tana Gwarumpa, Malik kuma suna maitama, yasa kwananta uku da zuwa ta shirya zuwa gidan Malik, har zasu tafi da Mahnoor tace a'a, ita bazata ba taje kawai. Tana zuwa ta sami Malik baya gida, sai Zeeh dan haka bata iya sakewa da ita ba, musamman da taga irin kallon da take mata, shi yasa ta kasa zama tace. "Aunty Zeeh zan tafi, idan Ya Malik yazo ki gaya mishi nazo!" Murmushi Zeemalik tayi sannan tace mata. "Idan kina raye ba! Idan kuma na barki a raye ba." Zeeh na gama fad'ar haka, ta juya tayi sama abinta. Tsoro ya hana Neemrah fita, kamar ta kira Mahnoor, sai kuma ta fasa, ta fita jikinta babu kwari, tana shiga motar ta, ta bar gidan, dan dama tasan gari kusan rabin rayuwarta a Nan tayi shi.
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/xsaRHDg9rab
Chapter 3
Na MrsUsman400
Alhamdulillah! Thanks just two page naga yadda kuke nunawa Kome da lokacin sa Love and caring! Jazakillahu Khair Aunty Ramlat! Nagode sosai 😍🤩
Ƙamar karta fita haka take ji, domin tashin hankali me cunkushe da tsoron Allah, ya kamata. Kiran layin Mahnoor tayi cikin kuka tace. "Don Allah ki cewa, Ya Malik ina son shi, ya kuma ji a ranshi zan kasance dashi har kar...." Hiting motar ta aka yi, tayi tayi ta kama birki abun ya gaggara, dan haka ta fashe da kuka, tana ji tana gani haka babbar motar tabi ta kanta, tare da cillata kasa daga babbar gada zuwa kasa. Koda ta fado mutane dayawa sun razana, dan aka suka shiga kai mata dauki da taimako.
A hanyar asibiti, tace ga garinku, da dakyar aka sami wayarta inda aka kira Mahnoor, aka gaya mata, tayi hatsari. Abin tausayi haka suka dibo jiki har da Zeemalik, suka zo asibitin. Sunyi kukan mutuwar Neemrah, daga nan mahaifinta ya kira yayar shi yace a bar mishi gawarta zasu tafi da ita, Kuwait duk da Malik baya cikin nutsuwar shi, sai da ya zubda hawayen sabida rashin Neemrah. Bai tab'a sanin zai yi kewar ta ba sai da aka tafi da ita, kasarsu sannan yayi kuka sosai. Anan kawar Neemrah tazo ta rungume shi, tana kuka. Sabida kaunar da suke wa family din su.
.... Tashi Zeemalik tayi daga cikin taro mutane, ta nufi kicin din gidan babu kowa, haka ta dauki hannunta ta daura a saman gas bayan ta kunna. Bata d'aga ba kuma bata fasa zubda kwalla ba. Shigowar tettah me aikin gidan ta ganta, a wannan mugun halin shine ta fita ta kira Malik. Koda yazo ta sameta hannunta yayi jajjur fatar ta ja ruwa, gashi har ya fara tsatsagewa. Immediately aka yi rushing dinta zuwa asibitin da yake mallakin Mahaifin Neemrah. Anan suka mata treatment tare da bata magani. After few days, anyi addu'o'in suka tattaro zuwa gida, a hankali Malik da Zeeh din shi suke rayuwarsu, tare da kulawa da junansu. Tsakanin Mahnoor da Zeeh basu ga maciji. Koda kuwa zasu buge juna ne, haka yayi matukar tasiri a zuciyar Zeeh dan haka takai Mahnoor, gurin malaminta, hmm bayan wasu kwanaki, maganar yasha banban sai gashi Mahnoor bata iya koda kallon banza wa Zeeh...
