ne ya kama shi da sauri ya mike, amma ina wani zazzaɓin yake jin kamar wanda yayi jinya na tsawon sati biyu. Dakyar ya nufi ban daki ya cika ruwa sannan ya shiga ya jima yana wanka kafin ya fito, a hankali ya kalli irin kwanciyar da tayi, ko dar bai ji tausayinta ba.
Asalima ganin abin da yayi dai dai yake, sannan kuma yana jin haushinta sabida ita taja mishi ya aikata haka, ba tare da yaji kome ba ya shiga hada kayan shi, yana gama hada kayan shi ya shiga niman daya wayar shi, dan biyu ne, yana samu ya ciro layin shi ya saka a ciki. Sannan ya shiga niman layin Zeemalik. "Malik!!!" Ta kira shi cikin kuka da tashin hankali. "Ina ka shiga ne? Don Allah kayi min magana, nasan dan muryan Film din da naji ne zaka ce ba zan kula ka ba." Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace mata.."toh Zeeh ya zanyi dake?" "Kawai ban yarda da garin bane don Allah ka dawo! Tsoron kar wata mace ta cutar min da kai nake ji! Nasan abinda zaka aikata nasan wanda ba zaka aikata ba dan nayi imani da Allah Mace bata gaban ka." Kashe wayar yayi tare da zubawa Inayat ido. "Me yasa kika rushe min Yardan da mata na tayi dani? Me yasa kika sanya ni ha'intar matar da babu ruwan ta da kowa sai ni! Na bar miki ciwo biyu, ciwon rashin kimarki, da kuma haka zaki rayu babu ke babu aure, na miki tambarin da ba zaki tab'a gogewa ba." Daga haka ya saka kai ya tattara kayan shi zai fita. Kome ya tuna sai gashi ya dawo ya gyara rufeta. Sannan yayi ficcewar shi. Cike da tausayin Zeemalik. Sabida yaci amanarta. Kuma yasan Allah ba zai barshi ba.
.... Yana fita ya kira driven shi yazo ya kai shi Airport. Yana zaune a cikin motar sai ga driven, yazo da sauri ya jashi. Ya bar garin Gombe baki daya.
----
Karfe bakwai ya shiga gidan shi, kamar mahaukaciya haka ya hangota a step, gaban shi ne ya fad'i. Da sauri ya zubda kayan hannun shi, ya isa gareta. Mik'ewa tayi kafin ta tako Inda yake ta nemi zuɓewa kasa, tare da mika mishi hannun ta na dama, ganin mugun aikin da tayiwa kanta ya sashi jin tashin hankali fiye da wanda ya baro a gombe.
Daukar ta yayi tare da fita da ita, suka nufi asibitin Maman shi. Anan aka shiga da ita emergency room. Zama yayi tare da dafe goshinsa. Idanun shi sun cika da kwalla. _Inayat masifa ce haduwa da ita ta zame mishi wutar daji, daga haduwar shi da ita take jaza mishi masifa_
Haka yayi ta ayyanawa a ran shi, har zuwa lokacin da likitan ya fito tare da zuba mishi ido. Kafin yace. " Mr Malik! Muje office" babu musu yabi bayan shi, suka zauna, sai da likitan ya gama kome sannan ya zuba mishi ido kafin yace. "Mr Malik zamu kai Matar shashin binciken ƙwaƙwalwa, domin abin da tayi ya bamu tsoro, badan Allah ya takaita ba, da ta yanke jijjiyar da take hade da zuciyarta.... 💋
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/TgIw7a4Byab
Chapter 9
MrsUsman400
*Wow Zeemalik team members thank You for The comments 💝💖💋 I'm think that Kome da lokacin sa! Zan iya ce mishi Super hit story👻*
"Kana hauka ne? Matar tawa make dangantawa da shashin binciken ƙwaƙwalwa! Zaka bar asibitin nan how are you! Da zaka danganta Matana da cutar hauka."
