duk abunda nayi maka kai ka siya, haba sekace baka da zuciya, ko baka gane magana"
Shiru yayi kawai yana kallonta yadda take ta masa masifa, shi yaga tana magana ma se yaji daɗi a ransa, dan yaga ta rage yawan kukan da take yi.
Ga mamakinta murmushi yayi maimakon taga yaji haushi.
"kawo man in tayaki shafawa" yai maganar yana ɗaukar robar man, ƙwacewa tayi tace
"bana so na gama"
Yusuf yace"Shikenan bari in baki guri kisa kaya"
"inma baka bani gurin ba baze hanani sa kayana ba"
Yayi murmushi ya miƙe cike da jin daɗin yasa ta magana, bayansa tabi kallo yana fita ta ajiye abunda ke hannunta ta shiga goge hawayen da ita kaɗai tasan dalilinsu.
Doctor Sufyan yana Office ɗinsa, yana jiran lokaci yayi ze shiga tiyata, wayarsa yaji ta fara ringin, ya tsaya ya ɗaga tareda yin sallama.
"Sufyan ne?"
"Eh nine"
"ina son ka kasa kunne ka saurareni dakyau, dukda nasan baka san dawa kake magana ba, hakan ya faru ne sakamakon sanin wanda kake maganar dashi a gurinka bashi da amfani, ina son ka saurareni da kyau kaji abunda zan gaya maka, kana jina ko?"
Sufyan yace "ina jinka"
"kamar yadda aka baka kwangilar sake kwantar da Daula, aka baka miliyoyin kuɗi akan karya warke, kuma kayi dan tuni wani percentage ya shiga hannunka, to nima aiki nake son kayi min, niba kwantar da Daula nake so kayi ba, kawar da Daula nake son kayi!!!"
Miƙewa doctor Sufyan yayi tsaye ya shiga waige waige karya je wani yaji abunda ake faɗa masa a waya, cikin rawar murya yace "amm.. Ban gane me kake fada ba fa"
"ƙarya ka keyi ka gane, kuma kaji me nace tunda ka iya karɓar kuɗi kake bashi wrong treatment, to zaka iya karɓar kuɗi ka kasheshi, likita ne kai babu me zarginka, tunda kowa yasan condition ɗinsa yayi worse, bazance ga abunda zan bi yaka ba, sedai da kanka nakeso ka yanke abunda zan bi yaka "
Wani wahallalen gumine ya dinga ratsowa Sufyan, gumi yake ji har tsakanin cinyoyinsa, yace " Amma kisan Alhaji Daula hatsari ne, dole se anyi bincike akan gawar sa, don a tabattar da abunda ya kashe shi, idan aka ganoni fa, ina da iyali da ƙananan yara nasan kasheni za'ayi, Daula babban Attajiri ne"
"meye marabar abunda kake masa yanzu da wanda nace kayi masa, sanin kanka ne wrong treatment ɗinma ze iya kasheshi, baka da damar cewa ba zakayi ba, saboda na maka tarko ta ko'ina, ina da duk yadda akayi ka karɓi kuɗi kake bashi wrong treatment, duk wata hujja daza'a kamaka ina dashi, idan kuma naga dama zan saka ɗauke ɗaya daga
'ya' yan naka ko kayi ko kuma ransa ya salwanta, zaɓi ya rage naka, sannan idan kaga dama ka gayawa wani"
Ƙit aka katse kiran, gaba ɗaya doctor Sufyan yaji kamar an zare masa laka, jikinsa se rawa yake ya duba wayarsa yaga anyi hiding ɗin lambar, dan ko unknown number be fito ba, duk sanyin Ac dake office ɗin shi gumi yake, kamar wanda ya tuƙa tuwon gidan biki a tsakae rana.
Yau da wuri Yusuf ya shirya, dan zebi ɗan megari kasuwa, ɗan megarin shima matashi ne be kai Yusuf ba, a bayan gidan megari nasa gidan yake, da matarsa da 'ya' yansa shida.
Har Yusuf ya gama shirinsa, aka kawo musu Abincin safe Widad bacci take, a hankali ya ƙarasa gaban katifarta ya janye bargon jikinta, bacci take hankalinta kwance, se yarintarta ta sake fitowa ta ƙara kyau a idon Yusuf, yayi shiru yana kallonta.
