Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ma ya daina yi mata dadi, dama tun zaman Hussein ƙamshin turarensa ya mamaye ilahirin jikinta ya haifarmata da kasala. Yanzun jikinta ya idasa mutuwa. "An fadamaka kowa irinka ne kenan." Abinda Hussein ya ce kenan bai ƙara uffan ba ya bar Hisham da dariya. Tunda ya soma cin abincin wani dadi ke ratsa kunnuwansa. Ya kasa ɗagowa har sai da ya yi nisa da soma ci, can dai ya dubi Hisham. "Nikam Princess dinka hala ta yi makarantar koyon girki ne." Haba! Ai daga Hisham din har A'isha da uwar gayyar Ramlat, dariya suka ya basu. Ya dubesu yana dan yarfa hannu, ya tsaida kallon kan Ramlat. "Mene abin dariyar?" Ta sunkuyar da kai tana murmushi. "Antinmu kinga karo na biyu wannan bawan Allahn na buga santi akan girkinki. Gaskiya yau goron da zai ba da kamata ya yi ya fi na rannan." Ita dai ba ta ce komai ba, ta kasa ci gaba da kai lomar, karshe ma miƙewa ta yi. "Na ƙoshi." Daga nan ta yi gaba da sauri ta koma cikin falon ta zauna ta basu baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima gogan bai ƙara magana ba har ya kammala ci ya mike ya bar Hisham da A'isha ma ƙusƙus. Wuri ya samu ya zauna yana danne waya, sai dai rabin hankalinsa a kanta yake. Tun yana satar kallo har ya koma kallon sosai. Karshe ya maida hankali saman wayar, whatsapp ya shiga. Ganinta online ya taɓota. "Thank you." Ta bude saƙon kafin ta saci kallonsa, murmushi yake amma idanunsa na saman waya. "Kallon fa? Kar ki mata kwace." Jin bing na shigowar saƙo ta maida hankali ga wayar. Abinda ta gani kenan, ta turo baki kadan ta kashe data gami da jefa wayar cikin jaka. Miƙewa ta yi ta dauki mayafinta ta nufi dakin baƙi. Hijab din jikinta ta cire ga gyara zaman mayafin ta fito. Lokacin su Hisham sun dawo falon. "Ba dai tafiya ba?" Fadin A'isha. "Tafiya zan yi, Hajiya ta ce kar nayi dare." "Kai kamar wata karamar yarinya. Ko hira fa bamu yi ba. Prince ka yi mata magana." Fadin A'isha a shagwaɓance. Sakin baki Ramlat ta yi don ita abin ma na A'isha da Hisham mamaki yake bata. Soyayyar dai kamar ana ƙaramata zuma. "Ji, toh banda uzurin gabana da zan ƙare a gidanku?" "A'a amma don Allah ki zauna, kinga fa yanzu shida, ga hadari a gari..." "Shiyasa ai zan tafi, kinsan ban fiye tuƙi idan ana ruwa ba." A'isha kuma ta rasa abin faɗi. Hisham dama bai ce ba, so yake abokinsa ya ce! Jakarta ta dauka cikin lallashi ta ce. "Haba Autar Hajiya, In sha Allah za ki ganni kwanannan, ai yanzun sai ana leƙowa ana dubaki. Yauwa Maman Twins ma sun ce na fadamaki suna nan zuwa." Jin haka yasa A'isha sakin ranta kaɗan. "Toh ai shikenan. Allah Ya kaimu." Ramlat ta amsa da amin tana murmushi. Hussein ya mike yana duba agogo. "Nima zan gudu." "Kamar hadin baki?" Fadin Hisham. Girgiza kai Hussein ya yi. "Yamma ta yi ga hadari." Gyada kai Hisham ya yi. "Ai shikenan, don ma dai kai din baki da hanci ne. Ba nisa sosai." Hussein bai amsa ba ya bi bayan Ramlat da tuni ta fice. Hisham na dariyar mugunta ya yiwa A'isha raɗa a kunne ya bi bayansu. "Innalillahi, garin yaya?" Fadin Ramlat a hankali tana jin kamar ta yi kuka. Hussein ya juyo yana dubanta, iska na faman ɗaga mayafin nata da ja