Uzuri! Ni Malik! Ni Malik Aliyu Mai Nasara! Kike cewa kinyiwa Uzuri! Ikon Allah! Toh sai naga karshen rashin kunyar ki a cikin garin nan, na baki kwana uku kije ki rubuta wasikar ajiye aiki ko kuma. Idan na taso ki, sai kin rasa inda zaki ajiye kanki a garin Gombe, daga yanzun ko fara danasanin kalmar uzurin da kika faɗa min!" Dariya ya bani sannan na kalle shi dakyau nace mishi. "Ikon Allah shi Malik Aliyu Mai Nassara yadi ne a a sabuwar kasuwa! Ko yadi ne a tsohuwar kasuwa, toh nawa kuɗin shi? Well tunda ba atamfar roba bace da sauki f! Ba mamaki na same shi a super market dan nan ne ake samun kayan attajirai da masu kudi musamman attajirai irinka ajevote, malam a bakin aikina ka same ni baka da hurumin d'aga min murya dan haka ku dauki mutumin da kuka kawo, dan ba zan dubaku ba sai da saka hannun Hukuma, idan bai maka ba akwai wasu asobitocci a garin ba federal medical center bane kawai asibiti." "Keee!" Ya daka min tsawa a har cikin raina naji tsawar shi, na sake murmushin takaici. Nace, " matsalar dukiya kenan mai da kowa take zararre, ka jira idan ka haifi Yarka kayi mata wannan tsawar ba dai Inayat Ahmad ba!" Daga haka nayi ficcewata daga asibitin, ina fita na sami keke napep na shiga abuna aka kai ni asibitin nake aiki ina zuwa na samu metrol sai zarya take kamar zata cinye ni, ina shiga ta harareni murmushi nayi sannan nace mata. "Mommy don Allah kiyi hakuri! Wallahi wani d'an tasha ne ya rike ni a asibiti ni kuma na haye mishi!" Dariya suka saka tare da cewa. "Yau Inayat tayi fada." Share batun nayi na cigaba da abinda nake na gama saka hannu kenan sai ga Dr Ishaq ya shigo cikin sauri fuskar shi babu walwala yace min." Fulani Lady! Don Allah taimaka min ki hada kayan aikin kulawa da mara lafiya, ga Abokina kuma dai wani part na asibitin nan yana zuwa, yazo da mara lafiya, wai yaje wani guri an sami matsala, shine ya kawo nan dan taimaka min a ceci rayuwar wanda ya kawo." Ba tare da na kawo kome a raina ba. Na shiga hada mishi kome, har gadon da zaa kwantar da mara lafiyan. Ina cikin hada allurai sai ga Dr Ishaq ya kuma shigowa yace min. "Taimaka ki kawo mana, yanzun Nan, yazo da zafin rai ne don Allah taimake ni kafin ya fusata" jikina yana rawa muka nufi inda suke a emergence, sai Safa da marwa yake, "yawwa Friend kayi hakuri gamu nan yanzun zamu duba shi." Sam daga ni har shi bamu samu damar kallon juna ba, shi yasa bai gane ni ba muka shiga aiki da sauri da sauri. "Inayat karki bari..." "What!!! Cikin fusata ya juyo muka kalli juna, ko dar ban ji ba, kawai na kauda kaina, tare da zan mikawa. Dr Ishaq tiren ya buge tare da zuɓewar kayan aikin, sannan ya fincikoni ya fitar dani waje ya cilla ni waje. "Kina ci a cikin arzikinta kaska! Kuma kina komawa gefe kina fesar da jinin, wallahi sai na sanya ki kuka tunda kika wulakanta ni a gaban mutanen da suke fatan haduwa dani. Hhhh" ya girgiza kai sannan yace." A cikin mintinan biyar kacal zan nemi tarihinki, wallahi wallahi kika sake nan da kwana uku na riske ki, ina tayaki murna Inayat Ahmad ko? Aikin gwamnatin ma zaki ga yadda zasu yi dake." Ina tsaye ya Shiga ciki kafin wani lokaci sai gashi nan dauke da doguwar takarda, kafin ya mika min na riga shi mikawa securityn bakin kofar, sannan na amshi kayana a hannun Mommy, "Mr Mai Nassara! Kai kana da Sa'a shi yasa kome zaka yi kake gaba gadi! Sai dai wannan karon nice zan zame maka hawan jinin da ba zaka iya amfani da kanka ba, sai ka tuna da bakin cikin da na cusa maka, sai na zame maka damuwa a duk lokacin da ka tuna dani ranka zai b'aci, Allah sai ya saka min kafin ka rubuto min takardan sallama, tuni na ajiye muku aikin ku, jikan d'an karuna masu arzikin dud duniya! Sai kayi nadamar da arzikinta ba zai saya maka ba" daga haka ban kuma magana ba na juya idanuna na cika da kwalla.
