Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kunne ya miƙa wa Hisham. "Madam." Hakan da ya faɗa ya ankarar da Hisham ko wace, suka gaisa sai dai ya ɗan yi turus jin muryar kamar ta babbar mace amma bai nunamishi ba. A karshe ya mikawa A'isha wayar kamar yanda ta buƙata. Ita kanta ta yi mamakin jin muryar mace kamar Hajiyarta. Abinda ta kawo, matar ƙatuwar murya gareta ne kawai, banda wannan ba wani abu. Sai da ta kawowa Hussein ruwa da lemu kafin ta koma wurin Ramlat. ***   "Kai kin ganshi? Wallahi kamar wani buzu." "Astagfirullah, ke fa matar aure ce." Ramlat ta katseta da sauri. Anan itama ta ankara da katoɓarar da ta yi, ta ja istigfari kafin ta yi dariya. "Allah kuwa ban faɗa don wani abu ba, kawai dai na ganshi ɗan gayu. Da ace ba ki taɓa aure ba kuma ke fara ce, ba karamin matching za ku yi ba." Daure fuska ta yi, ta ɗan ji takaicin kalaman A'isha, sai ya ɗan yi mata fami da irin cin zarafin da Halima ta yi mata a ofis. Ganin yanda fuskarta ta sauya ne yasa A'isha gyara zancenta. "Kiyi hakuri, wallahi ba wai ina nufin wani abu ba, kawai ganin irin yanda ya haɗu ne sai nake ga kamar bai dace ma ya auri wacce ta taɓa aure ba ball.." "A'isha! Ya isa haka don Allah ki rabu da ni. Wai ni sa'arki ce?" Ɗan taɓe baki A'isha ta yi tana murmushi. "Allah Ya ba ki hakuri babbar Yaya, na yi shiru." Ramlat ba ta ƙara magana ba don tasan ban hakurin ma irin na ƙannen zamani ne. Karshe ma miƙewa ta yi ta soma gyara mayafinta. "Tafiya zan yi, tunda har na miki mai wuyar ai shikenan." Anan ne kuma A'isha ta marairaice. "Wallahi ba zan iya cin abinci da baƙon nan a wurin ba. Don girman Allah ki yi hakuri ki zauna. Ya ce fa har gida zai kaiki." Gaba daya ta koma kalar tausayi tana roƙonta. Wayar Ramlat ta yi ringing, ganin Hajiya ce yasa ta nunawa A'isha "Kin gani dai da idonki ko? Uwata nemana ta ke yi." Daga haka ta ɗaga wayar, aikuwa tambayar da ta soma jefomata shi ne me ya tsayar da ita? Da sauri A'isha ta karɓi wayar ta yiwa Hajiyar bayani gami da roƙon alfarmar Ramlat ta jira har baƙon ya tafi sannan Hisham ya maidota. Dakyar Hajiya ta amince don ta ce ba hannunta idan Munir ya tambaya. Suka kammala wayar ta mikawa Ramlat, bayan gama jin bayanin Hajiya ta amsa da toh kawai kafin ta wurgamata harara. Dariya A'isha ta yi tana kara nema afuwa. *** Sai da suka idar da Magriba sannan suka hau saman dining table. Sai a sannan ne da Hisham ya matsa, Ramlat ta fito.   Bayansa kawai take hangowa don ya ba ƙofar ɗakin baya, ko kadan ba ta gane ko waye ba har ta ƙaraso da sallama. "Haba ko kefa Antinmu, amma ace tun ɗazu sai kiranki ake kina togewa." Murmushi kawai ta yi jin kalaman Hisham, shi kuwa Hussein jin an ce Anti yasa ya tsammaci wata babba ce don haka ya ɗago ya dubeta da zummar gaisuwa. Yanda bakinta ya tsaya a bude haka na shi ya dakata, mamaki ne a saman fuskar kowannensu. 