tayi gabana tace min. "Sabida bata baki da tsoron abokin tarayya, kina da rashin kunya, shi ya dauke miki karfin tsoron ki, amma ki taimake ni!" Matsawa nayi zan wuce. "Inayatu Rahman!" Tayi min magana da muryan Khady, juyawa nayi ta saka kanta akan kafad'arta. "Kiyi hakuri ba zan iya daukar ki ba, don Allah ki barni nayi rayuwa ta babu damuwar kowa.". "Toh shi kenan Nagode." Nayi ficcewata, ina jin shashekar kukanta, tsayawa nayi sam bana jin dadin rayuwa da irin wannan damuwar, dan haka nayi sauka na kasa, nan.muka baje hira, wanda ra bishi duk akai na ne,, har aka yi sallar magarib, da isha, sannan muka kuma buɗe hirar wasu suka yi wanka. Anan muka makale juna da Dr.
KWANA BIYU.
Kwanan su Nusaiba takwas, suka koma sabida na gaya musu nima tafiya Zanyi, amma shekara daya zan Insha Allah, na dawo kar su damu. Bayan tafiyar su dan har da Khady, wacce Hasshir ya makale mata, Mu kuma muna an shirye shiryan mu, na barin ƙasar. Matar dakin Neemrah, kamar zata yi hauka, ina jin ta naki kula ta, sai dai tsakanin na da Dr, kamar mu had'iye juna, tsabar son da muke wa juna, dan har yan uwan na, sun taya ni murna, tare da Fatan Alkhairi, yadda Hashshir, domin yana masifar kaunar Khady, idan bana manne da waya, zaka same ni ina manne da waya ta, sabida son da muka kasa furtawa, sai dai muyi tawa junan mu sako ta waya. Alaƙar mu tayi wani irin karfi da duk wanda ya zauna samu sai ya fahimci, mun son junar mu, koda wasa babu rashin fahimta, asalin fahimtar juna muke, Dr Ishaq Ahijo, mutumin kirki ne, yana da kamewa sosai, dan yake gaya min cewa, ai a gida kallon shi ake akan mutumin da aljana ta aura, shi kuwa lafiyar shi lau, kawai wata yake jira. A hankali lokacin tafiyar mu na karatowa, muna kuma sabon shiri sosai, domin kuwa zan bar yaran a hannun Ammyn Khady ma zata zauna a gidan domin Hasshir yace shi yaga matar auren shi. Munyi magana da Mahaifiyar Dr Yayar Mamah,tace nazo fa. Na gaya mata an tura ni karatu ni da Hamma Ishaq, ai kuwa nan tayi ta min nasiha, har da cewa, idan Ishaq yayi min rashin da'a na gaya mata, dan ina da uwa a raye. Murmusa mata nayi sabida ban ga wani abun da zai min rashin da'a ba, mutum ne kamili, sam zai yi wuya kaga ya kalli mace sau biyu, idan naga yana sunkuyar da kai hararar shi nake nace mish. "da zaka daina wannan pretending da yafi maka, da kake wani sunkuyar da kanka, ni bana son gulma." Murmuasa min yake tare da shafa sajen shi zuwa gemun shi. "Malik ya bude miki baki dayawa, amma idan da nisan kwana, wata rana zan rufe miki bakin kin nan domin kina yawan magana da shi, ni kuma bana son yawan Maganar nan" d'aga kai nayi sannan nace mishi. "Gaskiya na manta abinda yake buɗe bakin mutum ko zaka gaya min na nimo shi, dan wallahi sai ka gaya min meke bude bakin mutum." Mik'ewa yayi zai bar Office din shi. Nace mishi. "Kunyata kake ji? Toh madalla gwara da ka nuna min irin macen kunyar da kake ji, Kutt." Murmushi tayi yayi sannan ya bar ni a Office din Ni daya zai zabga murmushi nake.
