gashi bata da kowa a garin nan, idan ta koma gida tsoron mahaifinta yake hanata zuwa gurin Mahaifiyar ta, don Allah duk ranar da kika ga tashiga damuwa gashi ki bata, kudin dukka, Allah zai tsaya mata._
.. wani irin tausayin Inaya taba ta, gashi ta zauna sai share kwalla take, anya za a samu abokai na gari irin Khady, zama tayi a bakin katifar tace. "Maman yan biyu! Meye na kuka?" Cikin shashekar kuka nace mata, "na cire kuɗin haya dubu ashirin ga kudin cefenen kayan abinci, na ware. Sabulun wankin mu zan biya kudin reno. Maman Ummi kudin da ya rage dubu biyu ne, gashi basu da pampes din su, Allah ka dubi rayuwata." Rike hannuna tayi sannan tace min. "Haba Inayat, kiyi godiya sosai Allah zai kara miki, Insha Allah rayuwarki zata inganta, akwai sakonki. Amma dole ki hada da sana'a koda kasuwanci ne, domin rike iyalinki, Insha Allah Baban Yan biyu zai zo gare ki." Fita tayi sai gata da katon akwatin katako, tazo aka bude sannan ka cire Naira dubu saba'in da tara. "Khadijah ko?" Murmushi tayi min sannan tace..... Long page 🙄 😒
_Allah Sarki! Wallahi mun sami Matsalar wuta ne, yanzun haka ma charge na ya kone, zan je na sayo sabo! Kuma ina da da uzurin rayuwa ba iya typing ɗin zan tsaya ba don Allah kuyi hakuri zan yi kokarin kara yawan Pagen 🙏🏼_
#MrsUsman400
*_KOME DA LOKACIN SA_*
Chapter 24
A woman is like a tea bag, you never know how strong it is until it’s in hot water.
Wani kukan farin ciki ne ya kamani na sake shi a hankali, ina shashekar kuka, tare da rungume kuɗin ina jin shi kamar Khady ce a gaba, na d'ago kaina cikin kuka nace mata, "Khady mutum ce!" "Maman biyu ai tafi ƙarfin haka ma, matar tasan halicci." Haka mukayi kukan mu tare sannan muka share hwayen mu, daga ranar na tattara kuɗin na fara tunanin abinda ya dace, ina ƙoƙarin kula da yaran.
Cameroon.
Zaune suke a gaban Baffa, ya kura musu ido,tausayin rashin uwa tare da rashin nagartaccen uba yasa shi kasa aiwatar da nufin shi akan su na aurar dasu. "Zehrah! Abdul Hakim, yace yana son zai tafi dake can inda yake karatu kumasi, shin zaki amince da auren shi ko kina da wanda kike so?" Sake sunkuyar da kanta tayi tattaunawar su da balkisu ya dawo mata, a hankali. _Mama tayi laifi mai girma! Domin wanke laifinta daga zuciyar Zuri'ar ta, zamu sadaukar da kanmu da rayuwar mu. Idan Baffa ya baki abinda yake so ki amsa hannu bibbiyu, haka zai wanke laifin namar mu._ murmushi tayi wanda yake dauke da kwalla tace mishi. "Baffa duk abinda ka bani a rayuwata ina son shi, koda kuwa zai zame min guba, bazan tab'a dana sani da zabinka ba." Murmushi yayi sannan ya kalli Balkisu yace mata. "Ke ai mun gama kome ai! Kuma kin amshe kurma hannu bibbiyu." Gyada mishi kai tayi, sannan ya cigaba da cewa. "Zaku tattauna dasu, ban sani ba ko zaki iya zama dashi amma, yana aiki anan Yauden kuma ba laifi matsayin shi na babba zai iya daukar nauyin duk wata damuwarki. Jikokina ne kamar ku, kuma nayi imani zaku zauna lafiya. Insha Allah zaku yaba da zab'ina, sannan na tura gidan yan uwan babanku, sun bar min kome, amma kasancewar da uba ake ado ya sani zan Barsu suyi ikon su." Gyada kai suka yi, sannan ya kuma saka musu albarka suka mike zasu fita, yace musu. "Idan kuna da wanda kike so kuyi magana." Juyawa Zehrah tayi cikin nutsuwa kanta a sunkuye tace mishi. "Damu da kanmu duk ikon kan ne, bamu da wata damuwa kanka Mun, dan haka bamu da zab'i sai naka, koda kuwa yafi karfin mu, zamu zauna dashi a haka. Dan haka dukkan ababen ikonka ne." Murmushi yayi