kasa hasaso wani abin musamman ma da ta ga ta fito falon Kausar na mishi batun bikin da ake yi. Hankalinta ya kara kwanciya bayan fitar Hussein din da Kausar ta shiga budomata hotunan auren da ake yi tana kallo tana ƙara jin sanyi a ranta. Ta na kuma kara tabbatarwa zuri'arsu Hussein kyawawa ne tsantsa.
***
Bangaren Marigayi Baba Naziru wanda ya sha gyara da fenti daga AlHassan, nan aka kai Ramlat kafin lokacin da Hussein zai yi gininsa. A sannan yan uwanta suka hau aikin jere da ma sauran abinda duk ya kamata. A ranar daga su sai su, an kawomusu abinci da abubuwan sha.
Da daddare suna zaune ana hira, wayarta ta yi kara, Mr.Wuff. Murmushi ta yi ta dan mike ta bar wurin zuwa can wani dakin da ta tabbatar babu kowa ciki.
"Assalamu alaikum." Ta furta a hankali.
"Waalaikumussalam. Fatan an iso lafiya?"
Ta dan lumshe ido kafin ta bude tana bin dakin da kallo, shima gado ne aka shimfida a dakin, don wannan karon gatan da ta samu har gado biyu aka yi mata.
"Alhamdulillah."
Shiru kamar ba wanda zai tanka can kuma ya ce.
"Kin shiryawa abinda zai biyo bayan aurenmu?"
Ta ji maganar banbarakwai.
"Kamar ya?"
Murmushi ya yi mai sauti.
"Za ki haɗu da Uwargidana mana."
Ranta ya sosu matuka, kishi mai zafi na Zeenatu ya mamaye koina na zuciyarta.
"Ina ruwana da ita? Zamana da nata ba iri guda ba ne. Ko ba komai ita ai auren soyayya aka yi kamar a cinye juna."
"Sai aka fadamaki kema ba zan iya cinyekin ba? Wai meyasa kike son koyaushe ki nunan babu soyayya tsakaninmu? Dama akwai soyayyar da ta girmi aure?"
Ta kasa ba shi amsa don har lokacin kiran Zeenatu da uwargidansa da ya yi yana mata zafi, ta rasa rashin zuciya irinta Hussein da ya iya rayuwa da matar da ta rushe dukkan wani tubalin ginin rayuwarsa saboda son zuciyarta.
"Shiru ki ka yi?" Ya tambaya.
Ta dan turo baki kamar yana ganinta.
"Bani da abin cewa."
"Saboda kin san ba ki da gaskiya ne kawai. Na dai fadamaki, ki shiryawa hakan. Tsoro ba naki ba ne, dama na riga da nasan ke jaruma ce. Amma ban sani ba ko har a fannin kishiya."
"Wanda aka damu da shi ne ake kishinsa, tunda ba na kishinka me zai dameni da matarka? Don haka kar ka samu damuwa, ita dai za ka yiwa wannan kashedin. Zan kwanta sai da safe."
Ta katse kiran ranta a tsananin ɓace. Me Hussein ya gani a tattare da Zeenatu har yake mata son da ba zai iya rabuwa da ita ba wai? Ita ta rasa dalilin da yasa duk laifin da ta yi masa ba ya ganin ko ɗaya. Wato har shaidamata yake ta shiryawa haɗuwarta da ita saboda ya san ba zai yi kyau ba.
Ramlat ta yi kwafa, ta mike da zummar barin dakin sai ga saƙonsa ya shigo.
"Kashe waya ba shi zai sauya zancena ba, ba kuma zai hana na faɗi ba. Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana. Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya."
Ta harari wayar tana jin kamar shi din ta harara, sai kuma takaici yasa idanunta cikowa da kwalla ta yi azamar daukesu ba ta bari sun zuba ba. Daga nan ta ja tsaki ta fice daga ɗakin.
***
Washegari da safe suka gudanar da shagali irin na al'adarsu da suke kira Fansa, inda dangin Ango ke kawo kayan abin ci da sha ga dangin Amarya ba tare da sun ga Amarya ba.