Ana saura sati zanu tafi, naji bana son tafiyar dan ina yawan nazari akan tafiyar karshe na watsar, ana gobe zamu tafi Ammyn tayi min nasiha me shiga jiki inda ta nuna min girma da darajar da Allah yayiwa dan Adam, tare da nuna min kimata, nasiha dai kamar yadda mahaifiya zata yiwa yarta haka tayi min, sannan muka yi sallama, da dare.. na kwanta . Washi gari haka na rungume yarana na cike da tausayin su. Muka yi sallama da mutanen gidan. Tare da kowa, sannan aka wuce dani airport, inda na sami Dr Ishaq yana jirana, karfe tara na same jirgin mu ya tashi daga birnin tarayya Abuja.... Kuyi hakuri wallahi barci ya dame ni duk ma gama gajiya 🙏🏼🤧
https://my.w.tt/rAUzM8F4Zab
*_KOME DA LOKACIN SA_*
Chapter 33
I don’t care what it is in life: listen to your heart. If you do, no matter what, you win.
Ina kukene maza da Mata masoya kasuwanci, ga dama ta samu! Nesa tazo kusa! Ina masu sayan d'ai d'ai ko sari karku sake a baku labari, da arziki a garin su har gwara a garin mu, kai gwara a dakin mu, karku sake wannan damar ta wuce Ku
Ku garzayo kampanin *Greenleaf biotech* domin ya tanadar muku kayayyaki sama da guda 4500, Kama daga abubuwan amfanin yau da kullum kamar sanitary pad, pampers, baby wipes, sabulan gyaran jiki, man shafawa, magungunan qarin lafiya da magance cututtukan zamani kamar (infection, BP, diabetes da sauransu), kayan kwaliyya, sinadarin rage kina da tumbi, takalma, jakunkuna, air frying pan (baya buqatar Mai wajen suya) da ma wasu da dama.
Zaku iya siya domin amfanin kanku da iyalan ku, sannan kuma zaku iya yin sari domin saidawa ku samu riba me albarka.
Domin qarin bayani ku biyo mu ta wannan link din👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://wa.me/message/XMECES32SQEPK1
Ko ta WhatsApp group👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/BebpPIrkAPj1bfiqfZkkjH
~~~~~~~~
Ranar Alhamis muka sauka a ƙasar London, cikin nutsuwa muke saukowa a jirgi ni da Dr, yana rike da jakata, muna tafiya. Kasancewar mun shiga garin an fara k'ak'ar sanyi sai gashi na fara rawan sanyi, dama kuma tun a gida sai da ya gaya min ki nemi rigar sanyi, nace mishi shigar da nayi ya ishe ni, kallon shi nayi jikina yana wani irin ta wa, a hankali ya zare sweater suit din shi ya bani, ina sakawa na wasu lokuta na sauke ajiyar zuciya, sabida naji dumi, ga kamshin turaren shi me shegen dad'i, murmushi nayi sannan nace mishi. "Nagode!" Da idanun shi ya amshi godiyar. Hararar shi nayi sannan nace mishi. "Meye laifin bakin ka da ba zai amsa yace nima haka ba?" Share ni yayi dan ya fahimci tsokana ce kawai nake mishi kuma idan ya biye min zan ta damun shi da magana, har muka gama dibar kayan mu, muka fito. Yaron Mrs Muhmood muka gani, kallon Dr Ishaq nayi sannan nace mishi. "Toh ni zan tafi inda nafi wayo, kai kuma." Murmushi yayi sannan yace min. "Yayi miki kyau" tsayawa nayi a gaban shi, jikina yayi sanyi, na kalle shi bai damu da sanyin da aka hurawa ba, "ki je yana jiranki!" A sanyayye na juya zan fita, ya rike jakar hannuna, ya amsa sannan ya bude min kofar motar na zauna, murmushi ya sake min bayan ya rufe kofar ya sunkuya daidai window motar, yace. "Shi kenan? Zamu hadu gobe Insha Allah, sai ki nuna min gidan da kike." Kasa magana nayi sabida yadda nake jin numfashin sa a daidai fuskana ya sani kara sunkuyar da kaina, "ok kuje" ya buga motar bayan ya mike daga jikin motar, yana murmushi. Juyawa nayi bayan mun bar gurin ina kallon shi, Ishaq na musamman ne! Ina jin shi a raina da zuciyata,, Ni daya sai murmusawa nake...
