Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai nunota ake yi. Hawaye take dakyar take ganin gabanta, kai tsaye ta tari abin hawa zuwa unguwar Yakasai gidan Hajja.  I just published "BABI NA ASHIRIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/K6spRvSBkab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 21) "Yanzu na dai yaji kika yi?" Hajja ta fadi tana jin kamar ta tashi ta kara rufeta da sabon duka. Ramlat ta kalleta. "Haba Hajja, duka fa? Duka a waje har sai da aka kwaceni. Kiyi hakuri amma nidai ba zan koma ba." "Ku ne yaran yanzu! Babu yanda ba'a yi da ku akan ku yi hakuri ku bi zaɓin iyayenku amma sai ku tiƙe lallai sai abinda ranku ke zo. Ku lallai sai kun nunamana kun yi boko, koda dai wasunku ma ba bokon hakanan suke wannan tsiyar. Gashinan auren bai je ko'ina ba kin fara yawon dakan yaji. Ba bakin magana dai Ramlat, miƙewa ta yi ta shige ƙuryar ɗakin Hajja din ta yi kwanciyarta zuciyar na raɗaɗi. Har lokacin zafin marin da Aliyu ya yi mata ba ta bar jinsa ba.  Shikenan kowace mace na zaune gidan aure da daraja da ƙimarta, ita nata ya zube a idanun Aliyu? Da ace yana gani ai ba zai ɗaga hannu ya bugeta ba. Biki kam ta fasa zuwa ko za'a mutu. Tun tana jin sababin da Hajja ke yi har ta bar jiyowa, baccin wahala ya yi awon gaba da ita. ***   YAMMACI   Munir da iyalinsa ne suka yada zango wurin Hajja, daga gidan su Bilkisun suke shi ne suka ga dacewar su leƙo. Hira ta yi hira har Hajja ta gangaro kan Ramlat. "Ramlat kuma?" Fadin Munir cike da mamaki, Bilkisu ta ƙara buɗe kunnuwanta da son jin abinda ke faruwa. Hajja idanu sun rufe balle Munir din, sun mance matsayin  Bilkisu wurin Hilal balle kuma a wurinsu. Komai da ya faru ta kwararo mishi, miƙewa ya yi zumbur ya faɗa ɗakin. Bacci take tsakaninta da Allah, ba ta yi aune ba ta ji an kai mata wawan bugu a ƙafa. A firgice ta farka gami da salati.   Kallonsa take kirjinta na wani irin lugude, babu wannan ƙauna da tausayin na ƴan uwantaka a kwayar idanunnasa. "Tashi ki bar gidannan tun ban ɓaɓɓallaki ba!" Abinda ya ce kenan. Idanunta suka cicciko da kwalla tuni hawayen suka soma zuba. "Yaya Munir.." "Yimin shiru! Ni ba Yayanki bane, You have no right to call me Yaya! Kin maida mutane shashashai wadanda basu san me suke yi ba! Kin zaɓi Aliyu akan uban kowa yanzu kuma kin koma yawo bin gidajen dangi kina ɓatawa zuri'armu suna. Ba ki isa ba! Wallahi Ramlatu kin yi mugun kaɗan! Wato kin ga kin kasa kashe iyayenmu da baƙin cikinki, shi ne kika taho wurin tsoffinmu ki hallakamana su. Ai ke Ramla da ƴar halal ce ta gasken, ko kasheki Aliyu zai yi ba za ki kallemu ba balle ki kawomana kokenki. Daga yau na miki iyaka da mu, idan su iyayennamu sun kasa fadamaki cewa ke Annoba ce a garemu, toh yau ni Muniru na fada. Ki fita hanyarmu da zuri'armu. Wallahi bama sonki mun tsaneki! Ko mayya kike ya ci ace zuwa yanzu kurwar da kika ci a danginnan ya isheki." Ta kasa kwakkwaran motsi, daga yanda numfashinta ke bugu ta tabbatar ba mafarki bane. Wane irin tsana Munir ya yi gareta? Bude baki ta yi amma ta