Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ci?" Nan tayi min bayanin yadda take ji shareta nayi sannan na koma daki na rubuta mata magani da allura ta sayo na mata.. sannan na koma na samu Khady ta gyara kome har ta zuba mana abincin. Zama nayi muka Ci, sannan ta shirya ta bar gidan, dake aikin dare ne da ita. Ana kawo kayan Maman Abba, nayi mata allura sannsn na barta taji da sauran. A hankali rayuwa take kara tafiya, zuciyata da hankali na yana tare da yan uwana da Mahaifiyata, haka kawai sai naji maraici ya kamani, ban tab'a jin kewar Baba ba, kawai na ina kara jin haushi abin da ya aikata min, sosai. Sabida abinda yayi ba haka iyaye na gari suke ba. Dan haka na fita hanyar shi.   Gombe Mutuwar Maman Inayat bai sawa Baban Inayat yayi hankali ba sai ma ƙoƙarin ganin ya mallake gidan baki d'aya wanda take dan haka ya shiga kawo musu sayan gidan, yana cikin wannan yanayin Allah ya hada shi da hatsari, wanda yayi sanadin karyewan kafarshi, ya taru a guri guda. Anyi dauri yafi sau uku bai gyaru ba. Karshen kafar ashe kwayar cutar tsatsa ya shiga cikin kafar (TT), dan haka aka yanke kafar daga idanun sawu zuwa kwanji, karshe abokan shi da suke kai shi su baro shi suka daina zuwa gurin shi. Matan shi kowacce ta gaya mishi gaskiya ba zata iya daukar nauyin shi ba. Ya zata wasa ne sai da Hamisu yace a dinga bashi abunci sau biyu a rana, daya da safe daya da yamma, wai shine mai dama dama, domin duk iyayen su mata sun hana yaran taimaka mishi, wai kowacce tana fadin ai ba Ƴaƴanta kadai ya haifa ba, dan haka babu wanda zai bauta mishi tunda shima bai bauta musu na, sakayyar Allah yana daki ga ciwo ga yunwa abinda ya shiga barazana da lafiyar shi kenan, kafar da aka yanke ta cigaba da ruruwa, har zuwa gwiwar shi. Nusaiba da Mariam basu sani ba, sai wani Jumma'a da suka shirya zuwa mishi wuni, dan ko da suka gaya mishi mutuwar Maman su. Cewa yayi. "Ina ruwana, kune kuka rasata ni ai ina da wasa matar" wannan maganar yayi musu ciwo sosai, dan haka suka yi alkawarin ba zasu tab'a zuwa gidan shi ba sai dalili babba. Mijin Nusaiba ne yake gaya mata yaje gidan yaji baban ta bai da lafiya. Shine ya gaya mata, suka lokacin zuwa sake mazajen su, suna da rufin asiri, nan ya bata kudi yace ta saya mishi wani abu. Rike kudin tayi bata sayi kome ba, tafi son sai ta gan shi tasan me zata saya mishi, ko ta bashi kuɗin. Baba ya wulakanta yaran shi mata, dan gani yake koda ya kyautata musu, karshe Uwarsu ce zata more su, shi yasa koda aka fara batun auren su. Yaja ya noke, musamman Yaran Mama, dan yasan ba zata tab'a d'aga mishi hankali ba, kamar sauran matan shi. Sauran matan idan suka tashi aurar da Yarana yana ƙoƙarin shi sosai. Amma ban da Mama.      Karshe Allah ya taimaka ita da Inayat suka yi ta adashe, ana kwashewa zasu tafi kasuwa, kafin wannan al'amarin ya faru da ita, tare suka yi sayayyar kayan auren kanenta, aka zuba kayan a gidan wata makociyar su. koda auren yazo kome anyi shi cikin walwala dukda babu Inayat, amma shi kan shi sai da yaji kunyar duk abinda aka yi, sabida Mamah tana da jama'a, kuma Allah ya sanyawa mutane soyayyarta a zukatar su. Dayawan mutane basu san soyayya ba. Basu san daukaka ba. Gani suke kamar soyayya itace daukaka. Ko daukaka itace soyayya. Kowanne da cin gashin kan shi, zaka daukaka amma baka da soyayyar mutane toh daukaka ba zai amfane ka ba, da mamah ta fahimci, Allah ya bata jama'a da soyayyar su, sai ta kwantar da kanta ta kuma rike kimarta, sai gashi har gida suke biyota suna mata shatara na arziki, daga baya kishiyoyinta