***
Rashin nutsuwar da yake fama dashi kwana biyu ya ta'azzara, kwance yake daga shi sai Boxes ɗin shi, singlet ne a jikin shi irin me budadd'yar jiki, idanun shi lumshe kamar wanda yake barci, nan kuwa idanun shi biyu, ajiyar zuciya ya sauke lokacin da tunanin Inayat suka taru a zuciyar shi, ya rasa yadda zai bar kasar nan yaje ya ganta, koda kuwa bata yafe mishi ba, zai samu nutsuwar zuciya. Shigowa Zeeh tayi sanye da wata haf gown, ta nade hannunta a kirji, tana kallon shi, murmushi tayi sannan ta karasa inda take ta zauna a bakin gadon, bai bude ido ba dan yasan ma ita ce. Shafa cinyar shi tayi tare da sake mishi murmushi, kin buɗe idanu yayi ta haura saman shi, tare da kwanciya a jikin shi. Cikin sanyin murya. Tace mishi. "Ya MALIK!" Bude idanu yayi cikin gajiya da ita, dan wallahi ta gundure shi, niman kai yake da ita. "Ina son na shiga wani gasar da za ayi na red capter, don Allah.". Bude idanu yayi tarr akan ta, sannan ya mai da ya rufe. Cikin ko in kula yace mata. "Ina zaki kai min igiyar aurena?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da zuba mishi ido,dan matuƙar ta shiga gasar toh ta kuɗin ce! Zata zama wata abu na musamman a kasar Ingila. Zata sake magana yace mata. "Luk ni ba jahili bane! Sannan ba zan lamunci ki shiga gasar ba, dan karshe haka zaki na fita babu hijab balle mayafi. " "Ya MALIK!" Ta fada a rauna ne, "na gama magana tace." Ya gaya mata haka tare da lumshe idanun shi, cikin bakin ciki ta sauka akan shi tare da cewa. "Zan yi fa! Ko kana so ko baka so" sannan tayi juyawarta, tana bakin cikin wannan lamari, ace mutum kwana biyu aiki yayi tasiri akan shi kwana biyu ya ɓalle kamar bauna, kullum aikin kenan yau tana mishi aiki zai yi wata biyu zuwa uku, kafin na hudu sai ya kusan mata shegen duka. Wannan abu yana bata haushi , shi yasa yanzun koda karfin tsiya sai tayi. Dan haka ta shiga hada wani shegen aiki akan shi, tana. Me jin dole zuwa dare yazo ya bata hakuri tare da amincewa. Haka ta gama aikinta bai zo ba har washi gari. Bayan yayi musu booking na abincin da zasu karya dashi, tunda ya sauka ya biya tare da zama ya fara cin na shi. Yana kallon kofar d'akin ta, dan bata fito ba. Kamar ya haura sama amma ya share ta, yana gana cin abincin shi yayi ficcewar shi. Ita ta sani. Haka suka ci-gaba da zaman doya da manja har na tsawon sati Daya. Ta kuma hada wani aikin. Wannan karon ta samo shi dan bu, sai gashi ya ajiye mata sako zata iya shiga gasar, abin mamaki wannan lokacin sai ya zamana basu samun haduwa da juna, sai suyi almost three days basu saka juna a idanun ba, kuma ba kowa ya bata shawaran haka ba sai Tabawa, domin tayi alqawarin sai ta fidda ta a gidanta yarta ta shiga, rashin zamanta ya janyo mishi yawon gidajen abinci. Tunda ba girkawa take ba, gwara shi yakan shiga yayi musu ko taliya ce, suci har da ita tayi ta cewa ashe dama ya iya girki. Shi kuma ba haka bane matsalar shi, yana bukatar mace a kusa da shi, koda zai yi abun toh a nuna yayi bajinta, idan Zeemalik ta yabi abincin tana durawa tumbin ta ne,.dan haka ya daina damun kanshi da girki, sai dai su sayi abincin waje..
