Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nayi, tare da kallon yadda Baba ya koma kamar mahaukaci, kallona yayi sannan yaga ina kallon kofar d'akin Mamah, murmushi yayi sannan yace min. "Da alamu baki san uwarki ta mutu ba, sabida bakin cikin shigarki duniya! Dama ai ba wani abu bane mai zafi gado kika yi! Kuma kin tabbata tunda ta iya biyo namiji ta tsallake maganar iyayenta, kema ai baki yar a kasa ba, Kai ji yara  wannan Baturen ne da ya aurenki kuka haihu dashi ko a bariki kika kwaso shegu kyawawa haka." A hankali na juya zan fita domin bana iya rike kaina, har na isa bakin kofa, na juya tare da goge fuska na, nace mishi. "A wannan lokacin niman kusanci ga mahaliccin ka ya dace dakai! Hmm! Yayi kyau Ubangiji yana jin mu yana ganin mu, shi zai fidda gaskiya kome d'acinta. Na Barka lafiya." Na rike hannun yarana na, ban san me ya hanani kuka ba,. amma kuka ne a cikin zuciya ta, Mamah na ta rasu bamu hadu na, wannan wata irin masifa ce.". Daga nan asobitin mai Nassara na wuce niman Dr Ishaq, aka ce min yabar garin, musamman asibitin, innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Ya Allah..na fada a hankali. A gaggauce na koma kashare abinda idona ya hango min ya sani jin kamar zan fadi kasa, kayan mu aka watsar min a waje, Dr Jamil na zaune a samar motar shi, yana gani na ya sauko daga motar, "Inayatu Rahman! Toh dama na gaya miki bijire min dai dai yake da barinki kauyen nan, ga sakamakon haka,"  "Allah ka duba maraicina da yaran da ka bani Ya Allah karka bari wasu su wulakantanmu, Ya Allah na kame kaina daga fasadi Ya Allah karka bari wani ya cutar damu, Ubangiji kimata yake son tabawa, Ya Allah al'amarin aurena zan kar...." "Ammah! Kaka!"... Hello idanuna yana yaji sosai! Mu hadu gobe. *_KOME DA LOKACIN SA_*     https://my.w.tt/66CiC512Uab             Chapter 28 Better to keep your mouth shut and appear stupid than to open it and remove all doubt. A hankali na d'ago jajjayen Idanuna, na zuba a motar da tayi parking a gaba, tare da rike hannun Yarana, a hankali ta fito bayan an bude mata Kofar. Kallon yaran tayi tare da mika musu hannu, wani irin kuka ne ya kwace min, Na kira Allah ya kuma amsa min, Ya Rabbi Alamina ka kuma rufa min asiri duniya da lahira, kallona tayi sannan tace min. "Kuka bai kare ba? Ba gani ba! Take me like mother!". A hankali tasa ka kwashe min kayan mu, sannan aka zuba motar bayan mu, saukowa Dr Jamil yayi a hankali zai tawo gurin mu, ta kalle shi a sanyayye. Sannan tace mishi. "Ba zan tab'a barin ka ka cutar da ita ba, amma zanyi fatan Alkhairi tare da maka addu'ar Ubangiji ya kawo ka inda nake domin anan nake da zama. Nan zaka sayi rashin kunyar ka da kudi me daraja." Daga hakan ta riko hannun yaran ta saka a motar, sannan tace na shiga gaban motar. Tunda na shiga , nake jan zuciya. Duk Malik ya haifar min da wannan Matsalar, kara jin tsanar shi nake, kukan da banyi ba da shi nake yi yanzun, har muka iso Gombe, airport muka nufa inda muka sami private jet din Malik shi ya kawota, da murna yaran suke har da tsalle zasu hau jirgi. Har aka gama kome