Shekara daya da auren su, ya bude mata wani plaza a cikin garin abuja, dan haka lokacin da za a buɗe gurin, mutane da yawa maza da mata sun zo gurin, ana gama budewa wata yarinyar tazo, kusa da Malik tace mishi." Sir Malik Aliyu Mai Nassara ko?" Basar da ita yayi sannan yace mata."Yes!" Cikin rawan kai tace mishi." Please sir! Selfie!" Ta dauke su hoto, Zeeh na kallon su rintsa idanun ta tayi tare da bude su. Juyawa tayi ta bar gurin. Wayarta ta ciro tare da kiran Baby. "Hello baby! Ruwan battery nake so, ki turo min da yaron da yayi min aikin Neemrah nan, zai wanke min fuskar wata yarinyar ne yanzun a Mall din Zeemalik!" Katse kiran tayi tare da shiga ban daki ta naushi glass din Bayin, sai da suka jimata ciwo, bayan wani lokaci taji wayarta na tsiwa, dauka tayi tare da cewa."Baby ya iso ne?" Bata amsa tayi sannan tace mata. "Ok bari na turo mishi hotonta, dan ban bar gurin ba sai da na dauka." Bata b'ata lokaci ba ta dauka, tare da tura mata, sannan ta cigaba da kallon kanta a madubi. Hawaye na zuba mata. Zuwa wani lokaci Baby takira ta, sannan tace mata. "Ki fito gaye ya gama aikin shi." Da sauri ta fito daga ban dakin, duk da jinin da yake d'iga a hannun ta, sai da tafita inda taga cunkoson mutane. Ganin yarinyar da ta dauki hoto da Malik ne ya sanya ta jan tsaki, sannan ta ja hannun mijinta, kallon ta yayi cikin tashin hankali yace mata. "Yanzun yarinyar ta daukemu hoto fa! Amma duba kiga har an sami wanda ya lalata mata fuska, wallahi da zan san waye yayi mata haka sai na maka shi kotu!" Cikin kuka ta faɗa jikin shi tare da rungume tana yarfe hannunta, tare da nuna mishi hannun.ko tambayarta bai yi ba suka wuce asibiti. A can aka cire mata kwalaben hannunta, suna zaune ana saka mata bandaje, kawai taga nurse din tana satar kallon Malik, shammatar Malik tayi ta mari matar yadda sai da ta d'ago kanta a zafaffe, tare da kurawa juna ido, cikin masifa ta fara magana. "Dan Ubanki! Mara mutunci mijin nawa zaki zubawa idanu yar iska, dan Ubanki sai na kashe ki, sai naga gatanki a garin abuja." Sosai Zeeh ta kirkiro mishi tashin hankali, wanda yasanya dole ya biya kudi suka bar asibitin, tun a mota ya fara mata fada. Juyawa tayi a zafaffe ta zuba mishi jajjayen Idanunta tace mishi."wallahi matukar ka dage sai ka kula mace nice nan ajalin ta, na rantse da Allah bazan yi kaffara ba"
Daga haka tayi juyawar ta, abin tsoro ya bashi, dan haka bai kuma mata magana ba, bayan watanni suka tafi katagum, da zummar zasu yi kwanaki, dan haka da Malik suka yi tafiyar ya tsayar da kome nashi, kasancewar akwai karamin filin jirgin sama, a garin azare anan suka sauka. Daga nan suka wuce family house din su, lokacin da suka isa gidan, Da kanwar Zeeh suka fara haɗuwa yarinyar karama yar shekara goma sha biyu, da gudu tazo ta rungume Malik, kawai Zeeh ta fincike yarinyar ta makata da bango sai da jini ya fito ta bakin yarinyar da hancinta. "Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun! Abinda Malik ya iya furtawa kenan yana kallon Zeeh wacce sam haka bai dameta ba, sai ma kara fidda idanunta bada take waje, cikin gidan ma'aikatan suka shiga tare da gayawa Mahaifiyarta abin da Zeeh tayi, cikin tashin hankali mahaifiyarta ta fito ganin halin da Kubrah take ciki ya birkita mata hankali, bakinta na rawa tace."Zeenah me kika aikata kanwarki ciki daya kika mata iri dukar zaki kasheta ne? Me ta ci miki?"