'Wannan matar ko dagasken dai mayya ce?' Fadin Hussein a zuciyarsa cikin son gasƙata abinda matarsa ta hasaso a kan Ramlat. Mamakin yawan haɗuwartasu yake. Ta kai har ya ganeta, kamanninta sun yi zaman dirshan a ƙwaƙwalwarsa. Toh haka itama Ramlat, haduwarsu na ba ta mamaki. Da kuma ace ta san shi ne baƙon, da har ya fita ba za ta yarda ta fito ba. "Kun sa juna ne?" Tambayar Hisham ya katse kallon ƙurillar da suka tafi yiwa juna, kusan a tare suka kauda kai, ta ƙaraso ta maze ta zauna kujerar dake kallonsa. A'isha da Hisham dai abin mamaki ya basu, yanayin sauyawar kowannensu. "Ina wuni, an zo lafiya?" Ta gaisheshi cikin dakiya da kuma son kauda zargi daga zuƙatan ma'auratan da suka zubamusu ido. Shima ya amsa a tausashe.   "Lafiya." "Wai ba za ku amsamin ba, kun san juna ne dama?" Hisham mai naci, ya ƙara neman ba'asi. Hussein ya dubeshi da dara-daran idanunsa yana dan murmushi. "No, yau ne ma farkon ganin da na yi mata." Ta dubeshi da sauri, itama ita din ya kalla har lokacin murmushinsa bai gushe ba. Me yake nufi da yau ya soma ganinta? Ta dubi Hisham ta yi murmushin yaƙe kawai. "Uhm, idan ma ta yi wari ai ma ji, ko ya kika ce Princess?" Ya fadi yana duban A'isha mai kokarin zubawa Hussein abinci. Dariya kawai ta yi don ita kam kanta ya daure, ta kuma sani Hussein ya fi ƙarfin Yayarta. Da kamar wuya abinda Hisham ke nufi ya tabbata. Ramlat ji ta yi kamar ta ɗaga farantin tangaran din ta kwaɗawa Hisham a kai tsabar haushin da ya ba ta, shi kuwa Hussein shanyewa ya yi kamar bai gane inda zantukan Hisham din ya dosa ba. Tunda ta ɗora kai saman farantin da A'isha ta yi serving dinta, ba ta kara ɗagowa ba balle idanunsu su yi katarin haɗuwa. 'Dan uwansa ya fi shi kirki, sam bai da kirki wannan.' Ta fadi hakan a ƙasan ranta, a fili kuwa guntun tsaki ta ja wanda karaf ya shiga kunnensa. Ya ɗago a hankali ya dubeta, ƙaramin bakin ya kalla da mamakin ma yanda tsaki ya fito daga cikinsa. Koma mene ya san da shi ta ke. Murmushi kawai ya yi ya ci gaba da cin abincinsa a nutse.   Ita kuwa Ramlat gyara ƙafafunta da za ta yi, ta ji ta taka wata lallausar ƙafa kamar carpet. Alokaci guda ta yi aiki biyu, ta janye ƙafar a razane gami da dubanshi idanu a waje, kallon da ya jefamata ne ya yi sanadin ƙwarewarta. Ta shiga tari ba ƙaƙƙautawa su A'isha na mata sannu gami da zubamata ruwa a kofi. Shi kuwa ci gaba ya yi da kai lomarsa irin ko a jikinsa. Sai da ta sha ta samu nutsuwa kafin ta mike tsaye. "Ina za ki kuma?" Ta dubi A'ishar. "Na ƙoshi, gida ma nake son tafiya yanzu." "A'a ki jira, kinga ma Allah Ya so ni da rahmarSa. Tunda ga Hussein sai ya kaiki har gida tun da Madam dinsa ba ta nan, kuma ni sai na zauna na kula da tawa Madam din." Da wani irin sauri ta juyo ta kalli Hisham. Shi kuwa ransa fari ƙal, ya shinshino wani abin tsakaninsu. Koda ba soyayya ba, toh shakka babu akwai wata a ƙasa, bai yarda da cewar basu san juna ba.   "A'a, zan tafi kar ka damu." Daga haka ta faɗa ɗaki ta dauki jakarta da mayafi, jikinta har wani rawa yake tsabar kaɗuwa ta fito. "Ai fa na rantse sai dai ki jira abokina ya saukeki." Ji take inama Hisham din ba sa'anta bane yanda za ta ji dadin gasamishi baƙar magana. Dole ba yanda ta iya ganin A'isha na nanata mata ba haka suka yi da Hajiya ba, zama ta yi ta daure fuska kamar kunun tsamiya. Har ya kammala cin abincinsa bai ce musu uffan ba, sarai ya ji shirin Hisham din, ya kuma san da biyu ya yi. Shi dariya ma ya ba shi amma bai yi ta a fili ba, wato dai dagasken Hisham gani yake kamar wata alaƙar ce ta soyayya tsakaninsa da wannan baiwar Allahn.   "Alhamdulillah. Abinci ya yi dadi. Nagode." Abinda ya ce kenan yana goge baki da tissue, ya zura hannu ya ciro kudin da bai san adadinsu ba, ya ajiye saman tebur. "Ga tukuici ka ba Amarya." Hisham ya yi dariya sosai yana kallon falon inda A'isha ke zaune tare da Ramlat.   "Ai ba ita daya ta girka ba, kusan ma ƙarfin aikin Antinmu ce ko ince Yayarmu." Hussein ya ɗan ɗaga kafaɗa da sunan ko a jikinsa gami da miƙewa. "Nidai na bayar, girki kuma ya yi dadi." Murmushi Hisham ya yi sanin hali. Kudin ya dauka ya je ya dire saman cinyar A'isha. "Ga tukuicinku na girki, Abokina ya yaba." Ramlat ba ta ce uffan ba, A'isha ta shiga godiya bai ko amsa ba sai murmushi da ya yi mata. "Toh Madam, ni zan wuce. Allah Ya bar zumunci." A'isha ta mike tana ƙara yin godiya. Ya yi waje. Hisham ya dubi Ramlat. "Antinmu don Allah ki yi hakuri ki taso ku tafi." "Wai shi ya ce maka zai kai ni? Ni da ka bar ni na hau adaidaita." "A'a. Wallahi na san Hussein daidai gwargwado, yana da kirki. Ina tabbatarmaki har ƙofar gida zai kaiki." Ta sauke ajiyar zuciya, dolenta ta taso suka fito, Hisham da kansa ya budemata mazaunin kusa da direba ta shiga. A'isha na gefe tsaye tana kallonsu. Wanna dacewar da ta ke kira ba zasu yi ba, sai ta ga sun yi fiye da dukkanin zatonta. Murmushi take, wani irin murmushi mai haɗe da zumuɗi da kuma fatan alheri. Har Hisham ya zagaya suka yi sallama da Hussein da ke tsaye jikin motar ya riƙe murfin motar, ba ta daina kallonsu ba. Suka yi sallama ya kara yi mishi godiya sannan ya shiga motar. A nutse ya soma tafiya har ya bar layin, wani shiru ne kawai ke gudana tsakaninsu. Kowanne da abinda yake saƙawa a ransa. A ɓangaren Hussein murmushi ya yi, tunaninsa kawai Hajiyartasa, da za ta ga yarinyar a gaban motarsa yau kam hauka ne kawai ba za ta yi ba. "Kin hau motata ba ki sanar da ni inda zan kaiki ba." Wani kululun baƙin ciki ya tokaremata ƙahon zuci. Yana magana kamar ma ita ce ta ce za ta hau ya manta cewa bisa tilas take zaune a ciki. "Wace unguwa?" Ya tambaya kai tsaye ba tare da ya dubeta ba, kuma bai tsaida motar ba. "Sharaɗa." Ta furta a ciki-ciki, sai a sannan ya juya ya kalleta, fuskarta na kallon waje. Ya maida kai ga tuƙinsa, gudu kawai yake ita kam ko a jikinta.   "Alaƙarku fa?" Ta ji muryarsa cikin kunnuwanta, sai a lokacin ta dubeshi. Cikin rashin fahimta ta ce. "Me ka ce?" Fuskarsa a sake ya dubeta kaɗan, ta kauda kai shima ya kawar. "Alaƙarki da Hisham." Kamar ta ce ba matsalarta ba ce, sai ta ji ta kasa. Ta ɗan ja sakanni kaɗan kafin ta amsa. "Mijin ƙanwata ne." Ya gyada kai daidai sadda ya sha kwanar da za ta sadashi da titin sharaɗa.   "Sai ina?" Ta dubeshi, ita wannan magana guntu-guntun takaici yake ba ta, ganin ba ta gane ba ya ce. "Ina zamu yi?" Ta yi mishi kwatance har lokacin muryarta ba daidai ba, ta rasa dalili. Gyada kai kawai yake yana sauraronta da dukkan hankalinsa, har ta gama ya rasa dalilin da yasa bai so ta tsaya din ba. Ya numfasa ya shiga bin kwatancen har suka iso layin da take fadi. "Ya isa, zan sauka a nan." Ya dubi wurin, akwai jama'a ba laifi, gidajen unguwar ya kalla, ba laifi suna da kyan gani. "Kofar gidanku fa?" Girgiza kai ta yi. "A'a ba sai mun ƙarasa ba. Nagode." Gyada kai ya yi. Ta murɗa kofar ta ji ta gam! "Kiyi hakuri. Ina mai ba ki hakuri on behalf of my wife na abinda ta yi maki kwanaki." Ta ɗan tsuke fuska. "Wa kenan? Ai ban sanka ba balle har wani abu ya haɗani da matarka. Ni dai Ramlat kake nufi?" Wani murmushi ya yi da har haƙoransa suka bayyana, irin murmushin da Hajiya Zeenatu kadai ke da ikon gani. Ta ɗan kauda kai daga kallon da ya ke jifanta da shi, murmushin ya kara kashemata gangar jiki da ruhi. "Ramuwar gayya kenan fa?" Ta yi shiru ba ta amsa ba amma ta ɗan murmusa itama ganin ya ɗagota. "Shikenan. A gaida su Mama." Daga haka ta ji ƙarar cire lock. Ta dubeshi kafin ta fita ta leƙo ta window. "Nagode, zasu ji. Nima a gaidamin Hajiya." Kusan ta faɗa da biyu hakan yasa shi dubanta, lokaci guda suka yiwa juna murmushi, daga nan ta soma tafiya babu ko waige. Har ta isa ƙofar gidansu ta bude murfin kyaure, sai a sannan ta waiga, yana tsaye ga mamakinta bai tafi ba, cikin sauri ta shige gidan tana mai dafe kirji da wurgawa kanta tambayar abinda ta aikata. Shi kuwa ji ya yi kamar ana jan sa, kwakkwaran motsi kasawa ya yi sai aikin kallon tafiyar nutsuwarta har ta shige gidan. Wayarsa ce ta katsemishi tunanin da ya dulmiya wanda ko za'a kasheshi ba zai ce ga dalili ba, sai sannan ya tuna da cewar murmushi yake, murmushin da ya ƙi ɗaukewa daga saman fuskarsa. Hajiya Zeenatu ke kiransa, ji ya yi gabansa ya faɗi. Ya kasa daukar wayar, haka ta yi ta ƙara har ta katse. Gumi ya shiga tsastsafowa daga goshinsa, ya yi ribas ya bar layin. Gani yake kamar ya aikata wani ƙaton zunubi ga Hajiya Zeenatu. Ji ya yi ya tsani kansa, har lokacin gabansa faduwa yake don tsoro da fargabar inda zai ce mata ya ke. Bai samu nutsuwar kiranta ba sai da ya ganshi a ƙofar gidansa. "Ina ka shiga wai? Me kake yi? Wannan wane irin ziyara ce da bai isa a kammala a awa uku a koma gida ba?" Ya kasa tsawatarwa, ya ji ba shi da wannan kuzarin. Ƙarshe ma ya ɓige da bata hakuri da rarrashi. "Allah Ya huci zuciyarki, yanzu ganinan a gida. Wanka ma zan yi na kwanta na ci abinci a gidan Hisham." "Wanka? Wane irin wanka?" Ya ɗan yi shiru yana jin zuciyarsa na tuƙuƙi, tuhumar ta yi mishi kama da na zargi. "Me kike son ki ce?" Daga can Hajiya Zeenatu ta yi saurin gyara zancenta. "A'a ba komai, gani nayi garin da ɗan sanyi." Ya yi murmushi mai sauti. "Eh haka fa. Amma kin manta mijinnaki ba ƙazami bane ba ko?" Ta yi dariya, daga bisani suka yi sallama. *** HAJIYA ZEENATU...        I just published "BABI NA TALATIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/hTaZiBjDOab 🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️ *_Rufaida Umar_* Bismillahir Rahmaanir Raheem. 