suka shiga gaya mata tana maula da rokon sune, bata tab'a magana akan haka ba, ta barwa Ubangiji sanin shi akan bata abu uku da yayi, Jama'a, soyayyar mutanen, da kuma Daukakar mutanen, babban abin alfahari ne ka samu irin abu a lokaci guda. Wannan kenan, a kofar gidan suka haɗu kowacce mijinta ya kawo ta, mijin Maryama yana da mota shi ya kawo ta a cikin shi, mijin Nusaiba a kashin, roba roba. Lokacin da suka iso farin ciki ne ya cika su, kamar zasu me, Sannan Isah mijin Nusaiba ya isa gurin motar Hamid mijin Maryama, ya mika mishi hannu. Bai karb'a ba sai da ya fito, suka gaisa sannan suka ja gefe suna tattaunawa. "Yallabai da fatan baka gaya mata halin da yake ciki ba! Dan nima ban gayawa Nusaiba ba, na fison su ganshi da idanun su." Murmushi yayi kasancewar shi ya dan girma kadan, dan zasu kusan sa'a da Malik, shi kuma Isah ba zai wuce irin ashirin da takwas zuwa tara ba."kai haba, ai basu sani ba, kawai dai na mata bayanin bai da lafiya, kaga kenan zata fi fahimtar halin da yake ciki, ban da fitar hakkin shi na Uban da wallahi babu abinda Maryama zata zo yi a gidan mugun uba irin shi ba." Murmushi Isah yayi sannan yace mishi, "haka zamu yi hakuri mu taya su kyautata mishi,." Da haka suka juya gurin matan su, suka ga sun zuba musu ido, cikin mamaki suna kallon juna. "Ba dai gulmar mu kuke ba?" "A'ah Baby, akan me zanyi gulmarki kawai Yallabai isa ne yake bani shawarar ko zan nimo wata yar budurwa ce!" "Hubby! Maza kayi zubda yawun bakinka, domin naga baka da lafiya." inji Maryama da mijinta, satar kallon juna Mijin Nusaiba suka yi, tare da sakewa juna murmushi, domin basu iya bayyana soyayyar su a gaban mutane, amma kuma a bayan fage, mijinta mugun dan soyayya ne, idan yana gida rufe get yake yayita Zungure ta.             Sallama suka yi musu, kowanne ya kama gaban shi, domin kowa yasan yan Gombe da ƙoƙarin yin aikin Gwamnati da kuma kasuwanci. Bayan tafiyar mazajen su suka shiga cikin gidan da sallama, kallon su matan Babansu suka yi musamman yadda suka shigo cikin fara'a, tare da gaishe su, dakyar suka amsa, sannan suka zauna a kujeran yar tsuguno, suna kallon yadda gidan kamar ba ana suka rayu ba, ko ina ya mutu, babu wani Cigaba. "Inna Jumala, ina Baban yake?" Nuna musu kofar suka yi, a hankali suka nufi bakin kofar, wari da zarni ya musu sallama, daga bakin kofar suka tsaya. Suna kallon ikon Allah, da gaske dama hisabi tun ba ajiye lahira ba ake yin shi. Rufe baki Nusaiba tayi saboda amai da ya tawo mata,"munafukai nasan jifana Hammadada yayi dan yana zargin ni na kashe Rukayyah, shi yasa yake ta min jifa tsohon banza, yasa ka ido yaga yadda zan mishi. Ku fitar min a gida kafin na taso na dake ku da sandar hannuna, uwarku da ya gama ince zaman kanta ta koma sabida ta isa, toh jinin matsafa ya'yan karuwa". Wani irin kuka ne ya kwace musu, a hankali suka ja da baya, Maryam na girgiza kanta tace. "Ba zaka tab'a sauyawa ba, ba zaka saduda ba. Mun fita hakkinka a matsayin mu na ƴaƴan ka, Allah ya baka lafiya." Daga haka ta ciro kudin da yake cikin jakar ta, ta ajiye mishi sannan ta ja hannun Nusaiba da take ta amai. Suka fita a gidan.       