sannan yace musu. "Amma naga ke Zehrah baki gama makaranta ba? Kuma na san zaku so Yayar ku tanan tare daku.". Murmushi Balkisu tayi sannan tace mishi. "Addah Inayat bazata hana kome ba, ko tana nan ko bata nan. Bikin Magaji bai hana na magajiya. " Tana fadar hakan suka fita, Kawun su Habu ya shigo dakin, ya zauna sosai nan ya shiga mishi bayanin wani aikin da Zakiyah tasaka shi, yan uwan su na kasar Larabawa, sun jima suna tattaunawa kafin Baffa yayi shiru. Bayan ya dauki wani casbin shi ya shafa turare a jikin shi, sannan ya fara addu'o'in. Murmushi yayi sannan ya cigaba yace. "Ikon Allah! Ai laifin uwar shi ce da tayi fushi da shi, da ta janyo shi jikinta da babu abinda zai faru, sun sami duniya sun manta da cewa, su barci suke wasu na musu minshari, ka gaya mata ta fadawa Uwar shi dole sai tayi hakuri, sannan ta kuma cigaba da addu'a, masallatai da asibitoci da gidan marayu, Insha Allah zata ga ikon Allah, karta yarda tayi fushi, akan lamarin shi. Domin yana dab da dawo cikin nutsuwar shi matsalar shi daya ce, matar shi ta kafe shi a jikinta ne, idan ba ita taso ba koda an kira shi bazai yiwu ya dawo ba, sai ita da kanta ta dawo dan kanta.. amma Insha Allah kome yayi farko zai yi karshe domin kome yana tare da lokacin sa ne." Da wannan Kawu Habu ya fita ya gayawa Zakiyah.
London.
Karfe biyu na yamma, yana zaune ya zuba legs din shi a saman Center table, yana rike da wayar shi, ya nutsu sosai a kan internet, yana wani aiki na kamfanin shi da yake Nairobi na kasan Kenya. Kamfanin sarrafa tayar mota yake son yayi dan kwanaki ƙalilan da suka wuce sunyi hira da wani dan kasuwa wanda yake da hannun Jari a kamfanin motaccin shi ya mishi tayin ya bude kamfanin wani abu a kasar mana, dake mutum ne mai mugun kishin kasa da kuma son yadda harkokin kasuwanci a kasashe daban-daban na duniya shine ya fara tunanin buɗe kamfanin sarrafa tayar mota, na INMAL. Murmushi yayi sannan yace " da ace zaki haifa min yara sunan su zan saka a jikin kamfanin, wannan kamfanin kyautar daren farkon mu dake ne! Na baki shi, sabida kin cancanci kyautar haka." "Assalamun Alaikum!" Daga sama Zeeh ta leko sabida tashin hankali, bata san lokacin da ta shiga hada step uku uku ba, sabida zunzurutun kishin da ya kamota, Kamar zata yi kuka ta iso inda Su'ada take,bai kalle su balle Zeeh tasaka ran ya kalli Su'ada wacce kusan rabin manyan manyan boons ɗinta suke waje, sai kunnen ta da tasaka bluetooth, tana magana tare da lashe bakinta, tana satar kallon Malik, wanda hankalin shi yake kan waya, a dame Zeeh ta juya gare shi cikin jin haushi tace mishi. "Ya Malik! Ko zaka koma sama ne?" Gyara zama yayi sannan ya zuba mata ido, kafin ya zubga mata harara sannan ya ce mata. "Gidana ko gidanki? Kee !" Su'ada ta juya bayanta, cikin haɗe fuska ya nuna mata Hanyar waje, yana fadin. "Na kuma ganinki sai na sanya an rufe min Babanki maza out." Da sauri ta fita tare da yarda kullin da aka bata ta kawo, mik'ewa yayi. Zeeh tayi maza ta dauke maganin, tana zare idanu. Yana zuwa ya amshi maganin bayan ya murde hannunta, yana kallon yadda ta rud'e. "Kar na kuma ganin kafarki a waje, kuma ki wuce ki shirya mu tafi asibiti." Kamar zata fasa kuka ta nufi hanyar sama, ya bi bayanta, tana shiga d'akin ta ya shiga na shi, akan mirror ya ajiye kunshi... Bayan awa biyu, shi hankalin shi kwance Zeeh kuwa kuka take kamar ranta zai fita, a gaban likitan. Da yayi musu bayanin ba zata iya daukar nauyin ciki a jikinta ba koda ta dauka toh zai zube...