A hankali ya ɗan daki pillow ɗin da take kai, amma bata motsa ba, ya sake taɓa pillow amma still bata motsa ba, hannu yasa ya ɗan daddaki nata hannun, kamar me tashin ƙaramin yaro, juyi tayi amma taƙi buɗe ido.
"Widad" karo na farko a rayuwarta data ji ya kira sunanta, taji zuciyar ta ta buga da ƙarfi, ta buɗe ido ta kalle shi
Yace "ga breakfast an kawo karya huce, kuma inason zan fita ni"
"shine zaka wani durƙuso kaina haka? Kamar zaka shige cikina"
"ke komai nayi miki lefi ne? To sorry tashi karya huce kinji gimbiyar..
Kallonsa take taji meze ƙarasa, maimakon ya ƙarasa se yayi murmushi yace "tashi kije kiyi brush, muci Abinci "
Ta miƙe ta ɗau brush tayi waje, Yusuf ya gyara mata shimfiɗa, ya gyara ɗakin.
Widad ta fita tsakar gida, gwaggo tace "Amarya ina kwana"
Widad tace "lafiya ƙalau"
Gwaggo tace "Alhamdilillah ya ƙarfin jiki?"
"Naji sauƙi"
Gwaggo tace "to madalla"
Hari ta ƙurowa Widad ido tana so tayi magana, Widad tace
"idan baki dena kallona ba, sena saka butar hannuna na ɓallo miki wannan haƙorin da yake leƙowa idan kina magana"
Hari tace "ke hudas kike ko wudas, yau dai ban kulaki ba balle ace na shiga harkarki"
Widad ta Harareta ta wuce banɗakinta.
Data fito ta manta da batun Yusuf dake jiranta, ta tsaya gurin da take leƙen zomaye.
Seda tayi me isarta, sannan ta koma ɗaki.
seda taga Yusuf sannan ta tuna ashe ita yake jira suci Abinci, yace "naga kin daɗe?"
Kai tsaye tace "kallon zomaye nayi" , ta ajiye kayan brush ɗinta, tazo ta zauna ta buɗe kwanon farko, dakakken ƙuli ƙuli ne a ciki, ta rufe ta buɗe ɗayan dafaffen dankalin hausa ne a ciki da ɓawonsa da komai manya guda uku.
Ta kalli Yusuf tace "meye wannan?"
"Dankali" ya bata amsa
"kuma a haka? Ta yaya za'aci"
Yusuf yace "ga mahaɗin nan ƙuliƙuli a wannan kwanon"
Widad tace "ta yaya za'aci wannan abun ba tea?"
Yusuf yace "seki kora da ruwa" yai maganar tare da fara ɓare dankalin.
ta zuba masa ido, ya ɓare tsaf ya yayyanka shi a kwano, ya ɗebo ruwa ya ajiye mata yace "bismillah"
Tsayawa tayi tana kallonsa kamar wata sokuwa, ya ɗakko ɗaya ya dangwala da ƙuli ƙuli ya kai bakinta, ɗauke kanta tayi tasa hannu ta karɓa tasa a bakinta.
Ba zata ce babu daɗi ba, sedai gurin haɗiyewa ne daƙyar take yi, dan kasa haɗiyewa tayi seda ta haɗa da ruwa.
Dan haka shima ba taci dayawa ba tace ita bazata iya cin wannan abun ba, shaƙe mata wuya yake.
Yusuf ne yaci sauran, sannan yayi mata sallama ya tafi.
Sufyan abun duniya ya dameshi, ya rasa inda ze saka ransa, ba ƙaramin hatsari bane kashe shahararren mutum kamar Daula, amma kowa se saka rayuwarsa yake a hatsari saboda suna taƙamar suna da kuɗi, shiba abun ya kaisu gurin 'yan sanda ba, shi ze kwana a ciki.
Gaba ɗaya daren nan yakasa bacci, sedai juyi dafa da Asuba aka kuma sake kiransa, bashi da zaɓin daya wuce ya amsa wayar.
