har suka dawo.
***
Ta shiga binsa daga daki zuwa falo, da ya gaji sai ya tsaya yana kallonta. Ta turo baki kadan.
"Baby, meye wai?"
Ramlat cike da shagwaɓa ta amsa.
"Muhibbat ce fa Baban Ummi. Ta tako gidannan ya fi a ƙirga. Har ta haihu a yi suna ban je ba? Gaskiya ban kyauta ba wallahi."
Ya taɓe baki, ta kuramishi idanu tana murmushi cike da so da kaunarsa da yanzun ta ke ji ba kaɗan ba. Ya ɗan murmure hakanan ya yi haske kadan ba kamar a baya ba. Kasuwa ta dan dawomishi daidai don yanzun yana maida hankali sosai.
"Nayi zaton ma asibiti za ki cemin za ki, ashe ba haka ba ke yawo kike son fita."
Ta daure fuska.
"Ni lafiyata kalau, na fadamaka ba ba ciki bane. Ko ka manta na yi planning?"
"Planning wane iri ne wannan da za ki dinga amai da kwadayi? Yaushe rabonki ma da al'ada?"
Ta numfasa ba don ta wani dauki abin da muhimmanci ba don dama idan ba ta mance ba Nos ta fadamata cikin side effect din maganin har alamomin masu ciki ko daukewar jini zai iya jazamata.
"Shikenan zan je, amma daga nan zan wuce gidan Muhibbat. Don Allah!"
Ta fadi da sauri ganin yana kokarin cewa a'a, ya yi dariya.
"Shikenan, a gaishesu. Ki dai tabbatar kin je asibitin."
Ta rungumeshi gami da yin godiya. Ya bata sumba a kunci gami da bata kudin mota da na ganin likita.
Yana fita itama ta shirya tsaf ta goya Ansar ta fice.
***
RUBUTACCEN I just published "BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/pcYjI4bZBab
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
27)
"Ke kam sai ayi magana ki yi shiru."
Maganar Muhibbat ya katsemata tunani a karo na barkatai, ta kakalo murmushi ta dubeta.
"Kai ban ji ba."
"Cewa nayi ina Ummina?"
Cike da kaunar yanda Muhibbat ke sonta da abinda ta haifa ta amsa.
"Tana can gidan Hajiya."
"Kai jamaa, da alama dai Hajiya ta kwacemana Ummi."
Dariya suka yi lokaci guda. Hira dai ta yi hira har hakan ya mantar da Ramlat damuwarta na cikin da ke jikinta. Duk da amsar da Likita ya ba ta sadda ta mishi tambaya hakan bai gamsar da ita ba sai da ta ƙara tambayar Muhibbat.
"Wai nikam Sis, dama ana iya samun ciki ko anyi family planning?"
Muhibbat ta dubeta, me za ta yi ba dariya ba. Yi ta ke ba kakkautawa har sai da Ramlat itama ta dara.
"Mene wai na dariya toh?"
"Ah ba komai fa. Sai dai na harbo jirginnaki. Ai idan Allah Ya so ikonSa, ba planning ba, ko mahaifar aka juya sai ki ga an samu ciki. Meyafaru?"
Jiki a sanyaye ta ce.
"Implant na saka, abin mamaki wai ana yimin test aka ga ina da ciki. Wai gocewa ya yi."
Jinjina kai Muhibbat ta yi.
"Ana haka, na sha ji ana fadin haka. Wata har allura ta yi amma bai karɓeta ba sai ga ciki. To ke me zai dameki? Ai ko ba komai Ansar ya shekara."
Ajiyar zuciya ta saki, kuma fa hakane. Idan a baya munanan ɗabi'un mijinta ne ta ke gudu, yanzun komai ya kau, ya zama labari da yardar Allah.
Muhibbat ta ci gaba da ba ta shawara akan kar ta damu ba komai. A karshe ta ji zuciyarta ta yi sanyi.
Sai wuraren yamma ta yi mata sallama ta bar gidan bayan ta diremata turmin atamfa cikin wadanda ta samu na barkar Ansar. Godiya sosai Muhibbat ta yi kuma ko kadan ba ta raina ba duk kuwa da cewar ta fi karfinsa. Har kofar falon ta yi mata rakiya suka yi sallama.