Kashare Yau na tashi da nakuda, duk wani abinda ya dace na bukata duk na hada, sai ruwan zafin da nake sha a kai a kai, sannan na turawa Khady sakon ina nakuda ko zasu zo tare da Maman Tawah ta duba ni, babu b'ata lokaci suka iso. Tare da kayan aiki, dubani nurse din tayi sannan tace min. "Sister Inayat da saura ko zamu tafi asibiti ne?" Gyada mata kai nayi muka nufi asibitin. Tunda matan gidan suka ga mun fito Maman Ummi ta raka mu, suka kafa gulma, tare da cewa zasu zo su duba ni, ko ina kuka da ihu. Haka suka har suka tafi basu ganni ba. Haka na wuni ina fama da abu har zuwa karfe biyar na yammacin Laraba, kafin Allah ya nufa na haihu, cikin sauri suka shiga gyara jaririn, duk karfina ya kare, kafin su yanke cibi, wani ya kuma faɗowa, a raina nace. "Mugu Azzalumin! Ba daya ba har biyu ka zuba min ka tafi kabar ni da wahala." Mahaifan suka cire, tare da duba min sister Khady nacewa. Maman Tawah, don Allah ku dinke min ita, sosai." Cikin sauri na harari Khady sannan nace mata. "Baki da imani ne! Ban karu ba ai."  Dariya tayi sannan tace min. "So nake idan Baban two yazo ya kuma miki barnan da yayi, wallahi ya dagargaje bakin ki. Ya" kwafa tayi, cikin jin dadi. Tana goge Yaran, dinki kan nasha shi, dan kamar yadda Khady ta bukata haka aka dinke ni, ina kallon yaran cikin wani irin soyayya, "Allah sarki Mamah na, ko a wani hali kike?" Murmushi Khady tayi tace min. "Duk inda  take tana cikin amincin Allah." "Nagode sosai Khady kinfi karfin kawa sai Yar uwa." Murmushi tayi bayan ta sanya min babyn farko a kirjina, "Aliyu MALIK Mai Nassara Anoosh! Shine na farko" Ta faɗa min kai tsaye. Sannan ta kuma dauko dayan ta daura min a kirjina. "Rukayyah MALIK Mai Nassara Anoosha"  kwalla ne ya cika min ido, na fara kyaftawa tace min. "Bana son wani kukan shauki ki gaya min kin yafewa MALIK?" Daure fuska nayi cikin jin haushi nace mata. "Har abada bazan yafe mishi ba." Tab'e baki tayi sannan tace min. "Toh haka yafi tunda ba zaki yafe ba, da alamu har yanzun kayan aikin shi bai ladabta mana da bakin ki ba...💋 Zamu sha suna *_KOME DA LOKACIN SA_*          https://my.w.tt/DA8QfsbgPab             Chapter 21     Na MrsUsman400 No nation can rise to the height of glory unless your women are side by side with you.         Bayan sun gama shirya mu, aka mai dani dakin hutu, lumshe idanuna nayi tare da zurfaffa tunanin akan yadda kome yazo min cikin gaggawa, a hankali a raina na furta."wannan al'amarin ikon Ubangiji ne kawai, domin a da can ina jin sunan shi. Amma yau da na fitar da jinin shi tabbas, Ubangiji ya shirya haka ne da nashi ikon. MALIK ya rabani da kome nawa, ya raba ni da mutuncina da karfin tsiya, sannan. Sannan ya tafi ko wai-waiye bai yi ba, balle ya san ya bar baya da kura, motsin jariran naji na tashi a hankali na duba su, Kowanne yana cikin kayan Macen set din kayanta purple ne, namijin kuma set din sky blue ne, sai motsi suke, na rasa abin da zan iya musu, a sannu na kai hannuna na tab'a macen wacce tafi namijin kazar kazar, na d'agota, giranta a haɗe da juna, sak na ubanta. Karewa fuskarta kallo nayi, naga babu abin da na samu a jikin ta, sai baki. Kwalla ne ya cika min ido cikin takaici nace. "Wato tsabar mugunta har kome sai da ka ɗauke min akan yarana, Allah sai ya saka min!"  "Uwar masifa, meye kuma Yayana yayi miki? Don Allah ki gaya min meye yayi miki!"  Cikin bakin ciki nace mata, "toh har halittar yaran duk na shine! Babu abinda ya bar min da zance yarana ne!" "Toh sai aka yi ya-ya? Gani nayi dai yayi namijin kokari dubi yadda kika ba'ata mana yara da baki don Allah? Meye haka, karki damu idan tunanin Hero Man kike toh, dai kwalelenki yarinya domin dan uwana yafi karfin doguwar siririn me kama da priyanka." Banza nayi da ita, kamar ba dani take ba sabida ni dai banga kamar da muke da wancan ba'indiyar ba. Mika min cup tayi cike da shayi, ta ajiye min. Da gashashen nama. Kallon ta nayi zan yi magana, ta murguda min baƙi tayi sannan ta ajiye