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/atPphUdpTab
Chapter 25
In our struggle for freedom, truth is the only weapon we possess.
~WANNAN SHAFIN NAKUNE YAN JEKA DA FARI!🙏🏼💝TUBA NAKE DOMIN NA TAƁA JI KIMAR KU ALLAH YA HUCI ZUCIYAR KU~
Babbar damuwar ta yadda taga yarinyar tana kuka zata bita, yafi kome d'aga mata hankali. har ta isa masaukin ta tunanin kwayar Idon Malik da na yaran nan take, wannan abin da ban mamaki yake, soyayyar yaran kara samun matsuguni yake a zuciyarta, wani irin kauna take musu mai matuƙar wahala tayiwa wani na daban, har dare yayi tana nazarin Yaran da kuma Uwar su, musamman yadda taga kamarta da Neemrah. Ajiyar zuciya ta sauke. Tana kuma girgiza kafarta. Tare da fatan Allah ya nuna mata gobe, ta koma taga Yaran.
Cameroon
Shekaru uku baya. Kakan su ya daura musu auren, da jikokin shi maza, sabida biyayyar da suka yi alkawarin zasu mishi, kuma hakan ya kasance, sun amshi auren domin faranta mishi rai, duk da kowaccen su bata da ra'ayin mijin da aka bata, sai dai kuma hadin ya zame musu alkhairi, domin Balkisu da take tsammanin mijin ta me suna Abdul Rahman, kurma ne sai taga bs haka bane, zunzurutun rashin son magana ce yasa ake kiran shi da kurma. Dadd'awa sojan Kamaru ne mai matsayin conal, abun yayi mata dad'i, cikin ikon Allah ta samu miji irin wanda bata tsammaci samun shi ba. Sai Zehrah mijinta shima ya gama karatun shi yana koyarwa anan a jami'ar da ya gama karatu. Sau dayawa Kakan su yakan turo iyayen su. Akan suga irin zaman da suke yi. Kurma shine Yaron Habu na biyu, yana da wata babbar yar me sunan Maman su Inayat. Sai mijin Zehrah. Me sunan Faruq. Kuma shi Sha'aibu ne ya haife shi. Wannan dalilin ya sanya duk suka yi na'am da yaran. Kuma suna zaune lafiya domin Balkisu ta haihu, inda ta samu mace, bazato balle tsammani. Kawai ya sanya ma, yarinyar Sunan Mama. Inda suka sanyawa yarinyar Inan. Zehrah ce har yanzu Allah bai kawo ba. Kuma suna kan addu'a Allah ya basu mai amfani.
Gombe.
Mariam ta haihu, ta sami d'a namiji. Itama Nusaiba tana goyon cikin na biyu kenan. Alhamdulillah gidajen su babu matsala domin Mama ta basu tarbiyyar da ya dace. Kuma suma mazan su. Basu da wata matsala, suna zaune dasu da amana. Ishaq yana nan Gombe, dan har yau bai cire tsammanin haduwa da Inayat ba, dan gani yake tana kusa da shi, shi yasa yake garin gombe yana aiki. Kuma yana Cigaba da kula da Nusaiba da Mariam.