***
Juyi ya shiga yi da ita yana karawa, ita kuwa banda dariya ba abinda ta ke, hakan da ya yi ya zo mata a hagunce don ta yi mamaki. Ba ta zaci ganin irin wannan farin cikin a fuskarsa ba. Farin ciki ne da ya taho tun daga ƙahon zuciyarsa. Ya shiga sumbatar duk inda bakinsa ya kai a fuskarsa. Ta kauce gami da faɗawa kan kujera tana dariya lokaci guda tana mai watsa mishi harara.
"Kai don Allah Abban Ummi. Duk rawar ƙafar don cikin ne? Ciki na uku?"
Zama ya yi a gefenta gami da riko hannunta.
"Bar ni na yi murna kinji ko? Kyaleni Baby. Allah Yasa ki haifarmin mace na sanyamata sunanki. Kin cancanci komai daga gareni."
Ita dai murmushi take tana kara godiya ga Allah da tarin ni'imominSa wanda ba ya yankewa. Yau Aliyu ke ɗoki da zumuɗi mai yawa haka saboda ance tana dauke da juna biyu?
Kumatunta ya ja wanda ya maidota hayyacinta. Suka yiwa juna murmushi kafin ya jawota jikinsa ya soma aika-aika😜. Kukan Ansar ne da ya fado daga saman kujera cikin bacci ya katsemusu komai, kusan a tare suka isa wurinsa ya rigata daukarsa. Safa da marwa ya shiga yi yana jijjiga yaron, hakan ya bata damar tsayawa ta kurawa Aliyun idanu cikin duniyar tunani. Kwallar farin ciki suka cikamata idanu ta sharesu. Abbanta ya faɗomata a rai, ta tabbatar da yana raye zai fi kowa farin cikin shiryuwar Aliyunta.
Ta so ace Abba da Aliyunta sun yi rayuwa kamar na ɗa da uba tun a baya, ta so ganinsu tare a zaune suna hira da dariya. Sai dai kuma Allah bai nufi hakan da faruwa ba.
***
Labarin cikinta har gidansu, ta sha dariya wajen su Zulaihat da suka hadu a gida.
"Dama za ki ka da yin Ubangiji ne? Kallonku kawai nake."
Hajiya ke wannan zancen tana gutsirar goronta wanda ya zamemata jiki.
Ramlat ta yi dariya.
"Yanzu dole ki yaye Ansar fa ko?"
Rafee'ah ke zancen tana dubanta.
"Anya kuwa? Ni gani nake kamar ba matsala tunda ta ce likita bai hana ba."
Fadin Zulaihat.
"A'a ba zai yiwu ba, dole ma a yayeshi. Idan ya rame itama ta rame fa? Ai dukkansu abin ba zai zo musu dakyau ba." Hajiya ta furta cike da kulawa. Kulawar da idan Ramlat ta dubi ƴan uwannata ta ga dukkansu a cikin lamuranta suka tsoma baki sai ta ji dadi da farin ciki sun lulluɓeta.
A ranar dai haka ta koma gida ba Ansar don Hajiya ta ce ba zai yiwu ya ci gaba da shan mama ba. Har da ƴar kwallarta na tausayin yaron, don ma dai yana da kumarinsa.
Ganinta ita daya Aliyu ya ci dariyar da ta ishe shi.
"Ai koda ba ki yayeshi ba, da hannuna zan daukeshi na miƙa wa Hajiya ko na kaiwa Amarya shi. Ta ya za ki zauna kina ci gaba da shayarwa ga ciki? Ba zan yarda ba."
Ta turo baki ta shige wanka ta kyaleshi zaune gefen katifa.
Allah Ya taimaketa ba ta yi ciwon yaye ba sai dai sun kara ciccikowa.
Hankalinta ya kwanta ta koma rainon cikinta da zuwa makaranta abinta.
***
BAYAN WATANNI TAKWAS..
Binsa kawai take da kwando yayinda yake aikin lodar kayan jarirai kala-kala unisex.
"Don Allah ya isa haka Sweet Aliy."
Bai ko kalleta ba balle ya saurareta.