kasa furta komai, a hankali ta zame ta sauko daga gadon ƙarfen Hajja ta lalubi ɗankwalinta da mayafi da kuma jaka, jikinta har rawa yake tsabar wani irin ɓacin rai. Ita kuwa dagaske ko Aliyu zai dinga yanka namanta gunduwa-gunduwa ba za ta kara zuwa ta kai ƙararsa ba. Ba ta son koda kallon Munir don ganinsa take kamar wani bare a wurinta yanda yake dubanta a yanzun. A gaggauce ba ta ko tsaya sallah ba ta fito falon ya biyo bayanta. "Ke ina za ki je? Muniru korarmin ita ka yi? Ina kuma kake son ta faɗa?" Fadin Hajja tana miƙewa tsaye a rikice, Bilkisu ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya wani azababben dadi yana yawo daga kai har kafafunta tana ji kamar ta yi tsalle ta rungume mijinta. Burinta ta ga Ramlat a wulaƙance fiye da yanda ta yiwa ɗan uwanta. 'Kaɗan ma kenan!' Ta faɗi a ƙasan ranta, Ramlat kuwa ba ta ko lura da ita ba, ba ta tsaya amsa kiran da Hajja ke faman kwalamata ba, ta zura takalminta ta bar gidan. A hanya har tuntuɓe take yi tsabar sauri da tunani har ba ta kula da abinda ke gabanta. Haka har ta iso titi tunanin kalaman Munir ke mata yawo a kwanya. Wani wawan burki da aka ci, gami da salatin da jama'a suka ɗauka ya ankarar da ita dalilinta ne. Ta hau titi ba ta sani ba, ta hau ba'a hayyaci ba har mota na shirin ɗauke ta. Ta tsaya cak, mai motar wani dattijo, ya fito ya dinga surfamata ruwan masifa. Abu daya ta dauka a ciki, kalmar da ya yi amfani da ita. "Ba ki da hankali!" Wannan kaɗai ya tsaya a kwakwalwarta. Tana hawaye ta gyada kai. "Eh ban da hankali. Ka yi hakuri, ka yi hakuri." Abinda ta iya faɗi kenan kafin kuma ta tsinci kanta da ƙarasawa wurinsa ta durkusa. "Don Allah Baba ka yi hakuri. Wallahi banda hankali ka taimaka ka kaini asibiti." Kowa kuma sai ya tsaya kallonta, kallon taɓaɓɓiya, ita kuwa kuka take, kukan da take jin har ta mutu ba za ta daina ba. Kukan dana sani, kukan nadama. 'Bijirewa iyayenki ne ya jawomaki.' Wani bangare na zuciyarta ke mata tuni. "Ke mene haka? Tashi ki tafi na yafemaki. Allah Ya kiyaye gaba." Dattijon ya samu kansa da faɗa don abin kuma mamaki ya koma ba shi. Ta miƙe cikin bin umarninsa har da godiya ta ja gefen titi ta tsaya. So take ta tari abin hawa da zai maidata inda ta fito, gidan Aliyu. Gidan da a yanzu Muniru ya tabbatar mata nan kaɗai ne gatanta. Dakyar ta iya ɗaga yatsa ta tsaida napep har sannan idanun wadanda aka yi abin gabansu suna kanta. Ta fadi sunan unguwa ta hau ba ta ko tsaya ciniki ba. Ɗan sahun har da saita madubi yana kallonta, kuka take yi babu makari (hannu ko gefen mayafi), ba ta damu a ganta ba. Ba ta da zaɓi akan ko ɗaya. Nadama ce tsantsa da dana sani. "Bansan zai jawomin baƙin jini har haka ba, a lokacin giyar soyayya ce ta kwasheni. Ban san haka zan koma ba. Ramlat nada gata ta kowane bangare, iyayena ba su rageni da komai ba. Amma na kasa yi musu biyayya akan abinda bai taka kara ya karya ba, wannan wane irin sakamako ne? Ni na dawo haka?" A fili take zancen, ko kuma zantuka. Mai adaidaita sahu tun yana tsoro da yi mata kallon taɓaɓɓiya har ya gane kamar