***
London.
"Don Allah. Ya Malik ka barni na fita mana, ina son cin abinci. Kuma." Yadda ya watsa mata harara yasa ta had'iye yawun tsoro, a yanzun ita kanta tana mamakin yadda Malik yake cin Ubanta a tsanake. Babu hayaniya babu kome kawai zai ci mutuncin ta ba tare da ya duba dangantakar dake tsakanin su ba. Yana gama shiryawa ya juya zai fita ta riko hannun shi. "bani da kowa anan ƙasar sai kai bani da da ko ƴa Mahaifa ta lalace,kai kuma ka juya min baya, don Allah ka rufa min asiri." Janye hannun shi yayi sannan ya juya tare da d'ago fuskar ta, yace mata. "Kuskuren da kika min yana dayawa, kinyi min laifi amma na zabi zama dake bawai dan bani da zab'i bane kawai ina sonki da zumuncin iyayen mu ne. Zeeh ina son Haihuwa!" Cikin raunin murya tace. "Amma kai ne kace min ba zaka tab'a niman Haihuwa ba!" "Shiiiiii" ya saka mata hannun shi a baƙi. Sannan ya kuka juya ya fita abin shi. Zama tayi na fashe da kuka, tare da cin alwashin sai ta hana shi sukuni itama. A cikin shekaru uku, badan tayi dagaske ba da tabbas sai ya sanya zuciyarta bugawa domin kuwa tsakanin shi da Allah yake tubure mata, kuma haka zata yi hakuri dashi, ba tare da cewa kome ba. Karshe da ta nemi taimakon Tabawa tace ba zata iya ba, dan zuwa yanzun Malik yafi karfin su. A hanyar shi ta zuwa aiki. Ya zubawa laptop din shi ido, yana ƙoƙarin bin wani rubutun da ya gani a tweeter din Ammin shi. Inda take bayanin tsarin halittar Ubangiji, tare da cewa taga ikon Allah. Bata tab'a rayuwa anan ba, amma Allah cikin ikon shi ya bayyana mata wasu taurari acikin sararin samaniya, masu matukar burgewa da kyau. Murmushi yayi sannan ya jinjina wannan yabon dan yasan a da can shi takewa wannan yabon, a yanzun kuwa bai da ikon ta mishi yabon haka sabida yayi nisa da ita, kuma ya kasa zuwa gareta yana son tafiya kodan Inayat, yana son zuwa yaga yadda ta koma. _Kai idan ta kama ma ka watsar da ita a gefen hanya_ "innalillahi wa'inna ilaihi rajioun Ubangiji na tuba" ya furta a hankali tare da jin wani irin yanayi, Tabbas ya wulankata d'an adam wanda Ubangiji da kanshi ya karrama shi, amma shi wulakanta ta yayi, bayan shi yasan bai kyauta mata ba. Zare neck tie, din wuyar shi yayi har ya shiga meeting maganar shi Inayat ce, a lokacin da yazo da ita bai mata kallon macen da tasan darajar kanta, domin shi ganin yake suna aikin ne dan kawai niman suna, niman sunan kuwa yana cikin sake ragamar rayuwar su, iska mai zafi ya furzar sabida idan zai kwana ya wuni yana tuna yadda take sai dai yayi ta zubda eretic a jikin shi, shi yasa bai cika son yafita yana nazarin Inayat ba, dan duk sai ya bata jikin shi da damuwa, har aka gama meeting bai tsinana kome ba, asalima dakin shi da yake cikin office din shi ya shiga, yayi ta juyi yana bukatar mace a kusa dashi, Musamman Inayat. Me yasa duk tsawon lokacin da ya ɗauka bai tuna da ita ba, sai yanzun take yaji shi a high speed, had'iye yawun yayi, lokacin da hoton ranar ya dawo mishi kamar yanzun abin yake faruwa, sai jin shi yayi ya juye wata bakin man shi a jiki, dan Allah ya gani yana bukace da mace, ganin bai sami