yake wayar da Mahaifiyar sa ba ƙaramin birge ta yayi ba.
A ranta tace 'dama suma talakawa suna jin wannan shauƙin da ƙaunar na iyaye, inama Ammi na tana raye nima in kwanta a jikin ta in ji daɗi'
Ba tayi aune ba taji hawayen da bata shirya zubowarsu ba. Cire glass ɗin fuskarta tayi tana goge hawayen idon ta, katse wayar Yusuf yayi ya kalleta yace
"lafiya dai?"
"Lafiya cigaba da tuƙinka, ina so muje gurin nan kafin 5"
Ya jinjina kai ya ci gaba da tuƙin, wani katafaren hotel ne, motocine suke shiga suna fita a ciki, kowa harkar gaban sa yake yi, sedai mafi akasari kallo ɗaya zakayi wa mafi yawa daga mutanen dake shiga suna fita, ka gano rashin tarbiyya da ta ido a tattare dasu, musamman matan duba da yanayin irin shigar dake jikin su.
Yusuf yayi parking yana kallon Widad, ta buɗe motar ta tsaya tana ƙarewa harabar hotel ɗin kallo.
Da sauri Yusuf ya fito daga motar yana kallon ta, ta dubeshi tace "wait for me here"
ta sa kai da nufin shiga cikin hotel ɗin, da yawa mazan dake gurin nan hankalinsu ya dawo kanta, Widad ta haɗu iya haɗuwa, wani takaici ne ya kama Yusuf, ace 'yar musulmi ce da wannan shigar a wannan gurɓataccen gurin.
Bin bayanta ya kuma yi da sauri, ta tsaya ta kalle shi tace
"I said you should wait me inside the car, don't let anyone to see you here, don't tarnish your image because of me"
Ta sake juyawa, ba zato cikin zafin nama da zafin rai Yusuf ya riƙo Widad gaba ɗaya zuciyar su ta buga a tare, Yusuf ya kalli cikin idon ta yace
"Guri irin wannan be dace da mace me daraja kamar ki ba, Mahaifinki babban mutum ne be kamata aga 'yarsa a irin wannan gurin ba, ke mace ce kuma me daraja bekamata kowane gara ya dinga kallon surar jikin ki haka ba, think about it"
Nutsuwa Widad tayi seda ya gama tsaf sannan tace
"Cikani tun kan in wanka maka mari a gurin nan, kai waye da zaka gayamin abunda ya dace dani? this is my life style not yours, dalla Cikani Malam kana ɓatamin lokaci ni"
A hankali Yusuf yace "I am musulm, ina kishin yadda mutane ke ƙare miki kallo a haka, kalli irin mutanen dake gurin nan, da yawan su karuwai ne fa da mutanen banza, shigarki bata da maraba da wanda matan gurin nan marasa daraja suka yi"
Cikin isa tace masa "koba maruwanci ba, Nima shi nazo yi, am prostitute karka ƙara shiga rayuwa ta, na gaya maks"
Ta juya ta shiga Hotel ɗin da sauri, wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Yusuf, ya koma mota ya zauna yana tunani a ransa
'to wai kai Yusuf banda shisshigi ina ruwanka da ita ne?'
Wata zuciyar ta tambaye shi.
Yana nan zaune a mota kusan mintuna Arba'in, gajiya yayi da zaman motar ya fito ya zauna akan motar yana ƙurawa hanyar da Widad tabi ido.
Ba tsammani ya hangota tana fitowa, sedai fuskarta ɗauke da hawaye tana ta share hawayen da handkerchief, inda motar su take ta nufo idanunta jawur, wani ne ya biyo ta yana ƙoƙarin tsaida ita yayi mata Magana amma bata tsaya ba, tana zuwa ta buɗe motar ta shige.
Yusuf ya zagaya ya shiga ya kunna motar, gaba ɗaya se yaji ya tsargu da yanayin daya ganta, gaba ɗaya hankalinsa ya tashi "Are you ok?"
"Do you have any conscience with me being ok or not?" ta tambaye shi a hasale
"Yes i have" ya bata amsa, tsaki tayi ta ɗauke kanta tace
"drive very fast please" gudu sosai Yusuf yake amma azalzalarsa take wai ya ƙara gudu, kuma still bata dena kukan ba, kuka take me fallasa da tsantsar ɓacin rai da damuwa.