damuwa ce da ɓacin rai ya jawomata komai. Tausayinta ya kamashi, kamar ya ce dama duk wanda bai bi iyayensa ba, rayuwa za ta zo mishi a baibai, sai kuma ya ja bakinsa ya yi shiru. Dakyar ya samu ta mishi kwatancen inda za ta sauka, ta ciro dari biyar ta mikamasa babu batun karɓar chanji. A farko ta yi niyyar shiga gidan Maman Anas, sai kuma kalaman Munir suka tunzurata ta bude gidan Aliyu ta shiga. Mashin dinsa yana nan kuma inji a kunne shaidar ya dawo, tana shiga falon hayakin sigari da ƙamshin shisha ya karaɗe hancinta, ko mutum dakyar kake iya hangowa a falon. Ba ta yi mishi magana ba, shima bai mata ba sai ido da ya bi ta da shi har ta shige ɗaki. Bai taɓa zaton dawowarta a ranar ba, wannan ya ɗan kashemasa jiki. Yana son Ramlatu, abinda ya sanyawa ransa shine ba ta iya magana ba. Shi kuma ba ya son raini, idan shi ya fadamata, ya isa ne. Ita kuwa ba ta isa ta fadamasa ya kyale ba. *** Sallolin da suke kanta ta biya, zama ta yi tana lazimi har aka kira Magriba ta ɗora da shi. A hankali yunwa ta addabeta, ta fito falon. Hayaƙin ya tafi sosai, sai ta kula da labulayen da ya ɗaga, gami da ware fanka. Kai tsaye kicin ta shiga, Allah Ya taimaka tana da miya don haka taliya fara kawai ta dafa ta dumama miyar. Nan ma koda ta fito ba ya falon, ɗakinta ta wuce, ta dawo ta dauki ruwa ta koma ta kulle da muƙulli.   Tana cika cikinta ta jawo wayarta da zummar kashewa. Karo ta ci da sunan Muhibbat na yawo saman screen din da alamar message. Budewa ta yi ta soma karantawa.   *Assalamu alaikum matar yayana. Naji shiru ba ki zo ba, Yaya ya cemin ba ki jin dadi. Ba haka na so ba dai, amman ba komai. Allah Ya saukeki lafiya. Nagode sosai."* Wasu hawaye suka zubomata saman ƙuncinta, Muhibbat su ne irin matan da ake kira ƴan aljanna. Mace ce da ba ta da riƙo, ba ta da fushi. Idan ma ta yi, ba ta da wuyar sauka. Ta sani, laifukan da ta yi mata ba zasu ƙirgu ba. Ta tsinci kanta da rubutamata saƙo kamar haka.   *Kyawawan halaye su ne linzami a kowane tafiya. Su ne nagartar kowane ɗan adam da cikar kamala. Ki godewa Allah, kin dace da samun haka. Ina mai jin kunyarki a koyaushe. Ki yafemin, ni mai tarin laifuka ce gareki. Ki yafemin domin Allah.* Tana kaiwa nan ta aikamata, wayar ta ajiye ta mike ta soma kokarin rage kayan jikinta. Ruwa ma dakyar ta ke taɓawa ta yi alwala tsabar sanyin gari. Wayarta ce ta dauki ƙara, ta yi azamar dubawa. Hajiya ce. "Salamun alaikum, Ramlatu kina lafiya?" Wani rauni ta ji da na zuciya da gangar jiki. "Waalaikumussalam. Hajiya ina wuni?" Ta amsa kafin ta kara tambayar tana ina? "Ina gidana." Shiru ya dan biyo baya kafin Hajiya ta ce. "Toh Alhamdulillah. Bari na bar ki haka dare ya yi. Da safe ma yi magana." Daga haka Hajiya ta katse kiran ta bar Ramlat da bin waya da kallo. Sai kuma jikinta ya bata watakila sun yi magana da Hajja. Hakan bai mata dadi ba, kenan zargin Munir na jefa iyayensu cikin damuwa ya tabbata a kanta. ***   Ita kuwa Hajiya tun bayan Magriba Hajja ta kirata ta fadamata komai. A farko ma ta dauka Ramlatun gidan ta je.   