lokacin da suka haɗu dashi." A razane Zeeh ta d'ago kanta idanun ta cika da kwalla, tace. " Akwai macen da take son shi ne?" "Ki mana shiru nan ba gurin tambaya bane, nan gurin share kukan me kuka ne, dan haka ki ajiye min duk abinda yake jikinki,". Jikinta na rawa ta cire sarkan da yan kune,.tare da abin hannun da agogon kome hatta sarkan kafarta sai da tace(🙄🙄 ina masu cewa matar da ta saka sarkan kafarta yar gwagwarmayar ce, babu halin kwalliya kenan) dan haka ta zuge zip din jakarta ta zazzage kudin da yake ciki baki daya, sannan ta mike, kallonta matar tayi sannan tace Mata. "Zaki dauki wayarki kawai, sauran kuma kije, zaki sha mamakin abin da zaki gani, ko mace kika kira a gaban shi sai kunyi fada '." Haka tayi maka alqawarin abin da zata samu. Daga aikin da tayi mata, tana cire kayan da ta bata, ta mai da nata, sannan suka fita. Kallon tabawa tayi sannan tace mata. "Da alamu aikin zai yi tasiri dan ban tab'a ganin irin shi ba." Dariya tabawa tayi sannan tace mata, "lokacin da Lilah ta kawo ni ban yarda ba, sai daga baya kuma na fahimci haka babu wanda ya aikata iya aiki, tanawa manyan yan mafia. Haka yayi matuƙa sama mata daraja, sai dai bata damu da dukiya ba, da ta gina katafaren gida anan London." Jim Zeeh tayi sannan tace mata, "naji tace Bak'a Destiny! Me haka yake nufi!?" " Ehtoh tana nufi mijinki ya tab'a haduwa da wata yarinya maybe," ajiyar zuciya ta sauke kafin tace" Neemrah! Cousin sister din shi ce, nice na kasheta, maybe itace taso kawo min Shamaki a cikin aikina." "Hmm! Amma Lizah ta sanyata a da'irar mutuwa! Ba zata kuma damunki ba, Lizah bata son tayi maka aiki bai ci ba, sabida gazawa ne a gare ta, Lizah takan iya b'ata lokaci akan abin da zai amfane ka, amma bazata ta dauki faduwa ba, ta tsani faduwa ta tsani a kirata da mara nasara." Gyada kai kawai Zeeh take cikin wani irin jin dadi. Tare da wani mugun jan aji ta kafe Tabawa ido, sannan tace. "Yanzu zan juya my liego son raina, yanzun zan juya MALIK son zuciya ta, ya manta wancan matar da zata iya farka da shi cikin sauri, babu wanda ya isa shiga gonata, sannan babu shi babu Nigeria, har abada, ya dawo nan kenan. Mu rayu abun mu." Takawa suka yi (Fatan Alkhairi Zeemalik 🤨🙄)
***
Gombe.
Babu inda Mamah da Dr Ishaq tare da yan uwan Inayat basu shiga niman ta ba amma babu ita babu labari ta, tun Mama tana danne ranta har tasoma zama tana kuka, sosai take kukan rashin Ƴarta , dan tasan ita babbar mai laifin da mutumin da bai san darajar ta ba. Tana zaune ta saka abinci a gaba tana nazarin rashin Inayat da kuma kewar Iyayen ta, wasu zazzafar kwalla ne suka zubo daga cikin idanun ta, kamar wanda aka wurgo shi ya fado falon, ganin kyakyawan abin karyawa a gaban Mamah ya sashi gyara zaman babban rigar shi, sannan ya janyo kayan tea ya shiga hada kyakyawan tea mai mugun kauri ya cika kofi sai da ya shanye tass, ya sake wata jahilan gyatsa, sannan yaja ledar bread sai da ya mata wawuyar ci, sosai sannan ya zubawa Mamah ido wacce take kallon shi kamar ta ga abin tausayi. Domin ci yake babu sassauci..yana gamawa ya mike tare da kallon kome na falon gidan, ya wani gyada kai silently kafin yace mata, "ban da nasan wacece ke ai da nace ko kin fara bakar kasuwa ce. Amma nasan cewa daga hannuna kika fito, sannan kuma anya ba sayar min da Inayat kika yi ba, kika zo kika bude katafaren gida haka, koma meye bani kudi ko na kai ki kotun musulunci na tuhume ki da laifin babba." Wani irin tsoro ne ya shige ta once ta had'iye yawu, kafin ta juya a hankali ta dauki jakarta ta ciro gudan dari biyar ta mika mishi. Kallon kudin yayi in sosai, yana juya ta, kafin ya cilla mata, ya koma ya zauna aw2 wa 1áaá kujeran falon yayi Crossing legs din shi cikin ruwan masifa. Ya shiga gaya mata magana, sosai tun tana iya jurewa har ta fara biye mishi suna gayawa juna magana, kai karshe dai ya gaya mata maganar