''' Yau satin mu biyar da zuwa, muna daukar darasi yadda ya dace, idan na dawo Kum zan tafi makarantar da Ammyn ta sani, gashi Mrs Muhmood tana da kirki, itama gwana ce a girki da iya tattalin rayuwa, haka yayi matukar kara min kwarin gwiwa, domin ita take yaba min da yadda nake kokarin gwada abun da nake ɗauka, sai Ishaq. Haka yana da nasaba da yadda muka yarda da junan mu, a idanun mu da zuciyar mu, ta yarda da soyayyar juna, amma a zahirance mun kasa gayawa juna, sai b'oyewa muke, zan iya cewa tun zuwan mu, yake kokarin ganin ya gaya min, Amma ya kasa, sai ya barshi Kawai, sai mun kusan kammalawa sai ya gaya min. Kuma kowa ya ganmu zai kira mu da ma'aurata, amma kuma Ishaq yaki wani abu sai ma share ni da yake nima na watsar da shi a gefe.
***
Gombe.
Dakyar yaja da gindi ya fito bakin kofa yana fad'in. "Jumalo! Ki bani kunu mana, ko min kashin sai yunwa zata kashe ni." Dariya suka saka mishi tare da shewa. "Yanzun Baban Inayatu! Har kai ne kake niman a baka abinci kar yunwa ta kasheka, bayan nan Yaranka suka kawo maka kudi domin kaci abinci kace baka so su kwashi tsiyar su, Ai dama hakkin Rakiya ba zai Barka ba, kuma mu zuba da kai. Abinci ne dai sai dai ka mutu amma ba zamu baka ba, dan haka ka mana horon yunwa, sai dai mu fita mu nima ba dai ka nimo mana ba, ina dalili tunda muma mutane ne, sai ka raba mu da gidajen iyayen mu, mu zauna haka*+ babu ciyarwa ka tab'a yadda muke ji." Kallon su Asabe tayi matar Hamisu, tace musu. "Amma baku tsoron Allah! Duk fifikon da ya nuna muku akan Maman su Inayat,. Bai ishe ku ba. inayat taje aiki, ta dauki albashin ta raba daku, ai Allah ba azzalumin sarki bane, Yana nan yana ganin ku, kuka zauna kuyi ta cutar da bayin Allah. Yanzun kuce zaku gama da duniya lafiya, Wallahi sai kun biya abinda kuka aikata, domin Ubangiji yanzun tun a duniya yake hisabi ba sai an ji lahira ba. Kai kuma baban Inayat baka ga kome ba, nan Su Nusaiba zasu kawo maka kudi ka musu zagin kare dangin, sannan kayi tsammani Allah zai Barka lafiya, toh ga mala'ikun duniya nan Allah ya baka su, aiki ɗaya ya ishe ka, su kwashe kudin kuma su Barka a wulakance. Baka ga kome ba wallahi." Daga haka tayi wucewarta ɗakinta, dan ta gaya musu abinda yake ranta, kuma bata jin kome, dan ko kwanaki da Hamisu ya dake ta, yan uwanta maza yan kalare suka zo suka mishi shegen duka, tare da tsoma shi cikin kwata, suka kuma tabbatar mishi, wallahi ya kuma dukar musu kanwa sai sun sare shi gida uku, sun ajiye shi a kofar gidan, idan yana ganin karya ne bismillah. Haka Mahaifiyar shi, ya kwashe shi zuwa asibiti, yayi jinya dan kudin hannunta ya kare, ranar da suka dawo, Mariam da mijinta sun zo suka bawa Baban kudi yaki amsa bayan ya mata zagin wulakancin a gaban mijinta, haka suka fita suna tana kuka, sabida abin yayi mata cizo, shi kuma yaki daukar kudin Jumalo ta kwashe dubu biyar. Abinta, dakin suka shiga ita da Kishiyarta suka kalli juna sannan suka Jumalo