"Yallabai! Ba haka bane, listn to me, Matarka tana dama da cutar birkicewa ƙwaƙwalwa ne, shi yasa take iya cutar da kanta, and nan gama zata iya kirkiro abu tace ya faru, kuma bai faru ba. Cutar tayi tsananin dayawa, tun ba yau ba na fara nazartan matsalarta. Idan ka kawota ta had'iye wani abu me kaifi!" Cikin mamaki ya zubawa Dr Tony ido, ya tako gaban shi sannan yace mishi. "Ka gama aiki a cikin asibitin nan zaka barshi." Duk yadda likitan yaso fahimtar da shi, abun yaci tura, a fusace ya fita daga ofishin likitan ya nufa dakin da Zeemalik take Barci in peaceful! Shafa kanta yayi tare da kallon agogon karfe goma saura. Gaban shine ya fadi lokacin da ya tuna ya bar Inayat a kwance, kuma bai gayawa kowa ba, cizon lips din shi yayi. Sannan ya lallubi wayar shi, ya fara niman layin Dr Ishaq, bai dauka ba, sai dai ya tura mishi sakon kamar haka.
_Ka tura nurse suje su daukota domin na gama abinda zan yi da ita! Ishaq Abdul Qadr! Karka kuskura ka dibo that poor lady ka kawo ta gidan mu, domin idan Zeemalik ta ganta babu abin da ya dame ni, idan ta gadama zata iya cigaba da aiki a Mai Nassara clinic, kai dalla waye ita kawai ku dubata idan bata mutu ba kayi watsar da ita a bakin hanya, kayi tafiyarka, ita ta sani, ni zan bar kasan yau dan mata na bata da lafiya_ Cikin nutsuwa ya cire layin Dr Ishaq ya karya bayan sakon ya tafi, sannan ya koma kan Zeeh yana shafa kanta cikin yanayi tausayinta. Fita yayi daga dakin ya samu wasu likitocin suka shiga hada musu takardun shaida lafiyarta, zasu wuce wata asibitin a garin London. Kuma dama reshen kamfanin shi na sarrafa magunguna yana can. A cikin awa biyu aka gama hada musu kome, sai da ya shiga private Jet din su, sannan ya turawa da Ammin shi sakon basu ƙasar shi da Zeemalik ba lafiya. Kai hannun shi yayi ya shafa kanta, fuskarta yayi fayau.
_Toh ya kenan duk ranar da Zeeh dinka tasan kayi aure a wata duniya fa?_ dafe kirjinshi yayi cikin tashin hankali tare da tirr da Inayat, duk ita ta janyo mishi wannan masifar, kai shi kan zuwa gombe bai amfane shi ba, sai masifar da ya jangwalawa kansa. Cikin zuciyar shi yake jawa Inayat jafa'i yafi kwando dubu...
*** Yana dab da zai shiga cikin gidan shi, yaji sako ya shigo mishi. Yana dubawa ya sakon cikin tashin hankali ya juya da motar da mugun gudu, tsabar yana hada kashi mutane sai zagin shi suke, ana gaya mishi magana ba haka bane a gabanshi. Kamar mahaukaci haka ya isa Estate din, a gigice ya shiga ƙoƙarin shiga gidan.
Masu gadi suka so hana shi sai da ya gaya musu akwai mara lafiya a cikin gidan Malik. Dan haka suka bishi, koda suka shiga cikin gidan ya wuce master room din Malik. Daga bakin kofa ya tsaya sabida yadda yaga gashin kanta ya buzu a saman pillow, fuskarta na kallon sama, da sauri ya kira metrol Sis Rukayyah.