da ta kusan sanyata suma inda yace mata. "Bak'ar fata! Wacce ta rasa albarkan danginta, idan kin isa ke ba masifa bace ki tafi gurin Mahaifinki, ba zaki iya ba ko! Eh ai nasan ba zaki iya ba, tunda tsohon banzan yace karki taka mishi muhalli, toh bari kiji tun shekarun biyar da zuwan mu, naje na sami dangin ki na gaya musu kin shiga bari, kin sani na sake ki, dan kin kai ni kotu. Akan bana sauke hakkin ki, dan haka kika shiga bariki, ban kuma san inda kike ba, dan haka na rabu dake na zata zagi dawo ki nemi gafarar Baffanki ne, ashe ba h.." "amma Baba, zaka hadu da rahamar Ubangiji kuwa? Meye laifin Mamah da ta soka? Meye kuskuren soyayyar da tayi maka sama da wanda takewa hammadada, shine yau ka watsa mata kasa a idanunta! Ka lalata mata suna! Ka bata mata Soyayyar da mahaifinta yake mata, Baba idan ka rayu cikin salama, akwai dalilin da Allah yasa haka ta faru, kayi fatan mutuwar ka da rayuwar da zaka yi fatan ka mutu sau dubu sai dubu, azabar rayuwa sai ta maka kawayan sai ka ji ranka, duniyar ta isheka, Baba Mun gode da abin da kayi mana,! Inji Balkisu ta karshe maganar cikin Kuka me mugun cin rai, ta juya gurin Mama wacce take zaune ta kurawa baba Ido, tab'ata tayi kawai ta zube a samar kujera babu alamar rai a tare da ita. Dai-dai shigowa Dr Ishaq, wanda idanun shi suka yi jajjur, cikin firgici ta juya tare da cewa.
"Ya Ishaq! Ma..ma..h!" Maganar ta makale.. Kuyi hakuri Insha Allah zuwa 11pm zan wai-waiye ku..✍🏽
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/kCk1bzuMIab
Chapter 16
Na MrsUsman400
If you spend too much time thinking about a thing, you’ll never get it done.
Da sassarfa ya iso kan Mamah, ya tab'a hannunta na dama, yaji jijjiyar dake hade da zuciyarta yana bugawa ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya kalli Balkisu cikin damuwa yace. "Taimaka mu kaita mota." A hankali suka riketa, har waje suka sakata a mota, sanan Balkisu ta dawo cikin gida zata dauki abu ta sami Baba yana lallubar pursed din Mamah. "Yayi maka kyau! Ka fita tun kafin na baka kunya, tunda kai abin kunya gaba ka bashi ba baya ba, kai Jama'a Baba anya kana tanadin lahira kuwa? Kasan akwai tashin hankalin da yafi karfin kwanciyar kabari kuwa? Ka tab'a tunanin kwanciyar kabari kuwa? Wallahi Baba koda hakkin Mama aka Barka duniya ta isheka riga da wanda balle kuma da hakkin Iyayenka, Baba kaje mun yafe maka. Amma karka bari na kuma ganinka anan, domin ka ishe mu ka ishi rayuwar mu!" Daga haka ta shiga dakin su ta dauko hijab ɗinta da na Mamah, ta fito daga dakin ta samu baya nan, kuka take a hankali, har ta isa gurin motar, ta shiga suka nufi asibiti, lokaci zuwa lokaci, yana kallon yadda take sharar kwalla, tausayin ta hade da begen Inayat ya dira a zuciyarki a hankali ya furta. "Ina kike ne Inayat!" "Bamu san inda take ba, hakkinta yaƙi barin mu, Aunty ta sadaukar mana da kome nata, mu kuma mun barta ta tafi empty hand, ta tafi ba tare da tasan dadin mu ba, Me yasa ƙaddara tayi mana haka? Me yasa laifin Mama ya shafe mu?".kuka take tare da shasheka, hura iskar bakin shi yayi sannan ya juyar da kan shi. Har suka isa asibitin bata daina kuka ba, sai da aka kai Mamah dakin da ya dace, sannan ta zauna tana share kwalla, kifa kanta tayi a jikin gadon sosai zafin abin da Baban su yayi. A gurin take zaune tasaka Mamah a gaba da kuka, ita kanta bata yi tsammanin zata iya gayawa Baba Magana ba, amma halin da mahaifiyar su ke ciki yafi karfin kome, gashi da bakinsa yake gaya mata ya b'ata mata suna,.wasu irin kwalla ne suka kuma cika idanunta, taya Mamah ya auri wannan mutumin ba tare da tayi bincike akan halin shi ba, shi ba zuciyar nima ba, shi ba wadatar zuci ba, mutum mai mugun hali haka, gabaki daya, ya firgita musu mahaifiya, wallahi ya kuma zuwa, sai ta sanya an karya kafar shi zasu yi jinyar shi a can. Ta wani ciji cutie lips dinta irin na Inayat.