"baka da isasheshen lokacin ɓatawa gurin aiwatar sa wannan aikin, kana da yau zuwa gobe in Allah ya kaimu ne kawai, idan baka yi ba ni zan aikata maka abunda nace"
Aka katse layin, Doctor Sufyan yayi jifa da wayar ya dafe kai, matarsa ta lura da yana cikin damuwa ta tambaye shi ko lafiya, yace mata babu komai.
Widad bata taɓa shiga damuwa ba, tsawon lokacin data ɗauka tana rayuwar kaɗaici a rayuwarta se wannan karon, tunda Yusuf ya fita be dawo ba taji gaba ɗaya duniyar ta mata faɗi, gashi ita bata saba da kowa ba se shi, seta ji ta wani iri kamar ita kaɗaice a duniyar, koba komai ganin motsinsa yana rage mata damuwa.
Yau wuni guda tana ɗaki, ba wanda yake shigowa inda take, saboda bata da fuskar daza'ayi mata hakan, bayan tayi sallar la'asar yunwa ta isheta ta fito tsakar gida.
Gwaggo tace "Amarya lafiya dai ko?"
Widad tace "Naga har yanzu Yusuf be dawo ba kuma ni yunwa nakeji"
Gwaggo tace "Allah sarki, yau Harice da girki bata aiko miki da Abinci ba kenan"
Widad tace "kota aiko ba zanci ba, dan ƙazama ce"
Hari dake salla a tsakar gida ko sallamewa ba tayi ba tace "jar'uba kekam anyi mara albarka, nice ƙazamar?"
"Eh kece ƙazama, kalli zanin jikinki kalli faratanki, hijjabin jikinki ma me datti ne, sekiyi abu ki bani inci, an gaya miki komai nake ci?"
Wato Widad sam ta dena ragawa Hari, gwaggo tayi murmushi tace "Yanzu to me zakici?
Widad tayi shiru ba tace komai ba, gwaggo tace "Akwai Furar megari dana dama, bari in ɗebar miki"
Widad tace "Nagode"
Hari tace "Furar malam ɗin zaki ɗiba ki bata? Lallai Yaya akwaiki da neman gindin zama"
Widad tace "Eh ita za'a ban, ba zanci Abincinki ba"
Gwaggo dai ba tace komai ba, ta ɗebowa Widad fura a kofin silba ta bata, ta samu guri ta zauna tana sha.
Furar tayi zaƙi zau da zumar da'aka zuba a ciki, tana cikin shan furar can seta miƙe tsaye, gwaggo tace "kin ƙoshi ne?"
Widad tace "A'a Yusuf na ragewa"
Hari tace "Ohh ni jikar Hama, ji wata fitsara take cewa ta ragewa mijinta abu"
Wasu matane suka shigo su Uku, ɗaya 'yar babba biyu kuma 'yan mata da sallama suka shigo, Hari tace
"Ahh marabanku da dawowa, wai an sha suna"
Ɗayace ta kalli Widad tace "Hari wace wannan?"
Hari tace "wasu baƙine mukayi"
Ɗayar tace "kalleta kamar balarabiya"
Widad bata tanka musu ba ta koma ɗakinta.
Sukam bajewa sukayi a tsakar gida, ɗayar itama matar megari ce hansai, se 'yan matan Hindu da Hanne, suma' ya'yansa ne sunje wani ƙauyene, inda 'yar megari take Aure ta haihu.
Se bayan la'asar Yusuf ya dawo gida, kallo ɗaya zakayi masa kasan a gajiye yake, ya gaisa da mutanen gidan ya shiga ɗakinsu.
Ba sannu da zuwa bakomai Widad tace "Shine kaƙi dawowa se yanzu?"
Yusuf yace yanzun ma tun ɗazu na taho, akwai nisane sosai.
Ya ajiye kayan hannunsa, yaje yayi wanka, a ɗaki yayi salla saboda gajiya ya nemi guri ya kwanta yayi shiru.
Widad tace "to ni dai gaskiya ka dinga dawowa da wuri, kawai seka tafi ka barni nikaɗai, gaba ɗaya nagaji"
Yusuf ya kalleta yace "Aikin me kikayi kika gaji?"
"Aikin zama ba abunda nake, ba kowa a ɗakin nan seni kaɗai"
"Amma ai da mutane a gidan, seki fita kuyi hira"
"Ni gaskiya dana fita wannan me haƙoran take min rashin mutunci, nikuma ramawa nake"
Yusuf yace "Kidinga ƙyaleta, kinga babbace ba sa'arki bace ta girmeki"
"da alama ka manta Widad Nasir Daula ce ko?"