Da yammaci aka hau shirye-shiryen buɗar kai. Maryam Sambo (Cutie) ta fente fuskar Amarya da kwalliya wanda ya fi na ranar daurin aure. Maganar kyau ma na Ramlat ba sai an tsaya ana ɓata baki wurin faɗa ba. Ta yi kyau iyakar kyau, ga ta nan dai ba farar mace ba, amma Allah Ya mata baiwarSa a halittarta. Wannan karon ma Leshi ne golden cikin kayan da Hussein ya bata ta sanya an mata dinkin gown. Bilkisu dai gaba daya sai ta kara raina kanta, bakin ciki kuwa kamar ya kasheta. Ba ta taba zaton family din da Ramlat za ta shiga su na da wannan kuɗin ba. Hatta da muhallin Ramlatun, ya ci a kalla a ƙara kalla duk kuwa da cewar tsohon gini ne sai dai ya yi tsari sosai.
Gaba daya suka fita katon rumfar da aka tanada a babban filin tsakar gidan gadon na Marigayi Alhaji Gidado. An lulluɓe jikinta gaba daya da turmin zanin atamfa yanda ko fuskarta ba'a gani.
Nan kuma dangin su Hussein aka shiga fansar fuskar Amarya, Dada nan take da ba da Dubu ɗari na fansa, haka nan ma yan uwansu na Mubi da Maiduguri kowa ya shiga kawo nasa. Amrah ce gwanar faɗin nawa Amarya ta samu. Ita dai Ramlat na ƙunshe tana murmushi a ƙasan zanin don al'adar tasu ta burgeta matuka sai dai da zarar ta tuno batun haɗuwarta da Hajiya Zeenatu da Hussein ya yi sai jikinta ya yi sanyi sai dai kuma ta tabbatar addu'a ne maganin komai.
Hafsat a matsayinta na ƙanwar Ango ita ta mike don zaɓawa Amarya suna, a karshe ta radamata suna Amal. Sunan da kafatanin dangin za su dinga kiranta da shi kenan. Bayan an kammala aka kwashesu zuwa gida.
Da daddare ana zaune gaba daya ana hirar bankwana.
"Amal."
Suka yi dariya gaba daya jin sunan da Amrah ke kiran Ramlatun. Ita kam tasan kafin ta saba da sunan za'a jima.
Anan wata ma ke tambayar Kishiyar Ramlat.
"An cemin tana nan amma ban ganta ba."
"Anya ta zo Adamawa? Ina ji fa a Kano za ta zauna ita." Cewar Rafee'ah.
"Ta huta. Zama da dangin miji gari daya ai sai tsautsayi."
Babu wanda bai kalli Bilkisu ba, ita kuwa sai karkade kafa ta ke don dama da biyu ta yi maganar tana jira a tanka. Umman Amrah ce ta hana kowa magana karshe ma aka maida hankali ga hirar bikin yanda ya yi kyau.
Koda za ta kwanta tana ganin kiran Hussein ta ƙi ɗagawa don ba ƙaramin haushi ya ba ta ba. Karshe ma ta katse wayar.
***
A bangaren Hussein sam bai samu ya fita ko'ina da Hajiya Zeenatu ba sai a washegarin bikin bayan dangin Ramlatu sun kama hanyar Kano, ya zo tare da su AlHassan, Kausar da ɗiyarsa. Har yanzu akwai yan Maiduguri da Mubi wadanda ba su kai ga tafiya ba sakamakon dakatar da su daga yin hakan a Hussein ya yi, kowannensu na da labarin Hajiya Zeenatu, sai dai ba su ji cikakken ba sai yanzun da suke burin ji. Falon a cike yake, tun da ta ji suna juya harshe, wasu fulatanci wasu kuma yaren barbanci. Bayan an gaisa Hussein ya gabatar musu da ita sai kuma kai tsaye suka nufi ɗaya falon na Dada, babu cunkoson mutane kamar na farkon. Dada ta ƙuramata idanu, kusan koda ta girmemata ba da shekaru masu dumbin yawa ba. Suka gaisa da mutanen dakin, ita dai Hajiya Zeenatu an gaisa amma ba ta gamsu da kallon da kowanne ke bibiyarta da shi ba. Anti Amarya matar Kawu Modibbo itama gidan ta sauka, wannan karon dai Modibbo bai hanata ba, da biyu ya bar ta ta je don ya gama shan jinin jikinsa, yakan kirata akai-akai ya ji ko ana wani abin. Ita har mamakinsa ma ta dinga ji, ta kuma soma wani tunanin.