"Mom mijina ta rungume fa! Taya zan bar.." a sukwane ya rufe mata baki, sabida ya fahimci Tabbas zata iya fadar kome! Daukar yarinyar Mahaifiyar ta tayi ta kalli Zeeh tace mata. "Sabida namiji kike daki kanwarki ciki daya! Wannan da kika aikata ya tabbatar min, da zaki iya aikata kome sabida namiji, hmm AM so sorry, ki shirya indai namiji ne, sai ya kai ki ya baro." Daga haka suka wuce da Yarinyar asibiti, sannu a hankali abinda Zeemalik ta aikata ya watsu a familyn Mai Nasara, haka ya matukar d'aga hankalin yan uwanta da sauran mutanen, ba a gama da wannan labarin ba, aka kirata domin ayi mata fada, har da Malik din. Bayan Babanta da sauran yan uwan shi sun gama mata fada, kawai ta mike zata fita, har ta isa bakin kofar corridon dake part din kakarta, Ayayya kawai taji ana hira a wani daki, lek'awa tayi taga yaran kanen babanta ne, suke hira tare da yaba kyan Malik, tana jin daya a cikin su tace." Wallahi banda Aunty Zeeh tayi mana karfen kafa ai da nayi Crushing guy din nan, ga kudi ga kyau! Uwa uban nasaba, kan bala'i, na mutu da...." Jikinta har wani rawa yaƙe, rufe kofar dakin tayi, ta sami Yarinyar da take wannan maganar ta shake wuyarta, tare da ciro takalmin ta me mugun tsayi ta shiga dukar fuskar yarinyar. Tare da gwara kanta da bango tana fadin." Wallahi sai na kashe duk wacce ta Kuskura ta kalli mijina da sunan Soyayya, sai na hallaka ta, zan kashe koma wacece, tun da na iya nakasa kanwata babu shegiyar da zata shigo rayuwar Zeemalik, ba tare da nasaka ana kashe min yar iska ba. Ku kuma munafukai, sai na illataku, tana gamawa da yarinyar ta koma kan sauran yan matan, suma ta shiga musu duka kamar zata kashe su. Jin ihun su yasa aka zo aka ɓalle kofar, ganin yara cikin jini ya sa Malik kifa mata Mari, sai da ta fadi kasa." Kina hauka ne? Kashe su zaki yi?" Cikin kuka ta kalle shi tana faɗin." Eh nayi hauka! Na haukace akan ka, wallahi zan iya kashe duk wacce tace tana sonka. Don Allah ka rufa min asiri karka min kishi ka zama nawa Ni daya, karka raba mana kai da wata mace." Ta faɗa cikin shashekar kuka. Duk da laifin da ta aikata babba ne, bai hana mutane jin tausayin masifar da ya same ta ba, amma ban da mahaifinta, domin kuwa kallonta yayi cikin nutsuwa sannan yace mata."ince namiji kika zab'a? Ba dai akan namiji zaki iya aikata kome ba, toh kije na sallamawa Malik ke! Karki kuskura ki kuma takowa gidan nan, shi kam bazan iya dakatar dashi ba, sabida akwai hakkin mahaifin shi a cikin gidan, amma ke na cire hannuna akanki, bana kaunar na kuma ganinki! Kije kome da lokacin sa! Wannan lokacin naki ne hmmm! Lokacin mu yana zuwa" Fadawa jikin Malik tayi tana kuka, me tsumma ruhi da gangan jiki, tare da rike Hannun Malik. Shi kan shi tausayi take bashi, dan haka yaja hannunta suka bar gidan baki daya.