tace. "Nifa na sare da aikin Inayat nan kamar ya lalace, domin Kinga zuwanta nan babu wani abu da ya sauya, sannan Hamisu ya tabbata min da cewa mutumin da ya aureta ranar, yana cikin manyan masu kudin kasar nan, mun dai biya boka kudin shi, amma da alamu aikin bai yi ba, domin ai munce a ranar da aka daura auren zai sake ta, tare da mata korar kare, haka zai sanya ta shiga duniya, amma sai ganinta muka yi da yara.". Wani harara Maman Hindu tayiwa Jumalo tana fadin. "Baki da hankali, ai tabbatar da aikin yayi kenan, in ba haka ba. A ina ta samo yara biyu masu shegen kyau ai sai dai karuwanci, kuma karki yarda ki sare domin karshen rayuwarta kenan, Dan boka ya tabbatar min ba zata tab'a abin arziki a rayuwar duniya ba sai ta lahira idan ana yi acan tayi. Kai ko a lahira ba a fatan yarinyar tayi arziki domin duk sai tafi yaran mu daukaka." Shiru Jumalo tayi sannan tace. "Kuma haka yayi ba, domin nima na fara tsanar yar Banza, shi kuma wancan gurgun fa? Ko shima aikin bokan ne?" Tab'e baki tayi sanan tace. "Babu wani kawai halin shine, dan shi yace Yarinyar bata kama da zuri'arsa, ta dauko Zuri'ar mahaifiyarta ce shi yasa ya tsane ta, musamman yadda suka nuna basu son shi, kuma bawai ita daya bace hatta yan uwanta basu kama da shi, ai baki ga shegu duk mazajen su basu kudi be ba, hatta Zehrah da Balkisu, naji ance mishi duk masu kuɗi suka aura, Inayat ce bana kaunar naji ta auri me kuɗin nan." Haka suka yi ta zagin mutane, tare da kulla sharri son ransu, tare da alwashin ganin bayan Inayat da Yan uwanta. Sannan suka fito, inda suka tsayayyawa Baban su INAYAT kunu a wani ƙaramin kofi, suka dagwara mishi , sannan suka yi wucewar su.
***
A hankali take tafiya, Ni kuma sauri nake na fita daga mall din, sabida Ishaq yana jirana, banje juna muka yi lokaci guda wayar mu ta fadi, da sauri na dauko mata nata na mika mata sannan na dauki nawa. Ban tsaya kallon fuskarta ba nayi ficcewata, bin bayana tayi da ido, sannan ta ja tsaki... Ni kam kuyi min afuwa 🙏🏼🙏🏼🤦🏽♀️
https://my.w.tt/qqXNLMQV0ab
*_KOME DA LOKACIN SA_*
Chapter 34
I put my heart and my soul into my work, and have lost my mind in the process.
Ina kukene maza da Mata masoya kasuwanci, ga dama ta samu! Nesa tazo kusa! Ina masu sayan d'ai d'ai ko sari karku sake a baku labari, da arziki a garin su har gwara a garin mu, kai gwara a dakin mu, karku sake wannan damar ta wuce Ku
Ku garzayo kampanin *Greenleaf biotech* domin ya tanadar muku kayayyaki sama da guda 4500, Kama daga abubuwan amfanin yau da kullum kamar sanitary pad, pampers, baby wipes, sabulan gyaran jiki, man shafawa, magungunan qarin lafiya da magance cututtukan zamani kamar (infection, BP, diabetes da sauransu), kayan kwaliyya, sinadarin rage kina da tumbi, takalma, jakunkuna, air frying pan (baya buqatar Mai wajen suya) da ma wasu da dama.
Zaku iya siya domin amfanin kanku da iyalan ku, sannan kuma zaku iya yin sari domin saidawa ku samu riba me albarka.