'Yanzu wannan ce azzalumar matar da ta raba ni da ɗana?'
Dada ta faɗi a ƙasan ranta, nan da nan tsanar Hajiya Zeenatu ya kara cika zuciyarta.
"Amm..Dada. Hafsat ba ta nan ne?"
Dada ta dubi Hussein, alama ya yi mata da ido akan kar ta nuna wani abu. Ta yi dan murmushin yaƙe.
"Ta shiga wurin Amarya saboda kowa ya watse, kar a bar ta ta yi zaman kaɗaici."
Hajiya Zeenatu dai ba ta ce uffan ba amma a ranta tana ta tunanin dama Dadar ba ita kadai ce wurin mijinta ba?
"Zeenatu."
Muryar wata mata ta ji, daidai sadda ta juya ta dubeta. Zumbur ta mike ido waje ta ke dubanta.
"Hajiya Binta?"
Hajiya Binta mahaifiya ga Rasheed ya karaso tana murmushi. Hajiya Zeenatu ta dan saki jiki ta karasa suka rungume juna amma gaba ɗaya jikinta ya yi wata irin mutuwa. Ta dago ta dubeta.
"Yaushe kika zo ƙasarnan? Me kike yi a nan?"
Yanda ta yi tambayar a mamakince yasa Hajiya Binta murmushi tana kara hadiye mamakinta, don koda ta ji labarin duk abinda ke faruwa har kuka ta yi don tausayawa Hussein. Ita ta ba Hussein dukkan shawara akan ya ɓoye dukkan batun aurensa da Ramlatu gareta don ta san komai na daga shaiɗancin Hajiya Zeenatu.
"Ina nan tun sadda Allah Ya bayyanamana Husseini. Ko kin manta amintarsu da Rasheed?"
Ta gyada kai tana yaƙe.
"Ban mance ba. Rasheed din yana nan shima?"
"Eh yana nan, ya dan fita ne ma, yanzu za ki gan shi ya dawo."
"Ok." Shi ne kawai abinda Hajiya Zeenatu ta iya faɗa kenan jikin a matuƙar sanyaye.
"Dama kun san juna?"
Dada ta jefo tambayar ga Hajiya Zeenatu.
"Eh, Ƙawata ce."
Ta amsa a dake, saura kaɗan dariya ta suɓucewa Kausar, AlHassan ya sa ƙafa ya ɗan taka ta don ta gimtse.
"Bayan an zauna sai Hussein ya fidda waya. Hafsat ya kira ya ce ta taho sashin Dada tare da Amal. Hakan da ya fadi yasa ta fahimtar komai, don haka da toh kawai ta amsa.
***
Ramlat da tun soma wayar Hafsat ta kafeta da ido.
"Hamma Hussein ya ce mu je."
Ta gyada kai, ta yi wankanta ta ci ado da wata shadda da aka yi mata dinkin doguwar riga ya sha aiki. Ta cakare ɗaurin ɗankwali don Ramlat ba baya ba. Ta ɗora mayafi a saman kayan ta zura takalmi suka fita tare. Hakanan ta ji gabanta na bugu da sauri-sauri, ta kara kallon Hafsat wacce ke wani zumudin suna tafiya sai janta da hira take amma ba ta fadi dalilin wannan rawar ƙafar ba.
A ƙofar falon farko suka yi sallama, kunya sosai ya kama Ramlat don ba ta zaci ganin sauran jama'a ba. Ta durkusa a kunyace ta gaishesu. Cike da fara'a aka amsa, nan kuma wata tsohuwa ta ɗauki guɗa da biyu. Jin haka daga cikin dakin, sai ga Kausar ta leƙo, Hafsat na ganinta ta tsallaka.
"Adda, dagaske ta zo?"
Hafsat ta tambaya da raɗa-raɗa, Kausar ta yi dariya ta nuna ƙofar falon.
"Tana ciki."
Hafsat ta harari ƙofar.
"Makira, yau ƙarshenta ai ya zo."
Suka yu dariya sabida duk da harshen fillanci suke maganar, Ramlat ta karaso.