"A ina ka samu kudi haka?" Ta ƙara jefamasa tambaya don ita kam abin ma tsoro ya shiga bata duk kuwa da ta san yanzun Aliyun na samu fiye da baya. Ganin ta ƙi ɗaga ƙafa ta bi bayansa, ya janye kwandon ya yi gaba ya kyaleta yana duba wasu turaruka na jarirai.
"Wannan ba Ramlatu bace?" Jin an ambaci sunanta ne yasa ta juyawa bangaren da ta ji muryar. Kallon kallo suke da juna. Kamannin Hilal sak a fuskokinsu. Tuni ta gane su waye, Anti Fareeda da sai Murja da ƙaton ciki wanda haihuwa yau ko gobe.
Ta saki murmushi sadda suka ƙaraso gareta, Murja ko gaisuwarta ba ta amsa ba ta jefomata tambaya.
"Kema wani cikin ne da ke? Bilki ta ce haihuwarki biyu yanzu ta uku. Kin ji labarin auren Hilal ko? Kinga Allah ba azzalumin bayinSa ba ne."
"Dadina da ke Murja wataran kamar yarinya kankanuwa, ke har sai an ce miki ciki gareta? Saukinta daya ma na sunnah ne. Uhum, gwara ma da aka yi yunwa halin kowa ya fito. Da yanzun da auren Hilal za ta haifi shegu."
Kallonsu take, kamar wacce aka ƙullewa baki ta kasa magana, kirjinta wani tafarfasa yake yi. Ta juya kawai ganin idanunta ya ciki da kwalla. Fareeda ta kara magana.
"Kinsan ma naji ance mijin ƙanjamau ne da shi. Ga duka na safe daban na rana daban."
Ta ƙara daga kafarta daidai sadda Murja ta kara magana.
"Ai dama Allah ba azzalumin bayinSa bane, tun ka aje ko'ina yarinya ta soma ganin sakayya. Ni dama kishiya ya ƙaromata muga ta karshen soyayya."
Tuni ta yi gaba ta bi bayan mijinta kamar ba ta ji ba. Karo suka kusan yi, da sauri ya riƙe kafarta. Kallon kallo suke da juna, ya sa hannu ya gogemata hawayen.
"Meyafaru? Keda wa? Ina can ina kokarin biyan kudi na waiga ban ganki ba. Lafiya?"
Ya ƙarashe yana daga wuya kamar zai hango abinda ya ɓata rannata, bai ga kowa ba sai wasu mata biyu dake kallonsu.
"Ba komai fa, abu ne ya shiga idona."
Ya daure fuska, zai kara magana ta yi saurin giftawa ta gefensa ta soma tafiya gami da fadin.
"Don Allah mu je."
Bai bi ta kanta ba ya wuce zuwa bangaren matan yana dan dube-dubensa, so yake ya ga ko zai ga fuskar da ya sani cikin ƴan uwansa ko na Ramlat din amma babu ɗaya. Zai wuce ne ya ji wata a gefensa kamar da rada tana fadin.
"Ko shi ne mijinnata?"
Ya waiga ya kara kallonsu, shi ɗin suke kallo dai, hakan ya ba shi tabbacin su ne silar hawayen Ramlatu. Ganin dai zargi ne ba shi da tabbas ya sanya shi watsamusu banzan kallo ya wuce, duk suka sha jinin jikinsu suka kauda kai.
"Kinsan fa mashayi ne, kar ya kawomana duka." Fadin Murja a tsorace bayan tafiyarsa.
"Atoh, gwara ni banda komai, ke kam naƙudar dole zai sanyaki ko ya kaiki lahira."
Suka tuntsire da dariya sai dai fa ba haka suka so ganin Ramlat din ba. Alamun jin dadi sun bayyana a fatarta da kuma jikinta, sun so ganinta a yamushe yanda za su fi jin dadin kai labari, amma hakan ma da suka yi mata sun dandana mata wani bakin ciki. Wannan yasa hankali kwance suka ci gaba da siyayyar abinda ya rage ga Murja.
***
Tun a hanya yake masifarsa jin diramar da ta yi a shagon da ya uwan Hilal, har suka dawo gida, ita dai ba ta iya tankawa ba banda hakuri da take ba shi. Koda suka shiga ita ya bari da baza kayan tana kallo, kallon take amma zafin kalaman su Murja ya tsayamata a ƙahon zuci.