mata rigar. Tayarta ya gani a sace. "Ya Salam, Antinmu garin yaya hakan ta faru?" Fadin Hisham sadda ya karasa yana kyafkyafta idanu ganin iska na neman yi mishi lahani. Kamar ta yi kuka ta dubi Hisham. "Wallahi nima bansani ba." Ta furta cike da takaici. A'isha ta danne dariyarta, game din dadi yake mata sosai. Tuni Hussein ya bude motarsa ya shige ya ba ta wuta. "Shigo na kaiki." Abinda ya ce kenan. Ta dubeshi ta maida duba ga su Hisham. "Je ki don wallahi hadarinnan yanda ya haɗe ba zan iya fita ba. Sai dai ko ki kwana zuwa safe." Ta haɗa daga shi har A'ishar ta watsawa harara. "Gobe na ƙara zuwa gidanku." Nan kuma suka hau aikin ban hakuri, ta karasa ta bude gidan gaba ta zauna. Hussein ya dubi abokinsa. "Sai mun yi waya." Daga haka ya fice bayan Maigadi ya budemusu ƙyaure. *** Tunda suka kama hanya yake murmushi, ya san ko mene aikin Hisham ne. Amma hakan ba karamin dadi ya yi mishi ba, ya juya ya kalleta. Ta takure kanta wuri guda, ta wani rungumi jaka. Basu yi mintuna biyar da soma tafiya ba aka soma ruwa dagasken gaske. Ganin irin karfin ruwan yasa dole ya taka burki ya sauka ya gangara gefe. Wayarta ta yi ringing ta duba, Hajiya ce. Hakuri ta bayar gami da bata tabbacin ta taho. Hajiya na faɗa akan ba ta ji dadin hakan ba suka yi sallama. Tasan a zatonta ita ke jan motar, ba zata fadamata ga abinda akai ba. "A dalilinki na zo gidan Hisham." Ya fadi kansa tsaye yana kallon yanda ake zuba walkiya da ruwa kamar da bakin ƙwarya. Ta dubeshi da mamaki, maimakon murmushi, wani kwantaccen damuwa ta gani shimfide saman fuskarsa. Ya karkato yana dubanta, ta kauda kai saboda nauyin da kwayar idanunsa suka yi cikinnata. I just published "BABI NA ARBA'IN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/GhWrzYe49bb 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ _*Rufaida Umar*_ Bismillahir Rahmaanir Raheem. 41) *Assalamu Alaikum yan uwana. Fatan Alheri ga dukkanku. Ina matukar farin ciki da irin addu'o'inku gareni. Allah Ya bar zumunci. Ameen.* *Ban kammala Exams ba, amma aski ya zo gaban goshi. Nagode sosai.* "Kar fa ki fassara kalamaina." Ta yamutse fuska kadan. "Fassara ta me?" Ya yi murmushi yana dubanta sannan ya maida kai ga tuƙinsa. "Akwai hoton da nake da buƙata a wurinki." Ta saci kallonsa. Ba ta tanka ba ya ɗora. "Wata little angel da na gani kwanakin baya kin ɗora hotonku tare. Ita ba ƙatuwa ba kuma ba siririya ba. Fara ƙal." Da gaskiyar Bature da yace Blood is thicker than water.  Fati yake nufi. Murmushin da ba ta san ta iya shi ba ta shiga yi kafin ta saita kanta da tunaninta. "Ka santa ne?" Taɓe baki ya yi gami da girgiza kai. "Ko daya, kawai dai yarinyar ta burgeni sannan ina jinta kamar ƴar da ta fito daga jikina." "Alhamdulillah." Tsabar ruɗu yasa ta furtawa a fili har ya kai dubansa gareta. "For?" Ya nemi ba'asi. Murmushi kawai ta ke yi. "Murmushin fa? "Ba murmushi nake ba." Ya dubeta sai kuma ya yi dariya. "Toh kuka kike yi." Ta shafi bakinta sai kuma ta sunkuyar da kai tsabar kunya.  