ta kaunaceshi, sai dai abin ya faskara.
***
KANO
Wata wawuyar dariya Hajiya Zeenat ke yi tana ƙara rungume wayarta a kunne, ƙafafunta kamar za su rabu da cinyarta tsabar girgizasu da take. Kallo ɗaya za ka yiwa yanayinta ka fahimci ko ma wane kalar labari ake ba ta ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba.
"Kai Dikko! A ganka nan a bar ka inda kake! Da ace za ka san daɗin da wannan labari ya min za ka sha mamaki. Kai ma kwallon shege ne!"
Can kuma ta ƙara nutsuwa ta ce.
"Kana ji na? Kar ka sake ka yi wasa! Kar ka ɗaga ƙafa, wani ganin ba ta sonka ko ta tsaneka wannan duk a banza ce muddin ta faɗo hannunka. Ka dai ƙara ƙaimi wajen sakarwa makwaɗaitan iyayennata aljihu, na tabbatar maka ƙarfin dukiya ya fi komai tasiri a duniyarnan. Don ubanta dole ma ta sarara ta aureka. Ni kuma na maka alƙawarin wata kyauta mai tsoka muddin ka mallaketa matsayin matarka."
Jin haka daga can ɗaya ɓangaren, Chairman ya shiga zuba godiya da kirari, wannan ya ƙara fasa kan Hajiya Zeenatu, har wani lumshe ido take tana murmushi, koda ta ji motsin saukowar mutum daga bene ta yi sallama ta ajiye kan wayar. Duban mijinta ta shiga yi tana murmushi sosai, ranta na wani irin sanyi kamar ƙanƙara. Shi kuwa bai san ma tana yi ba, kacokan hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa na Hisham game da kasuwanci na haɗin gwuiwa da suke son yi.
Har ya sauko ya ƙaraso bai kammala ba, ganin irin kallon da ga ke jifansa da shi yasa shi fadin.
"I will call you back." Daga nan ya katse wayar.
"Lafiya?"
Abinda ya ce kenan. Ta yi farr da ido, ya kauda kai.
"Ba komai, kawai dai kyau ka yimin Yallaɓaina."
Ɗan murmushi ya yi bai ce uffan ba.
"Amm, dama ina son zuwa asibiti."
Ya dubeta.
"Meke faruwa?"
Cike da ƴar damuwa ta ce.
"Kwanakinnan komai na ci sai na ji kamar zan yi amai, ga yawan kasala."
Kirjinsa ya bada dam! Haka kawai zaton da ya yi sai bai mishi wani dadi sosai ba. Ya daure ya gyada kai da murmushin da ya fi kama da yaƙe.
"Ya kamata ki je, ba'a wasa da lafiya."
Ta ƙara rausaya ƙwayar idanunta.
"An gama Baby, da safe za shirya na je. Fatana Allah Yasa mu ji alheri."
Ta ƙarashe tana shafa cikinta, ya yi murmushi kawai ya maida hankali kan wayarsa. Hotom Fatima ya buɗe yana kallo, gani yake idan har Hajiya Zeenatu za ta haifamasa irinta, toh yana marhaba. Kaunar yarinyar ya ke ji sosai. Abu daya ya tuno da ya ji ba dadi, wato dai rabon da ya ga Ramlat ma a online tun ranar da ta turo mishi hoto.
"Wannan kuma wacece?"
Tambayar Hajiya Zeenatu da ya yi saurin maidoshi tunaninsa. Ya sauka daga whatsapp din ya rufe wayarsa, cikin faɗuwar gaba ya ƙirkiro ƙarya ya shirgamata.
"Ƴar sister din Hisham ce. Ta miki kyau ko?"
Nan da nan annashuwar saman fuskar Hajiya Zeenatu ya dawo, ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi.
"Sosai yarinyar ta yi kyau. Zamu haifi fiye da hakan ma."
Ya gyaɗa kai kawai.
***
"Wai wa ya faɗamaki ina sonsa? Ni wallahi ban taɓa sauraronsa ba."
Ramlat ke faɗi a gundure, gaba ɗaya zancen Chairman ya isheta. Ta kuma lura mitar Rafee'ah ba mai ƙarewa ba ce.
"Ai shikenan, idan dai kina son a tabbatar da hakan sai ki daure ki fiddo miji. Ko kuma shawara, ki samu Baba Dakta kawai ki faɗamasa."