"Muje ko?"
Sai kuma ganin Kausar suka shiga gaisawa, wasu mutan falon duk sun mike sun biyo baya don ba su kaunar abinda za'a yi ya kasance babu su.
Gaba ɗaya ana zazzaune har Hajiya Zeenatu da ta soma sakewa ganin Hajiya Binta har su na hira. Tana so ta tambayeta yanda su Dada suka ɗauketa amma babu dama tunda ba su keɓe ba. Ba su kadai ne a falon ba. Sallamar da aka yi duk ta dawo da hankulansu bakin ƙofar musamman ganin yanda wuri ya ɗauki guɗa.
Hafsat ce ta soma shigowa sai Kausar, bayansu kuwa Ramlatu.
Wani irin miƙewa tsaye Hajiya Zeenatu ta yi a matukar gigice. Babu chanjawar da za ta yi ta kasa ganeta tsabar tsantsar tsanar da ta yi mata. Ido waje ta ke duban Ramlatu, daga kan kafafunta har zuwa dukkan gaɓoɓinta babu inda ba ya rawa. Ba ta ƙara razana ba sai da ta ji muryar wata na fadin.
"Ƙaraso ciki ki zauna, Amaryar Husseini. Lale lale da kyakkyawar halittarnan."
Wani ihu Hajiya Zeenatu ta kurma kafin ta yi tsalle da nufin isa ga Ramlatu.
I just published "BABI NA SITTIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1021339453?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=4X2TU9EgqK9sZlhD1RiJLYSmRa3JHzKonALRYeMQgs42rcaB4hSZEFfZEuyDyjNLmgxQTxRGGIYovRiJIB7fWJjhHoMqPgV6u1FPxMnKYkUE%2FDXuKH3NHflk4iDkMg3R
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
60)
Caraf aka damƙe hannunta, ta dubeshi tsakar ido ya yi mata wani kallon banza, kallo na tsana da ya jima yana dannewa. Idanun Hajiya Zeenatu ya yi wani mugun kaɗawa. Ganin komai ta ke kamar a mafarki. Wani irin uban zufa ya haɗemata duk da iskar da fankokin ke bayarwa. Yarfar da hannunta ya yi. Bai kuma yi wata-wata ba ya dauketa da mari hagu da dama. Kallo daya idan ka yiwa fuskar Hussein za ka fahimci tsantsar ɓacin ransa. Abu ne da ya jima yana dannewa. Hannunsa har rawa yake sadda ya ke nunata da yatsa yana magana.
"Ko a mafarki! Kar ki ƙara tunanin cutar da matata!"
"Hussssseiin.." Ta furta da rawar murya ga hanjin cikinta da ta ke jin sun dunkule wuri guda. Idan ba ta yi ƙarya ba ma, ta ji fitar tagwayen tusa daga jikinta.
"Yes, Hussein ne. Wanda kika kashewa rayuwar shekaru biyar! Kika raba shi da asalinsa! Ki ka tauye kuruciyarsa don kafirin zuciya da zalunci irin naki! Idan ke mahaukaciya ce da ba ki gano kuskurenki ba, kika daukemu shashashai ki ka ci gaba da yin yanda ki ka so da tunanin kin ci galaba ko kuma tunanin ni Hussein ina sonki, kin yi ƙarya. Kin manta yanda muka hadu kuma muka rabu a farkon haɗuwarmu? Har tunaninki ya ba ki damar hango ni matsayin masoyinki? A'a, kin yi kuskure! Dama wannan ranar nake jira. Na auri mafi soyuwa a wurina da iyayena, mafi ƙi a wurinki sannan na yar da ƙwallon mangwaro na huta da ƙuda! Ko ba komai yanda kika tako garinmu kika daukeni cikin dangina, hakanan na dawo."
"Hussein! Karya ka ke! Karya ka ke wallahi! Ni za ka ci wa mutunci?! Ka san irin son da nake maka?! Ka rasa wa za ka auro sai wannan baƙar ashanar?"
Nan fa ta tubure ta dinga maka ashariya, wani marin ta ji, wannan karon ba Hussein ba ne. Dada ce da fuskarta ta gama jiƙewa da ruwan hawaye.