muka bar gombe hawayena bai kafe ba, Yau nake jin mugun kewar yan uwana. Bani da kowa sai Allah. Yau ina rayuwa ne kamar mara gaskiya. Tunda muna muka iso abuja na fahimci ban san ko ina ba, yau ga ƙaddarar Malik ya kawo ni. Tun kafin mu isa motar gidan su ya zo jiran mu, muna sauka ta kalle ni. "Barka da zuwa Abuja." Murmushin yake na mata, sannan na sunkuyar da kaina, muka nufi inda jerin gwanon motarta yake. Muna shiga na fahimci canjin yanayi da na rayuwa ya same ni, don kuwa yaranta da suka zo tare mu, har da wani dan matashin saurayi me mugun kama da MALIK, haka suka shiga rige rigen daukar su Anoosha, suma kuma yaran basu ki ba, dan har ina mamakin su. Har muka iso Unguwar su dake maitama. Na kasa magana, sai dai kuma ina matuƙar son na keb'ence ni daya na, sabida muyi magana da Khady. Wata matashin wacce ba zata wuce sa'ata ba ita ta iso cikin mamaki tana cewa. "Ammyn ba dan ni naga Gawar Neemrah ba, da wallahi babu abinda zai hanani cewa ita, tashin hankali. Wannan ai sai ki samu gudu. Shigo daga ciki." Cikin murmushi Madam Azizah tace mata, "da na gaya miki baki yarda ba fa! Sai ma tamtamar da kike, dubu yadda Ubangiji yayi nashi ikon!" Murmushi Kuwwah tayi wacce take dauke da Anoosh tace. "Addah dubi yadda wannan nake kama da Ya MALIK, ita kuma Ta hannun Hajna tana mugun kama dake, ko Haysam!" B'ata rai yayi cikin shagwaɓa sannan yace musu. "Toh ina ruwana! Addah kice su bani yaran na gani nima, Tunda a airport Kuwwah da Hajnan suka sauke yaran sun barni empty hand." Dariya suka saka musamman da ya watsa hannun alamun yaji haushi bai dauki Yaran ba.  "Ku haka ake tarb'an bako, babu ruwa babu zama kun bar bakuwa a zaune." Riko hannun na Mahnoor tayi muka shiga wani katon falon da zai iya daukar mutane hamsin da wani abu, sannan ta danna wani ƙararawa sai ga wasu mata har su uku, suka shiga jera abincin da suka tawo dashi, ina kallon Abincin, yayi min kyau. Amma kuma haka zan sake jiki naci abincin. Dan haka cikin wani irin yanayi na kin sakewa dasu nace musu. "Na koshi da!" Juyawa suka yi suna kallona, nima kuma kallon tsoro ƙarara na nuna musu, murmushi Madam Azizah tayi."ku kai mata d'akina." Haka suka kwashe abincin  suka kai min d'akinta, ta sani a gaba har dakin inda na sami abincin, kallonta nayi sanan na sunkuyar da kaina nace. "Ammyn Nagode, Insha Allah gobe." Kiyi waka keda yaran sai kuci abinci gobe sai mu tattauna." Fita tayi ta barni a d'akin, sannan na sauke ajiyar zuciya. Wanka nayi Musa sannan nayi nawa, ina fitowa na samu an shirya su, cikin kananun kayan mu, sai wani narkewa suke a jikinta kamar wasa manshanu.  Ajiye min wata doguwar riga tayi me bakin mayafi. Sai cream da wasu abubuwan kwalliya.  