31) HAJIYA ZEENATU..   Niamey, Nijar. Tun ajiye wayartasu zuciyarta ta kasa sukuni, ta yi shiru kawai ta zubawa talabijin idanu ba don yana fahimtar yaren ba.   "Ba za ki daina shirmen tunanin ba ko? Na fadamaki ba sau ɗaya ba kuma ba sau biyu ba, mun zo inda za'a share kukanmu." Hajiya Batool Aminiyar Hajiya Zeenatu ke wannan zantukan. Ajiyar zuciya ta yi ta ci gaba da kallonta, dama tun soma maganar hankalin ya koma kanta. "Nasan da haka, amma ina jin tsoron tabbatuwar wancan lamarin Batool, kema kin sani kamar yanda na sani, kwaɓewarsa ba za ta yi kyau ba." Wani dan bazawarin murmushi Hajiya Batool ta saki. Ga ta dai siririya da ita amma naira sun zauna. Yatsunta ta jera zobunan gwal har ya yi yawan da bai yi kyan gani ba. "Ai sai ki yi, gobe da safe wanda zai mana rakiya zai zo mu tafi. Idan ba ganin wannan saurayin mijinnaki a kwalba kika yi kina juyashi ba, ba za ki kwantar da hankalinki yanda ya kamata." Sai a sannan ta yi dariya sosai, ranta kuma ya koma ƙal kamar takarda. "Na ci wuya kafin na cimma dukkan buri a kan Hussein, kema kin san da haka ai. Huum, sai yanzu rana tsaka bayan na gama sanin wa nake tare da shi, wata banza ta zo ta tadamin hankali. Anya kuwa ma dagaske Gora yake? Ni dama tun sadda naga ya hau canki-canka da matsalar da ta kawo wata budurwa, na shiga shakku a kansa." "Toh ba na fadamaki ba, yanzu haka kawai kudinmu ya ci. Akwai irinsa da yawa ai, ba tsoron Allah su zalunci mutane su damfaresu." Fadin Hajiya Batool har da yamutse fuskarta mai kama da kashi. Ta mance su kansu ba tsoron Allahn suka sa gaba ba. *** Washegari kuwa da sassafe sai ga wani tsamurmurin buzu mai jin Hausa raɗau ya zo Hotel din da suka sauka. Shi ya yi musu jagora har wurin Isuhu Bakka Tsoron Allah. Layi sosai suka tarar amma kasancewar ɗan rakiyar ba baƙonsa ne mutumin ba, yasa ya basu umarnin su jira sannan ya shiga ciki. Can ya fito ya musu umarnin su taso. A bakin kofa suka tsaya suna ji mazauna wurin wadanda mafi yawansu mata me, su na zaginsu da yaren kala-kala, Hajiya Zeenatu da Hajiya Batool suka kalli juna don abin ma dariya ya basu. "Wai fa harara a duhu." Fadin Hajiya Batool. Wacce ke ciki na fitowa suka faɗa ɗakin bisa jagorancin ɗan rakiyarsu. Wani ƙaton mutum ne fatarsa har wani ja ta ke yi, yana zaune saman wata ƙaton carpet gefensa kayan tsubbu ne kala-kala, ya naɗe fuskarsa da farin naɗi sai kayan jikinsa baƙaƙe. Kallo ɗaya za ka yi mishi ka san buzun ne na gasken gaske. Suka gaidashi sai dai yarensu ma ba ji yake ba, ɗan rakiyar ya juya harshe ya shiga nanata abinda suke faɗa. Tun da ya soma bai katseshi ba kansa kawai yake gyaɗawa gami da yi musu kallon ƙurillah. Can ya watsa tambayar wacece a cikinsu. Saurayin ya nuna Hajiya Zeenatu ganin ita ke koro jawabin. Ya yi mata kallon tsaf sannan ya maida kai ga ƙasar dake shimfiɗe gabansa. Tambayar sunan mijinnata ya yi da kuma ita kanta. Bayan an faɗamasa ya ci gaba da zanensa a kan ƙasa can ya ɗago ya dubi saurayin yana murmushi yana jawabi, sai da ya gama tsaf sannan saurayin ya dubesu, dama duk sun matsu su ji abinda ke faruwa. "Cewa ya yi, ya ga ma mijinnaki saurayi ne, kuma ƴan biyu ne.  