"Rufemana baki! Makira azzaluma kawai! Kina zaton wawaye ne mu! Allah Ya isa tsakaninmu da ke! Alhakinmu da kika ɗauka na tsawon wannan lokacin sai Allah Ya sakamana walla.."
Kuka ya ci karfin Dada har muryarta na shaƙewa, kusan ma da yawa hawayen suke yi musamman don tausayin Dadar wacce ta yi uban jinya da Hussein ya ɓace kafin ta samu waraka amma fa koyaushe cikin kuka ta ke da addu'a. Ramlat ita kanta kukan ta ke yi sosai, daidai sadda Hussein ya zura hannu a aljihu ya fiddo takarda ya kama hannun Zeenatu ya damƙamata.
"Meye wannan?! Me kake nufi? Dama ka kawo ni cikin danginka don ka ci mutuncina? Me ka ke son ka cemin?"
Tana maganar tana jijjiga takardar yayinda take kuka har da majina. Ɗigon tausayinta ba wanda ya ji don dama kowa da tabon shekarun da ya yi cikin zulumi da kewar Hussein a zuciya.
Wani irin tsalle ta daka da zummar shaƙo wuyan Ramlat sai dai tuni matan suka damƙe ta, Hussein shi kallon mamaki ma ya tsaya yi mata na irin wannan ƙarfin halin wai ɓarawo da sallama. Zagi take ƙudundumawa tana kiran sai ta hallaka duk wanda ke shirin rabata da farin cikinta.
"Modibbo ya yi gaskiya! Dama ya ce kar na zo! Kar na zo! Ba sona ku ke yi ba! Ashe da gaskiyarsa! Wallahi Hussein ka yi kaɗan! Zamanmu har abada ba na ƙare ba ne! Yanzu aka fara!"
Gaba daya Hajiya Zeenatu ta birkice, fuskarta kace-kace da hawaye ga majina tana aikin jansa. Idanunta yanda ya rufe har ba ta san me ke fita daga bakinta ba.
Kowa a dakin ya shiga salati jin sunan da ta ambata.
Hussein ya ma kasa magana sai murmushi, ga duk wanda ya gani kuma zai fahimci na zallar takaici ne kawai. Dama shi kadai ya zarga, duk kuwa da bai gama tabbatar da hakikanin lambar wayar da ya ɗauka a wayarta ba tunda ba shi da lambarsa, amma daga kiran da ya yi sau daya da kuma muryar da ya ji, jikinsa ya ba shi tare suke komai. Hannu kawai ya harɗe a kirji bayan ya ja baya ya ci gaba da kallon diramar da kowa ya ke jin sunan wanda ta ambata, babu wanda ya zata. Dada kuka sosai ta ke yi don har numfashinta na sama, wannan ne yasa AlHassan janyeta zuwa ɗaki don kwantarmata da hankali. A hankali Hussein ya juya zai fice, wannan yasa Hajiya Zeenatu bin bayansa fuuu bayan ta ture duk wanda ke gabanta. Koda ta kalli Ramlatu, wani banzan kallo kawai ta watsamata na za mu haɗu sannan ta yi gaba don tasan ba damar taɓa ta yanzun. Hafsat ta yi caraf ta dauki jakar Hajiya Zeenatun ta buɗe ta cusamata takardar da Hussein ya bata wanda ta yi wurgi da shi a tsakar ɗakin sannan ta bi bayanta da sauri.
AlHassan dake ɗakin tare da Dada jin ƙugin tashin mota ya mike da sauri ya fito. Ganin babu Hussein a falon yasa da sauri ya fita.
"Kar ka sake ka budemishi gate!"
Ya fadi da ɗan ƙarfi yanda Maigadin zai ji kuma da harshen fulatanci. Nan da nan Maigadin ya fasa. Hussein ya ci burki, ita kuwa Hajiya Zeenatu dake bubbuga gilashin mota tana bin motar don ya saurareta, itama ta tsaya cak. Hafsat wacce tuni ta jefamata jakarta tana tsaye kallon dirama da ƙarfin hali irin na Zeenatu. Daidai sadda Hussein din ya fito daga motar. Hajiya Zeenatu ta cakumi wuyan rigarsa bai yi wata-wata ba ya hankaɗata. Sai yanzun ya tuna da akwatin kayanta da ke boot din motar, tun a can gidan ya nunamata za su kwana biyu gidan Dada, don haka ta haɗo komai na kayanta. Ya buɗe ya fiddo akwatin kafin ya ja hannunta tana binsa ta na magana kamar zautacciya.