Ya sanya hannu ya kunna music. Wannan karon ma dai muryar Nancy Ajram ke tashi. Abinda Ramlat ta fahimta, Hussein ma'abocin jin waƙoƙin larabawa ne. Shiru ya biyo baya har suka kai ƙofar gidan su Ramlat. Kirjinta ne ya bada dam ganin Yayanta Munir tsaye a jikin motarsa yana amsa waya. Tunda motar ta tsaya ya ƙuramata idanu yana son ya shaida waye.   Hussein ya dubeshi sadda ya ke ƙoƙarin cire Seat Belt din da ya sanya.  Kamanninsa da Ramlat kawai ya gani da kuma irin firgicin da ke saman fuakar Ramlat din, ya fahimci ko waye. Bai cewa Ramlat komai ba ya fita, itama ganin haka ta fito kirjinta na lugude. Yaya Munir da ganin Ramlat ya ba shi mamaki, dakyar ya iya miƙawa Hussein hannu suka gaisa. Ita kuwa Ramlat tana gaidashi wuf ta faɗa cikin gida.   "Ke kuma lafiyarki?" Tambayar da Hajiya ta watsomata kenan ganin shigowar da ta yi a hargitse. Girgiza kai ta yi ta zauna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki. "Ba komai." "Hala kin haɗu da yayannaki a waje?" Ta gyaɗa kai, ba ta kai ga bata amsa ba sai ga Munir din. Abinda ta ke gudu ne ya kasance, faɗa sosai ya shiga yi akan don me za ta shiga motar abokin Hisham. Hajiya dai mamaki ƙarara don ba ta da  labarin hakan. "Ku yi hakuri, wallahi tayar ce ta sace. Ga Auta ba lafiya shiyasa dole Hussein din ne zai kawoni. Kunsan yanayin unguwarsu ba'a samun abin hawa cikin sauƙi." Ta faɗi jiki a sanyaye. Harara Yaya Munir ya danƙara mata. Hajiya kuwa jin Hussein ne yasa ba ta ƙara uffan ba. Dakyar dai ta lallaɓashi ya tafi. Bayan fitarsa ta miƙe ta yi ɗaki, sai bayan sallar isha'i sannan ta fito, ta ƙara wanka ta sanya doguwar rigar bacci da ƴar hula. "Gidan gaba ɗaya sai ya yi ba daɗi wallahi." "Uhm, ni zan faɗi haka ba ke ba Ramlatu, nayi kewar yarannan kamar na kira waya a maidomin su." Murmushi Ramlat ta yi ta zauna. "Hajiya kinsan wani ikon Allah? Yau da kansa ya tambayeni hotin Fatima. Wai haka kawai yarinyar ta burgeshi, na aikomasa hotunanta." Hajiya ta ɗan yi shiru alamar nazari. "Fatima wacce?" "Ɗiyar baƙonmu na Adamawa." "Ikon Allah, jini ba wasa ba. Allah Sarki." "Ni kaina nayi mamaki." "Allah Ya ci gaba da taimakonmu, in sha Allah za'a dace. Wataran komai zai zama labari." Cikin gamsuwa Ramlat ta jinjina kai tana murmushi, fuskar Hussein na yawo cikin ƙwayoyin idanunta. "In sha Allah." Ta maimaita. ***   Ranar litinin da tana kammala shiri ta fito, a gaggauce ta karya ganin tana dab da makara. Haka ta fito titi don har sannan Hisham bai ga damar maidomata motarta ba, ba kuma ta ƙara kiransa ba tunda ta ji yana kiran shi ba shi da kuɗin gyaran taya toh ta san da biyu ya ke yi.       Ta yi tafiya kaɗan kafin ta fito bakin titi ta samu abin hawa. Zamanta keda wuya cikin Napep, wayarta ta ɗauki ƙara. Halima ce. Kamar ba za ta ɗaga ba sai kuma ta ɗauka. "Ke kuwa Ramlat ba faɗa me ya kawo gaba? Shikenan don kin bar Revenue  an rabu?" Yaƙe ta ɗan yi kamar a gabanta. "Ayya Halima ba haka bane. Allah Ya huci zuciyarki. Fatan kuna lafiya, Ya sauran mutanenmu?" "Uhm, lafiya kalau, sai dai kin tafi kin bar baya da ƙura." Da mamaki ta ce. "Ban fahimta ba. Wani abu aka yi?" "Eh, yanzu ba wanda bai san cewa Chairman yana sonki ba. Idan ma kina tunanin bamu sani ba gwara ki san cewa ƙwai ya fashe." Wani ɓacin rai ya zo wa Ramlat wuya, ta danne komai. "Shi ne me? Don yana sona