Sai da na shirya tsaf. Sannan na zauna na fara basu abinci, Daya daga cikin yan matan ta shigo tana rike da roban Fan vanilla ice cream, ta mikawa Anoosh cikin murmushi tace mishi. "Kai Sunan Dad ne da kai gashi kasaka min albarka. Kema kuma kina kama da Addah Mahnoor, karba kisha." Akwai wani abu da yake tab'a zuciyar Uwa! Duk yadda kake son sanin wacece ita! Toh ka kyautatawa D'anta nan zaka san wacece ita, kasa jure abun nayi na sake lallausar murmushi sannan nace baku cewa. "Aunty Thank You ba"  kallon na Hannun Anoosh, Anoosha tayi ta kuwa dire robar tace. "A ba co. Ayi min kalami." Kunya sai ta kamani dai dai shigowar Madam Azizah, taga yadda Anoosha ta ke shirin bare baki tace min. "Bana son saurin hannu me kuma tayi miki?". Zan yi magana Wacce ta basu kyautar tace. "A'a Ammyn dani ce. Wai na bata ice cream ne shine ta wurga bayan ta kalli na hannun Dad." "Ai baki isa ba, kije ki dauko mata babba irin na shi. Kuwwah karki kuma haka, domin ba a banbance musu KOME dan tare aka haife su.," "iyi hakuri Ammyn" na fada juyawa tayi tazo gurin Anoosha wacce ta rungume ni tana kuka, shi kuma Anoosh ya mika mata roban, buge hannun shi tayi bata so. Haushi kamar na had'iye zuciya, domin iya kunya naji shi,sai da aka kawo mata nata, sannan ta daina kuka, shima kuma ya kama nashi wai ta buge hannun shi. Sai da suka gama birkita min lissafi. Sannan suka yi shiru. Har dare ban wani fito ba, duk da ina magana da Khady. Da kuma irin sauyin kaddarata da ba samu. Washi gari        Tun asuba da ba tashi nayi wanka tare da gyara jikina, sannan na kama yaran nayi musu, suna rikici haka na shirya su cikin kayan su wanda muka zo dashi, sannan muka sake komawa. Gado bamu tashi ba sai karfe goma sha biyu, nan muka yi brush dan har an kawo mana abinci. A hankali na basu suka ci. Maganganu Mahnoor yana dawo min, jiya da ta shigo zata ta koma gidanta. "Duk da kinki cewa kome akan Yaran nan, amma ki sani ina da yakinin  Yaran nan jinin mune! Duk da bana da lokacin da zan iya fadar abun da nake da yakinin faruwar shi, Wannan yaran Malik ne! Dan nasan Yaje Gombe shakaru baya, kuma, naji labarin kamar yayi aure. Dake bani da hujja shi yasa ba zan takura miki ba, ban ga laifin ki dan kinki sakin jikinki damu ba, amma ki sani muna miki kallon. Wata abu me daraja ce,kodan Kamar da kike Da Yar uwarmu da ta rasu zamu rike ki da Yaranki." Tana gama fad'ar haka tayi ficcewar ta waje. Har cikin dare sai da na tuna batun, Malik ya cuce ni, ya cuci rayuwata. Da naga tunani zai hanani sakat ya sani tashi sallar dare. Kafin na samu nutsuwa har barci yayi gaba dani.      Bayan mun karya, sai ga Madam Azizah ta shigo, tashi Anoosha tayi tare da rungume ta, tana sauke ajiyar zuciya, kamar nayi mata wani abu. Sannan ta kalle ni. "Me kika mata take ajiyar zuciya?" Murmushi nayi sannan nace mata. "Wai zata fita ne, na hanata." Murmushi tayi sannan ta zuba min ido, kafin tace min. "Ko zaki tashi ki kai su, makarantar mu dake cikin Estate din nan, zasu basu kome har da unifoam."  Gyada kai na nayi saboda haka yayi min dad'i. Kamar yadda ta gaya min muka nufi makarantar nayi musu kome, inda na boye asalin mai Nassara. Na Barsu da M Aliyu. Haka yayi matukar tasiri, dan babu wanda zai gane yaran shi ne.              