Yusuf yace "ya za'ayi na manta nina isa? Yau ba'a kawo komai bane yunwa nake ji"
Widad ta taɓe baki tace "wannan ƙazamarce tayi girki, ni kuma nace ba zamu ciba, shine Mama ta bani furar mijinta"
Buɗe baki Yusuf yayi yace "ba dai ce mata kikayi ƙazama a gabanta ba?"
"idan na gaya mata zata cinye nine?"
Yusuf ya dafe kai, ita Widad a rayuwar ta bata san kara ko alkunya ba sam.
Ta ɗakko kofin furar nan tace "gashi nasha na rage maka"
Yusuf yace "dagaske ragemin kikayi?"
"is there anything special, dan na rage maka?"
Yusuf yace a"a a ransa kuma yace "lallai kin damu dani"
Yusuf yace "Naje kasuwa, naga abubuwa ana saye da siyarwa ba laifi, ɗan megari ze aran kuɗi, inga me zan fara siyarwa, ranar daba kasuwa kuma naje wani gurin inga me zanyi"
"to duk meye na wannan wahalar?, naga dai barin gurin nan zamuyi"
"A'a yakamata in koma ciyar dake da kaina, da duk buƙatunki be kamata mucigaba da ɗora musu ɗawainiya ba, nauyinki a kaina yake yanzu"
Kallonsa tayi tace "don't bother yourself, wannan fa ba Aure neba"
"meye inba Aure ba?"
Tace "Shiri mana"
Yace "Ba ruwan Allah da shiri, kuma koda shirin ne aini yakamata in kula da Gimbiya ta"
"karka ƙara cemin gimbiyarka"
Yusuf yayi murmushi yace "Lokacin da muna gida gimbiyar Daddy ce, yanzu kuma da muke nan ba wanda kika sani seni, dan haka gimbiyata ce"
Tsaki tayi ta miƙe daga inda take zaune, Yusuf yace "Komai naki me kyau ne Widad"
Ko Kallonsa ba tayi ba tayi masa shiru, yace "ga Alƙawarin da nayi miki, na samo comb da ƙyar a kasuwa, yaushe zamu gyara gashin namu?"
Ficewa tayi daga ɗakin ta barshi, shi kuma ya dinga murmushi ganin takaici ya hana ta magana, Yusuf yace da haka da haka gimbiya"
Sufyan fa hankalinsa gaba ɗaya ya gama tashi, ya hanga yaga bashi da wata mafita data rage masa banda ya aikata abunda akace, ya haɗa allurai a cikin syringe ya zauna ya zuba musu ido, gabansa nata dukan biyar biyar, kiransa akayi a waya, hannun narawa ya ɗauka
"Ka shirya aiwatar da aikinne ko kuwa?"
Cikin jan numfashi Sufyan yace "Eh na shirya"
"shikenan, ina jiran sakamako a yau, ka duba wayarka zakaga Alert ɗin kuɗi"
Sufyan bece komai ba ya ajiye wayar yana yakice gumi.
Zuwa yanzu Widad ta fara dangana, ta ɗan fara sabawa da halin data tsinci kanta a ciki, Cikin dare Widad tana bacci tayi juyi, hasken farin wata ya hasake ɗakin, ta hangi Yusuf a zaune akan shimfiɗarsa yayi tagumi,
Da alama tunani yake.
A ranta tace 'Ashe shima yana damuwa, amma ya dinga basarwa yace nize hanani kuka'
"wai tunanin mekake?"
Firgigit ya dawo hayyacinsa, yace "idonki biyune?"
"A'a mafarki nake na maka magana"
Yusuf yace "hmm ba tunani nake bafa, cinnaka ne ya cijeni na kasa bacci"
"yaushe ka fara ƙarya?"
"dagaske nake" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje, Alwala yaje ya ɗauro yazo ya tada salla, Widad kam baccinta ta koma.