mene a ciki Halima?" "Aa ba komai bane, Allah Ya ba ki hakuri. Yanzun sai na faɗi zancen da zai yimin sanadin wurin neman halal ɗina. Dama shawara zan ba ki kawai don matar Chairman ba kanwar lasa ba ce." Don tsananin ɓacin rai ba ta san sadda wani wawan tsaki ya suɓucemata ba. "Daga ita har mijinta basu ɗaɗani da ƙasa ba, ke kinsan ni kuma kin san halina. Bana kallon mutum irin Chairman matsayin nagartaccen namiji da ya isheni kallo ballantana har na ƙulla alaƙa ta dindindin da shi, wato aure. Ke dai da ya tsolemaki ido har ki ka kasa haƙurin bar wa cikinki gulmar sai ki je can ki ƙarata." Daga haka ta katse wayar ta kasheta gaba ɗaya ma tsabar takaici da ɓacin rai. Har suka isa ta sauka ba ta ji sassauci a ranta ba. Ita ta soma zargin ma Halimar ce ta kwatantawa Chairman din gidansu na Yakasai. Can kuma ta ja istigfari a ƙasan ranta. *** * ADAMAWA* AlHassan ke ta zuba sauri a hanyarsa ta komawa cikin babban shagon siyar da kayayyaki na Alkhairat Mall adalilin mantuwar da ya yi na wallet ɗinsa saman teburin Cashier. Karo suka ci da wani matashi da kallo ɗaya za ka yi mishi ka san ruwa biyu ne, kamar dai ɗan Sudan kamar kuma ɗan Nijeriya. "Sorry please." Faɗin AlHassan kenan yana dubansa a fisge, Matashin ya zaro ido kafin ya saki ƴar dariya yana nunashi da yatsa. "Hussein!" Daga haka ya rungumeshi yana dariyar farin ciki, AlHassan ya tsaya cak! Ya kasa magana kwakkwara, can dai ya ɗago ya dubeshi da kyau, kamar ya so sanin fuskar sai dai Allah bai ba shi ikon tunawa ba. Rasheed da ya lura da irin kallon da yake binsa da shi, sai jikinsa ya ɗan yi sanyi. Daidai sadda wani ma'aikacin wurin ya nufosu, duban AlHassan ya yi. "Yallaɓai ai na fita ban iskeka ba mun yi saɓani, ga wallet ɗinka ka manta." Ya karɓa da godiya, Rasheed dai kallo yake sai kuma a sannan tunaninsa ya ba shi anya kuwa wannan Hussein ɗin da ya tako takanas daga ƙasarsa don ya gani ne? Nan da nan jikinsa ya ba shi Twin brother ɗinsa ne wato AlHassan Aminu. "My name is Alhassan Aminu, Hussein's Twin Brother." Rasheed ya shiga murmushi da gyaɗa kai, bai lura da yanayin sauyawar fuskar Alhassan din ba, daga yanayin farko zuwa wani yanayi na daban mai nuni da alhini da kuma sosuwar rai.   Alhassan ya nemi su ɗan fito farfajiyar wurin. Ba musu Rasheed ya bi bayansa. Ji yake kamar ya yi tsuntsuwa ya je ga Abokinnasa, shekarun da suka gabata ya yi masifar kewarsa. A hanyar ma su na tafe ƙorafi ya ke zubawa AlHassan na yanda Hussein ya kasa cika alƙawarin kawo mishi ziyara sai shi ne ya cika a karshe. "Kusan satina ɗaya a garinnan na kasa gane gidanku, har na fidda rai don har na yi komai na komawa garinmu sai yau cikin ikon Allah muka haɗu da kai." Duk yana maganar ne cikin harshen turanci, Alhassan ya ba shi address din gidansu kafin su yi musanyen lambar waya suka rabu. Rasheed dai ya yi mamakin dalilin da yasa bai ba shi lambar Hussein ba, ya so tambaya kawai sai ha bar wa cikinsa. Da wannan ɗokin ya nemi adaidaita ya koma masaukinsa, siyayyar da bai yi ba kenan tsabar murnar cimma abindanya kawoshi. Tun a hanya ya kira mahaifiyarsa yake labarta mata haɗuwarsa da AlHassan da yanda ya rungumeshi a zatonsa