Cewar Rafee'ah.
Ramlat ta yi shiru, da sun san damuwar da take ciki na son maso wani da basu takuramata da zancen Chairman ba.
"An faɗamaki Baba Daktan shima zai saurareta ne idan ba wani ta kawo ta ce shi za ta aura ba? Malama ki yiwa kanki faɗa tun wuri wallahi idan ba haka ba za'a ji kunya. Baban Twins yana da labarin Chairman Dikko, ba abinda ban sani ba na tarihinsa."
Wannan karon ma shiru ta yi, Ramlat ta yi dana sanin dawowarta gidan da wuri, da ace ta san da zuwansu ba abinda zai kawo ta. Ta dawo ta iske Hisham ya gaji da zolayar ya aikomata motarta. Yinin ranar da tunanin Hussein ta cinyeshi, don dakyar ta dinga fuskantar aikin da ke gabanta, yanzun kuma ta zo ta iske yayyunnata, sun sanyata tsakiya kowanne da kalar nashi zancen.
Tsam! Ta mike tsaye ta kwashi tarkacenta na ofis da zummar wucewa.
"Au, mu za ki yiwa rashin ta ido? Don ana faɗamaki gaskiya?"
Ta kasa ba Anti Zulaihat amsa, cike da damuwa ta dubeta kawai.
"Wuce abinki, ke kika sani. Rayuwarki ce."
Ta furta a zafafe, Ramlat ta ciji lebbanta tsabar takaici, karshe ta yi gaba zuwa daki tana ji Hajiya na fadin su bita a sannu.
Ruwan ma kasa watsawa ta yi don haka ta bi lafiyar gado ta kwanta, a hankali ta shiga fitar sa hawayen baƙin ciki. Kewarsa ta ke ji kamar ta yi me, ga wani irin sonsa da ke nuƙurƙusarta, kwana biyu ba su yi magana ba, bai ganta online ba kuma bai nemeta ta waya ba. Wannan yasa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ke haukan sonsa. Ta kai minti goma sha biyar a haka ba ta iya ko motsawa ba, tausayin kanta take ji, da ace su Ummi na gidan, ko ya ya zasu ɗebemata kewa, kiran sallar Magriba ce ta tasheta. Ta faɗa banɗaki ta kama ruwa ta yi alwala.
Sai da ta idar da sallah kafin ta ninke Hijab ta fice zuwa falon. Wannan karon ta yi ƙoƙarin saita zuciyarta ta ƙaƙalo walwala, suka ci gaba da hira da ƴan uwanta kamar wani abu bai faru ba. Tattaunawa ce game da bikin da ya taso a Daura, wanda zasu tafi dukkansu don karshen sati ne. Su ma basu ƙara tayar da batun Chairman ba.
Sai bayan sun bar gidan, Hajiya ta shige daki don watsa ruwa, itama ta faɗa nata ɗakin da niyyar hakan.
Ganin hasken shigowar saƙo bai sa ta yi wani rawar ƙafa ba, hakan ya faru ba adadi a yini biyunnan, sai dai daga ta duba, saƙon Muhibbat ne ta ke gani, wani lokacin Hilal, wani lokaci kuwa saƙon kamfanin layukanta. Tunanin hakan yasa ta ƙin daukar wayar har sai da ta fito daga wanka ta gama shafe-shafenta ta shirya cikin riga da wando na bacci. Ta dora rigarta na sallah ta shimfida darduma. Sai da ya idar da sallar Isha'i ta yi duk abinda ya dace sannan ta ƙara samun nutsuwa.
Kai tsaye ta nufi wurin wayar, sunan da ta gani a saƙon ya sa ta jin nauyi a ƙafafunta, kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki, haka ta buɗe bayan ta zaune gefen gado.
*Na lura kina da kishi, wato don ban nemi ki turomin hotonki ba ne yasa ki ke shan ƙamshi ko? Oya, a turomin yanzu. Happy?*
Lumshe idanu ta yi tana murmushi.
I just published "BABI NA ARBA'IN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ysuMTT3Orcb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
42)
Dukkan godiya tabbata ga Sarki Allah. Tsira da aminci su kara tabbata ga Ubangijin Talikai.