***
"Aiki ya sami manyan na shiga uku! Inayat wannan shine ake kira one bugu one dauka, wannan kwanciyar, haka don Allah tashi," cizon lips dina nayi kafin na tashi, zaune bawai dan cikin ya girma ba, a'a tsabar azabar laulayi kawai ya ishe ni. Hararar ta nayi sannan na kuma malalewa zan bi kasa, ta riko ni dariya yana kamata. "Allah kina sani jin kunyar amsa sunan nurse, ki dubi mugun abu sai kace akan ki aka fara laulayi!"
"Don ki rabu dani, wallahi duk kece kika ja min azabar wannan abun, kin san yadda na tsani kaina akan wannan cikin? Allah banda ina tsoron Allah da na zubda shi na tsani MALIK Aliyu Mai Nassara, idan na kama shi sai na mishi rashin mutunci sama da wanda yayi min! Wallahi na ga wanda ya sanshi sai na keta mishi rashin mutunci kafin na isa kan shi mara mutuncin". Kallon ta Khady keyi baki sake, kafin tace mata. "Toh Allah Nagode maka da ban san Malik ba, amma da duk alamu Malik namijin duniya ne, wallahi ya iya tsiya, tunda ya iya miki bidiri tun safe har biyar na Yamma, ba da sauki ne dashi ba. Domin mutane irin shi wallahi.".
"Babu Allah a cikin lamarin shi, sun san yadda ake juya taro ya zama sisi but basu tab'a niman Ubangiji ya dafa musu ba, taya kike tsammaci zan mishi idan ya shigo hannuna?" Shiru tayi sannan tace mata. "Ko dan kina da makamin da zaki yake shi ba? Sannan zan baki shawara kiyi hakuri da abinda yayi miki, babu dad'i kan but Allah ya hada ku, kuma dole ki reni abun shi a tare dake, abin da zaki haifa shine makaminki." Tana fadar hakan ta mika min jug din da ta kawo min da ƙanƙara. Tashi nayi zaune sannan nace mata. "Kin kyauta d'azun na dafa zobo, wallahi ina jin kwadayin shi, kin gan shi." Da gudu Abba ya shigo tare da mika min kwanon da ya kawo daga gurin Maman shi, ya ajiye min sannan yace. "Inaya inji Mamah ko! Tace ki san mata miyar ki da kika yi d'azun wai zata zubawa baban mu ne a cikin abincin shi." Kallona Khady tayi sannan ta share batun. Na dauko miyar na zuba mata na kalli agogon na, sannan na zuba mata. Yaron ya fita da gudu, can sai gashi nan an kuma turo min shi, "wai inji Maman Ummi wai itama sannan ki zuba mata da doya." Shiru nayi kafin nace mishi. "Kace bani dashi." Da sauri ya fita, kallona Khady tayi sannan tace min. "Yaushe aka fara zumunci da su?" Kamar bazan gaya mata kome ba na buɗe bakina nace mata. "Tun ranar da tashigo gaishe ni na zubawa Yaron nan Abba, abinci shikenan bani da ikon yin girki sai tazo min." "Hmm! Toh Wallahi karki yarda, idan nasu ne zasu baki ne? Kawai samun guri kowa yana b'oye nashi gaki baki san ciwon nima ba, karki basu. Idan abincin ki ya kare zata baki nata ne, sabida samun guri." Dake bani son dogon magana yasa naki biye mata, an kusan shan ruwa dan haka na shirya kome, tare da Khady muna yi bude bakin, dake tace zama dani yasanya ta dawo da ibadarta yadda ya dace.murmusa mata kawai nake. Bamu gama ba sai takwas muna gamawa muna nufi asibiti, anan muka kwana, da safe na dawo a gajiye, shiga daki na dafa ruwan zafi zanyi wanka, kawai naji suna gulma na kasa kasa. "Eh da alamu anan asibitin ta kwaso cikin ai, amma in dai haka ilimin boko yake gwara na mutum banyi ba. Ina dalili ga mace har mace Am...." Gani na rike da bokitin wanka yasa su suka watse, har sun wuce ni, mace musu. "Banda kaddarar rayuwa! Ba zan zo nan kuna jifana da mugayen tunanin ku ba, sannan cikin jikina ba shege bane, sa uban shi kamar kowa." Daga nan nayi wuccewa ban d'akin, ban kuma magana ba, dan nayi imani da Allah raina ya baci wanka nayi tare da kananun magana, ma fito. Sabida ban yarda dasu ba ko kayana idan na wanke sai. Dai na kira Khady ta kai min gidanta.