saukin haka ba, yasa shi barin Office din da gaggawa, zuwa gida. Inda ya sami Zeeh tasha kuka tana barci sai jin shi yayi yana sarrafata kamar zai cinyata, tuni tabi yarima aka sha kida, yana yi yana kiran Inayat. "Don Allah karki tafi ki barni, wallahi ina jin dadin haka tabbas ke koramata ce lambuna ce,ke wayyo Allah na, zaki kashe ni da dadinki.". Gabaki daya ya gama haukace mata, kuma yana sussuce sai Zungure ta yake sai da ya tara mata gajiya ya kyaleta.. ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya. "Ya MALIK!" Mik'ewa yayi tare da nufar ban daki ya haɗa ruwa wanka, sannan ya fito, bai san me yasa ba, duk abinda tayi mishi yana ranshi amma idan ya tuna son ne sila sai yaji kome ya tsaya mishi cak. "Idan zaki iya mik'ewa ki mike idan ba zaki iya ba Cigaba da kwanciyar ki." Shiru tayi kafin tattaro karfinta ta mike zaune, tana jin wani irin azaba, *Inayat* kalmar da zuciyarta ta bata kenan shiru tayi sannan ta sauka zuwa ban daki ta shiga ruwan domin fasa jikinta. Ta same shi kwance cikin ruwan, idanun shi lumshe, gargasar jikin shi kwance lub. "Kiyi abinda ya kawo ki, bana son kallon kurilla. Had'iye yawu tayi ta cigaba da abinda ya kawota sannan can ta kasa hakuri. "Wacece Inayat?" Bude idanu yayi tare da table baki sannan ya gyara kwanciyar shi cikin ruwan, wato ita zai mai da Mahaukaciya. Mik'ewa tayi cikin fushi ta fice. Kiran sunan Inayat ya kuma dawowa mishi da kome. Cikin shekaru uku baya, ji yaƙe kamar ba zai iya rayuwa da ita ba, lokacin da ya iya dubu biyar kudin sadakinta, ya kuma wulakantata a wannan lokacin bai tab'a rikewa a ranshi zai daw... Jin karar bude kofa bai sashi ya bude idanun shi ba, sai dai jikin shi ya bashi akwai wani abu. Bude idanun shi yayi dai-dai da d'aga wukar da Zeeh tayi zata caka mishi, cikin zafin nama ya saka kafa ya tokareta sai da ta bugu da bangon bakin dakin. Kasa motsi tayi iyaka kokarinta da ta tashi ta kasa, sake wukar tayi, ya fito cikin ruwan yayi wani wankan zuciyarshi tana zafi. _Yallabai Matarka tana fama da cutar birkicewa Ƙwaƙwalwa, sabida yadda take iya cutar da kanta, tare da had'iye wasu abubuwan cutarwa._ wani irin yanayi yaji a ran shi ba dai maganar Dr Tony bane zai tabbata, domin shi ya fara gaya mishi tana fama da cutar birkicewa Ƙwaƙwalwa. Da sauri yaja towel, ya daura sannan ya dauke ta, maganar na kuma dawo mishi. _Idan har baka kula ba hatta kai zata iya yunkurin kashewa_ innalillahi wa'inna ilaihi rajiou, ya faɗa a kasan ranshi. Tabbas akwai matsala domin kuwa da yanzun yasha wuka, yanzun kan ya yarda Zeeh ta haukace, sosai tayi hauka tuburan indai zata iya kashe shi. Da wannan tunanin ya dauke ta zuwa dakin ta, ya rufe ta, sai da ya gama shiryawa sannan yazo ya dauke ta suka nufi asibiti. An kwantar da ita, a ka shiga binciken ta, sosai domin yayi musu bayanin yadda ya kamata. Sannan ya bar asibitin. Babbar damuwar shi ta inda zai fara niman Inayat dan yasan ya rasa Number Dr Ishaq. Domin shine kadai yasan inda zai same ta. Bai dawo asibitin ba sai yamma, koda ya shiga ya sameta zaune ta bawa kofar baya. Bai damu ba, ya shiga