Ina kara amfani da wannan damar wurin godiya gareku gaba daya. Alhamdulillah na kammala exams lafiya sai fatan sa'a in sha Allah. Ina godiya da hakuri da uzurinku gareni. Allah Yabar zumunci. Ameeen. Sai dai kar ku manta dama ba kullum nake posting ba, ina tsallake kwana daya. Allah Yasa mu ga karshen Ƙarfen Ƙafa lafiya. Ameen.
******
*Ya ya zan yi in misalta soyayya..? Ya ya zan yi in fasalta soyayyaa..? Ita ce ba'a siye da kudi duk dukiyaa..Ita ce mai gida na mulki shi ne zuciyaaa..Ta sanya mai ƙarfi ya sunkuyaa..ya zubda hawayen idaniyaaa..!* Umar M Shareef
Hoton ɗan aljan mai murmushi kawai ta tura mishi. Aka yi sa'a ya hau online. Ganin ya buɗe ta yi saurin kife wayar ta runtse idanu kamar yana gabanta, kirjinta na wani dukan tara-tara. Jin ƙarar shigowar saƙo yasa ta karkata wayar a hankali kamar marar gaskiya ta duba.
*"Please."*
Don ƙara tabbatarwa ta ƙara murza idanu ta duba, roƙonta fa ya yi? Anya? Kuma akan hotonta? Ina Hajiyarsa?
Duk wannan tambaya ce da babu mai amsamata sai shi, har abada kuma ba za ta tambaya ba. Ta jingina kanta jikin gado tare da miƙar da ƙafafunta.
*"Angel ɗina ya hana ni aikawa kowa hotona."*
Ta ba shi amsa duk kuwa da cewa ba ta ji dadin amsar ba, sai dai ta lura idan ta biyewa kanta, za ta iya tona asirin zuciyarta har ya gane inda ta dosa.
Ya buɗe, kusan mintuna biyar shiru, goma, sha biyar, duk shirun ne, shi bai sauka online ba kuma bai ce uffan ba. Ramlat dai har bacci ya soma fisgarta babu amsa daga Hussein. Don haka ta ajiye wayar ta mike ta kakkaɓe shimfidarta ta kwanta. Ta soma addu'oin kwanciya bacci kenan wayarta ta yi ringing. Da sauri ta kai idanunta, lambar da ta gani ya hargitsa kwanyarta, miƙewa zaune ta yi b shiri. Sai da ta kusan yankewa kafin ta samu nutsuwar ɗagawa. Leɓɓan ke rawa, zuciyar na ƙara ƙaimi wurin bugu sai dai lanƙwasa harshen har ta iya haɗa kalma kwakkwara ta gagara.
'Haka so yake?' Ta jefawa zuciyar tambaya. Ta san ba wannan ne farkon soyayyarta ba, wanda ta shimfiɗa a baya ya girmi wannan. Sai dai wannan shigarsa da tasirinsa mai sauri ne kuma mai sanyaya zuciya da ruhin ma'abocinsa.
"Kin yi shiru."
Ta dawo daga duniyar tunanin abinda ya yi mata nisa, TAZARAR DA KE TSAKANINSU kamar tazara ƙasa da sararin samaniya ne. Ɗumi ta ji a kumatunta, wani ɗanɗano na gishiri ya sauka a leɓɓanta ta cije leɓɓan. Kitt! Ta katse kiran, ba ta tsaya anan ba sai kawai ta kashe wayar gaba daya ta jefa gefen gado. Kwanciya ta yi ta runtse idanu, me ya rinjayeta har haka? Hussein fa? Kamanninsa suka yi dirar mikiya cikin idanunta, tunaninta ya ɗauketa ya cillar tun daga ranar da ta soma ganinsa har zuwa yanzu da suke tare.
"Ka fi ƙarfina Hussein, Allah Yayemin wannan jarrabawar."
Ta furta a fili, ta yi addu'a ta kunna Mp3 Suratul Baƙara na tashi a hankali tana bi. Tun tana tunani har bacci ya yi awon gaba da ita.
***
"Baƙo?"
Ta furta a mamakince tana mai tsurawa Baba Maigadi idanu, tana kyautata zaton kunnuwanta ne basu ji daidai ba. Daga ita sai hijab saman rigar baccinta wanda ta dora zani a samansa.