A hankali rayuwa take tafiya, cikin jikina yana niman wata biyar, dan ma ina da tsayi sai ya koma ya zauna min a kuguna da kuma kirjina, duk inda ba wuce sai an bini da ido, sai na daina fita idan ba gurin aiki ba.
***
Jikin Maman su Inayat sai godiyar Ubangiji, bata magana amma tana yawan kuka, wanda yake da nasaba da Mantawa da tayi da iyayen ta. Tare da Inayat. Bata hmm bata humm sai an juya ta anyi mata kome, sannan take iya sukuni, abun tausayi. Haka suka sami sati biyu Mariam da Nusaiba suna zuwa, wuni Zehrah da Balkisu suke zaman jinyar ta, ranar da ta fara magana abin da ta fara cewa. "Don Allah ku kai Ni gurin Baffana don sonku da Manzon Allah." Yadda tayi maganar ya tab'a zuciyar Dr dan haka yasan Balkisu da Zehrah suka hada kayan su, aka sallame su, sannan ya dauki hutu nan da sati daya. Koda suka isa gidan su, sun shirya kome akan lokaci. Kullum Mamah waqar ta, a kaita Baffa, sosai Dr yayi musu sayayya na tsaraba sannan suka saka ranar tafiya.
***
"Malik! Ina wannan matar da na yanka fuskarta?" Cikin dariya kamar wawa ya sake yace mata.
"Ai ta koma Poland da ya gaggen fuskar ai kinyi mata kwalliya na musamman." Cikin wani irin Iskanci ita gata ishatu, tab'e baki sannan tace mishi."da yanzun zan mutu kara aure zaka yi?". Shiru yayi sannan ya d'ago kan shi kafin yace mata, "ko mutuwa kika yi zan biki, dan ban shirya matsala ba, don Allah ki bar kira mace kin ji!". Cikin tsiwa tace mishi."dalla malam kayi min shiru sai kace da gaske, ince nan kake wani kula yan matan ka, sai na ci Uwar yarinya idan na kuma ganinta da kai, sai na farko cikin ta na fidda kayan cikin ta na cinye tsabar kishin ka, dan haka a kiyaye idan ba haka ba, zan kashe mace akan ka." Duk barazanar da zata mushi, bata tab'a nuna mishi itace ta kashe Neemrah ba, sabida tafi kowa sanin halin shi kuma zai iya yin kome akan laifin da tayi mishi, ita kuma bata shirya bashi hakuri ba, Sai dai shi ya bata hakurin tunda shi yayi mata laifin kula yan matan waje.. ✍🏽🤦🏽♀️🤧🤤 Barci.
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/Z4fSQukeKab
Chapter 17
Na MrsUsman400
A wise man can learn more from a foolish question than a fool can learn from a wise answer.
Ranar asabar suka bar garin gombe, cike da kewar Inayat dan sun san da tana nan da ita za ayi tafiyar, amma babu ƙaddara ta riga fata. A hankali suka kama hanya tafiya ba na kare ba balle su saka ran sun kusan isa. Lokaci zuwa lokaci Mama tana Share kwallar da ya cika mata ido. Sabida girman kuskuren da ta aikata, yau tana kuma girgiza kai sabida rashin amana da Baba Amadu ya gwada mata, had'iye kukan tayi tare da toshe bakin ta,
(A sauka lafiya)
***
Kallon cikin nayi, a cikin unifoam. Wani irin kunya ce ta kama ni, duk da an fara sanyi, amma zafi nake ji. Tsaki na ja, sannan na kuma dauki rigar sanyin da na saya wancan watan. Kamar nayi kuka haka nake jin zafin jiki na.. kallon agogon wayata nayi na kuma kara sauri, jin cikina yana kugi ya sani sake zuba dumamen da nayi na fara ci, ina tsaki. Har na koshi sannan na kuma shiryawa zan fita Maman Abba ta tare ni tana son gaya min magana. Kau da kaina nayi. Sannan na nufi hanyar fita.