........ Koda suka dawo Abuja ta jima tana cikin damuwa, kishin Zeemalik, takai ko kawarta Baby bata tab'a ganin Malik ba, amma zata saka tayi mata aiki akan Malik, dake ita baby ba namiji bane a rayuwarta shi yasa bata tab'a damuwa da son sanin mijin kawarta ba. Shekara daya kacal, amma Zeeh tayi yan aiki sun kai goma sha biyar, sabida kawai kar su gan mata mijinta, yasa take Korona su, ko kuma idan kika fito bazata Malik ya ganki, toh kafin ki bar gidan sai ta miki mugun duka, bayan ta watsa miki ruwan zafi a fuskar da ta kalli mijinta, sannan tayiwa yar aiki barazanar sai ta kashe ta har lahira, haka suke barin gidan cikin tsoro da tashin hankali, bayan wasu watani, suka fita ita da baby babban damuwar zata duba Mall ɗinta ne, daga nesa ta hango motar Malik wanda aka saka Malik444, a jikin Number motar, tsayawa suka yi ta fita, shiga tayi gurin cin abinci ne ya hadu gurin, a hankali ta nufi inda ake sayar da abincin tayi odar su, ba tare da taji kome ba, ta dauki abinci tare da hadin kome ta saka aka juye mata a tiren, tana zuwa ta sami dai-dai inda matar take ta juye mata, gabaki daya akanta....
#Zeemalik...
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/P91R2J0ttab
Chapter 4
Na MrsUsman400
"Zeeh!!!" Malik ya daka mata tsawa, fesss ta d'ago tare da zuba mishi ido, cikin ko in kula. "Malik! Kai nawa ne! Kuma duk duniya babu macen da ta isa ta kawo min Shamaki da kai ba tare da na illata ta ba." Ta faɗa tare da yanke hannun matar, sai da jini ya fesu a fuskar shi. A razane ya kalle ta, ta kuma kai hannun zata yanki matar, ya rike hannun ta, idanun ta sunyi jajjur. Cikin kuka tace. "Me yasa kake son juya min baya, iyaye na sun rabu dani sabida kai, kai kuma kana abun da ranka yake so, wallahi gwara na mutu akan na ganka da mace!" Ta juya da mugun gudu zata fita ya riko hannunta, yana girgiza mata kai. "wallahi kasuwanci muka zo yi anan, wallahi bakuwa ce daga Ghana, ki yarda dani Matar Malik!" Kallon matar tayi, wacce ake shirin fita da ita, sannan ta mai da kanta gurin Malik, tace. "Ka bata hakuri! Ba laifina bane sonka ne sanadi" daga haka ta riko hannun shi baki daya ta manta da kawarta Baby, wacce tayi mutuwar tsaye sabida ganin haduwar Malik. Dole Zeemalik tayi hauka,Malik namiji ne irin wanda ake nima, amma ita bata ra'ayin namiji da koda tsiya da bala'i sai ta ji yadda yake.
Tab'e baki tayi, taje ta shiga motar ta, tabar Unguwar. Koda suka shiga gida. Kwace hannunta tayi, ta haura sama da mugun gudu, tana shiga d'akin ta ta faɗa kan gado ta fara kuka, kamar mahaukaciya. A sanyayye ya biyota zuwa dakin, yayi rarrashin duniyar nan amma taki fahimtar zuciyarshi, karshe zuba mata ido yayi. Tana tashi ta zuba mishi jajjayen Idanunta, tana jan hancinta tace mishi." Kayi min alqawarin ba zaka tab'a min kishiya ba. Kai ka hana ni maganar Haihuwa, kuma yanzun." Rike hannunta yayi, cikin nutsuwa yace. "Ba zan taba barin ki ba, wallahi ba zan tab'a kallon wata mace da sunan halitta ba, wallahi duk matan duniyan nan maza nake kallon su, ina sonki my everlasting! I love you! More than I luv my self, kin yarda dani." K'amk'ame shi yayi tare da zubda kwalla, ta d'ago. "Insha Allah nice matar ka a gidan duniya, nice matar ka a gidan lahira." Had'a goshin su yayi a hankali ya daura bakin shi akan nata, daga nan baka jin kome.