Guri Yusuf ya samu yayi parking ya juyo yana kallonta, ba tace komai ba tasa hannu a jakarta ta ɗakko wayar ta, ta ɗan daddana sannan ta saka a kunnen ta, tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace "Hello Daddy"
Yusuf baya jin me mahaifin Widad ke cewa, cikin kuka tace "please Daddy I want Flight back to U. K, i regret coming back to Nigeria, please Daddy talk to Bulama ask him to set up my visa"
Shiru ta ɗanyi sannan tace "Daddy don't take it for granted please, i can't define what happens today, dan Allah kace ayimin visa in koma"
"Daddy why? Kayi shekaru ba tare da ni ba se yanzu zaka ce baka so inyi nesa da kai? Karo na biyu ina neman abu kana ƙin Yimin, shikenan Daddy bayan ciwon Ƙwaƙwalwa am at risk of having cardiac attack" ta saki wayar ƙasa ta cigaba da kuka.
Yusuf ya cika da mamakin meyasa Widad kuka haka? Akwai buƙatar yasan me taje yi Hotel.
"malam kayi sauri ka maida ni gida, ka tsaya kana kallo na"
"Bazan iya tuƙin ba muddin zan cigaba da jin kukan ki" yai maganar fuskarsa ɗauke da damuwa
A hankali ta ɗago idanunta da suka yi jawur, ta saka ana Yusuf tana son gano gaskiyar abunda ya faɗa
"to meye haɗinka dani da kuka na ze dame ka, just drive ba ruwan ka da kukana, kayi abunda ke gabanka"
A hankali ya kunna motar, ya bata wuta ya cigaba da tuƙi, sedai gaba ɗaya hankalin sa baya jikin sa, yana can yana tunani daban daban.
Ihun Widad ne ya dawo dashi hayyacin sa, sannan ya lura da abunda ke shirin faruwa, duk yadda yayi ƙoƙarin kaucewa motar, seda me motar ya daki tasu.
Dafe kai Yusuf yayi yace "Subhanallah"
A fusace ta kalli Yusuf "Are you out of your sense, see how you ruin my life, kashe ni kake so kayi? Baka gani ne? Dama so kake ka kasheni, an haɗa baki da kai zaka kashe ni ko? Dama na sani"
Kafin Yusuf ya bata amsa tuni me waccan motar ya fito yana zazzaga bala'i, an lotsa masa mota se an biya shi.
Yusuf ya buɗe motar ya fita jiki ba ƙwari, ya kalli mutumin ze kai shekaru Arba'in, Yusuf yace
"Dan Allah kayi haƙuri, birki ne ya ƙwacemin, kuma kaga traffic ta tsaida hannun ka amma baka tsaya ba, kuma ni na riga na taho da gudu, amma dai kayi haƙuri"
"Shut up my friend, ni zaka gayawa traffic ta tsaida hannu na? Titin naka ne kai kaɗai da zaka dinga wannan gudun, banza shashasha kuma wallahi seka biya ni asarar da kayi min kokuma kaga abunda zan maka"
Tuni mutane suka fara taruwa, suka cika gurin ana ta bawa Mutumin nan haƙuri, dukda zagin da yakewa Yusuf amma haƙuri yake bashi, amma mutumin nan ya rintse ido yana zazzaga masifa yana cin zarafin Yusuf, hakimar kuwa ko fitowa ba tayi ba tana mota a zaune.
Yusuf yace "Amma naga idan laifi ne fa kaine kayi bani ba, Amma se baka haƙuri nake kana cigaba da cimin mutunci a gaban mutane, shikenan Yimin duk abunda zaka iya ka huce"
Yusuf dama gashi a cikin damuwa yake, ga shi ze zagin sa mutumin yake, aikuwa nan da nan temper ɗinsa ta hau zuciyar sa ta shiga tafasa, dan haka se yayi shiru ya dena cewa komai.
Mutumin ya cigaba da zazzaga masifa "Do you know who I am da zaka dingamin magana da gadara,? I will show you what am capable of doing, sena nuna maka ni waye, sena sa an sauke maka wannan rashin ɗa'ar taka mara tarbiyya kawai"
"You are nobody More than stupid Malam, waye kai idan har kai wani ne bazaka tsaya kana ɗaga murya akan wannan banzan gwangwanin motar taka ba, kayi abunda zaka yi an bige motar taka, ina son inga kai waye, kuma me zaka iya?"
Gaba ɗaya suka juyo inda Widad ke magana da jajayen idanunta.
Mutumin ya kalli Widad yace
"Lallai ka ɗakko karuwa a mota, dole ka ɗagamin murya danka birgeta, zanyi maganin ku daga kai har ita"
Ya ciro wayarsa yana waya.
Yusuf a harzuƙe zeyi magana Widad ta ɗaga masa hannu alamar yayi shiru.
Ta ɗakko wayar ta tayi 'yan taɓe taɓe.