Shi kansa ƴan uwansa basu zauna ba, suna ci gaba da nemansa sannan sun tashi tsaye da addu'a irin wanda sai an yi dagaske. Ya kuma ce akwai mace ɗaya da babu makawa sai ya aureta koda za'a shekara goma ne, rubutacce ne. Ita ce za ta rushe dukkan wani gini da kika yi. Ai ya ce ya gani, ba wurinsa kika soma zuwa ba, kafin zuwanki nan, akwai wanda  ya yi maki aiki." Hanjin cikin Hajiya Zeenatu suka ƙulle, iskar fankar dake kaɗawa bai hana gumi ya tsastsafomata daga goshinta ba. Ta haɗiyi miyau, ta dubi Isuhu don bilhakki fargaba da tsananin kishi ya mantar da ita ba ya jin yarensu. "Ya kammanin yarinyar yake?" Saurayin ya faɗamasa. Girgiza kai ya yi gami da yin yare. Duk suka zubawa saurayin idanu suna jiran jawabi. "Ya ce ba zai ce ga kamannin ba, amma yanzun haka sun haɗu da juna." Ta haɗiyi miyau hankalinta a matukar tashe, idanunta har hangomata Yarinyar kwance jikin Hussein yake. Dagaske dai Gora ba ƙarya ya faɗamusu ba. Nan da nan idanunta suka kaɗa har da ƴar kwallarta. "Don Allah Malam ka taimakamin, wallahi ba zan iya haɗa Hussein da kowace ɗiya ba. Idan har Hussein ya rayu da wata mace koda ta hanyar fasiƙanci ne zan iya mutuwa wallahi. Nidai ko kasheta ne a yi kawai na huta. Idan har mutuwarta zai sauyamin kaddarata shikenan. Ko nawa ne zan biyaka wallahi." Tana kaiwa nan, saurayin ya faɗamishi. Ya yi shiru yana ci gaba da bugun ƙasarsa kafin ya ɗago ya yi jawabi. "Abu ɗaya ya ce za'a iya, shima yana da matuƙar wahala, bai kuma yi miki alƙawarin lallai ne ya yiwu ba.  Idan har za ki iya ku bar garin da ku ke yanzu zuwa wani. Ya kasance komai naku ya sauya daga wannan garin don yana da tabbacin koma wace ce a garin ta ke. Amma kuma ya ce zai wahala shi mijinnaki ya amince da hakan. Sannan yana mai ba ki shawara da kar ki yi wasa da abinda zai ba ki na mallaka, muddin kika yi sake ƴan uwansa na dab da sanin inda yake. Bayyanuwarsa garesu kuwa daidai yake da rushewar duk wani tubalin da ki ka gina." Hajiya Zeenatu ba baka sai kunni, gyada kai kawai ta ke. Ai ko bangon duniya ne za ta iya zuwa muddin mijinnata ba zai suɓucemata ba. Sai dai dagasken itama ta sani, abu mawuyaci ne ya amince da barin garin Kano. "Naji, zan kiyaye ko menene. Zan bi dukkan tsarinsa." Isuhu ya gyada kai cike da gamsuwa bayan ya ji bayanin daga bakin saurayin. Miƙewa ya yi ya shige ƙuryar ɗaki. "Hajiya Zeenatu, ki ce gwara da muka zo?" "Uhum, bari Hajiya Batool, gaba daya cikina ma ya kaɗa wallahi kamar na saki a wando. Jikina yana bani cewa wannan tsinanniyar yarinyar ce da ke bibiyarmu kamar mayya. Ai ko birnin Sin ya ce na koma zan koma balle kuma na bar garin. Naji na yarda zan damƙa amanar dukiyata ga Manaja, idan ya so ko mene ni din sai na dinga zuwa Kanon. Ba zan zauna a yimin sakiyar da ba ruwa ba. Shekara nawa ina yawon kashe kuɗi da fashi a maƙabartu akan Hussein? Ko wacece ta yi kaɗan." Ta ƙarashe a kausashe. Hajiya Batool ta shiga jinjina kai. "Nima ban yarda da ki zauna ki