idan laifi nayi kayi hakuri ba zan kuma ba. But am bored da zaman doya da manjan da muke." Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya riko hannuna. Yace min. "A ranar da zamu yi hatsari, kin san me ya faru? Duk wani lokacin da Malik ya haɗa duk wani dukiyar shi ya saka sunan yaran shi, sannan ya dauki wasu ya bani. Dukiyar da ya bani domin na rike ki, dayawa yake har nayi fatan na mutu na bar mishi ke, badan kome ba sai dan yadda yake kaunar ki, Ya bani amanar mahaifiyar shi da kanen shi, yara kuwa ya tabbata ko bayan ranshi zamu iya rike shi. Inayat Aure! Haihuwa! Arziki! duk na Ubangiji ne wani bai isa ya baka su ba! Kishi masifa ce, Kishi irin na Zeinaf masifa ce, Yarinyar bata da imani, shi yasa jiya da naga tana bin bola. Tare da haukar tuburan ban ji tausayin ta ba, sabida abinda ta shuka shi ta girba." Kwallar tausayin Malik ya sani matsawa jikin mijina na kwantar da kaina,nace mishi. "Ni da baby muna kewarka, yanzun ka bar Asibiti kenan?" Gyara min kwanciya yayi a jikin shi sannan ya ce min. "Dole ma kuwa, abubuwan da Malik ya bari suna dayawa, ba zan iya hada aiyuka da yawa ba." A hankali Yaren mu ya juya zuwa Yaren kewar mijina da bukatar shi...
Bayan wasu watanin aka kirani daga Gombe, Baba bai da lafiya. Dole Ishaq ya raka ni, gashi cikina ya tsufa, haka naje na same shi babu inda yake, asibiti muka kai shi, daga nan aka tabbatar mana yana da ciwon suga, dole aka yanke masu kafar duka biyu, gidan da na gina na gombe aka kai shi, tare da Hamisu sabida. Sannan matan shi kan naki yarda su dawo, wannan gidan dai shi na saya musu, suka zauna nace musu gidan da na gina domin Mahaifiyata bazasu zauna ba. Dan basu so ni ba, yaran su kuwa suna nan a sake ana buga zawarci kazamin ma kuwa, Allah ya kyauta.
.. bayan an gama kome muka dawo, a gidan Ammyn muka sauka, tana ganin mu ta fara dariya. Tace. "Son baka da tausayi zan kwace y'ata fa" shafa kan shi yayi tare da sake murmushin jin dadi yace mata. "Ammyn ayi hakuri tafiyar ta tace, amma ba zan kuma ba." Murmushi nayi tare da basu guri dan naga suna son magana da juna me muhimmanci, sun tattauna kuwa, sannan ya turo Haysam yayi min magana muka nufi gida. Bayan mun bar mata Yaran a gidan ta. Zehrah ta haihu inda ta sami d'a namiji aka san mishi Malika, ranar nayi kuka sosai dan burin mu ne da Ishaq. Hanani zuwa sunan yayi tare da cewa na duba kaina kafin naje sunan wasu. Haka nayi hakuri dasu.
....
Tafiya take tana fadin "baki isa ba Neemrah, sai na kashe ku, sai na kashe Malik nawane" wata mota ce baka ta tsaya wasu kartin maza suka sauka tare da kamata suka sata a cikin motar, sannan suka bar gurin da ita.
Wani gida suka kaita can wajen gari, gidan matsafa ne a cikin suna tsafi da mahaukata, suna ganinta ogan su ya fara bayanin yadda take itama kaucacciya ce kafin yanzun ya haukace dan haka abu uku zai yi amfani a jikinta su kwanta da ita sai su kwakule idanunta, da nononta na dama, su kusan rai goma sha biyar, suka kwanta da ita, tun yana ihu da niman ceto har ta suma, daga nan suka yanke tare da cire abinda zasu cire aka dawo da ita inda suka dauketa.
Washi gari da safe, har gawanta ya zama kore shar, akan akayi ta yadawa a social media. Wannan abun ya masifar firgita ni, duniya ba a bakin kome yake ba.
Shi yasa na kuma nitsar da kaina, tare da nuna Yardan Ubangiji, shi zai mallaka min mijina, babu ruwana da mugun kishi Dan masifa ce, Ina kokarin kyautata alakana da mahaifina, Mahaifiyata da Malik babu ranar da bazan sanya su a sallah na,.
. Bayan wata biyu na haihu, inda na samu Yan biyu duk mata, aka sanya sunan Maman Ya Ishaq da Kuma Ammyn, muna kiran su Aamal da Aamilah, tako Ina Budi yake shigowa mijina, Baban mu kan Yanzun ya saduda ya koma Kamaru inda ya koma gida da matan shi. Dan yace idan ya tafi babu ruwan shi su nemi wani mijin yaran shi kuwa yace idan zasu iya su zo su tafi dangin shi. Na bukatar shi. Ganin yadda muka zama wani abu a cikin su. Yasa suka bishi basu san ba haka bane, dan haka koda suka bishi abin sau du'a'i kawai.
----
Rayuwata tafi dan anyi bikin Kuwwah da Hajnan, Haysam yana jami'an sojin Amurka, anan yake karatun shi.
Kanena suma sun kuma Haihuwa, Dan Nusaiba yaranta uku. Mariam yaranta huɗu, ita da Balkisu uku, Auta biyu. Sai Ni me huɗu.
Kakan mu kuwa muna kuka shi hatta mahaifiyar Ya Ishaq, Yarana ta ko ina suna samun kulawa, Mahnoor yaranta biyar, yan baya da aka aurar dasu yaran su daya d'aya. Na yarda kome da lokacin sa, kuma idan yayi ba makawa sai ya faru, Khady tana auren Yayan Neemrah Hasshir har da yaran su biyu ya kuma saya ta dauki Habib ta haɗa su yanzun suna Kuwait, Maman Ummi kuwa sai da naje har kashare na nimo ta, tare da mata abun Arziki, matar da ta fara taimako na, lokacin fadana da Malik ita ma na shiga har garin nayi mata alkhairi. Ammyn ta kai mu har Kuwait, mun ga dangin
Bayan shekara biyar.
Ina taya shi saka kaya, kawai ya zuba min ido. "Abu daya ya rage ki karasa min shine! Inji Malik yace don Allah ki yafe mishi." Mik'ewa nayi sannan na rike hannun shi nace mishi. "Yayana mijina! Akwai wanda zaka nimawa yafiya ta ban yafe mishi ba? Ai tuni na yafewa MALIK, sai dai kayi min Addu'a Allah yasa wannan kunshen jikina Little Malik ne! " Murmushi yayi sannan yace min."Insha Allah zaki haifa min Abokina." Nima murmushi nayi mishi. Tare da gyara mishi wuyar rigar shi....
*_Alhamdulillahi anan na kawo karshen wannan labarin, nasan ba zai muku dad'i ba, amma ina baku hakuri sabida uzurin da yazo min! Dole na yanke Labarin kome da lokacin, team din Malik ina me kuma baku hakuri sosai! Kuyi hakuri Next book dina zaku ji dadin shi sosai har bazaku so ya kare ba.. Allah Ya ƙaddara saduwar mu a cikin MY FIRST WIFE (MAH+NOOR) Lovestoryn da baku tab'a jin irin shi ba, labari me cike da Mamaki da al'ajabi! Insha Allah Free Book ne shima sabida Fans dina🤩_*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 22