***
Bayan shekara biyar...
A cikin wannan lokacin ba karamin ɓarna, Zeeh tayi ba. Ba tare da sanin Malik ba. Ta nakasa yan mata tare da salwantar da rayuwar wasu, kawai akan mijinta, takai Zeeh idan Malik zai fita tana saka masu bibiyar shi. Saboda tsaro. Sau uku yana kawo mace sakatariya, ana samun an watsa musu ruwan battery ko kuma a buge su a mota, haka yasa ya daina ajiye mace a Office din shi saboda tsoron kar a kashe su. Yau cikin nutsuwa take shiryawa tare da saka wasu manyan white gold, sabida bikin Mahnoor. Duk da ranta baya son zuwa amma bata da yadda zata yi, tana gamawa ta dauki key din motar da ya saya mata last week. Rolls royce wanda kudin shi ya kai tsabar Naira miliyan dari da hamsin, tare da jin kanta take tafi kowa sa'a. A hankali ta shiga motar tare jan motar tana wani lumshe idanunta. Wakar Joe, wanda yayi i wanna know. Tana tafiya tana murmushi ita kad'an ta. Har ta isa gidan surukarta inda ake bikin Mahnoor. Tun da ta shiga gidan ta samu anata. Tun da ta shiga ta fara b'ata rai. Sabida haduwa da tayi da wasu cousin sisters din Malik, tuni ta shiga cikin gidan. Tana ji kamar ta juya ta bar gidan, tun da ta shiga ta gaida Hajiya Azizah. Ta fita sannan ta kira Baby tana faɗin. "Yaushe zaki tafi Charanchi?" Shiru tayi sannan tace mata. "Toh kawai kice mishi yayi min ma gabaki daya! Yadda babu wata mace da zai gani kome ya faru."
Tun da ta gama wayar take zaune can Baby ta kirata, sun yi magana kafin tace mata toh gata nan zuwa. A ranar ta bar garin abuja, suka nufi can katsina inda aka yi mata aikin da bokan da kan shi sai da yace mata. "Kina da sa'a! Amma kuma karki sake da cewa wani abu bazai iya faruwa ba! Domin a cikin Yan matan da kika kashe Akwai wacce taso mijinki kamar zata yi hauka, kuma kin kasheta tana cikin soyayyar mijinki, ban san me zai faru ba, amma ki kiyayye dalilin da zai kai kome ya faru. Gashi nan ki ciyar da shi, karki bari wani ya wuce kwanakin da zasu zo nan gaba. tsakanin shi da mace, sai dai ya mata kallon da zai yiwa madubi."