"Hussein ina sonka! Ban taɓa son wani namiji dagaske ba sai kai! Ka yimin rai kar ka rabu da ni! Kar ka manta da dukiyarmu, na tuba ka yafemin don Allah."
Wannan karon da alamun karaya sosai a muryarta, shi kuwa shareta ya yi bai ce uffan ba har sai da ya fidda ita daga ƙofar gidan gaba ɗaya. Daidai sadda Rasheed ya dawo gidan don ya ɗan fita. Ganinta ya gane abinda ke faruwa don yana sane da shirin Amininnasa. Akwatin ya diremata ya dubeta a wulaƙance.
"Sai ki kama hanya ki bar garinnan idan kinga dama, idan ba ki gani ba ki zauna ki ƙara gwada kashe Ramlat ki gani ko zan bar ki da rai."
Daga haka ya juya ya dubi Buzun maigadinsu mai jin fulatanci, cikin fulatancinsa wanda ya ɗan farfaɗo ya ba shi umarnin koda wasa kar ya bari ta shigo gidan. Daga nan ya komai ciki tare da Rasheed.
"Na dauka wurin Kawu za ka je. Shiyasa na fito don tsayar da kai."
Alhassan ya furta yana dubansa. Ya shafi suma gami da runtse idanu, radadi ya ke ji idan an ambaci sunan Kawunnasu azzalumi kuma maƙiyinsu da har yau sun rasa gane kan ƙiyayyarsa.
"Nan na so zuwa amma na fasa. Zan jira hukuncin Dada."
Daga nan ya shiga motar, AlHassan ya yiwa Rasheed ido alamar ya bi bayansa. Ba musu ya zagaya gefensa ya bude ya shiga. Kallonsa kawai ya yi bai ce uffan ba, bisa umarnin AlHassan din ya bude masa ƙyauren ya fice. A hanya suka ga Hajiya Zeenatu jaye da akwati tana tafe tana waige. Ganin motarsa har hannu ta sanya da nufin tsayar da shi, ya ƙarawa motar wuta gami da jan tsaki.
***
Tun faruwar wannan lamari, tsoron Allah ya ƙara shiga zuciyar Ramlatu. Ta ƙara tsoron ƊAN ADAM tunda har nasa bai kyale ba. Wane irin zamani ne wannan? Haka ta yi ta tunani bayan ta koma sashinta. Waya suka yi da Hajiya ta labartamata dukkan abinda ya faru. Salati Hajiya ta sanya gami da ƙarawa, ba abinda ya girgizata sai na jin sunan Kawun Hussein din da ya fito a maganar. Addu'a ta yi gami da ƙara jan kunnen Ramlat akan addu'a da kuma kiyaye Azkar safe da yamma. Daga bisani ta kira wayar Amrah wadanda basu jima sosai da isa Kano ba. Nan ma dai duk hirar suka yi.
"Wannan kaɗai zai nunamaki ba karamin matsayi kike da shi a wurin Mijinki ba. Sai ki zage damtse ki kwantar da hankalinsa a wannan gaɓa, kinsan ba karamin damuwa zai shiga a kwanakinnan ba."
Wannan shi ne zancen Amrah, nan fa daga Rafee'ah ta kirata, sai Maman twins can kuma A'isha. Kowa mamakin jin abinda Hussein ya yiwa Hajiya Zeenatu ya ke yi, a gefe guda kuma ana tayata farin ciki don zama da Hajiya Zeenatu masifa ne.
Don kanta ta gaji da wayar ta ce musu chajinta ya ƙare ta kashe. Miƙewa ta yi ta shiga daki, wanka ta ƙara yi, ta fito ta zauna gaban madubi ta na kallon fuskarta da ta mulmule ta kara kyau adalilin gyaran da ta sha.