"Mtsw. Sai ki zauna ki yi ta kuka akan abinda ba wanda ya isa ya sauyamaki. Ko mene ya riga da ya faru, akwai dan iskan da zai hana. Don ubansu me suka ce? Da shege za ki haifa a gidan Hilal din ko? Dama hakan ce ta faru naga uban da zai hanani dauko ƴaƴana!"
Ta dubeshi a razane, sai kuma ya shiga istigfari. Ransa sosai ya ɓaci don shi a duniya ya tsani a yi mishi abu bai rama ba. Ya so ace a gabansa suka yi yanda zai zazzagamusu bala'i ya nunamusu haukartasa.
A karshe kuma ya koma lallaɓata, ya shiga jan ta da hirar Baby gami da nunamata kayayyakin su ka shiga dariya zuciyarsu ta yi sak.
***
Rayuwarsu abin sha'awa, zama na so da kauna da aminci irin wanda Ramlat ta jima tana mafarki, Allah Ya tabbatarmata da shi. Tana zuwa makaranta abinta, Amrah na nan ta ƙi kula kowane saurayi don ta rantse sai ta kammala karatunta.
Babu laifi suna zumunci da yan uwan Aliyu yanzun musamman wadanda suka hada uwa. Sukan zo itama ta jajjemusu tare da Aliyun.
A yanzun ba abinda ya fi burgeta sai zaman karatun da Aliyu ke dauka duk karshen sati wurin wani Limamin unguwarsu.
Haihuwar Ramlat ya kama a watan azumin Ramadana, alokacin bai fi sati uku ya yi saura a kama azumin ba.
A sannan karatu ya dau zafi don su na aji na biyu zango na farko sakamakon yajin aikin da aka dinga tafiya wanda hakan ya ɗan kawomusu cikas a karatun.
Wataranar Asabar tana zaune a tsakar gida ta dage tana research a Google na wani project da aka bata. Aliyu na daga gefenta ya kwanta saman filo ya zubawa sararin samaniya ido yana kallo. Shirunsa da ta ji ya yi yawa ne yasa ta dubansa. Ganin hankalinsa ma ba ya kanta ne ya sa ta mika hannu ta ɗan matsa yatsun ƙafarsa suka yi ƙara. Ya juyo ya dubeta gami da ɗan lumshe idanunsa ya bude.
"Lafiya? Me kake tunani?"
Murmushi ya ɗan yi.
"Rayuwa nake tunani Baby. Duniyar tsoronta nake kara ji, tuna watarana zan mutu fargaba hakan ke sanyani. Idan na zauna ina lissafi sai na ga kamar ban taɓa aikata abin kirki ba. Tun ina saurayi iyayena ke shaƙar bakin cikina, na tsoma kaina a harkar shaye-shaye. Na dauki rayuwar da ba tawa ba, yawo da ƴaƴan masu hannu da shuni, na ɗorawa kaina. Na baƙanta ran jama'a da dama, a karshe ko ban aikata zina ba, na shafa jikin matan da ba nawa ba. Idan na tuna akwai ranar da zan koma ga Allah, a binne ni cikin raminnan, a doramin itace a kara bina da kwali sannan a rufamin ƙasa a fuska, ina shiga matsanancin tashin hankali Baby. Daidai da ɓangarenki na cutar da ke, na kasa daukar nauyinki, na kasa kula da lafiyarki, na kasa ciyar da ke a lokuta da dama kamar yanda sutura da shanki bai cikin damuwata a wasu lokutan. Ban tsaya anan ba na jawomaki abin gori, na kashe aurenki don na rayu da ke. A sanadina iyayenki sun zubar da hawaye a kanki, nayi amfani da karfin son da kike yimin na yaudareki. Anya duk wannan tarin saɓon da nayi, Allah zai dubeni Ya sanyani sahun muminan bayinSa?"
Kallonsa take tun soma maganarsa, kamar yanda take fitar da hawaye, haka shima yake fitarwa. Girgiza mishi kai ta shiga yi. Ta ture litattafan ta karasa gareshi gami da damƙe tafin hannunsa cikin nata.