"Nima kaina nayi mamaki Ranki ya daɗe, sai dai kuma kallo ɗaya na yi mishi uzuri."
Daga haka ya juya bai ƙara dogon jawabi ko ƙarin bayani ba. Ta bi bayansa baki galala sannan ta ɗago idanunta ta dubi agogo dakyau. Bakwai da rabi da safe.
'Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!'
Ta furta a zuciya, Hajiya ba ta kai ga tashi ba. Itama baccin ta kasa, ta rasa ya za ta yi da ranta, babu jimawa da fitowarta falo ta ji kwankwasar Baba Maigadi, ya kuma isar da saƙo ya bar ta tsaye da mamaki da fargaba. Ta dai daure ta yi shahada ta zura silifas ta fito. Fuskarta fayau sai dai albarkacin ruwan alwala da ta yi yasa ya yi kyan gani.
Ido da ido suka dubi juna, daga shi sai riga da wando na sport. Ya zura hannu cikin aljihun wando, idanun sun yi luhu-luhu hakanan sun kanƙance, gashinnan a birkice kamar yanda fuskarsa ta nuna. Ta kasa kauda idanunta kamar yanda shima ya kasa kauda nasa, kirjinta lugude yake kamar ana surfa gero. Ya tako har gabanta ya tsaya.
"Me na miki? Ki fadamin laifina, kiyi hakuri."
Ta lumshe ido ta bude don mamaki, sai a sannan ta samu damar magana.
"Me ka yimin Hussein? Ba abinda ka yimin ni."
Ya girgiza kai, ta kalleshi sau daya ta kauda idanunta da sauri.
"Kin kashe waya ba ki yimin magana ba, don nace ki turon hoto? Wasa nake maki. Ki yi hakuri, na shiga rayuwarki da yawa."
Ta girgiza kai, kamar yanda idanunsa ya kaɗa, haka nata ya cicciko da kwalla.
"Ni wallahi ba abinda ka yimin, kuma maganar da nayi wasa ce kawai nayi ba wai da wata niyya ba. Shi ne dama ka doko sammako? Ka yi hakuri."
Ya yi shiru bai daina kallonta ba. Ganin shirun ya yi yawa ta kara kallonsa.
Hussein tambayar kansa yake abinda ya ruɗashi, ya hargitsa tunaninsa. Mene abin ɗaga hankali don Ramlat ta kashemasa waya? Me ya birkita kwanyarsa har bacci ya kauracewa idanunsa kamar yanda ya kasa bambance daidai ko akasinsa? Hajiya Zeenat baccinta take sharɓa ya fito, meyasa tunanin ta farka ta nemi ba'asi bai faɗomasa a rai ba sai yanzun da ganin Ramlat ya haifarmasa da sukuni da kwanciyar hankali? Sai dai kuma akwai wani duhu da ya kasa nemo haske a cikinsa, watakila sai nan gaba! Ya ayyana a ransa.
"Shikenan, zan tafi. Ki gaida su Mama."
Daga nan ya juya ya shige motarsa, iska da sanyin safiyar na busata, ba ta fasa kallonsa ba har ya shiga motar. Gilashin ya sauke yana kallonta, sakanni biyu zuwa uku kafin ta farga, ta juya da sauri ta faɗa gida. Ya ja motar kamar wanda kwai ya fashewa a ciki.
Allah Ya taimaka Hajiya ba ta falo, da sauri ta shige dakinta ta rufe, a bakin ƙofar ta zame ta cure wuri guda, kuka ko dariya za ta yi? Ba ta sani ba, ba ta da tabbacin abinda kwakwalwarta ke kokarin hasasowa sai dai ta jera Hussein a sahun mutanen da suka san ƙima da darajar *ƊAN ADAM*. Ta sauke ajiyar numfashi tare da neman tsari daga Ubangijinta akan sharrin zuciya da saƙe-saƙenta.
***
"Daga ina kake?" Ta yi tambayar ba tare da ta bari ya ƙarasa fitowa daga cikin motar ba, ya kalleta kallon tsaf. Gabansa na faɗuwa sai dai akwai wani ƙwarin gwuiwa da yake ji na iya kallon cikin idanun Hajiyar da ɗan ƙaramin kuzari.
"Bai kamata ki fito haka ba."