Bai damu ba, yace min. "Swiper your tears dan baki yi kuka ba tukuna sai na sanya ki kukan da Babu wanda zai jiki, ƙi b'oya Kafin na fara niman ki lungu da sako." Daga nan ba kuma jin me yake cewa ba, na tari abin hawa zuwa gida, tun a hanya na samu sakon Dr Ishaq, na ban hakuri tare da sakon hakkina na kwanakin da nayi da kuma kyauta wanda asibitin tayi min, tun kafin na isa Unguwar mu, kwalla ta zubo min, ban tab'a jin takaici irin na yau ba. Yau daya mugu ya raba ni da aikina.
Duk da ban kyauta ba, amma akan gaskiya na nayi aikin, domin kwanakin baya wani inyamuri ya buge wani mutum aka kawo shi, Aunty Nanah ta amshi mutumin, karshe wanda ya buge shin ya nemi guduwa, sabida mutumin ya rasu, shine da aka kawo yan sanda suka tafi da Mr Alex, mu kuma aka mana taron bita akan lallai muyi kokari duk wanda aka kawo hatsari toh mu tabbatar an kawo sa hannun yan sanda, ko kuma da yan sandan, da ya bini da lalluma wallahi ba zamu kai da haka ba, amma dake giyar kudi yana diban shi. Shine ya min sanadin da na rasa aikina. Cizon bakina nayi tare da kauda kaina hawaye na zuba min, d'an gaba da majalisar Baba na sauka, can sai gashi ya mike ina biyar me abun hawan, yazo gaba ya mika min hannu yana b'ata rai yace.
"Bani na kashewa wancan dubu goman ya kare, kuma bana son a rena ni!" Wani irin kuka ne ya zo min nace mishi. "Baba na rasa aikina yau, a daya asibitin da nake aikina, don Allah ka barni zuwa jibi zan baka." Nan ya shiga fada tare da cewa. "Toh wallahi na gaji da ganinki, ki nimo miji ko kuma na bada ke sadaka wallahi bazan yi kaffara ba sadaka zan ba dake babu ko sisi. Zan nada aurenki..."
_Toh bayin Allah gashi gobe za a koma School! Toh ban san ya zamu yi ba fa_
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/geSaSHhgwab
Chapter 6
Na MrsUsman400
The page is for you! Fai'zation💝💖
Wasu irin tears masu mugun zafi, suke zuba min nakasa swiper din su, i wish myself da bana raye, i didn't know Wai nake raye a cikin duniyar da yake cike da mutane irin su Babu masu shegen Selfish. Kura mishi ido nayi a hankali na juya na bar inda yake. Na shiga cikin gidan. Na sami mutanen gidan mu da makota suna ta hira. Ko inda suke ban kalla ba. Na shige dakin mu. Kallona Balkisa tayi sannan ta tawo inda nake tana faɗin "Aunty lafiya" kasa magana nayi na had'iye kukan sannan na cusa kaina a tsakanin cinyoyina. Na jima a haka, sannan muka jiyo muryan Baba yana shaidawa Mutanen gidan Jibi alhamis daurin aurena, dan ba zai fasa ba niyyar shi ba.
Cikin tashin hankali Mama take bashi hakuri ya d'aga min lokacin kafin nan da bikin su Nusaiba. "Ai kice dama kece kike zugata karta aure? Toh ba zan d'aga ba! Kuma aure anyi an gama koda kuwa zata mutu ta dawo ne!" Daga haka ya kade rigar shi ya fita, majalisar su.