Domin qarin bayani ku biyo mu ta wannan link din👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://wa.me/message/XMECES32SQEPK1
Ko ta WhatsApp group👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼
https://chat.whatsapp.com/BebpPIrkAPj1bfiqfZkkjH
~~~~~~~~~~~~~~~~
Kad'a kanta tayi tare da shigewa abin ta. Ni kam ina fita, abinda na fara yi shine niman taxi din da zai kai ni inda Ishaq yaƙe, cikin sauri na samu. Tare da jefa wayar a jakata. Ina isa na hango shi zaune, murmushi nayi mishi tare da zama muka cigaba da hirar mu, a can kuwa tana gama sayan abinda ta saya, ta fito ta samu har Malik ya iso, tana zuwa ta shiga motar, tare da murmushi. Bai kalle ta ba. Ɗan wani irin yanayi yake ji yau din nan, koda suka isa gida, ajiye ta. Ya bar gidan, yana isa Office din shi. Ya fara tattara duk wani abun da ake bukata dan zai shiga meeting, kamar da wasa ya nemi wani Document din shi da yake cike da tsarin kasuwancin da zasu, dafe goshinsa yayi sannan ya furza da iskar bakin shi, kafin ya tuna ai tana bed side din shi. Dan haka ya lallubi wayar shi ya shiga kiran layin Zeehmalik, bai samu ba. Ya kuma gwadawa.
.... Muna cikin dariya naji wayar tana kara amma kasancewar ba wayata bace, ban kawo a jakata bace, sai da aka kuma kira na biyu, sannan Ishaq yace min. "Ki duba wayarki ce take kara!" Cike da mamaki, na kalle shi. "Bafa wayata bace! Ka duba ko naka ne!" "A'a duba dai! Na ki ne!" Baki sake na saka hannu a cikin jakar na ciro wayar iphone pro ta ɗauke, sake shigowa kiran yayi. A tsorace na zubawa wayar ido hannuna yana rawa, ban san lokacin da wayar ta subuce ba. Zan iya manta kome amma bazan tab'a manta fuskar shi, hawaye ne ya shiga saukowa daga cikin idanuna, Dr Ishaq ya sunkuya tare da ɗaukar wayar, hoton kan watan ya kuma bayyana tare da shigowar kiran. Dauka yayi jikin shi a Mace yace. "Ina magana da waye?!" Cikin masifa ya ce." Kana magana da mijin me wayar ce!" Ya faɗa cikin tsawa, murmushi Ishaq yayi sannan yace mishi. "Ok toh gaskiya an sami matsala, domin kuwa anyi musayar wayar da ta mata na, zaka iya zuwa ka amshi Wayar ku." "Kana ina?" Ana ya gaya mishi abinda muke, yana gama waya da shi na mike zan bar gurin, ya riko hannuna. Tare da zaunar dani yana kallon kwayar idanu na, sannan yace min. "Ina zaki? Ina duk wani zafin rai da kike rike dashi? Ki nutsu yazo ya ganmu a tare, wannan ma wata nasara ce, da kika samu akan shi. Karki damu da yadda kome zai zo miki, amma ki saka a ranki Malik zai zama naki ki d'aya, Insha Allah!" Kura mishi ido nayi hawaye na zuba min, sannan na girgiza mishi kai tare da cewa. "Bana kaunar shi! Har abada bana son shi, rayuwata da tashi akwai bambanci, ka kira min wayata ka ji a wani hali yake, dan ban san matar a fuska ba, sai yanzun da naga hoton a wayarta," kiran wayar yayi tare da nutsuwa yana jiran a dauka..