min a gaba na tace min." Gobe Ummana zata zo,  na gaya mata kin sauka lafiya, amma zaki sha ruwan zafi Ƴa nan!" "Toh uwar nan!" Na gaya mata, shiru tayi na wani lokaci, kafin tace min. "Baki tab'a tambayana wacece ni ba?" Murmushi nayi Mata sannan nace mata. "Me zan tambaya? Bayan na san ke din nagartacciya ce! Me nake bukata bayan haka." Murmushi tayi sannan tace min. "Wani lokacin ƙaddara takan ya sauyawa tare da taimakon wasu mutanen! Yancin da na samu, yana cikin sauyin kaddarata ce. Ni yar kabilar terawa ce, mahaifina da Mahaifiyata dukkan su terawa ne, idan kika ji mace tace bata son kishiya tsoron abinda zai wargaza mata rayuwa take,  mijina babban ma'aikacin gwamnatin tarayya ne, albashin sa ba na wasa bane, dan yana daukar dari biyar da talatin, dubu fa. Dan haka kome nawa ya fita daban a cikin mutane. Hatta dangin shi sun san yana girmama alamarina. Mahaifiyar shi tana sona kamar ta goyani." Numfashi ta sauke sannan tace min,"duk wannan soyayyar ban haihu ba, sabida Allah bai bani ba. Kuma karki manta matsalar da ga shine ba ni ba, dan haka yan uwan shi, sun damu sosai dan gani suke zan iya rabuwa dashi.  A kwana a tashi ya hadu da wata mata irin yan siyasan nan, ta makale mishi tun abin bai damuna har ya fara damuna, karshe dai magana ya tabbata zai auro Zulaihat, aka sha biki ta tare. Tun daga ranar da ta shigo, na samu tawaye daga mijina da dangin shi, dan bata wuce wata uku ba, ta fara laulayi. Ban yi mamaki da al'amarin Ubangiji ba. Sai na nutsu muka yi ta murna. Karshe dai ban san me ya faru ba sanadin cikin muka rabu da mijina, domin kuwa ba zance ga dalilin ba, sai dai mun kacame da fada ne karshe ta fadi suka ce wai na zubda mata ciki dan ni ban haifa ba, yana zuwa babu bin ba'asi yace min naje ya sake ni. Har saki uku." Tana masifar son mijinta dan babu ranar da bazata bani labarin rayuwar ta da mijinta. Kwalla ta goge sannan tace min. "Ina son Habib, haka na dawo gida nayi zaman zawarci, wani alhaji Musa ya fito ya aure ni, shi kam babu dad'i zaman mu domin kuwa, wallahi baya bani hakkina a gado, ina dalili na saba mijina tana sex dani cikin jin dad'i. Tuni na balle auren, domin auren irin su Alhaji Musa, turaki zasu ga kudi babu kayan aiki, lafiyayyar mace irina ko ka bani arziki ko kar ka bani arziki indai kayan aikinka lafiyayye ne, zamu tafi koda kuwa sai kayi faskare ne ka ciyar dani Alhamdulillah zan zauna a haka. Da na fito ne wani na kuma wani auren abokin aikin mu, shi kuma iyayen shi suka hanani zama, tun daga nan na ajiye auren tunda Allah zai bani ikon rike kaina, ina cikin zamana, kwatsam sai ga Habib. Hmm tsautsayi ranar da yazo kamar zai hauka ce shi bai sake ni, naki kula shi. Haka yayi ta kira min mutane suna min magana naki kula shi, daga karshe ya amince ya sake ni don Allah nayi hakuri na koma d'akina, ana ne nace ban iya ji ba, da  bazan koma ba. Wasa wasa wankin hula ya kai mu ga dare, ya kada ya raya na koma fir naki, dan haka yayi tabin dangina har suka daura auren ban sani ba, sai bayan sati biyu yazo." Shiru tayi tare da kauda kanta, kafin kwalla ya zubo mata, yayi min bayani naki na yarda dan wallahi ina da masifar taurin kai, tunda ya bini naki, Habib ya bini da karfin tsiya sai da ya biya bukatar shi, sannan ya sauka a kaina yana fadin. "Amma mata kika aura ko? Naji yadda na barki baya haka kike yanzun, ba damuwa zanyi maneji a haka, tunda haka ne gani nan na dawo miki," kuka na saka tare da jifar shi da pillow, a haka ya shiga ban daki ya haɗa min ruwan wanka muka yi tare duk da ni matsamin, muna