Ni kam na gaji da damuwa, kawai na zubawa sarautar Allah ido. Har dare ina jin su Yadiko suna yadawa Mama magana, ko leken waje ban yi ba. Washi gari da safe na shirya da wuri, na nufi FMC, ina shiga wajen aikina na samu sakon dakatarwa tare da canjin gurin aiki har can billiri. Wani irin tashin hankalin ya kama ni, kuma sun sani lallai na tafi garin a yau, domin nayi sign. Bank na wuce na cire kuɗin mota, sannan na nufi tashar mota. Ban gayawa gida ba, muka tafi. Tafiya me shegen tsayi da nisa, kafin muka isa garin. Kusan sha biyun rana, wani irin kwalla ne ya zubo min sannan na wuce asibitin garin wanda shine asibitin da ake hidimar macizai na nigeria baki daya, na nufi inda aka turani. Naje nayi musu bayani, suka amshi takardana sannan metro tace min. "An dakatar da ke, har na wata uku babu albashi, sannan zaki dawo nan sha biyar ga wata june, dan haka ina baki shawara kiyi kokarin niman sauyin gurin aiki, wanda yake kusa da Gombe domin zai fi miki sauki. Nima kuma zan taimaka miki, domin naga sauyin gurin aikin ba a kara miki albashi ba, sai ma kara rage miki shi da aka yi. Zan hada ki da wanda yake Office din zai taimaka miki Insha Allah, Yarona ne" sharrr naji kwalla sun zubo min, da sauri na goge sannan nace mata. "Nagode Mama, Allah Yasaka miki da Alkhairi" murmushi tayi sannan tace min. "Karki damu. Ai naga bayanin su, kuma na tabbatar sun miki kyakyawan sani, kawai wani damuwar suce," haka tayi ta jana da hira har gurin karfe biyu saura nayi sallah sannan ta haɗa Ni da yaron ta, muka yi magana ya kuma tabbatar min da zai taimaka min Insha Allah, sannan na fito, magana na gaskiya matar da d'anta ba musulmai bane amma suna da zuciya me kyau, nayi godiya sosai, sannan na kuma taso jiki ba baro billiri, tun a hanya aka turo min sakon ta wayata na cewa. *_Aunty kiyi maza kizo gida ba lafiya! Don Allah ki tawo da wuri_* ji nayi zuciyata kamar zata fado. Saboda tashin hankalin da nake ciki, ga wani irin tsoro da ya kuma kama ni, dan haka cikin rashin kuzari na kifa kaina, kan karfen motar ban bude ba sai da muka tsaya motar ta sami matsala, tun karfe uku da rabi muke gurin har karfe biyar sannan muka taso daga wannan hanyar muka nufo gombe, bamu yi nisa ba, muka kuma samun matsala. Dole muka hakura da motar sannan muka tsayar da wata da zata tafi muka shiga ciki.
Wasa gaske, bamu shiga Gombe ba sai karfe bakwai saura kad'an, muka shiga garin sannu a hankali na sauko daga motar. A sanyayye na fito daga tashan na tsari abin hawa.
Ina shiga na sami wani mutum a bayan motar zama nayi sannan muka fara tafiya mun kusan Unguwar mu, wata mata ta tsare mu, itama tana shiga. Ta zauna har mun fara tafiya sai ta kalle ni.
"Suna na Nawal! Kefa?"
Murmushi nayi sannan nace..
"Inayat!" Kallon juna suna yi da na can gefe na, kafin na kuma yin wata yunkuri har sun watsa min wani abu, ban kuma sanin inda kai na yake ba. Sai gurin karfe biyu na dare na kalli kaina kayana ne dai a jikina sai kuma dakin da nake ciki. Gefe can yana ta aiki. Bai min magana ba, nima kuma ban yi wata magana ba. "A rayuwata ina son sa'in'sa da mutanen da suka gaji arziki da dukiya! Sabida nasan idan nayi haka bazai ɓata min rai ba, i hater talaka futuk, wanda yake struggling na rayuwa yace zai d'aga min murya, miskinin da bai da arzikin da zai yi alfahari dashi, matsiyacin da gidan da yake zaune ta hayace. Mayunwanci da bai iya ciyar da kan shi sai yar shi tayi aiki ta ciyar dashi, wai shine hmmm. Zaki d'aga muryan ki ga Mamallakin miliyan dubu sau dubu! Inayat kike ko? Hmm!" Yayi murmushin gefen baki, sannan yace min! Zaki iya tafiya, amma ina tausayawa rayuwarki dan kin dauko abin da yafi karfin ki." Banza nayi dashi na bar dakin, a sanyayye na bar hotel din, wani irin takaici