---
Tana sama taji wayar yana ƙara dan haka a tunaninta mijinta ne dan haka ta sauko da mugun gudu. Kamar zata tashi sama, dan har step uku uku take hadawa, tana saukowa kiran na yankewa, sake kira aka yi ta dauki wayar da niyyar amsawa sai faduwa yayi a hannunta ta fasa ihu, kamar mahaukaciya. Wani irin kuka ne ya kwace mata, "Taya haka zai faru? Wallahi mijina bai da wata mace bayan ni. Ya Allah kasa wannan ba yaran shi bane, ina zan saka rayuwata. Ya Allah ka rufa min asiri domin idan Malik ya hadu da wata mace na kaɗe har buzuna." Abin da aka gaya mata shekarun baya ya dawo mata, *_Mun kashe Neemrah! Kome ya yadda ya dace, sai dai ki sani! Kiyi kokarin raba shi da dangin shi balle su tuna dashi a sashi addu'o'in! Ki nisanta shi da dukkan wata mace, wacce zata kasance mai tsananin kama da Neemrah! Ki nisanta duniyar shi da kowa! Karki yarda alaƙar shi tayi nisa da wata mace! Haka zai sanya shi zama naki ke ɗaya, mallakin ki. Daga zarra ya hadu da Shaidaniyar mace! Daga ranar kome zai zame miki cikas! Ki rike abinda na gaya miki karki yarda wani kuskuren ya tab'a rayuwar shi!_* wani irin ihu tasaka tare da rike kanta tana sake huci, kamar wacce ta had'iye kunama, dole yau ta kashe MALIK! "Dole na kashe ka! Dole ka zama nawa ni daya, mu tafi wata duniya mu rayu mu kad'an mu! MALIK kai nawa ne ni daya na, dole na ka zama nawa har abada." Ta kuma sake wani irin huci. Kamar zakanya, lokaci guda halittar fuskarta ya juya kamar ba mutum ba, sai tafiya take kamar wata dabba, a tsakar falon. Tana huci tare da gurnani. Can ta koma gefe, tare da matse kanta a tsakiyar cinyarta, ta k'amk'ame jikinta. Ta kuma sake kuma tana faɗin. "Ni zaka ci amanata? Ni ce zaka yaudare ni, a ina aka samu yara masu kamancecceniya da kai, Wallahi sai na dauki fansar abin da kayi min. Wallahi sai na kashe ka na kashe kaina, Malik kai nawa ne ni daya babu wanda ya isa ya kwace min kai." Haka take kuka tana kuma jaddada abun da zata aikata mishi idan yazo mata.
---
Bata dauki wayar ba, ni dai damuwata wayata, muna zaune duk na gama tsurewa kamar mara gaskiya, wai dama duk cika baki nake, daga jikin zai zo kamar na sake zawayi a wandona. Muna zaune ya iso bai gane mu ba, daura kaina nayi a kafadar Ishaq, har ya iso gaban mu. "Hey!" Inji Malik, cikin Wani irin Izzah ya juya tare da zuba mana ido, wani irin kaduwa kamar zai fadi, ya dafe kujeran da yake gaban shi. Ya kura min ido, ya kuma juya ga Ishaq. Take kan shi ya shiga sara mishi ya tafi kamar zai zube, ya tsaya akan kafarshi. Wani irin abu yake ji a ran shi, me cike da mamaki hade da ruɗa ni, zama yayi ya dauki goran ruwan gaban Mu ya kafa bakin shi sai da ya shanye tass..sannan ya bude rinannun idanun shi, kewarta da begenta suna kuma dawo mishi sabi dal a ran shi. Ya kuma kura mata ido, sannan ya kalli Ishaq cikin basarwa yace mishi. "Ina wayar mata na?" Mik'ewa nayi nace wa Dr Ishaq! "Baby, bashi wayar shi ya bani nawa sai muje dan ina jin yunwa." Murmushi yayi sannan ya mika mishi wayar matar shi, sannan ya mika mishi hannu suka gaisa. "Ishaq ya bayan rabuwa? Ya aikin ka? Da matar ka?" Murmushi Ishaq yayi sannan ya nuna mishi Inayat! Yace mishi. "Ga Iyalina! Aiki kuma muna tab'awa ba laifi.". Daura daya akan daya yayi sannan ya kalli Ishaq yace mishi. " Ayya! Haka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 22