo karshe. Kar wannan ya dameka. Ya kamata ka wuce gida duk ka ɓata jikinka da jini."
AlHassan ya jinjina kai yana gyara zaman gilashinsa, suka yi sallama aka tafi aka bar Hajiya ita kaɗai ta na jiran likitoci su kammala su ba ta umarnin shiga.
A harabar asibitin bayan tafiyar Munir da Zulaihat, Hisham ya dubi AlHassan.
"Dama nayi mamakin ta yanda za'a ce wani abin zai sami Hussein. Ba wai ba za ya taɓa faruwa ba ne, sam aa, sai dai idan har zargina ya tabbata da hannun Hajiya Zeenatu a abinda ya faru ga Ramlat to ba zai taɓa zamtowa an riski Hussein a wurin ba. A irin son da Zeenatu ke yiwa Hussein ba za ta bari a haɗa baki a cutar da shi ko ya ya ba."
"Kai ma kana da labarin Hussein kenan?"
AlHassan ya tambaye shi da gaggawa. Ya gyaɗa kai yana duban agogo.
"Ina da labarin komai, na taƙaice maka Hussein aminina ne, bani da aboki sama da shi a faɗin duniya. Sai dai kuma ya dace ko me zamu yi kada ya wuce gobe, idan ba haka ba za mu rasa damar mu."
"Me kake nufi?"
Tiryan-tiryan Hisham ya ba shi labarin duk abinda ya sani dangane da Hussein. Ya ɗora da faɗin.
"Babu damar a yiwa Hussein zancen ƴan uwansa, ba ya so. Da zarar ka tambaye shi game da asalinsa, kansa zai ɗau zafi ya sauya gaba ɗaya. Ransa kuma idan ya yi dubu toh zai ɓaci. A ranar idan mutum bai yi dagaske ba girmansa zai iya faɗuwa a idanun Hussein."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Mace ce? Ita ta rabamu da Hussein? "
"Hum, sai addu'a." Hisham ya furta, a ƙasan ransa yana jimamin yanda AlHassan zai ji idan ya gane da sa hannun Kawunsa ciki. Hakan yasa bai faɗamasa ba har sai gaskiya ta yi halinta.
"Ya za'a yi na gan shi yanzu? Bana so su kai ga barin ƙasar."
"Kada ka damu, a gobe da safe in sha Allah zan haɗaka da ɗan uwanka. Za ku ga juna."
Murmushi AlHassan ya yi mai haɗe da dariyar farin ciki, kasa hakuri ya yi sai da ya rungume Hisham yana murna.
"Na gode, Na gode sosai. Allah Ya bar zumunci."
Hisham ya yi dariya gami da dukan kafaɗarsa.
"Ameen. Kar ka samu damuwa. Ka kara godewa Allah, sannan Ramlat. Ba karamin namijin ƙoƙari ta yi akan ɗan uwanka ba."
Murmushi sosai AlHassan ya yi tare da fatan Allah Ya ba ta lafiya.
Hisham ya amsa kafin su yi sallama, shi ya nufi gida, Hisham kuwa ya zarce Police Station don jin abinda ake ciki.
***
_*LAMIƊO CRESCENT*_
Safa da marwa ta ke faman yi a tsakar falon, ta ɗauki waya ya fi a ƙirga. Kiran Halima ta ke jira kamar yanda suka yi alƙawari.Ta kira Hajiya Batool ya fi sau goma don ta ji ko sun yi waya amma shiru ka ke ji, Malam ya ci shirwa. Ta kara kai idanunta kan wayoyin Hussein da ke ajiye saman kujera. Baƙin kishin Ramlat ya ƙara ƙarfi a zuciyarta. Ta gwada amfani da yatsarsa ta buɗe wayar, hakanan ta gwada shiga lambobin Ramlat, HEART da ta gani a rubuce ya sanha ta saki ƙarar da har sai da John suka fito daga kicin zuwa falo. Ta dakamusu tsawar da dole suka koma.
Hajiya Zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani malolon abu ya tokaremata maƙoshi. Awanni biyu kenan da ta ba Hussein lemo ya sha wanda ya yi sanadiyyar baccinsa, a wannan lokacin ba abinda ta ke burin ji sai saƙon mutuwar Ramlat. Wayarta ta yi ƙara da wani irin zumuɗi ta duba. Tsaki ta ja ganin lambar Kawu Modibbo, sai da ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 40 Chapter of 58