Ya fadi a sanyaye ganin daga ita sai doguwar rigar bacci, damtsen hannun duk a waje ga tumbi da ya ɗaga rigar. Hajiya Zeenat idanunta a kaɗe, ji take kamar ta shaƙe wuyan Hussein saboda wani irin kishi da ya mamayeta. Tasan ƙarya ne a kowane yanayi mace ta ga Hussein ba ta ƙyasa ba, ta kuma sani ba zai taɓa zuwa wajen kowace mace ba musamman da safiyar fari. Amma tana son tabbatar da inda ya je don ta samarwa zuciyarta hujjar da za ta nutsu sosai.
Gaba ya yi zuwa cikin gidan, ta mara mishi baya. Yana niyyar taka matattakala ta riƙe hannunsa. Ya runtse ido da sauke ajiyar zuciya alamar gajiya, bai bari ta ƙara tambaya ba ya tari numfashinta.
"Wasu takardu na kaiwa Hisham. Shikenan?"
Ta bishi da kallo tana mai sakin hannun, ya haye sama. Ƙarya abu ne mafi muni cikin munanan ɗabi'u, ya shiga istigfari a ƙasan zuciyarsa. A ɓangaren Hajiya Zeenat, tasan waye Hussein, ƙarya ba ta daga cikin shirginsa, don haka sai ta gasƙata amma ta soma jin tsanar Hisham a ƙoƙon ranta. Yana neman shigemata hanci da ƙudundune. Ta yi ƙwafa kawai ta bishi saman.
Kwanciya ya yi ya rufe har kansa da bargo saboda bai shirya amsa wasu tambayoyin daga Hajiya Zeenat ba bayan wancan. Murmushi ya tsinci kansa da yi, murmushi sosai, Ramlat da firgicin dake kwance samam fuskarta shi ya ƙayatar da shi a yanzun.
***
"Jimin ja'irar yarinya! To ba kya sonsa wa kika kawomana za ki aura? Ko an faɗamaki akwai wani cikin iyayennaki da za ki je wa da wannan magana su ɗauka?"
Dada ke wadannan kalaman sadda Ramlat ta kai mata ziyara da kuma roƙonta akan a janye batun Chairman. Jin abinda ta ce Ramlat ta ɓata fuska.
"Da ace kinsan waye shi da ke za ki zama farkon wacce za ta ce aa."
Ta zayyanemata kaf labarin Chairman, tun Dada na faɗin toh meye a ciki? Har ta yi shiru tana gyaɗa kai. Ramlat na kaiwa aya ta dubeta.
"Toh yanzu ya dace ace kun bayar da jininku ga wannan mutumin? A ma ɗauke duk wannan, bana sonsa. Ba shi da kyawawan ɗabi'un da zan kaunaceshi dominsa. Bana son na maimaita gidan jiya, abin nufi, ina gudun na saɓa umarninku a karo na biyu naga ba daidai ba."
Murmushi Dada ta yi ba tare da ta furzar ba. Ta jinjina kai.
"Ai shikenan, zan yi magana da shi Bellon, ya dace su yi bincike mai kyau a kansa, idan da hali ma gwara a tattara a ajiye zancensa gefe. Sai dai kuma da sharaɗin ki fiddo miji nan kusa. Da ƙananun shekarunki ba zamu zubamaki ido ki yi ta zama haka ba aure ba kuma kina yawon wurin aiki, babu ƙima da mutunci a hakan Ramlatu."
Ramlat ta gyaɗa kai cikin tausayawa kanta.
"Ki tayani addu'a Dada, Allah Ya zaɓamin nagari."
Dada ta amsa da amin. Ta ɗora da faɗin.
"Yaushe angwayen nawa zasu dawo ne?"
Murmushi Ramlat ta yi, tana gyara zaman mayafinta, takanas ta biyo daga wurin aiki don ta roƙi alfarma wurin Dadar.
"Ni kaina ina kewarsu, amma mun yi waya da Muhibbat ta cemin za ta je ta ɗaukosu zuwa gidanta su yi kwana biyu tukunna ta maidosu. "
"Allah Ya nunamana. Za ku je Daurar?"
Dada ta ƙarashe tana ɓallar goronta daidai sadda Ramlat ta dauki jakarta.
"In sha Allah zamu je. Inace su Nusaiba ma duka za su je?"
"In sha Allahu. Ai bikin na gida ne."