Wani irin bakin ciki yake ji kamar zuciyarshi zata fashe ya karanta sakon yakai sau goma, can sai ga motar asibitin da Sis Rukayyah, suka shigo ita da Abidah da sauri suka shiga dakin, d'ago kanta suka yi. Suka ga ya koma baya. "Dr Ishaq ka shigo fa, domin bata numfashi fa." Da sassafar ya shigo kamar zai zube kasa, ya ma rasa yadda zai yi da ita. "Metrol kawai ku kintsata mu tafi asibitin." Ga baki daya suka rasa yadda zasu yi da ita, karshe kallon shi suka yi Abidah tace. "Dr babu kayan da zamu saka mata." Cikin wani irin zuciya yazo ya dauketa cak ya fice da ita, Yarinyar da yake dab da furta mata kamar so! Yarinyar da ya gama jingina burin shi akanta, yarinyar da yake mata kallon macen da yake so! Itace yau a matsayin matar Aminin shi! Abokin shi. Itace Amininshi yayi mata sassari da auren shi. Wani irin zalinci Malik ya shiryawa yarinyar da babu ruwanta. Da wannan tunanin ya sakata a cikin motar, sannan ya shiga motar shi, ya zauna. Motar asibitin tana gaba yana bin su har cikin asibitin. Inda ya hana kowa tab'ata shi da kan shi ya shiga da ita har cikin emergency room, tare da metrol da wasu Nurse har uku, suka shiga duba ta. Kasa zama yayi tunda ya sa mata ruwa da kanshi ya fita, dan ba zai iya zama yaga halin da take cikin ba. Dan ya fara jin abinda Dr Umaimah take fada.
"Gaskiya wanda yayiwa Inayat Ahmad wannan cin zarafin yayi yawa, haba jama'a dabbancin yayi yawa wallahi, kalli yadda gaban yarinyar nan yayi, haba don Allah sai kace ya samu jaka. Don Allah taya zan dinke jikin yarinyan don Allah. Ni kam ban san ya zan dinke ta ba, don Allah kai Allah ya isan mata." Tana aikin fada, Metrol sai da ta shiga zubda kwalla, sabida yadda gurin ya kumbura sosai. Sai da suka cire tausayi suka mata dinkin sosai, sannan suka mike a hankali bayan sun shifa mata cream. Tattara mata gashin kanta Abidah tayi sanan ta tufke mata shi, suka turata wani daki. Dr Ishaq yana tsaye suka wuce da ita, fuskarta yayi wani irin.
---
Sallamar shi na biyu Zehrah ta leko, kallon shi tayi sannan tace. "Kamar na sanka, ka tab'a kawo Aunty a motar ka." Murmushi yayi sannan yace mata. "Eh ni ne, Dr Ishaq. Idan da hali ina son ganin Mamanki!" Kallon shi tayi cikin tsoro. Zata yi magana yace mata " Please" shiga tayi cikin gidan jikinta a sabule, ta kalli Maman su kafin tace mata. "Wannan abokin aikin Aunty yana waje, wai kizo." Kallon ta tayi kafin tace mata. "Toh!" Zuciyarta yana wani irin bugawa, take tasoma jin numfashina yana kaiwa da komowa, da sauri sauri. Hijab ɗinta taja, daga bakin kofar ta. Ta fito jiki a sanyayye. Ta d'an leko tana kallon shi kafin tace mishi."sannu bawan Allah." "Hmm! Mamah gashi dare yayi, ko zaki zo muje asibiti Inayat tana can bata san waye akanta ba." Yace mata a hankali. Kasa magana tayi sabida rudewar da tayi ta ma rasa inda zata saka ranta kiran Nusaiba da Balkisu, sai Mariam da Aura suka fito tace."muje!" Kallon yadda ta rufe yayi ta kasa amsawa yaran tambayar da suke mata. Sai dai tace musu. "Muje" a hankali suka shiga motar shi, duk ya kwashe su. " Ya Allah! Mun tuna da wulakanta amanar da ka bamu, Ubangiji ka taimake ni kar Inayatu ta rasa rayuwarta, ban san me zance maka ba." Sai kuma ta rushe da kuka. "Yana daga cikin dalilan da