Daga haka ya sauke mishi kuɗi me mugun yawa. Sannan suka bar gurin shi. Kallon ta Baby tayi sannan tace mata. "Amma Zeemalik! Ina ga ya kamata kiyiwa kanki fada! Sabida namiji da kike kishin sa, shi fa ba damuwar shi bane fa, idan har Allah ya nufa zai kara au.." tasss ta Wanke Baby da mari tare da faɗin! "Zan kashe ki! Kuma na kashe banza, ni kike kirawa kishiya wallahi ahir dinki, sai na salwantar da rayuwar ki a banza. Yar iska, dan Ubanki waye gatanki a garin Abuja ban dani, karki fara.". "Allah ya baki hakuri amma ki sani gaskiya na gaya miki, kina shirinki Allah yana na shi, kuma nashi ce gaskiya. Wallahi naji tsoron maganar cewa akwai wacce taso mijinki kamar zata yi hauka, Neemrah ce, innocence lady, Amma Kika zubda jinin ta, don't forget Allah bazai bar hakkinta ba, wallahi kiji tsoron." A fusace, Zeeh ta shake wuyarta kamar zata kasheta. Tana faɗin."wallahi baki isa ba, ko Neemrah ce ta dawo sai na kuma kasheta har lahira, zan kashe ki." Tarin da Baby take yasa Zeeh ta Kyaleta tare da juya mata baya, tana share kwalla. Tun daga ranar Zeeh ta rabu da Baby duk yadda baby naso su shirya fir taki, dan dole ta Kyaleta. Bayan gama bikin Mahnoor. Ranar da taje gidan Mahnoor din dan ganin d'akinta, anan ta haɗu da wata yarinya tana kallon album din bikin, kawai idanun ta ya sauka akan fuskar Malik, wanda yake sanye da farar shadda na ranar daurin auren, ta fara zuzzuta kyan shi, da tsarin shi, lumshe idanun ta tayi, tare da bude shi akan Yarinyar, bata son barwa Mahnoor abun kunya ya sata tab'a. Tab'a wasu noct da ake daura karfen labulen kawai ta zuba a bakinta,. Ba tare da ta zuba yawan su ba, aikuwa suka tsaya mata a makogaro, ta fara kakari tare da aman jini. Daga wuyarta. Kuma bata fasa kallon yan matan ba, idanun ta za zubda kwalla.
Cikin tashin hankali Mahnoor takira Malik aka nufi asibitin Maman su wanda yake nan Gwarumpa, dakyar aka ciro mata abinda ta had'iye.
Tun daga lokacin, take mugun gudun zama cikin mutane, musamman wanda tasan akwai yan matan da suke yan uwan da Malik, Katagum kan ta ajiye su dan ta manta dasu. Ma kawai rayuwarta take da malik.
Bayan wani lokaci me tsayi Hajiya Azizah ta fara damun su da maganar Haihuwa, tun tanawa Malik har ta kai ta kira Zeeh take tambayarka ko lafiya akan rashin haihuwa akan indai suna da matsala su magance idan kuma babu toh kuwa Malik zai auri Zinnirah Kanwar Neemrah, a ranar Zeeh kamar zata tayi hauka da tasaka Malik a gaba da kuka, babu shiri suka fita kasar India, inda aka tabbatar musu da mahaifar Zeeh baza ta iya daukar nauyin ciki ba koda kuwa ya sati biyu ce balle wata tara, wannan yanayin da ta shiga yayi masifar jijjiga ta, haka yasa ta zubawa Malik ido, bata ce kome ba. Yana tab'ata zata fashe da kuka. Cikin karfin hali ya rungume ta tare da cewa. "Zeemalik! Har abada bazan miki kishiya ba, kin sadaukar min da kome, kin rabu da iyayenki sabida ni, yau gashi sabida ni kin rasa mahaifar ki sabida ni, Zeeh idan ban cika miki alqawarin ki ba ni ba d'an halak bane!" Da wannan yayi ta lallashinta har tayi shiru, tun kafin ta dawo India ta nimo Baby. Aikuwa ta mata aikin da aka rufe bakin kowa.
A haka suka ci-gaba da tafiya har zuwa yanzun shekarun su takwas, kullum idan zai tafi aikin shi wani gari sai ta ta gaya mishi kar ya manta da batun alqawarin da ya daukar mata, kuma zai gaya mata, yana sane da ita, idan ka cire ragwanta da take nuna mishi Zeemalik bata da Matsalar kome. Da wannan suka rabu ya nufi Gombe.... kome me zai faru..
_Sorry_
*_KOME DA LOKACIN SA_*
https://my.w.tt/Z6IOv0Wjvab
Chapter 5
Na MrsUsman400
🤪 You guys waiting for next page..
12:30 pm in Gombe..