tare da jan kujera ya zauna suna fuskarta juna. Hawaye ke zuba daga cikin idanunta. "Bana son ganinka!" Ta gaya mishi kanta a sunkuye. Shiru yayi sannan ya zuba mata ido, shi bai masan yaushe ya aureta ba, asalima ba zai iya cewa yana Sonta ba, kawai yasan Neemrah itace macen da ya fara shakuwa da ita. Duk da kasancewar ta yar Kawun shi, bai tab'a jin soyayyarta ba, sai bayan rasuwar ta,Mace daya tal yaji wasu abubuwa na musamman akanta, ya kuma ji zafin yadda ta tozarshi a cikin mutane, zai iya rantsewa da Allah Inayat tayi mishi mugun duka a zuciyar shi, tunda daga haduwar Farko, abin takaici rashin kunyar da rashin tsoronta yasa shi jin tsanarta, ya tsani mace mara kunya, a iya tunanin shi ya zata idan mace bata da kunya da Rashin tsoro dan sun san wasu mazan ne, shi yasa da MD ya gaya mishi alaƙarta da Dr Ishaq, yasa shi tunanin kodai Ishaq ya sauya halayyar shi ne, tunda koda suka yi karatu a jami'ar cambridge, kowa yasan halin su basa kula mace kuma basu da ra'ayin mace, sai dai ya fahimci Ishaq na masifar kaunar Yarinyar, shi kuma yayi alqawarin gyara mata zama ne, shi yasa ya ajiye amintar su, ya auri Yarinyar da Aminin shi yake matukar kauna. Zai koma tunda lafiyar shi lau, ko zai samu Haihuwa a tare da ita, shi ko Haihuwar tayi zai iya barinta ta koma gurin Ishaq shi kenan. "Nace bana son ganinka!" Maganar Matar shi ya dawo dashi daga duniyar tunani, da mamakinta sai taga ya mike tare da tattara wayoyin shi, kawai ya bar mata d'akin. Wani sabon kuka ne ya kamata, dan haka ta cire alluran da aka sanya mata drip wato callula, ta shiga huda kanta dashi kamar mahaukaciya, (😏🙄😒🤦🏼♀️ nasan duk bakin mutane ne ya kamaki!) Shigowar nurse taga abinda take yasata ta fita da gudu, tana kiran dr...... A hanyar shi ta komawa gida yaga Yarinyar Tabawa, tana ta tsare shi ya kauda kai abin shi. Domin baya son magana.
Kashere
Washi gari Jumma'a. Bani aikin safe sai rana, sabida kukan da Anoosha tayi Yasaka mata zazzaɓi, magani na bata sannan na gyara mata kwanciya a jikina, Anoosh shima ya kwanta, tunda na basu abinci suka dan tab'a, nake nazarin abinda ya faru jiya. Mik'ewa nayi na gyara musu kwanciyar su, sannan na nufin waje na dibe ruwa a rijiya na yi mana wanke wanke, kafin na mai da hankali na. Nayi wankin kayan mu, ina idarwa na koma dakin na fara tunanin me zan girka mana, kawai na mike tare da ɗaukar dari biyar na nufi kasuwa naje nayi mana cefene kayan miya, dan ina son tuwo miyar eguzi ne, kuma suma yaran suna son tuwo sosai. Ban wani jima ba, na hango mota uku a kofar gidan, jikina ne yayi sanyi. Saboda ban sha'awan alaƙar mu tayi nisa da Madam Azizah,sabida kar tazo ta fahimci kome daga baya su saka karfi su rabani da Yarana, tun daga tsakar gidan na fahimci Itace, sabida ihun da yaran suke ana bata labarin tuwatu wato karatu, kallona Maman Abba tayi sannan tace min. "Hala uwar baban su Yan biyu ko? Dan naga kamar su da Anoosh ta b'aci, Inayat indai babu damuwa ko koma hannun baban Yaranki mana, ai kowa rai ya amfana yafi game shi, ace kowa yana miki kallon me zaman kanta" a razane na kalleta