matan kabilu suka fimu nesa ba kusa ba, Iyaye matan sukan sadaukar da Rayuwar su domin yaran su, duk abinda d'an zai yi bazai tab'a mantawa da Mahaifiyar shi ba, amma ku Allah ya wanke ya baku Ƴa ta gari, kuka wulakantata, kuka ci zarafin ta, toh kuje kuga nakasar da kuka ja mata. Idan Allah ya kare lafiyarta." Daga haka yaja bakin shi yayi shiru, har suka iso asibitin, ya kai su dakin da take. Gwanin ban tausayi, gashin goshinta yayi luf luf, ya kwanta. A hankali zaka fahimci tana fidda numfashi, idanunta da bakin ta sunyi jajjur. Sai gefen fuskarta da ya kumbura ga shaidan hannun da ya fito sosai. Dukkan su kuka suke tare da jin tashin hankali, dan gani suke kamar ma ta mutu. Haka suka sha kukan su, anyi anyi su bar Asibitin suka ki, dole aka bar su a bakin kofar ta, kowa na barci amma ban dasu, karshe ma shiga dakin suka yi dukkan su, suka zuba mata ido. Mama da Maryam suka shiga ban daki suka dauro alola, suka fara nafilla, har zuwa asuba. Sannan suka daura da raka'atul fijri, kafin suka yi sallar asuba. Zama Mamah tayi ta shiga addu'o'in. Har rana tayi, tana kuka tare da nimawa Inayat sassauci. Dan haka tana idarwa, tacewa su Balkisu."maza ku koma gida, nasan yanzun babanku yana can yana fada, don Allah ku gaya mishi halin da take ciki a nutse, sai ku tawo mana da kayanta, sannan ku biya ta gidan Uwani akwai kudin adashena ta baku, insha Allah zan tsayawa Inayat ba zan kuma barin wani abu ya tab'ata ba." Fita suka yi tace Nusaiba ta zauna. Bayan fitar su. Gadon da Inayat take kwance ya shiga jijjiga, kamar ana jonata da wuta, har sai da Metrol suka zo suka mata allura, sannan ta koma ta kwanta idanunta a kafe, wani irin ajiyar zuciya taja bakinta yana wasu yana motsi, kai kunne Metrol tayi. "Allah kana ganin abin da yayi ya Rabbi Kabi min hakkina" a hankali kuma tayi shiru tare da lumshe idanun ta, bayan ta sauke ajiyar zuciya a nutse. ** A gida kuwa su Balkisu suna isa Baban su ya nemi zai musu magana, Zehrah tace."toh daga asibiti muke Aunty Inayat ta mutu." Sake karfen duga yayi akan kafarshi ba tare da ya fahimci akan kafarshi ne ba sai da ya fasa mishi babban d'an yatsar shi ya sake salati tare da durkusawa. Jini na zuba sosai, kasa jure abun da Zehrah tace ne ya kalleta. Cikin raunin murya yace mata."toh yanzun batun ginin gidan da tayi kusan dai dole dani a cikin gadonta. Sake baki kowa yayi sabida a farkon abin sun zata nadama ce tazo mishi sai da ya tona kan shi sannan suka fahimci ai hali a jikin rai ne, babu mai sauya maka sai Allah. Dan haka wasu suka shiga gyara dakin su, Balkisu da Maryam suna cikin dakin su. Zehrah ta hura wutan abinci. Sai lokacin mutanen gidan suke tambayar su lafiya, nan suka gayya musu basu da lafiya, take suka juya kan Babansu Inayat da cewa. "Kai ma malam yarinyar nan kamar wacce ta tsare maka wani abu, gashi nan ta haɗa da wanda zai lashe ta. Tunda ai kace mutumin attajiri ne, waye ya sani ko dan yan kankai ne." Inji Jumalo, nan suka yita tsagalgale shi, tare da ganin laifin shi., Kallon shi su Balkisu suke babu wacce ta kuma magana,... A can asibitin kuwa, har yanzun bata farka ba, dan gabaki daya, suma likitocin sun sare da ita, sai da aka shafe awa goma sha biyar, kafin ta shiga ƙoƙarin farkawa. Duk suna bakin kokarin su, amma sai da suka so razana, domin tana buɗe idanunta zata kuma maida shi ta rufe. Komawa har....👻