"Inayat kike? Toh kin san a zamanin yanzun zina abin ado ne a gurin yan mata, dan wasu har kafaffe suke da cikin shege."
Wani irin abu naji ya tsaya min a wuya, ban kula ta ba nayi ficcewata. Daga nan ban tsaya a ko ina ba sai gidan Malam. Ina shiga ya kalle ni cikin mamaki, nace mishi. "Baba Malam, ina son tashi daga gidan ka, don Allah ko zan sami sauran kudina na watanin da suka rage min naje na kama wani haya?" Kallona yayi sannan yace min. "Zaki samu, amma meye ya faru?" Zuciyata yana tafasa, nayi shiru. Kafin na ce mishi. "Kawai na gaji da gidan ne" "shi kenan! Insha Allah zan baki zuwa jibi!". Mik'ewa nayi sannan nace mishi" nagode” daga haka na bar zauren gidan, shiru yayi kafin ya shuri takalmin shi ya nufi gidan, tun daga bakin kofar gidan yaji muryan Asabe tana fadin. "Maman Abba kin yi min dai-dai, duk wanda ya goyi bayan wannan me kama da mutanen boye munafiki ne, yarinyar karama tazo gida da ciki, bamu tuhume ta ba, gashi dan girman kai ko magana sai ta gadama take mana, dan iyayi kamata tayi tace ba zata ci ba, me tafi mu?"
"Hmm! Maman Ummi, keda kika ji Iskanci ranar taga ina taliya da jajjege, nayi mata tayi munafuka tana so taki amsa, sai ga wannan anamimiyar kawarta tazo, suka fita hmm washi gari naga itama tayi irin ga kishiyarta, toh dan Ubanta sai ta bar mana gidan. Wa yasani ko garin shegen karatun bokon sune ta kwaso tsarabar cikin shege.". Iska yaja sannan ya juya abin shi, yana mamakin yadda Inayat bata kula su ba, dan da wata ce sai anyi dambe da ita, shi bai ga wani mugun abu a tare da yarinyar ba, dan ko lokacin da suka sanya mazajen su zo akan ya koreta ya ce musu su kawo mishi hujjar koran ta har yau basu kawo ba, shi kuma baya jin yayi wata magana shi yasa ya zuba musu ido, yarinyar da ko a ina tagan shi take mugun girmama shi, da suka ishe shi da surutu ya kirata akan cikin jikinta, bata boye mishi ba ta gaya mishi abinda ya faru da ita, kuma ya yarda da ita, dan haka zai musu iyaka da ita kawai sabida baya son Damuwa, kai ya fasa bari ya nima mata wani gidan kusa dashi. Zai fi mata can tunda babu zaman lafiya ba lallai bane matan su barta a zauna lafiya. Ga kuma ciki karsu cutar da ita wani abu ya faru ya rasa inda zai saka rayuwar shi, duk bata fasa mishi sunan mijinta ba, yasan tabbas ba karamin mutum bane, kawai gwara ya nima mata wani. Da dare ina zaune aka turo wai naje dakin Maman Abba, gyara zama nayi na cigaba da abin da nake, sai da mijinta yazo yayi sallama sanan na saka hijab na fita, ina zuwa na same su suna magana da mai gidan da muke, nuna min guri yayi na zauna. Sannan yace min. "Baki gaya min hujjar ki na tashi a gidan nan ba, shi meye ya faru." Murmushi nayi me ciwo, sannan nace mishi."Baba Malam, ni babu abin da aka yi min. Kawai bana son rayuwa cikin dabobbi ne, shi yasa." Shiru yayi Maman Ummi tace. "Da fatan ba mu bane dabbobi!" Gyara zama nayi sannan nace musu. "Baku san wacece ni ba, kuma bayan haka ni din ba kowa bace, amma kuna kuskuren tab'a min abun cikina da kazaman maganar ku, ban tab'a ranka muku ba, tun tashina ban iya fada ba, kuma bazan koya akan ku ba, sabida baku da abin da zai sanya ni fada akan ku. Ban yi alfahari da samun shi a matsayin miji ba, amma wallahi da zai san da zaman cikin jikina. Kika iya bude bakin ki, kika kira cikin da sunan shege." Murmushi nayi ina girgiza