gamawa ya sani a gaba da rarrashi tare da bani hakuri. Ranar dau kusan biyu na dare yana garin nan,.kafin ya mike tare da ce min. "Toh bako zai yi halin shi, kiyi hakuri idan na zalince ki, ka yafe min. Zan tafi Allah ya ƙaddara saduwar mu," tawowa yayi ya sumbaci goshina, sannan ya juya abin shi, duk da yadda nake jin son shi bai sani iya amsa mishi kome ba, sai dai yana fita naji tashin hankali da wani mugun tsoro, kwanciya nayi ban farka ba sai karfe tara na safe domin na makara, ganin Mami tare da Umma, a zaune suna kallon na, ma tashi da sauri na shiga ban daki nayi alola sannan na gabatar da sallah, ina idarwa na zuba musu ido,.kafin naji hanjin cikina ya haitsine, cikin fargaba na tambaye su "mami. lafiya?" Gyara zama Mami tayi sannan tace min. "Waye ya baki lafiya?" Nayi maza nace mata! "Allah"  sannan ta kuma tambayana "waye ya baki ya baki rayuwa?". Cikin rauni na ce mata "Allah! "Idan ya kuma baki ya kuma baki ya kuma kara miki, ya wadataki Ta ko ina me zaki ce mishi?!"  Wannan karon kuka nake a sanyayye nace mata. "Alhamdulillah!" Mik'ewa tayi sannan tace min. "Sako hijab dinki Muje" rike hannun ta nayi kuka yana tawo min a hankali, nace mata. " Allah ya amshi rayuwar Habib ko?" Rungume ni tayi sannan tace min."da sannu Allah zai mishi sakayya, domin sun kashe shi ta hanyar kisar Wulakancin." "Alhamdulillahi, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji ka gafarta mishi," daga haka muka nufi  gombe, muka samu har an kai shi gidan shi na gaskiya, toh me ya faru? A bakin  drivan shi aka ji abin da ya faru, domin kuwa har dashi, a cikin mutanen da matar Habib ta biya suka kashe shi, ki yayya aka yi garin dauka a waya sai gashi ya daura a Status din shi. Ina Habib yake ce mishi, " Yusha'u! Meye nayi maka da zafi? Duk zaman da muka yi da kai ban cancanci haka daga gare ka ba, amma kai Zulaihat ta biya zaku kashe ni." Kawai cikin rashin imani da tausayi yayi ta buga mishi karfe a kan shi, sai da ya daina motsi, sannan sauran suka sara shi, yadda babu dad'in gani dai! A bakin shi aka ji wai ashe ta ce mishi indai zai dawo dani, sai dai mu zauna a lahira ba da duniya ba. Shine ta kashe min shi, Inayatu Rahman, ban taba shiga cikin tashin hankali ba kamar mutuwar Habib wanda ya bar baya da kura, bayan an kama mutanen da suka kashe shi ne, aka kuma fara ƙoƙarin raba abin da ya bari sai ga cikin da na gama lissafin shi yazo ranar da aka kashe shi, a ranar Ubangiji ya fidda rayayye a jikin shi. Bayyanar cikin ya kuma dawowa da kome baya, inda aka yi ta rigima wai ba cikin shi ba, karshe dai cikin ikon Allah, har na haihu yan uwan shi suka zo, tun  da aka fito musu da yaron, suka yi sanyi basu kuma daga min hankali ba, karshe dai aka da wo dani gida, aka min wanka babu hidimar suna, dan Ni bana son hayaniya, ranar da Yaron ya cika bakwai suka mai da mishi Habib, haka suka cire hakkin Mahaifiyarshi, sauran ni da yarona, dan haka na tattara na kau bank, na ajiye mishi hakkin shi. A hankali kome yake tafiya har na yaye yaron na barshi a hannun Iyaye na, na dawo bakin aikina. Tunda zan iya tsare kaina babu amfanin d'aga hankalina akan sai nayi aure." Zuba mata ido kafin nace. "Me ya faru da Zulaihat?" Murmushi tayi sannan tace min" suna gidan yarin, a can zasu gana rayuwar su, ni kuma ina fatan na cika da imani.". Dariya ta bani dan tausayi na tausaya mata amma bane jin zan barta haka babu aure shine cikar kamalarta, a sannu muka yi ta hira jifa jifa, har aka sallame ne, sannan muka nufi gidan da nake, tun daga bakin kofar na fahimci Naman Ummi tayi aiki sosai... 