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/6rcnMVdfAab
Chapter 10
Na MrsUsman400
"Dr Ishaq! Har yanzun numfashinta yaki." Inji Dr Umaimah, wacce take ƙoƙarin ganin numfashin Inayat ya dawo dai dai, cikin ikon Allah dakyar numfashin ya dawo yadda ake bukata allurai suka zuba mata a drip ɗinta, sannan suka fita jan kujeran yayi ya zauna. Daga jiya zuwa yau ga baki d'aya ta motse kamar ba ita ba, sai dishewan da tayi. Kar'ar hancinta ya fito zirr. Sai kwarmin idanunta da suka fada kamar wacce tayi jinyar shekaru. Kamar wanda aka tsikare shi da allura. Ya fita da sauri dan bai ga amfanin kallon matar da bana shi ba. Yana fitowa ya kalli Mamah tana fama da share kwalla. Kamar zai mata Magana, sai ya fasa yayi tafiyar shi. Bayan awa biyar cif. Na bude. "Ƙaf ƙaf!" Naji karar tafiyar agogo, juyawa nayi a hankali na sauke akan agogon da ya ke jikin bangon. A hankali kome yake dawo min daki-daki. Kome yana zuwa min kamar majigu kome na rayuwa yana da mafari kome yana da farko rawa farkon itace kaddarar mutumin da ban sani ba! Tawa mafarin itace iftila'in MALIK!!! Shine kalmar da zuciyata ta ambata, wani irin siririn hawaye ne yake bin gefen idanuna. A hankali na d'an motsa jiki na da yayi min tsami, sannan na lumshe idanuna a karo na biyu. Sannan na bude shi lokacin da naji muryan Metrol Mommy Rukayyah naji na bi kofar dakin da ido, sannan na mai da idanuna na rufe. Duk sun shigo suka gama min gwaje-gwaje ban bude ido ba, ina jin su. Suna fita Dr Umaimah tacewa Dr Ishaq. "Inayat tana fusace tunda bata yi wani abu ba, ka gayawa danginta su kula da abinda zai d'aga mata hankali, dan yanzun tana cikin damuwa sosai." Shiru yayi sannan ya juya ya sami Mamansu da Maganar kar a shiga ma yace dan ba abun mamaki bane ya iya birkice musu. Suna cikin tattaunawar sai ga Baban su Inayat. Baza idanu yake yana jiran karin bayani. Itama Maman ce tayi mishi bayanin halin da Inayat take ciki. Kallon Maman Inayat yayi sanan yace mata. "Amma da kuka kawota asibitin kudi kunsan ba shi nake da ba! Sannan kuma ita Inayatun ba haka kowacce mace take hakuri a gidan mijinta ba, ko tallatar kai, ban da lalacewar duniya har guzuma irin Inayatu zata suma sabida an raya sunnah fiyayyen halitta da ita tirr, kuma ina miki kashedi magana na yanan idan kina son aurenki kar naga kafar Inayatu a gidana. Sai ta nimo mijinta, idan ba haka ba toh wallahi a bakin aurenki." Kad'e babban rigar shi yayi abin shi ya cikawa bujen shi iska. Shiru Maman tayi tana jin ciwon abinda yayi masu, ita bazata iya barin Inayat haka,,, duk abin da yake faru duk naji su. Murmushin tausayin kaina na sake, a hankali nace. "Zan tafi nayi nisa daku, zan muku tazara tsakanin mu. Zan tafi inda ba zaku kuma jina ba sai dai idan nice naso haka.. daga nan na share kwallar da take kokarin zuba min, ina kallon kofar d'akin. A hankali na d'an mike k'adan sannan na sauka daga gadon. Na shiga ban daki nayi wanka da alola, sannan na fito naga kayana a gefe a hankali nake takawa har na isa gaban kayan na dauki doguwar riga na saka. Sannan na kuma dauki hijab na yafe, salollin da suke kaina nake son saukewa.