yana kama shi, me yasa ya kalleta ta tafi da bai mata kome ba, amma yasan ko babu kome yau ya bata mata rai, kuma ya lalata mata suna. Dan yasan yanzun haka mahaifinta yana can yana hauka. Murmushi yayi sannan ya cigaba da aikin shi kamata yayi tun jiya ya koma, amma wannan yarinyar taja mishi aikin shi ya dawo baya, yanzun gashi taja mishi rigima da matar shi. Tun jiya da bai koma ba, gashi nan fushi da shi. Sai ya Azabtar da Inayat yadda gobe ko muryan shi taji sai ta shiga hankalin ta. A can Abuja kuwa, tsabar tashin hankali kuka tayi ta mishi tana gaya mishi tana jin wani irin a ranta, sabida faduwar gaban da take ji akan shi ita don Allah don Annabi ya dawo Yasaka a karasa mishi aikin tana kewar shi. Amma ya lallabata zai hau mata magana tace mishi. "Ina jin tsoron Allah ina tsoron zaman ka a Gombe nan, kawai don Allah ka dawo kafin mugun yanayi ya shigo mana, ni wallahi tsoro nake ji." Shi kan shi yasan gaskiya ta faɗa amma bai kawo kome a ran shi ba sai ya bar shi akan mugun kishin sa da take yi ne. Bayan sun rabu ta kira Baby Nadra, sun jima suna tattaunawa kafin suka kashe, sannan ta zauna a tsakiyar gado, tana kuka sabida yadda jikinta yake bata kamar Malik yana tare da mace a wannan lokacin, kusan kwana tayi a zaune sai da asuba yayi ta kwanta, domin ita dai Sallah ba damunta yayi ba, kuma bokanta ya gaya mata cewa, matukar tana sallah aikin su warwarewa zai yi, sannan shima Malik tayi ta kokarin tana hana shi sallah akan lokaci, sabida kar aikin ya lalace. Washi gari da safe, Baby ta kama hanyar Katsina, karfe sha biyu ta isa garin Charanchi, daga nan tanufi kauyen da bokan yake tayi mishi bayani, ya jima yana aiki tare da hada gumi, sannan ya kalleta, ya girgiza kai yana fadin. "Akwai matsala! Tasan yadda zata raba mijinta da garin da yake yau kafin rana ta fadi ya isa gidan ta! Idan kuma ta sake mummunan yanayi ya shiga cikin alamarinta toh babu makawa zata iya shiga tashin hankali na har abada." Zaro ido Baby tayi sannan tace mishi. " Baba idan na gaya mata wannan bayanin kashe ni zata yi! Dan haka mu bar maganan nan a nan ni da kai, ga hakkinka, daga yau bazan kuma zuwa ba, sabida ni na bar abin da nake zan koma gaban iyayena nayi aure, kishi irin na Zeemalik sai addu'a. Ni na gama maka nawa. Idan kuma zaka ci kudinta Allah ya taimaka." Tana fadar hakan ta bar dakin ta fita daga kauyen baki daya. Bin bayanta boka yayi sannan ya b'ata rai kafin ya lallubi Number Zeeh ya shiga niman layin ta, dakyar ya shiga sannan ya gaya Mata kawarta taci amanarta, kuma zai cigaba da mata aikinta, bai gaya mata abin da yake ji game da mijinta ba sai yace mata maza tayi yadda zata yi mijinta ya dawo garin Abuja, karta bari ya kwana a Gombe duk rintsi. Daga haka ya kashe kiran, ya faɗa a fili yana cewa. "Idan babu wakilan barna ina zamu cigaba, ina zamu samu arzikin da zamu lasa, dole mace me kishi wata rana kishin ta ya ja mata d'an danasani," daga haka ya cigaba da aikin shi.... A daren na nufi Unguwar mu babu kowa a titi, da naga zan ta tafiya babu kowa sai na koma kofar wani gida na zauna tare da cusa kaina cikin babban hijab dina, ina zubda kwalla. Ina gurin ga mugun tsoron da ya cika min zuciya, ina zaune a gurin aka kira sallah farko,ban tashi ba aka kuma kiran wani kafin a shiga sallah. Da sauri na mike tare da nufar hanyar gida sabida ganin mutane suna tafiya masalaci, daga nesa na hango baban mu, take y'aya'n hanjina suka cure guri guda, jikina ya shiga rawa, na isa bakin kofar gida zan shiga ya tsare min kofar gidan. "Ki koma gidan da kika kwana, ki tawo dashi tunda kin ja min tsiya an rabani da gidan da nake haya na tsawon shekaru talatin da wani abu, dan haka ki koma gidan dan wallahi kika shiga min gida a bakin auren uwarki!"