A sannu kome ya fara tafiya min, sai da nayi kwana goma sha biyar, sannan na fara aiki a cikin asibitin su..har zuwa lokacin. Ban sake jiki dasu ba, yara na ma rike su nake wani lokaci a daki gashi Yaran sun shiga ransu sosai. Ina jin Kuwwah tana cewa. "Ammyn don Allah kicewa Ammah su Anoosha don Allah tafi toh mana dasu. Wallahi akwai bakin da zanyi ne, kuma na daura hotunar sune a IG na." Dariya tayi sannan tace mata. "nima ina jiran ta bani aron sune yaran Sun kama min zuciya." Ina jin su, na share batun su. Sai da na gama ikona sannan na sake su, suka fita. Ai ban kuma ganin keyar Yaran ba, sai washi gari. Sun zo amsar Unifoam. Kasancewar aiki ya sani a gaba, ranar dakyar na basu kayan ko shirya su ban yi ba, na nufi asibiti.     Da rana nazo na samu an kawo musu masu reno, dukkan su larabawa ne, irin wanda ake basu horo na musamman domin kula da yara da kuma harshen iyayen su.  "Kiyi hakuri! Naga yaran sunfi dacewa da koyar harshen Larabci ne yasani dauko masu renon yara, sannan Kinga kenan zaki samu lokacin kanki, da wasu abubuwan." "Nagode! Amma kuma kashe kudin."  "Ni a matsayin ya na dauke ki." Daga haka ta barni tsaye a gurin. Koda na gayawa Khady, dariya tayi tare da cewa, "karki damu amma na fara hango miki kura fa"  shiru nayi sannan nace mata."bani da lokacin kaina na, aiki muke ba dare ba rana, gashi zamu je workshop. Wani watan." Dariya tayi sannan tace min."ba wannan kurar ba, kinsan da zaran kika cika shekaru hudu Malik bai dawo ba, babu auren shi a kanki?" Gabana ne ya fad'i. Cikin inda inda nace mata. "Toh sai me! Haka nake son naji dadin zabga mishi rashin mutunci." "A gidan su? Zaki zabga mishi rashin mutunci?" "Kina tanka min ne? Kawai manta Amma lokacin na zuwa." "Toh nima dai next year muna tare, dan zanyi aiki da babban asibitin abuja."  "Wayyo Allah na, Uwata sai kin iso." Dariya da murnar da nake ya kasa b'oyewa.  Har muka gama. Lokaci ya tafi ni kaina ban kawo zan iya sake jiki da Familyn mutumin da na tsana, dan haka nayi ta kokarin koyawa yarana mugun hali, domin na rantse sai Malik yayi dana sanin abin da ya aikata dole nayi amfani da Yaran shi gurin ramawa, idan na koya musu k'iyayyar shi, zai yi wuya ya samu kan su, dan haka nake gaya musu nice Maama da Daddysu,  ya cuce ni ya tafi ya barni, shi ba good man bane, yayi hurting dina, yadda nake kokarin nuna musu abin tare da cewa, bani da kowa mama na ta rasu, Sabida Daddysu, Baba na yayi yayi throw din out saboda Daddysu. Idan ina gaya musu haka nakan ga k'iyayyar MALIK a idanun Anoosha, Anoosh sai dai yace min. " Malam din Icilamiyya ace mana babu cau fici da iyaye, kuma Allah yana con macu yabiya."  Kura mishi ido nayi sannan nace a raina wato shi dai Anoosh ba zai taya ni, sai na zuba mishi ido. Anoosha kuwa ita har ce min take bana con Daddy Anooci. .. bayan wasu kwanaki, sai gashi yau zamu taron karawa juna sani na World Health ornaganiziton, tun safe da na tashi nake jin dadi da nutsawa, kallon kaina nayi a madubi, naga yadda k'uguna ya kuma fitowa rass, daga cikina ya bada wani irin suffa kamar kalangu, dake Ammyn su Malik Yar boko ce kuma tana son gyaran jiki, sai gata da wasu magunguna na larabawa, babu wani abu da zai cutar da mutum a cikin maganin, ta bani nake sha,  bata gaya min na meye ba. Amma na fahimci Boons suna sun kuma kara girma, tare da cika sosai, idan na saka kaya suka d'an kame Ni daga sama, sai kaga sun fito saman rigar kamar an hura balloon.  