jikina yana tsuma, dama kallon da ake min kenan. Lallai Malik ya cutar dani. Wuceta nayi tare da nufar cikin dakin, da sallama. "Amin wa'alaikimun Salam, Ammahn mu ta dawo." Inji Madam Azizah, a sanyayye na sake ledar sannan na gaisheta. Tsugul Anoosha tazo ta bude ledar, tana fidda abin da nasayo, tana kallona kamar zata yi kuka tace min. "Ammah! Ina bobo?" Kunya ce ta kamani, na rasa bakin bata amsa, rikota Madam Azizah tayi tana kallon yadda na takure a guri guda, Al'amarin yarinyar nada girma a zuciyarta, d'aga wayarta tayi sannan tace. "maza ka shiga kasuwa kasayo min bobo katan biyu." Da sauri na kalle ta, murmushi tayi min, sannan tace min. "Ki sake jikinki, dukkan mu abu daya ne, ga kuma tarin soyayyar da nake musu, shi yasa na taso naga yadda Anoosha ta kwana ita da Anoosh, ya sunan su?". Gabana ne ya fadi muryana na rawa nace mata. "Namijin sunan shi.". Kasa fadar sunan nayi ina murza yatsun hannuna,, kallon yadda nake kokarin b'oye yanayin da nake ciki ne yasata ce min. "Toh ita mace da?" "Rukayyah shi kuma Aliyu!" Murmushi tayi sannan tace min. "Hala sunan Babanki ne ko? Dan naga kina jin nauyin fadar sunan ni.kums sunan mai gidana ne. Ita kuma wannan sunan Yar Kawuna ce, wacce ta b'ata shekaru masu yawa, dukda shi Mahaifin shi bafulatani ne daga Sudan. Amma Mahaifiyarshi balarabiyar Kuwait ce!" A razane na kalleta jikina kamar an zare min laka, sannan ta cigaba da cewa, "lokacin da na tab'a ganinta Malik yana da shekaru goma, muka tafi garin su, toh bamu sake haɗuwa ba, amma yau da naganki tare da yaran nan ya tuna min ita, gashi har da mai sunanta, Kina kama sosai da Mahaifiyar mu, domin kamar su da Neemrah ya b'aci sosai, Yarana biyar maza biyu mata uku, suna Abuja, amma Babban yayi tafiya har yau ban san inda yake ba." Zuciyata tace tayi ta kokwanto, kafin na kuma watsar tare da bude bokitin shinkafar tuwo na zuba a cikin roba tare da saka mishi ruwa, na fita na wanke, sannan ya shiga kitchen ɗin tsakar gida na dibo gaushi, na zuba akan gawayi na wanke tunkuyar na daura girki, kafin na shigo har ta fara gyara min ganye. "Laa barshi zan." Murmushi tayi sannan tace. "Yau daya zan miki aiki, duk da gidana cike yake da masu girki, yaran sun hanani kome, sai dai naci na kwanta, haka ta gyara ganye, na wanke tace na bata ta yanka, so naki amma ta amsa, "ai naga da ace mijinki zai iya rabuwa dake ai da zaman ku zai yi kyau da MALIK!" Wani irin bugun zuciya naji tare da d'agowa na kalleta, "A'a! Kawai na fada ne, dan kusan halinku daya ce, baya son magana sosai" sai yanzun na fahimci, tana son na dinga biye mata muna hira ne. Murmushi nayi, sannan nace mata. "Ina magana ai kawai." "Assalamu alaikum! Hajiya ga bobon." Da sauri na fito na amsa, sannan na ajiye dayan kafin na koma na dauko na biyu, aikuwa Anoosha na gani tasaka ihu a bude mata, haka aka bude mata, tana sha, zata wurga da wani ta kuma ɗaukar wani, zata dauki na uku, na buge hannunta, aikuwa tasaka kuka. "Zoki amshi abinki ki rabu da Amma mu, idan muka tafi Abuja ai bazata hanaki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 22