"Kar ka kara irin wannan kalaman, Ubangiji Mai Rahma ne. Wanda ma bai tuba ba, kira Ya ke yi akan ya zo ya nemi gafararSa zai yafemishi, ballantana wanda Ya kusantoShi da neman gafara ba? Ai shi At-Tawwabu ne Mai yawan karɓar tuban bayinSa. Koda wasa kar ka sake zuciyarka ta jefaka cikin kokwanto Allah Ba zai gafartamaka ba. Ka yi irin tuban da Ya ke so, ka kuma nemi gafarar wadanda ka aikatawa ba daidai ba. Me ya fi wannan dadi? Abinda ya riga ya faru ba mu isa mu sauyashi ba."
Gyada kai Aliyu ya shiga yi sai kuma ya yi shiru, Hilal, shi ya faɗomasa a rai.
"Na nemi wata alfarma?" Ta tsinci muryarsa karo na biyu. Ta kara dubansa ta gyada kai.
"Hilal, ki nemar mini gafararsa, ki ce ya yafemin koda ace Allah bai ban ikon saduwa da shi ba a rayuwa."
Ji ta yi gabanta ya fadi, ta daure fuska gami da harararsa.
"Bana son irin wadannan kalaman naka. Kana magana kamar wanda ya ga mutuwa."
Ta ba shi dariya sai ya murmusa gami da shafa fuskarta ya sumbaci hannunta dake sarƙe da nashi.
"Ke kuma ba kya so ko me? Malam ya cemin hakan na karawa Bawa imani. Kinga yanzu ko ba komai mun samu lada. Ke tsaya ma, sai fa ki ce za ki yi aure idan na mutu ko? Duk wannan tarairayar wani za ki yiwa? Caɓ!"
Maganar ta ba ta haushi, fisge hannunta ta yi ta dauki littafi ta dauka ta shiga makamishi a kirji.
"Bana so! Bana so! Ka daina yimin wannan zancen."
Ya riƙe hannuwanta gami da jawota jikinsa yana dariya.
"Allah Ya huci zuciyarki toh. Na tuba, ai mutuwar ma sai dai ta daukemu tare In sha Allah. Sha kuruminki."
Sati uku da wannan maganar....
***
DUK MAI RAI...
Ranar juma'a wanda ya kama acikin goman farko na azumin Ramadana, tun tashinsu take jin wani irin nauyin jiki, haka kawai ta ke jin babu dadi daga yanayin kallon da Aliyu ke bibiyarta da shi. Daɗin daɗawa, duk inda ta sanya ƙafa yana biye da ita, idan ta yi magana sai ya koma wurin yaransa wanda tuni ya cire kunya ya je gidan Hajiya ya kwaso su.
"Abban Ummi, lokacin sallah ya yi, ka tashi ka je tunda yau dai ka ƙi kasuwar."
Ya sauke Ansar daga saman cikinsa ya mike zaune. Daga shi sai jallabiya doguwa. Dan guntun tsaki ya ja yana murmushi.
"Yau din ne ganinan dai Baby. Jikin babu dadi kamar dai mai fama da zazzaɓi."
Ya ba ta tausayi.
"Toh ko za ka karya azumin ne?"
Girgiza kai ya yi lokacin da ya mike.
"Haba dai? A'a. Kedai ƙatuwar gandiya ki yi ta shan abinki, daga baya na sha dariyar ramuwar da za ki yi."
Ta ɗan harareshi kafin ta dubi su Ummi.
"Oya ku zauna nan ina zuwa."
Daga nan ta mara mishi baya zuwa dakin, wanka ya shiga don haka ta fiddo mishi farar shadda da hula. Yana fitowa ya shiga shiri.
"Ya kamata muje Daura idan kin haihu."
"Toh." Ta ba shi amsa gami da ƙarasawa ta shiga taimaka masa wurin shiri. Kallonta kawai yake bayan ya sanya kaya tana sharce mishi gashi da comb. Jikinta ya yi sanyi da kallon, ta hura mishi idanu.
"Wai lafiya Abban Ummi?"
Ya sauke ajiyar zuciya.
"Ba komai. Bari na gaggauta tafiya ko ya ya na samu huɗuba."