Bom-bom kuwa ba laifi kome ya zauna min, har wani gogewa skin dina yayi. Rashin lokaci yasa Ita da Mahnoor suke kokarin min sayayyar kayan amfanin jiki sosai.  A hankali na daura dan kwalin kayan aikina, sannan na riko hijab din a hannun na, na fito na samu duk sun gama cin abinci zama nayi ina cin bawa, ina idarwa naga lokacin ya tafi, da sauri na nufi hanyar dakin Ammyn, har zan wuce naga wani kofar daki, kawai sai naji ina son shiga dakin. A hankali na bude kofar,  labulen window na bude, kallon Jikin bangon dakin.nayi wani tangamemen hoton balarabiyar sanye da fararen kayan aiki, sak nawa. Ga kamar mu da tayi yawa, sai dai ita fatarta yafi nawa ja. Amma kome namu iri daya ne! A hankali na taka zuwa window inda naga wata yar takarda, an rubuta. _Har abada bazan daina kallon ka ba! MALIK! Kaso ni ko d'an kad'an ne._ tab'e baki nayi tare da kallon hotonta wanda nake ganin tsantsar farin ciki a samar fuskarta, gaban mirror ɗinta naje, sabida ganin dairy ɗinta da kuma bironta, ta.  Bude littafin nayi shafin Farko. Ta Rubuta. _In da rai da rabo wata rana Zan sami soyayyarka amma ba lallai ta amfane ni ba! Dan nayi nisa! Ubangiji ka turo wacce Malik zai mata so kamar yadda na zaucce akan shi Allah ka cika min Burina ko bayan raina Ka turo mishi wacce zata zame mishi garkuwa daga Sharrin Zeemalik!_  shiru nayi tare da cewa. "Wacece Zeeh Malik?" Wani irin iskane kamar an watsa sanyi dakin me mugun karfi, ban san lokacin da na k'amk'ame jikina ba, nayi saurin fita daga d'akin, ajiyar zuciya na sauke sannan na nufi dakin Ammyn, rufu kofar aka yi gammm! Ya sani juyawa da sauri wani irin mugun tsoro ya kamani, da sauri na shige dakin Ammyn tana sallar walaha, dake dakin ta biyu ne, na kasan tabar min, na saman kuma ta zauna abinta, ina shiga na zauna a hankali tare da zuba mata ido, tana sallama. Ko addu'o'in bata shafa ba. "Inayat! Lokacin yana tafiya fa." "Eh nazo. Miki sallama ne! Zan tafi." "Allah ya tsare, kiyi sauri."  A hankali na mike tare da barin d'akin, na nufi sauka. Kallon kofar dakin nayi naga kamar gilmawar mutum da sauri na wuce abuna, ina sauka kasa na sauke ajiyar zuciya, nace. "Bani kuma haurawa sama!" Har na fito waje, zamu fita daga gidan kamar ance na juya naga kamar mace a jikin window dakin Neemrah! Sake juyawa nayi babu matar. Dafe goshi nayi domin kuwa na firgita. A raina na ce bani kuma shiga tunda babu wanda ya aike ni, mun isa inda za ayi taron, tun da muka shiga bamu fito ba, sai faduwar gaban da nake ji, karfe ɗaya aka tashi break, domin muci abinci, dan haka ina fitowa wayata tana ringing. Hannu na saka domin na dauko shi ina tafiya bazan iya cewa ga abinda ya faru ba amma Tabbas! Haduwar mu ta kuma sauya min kaddarar! *WAYE HAKA? ANYA BA MALIK bane?