*A garin London kuwa Madam Zeemalik ce ta bude idanunta ta zubawa mijinta su, musamman yadda ya d'an faɗa. Kwanaki hudu da zuwan shi ya faɗa sosai, dan wani irin zazzaɓi yake ji. Tun ranar da yayi tarayya da Inayat. Shi kansa yana son ganin likita, amma matsalar Zeemalik ne a gaban shi. Shafa sajen shi tayi cikin jin dadi. Sannan ta ture kan shi kad'an, bude idanun shi yayi tare mik'ewa a hankali yana murmushi yace mata. "zeemalik!" D'aga mishi hannu tayi sannan tace mishi." Wacece ita? Nayi mafarkin wata mace kuma wallahi ina jin ka boye min wani sirri, gaya min wacece ita da take ce maka raggon maza! Ka gaya min wacece ita?" Ta faɗa da karfi, "Kinga Zeeh babu wata mace na gaya miki kallo nayi, kuma a" cikin fusata tace mishi. "Kayi min shiru! Munafuki, annamimi, wato wannan shine abinda kake aikatawa. Da sunan kayi tafiya, kaje kana sheke ayarka, meye na rage ka dashi wallahi ko ka gaya min wacece ko kuma na kashe ka na kashe kaina. Kuma ina tabbatar maka sai na kwashe maka Manhood dinka, idan baka gaya min ba." Wani irin zufa ke karyo mishi kamar wanda ya shiga ruwan sanyi. Ya bude baki zai magana tace mishi. "Kayi min shiru! Ka kuma gaya min wacece karuwar ka? Na rantse da Allah sai na mata tsarki da ruwan battery, ba zaka gaya min ba!" Yadda take zare ido hancinta na huruwa kawai zai tabbatar maka da ta zare, amma ba zarrewa bane abu ne da take da yakinin ya faru, tsabar kishi ya rufe mata idanu. Shigowar likitocin da suke dubata ya taimakawa Malik ya fita, tunda fita yake zaga cikin asibitin sabida yadda brain ɗin shi ya dauki charger, kacokan ya daura laifin faruwar kome akan Inayat, ita ta shigo rayuwar shi ta lalata mishi kome nasa, gaskiya da zai kuma ganin ta, sai ya kuma mata rashin mutuncin da zai sanya ta gane Allah daya ne. _Amma kuma wani hali take ciki?_ wani shashi na zuciyar shi ta sheko mishi tambayar tsaki yayi a fili yace"oho idan taso ta mutu ma, Insha Allah daga yau ba zan kuma tuna abinda ya shafi Gombe da kewayenta ba. Dan kar wancan farar kazar taji a ranta ina bibiyar ta." A hankali yake wannan maganar, haka yayi ta zaga asibitin, can ya tafi wani shashi ya biya kome sannan yaga likita saboda zazzaɓin da take bibiyar shi, tsoro ma yake ji kar ya lakato wata masifa a jikin Inayat, wacce zata hallaka shi. Bayan gwaje-gwajen da aka mishi gyara zaman Medical glass din shi yayi sannan yace mishi. "A gaskiya baka da wata matsala, sai dai ta zubar ruwan jikinka, wanda hakan ya faru ne sabida kasha wani abin karin kuzarin, dalilin jimawa da kayi kana biyan buƙatar ka, ruwan da kayi ta fitarwa ya shafi na jikinka sosai. Shi yasa kake jin zazzaɓi. Badan maganin ya sake ka ba da jini zaka yi ta zubdawa, sannan ka kiyayye tare buƙatar ka, itama tana haifar da haka duk ranar da ka fitar da ruwan da yawa haka. Toh kusan hakan ce zata kuma faruwa don Allah ka kiyayye lafiyarka!" Magani ya rubuta mishi sannan ya fita ya saya shima lokacin