Rokon shi nake sabida naga dayawan mutane sun fara wucewa masalaci amma ban da Baba dan shi sallar ma sai gari ya sha iska, asuba ya bar Gombe yake sallar safiya, cikin tashin hankali nace mishi.."ka taimaka na dauki kayana akwai kudi a cikin jakata." Wani kallon banza yayi min sannan yace min.."wallahi kika shiga sai na kashe ki! Dan haka ki koma gurin da kika fito, sannan har mutane suka fito muna jayayya dashi karshe sai da yaga mutane sun fito dayawa yace musu. "Ko akwai me bukatar auren Sadaka? Ba sai ka biya ko sisi ba! Kawai ka rabani da wannan masifar da ta dame ni, akwai me bukatar auren Sadaka?' Daga can aka ce "Eh...!Is not easy typing
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/p4CX5KL1wab
Chapter 7
Na MrsUsman400
Aure! Haihuwa! Arziki! Mutuwa! duk sha'anin ne na Ubangiji wani bai isa ya baka su ba! Karka gorantawa wani domin Allah yana sane dashi! Wance taki aure! Wance taki haihuwa! Wance ta rasu a ganiyarta! Kun manta sha'anin Ubangiji ne! Babu wanda ya isa ya arzurtaka! Duk abinda ka ga yazo maka rabonka ne! Dan haka mu yarda kome da lokacin sa! Thank You 💝💖
"Dummm!" Gaba na ya fadi! A razane na kura mishi ido, kwalla na zuba min, girgiza mishi kai na fara cikin tashin hankali, na zube akan kafaffuna, na fashe mishi da kuka ina rokon shi. "Don Allah karka min haka! Ka rufa min asiri! Karka wulakantani!" Murmushi yayi sannan ya tako zuwa gaban Babanmu. "Baba nawa ka yanke mata sadaki?" Yatsina fuska Baba yayi sannan ya kalle ni yana cewa. "Alhaji! Kana kyakyawa me zaka yi da me mugun kashi! Duk kanenta sunyi aure, kaga ka nimo waliyinka in daura muku aure, indai tayi maka!" Cizon pink lips d'inshi yayi tare da sauke ajiyar zuciya yacewa Baba. "Ina Baba sadaka zaka bada tsaleliyar budurwa haka?" Wasu irin kwalla ne suka shiga zuba daga idanuna. "Toh yaro tunda ka naci bada dubu biyar, nayi mata adalci ai! Tunda tsabar rashin sanin ciwon kai, ita tayi min sanadin da aka kore ni a wannan gidan da na shekara talatin a cikin shi, haka bai ishe ta ba ta kuma lakato rikici da wani me kuɗin kasar nan, ni ban sayi hatsi na cusa a cikina ba, yau ta janyo min fitina da zan nime inda zan fake, ga tarin iyalin da surukai na, Ai wallahi sai Ubangiji ya baki me nuna miki iyakarki kuma ban yaf..." "A'ah baba dattijo! Zan iya fasa aurenta waye zai yarda da mace mara albarka? Ga dubu biyar dinka" ya juyo ya kalle ni cikin jin dadi, sannan ya sake wani irin murmushin mugunta kafin yace mishi! "Ga dubu hamsin ka rike hannunka, kuma zan sami wanda ya sayi gidan nayi mishi magana." Dan haka a barta ta shiga cikin gidan, dan bana bana bukatar kome sai mata ta!" Sam baya tunanin kome sai ɗaukar mataki akaina, bai tab'a nazarin abinda zai iya tafiya ya dawo ba shi kan shi kamar wanda ake tunzura shi, dan haka yake ji lallai ko ba zai aikata kome da ita ba tabbas sai ya aureta, sannan zai samu nutsuwar zuciya. "Toh sai ki shiga, me farar kafa. Ba dan albarkacin shi ba, da wallahi bazaki shiga min gida ba, mai kama da aljanu wai." "Baba baka son na aureta ne?" Ya katse Baba daga zagin kare dangin da yake min,
"Ai d'an nan yarinyar ce da ban haushi take, shi yasa nake zage ta, amma ba zan kuma ba tunda zaka aureta!" Malik bai kula shi, ya cigaba da danna wayar shi can bayan kamar minti goma sai ga Dr Ishaq ya tawo, mika mishi hannu yayi suka gaisa, gefe suka koma cikin mamaki Dr Ishaq ya kalle shi yana jinjina qarfin halin shi yace.