* Allah yau baku da Update uku biyu ne zaku samu na biyun sai dare 🙏🏼 *_KOME DA LOKACIN SA_*     https://my.w.tt/0rQUEQnPVab             Chapter 29 Everyone thinks of changing the world, but no one thinks of changing himself. .... Ban san yana gaba na, ba tunda hankalina da kaina yana bisa jakata, sai gara goshin mu, muka yi lokaci guda nayi baya zan fadi. Cikin wani irin zafin nama, ya kai hannun shi bayana, yayinda kome na hannuna ya watse, idanuna a rintse wani mugun tsoro ya kamani, dukkan hannuna biyu suna bisa kirjin shi. Kura min ido yayi cikin nutsuwa, ga kuma yadda ya tsaya ina stylish cike da mamaki tare da dinbun al'ajabi yake kallon Eyelashe ɗinta, wanda suka mike zara zara bakinta kuwa ta dan cune shi gaba,sannan fuskarta da ta kwaɓe shi kamar zata fasa kuka, har yanzun dai bata bar yaranta ba. Lokaci guda yaji zuciyar shi tana azazzalar shi da ya ambaci sunan ta, amma tsoron kar tace Mishi ba ita bace ya sashi shagala da kallon fuskarta wanda yake cike da annuri, shi kanshi ya manta da inda suke dan a bukace yake da niman wanda ya san inda take sai gashi Allah ya nufa taron nake kolin lafiya ta duniya ta haɗa su. Cikin wani irin yanayi da tsoron gudun karta ba ita bace, ya sashi bude bakin shi kamar me ciwon hakori yace "Inayatu Rahman Ahmad." Cikin wani irin yanayi na bude idanuna akan shi, tare da kafe shi da ido, cikin tsannanin kewar shi kura mishi ido nayi  ban san me zance nake ji ba, amma zuciyata har wani irin bugawa take, sake riƙe rigar shi nayi domin gani nake kamar bashi bane, sake lumshe idanuna nayi, sannan na kuma buɗewa a hankali, bakina na rawa, amma na kasa furta kome,  Tafin mutane ya dawo damu yanayin da muke ciki, cikin sauri na ture shi zan fad'i ya d'ago ni da sauri, sai da kirjin mu ya kuma haɗuwa, cikin tashin hankali na yi maza na janye daga jikin shi. Murmushi yayi tare da kallon fuskokin mutanen gurin a hankali ya furta " she is my Wife! Nurse Inayat Ahmad. Mrs Ishaq Ahijo." Take kowa ya watse tare da nuna mishi bajintar da yayi, ko da yajuyo nayi nisa, domin kunya ce ta kamani, abin da muka aikata. Da sassarfa ya iso gurina. Yana hakki." Kin yi mamakin gani na?" Banza nayi dashi sannan ya kuma wurgo min tambaya! "Me yasa baki waiwayi baya ba?" Wani b'acin rai ne ya kamani ban san lokacin da nace mishi."meye a bayan!" Na juya tare da niman bayan." Inayat!" "Please! Ishaq, bana son damuwa. Ina cikin wani Uzuri ne!" "Amma ki saurare ni!" "Koma meye kabar shi bana bukatar ji! Tunda da saka hannunka ya tozartani! Da wancan ranar kome bai same ni ba, da kai da Malik kun lalata min Futures dina, yanzun da ka..." "Bashi bane! Kin biye Mahaifiyar!" Murmushi me ciwo nayi sannan nace mishi."Duk cikin makircin da kuka shirya min,.ta hanyar bakanta min rayuwa da yayi sanadiyar mutuwar mahaifiyata!" Zaro idanu yayi waje, cike da mamaki, "waye ya gaya miki kece sanadiyyar mutuwar ta?" Banza nayi dashi na nufi inda zan sayi ruwa da drinks, "Inayat! Mahaifiyarki a gidan su ta rasu! A gaban mahaifinta da danginta!" "Ni wanda ya gaya min ba zai min karya ba, ya ce min sanadiyya tace ta rasu,tunda na shiga duniya!" Waya ya ciro a aljuhun shi ya bude ta tare da kira, tan shiga ya ajiye min, "zoka dauki abarka." Cikin b'acin rai da na sanya shi ya