Hussein ne. Ta tayashi murna sosai sannan suka yi sallama. ***   *KANO* Tana zaune bayan kammala wasu aikace-aikace, ta tuna da cewa wayarta a kashe ta bar ta gaba ɗaya yinin ranar, da sauri ta jawota ta kunna. Mintuna ƙalilan da kunne Data, saƙonni suka shiga faɗowa daga Whatsapp. Wanda ta ke burin ta ga ya aikomata saƙo babu shi a ciki, har tana shirin ajiye wayar sai ga text message ya faɗo, ta duba. Ba ta kai ga buɗewa ba sai ga kira, duk daga mutum ɗaya wanda ta daukeshi SPECIAL.   "Kashe mutum kike kokarin yi." Ta ɗan dafe ƙirji kafin ta saita kanta tuna a inda ta ke, lumshe ido ta ɗan yi tana murmushi. A baya zabta ƙaryata idan wani ya ce za ta ko kalli wani ɗa namiji ta ji ya burgeta balle ta kaunaceshi, a yanzun kuwa tana jin Hussein a ranta. Da wani irin ƙauna mai sanyi, da wani irin so mai cakuɗe da sinadarai masu ban mamaki. "Tuba nake yi, me na yi?" Ya sauke ajiyar zuciya wanda ya ratsa kunnuwanta. "Kin kashe wayarki bayan kinsan na kamu da son Beautiful Angel dinnan da kika ɗora a status."   Runtse idanu ta yi cikin son haɗiye abinda kunnuwanta su ka yaudareta da son ji. Maimakon hakan sai ta ji abu daban, cikin sarewa da sanyin jiki ta amsa. "Ka yi hakuri, na ma manta cewa na kashe wayar. In sha Allah yanzu zan turamaka." "Ok! Na gode, ina jira." "Toh." "Naji muryarki ta sauya, hope komai lafiya?" Ta ciji leɓbanta na ƙasa tsabar haushin kanta da ya kama ta, toh mene dalilin da za ta ba shi damar fahimtar wani abu? "Lafiya kalau, ina wurin aiki ne." Shiru ya biyo baya can kuma sai ya amsa. "Ok ba damuwa. Idan kin koma gida kya turomin. Thanks." Daga nan ya katse kiran. "Ke kam dai naga alamar da wani gwanin naki kike waya." Ta kai duba ga Hajiya Salma, darakta din department din da ta ke. Kasancewarta mace mai raha da haba-haba yasa ake sonta. Ga ba ta da wuyar sabo. Murmushi kawai ta yi ba ta ce uffan ba. Ta faɗa whatsapp, Hussein din ma ba ya online, haka ta turamasa duk hotunan Fatima da ke kan wayarta har wanda Fatiman ke tare da Hafsat. Babu dai nata ko ɗaya a ciki. Karfe biyar da kusan rabi ta bar Ofis zuwa gida. Gaba daya jikinta a sanyaye yake sakamakon soyayyar da ta ke yiwa kanta shamaki da ita, amma kamar zuciyar ba ta jin kashedinta. Ƙara cusa kanta take yi cikin lamuran Hussein dumu-dumu. Idanunta ga cicciko da kwalla, ta sharesu. Ya dace ta yi baya-baya da shiga shirginsa tun kafin ta yi nisan da ba ta jin kira a sha'aninsa. Ko babu Hajiya Zeenatu, Hussein ya fi ƙarfin ajinta. A ganinta, wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa.    Haka ta wuni cike da kasala, sai dab da Magriba sannan ta fito ta faɗa kicin, kunu ta dama, ta zubawa Hajiya  wacce ke azumi cikin flask mai riƙe zafi. Dama ta iske tuni an yi Ƙosai. Wannan tasa ta haɗamata da lemun zoɓo da ya sha kayan ƙamshi. Sai da ta tabbatar ta haɗa komai saman darduma kafin ta koma ɗaki, alwala ta ɗauro. Wayarta na kyallin shigowar saƙo don haka ta duba.   *"Thank You."* Abinda ya turomata kenan. Murmushi kawai ta ɗan yi ta shimfiɗa darduma.   