Yusuf yana cikin sallar ne yaji A gigice Widad tace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah Daddyna"
Ta miƙe da gudu tayi hanyar waje
(Up Up masoya littafin AƘIDATA, Comments ɗinku na matukar ƙayatar dani, shike bani ƙwarin gwiwa nayin posting, Allah ya bar ƙauna 😍 😍 😍)
Share, share and share please 🙏 🙏 🙏
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
NOT EDITED
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 36_37
Riƙeta gam Yusuf yayi, yayin da ta cigaba da fizge fizge tana kuka, a hankali Yusuf ya zame ya zauna da ita a jikinsa, ya toshe mata baki, saboda dare ne nan da nan sautinta ze iya cika ko'ina.
Yusuf yace "Widad, ki nutsu mana darene yanzu karkisa hankalin mutane ya dawo kanmu, mafarki kikayi fa"
Girgiza masa kai ta shiga yi, cikin kuka tace "is not just a dream, wani abu na shirin faruwa da Daddyna, ka ƙyaleni inje in ganshi, wani abu ze sameshi"
"yanzu idan kika tafi ina zaki? Daddy Addu'ar mu yake buƙata, tun ɗazu nan salla nake ina mana addu'a muda iyayen mu, Insha Allah babu wanda ze iya cutar dasu, kuma Saleh ya cemin ya gaya masa muna nan tare, kidena kuka"
Girgiza kai take tana kuka tace "Daddy na, shikaɗai ya ragemin bani da kowa, bana son in rasa Daddyna, idan na rasa Daddy babu sauran me ƙaunata sedai dukiyar daze bari, wayyo Allah Daddyna, ya Allah secure my Dad, Allah yasa in koma in tarad da kai a raye"
Gaban Yusuf ne ya faɗi, ya tuna abunda Saleh ya gaya masa game da mahaifin Widad.
Kuka take sosai jikinta har rawa yake, ga wani irin gumi daya rufe ta, ɗora hannunsa yayi a saman ƙirjinta, se bugawa zuciyarta take da ƙarfin gaske.
Yusuf ya shiga karanta mata dukkan Addu'ar da tazo bakinsa, a hankali zuciyarta ta rage bugawa da sauri da sauri, can kuma bacci ya ɗauketa, ta shiga sauke Ajiyar zuciya.
Yusuf ya miƙe a hankali da ita, ya kaita kan katifarta ya rufe ta da bargo, ya koma ya sake alwala ya cigaba da sallar sa.
Alhaji Musane keta sintiri a cikin ɗakinsa, se safa da marwa yake ya kai gwauro ya kai mari, ya rasa abunda yake masa daɗi, sosai maganganun Saleh sunyi tasiri a zuciyarsa, sosai zargi ya ɗarsu a ransa cewar a cikinsu akwai wanda ya zame yake shirin cin amanarsu, kamar yadda ya zame a baya yaso ya haɗa kai shida Alhaji Bukar.
A fili ya furta dole "inyi wani abu akai"
Juyowa yayi yaga Nurat a tsaye a ƙofar ɗakinsa da tray ɗauke da kayan marmari a ciki, a fusace yace "dan uwarki laɓe kika koma Yimin ko?"
Cikin dakewa tace "meyasa zan maka laɓe kuma Daddy, tun ɗazu nake sallama amma baka amsa ba"
"Kuma shine seki tsaya ki laɓe?"
"Daddy bafa laɓewa nayi ba"
"zoki ajiye kayan nan ki fita ki ban guri"
Nurat taje ta ajiye masa tray ɗin ta fita, gaba ɗaya Nurat ta lura mahaifinta a kamar a ruɗe yake, akwai abunda yake damunsa, zata so sanin abunda yake damunsa, dan wataƙila yana da alaƙa da harƙallar da suke ƙullawa akan Alhaji Nasir da iyalansa.
Bayan sallar Asuba yau a masallaci, Yusuf ne ya tsaya ya ɗanyi wa mutanen ƙauyen Nasiha akan neman ilimin Addini, ta hanyar janyo musu ayoyi da hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, be fito yace musu basu da ilimi ba, amma a cikin bayanin da yake musu ya kawo musu misalin yadda mutum ze kawo raka'oin daya rasa idan yazo bin jam'i, nan suka dinga gano irin tafka tafka da kwaɓar da suke yi.