Ta amsa da toh, ta dauki darduma ta feshe da turare ta miƙa mishi, har kofar falon suka yi mishi rakiya. Ya dawo da baya ya dubeta.
"Kinsan me za ki dafamin yau?"
Kai ta girgiza.
"Ɗanwaken nan mai ɗan karan daɗi."
Ta yi dariya.
"Mutum ya yi azumi ya nemi ɗan wake? An shiga uku da wannan dan waken."
"Kema kinsan ina sonsa."
Ta gyada kai tana dariya, ita kuwa ta san yana son dan wake, har tayata sakin ɗanwaken yakan yi.
"Sai na dawo."
Ta amsa gami da yi mishi addu'a kafin ta koma ciki.
***
Tun tana kallon ƙofa har karfe uku, kwakwalwarta ta bata ya biya wani wurin daga masallaci hakan ne yasa ta kwantar da hankalinta ta ci gaba da shirin kayan shan ruwa. Ba ta jin dadin jikinta dauriya kawai ta ke, da ace ta cika watanni tara cif, da sai ta ce naƙuda ne duk da cewar yanzun ma za ta iya haihuwa don sati kawai ya rage ta shiga watanni tara.
Kofar gidan da ake kwankwasa ne yasa ta saurin baro kicin din da murnarta ta fito, jikinta ke bata Aliyun ne sai dai ta yi mamakin dalilin da yasa bai tafi da nashi mukullin ba.
Maimakon Aliyun, sai ta ji muryar makwafcinsu Baban Maryam.
"Baban Maryam ina zuwa."
Ya amsa da toh, ta koma ciki ta dauko katon hijabi ta rufa, kirjinta na bugu, dakyar take jan ƙafa har ta karasa ta bude.
"Amm, dama lambar wayar Malam nake so."
Ta gane Malam, mahaifin Aliyu. Ba ta yi mamaki don yasan waye Malam ba saboda kusancinsa da Aliyu a unguwar ya fi na sauran makwabtan. Dafe kirji ta yi.
"Lafiya?"
Murmushi ya kakalo.
"Lafiya kalau Alhamdulillah. Wata ƴar magana zamu yi."
Ta ɗan yi shiru, kamar ta tambayi mijinta sai ta ga rashin kyautuwar hakan. Komawa ciki ta yi ta dawo da wayarta ta bude lambar hannunta har rawa yake yi ta miƙa mishi ya kwafe. Godiya ya mata sannan ya wuce, dakyar ta iya rufe kofar.
Shi kuwa Baban Maryam gidan ya shiga a gaggauce ya nemi matarsa Hajara ta je ta zauna tare da Ramlat don Aliyu ya rasu a masallaci. Allah Ya taimaka tare suka tafi kuma sun samu zama cikin masallacin. Kuka Hajara ta sanya gami da salati. Ya yi saurin dakatar da ita.
"Ya isa don Allah kar ta ji ta razana, yanzu yana can mun kai shi asibiti don a tabbatar ko mutuwar ce. Ta gyada kai sannan ta rarumi Maryam ta goya a baya ta fice gidan Ramlat.
***
Ramlat na ganinta sai ta kara rudewa, dakyar Maman Maryam ta iya danne kuka da damuwarta ta shiga jan ta da hira da dariya kamar gaske. A karshe ta samu ta ɗan sake sai dai bini-bini za ta dubi wayarta, a karshe da ta gaji ma duban Maman Maryam ta yi.
"Wai ke kam ba ki da aiki yau ne? An fa yi la'asar. Ki tashi."
Tausayinta ya kama Maman Maryam, tun zuwanta ta hangi damuwa tsantsa a saman fuskarta. Tasan ko ba komai jikinta ne ya bata. Maman Maryam ta daure ta harareta, za ta bada amsa kenan aka shiga kwankwasa kofar gidan. Kusan ma sakin ludayin miyar ta yi don yanzu a ɗan karamar cylinder na gas take girki, Maman Maryam ce ta karasa ta kwashe mata sauran ɗan waken ta kashe wutar. Ta bi bayanta tana salati don tasan yau kam mai faruwa ta afku, rabuwa ta har abada ce ta samu Ramlat da Aliyunta.