Hajiya ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba,  ta kira Munir ta yi mishi tas ta kara da fadin. "Don ka wulaƙanta ƴar uwarka a gaban Bilki me yake yi? Idanunka sun rufe ka mance wacece Bilki a wurin Hilal! Ko bayan ranmu kai ba mai rufe sirrin Ramlatu bane? Wato ka gwammace Ramlatu ta shiga duniya a bayan babu mu, akan ta zauna cikin sutura a gidanka? Wallahi Muniru koda wasa na ji ka ƙara sanya baki cikin lamarin Ramlatu sai na saɓamaka tunda ba alheri ne ke kai ka ba!" Daga haka ta katse kiran tana hucin ɓacin rai. "Me ya yi?" Muryar Abba ya sanya kirjinta dokawa tara-tara. A falonsa take wayar duk a zatonta wanka ya shiga. Ya ƙaraso yana dubanta. "Me ya faru ga Ramlatun?" Ta rasa me za ta ce, dole ta fadamasa. Ransa ya ɓaci, shima wayar ya cira ya kira Muniru. Ranar dai Munir sai da ya yi dana sanin zuwa gidan Hajja har ta kai shi da ganin abinda zai jawomasa ɓacin ran iyaye.    Bayan kammala wayar, Abba da kansa ya umarci Hajiya ta kira Ramlatun ta ji inda take. Hankalinsu bai kwanta ba sai da suka tabbatar tana gida. "Goben ba kiranta za ki yi ba, da kanki za ki taka ki je gidanta." Abinda Abban ya fadi kenan bayan kammala wayar Hajiya da Ramlatun. Hajiya ta jinjina kai, Abban har ya mance da alwashin da ya ci na cewa ba dai su taka gidan Ramlatun ba idan  ta auri Aliyu. Murmushi kawai ta ɗan yi. Ɗa da mahaifi kam sai Allah. ***   "Sau nawa zan ce ka rabu da ni? Na gaji da tuban muzurunka!" Ta fadi a fusace bayan ta yarfe hannunta daga nashi. Aliyu ya kara marairaicewa. "Ki yi hakuri Baby, kema kin sani ina sonki. Ban san meyasa kika kasa gane cewa raini kawai na tsana ba. Wannan kaɗai ne dalilina na kai maki hannu. Amma wallahi matukar kin kiyaye ba zan ƙara ba. Ki yi hakuri don Allah." Ta yi shiru kawai ta kyaleshi ta ci gaba da ninke kayan wankinta. Kwanaki biyunnan kayanta na wanki sun taru, ba ta iya wankin saboda kasala da kuma zirga-zirgar makaranta. "Yauwa ki haɗa kayan wankinki wuri guda, yau zan kai maki wurin mai wanki da guga. Naga ma zannuwan gadonki suma sun yi dauɗa." Ranta ya ɗan yi sanyi amma ta waske ba ta nuna ba. Duk daurewarta da rashin sakin fuska sai da Aliyu ya rinjayeta suka shirya. Karshe ma har ya ja ta dakinsa ya biya bukatarsa. Sai gasunan suna hira da dariya abinsu. Shi ya taimaka mata da komai na gidan suna dariya. Wayarta ta yi kara suna falo a zaune suna hira. Ganin sunan Hajiya ta dauka da sauri, wannan karon muryarta a sake ba kamar jiyan ba. "Gamunan a kofar gidan naki. Allah Yasa dai shi dinne, nan dai Rafee'ah ta kwatantawa Malam Tanko." Ta dauka mafarki take don haka ta kaiwa cinyarta duka, aikuwa sai ta mike har da doka tsallen murna, Aliyu na kallonta kawai. "Toh Hajiya bari na leƙo na gani." Ta katse kiran a gaggauce ta dauki ɗankwalinta ta daura. "Ya dai?" "Hajiyata ce ta zo Sweet Aliy, ka tayani murna." Ba ta ma saurareshi ba ta fita da sauri. Aliyu ya bita da kallo yana tunanin anya kare bai lashewa Ramlatu zuciya ba. Tsohuwarnan ba ta taɓa takowa gidansu ba sai yau. Amma ya zama dole ya danne ɓacin