Wani mutum yace "gaskiya Malam Yusufa munji daɗin wannan bayanin naka, danni harga Allah na ƙaru da abubuwa da dama, danni wallahi na zata idan mutum yayi alwala in yayi tusa indai ba tayi ƙara ba to bata karye ba"
Na kusa dashi yace "Nikuma wallahi na zata ko sujjada ka samu in ana salla shikenan ka samu salla, dan Allah yakamata ka cigaba da yi mana wannan bayanin idan anyi sallar Asuba ko kuma da daddare mudinga taruwa anan kana ƙara fahimtar damu abubuwa"
Megari yace "hakane kam, Yusufa idan bamu takura maka ba, muna buƙatar hakan"
Yusuf yace "Ai babu batun takura ranka ya daɗe, mafi alkairin mutane shine wanda yasan ilimi kuma ya sanar dashi"
Seda gari yayi haske tukuna suka watse, suna mamakin kurakuran da suke aikatawa a sha'anin addininsu.
Yana shiga gidan yayi karo da wata budurwa tana koro dabbobi daga turke zasu fita kiwo, tana ganin Yusuf tayi turus tana kallonsa, har Yusuf ze wuce tace masa "Ina kwana"
Yusuf yace "Yawwa lafiya ƙalau sannunki"
Yai gaba abunsa, ƙura masa ido tayi harya wuce ya shige ɗakinsu, anan ta tabattar da cewa shine mijin wannan farar matar me gashi.
Da sauri ta koma ɗakinsu, tana kiran "Hindu, Hindu"
Hindu dake sharar ɗaki tace "lafiya kikemin wannan kiran?"
Hanne tace "kinga mijin wannan farar matar nan ta jiya kuwa?"
"me yayi?" hindu ta tambaya
"innalillahi, wallahi ban taɓa ganin namiji me kyau kamarsa ba"
Hindu tace "har Lamiɗon rigarsu gwaggo?"
Hanne tace "wallahi harshi, taɓ bakiga kyau ba masha Allah, ban taɓa ganin namiji me kyansa ba"
Hindu tace "bakiga matarsa bama, fara me kyau"
Hanne tace "dalla wannan da gani bata da mutunci, kinga kallon da tayi mana jiya kamar taga kashi, da gani bata da mutunci"
Hindu tace "ke Hanne karkice haka, aikinga bata sanmu ba"
Hanne tace "ke dallacan Allah yasa in kuma ganinsa"
Yusuf ya shiga ɗaki ya tarar da Widad a zaune, ya kalleta yace "ina kwana?"
Kallonsa tayi kawai ba tace komai ba, Yusuf yace "Munyi magana da ɗan megari na bashi kuɗi, zeje cikin gari ze siyo miki kayan tea da sauran abun buƙata"
Ita dai ba tace komai ba, sema lumshe idanunta da tayi.
"wai meke damunki ne kuma?"
"Bakomai"
"zakiyi wanka ne? Ina son zan fita"
Tace "kaje kawai, zanyi komai da kaina"
Yusuf yace "Aini tsoron fitarma nakeji, jiya da daddare ki tsoratani sosai, kar in fitane kema kice zaki tafi"
Shiru tayi masa ta ƙara rufe idonta, "Widad" ya kira sunanta, a ɗan hasale tace "meye ne?"
"Inaga bari in haƙura da fitar nan, bari inje inyiwa abokin tafiyar tawa magana se in dawo"
"Nifa ban hanaka tafiya ba, ba inda zani jiyanma na tsorata ne mafarkin da nayi"
Yusuf yace "dagaske idan na fita bazaki tafi ki barni ba"?
Ɗagowa tayi tana kallon cikin ƙwayar idonsa, ta jinjina masa kai alamar eh, yayi murmushi yace
"to bari inje in wanke mana kwanuka, in wanke miki banɗaki se in tafi, sena dawo, in a kawo abun karyawa kiyi breakfast ɗinki kawai, base kin ragemin ba"
Yai maganar tare da miƙewa ya fice, ya kwashi kwanukan ya zuba ruwa, Hanne ce ta hango Yusuf da kwanuka, ta taho da sauri tace
"kawo in wanke maka"
Yusuf yace "A'a bakomai nagode, yanzu zan wanke in gama"
"dan Allah ka kawo, ai be kamata kayi wanke wanke da kanka ba, idan Baffa ya gani ma ze iyayi mana faɗa"
Yusuf yace "kema 'yarsa ce ne?"