Ina dab ina shirin haɗa kayana, dan na gama, aikina na safe zan koma asibitin kudin da nake musu aiki. Sauri nake dan naso na makara, ba wani shekaru ne dani ba, dan ban wuce ashirin da ba.Sai dai ina da tsayi kuma siririya ce ni, amma kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, domin ina da halitta sama da kasa, duk da kuwa na kasance mara auki( sirara ga book din ku) eh toh dayawa badan ina da boons da bom-bom ba, toh abin da mutane zasu kirani shine muciya da zani, sai Allah ya tarfawa gari na nono.
Mahaifina da Mahaifiyata Fulani ne, amma abin takaici Baba bai da zuciyar fulani, mutanen da aka san su da niman na kansu, toh babu bai dashi, kuma baya fatan fita ya nima.
Kyau a gurin Mama na dauko shi, domin kyakyawa ce na gaban kwantaccen, sabida kyan da take dashi a lokacin yan matancin ta, yasa manema suka ja baya da nimanta wai cewa suke mace me kyau dayawa hatsari ce a cikin mutane. Shi yasa nima kuma dayawan mutane suke gaya min cewa na cika kyau, da ace ban da kyau sosai da tuni na sami abokin rayuwa. Wasu suna danganta haka da cewa, ai sabida kyauna yasa bakin aljani ya aureni. Ban tab'a yarda da hakan ba sabida nayi imani da wanda ya saukar da Alqur'ani, kuma nayi karatun akan addini, sosai shi yasa babu abinda mutane zasu gaya min naji d'acin shi. Ina fitowa aka kawo wani mara lafiya, wanda aka buge shi, tsoho ne sosai. Ya tsufa kuma gashi yaji rauni jini na zuba. Kallonsu nayi zan wuce Sister Karimah tace min. "Inayat! Ina zaki taimaka ma kafin likita yazo hatsari ce!" Ban kalleta ba nace mata. "A dokar aikin mu, muna bukatar hukumar yan sanda, dan haka kuyi kokarin ganin sun zo sai mu duba shi dan bazan kuma shiga irin case din Mr Alex ba" ina fadar haka na juya na fara sign. "Don Allah baiwar Allah ki duba shi mana sai kace ba musulma ba." Juyawa nayi na kalli mutumin da yake wannan maganar nace mishi. "Aikina hurumina ne, dan haka idan wani abu ya biyo baya yanzun sai a iya juya min baya don Allah ka barni akan aikina kuyi report wa yan sanda Ni kuma zan tsaya na tabbatar an kula da lafiyar shi." Ganin da gaske bazan duba su ba har na fara barin sallawun idan sun kawo d'an sanda Karimah ta duba su, ashe mutumin ya fita can sai gasu da wani mutum ban juya ba, sai dai kuma naji yana cewa."Yallabai gata nan wallahi taki duba bawan Allah nan fa!" Juyawa nayi idanuna ya sauka akan shi, kauda kaina nayi cikin sauri na dauki jakata ina warware nikkab dina zan saka yace min."ke wacce irin jahila dabbace mara amfani a cikin al'umma! Ke wata irin jaka ce da bata san me take yi, a kawo mutum cikin bukata kice bazamu duba shi ba, sabida jahilci ya miki katanga da saninki! Wawuya jaka, baza a kawo d'an sanda ba, sakarya kawai." Kallon shi nayi daga sama har kasa, sannan nace mishi. " A duk inda zan mu'amalanci mutane, nakan musu duba biyu ne! Na farko waye yake maganar nan! Na biyu suturar jikin shi, daga nan sai na kai shi ajin karshe bani da lokacin ka nayi maka Uzuri! Baka san rashi ba! Samu kasani a rayuwarka, tunda haka ya nuna daga jikinka. A kan aikina nake zagina! Nayi maka Uzuri, sister Karimah don Allah ki tabbatar an kawo yan sanda cikin case din idan kika sake wani tsautsayi yaja ki, toh na dai gama nawa.!" Na saka kai zan fita ya finciko ni, yana kallon fuskana. "Albashin wata biyun da kike dauka shi ne nake biyan me yin aikin ban ruwan fulawa a gidana, ni kika ce kinyiwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 22