🙏🏼 Don Allah kuyi hakuri wutar mu ta lalace... Sai ranar da kuka kuma gani na....💋 *_KOME DA LOKACIN SA_*          https://my.w.tt/Q9sw6sZXQab             Chapter 22 All our dreams can come true, if we have the courage to pursue them.            Cikin wani irin kulawa Maman Ummi da Khady suke bani, yaran kuwa Matar Baba Malam ce tazo ta wanke min su, tana gamawa aka miko min Aliyu na bashi nono. Kallon yaron nake, ina satar kallon su Khady.."ranki shi dad'e! Ko zaki taimaka ki bashi nonon, ba waliyi bane irinki da kunya zai hanaki fadar sunan ciki."  Kauda kai nayi sannan na juya musu baya, na fara saka mishi nonon, anan aka yi abin kunya. "Khady ya ki amsa da."  Zuwa tayi gaba na, ta amshi Yaron, ta gyara min zaman shi, sannan ta kuma ciro nonon. Ta saka mishi a bakin shi. Ai kuwa ya kama da karfi, da sauri na cire, ina zare idanuna. " Wallahi da zafi bari na huta sai a kuma saka mishi." "Inayatu Rahman ki tsaya min na saka mishi abincin shi, kowa ce uwa sai da ta iso wannan lokacin, Kinga kenan kome ya kan ribaci lokacin sa,.dan haka ki bari na saka mishi abincin shi please,"  cikin damuwa Maman Ummi tace min. "Haba malama Inayat, muna miki kallon wayayyar mace ashe ba haka ba, Innarki ma haka ta shayar dake fa, taya bazaki shayar da shi ba, lokacin yake bukatar ki, kome da lokacin sa, wata rana sai labari. Yanzun lokacin ki kula dasu, dan haka koyi yadda zaki tattalin su, domin wata rana su tattalaki." "Karku ga laifinta, bafulatana ce. Dan haka ni na mata uzuri ku bata guri." Aikuwa suka mike duk suka fita, na nutsu na basu duk da zafi, amma bai kai zafin tsanar MALIK ba, hawayen dake zuba min bana kome ba ne, sai na tsanar MALIK. Yau ina jin zafi da ciwon jiki ne sabida shi. ba zan tab'a yafe mishi ba, kuma idona idan shi, sai ya san yayi da mace. Kwafa nayi lokacin da na ajiye Anoosh, na dauki Anoosha. Itama na bata har sai da tayi barci. Sannan na mike tare da kiran Khady tace min. "Don Allah kar suna na ya kare, gani nan taimaka kiyi wanka kuma kar a shiga ruwan zafi sosai dan kayan dinki zai warware, Kinga dole a kuma sabon dakin." "Insha Allah mugun fatar ki ya tsaya akan mugun mutum."  Dariya tasa min sannan ta karaso inda nake cire kayana, tace min." Allah ina gaya miki, duk ranar da kika kuma shiga hannun mu, Alqur'an sai kin yi kuka da majina." Tab'e baki nayi sannan na saka hijab, na fita abuna. Ta kuma saka min dariya, sai da ya kular da ni."      Bayan Matar Baba tayi min wanka, na fito a hankali Maman Ummi tace min."Maman tawayen, ko zaki ci tuwo miyar kuka?" Yadda tayi maganar sai ya kashe min jiki, bana son daurawa kowa damuwata, dan ma matar bata gajiya ne, amma wallahi kamar ta kwanta min, take yi sabida kawai duk abinda zata bukata na asibiti idan na ganta tazo bana barinta ta tayi, duk nike mata, har sayan magani. Kusan rayuwar mutanen da ba a cikin gari suke ba, gashi babu karfi balle wadata kome ma dai sai a hankali. Shi yasa na bata shawarar ta fara sayar da kayan miya da wasu abubuwan a cikin gidan, dake muna da dan tazara kafin mu isa shago ko kasuwa. Shiru tayi sannan tace min bata da hanyar jari, ban ce mata kome ba na share batun, har kusan wata guda sannan na bata dubu biyar, tafara alhamdulillah dan tana samu sosai. Murmushi nayi mata sannan nace mata. "Saka min ai zanci." Cikin jin dadi ta koma kitchen din, dariya da shewa Asabe suka saka. Koda ta kawo min, na zauna naci Sosai.               Cikin kwanaki ƙalilan na gyagije kamar bani ba, ina zaune Khady ta sani a gaba, lallai

Chapter 10 of 22