ransa, ko ba komai yana saka ran ba hannu Rabbana za ta zo gidan ba. Ya mike ya shige dakinsa don sanya sutura ta kamala madadin singelet da gajeran wando dake jikinsa. Hajiya ta shigo bisa jagorancin Ramlat ta zauna. Jikin Ramlatu har rawa yake don ta ma rasa irin tarbar da za ta yi mata. "Hajiya ki ƙaraso dakina." "A'a bar ni anan dai." Fadin Hajiya tana ƙarewa falon kallo, ba laifi ya yi kyau. Aliyu ya fito da sallamarsa. Nutsuwar da ya yi da kuma kalar gaisuwar da ya yi ga Hajiya ba karamin burge Ramlat ya yi ba har mamaki ya kusan kasheta a zaune. Hajiya ta amsa fuska a ɗan sake, kafin kuma ya mike yana amsa gaisuwar A'isha ya fice daga gidan. Ba wani jimawa Hajiyar ta yi ba amman Ramlat ta ji dadi ba kaɗan ba. Ta so Hajiyar ta ci abinci ta ce sam. Dakyar ta samu Hajiyar ta karasa ɗakinta ta gani da kuma kicin. "Gida ya yi kyau, Allah Ya yi albarka." Ta furta sadda take karewa kicin din kallo. Da zumuɗi Ramlat ta amsa. Har kofa ta yi musu rakiya tana jin kamar kada su tafi, farin cikinta ma har da saƙon da Abbanta ya aikomata na kudi. So yake ta rage tambayar Aliyu komai musamman na dawainiyar makaranta, burinsa ta zauna lafiya ba tare da ta miƙa hannu da yawan bani-bani ga miji ba. ***   BAYAN WATANNI TAKWAS Dubansa ta ke ranta a ɓace, shi kuwa tsayawa ya yi yana karemata kallo. "Ba don tulelen cikinnan ba Baby, wallahi da sai na kifar da ke na bi ta kan gadon bayanki na fice." Ta gyada kai. "Za ka iya ai! Wannan kadan ne daga aikinka. Aliyu ina aka taɓa haka? Tun yaushe nake maka batun kayan Baby kana yimin kwana-kwana. So kake na je asibiti a zageni? Kai kullum zancenka ba zai gagara ba! Kullum zancenka kenan! Ni na fadamaka lallai i lalla sai ka yimin abin kece raini? Naji na yarda ko nawa ka kashe ka siyi irin wanda kake da muradi wannan kai ta shafa, amma wannan na amfani urgent bai kamata ka yi wasa da shi ba." Ta fadi kamar ta yi kuka. Ta gaji da gafara Sa ba ta ga ƙaho ba. Haihuwa ta matso kullum cikin ɓoye laifin Aliyu take tana cewa ya siya kayan haihuwa don ta gaji da abin maganarsa. Auren da duka-duka ko shekara biyu ba su rufa ba ta kai ƙararsa ya fi a ƙirga, ciki ne kadai ke sanyawa ba ya kai mata bugu yanzun, amma fa bai fasa dukkan wani rashin mutunci ba, sai abinda ya ƙaru. Ga sauyin rayuwa da ta ƙara lulluɓesu, komai sai a hankali. Ta lura ba shi da niyyar yin ko yaya ne. "Kin gama?" Ya fadi yana hade gira. Ta kalleshi a kaikace, duk shan sigari da shaye-shaye ya ƙara motsar da shi, koyaushe ci yake amma a bushe. Leɓɓansa kuwa baƙin da suka yi ko sha'awa basu ba ta. "Nace kin gama?" Shiru ta kara yi mishi. "Ke bari ki ji, ya dace ace kin gama sanina amma kamar bokon kike zuwa  kawai ba don ki amfana da iliminki ba Baby. Ni Aliyu ba ki isa ki sauya ra'ayina ba, abinda nayi niyya shi zan aikata. Ko yau kika haihu washegari zan siyo duk abinda ya kamata, na fadamaki akwai kudadena a wurin Shamsu Case, wannan satin zai ban, a kanki da Babynmu zai ƙare. Ke wai ba daga gidanmu za'a kawo kayan ba ma? To ki samamin lafiya." Zai gifta ta kara