***
"Hajiya? "
Abinda ta ce kenan da mamaki ƙarara, idanunta suka cicciko da kwalla, ko'ina na jikinta ya fara rawa.
Hajiya ta shigo gidan sosai sai Umman Amrah. Ta ja hannunta suka shiga ciki ba ta ko tsaya amsa tambayoyin da Ramlat ke jifansu da shi ba.
"Meyafaru Hajiya? Kin yi shiru. Ki fadamin. Umma menene?"
Babu mai amsawa.
Sai da suka shiga ciki suka zaunar da ita suka yi mata doguwar nasiha da ya sanyata kuka, Abba kawai ta shiga tunowa. A karshe suka sanarmata labarin mutuwar Aliyu. Abin mamaki sai kukan ya tafi, ta shiga murmushi, murmushi sosai.
"Ramlatu, kinji abinda na ce?"
Hajiya ta fadi a ɗan tsorace don a zatonta ko taɓuwar hankali ce. Ramlat ta girgiza kai ta a murmushi gami da jan majina.
"Ya yi mutuwar da bai kyautu na zubar mishi da kwalla ba ai, ya yi irin mutuwar da kowane DAN ADAM zai so ya samu irinsa. Da azumin Ramadan a bakinsa, cikin dubban jama'a, a hanyar bautar UbangijinSa. Idan ba godewa Allah ba, na yiwa Aliyu addu'a, me ya kamata na yi?"
Wannan tawakkalin nata ya raunana zukatansu, ta kuma burgesu ainun.
Suka wuce da ita zuwa gidan iyayen Aliyu inda anan aka kai gawar Aliyun. Abulle tun da aka yi mutuwar tana kwance ba ta san inda kanta yake ba. Maza da mata kuka ake yi akan rashin Aliyu. Aliyun da dama a cikinsu suka tsana.
Tuni an mishi sutura, kowa kallonta yake da mamakin yanda ta daure. Da katon cikinta ta durkusa gaban gawar Aliyu ta yi mishi addu'a sannan aka ɗaukeshi a makara aka fita da shi. Wannan fitar ce ta daga hankalinta, ta sani idan aka tafi an tafi kenan. Ba za ta ƙara ganinsa ba, ya bar gidan kenan bari na har abada. Tun tana ganinsu daidai har ta soma ganin bibbiyu kafin ta zube a wurin.
Koda ta farka bayan an yayyafamata ruwa, sai ta farka da wani irin azababben naƙuda. Tuni aka rarumeta zuwa asibiti.
A wannan yanayin Ramlatu ta haifi ɗanta namiji.
***
Rashin Aliyu babban rashi ne da ba za ta taɓa mancewa ba. Ta yi rashin Abba, ta zo ta rasa Aliyunta. Mutane biyu mafi girma da daraja a gareta. Cikinsu ba wanda bai taka rawa a rayuwarta ba. Sai a sannan ta yi kuka iyakar yinta, ta rungume jaririnta a jiki tana jin kamar ta hadiyeshi don so da kauna. Kamanninsa da Aliyu kamar an tsaga kara an karya, hatta da hasken fatar Aliyu ba abinda ya bari. Hirarrakin da ya dinga yi mata a kwanakin ne ya shiga dawomata, ta kuma fahimci ba na komai bane face bankwana. Irin ba kwanan da idan an tafi ba za'a ƙara waiwaye ba. Ba za'a kara dawowa ba sai dai a je a tarar.
"Sunansa Affan."
Abinda ta ce kenan tana duban Umman Amrah. Umman ta yi mamaki don ta dauka sunan mahaifinsa zai ci, sai dai ta gyada kai ta karɓi yaron ta kaiwa Malam don ayi mishi huduba. Ita kuwa sunan da Aliyun ya zaɓarwa ɗan kenan tun kafin ya zo duniya, ba ta ga dalilin da zai sa ta sauya ba.
Tun daga lokacin rayuwarta ta dawo sabuwa, tun daga nan komai ya sauya. Ta koma mai yawan daure fuska a maimakon sakinsa, ta zama wata shiru-shiru irin shirun da sai ta so take sakin jikinta ta yi magana da dariya. Har ta kammala takaba ta koma makaranta ba ta sauya zani ba. Hajiya ta rungumi jikokinta kamar ita
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 58