kaina, sannan na mike tsaye na karasa abin da yake raina nace mata. "Wallahi dake da dangin ku sai kun wayi gari a gidan yari, hmm mutumin da bai san gaskiya ba zaki kira dan shi ko yar shi da shege. Baba idan ka samu kudin zan tashi jinin Insha Allah." Daga haka na bar gurin su, nan suka shiga wani jahilci shirmen su, ban samu ba, shi dai Baba yayi musu fada akan abin da suka min, bayan na bar gurin ne, na koma d'akina, na zauna tare da tagumi, yadda cikin ke juyawa ya bani tausayi *SHEGE* kirjina ne yayi min nauyi, sabida girman kuskuren su, ban tab'a jin tausayin cikin jikina ba sai yau, k'iyayyar MALIK ya danne soyayyar uwa da Ƴaƴanta, san bana kaunar wani abu ya Hadani da MALIK, "Allah ya isa ban yafe ba Malik ka cutar da rayuwata,ka sanya zargin mutane tayi yawa akaina, Malam ba zaka tab'a ganin nasara a rayuwar ka ba, Malik wallahi sai kayi mummunan karshe, Ya Allah kamar yadda ya wulakantani ka wulakanta shi, Ubangiji ka min sakayya da abin da yayi min, Ya Allah ka dakushe farin cikin shi kamar yadda ya dakushe nawa, Ya mai dani mara galihu, ya mai dani mara ma'ana a cikin al'umma. Zan rungume cikin daga yau zan sosu fiye da kaina, sai na cusa mata k'iyayyar ka yadda kana son ta tana kin ka, Allah kasa mugun abu ya same shi mota ta bi takan shi mugu kawai, ya cuce ni. Ya mai dani ba cikakkiya ba, ni ba budurwa ba ni ba bazawara ba, Ni ba matar aure ba." Haka nayi ta kuka ina fada Baba da yazo yayi min sai da safe a hankali ya juya ya bar kofar d'akina, cikin mutuwar jiki....
***
Tafiya tayi tafiya tun Zehrah na jan su da hira har tayi shiru, sunyi tafiya sosai, kafin suka isa garin Gyambu, daga nan suka wuce bakin boda, a can ne aka nime a hana su shiga, sai da suka da Dr Ishaq ya bada cin hanci sannan aka Barsu suka wuce, tafiya ce babba a gaban su, dan daga nan suka wuce Yaunde, na jamhuriyar kameru, tafiyar zai iya kai su wani lokaci gashi basu san kan gari ba, dan haka suka nime gidan baki suka sauka. Jikin Mamah ya kuma rikicewa sosai, a duk lokacin da maganar Baba ya fado mata, sai taji numfashinta yana wani irin hawa da sauka, sai da Ishaq ya saka mata ruwa da alluran barci, kafin ta samu hutu, dukkan su uku suna zaune a jikinta har asuba yayi, lokaci zuwa lokaci Ishaq na fita yana daukar waya, kafin ya dawo. Har asuba yayi shi ya jasu sallah, kallon ledar abincin jiya yayi babu wanda ya samu arzikin cin abincin. Haka suka kuma shiryawa tare da daukarta suka nufi Adamawan kamaru da ita, tafiyar da ta dauke su awa shida da rabi. Tun daga shiga garin suke tambayar gidan Hammadada, basu samu ba, ba kamar suyi kuka dakyar suka nufi wajen garin Sosai suka fita daga garin suka nufi kauyen garin, tun a wani garin farko da suka tambaya aka gaya musu su kara gaba, zasu same garin Insha Allah. Jikin su yayi sanyi, musamman Mamah da take fama da jikinta.
*Don Allah kuyi hakuri! Yau gaba ki daya nayi busy ne,gobe ba zaku samu ba sai Jibi Insha Allah 🙏🏼✍🏽*
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/kCPZxkq2Lab
Chapter 18
Na MrsUsman400
The more we give, the more we receive. It's important to give back, because the seeds you plant today, you will harvest tomorrow.
Gudu yake sosai kamar zai tashi sama, amma bai kai ga isa inda yake so ba, ya faɗa wani dark forest me cike da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 22