zuba ido komai ya lalace ba. Bari ya fito na shigar da nawa ƙoƙon barar akan wannan shegiyar surukartawa da ke neman mallakemin ɗa. Haba, komai yanzu nashi ƙarewa yake yi a wajenta?" Hajiya Zeenatu dai ba amsa, kowa ya ji da nashi matsalar. Ba jimawa ya dawo dauke da wasu jarkoki biyu na ruwan magani sai wata leda. Tiryan-tiryan ya yi bayani. Ɗan rakiyarsu ya kallesu. "Wannan jarkar ya ce tsakar dare za ki tashi daidai sadda hasken farin wata ya fito, za ki fita tsakar gida tsirara ki yi wanka da shi har na kwana uku. Shi kuwa wannan ɗayan, tsarki za ki yi da shi ki yiwa Mijinki girki da shi har na tsawon sati daya ya ci. Sai wannan ƙullin maganin, ki tabbata kin sanya cikin turare irin mai maiƙonnan, ki dinga shafawa duk sadda mu'amala da ta haɗaki da shi. Shi kuwa wannan layar, a tsakiyar bola za ki binneta ba tare da kowa ya ganki ba, wannan layar shi zai sa ki mallaki mijinki yanda ko uwarsa ba ta isa ta ganshi ta ce ya biyota ya je ba. Shi kuwa abincin da za ki girka masa, shi zai mantar da shi yarinyar muddin ku ka bar garin, ba kuma zai ƙara tunawa da ita ba balle har ya ji yana son zuwa ya ganta. Kinga kenan babu damar da zai ƙara sanyata a ido, idan ya sanyata a ido toh komai zai rushe." Tunda Hajiya Zeenatu ta ke, ba'a taɓa yi mata bayani kan aikinta ba ta ji ɗigon farin ciki ba sai a wannan karon. Gaba daya jinta take kamar wacce aka ɗaure da jijiyoyin jikinta, ta kasa kwakkwaran motsi banda kai da ta gyaɗa, shima sai da Hajiya Batool ta taɓota. Hawa saman bola ta binne ba matsalarta ba ce, ta shiga makabarta ma ta kwaƙule ido akan abin duniya wannan ba ta ɗaukeshi wani abu mai wuya ba. Tsakar dare ne ta tabbatar ba wanda zai iya ganinta kan bola, za ta iya wannan. Abu mafi ciwo mai sanyamata ta ji ta tsani kowace ɗiya mace, bai wuce na zuciyar Hussein da wata za ta mallaka ba. Wannan ya fi komai yi mata zafi. Gani take kamar ta hakura da sauya garin ta zauna ta bibiyeshi har ta yi tozali da yarinyar ta cakamata wuƙa a maƙoshi. Murmushi ta yi, sai lokacin ta samu sukuni, sai a sannan ta samu mafitar da a ganinta ya fi na wannan Malamin. Koda ba ita ba, za ta sanya a kashemata ita yanda wata ma ba za ta ƙara sha'awar shiga rayuwar Hussein ba. Har Hajiya Batool ta gama shigar da nata koken aka ba ta magunguna, Hajiya Zeenatu ba ta san anyi ba don ta tafi tunanin yanda za ta kashe baƙar dagar da ke shirin ruguza gininta. Isuhu kallon Hajiya Zeenatu kawai yake yana nazari, a ido ma karantar mutum yake balle kuma ga ya buga ƙasa. A jikinsa yake jin ba za ta aikata yanda ya ce ba sai abinda zuciyarta ta saƙa mata. Murmushi kawai ya yi don ya ga irinsu da yawa. Ya kuma tabbatar za ta yi kukan nadama, da ƙafarta za ta dawo wajensa ta nemi wani taimakon, a lokacin ne zai nunamata iyakarta. Suka kammala suka biya maƙudan kuɗi kafin su mike su fito, saurayin shi ya kai musu har mota sannan ya wuce da su gidan ƙawar Hajiya Batool, Hajja Mari (Maryam). Kasuwanci ne ya soma ƙulla ƙawancensu, saurayin yaronta ne yardajje mai mata ire-iren aikinnan. Ita ta haɗasu

Chapter 26 of 58