"Kana nufi zaka aureta ne? Dan akan abin da ya faru shekaran jiya? Malik a sanina da kai, baka da mugun hali! Me yasa? Meye Inayat tayi maka? Me ta tsare maka? Ka rabata da aiyukanta bata damu ba, jiya kasa an sato maka ita dan kayi mata tijara haka bai maka ba sai ka daura mata dabaibayin ka! Don Allah na fanshi Inayat da abotar mu, don Allah ka barta ta tafi tayi rayuwarta ai kayi mata tabo, kuma zata cigaba da jin shi har.." "kawai ka gaya min cewa girlfriend dinka ce mana, ka zata boye min da kake ban sani bane? Ai an gaya min kana sonta, kuma ka shirya wannan wayar zaka gabatar da kanka, amma kuma."
Cikin takaici ya kalli Malik irin kallon baka da imani, kasa magana yayi, idanun shi sunyi jajjur. Yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi. *_Allah sarki! Inayat ashe ba rabona bane ke! Nayi shiru mara amfani. gashi Malik zai shata mana shinge me ƙarfi a tsakanin mu_* "ranka shi dad'e! Zaka samu karb'an min auren ko sai baje na amshi abuna?" Ya jefa mishi tambayar yana me tsare shi da sexy eyes din shi, ajiyar zuciya ya sauke cikin mutuwar jiki, Dr Ishaq ya isa gaban Baba ya durkusa, sannan tace mishi." Bismillah! Baba" jikin Malik ne yayi mugun sanyi, ganin yadda Ishaq din ya durkusa, aka kuma daura auren cikin mintinan arba'in, tare da halartar mutanen Unguwa, har Baba yana iya d'aga murya yana gaya musu, a dubu biyar aka daura auren.
A cikin gidan kuwa tun da na shiga ake yada min habaici, tare da gayawa min magana, ina saka kafana zan shiga dakin Mamah. Tace min. "Karki shigo min daki! Inayat kije na yafe miki, nagode da tarbiyyar da na miki tare da ɗaukar cikin ki da nayi." "Amma! Mama me yasa kika biyewa Baba? Na zata ke irin iyayen nan ne masu zab'an y'ay'an su sama da kome a duniya! Amma ba komai! Tun da dama Kome da lokacin sa! Allah ya bamu yawan rai! Aunty me kike bukata a kawo miki?" Inji Zehrah! "Takarduna sai kayan sawa na, kala biyu sun ishe ni" juyawa tayi ta shiga hada min kome har da duk wani abin da ban tambaya ba, duk sai da ta haɗa min, ina tsaye matar Hamisu ta shigo, yarinyar muna mutunci da ita, kuma bata daukar renin cikin gidan mu, riko hannuna tayi sannan taja ni zuwa layin su. "Nasan baki yi sallar asuba ba, toh ki shiga kiyi!" Haka na zaga ban daki na kama ruwa, sannan na fito nayi alola, tun da na shiga na samu ta ajiye min abin sallah, nayi la'asar din jiya da magarib da isha sannan nayi sallar asuba, ina sallama naji muryan Baba, yana fada akan me Adama zata jani zuwa d'akinta, nan yayi ta masifa . Kasa cin kome nayi na mike dan na idar da addu'a kenan na fito. Ashe a wajen ne Malik yace mishi. "Baba ka turo min ita, zamu wuce." Daga fadar haka shine ya shigo gidan yake hargagi. Daukar kayana nayi zan fita, ya daka min tsawa. "Ina zaki tafi da wannan tulin kayan?" "Amma dai kasan dole zata bukaci kayan sawa, kuma in Allah ya yarda kamar yadda ka wulakantata ka tozarta ta, kaci mutuncinta, sai Allah yayi maka duk abin da kayi mata, ba kayiwa mahaifiyarta barazana zaka saketa idan kaji labarin ta shiga dakinta ba, Baba ina gaya maka sai shara yafika daraja ga yaran nan, Itama Mamah da laifinta taya zan haihu har na iya kasa daukar mataki akan D'ana wallahi bari na gaya maka idan zan rabu da Hamisu, yan kalare zan kira su datse min banza dan kar yace zai karban min Yarana. Ke kuma Aunty Inayat kije tayu wani arzikin ce take kiranki gadon masifa talauci yake mandake ki a gida." A sanyayye na fita, gani na da uban kaya, ya b'ata rai tare da hade goshin sa, yace.." gidan uban wa zaki da wannan tsimokarar, Ishaq amshi kayar zata bugata
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 22