tare hanyar, shi dariya ma ta ba shi. Gaba daya hancin ya bude ga uban rama da ta yi. Wuyanta wani baƙi da ya ƙara ba'a magana, hakanan fuskarta. "Naji, naji za'a kai daga gidanku, amma don Allah ka yimin wannan alfarmar ka fidda kanka da kuma ni kunya a asibiti, haba Aliyu, ta yaya zan je banda ko zanin rufe yaro? Na gama cika baki a ko'ina ka yimin dukkan siyayyar da ta dace, haihuwa fa ba'a saka mata rana, ko yaushe za ta iya kama mutum." Tsaki ya ja. "Shikenan, ba dai rigar jariri ba ce da famfas? Zan tahomaki da su." "Ba su kadai ba ne, ko ka manta da list din da na ba ka na asibiti?" Ya taɓe baki gami da sanya hannu ya kauda nata hannun jikin ƙofa. "Ki turomin ta text." Daga haka ta kauce din ya fice, ranta fatan ya kasance gaskiya take. Alokacin kuwa ta fiddo takardar ta shiga rubuta dukkan muhimman abubuwan ta aikamasa. Fatanta Allah Yasa ya siyo din, zuwa yanzu ta gama sanin Aliyun ba shi da tabbas ko kadan. Zai yi wuya ya daukarmata alkawari ya cika. Rayuwa yanzun ta kara juyamusu baya, kasuwa ta ja wa Aliyu baya sosai, hakan kuma har da rashin maida hankalinsa ga abinda ya dace. Babban bakin cikinta yanda ba damar ya ganta da ƴan chanji sai ya san yanda ya yi ya dauke. Ta sha zuwa ta ganshi cikin sif dinta yana mata bincike. Wannan abu ya fi komai ci mata tuwo a kwarya. Idan ma ya dauka ta riga ta san a mashaya yake ƙarar da su. Akan hakan har yaji ta yi zuwa gidansu, ta share dukkan gargadin Munir ta watsar. Sai da ta yi kwanaki goma cif sannan Aliyu ya kasheta da dadin baki ta shirya ya zo suka tafi. Iyayen kawai kallonta suka yi. Kusan a yanzun ma basu kaunar shiga faɗanta da Aliyu don a karshe kunya take ba su. *** "Please kar ki dameni, sata kike so nayi na kawomaki wai? Ban samu kudi ba, iyakar abinda zan iya yi kenan. Mtsw." Ta bishi da idanu kafin ta maido duba ga kayan da ya siyomata. Gwanjo ne, gwanjon ma ba masu kyau ba. Rigunan jarirai ne, biri da wando kala uku sai karama ta ciki shima kala uku sai wani tsohon showel fari wanda ya tashi daga farin ya koma ruwan madara. Sai kuwa famfas leda guda. A gefe kuwa Pad din mata ce karamar leda guda sai man goya da reza. "Shi kadai za ka iya siya Aliyu? Wannan su ya dace da haihuwarka ta farko? Ɗan farko fa Ali..." "Dillah Malama ki yimin shiru mana!" Abinda ya ce kenan a tsawance wanda bai ko girgizata ba, idan da sabo ai ya ci ace ta sabI think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/HMV9ZSdNmab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 22) "Ba zan yi shiru ba saboda wannan wulaƙanci ne! Ka wulaƙantani da abinda ke cikina. Haba Aliyu! Sai ka ce ba kai ka min cikin ba? Wai dama soyayyar da kake yimin a baki ne? Wane zaƙin kalamanka ne ban ji ba akan ɗanmu na fari kafin na shigo gidanka? Wannan shi ne tukuicin son?" Ta ƙarashe kamar za ta fashe da kuka, idanun sun kaɗa tsabar baƙin ciki da ɓacin rai. "Mtsw. Soyayyar ta ci uwarta! Soyayya ta wuce wanda na nunamaki a shimfiɗa? Inace yanzu tukuicin son ne a cikinki? Da ace bana haihuwa ni bansan ma irin gorin da za ki yimin