dawo gaba na, ya tsaya min. Sai duk na diririce! Zuba min ido yayi kafin yace min. "Ki buga wayar da kasa shine zan fahimci taurin kanki. Kuma aka tashi kika yi tafiyar ki, sai na gayawa Dattijo Hammadada, ba iya shi ba hatta Balkisu da Zehrah, tare da Nusaiba da Mariam. Fahimci abinda kika min, ruwanki ne ki amsa wayar ruwanki,ki fasata zan iya sayan goman ta ba tare da naji ko Dar ba." Cikin tsiwa na murguda mishi baki sannan nace mishi. "Waye ba zai iya saya ba, dadin abin ni ba." Yadda ya juyo min a zafaffe ya sani had'iye maganar, murmushi yayi sannan yace."karamar mara kunya na zata zaki iya cigaba da maganar ne." A kasan raina na ja tsaki tare da cewa. Dalla dube shi mutum sai kace bishiyar kuka, ba dole ba had'iye maganar ba, tunda ka tawo zaka mauje ni. Yadda na kura mishi ido cikin takaici da jin haushi. Ya sashi kyalkyalewa da dariya yana kallona. Duba wayar nayi tare da ganin sunan Mariam, a hankali nasaka a kunne na. "Hello Hamma Ishaq!" Ta faɗa a sanyayye, kasa magana nayi dan ban san me zan cewa kanena ba, a hankali na zare wayar ina kallon shi, idanuna cike da kwalla, na ajiye mishi wayar nace mishi. "Don Allah kace masu na mutu." Daga haka na barshi a gurin, fita nayi daga gurin taron baki daya, na nufi wani gurin na zauna, tare da kifa kaina, ina kuka. Zama yayi tare da cewa. " Bazan iya gaya musu kin mutu ba, amma zan baki lokaci idan kin bakaci sanin inda suke zan miki jagora, Ya mijinki yana nimanki kuwa.?" Juyawa nayi na kalle shi idanuna cike da kwalla nace mishi. "Mutumin da ya iya Mantawa da Mahaifiyar shi, Ni wacece da ba zai iya Mantawa dani ba."  Shiru muka yi kafin ya kalli agogon shi ta zallar silver, saura minti goma a koma taron, "kina nufin kin san kome akan shi kenan?" Girgiza kai nayi ina ƙoƙarin share kwalla ya mika min hanky, "ina tare da mahaifiyar shi.." cike da mamaki, yake kallona, kafin ya mike, "i holp dai babu wani relationship mai tsayi a tare da ku, bayan abinda ya faru?" Shiru nayi tare da share zancen na kauda kaina. Yayi saurin tare ni, "tambaya nayi zaki wuce Ni?!" "Amsarka bata nan, idan kana bukatar shi. Sai ka bari idan an tashi." Ji yayi kamar zuciyarshi zata daka tsalle ta diro waje, tsabar tashin hankali, ba dai Malik ya ja mishi hanyar rasata ba kenan? Ya tambayi kanshi, ganin bai da me bashi amsar ya sashi bin bayanta. Koda suka koma ciki. Anyi jawabai tare da nuna musu muhimmancin, basu horo da za ayi na tsawon wata shida, idan sun kammala zasu kuma zuwa kasar Ingila taron kasa Da kasa, amma dole sai wanda suka samu damar yin nasara a bada horon. Haka muka tashi lokacin Sa'idu yazo ɗauka na, Babu yadda Ishaq bai so mu tafi ba naki, saboda kare kimar aurena, muna isowa gidan. Na samu Mahnoor tazo. Murmushi ta sake min sannan tace min. "Don Allah zoki tayani Bawa Ammyn hakuri, na kawo kaya amma taki saya wai sai ta dauki na kudinta da take bina." Murmushi na sake mata a karo na biyu, sannan na kalli Ammyn nace mata.", amma dai." "Jeki huta ki rabu da ita, aron kudina tayi kusan shekara daya, shine da Allah ya tashi kamata, ta

Chapter 14 of 22