Fadin Dada, a karshe suka yi sallama ta fice ba ta ko yi sallama da sauran jama'ar ba don tana jin haushinsu ganin mafi yawa na goyon bayan Chairman. Ita mamakin ma irin karɓuwar da Chairman ya yi a gidan ta yi don ko a gidansu bai samu hakan ba.
***
Tsakaninta da Hussein sai gaisuwa, ta rasa dalilin sauyawar alaƙarsu. Wani jzolaya da wasa duk ya daina. Kamar wani kalma na sabo bai taɓa ratsawa tsakaninsu ba. Wannan ya jefata damuwa, ga matsin lamba daga Chairman wanda ba dare ba rana sai ya kira. sai dai har ya kammala ringing ba ta ɗauka, idan ya dameta kuwa ta latse wayar gaba ɗayanta.
Tafiyarsu Daura ta gabato har Hajiya zaa je wannan karon sai Amarya Hunainah wacce ta saki jiki da su sosai ake zumunci ba kamar Bilkisu ba wacce tun hayan auren Munir ta haɗe danginsa kaf ta jerasu layin munafukai. Wannan ne ya siyawa Hunainah daraja da ƙima ba kaɗan ba a idanun su Ramlat. Gidanta ne dai har sannan Ramlat ɗin ba ta taka ba, ba kuma don wani abin ba.
Ana gobe zasu wuce gaba daya su Rafee'ah har Hunainah mai karamin ciki sun zo cikin gidan kwana, Aisha ma ta na nan ta zo ayi sallama. Hira suke yi cike da nishaɗi ana dariya, sallamar Munir ce ta katsesu. Suka amsa ya dubi Ramlat.
"Ke wancan na wajen ne Chairman din naki?"
Nan da nan annashuwar Ramlat ta dauke.
"Zuwa ya yi?"
Ta fadi ranta a ɓace, tasan ya kira ta ƙi ɗagawa ya yi mata text akan zai zo su gaisa ta maida masa martanin ba ta buƙatar hakan.
"Nikam dai bari na leƙa naga waye wannan Chairman din."
Rafee'ah ke faɗi tana ƙoƙarin miƙewa.
"Shi auren a igiya kika ratayeshi? Ba ki da kai fa Rafee'ah naga alama."
Munir ya fadi gami da harararta.
"Goɗai-goɗai da ke kina abinda ko Auta ba za ta yi ba. To ki je ki ce masa me? Ki leƙa wuta ma ko?"
Dariya suka sa mata idan ka cire Ramlat da ta yi daki ranta na ƙuna. Kamar ba za ta fita ba, sai kuma ta yanke ta je kawai ta tunkare shi komai zai faru ya faru. Mayafin rigar jikinta ta yafa. Koda ta fito lokacin Hajiya na zaune.
"Ke dama haka kike zuwa hirar fuska kamar baƙin tukunya?"
Munir ya faɗi yana duban Ramlat da ta nufi Hajiya don sanarmata.
"Yaya Munir nidai da ka roƙarmin alfarmar mutuminnan ya bar zuwa gidannan. Na faɗamasa ya kyaleni bana sonsa wallahi."
Taɓe baki Munir ya yi.
"Au, wato dai gidan jiya kike neman a maimaita? Ai yanzu babu mai miki dole Ramlat, a baya ma ba'a iya anyi maki ba sai yanzu? Ta inda aka hau ai ta nan ake sauka, ki samu wadanda suka karɓi kuɗinsa."
Yanda gaban Ramlat ya buga da ƙarfi, haka fuskokin Hajiya da su Zulaihat ya nuna razani da mamaki.
"Me kake nufi? Kuɗin auren Ramlatun su Yaya Bello suka karɓa?"
Munir ya dubi Hajiya yana mai murmushin tambayarta.
"Haba Hajjaju, a karɓi kuɗin auren Ramlatu ba ki sani ba? Kawai dai yana sakarmusu bakin aljihu ana bushasha."
Wani wahalallan ajiyar zuciya Ramlat ta sauke, cike da bakin ciki ta kama hanyar ficewq daga falon. Maganar su dinma sai suka bar ta anan adalilin Hunainah dake wurin, ko ba komai suna buƙatar sirri.
***
"Girman kujerarki ce tasa na jure dukkan wata shanya da kika yimin, sai dai koda na bushe ganinki ya maidani ruwa tsundum."