ba. Ramla abinda zan iya siya kenan, banda arzikin da ya fi hakan, idan kuma sata kike so na yi ni Aliyu ba ɓarawo bane, na zan fara a kanki ba. Ko yau kasuwa ta tashi ai ɗan koli ya ci riba. Har mamakin ma yanda kike kokarin sauyamin tunani nake wallahi, bani da tabbas ko kin soma bin malaman tsubbu. Ina mamakin yanda wataran nake bin ra'ayinki na aikata abinda ban yi niyya ba. Dadin abin Babana Malami ne, zan bazama neman tsari." "Yau kuma shirka kake zargina da aikatawa? Kodayake ba ka da laifi, ko me ka aikata laifina ne da na nace akan aurenka. Dama kyakkyawar damina daga bazara akan gane ta! Aliyu wannan bakin cikin ya isheni, na gaji da shaƙarsa. Aliyu kai da abinda ya shafeka bana sonsu, ka sauwakemin na koma na yiwa iyayena biyayya ko zan ga haske a rayuwata. Na jima ina nadamar aurenka, yau kam na gaji. Na hakura da kai ko kai kadai ne ɗa namiji a duniya." Wata dariya ya yi mai ban haushi da ya sanya hawayen da Ramlat ke dannewa suɓucewa ya zubo. Ya shafi fuskarta ta buge hannun ta ja baya tana sheshsheƙa. "Baby, wallahi kinji rantsuwar ɗan musulmi ba wanda ya isa ya rabani da ke. Aurena da ke mutu ka raba. Kar ki ji ina batun wai bana sonki, ba zan iya rabuwa da ke ba har abada. Kiyi hakuri dai mu ci gaba da lallaɓawa a haka. Maman Baby kuma Baby." Daga haka ya soma tafiya zai bar ɗakin, ta yi wani irin zabura ta bi bayansa ta rike rigarsa ƙam ta baya idanunta har rufewa suke yi. "Sake ni Aliyu. Domin Allah ka sakeni!" Ta zame ta durkusa a ƙasa mararta na tsunkulinta. Ya dubeta ya ja tsaki. "Wai Baby kin san tsinuwar Allah da Mala'ikun da kike jawowa kanki bisa wannan furucin? Baby na fadamaki ba zan sakeki ba. Ban aureki don na sakeki ba har abada." Ta ci gaba da kuka sosai, ya fisgi rigarsa ya yi gaba ya kyaleta anan. Sai da ta yi mai isarta kafin ta mike jikinta duk ya yi mata nauyi ta zauna gefen gado tana faman tunani. Kayan ta kara kallo ta kauda kai. Ba ta da ko sisi a hannunta balle ta fitar ta siya abinda ya dace, idan kuma ta bar kayan da Aliyu ya kawo ita ce da jin kunya a asibiti. Don haka ta mike ta tafasa ruwan zafi ta kawo ta jiƙasu. Tunani sosai ke daukarta ranta na suya, tana kokarin yin takatsantsan adalilin kulawar da aka ce ta yi saboda muddin ba ta yi wasa ba za ta kamu da hawan jini. Mararta na kara murɗamata. Ta yi kokarin tashi ta wanke kayan sai dai ta kasa. Abu kamar wasa tun yana yi yana lafawa har ya soma yin tsanani. Aka yi Magriba, Isha'i ta zo ta gifta, ba labarin Aliyu, cikin kuma bai bar ciwo ba. Juyi kawai take tana salati, cikin taimako na Ubangiji wayarta ta dauki suwwa. Ta kai hannu ta daga ba ta tsaya duba sunana ba ta sanya a kunne. "Assalamu alaikum." Daga jin muryar Abbanta zuciyarta ta karye, shi kuwa ya kira ne ya yi batun bude account na banki da ya ce ta yi, ta soma kuka ba ta ko iya amsa sallamar ba. "Ya Salam, Ramlatu? Lafiya kuwa?" "Abba cikina, ciwo yake min." "Ina shi Aliyun?" "Ya fita." Ta amsa murya na rawa. "Kwantar da hankalinki, yanzu zan turo Rabi." Bai tsaya sauraron komai

Chapter 18 of 58