_*Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana. Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya.*_
Ta tuna kalaman Hussein, a hankali ta ci gaba da murza man a wuri guda na fatar hannunta. Kenan yana nufin ita ɗin ya ke so? Ita ce abar sonsa? A abinda ya faru, zallar ƙiyayya ta gani ya nunawa Zeenatu yayinda ita duk wani a wurin zai shaidi yana sonta. Wannan tunanin ya janyo ta sunne kai tana murmushi, murmushin da ya fito tun daga ƙasan ranta. A hankali ta ɗago kai ta dubi madubi, ba zato ta hangeshi tsaye jikin ƙofar ɗakin. Ta yi sauri ta kauda kai. Kasa motsi ta yi gaba ɗaya don ba halin ta miƙe sakamakon guntun tawul dake jikinta. Tunaninta ma tun yaushe ya ke tsaye a kanta. A hankali kuma ta ga ya juya ya fita bai ce uffan ba. Ta dafe kirji gami da sauke ajiyar zuciya sannan a gaggauce ta mike bayan ta fesa abinda za ta fesa. Ko ba'a faɗa ba, mijinnata yana tattare da damuwar da ya ke buƙatar kulawarta. Ta gama gane irin ɗaukar da Hussein ya yi mata kamar yanda ta soma amanna da zancen soyayyar da ya ke magana bayan aure. Riga da siket ta sanya na atamfa, ta yi ɗaurinta tsaf sannan ta fesa turare ta fita gabanta na faɗuwa. Fatanta Allah Yasa ya huce. Koda ta fito ana kiraye-kirayen sallah, har a sannan ba ta samu tsarki ba. Ba ya falon amma ya ajiye wayoyinsa da agogo, wannan ya sa ta fahimci alwala ya shiga don haka itama sai ta koma ɗaki don kunya ta ke ji ya fahimci halin da ta ke ciki. Tana ji sadda ya fice daga falon sannan ta fito. Mintuna kaɗan bayan idar da sallah sai ga Hafsat tare da Kausar. Fatima ta ruga a guje ta rungumeta yayinda Hafsat ta karasa ta ajiye kwandon abincin hannunta saman tebur. Zama suka yi aka gaisa. Nan kuma aka shiga maida zance.
"Nifa Adda Amal ba wanda ya bani mamaki sama da Kawu. Wallahi ban san rashin kaunar da yake yiwa iyayenmu da mu ya kai girman hakan ba. Ai shiyasa yau nima na rama a kan ɗansa, ya kirani har ya gaji ban ɗaga ba, karshe ma na aikamasa da zazzafan saƙo. Rasheeda fa ki ga ta kasa zama ma a gidannan ta tafi gida Adda Fati saboda kunya da kuma bakin cikin abinda Babansu ya aikata. Anti Amarya ma wai mijin ya kira ta je can yana nemanta."
"Toh ke Hafsat ai dole, amma bana goyon bayan ki wulakanta Tahir tunda ba shi ya yi maki ba. Asalima ke da bakinki kin faɗi irin zafin da ya ke ji na yanda Uban yake hana su zumunci da mu."
Kausar ke maganar kafin ta maida hankali ga Ramlat.
"Kinga shawarar da zan ba ki,wallahi ki tashi sosai ki riƙe mijinki hannu bibbiyu. Kar ki ga kin rabu da Hajiya Zeenatu ki ɗauka shikenan, ba ita kaɗai ce mayya me kwacen miji ba musamman ma a garinnan. Mijina gashinan har yau ban gama fidda ran watarana ba zai ƙaromin abokiyar zama ba don yanda ƴanmata da zaurawa ke farautarsa tamkar nama."
Suka yi dariya. Kausar ta girgiza kai ta nuna Hafsat da yatsa.
"Ba abin dariya ba ne, ke ai kin san komai. Ke za ki ba da labari, ko ƙawayenki na makaranta ba sai da na takamusu burki da zuwa gidana ba?"
Dariyar dai Hafsat ta ƙara, ita kuwa Ramlat sai ta ɗan tsunduma tunani, wato dai bayan wani yaƙin akwai wani, amma bai kai wancan ba. Motsin bude kofarsa ce ta sanya su jan baki su yi shiru don ɗazun dama sun baro shi ya shiga bangaren Dada, tare yake da AlHassan. Zama suka yi Hussein na mai kama hannun Fatima da ta yi tsalle ta faɗa jikinsa. Da wani murmushin samun
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 51 Chapter of 58