Murmushi yake yana ci gaba da dubanta, jinsa yake kamar wani saurayi mai shekaru talatin idan yana gabanta. Ramlat ta dubeshi a ɗaure.
"Ina haɗaka da girman Allah da ManzonSa s.a.w ka fita hanyata. Kaga mu ba yara bane da za mu tsaya muna magana da maimaici. Ina za ka ji daɗin zaman aure da wacce ba ta jinka a ranta? Wane kyautatawa ka ke tunanin za ta yi gareka?"
Chairman ya yi wata ƴar dariya.
"Kina tunanin barazanar kisa a daren amarcinmu zai sa na sake ki? Aa Hajjaju, wannan namiji ne ba muna maza ba. Ba ki da abinda za ki faɗarmin da gaba har ya yi sanadin rushewar alaƙarmu."
'Innalillahi..' Ta kai har ƙarshensa yayinda jiri ke neman kwasarta. Dakyar ta samu ta daidaita tsayuwarta bayan ta dafe Black Camry din Chairman. Wani yawu ta haɗiya.
"Me kake nufi?" Ta fadi cikin sarƙewar harshe. Chairman ya yi dariya karo na biyu.
"Abun dariya, kunkuru ya yiwa busjiya ƙafa, banda abinki Ramlatu ai maganar duniya ba ta ɓuya, kin ɗauka haka kike zaune ana ganin ina neman aurenki ba'a kawomin sukarki ba? Ai ba zai yiwu ba. Kedai ayi sha'ani kawai."
Shiru ya biyo baya ga idanunta sun cicciko da kwalla.
"Idan ka gama zancen zan koma ciki."
Chairman ya marairaice.
"Haba Ramlatu, me kike gujewa a auren mutum irina mai muƙami da kuma rufin asiri? Kinsan adadin matan da ke neman irina kuwa? Da za ki ga matan da ke bina za ki cika da mamaki. Ramlatu sonki nake dagaske amma kin ƙi fahimta. Da ace na biyewa Kawunnanki da tuni an daura auren, yanzu ma abinda ya kawoni batun turowa ne suka bn iznin nayi, shi ne na zo mu kara daidaitawa kafin lokacin."
Kamar wacce aka harbawa mashi, haka ta ji wani radadi a kirjinta. Daidai sadda ta ke share hawayen da ya zuba saman kuncinta ta kalleshi.
"Me ka ce? Iznin ka turo fa suka yi maka?"
" Kwarai kuwa, kuma kinsan dama ce da ba zan taɓa bari ta suɓucemin ba. Na zo ne don kawai na kwantar da hankalinki, ki ƙara samun nutsuwa da ni don idan har ina numfashi kina yi, babu wanda ya isa ya rabani da ke."
Ranta ya ɓaci ainun.
"Sai mu gani inda ake dole! Aure ne bana yi, ba zan aureka ba. Ina mai tabbatarmaka ko ka turo babu inda zancen zai ɗara."
Daga nan ba ta juya ba ta ko waigo ta ji dalilin kiran da ya shiga kwalamata ba.
***
"Lafiya?"
Kusan lokaci guda suka jehomata tambayar ganin yanda ya faɗomusu ɗakin. Ta kasa magana sai kallo, karshe ta wuce ɗaki.
Ganin haka Munir ya mike ya fita waje, Chairman ya shige abin hawa har ya fice. Ya dawo ciki ya sanar da su ya tafi.
Gaba daya suka bita dakin idan ka ɗauke Hajiya da Munir da suka faɗa tattaunawa game da lamarin Ramlatun.
"Ai mafita fa a wajen su Kawu shi ne kawai ta nemo wani ta kai musu. Yanzun bata da abinda zai kwace ta a hannunsu. Su gani suke sun kama dami a akala. Rannan ma na shiga gidan na tarar Malam (Kawu Rabe) yana ta rubutu, wai mai neman auren Ramlatun yake rubutawa na tsarin jiki. Kinga kuwa ba karamin kamu suka yi mishi ba, fahimtar da su barin aurennan sai da taimakon Allah."
Hajiya ta yi salati. Tana mamakin ƴan uwannata, idan kuma ta tuna wasu abubuwan da suka wanzu a baya na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 36 Chapter of 58