Misalin ƙarfe takwas da rabi suna zaune a falo tare da Hajiya, kallon Tarkon Ƙauna suke a tashar Arewa24. Gaba ɗaya hankalin kacokan yana kan talabijin, sallamar Baba Maigadi ta ɗauki hankulansu. Suka amsa. Saƙon Ramlat ta yi baƙo yake tafe da shi. Nan da nan ta ɗaure fuska, tana da tabbacin Chairman ne don dama Kawu yace ta zuba idanun ganinsa a satinnan. Umarnin Hajiya ta bi kawai ta miƙe ta shiga ɗaki, Hijabin sallarta ta zura ta fita. Kamar dai yanda ta tsammata hakan ce kuwa, yana tsaye ya sha wata narkakkiyar shadda da aka yi mishi aiki a jiki. Ƙaton tumbinsa shi za ka soma haskowa kafin ma ka kai ga ganin komai. "Mtsw." Ta ja guntun tsaki tana jin kamar ta juya, dolenta ta daure ta ƙarasa. Ganinta ke da wuya, ya ƙara daidaita tsayuwarsa yana mai ƙuramata idanu ga wani haƙoransa da suka bayyana shi a dole murmushin ƙauna ya ke. "Ranki ya daɗe Ramlatu." "Ina wuni." Ta gaidashi ciki-ciki. "Lafiya kalau Hajjaju. Wato sai kika ganni kwatsam. Wallahi kasa hakurin na soma kiranki nayi saboda jina nake kamar na shiɗe jiya tsabar tunaninki da ya.." "Ina mai neman alfarmar ka tafi kai tsaye ga abinda ya kawoka, komai nawa nakan ba lokaci muhimmanci. Da ace dai ka sanar da ni zuwannaka tun wuri zan fi samun sukunin tsakurar maka mintoci kaɗan daga lokutan da nake sa shi. Yanzu dai akwai abinda nake yi ka katsemin hanzari. Amma bari na ƙara faɗamaka haƙiƙanin abinda ke zuciyata dangane da kai. Inaga hakan zai taimaka wajen ganin ba mu shiga haƙƙin juna ba." Chairman Dikko wanda ya zubamata idanu kamar ya haɗiyeta tsabar so, ya jinjina kai gami da gyara tsayuwa. "Na ji abinda kika ce, ko daga yanda kika tarbeni nasan me kike nufi, kar ki manta kin faɗamin ai tun kafin na tako nan. Amma Hajiya Ramlatu, duk wasu bayananki ba zai sa ni Dikko na haƙura da ke ba, ina sonki, wani irin so da rabona da shi tun a kan Mairo uwargidata. Don haka zan jure dukkan ƙiyayya, na rantsemaki da Allah kika shigo gidana ba za ki ƙara marmarin fita ba saboda daɗin da zan jiyar da ke. Ga kuma madarar ƙauna." Ya ƙarashe da wata shaƙiyiyar dariya. Ta bishi da kallon tsana, ta sauke idanunta kirjinta na ƙara zafi. Kasa cewa komai ta yi har ya kammala sumbatunsa, karshe ta dubeshi. "Dare ya fara, na kuma gaji da tsayuwar." Ya sauke ajiyar zuciya gami da duban agogo. "Wallahi ban san lokaci ya ja har haka ba, amma nidai don Allah ki ƙara dubawa tunda dai su Kawu sun riga da sun ba ni ke. Kinga kuwa babu abinda zai hana aurenmu, ki sanyawa ranki salama ki yi tunanin alherikan da ke jiranki a gidana." Ta ƙara ɗaure fuska, ba ta bari sun yi doguwar sallama ba ta juya ta nufi ciki. Ba jimawa da shigarta sai ga Baba Mai gadi da ledoji har uku shaƙe da kaya, da sauri ta karɓa da zummar maida mishi, babu shi babu motarsa. "Ai ina ce miki ya wuce, ba ki ji ba." Faɗin Baba Maigadi, cike da takaici ta dubeshi.   "Don Allah Baba kar ka kara amsar saƙon wannan mutumin." Baba ya ɗan yi shiru, ita kanta Ramlat din sai ta ga rashin kyautatawa tunda dai Baba Maigadi ba ruwansa da alaƙarsu. Juyawa ta yi ta koma ciki. "Wai ke wannan kumburin da kike yi, ba fa wanda ya matsa akan sai kim aureshi." Hajiya ta furta tana dubanta. Ramlat da tuni idanunta sun cicciko da kwalla ta amsa. "Ni Hajiya abinda ke tayarmin da hankali, bai wuce yanda Kawu ya yi saurin aminta da shi ba. Fisabilillah babu bincike babu komai? Ni nasan waye Chairman, ba abinda suka sani a kansa." "Ke wa ya faɗamaki ana dogon bincike akan mai muƙami ko dukiya? Hum, Ramlatu a zamaninnan ba'a wannan. Bar ganin Yayyuna ne, amma na fi ki sanin halinsu. Ke dai ki dage da addu'a, muddin kuma kina son ki shafe maganarsa toh wallahi ki watsar da komai ki fiddo mijin aure. Shi ne kwanciyar hankalinki da namu baki ɗaya. Ai kin dai ji abinda Uwani ta faɗamaki. Yanzu da ace kin tsaida hankali wurin ɗan uwan mijinnata ai da yanzun sai dai wata maganar ba wannan ba." Ramlat kirjinta ya yi nauyi, ta share hawayen da ya soma sauka saman fuskarta. Miƙewa ta yi ba ta ko yi marmarin ganin abinda ke cikin ledojin ba ta faɗa ɗakinta. Gefen gado ta zauna gami da zabga tagumi. Tana cikin tsaka mai wuya, ita ta sani. Wanda ta ke masifar so kuma ta ke jin za ta iya aura bai san ma tana yi ba. Runtse idanunta ta yi tana mai sa hannu ta dafe kanta.   "Ya Allah!" Ta furta a fili, fuskar Hussein kawai ta ke gani cikin ƙwayar idanunta. Ta buɗe idanun, tuni sun kaɗa sun yi jazur. A hankali ta kai duba ga hotonsu na Family, Abbanta ta ƙurawa idanu. Take dukkan wani faɗi-tashi da aka yi akan zancen aurenta da Aliyu ya faɗomata. Murmushi ta yi da ya fi kuka ciwo, soyayyar Abbanta ya mamaye zuciyarta, yanzun komai ya zama tarihi. Abba ya bar ta da kewa ta har abada, hakanan Aliyu. Ta tsinci kanta a sabuwar rayuwar da ba ta san abinda zai haifarmata a gaba ba. *** ADAMAWA Misalin ƙarfe biyu da mintuna na ranar Talata, Rasheed ne zaune yana faman haɗa gumi ga idanunsa da suka kaɗa suka yi ja tsabar tashin hankali. Labarin ɓatan amininnasa ya matuƙar girgiza shi. "Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ya furta a fili, Dada dai hawaye ta ke yi hakanan Hafsat da ke raƙuɓe a gefe ta dora hannu saman cinyar Dada. Rasheed ya dubi AlHassan cikin harshen turanci. "Ban ji dadin wannan labarin ba sam! Sai dai ina ji a jikina duk inda Hussein ya ke yana raye, bai mutu ba. Sannan meyasa ba ku yi cigiyarsa ta gidajen rediyo  da talabijin ba? Na dauka wannan ce hanya mai sauki da za ku yi saurin ganoshi." AlHassan ya jinjina kai. "A farko duka mun yi wannan amma a karshe sai muka watsar mu ka fawwalawa Ubangiji. Ni kaina ban yarda cewa Hussein ya mutu ba. Amma ya zamu yi? Babu inda ba mu nemeshi ba, sai dai ba wani labari." Rasheed ya runtse idanu cike da ɓacin rai, ransa na suya. "Kuma babu wani abokin gaba da ya ke da shi? Wanda ku ke zargi?" "Babu." Rasheed ya yi shiru, so ya ke ya tuna ko akwai abinda ya manta game da Hussein. Duk iyakar kokarinsa ya kasa, a ƙarshe dai AlHassan ya shiga roƙonsa akan ko labari ya ji na abinda ya danganci Hussein don Allah ya sanarmusu.  Bai bar gidan ba sai da ya ci abinci, nan ma kawai cusawa yake, ba zai ce cimarsu ta bambanta ba don shi kam ruwa biyu ne, mahaifiyarsa ƴar jahar Katsina ce. Jimami da alhinin ɓatan Amininnasa ne ke sukarsa. Da wannan ya musu sallama ya bar gidan. Ranar dai ya tayarmusu da alhinin Hussein, wunin ranar sun yi shi sukuku ba daɗi idan ka cire Taheer da bai san me ake ba. Burinsa kawai ya shaƙu da Hafsat kuma

Chapter 35 of 58