Hanne tace "eh nima' yarsa ce nida Hindu, muje wani ƙauyene suna, se jiya muka dawo"
Yusuf yace "Allah sarki, Allah yayiwa rayuwar ku Albarka"
Cike da jin daɗi Hanne tace "Ameen" ta karɓi kwanukan, yace "in kin gama, seki kai mata ɗakin"
Hanne tace "to" tana mamakin ace yana da mata amma shize wanke wanke, Yusuf ya janyo ruwa a rijiya ya wanke banɗakinsu, yayi wanka ya fice.
Hanne ta gama wanke wanke, ta tafi ƙofar ɗakinsu Widad, ta tsaya tana sallama, ƙasa ƙasa Hanne ta shiga ɗakin ta cewa Widad "ga kwanuka inji mijinki"
"Ajiye anan"
Hanne ta ajiye, ta juya ta fita tana mamakin wannan irin nuna isa na Widad.
Anwar ya gayarawa Daula jikinsa, ya canza masa kaya ya bashi Abinci da sirinji, ta cikin robar dake hancin Daula, ya gyara ɗakin ya tattara kayansa marasa kyau ya fita ze bayar akai gida su Nura su wanke.
Sufyan ne ya tinkari ɗakin da Alhaji Nasir yake, gaban sa se faɗuwa yake, ji yake kamar kowa kallonsa yake a baranda ya haɗu da Anwar, suka gaisa da Anwar, doctor Sufyan yace "ina zaka haka Anwar? Kasan bama san ana barinsa shi kaɗai"
Anwar yace "yanzu zan koma, kayan nan na fito dashi zan kaiwa direba ya kai gida a wanke"
Sufyan yace "to masha Allah, ga wasu magunguna na rubuta, idan ka kai kayan wankin seka biya pharmacy ka siyo"
Suna nan tsaye aka fito da wani mutum ya mutu an turo shi a gado za'a fita dashi.
Anwar yace "doctor, dan Allah nasan lafiyar Alhaji ba a hannunka take ba tana hannun Allah, dan Allah ka ƙara ƙoƙari, bawan Allah nan kullum jikinsa ƙara rikicewa yake"
Sufyan ya dafa kafaɗar Anwar yace "karka damu Anwar, kamar yadda ka faɗa sauƙi na Allah ne, Amma muna fatan Allah ya bawa Daula lafiya"
Anwar yace "shikenan nagode, bari inje"
Anwar yayi gaba, Sufyan ya tsaya a gurin yayi shiru, sannan yayi gaba jikinsa gaba ɗaya babu ƙwari, a haka ya taka har yaje ƙofar ɗakin da Daula yake, yasa hannu ya murɗa ƙofar ya shiga, sedai me yana shiga yaga wayam ba kowa akan gadon, ya ƙarasa gaban gadon da sauri ya yaye bargon kai, ba Daula babu alamarsa, ya buɗe banɗaki ya duba nan ma kowa, ya duba bayan ƙofa zuwa ƙarƙashin gado, amma be ganshi ba ƙarewa har fridge ya buɗe amma bega alamar Daula ba.
Cire gilashin dake idonsa yayi yana zazzare ido, yana waige waige kamar Ɓarawo
Fitowa yayi da sauri daga ɗakin, aikuwa yayi karo da Anwar, Anwar yace "doctor Sufyan ya dai? Naganka a haka? Na kawo maganin"
Doctor Sufyan yace "Amm... Mmm.. Nace ina Mara lafiyar ne?"
Anwar yace "kamarya? Yana ciki mana"
Sufyan yace "Baya nan na duba ko ina ban ganshi ba"
Anwar yace "kamar yaya? Ya za'ayi in fita barshi, daga zuwa siyo magani kace baka gasnhi ba? Sekace wata eiga, mutumin da komai sena masa ta yaya ze iya fita?"
Sufyan yace "Nima abunda ya bani mamaki kenan, na duba ko'ina ban ganshi ba, har banɗaki na duba baya nan"
Kallon tuhuma Anwar yayiwa Sufyan yace "Amma gaskiya ni
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 35