da ya koma dakin Zeemalik ya sameta tayi shiru, tana kallon kofar, a hankali ya shiga dan wani masifaffen tsoronta yake ji. Kallon shi tayi cikin kuka tare da mika mishi hannu, da sauri ya isa gabanta, ta faɗa jikin shi tana kuka, tare da gaya mishi. "Ina jin tsoron Allah, ina jin tsoron ranar da zaka fada komar wata mace, dan nasan zan wahala, don Allah stay with me!" Cikin tausayinta tare da kwashewa Inayat Albarka ya shiga shafa kanta yana faɗin. "Insha Allah kece Mata ta , a duniya kece a lahira. Bana fatan na miki kishiya har karshen rayuwata." Ya fadi haka tare da rintsa idanun shi, yana jin wani irin ciwo na zalintar matar shi da yayi, "kai Allah ya Isar min ban tafe mi.." a gigice ta d'ago kanta, idanun ta rau-rau tace mishi. "Meye nayi maka?!". Shafa kanta yayi sai yanzun ya fahimci ashe a wajen yayi Allah ya isan!.. "Ni da mafarkin da kike yi ne akan kishiya, shine nake tsinewa mafarkin tare da ja mata Allah ya isa, akan lallai." Rufe mishi bakin shi tayi da nata, sun jima a duniyar romasiya, kafin suka tsaya daga nan dai aka dinke ya shiga mata alqawarin duk duniya babu waya sai ita, kuma babu ita babu kishiya, har duniya ta tashi, abun tausayi haka yayi ta mata alqawari kamar babu gobe.
* A hankali sauki yake samuwa, ina kuma kara aniyar barin kowa, ranar da na cika kwana takwas, aka sallame ni. Ina zanje tunda Baba yazo ya saka Mama a gaba sun tafi, dan haka na dauki wayata da yake cikin jakata, na turawa Dr Ishaq sakon. *_Idan ba zaka damu ba ina don Allah ina son kayana zan koma gida._* shiru shiru har kusan awa daya sai da na tashi a hankali nake tafiya har na isa bakin Office din sa, naji kamar an kira suna na. "Bafa zina bace kuma ba fyade bace, Yallabai ka fahimci wani abu, Ni na amshi aurentawa M. A auren ta, kuma ga sakon shi nan yace a mai data bakin aikinta, matar shi ce dan haka ina ganin ko bata yi aiki da Asibitin ba, dole mu ware mata kuɗin da zata yi ta buka...." Kamar Mahaukaciya na shiga cikin office din ina kallon su, kafin nace. "Dr Ishaq ina kayana suke? Zan koma gida ina sauri." Kallona yayi sannan ya kauda kan shi yana faɗin. "Kije ina zuwa!" "Babu inda zani! Kawai ka bani kayana, dan wallahi matukar baka fito ka bani kayana ba toh tabbas gawata zaku fitar a cikin asibitin, bana kaunar jan numfashi a cikin asibitin mai Nassara, bana kuma fatan na bude idanuna na ganni anan idan ba haka ba wallahi zan muku asarar indai ban kashe kaina ba." Fita yayi na juya gurin MD na asibitin, daukar marke nayi naje gaban kofar da zai kai ka Office din Malik na rubuta. Kome da lokacin sa! Sannan na fita a hankali daga cikin office din, kuka nake dannewa amma bana tunanin zan iya rike shi, dakyar na fita daga asibitin, Na samu Ishaq ya bude min kofa motar shi kauda kaina nayi, sannan na bude bayan motar na dauki kayana, "Amma dai ki min adalci! Meye laifina, kizo zan taimaka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 22