Mutane suka ja gefe suna son ganin ƙarshen dramar, mintuna kaɗan sega motar 'yan sanda, suka zo suna wuri wuri, mutumin ya nuna musu Yusuf yace "gashi nan shine, ku kama shi shida wannan koɗaɗiyar Yarinya me kama da sadakar Yalla"
Tuni ɗaya daga ɗan sandan yaje ya cakumo Yusuf, sedai me ɗan sandan ya jiyo bindiga a jikin Yusuf!!!
SHARE PLEASE 🙏
__Masha Allah nagode da addu'oinku Daddy yana samun sauƙi Alhamdilillah nagode sosai Allah yasaka da alkhairi __
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 12
Ɗan sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.
A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya ɗakko ID card ya nunawa ɗan sandan, washe baki ɗan sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace
"Dan Allah Yallaɓai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na bashi haƙuri yaƙi haƙura"
Mutumin ya ƙaraso inda su Yusuf suke yace "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku kulle shi har se nazo station ɗin"
Ɗan sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.
Widad tace "ina so a duba Accident ɗin nan, idan direba nane yake da laifi, zan biya shi kuɗin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze durƙusa ya bamu haƙuri, saboda cin zarafi da ɓata mana lokaci da yayi, in kuma yaƙi a tafi da shi, ajiyata ne a kulle shi se nazo"
Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka ɗau sowa.
Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka durƙusa ka bawa direba na haƙuri akan cin zarafin da kayi masa"
"Wallahi baki isa ba keɗin banza, in bawa wannan wulaƙantaccen haƙuri, kin san koni waye?"
Ɗaya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace "kai wallahi wannan' yar masu ƙasa ce, idan taso zatasa a ɓatar da kai gaba ɗaya wallahi, kayi abunda tace kota sa a ɗaureka"
"wannan ƙaramar yarinyar 'yar cikina?"
"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu ne"
Mutumin ya dawo a ƙule ya kalli Yusuf yace "Yi haƙuri"
"Akan gwiwowinka zaka durƙusa ka bashi haƙuri" cewar Widad
Cikin tsawa wani ɗan sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"
A hankali yaja da baya ze durƙusa, Yusuf yayi saurin riƙe shi tare da girgiza kai ya kalli Widad yace "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi haƙuri dan Allah, ni zan durƙusa in baki haƙurin a madadinsa"
Dama Widad tasan Yusuf baze taɓa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin shi ɗin bakomai bane.
"Shikenan tunda ya haƙura, gobe in Allah kaimu, yaje station ɗinka ya karɓi kuɗin motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"
Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya.
Dare yayi musu a gurin nan saboda wannan incident ɗin, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa suka tafi.
Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu daya gama kaɗewa, ƙarshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.
suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buɗe musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi parking, har ya gama abunda zeyi ze buɗe motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar.
fita yayi ya zagaya ya buɗe mata ƙofar, yace "Munzo fa" ɗaga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ƙafafunta da take jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yunƙuro ta fito, sedai tana fitowa ta tafi luuu zata faɗi, cikin zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar riƙeta ta faɗa a jikinsa.
Ƙirjinsa ya dinga bugawa da ƙarfi, saboda jin hakan wani irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me raɗa yace "Are you ok?"
Jinjina masa kai tayi ta sake ƙoƙarin miƙewa, amma still jiri ke kuma ɗibarta, tafiya take tana tangaɗi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa riƙe da ƙaramar jakarta da kuma wayar ta.
A babban falon ta zauna tana riƙe kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ƙoƙarin cire takalmin ƙafarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin.
Yusuf ya taka inda take ya durƙusa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire mata.
Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.
Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'
"ko za'a kira likita ne?"
"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.
"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"
"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana ɗaki ka tafi ka ban guri"
Ɗan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.
Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "
Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daɗin yadda mahaifinta ke mutuntani"
"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"
"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"
"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"
"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "
"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa wannan a ranka"
Tana gama faɗar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.
Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.
Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa, yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.
Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace "Eh nine"
"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin
Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"
Ɗaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya ɗago yana kallonsu, babban yace
"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"
"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faɗa babu alamar tsoro
Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace
"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"
Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.
"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar ɗaya daga cikin su
"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi yunƙurin cutar dani"
Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.
"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"
haka suka barshi a gurin suka tafi.
Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.
ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar da Widad ta bashi ɗazu.
Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"
Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke buƙatar nazari.
"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"
Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se ɓarawo ne ya ɗauke shi.
*******************************
Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"
"Bana jin daɗi ne Umma"
"dan baka jin daɗi seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya miƙe ya shiga yai wanka, kayan breakfast ɗin ta kawo masa ɗaki, ta kalle shi tace
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"
Yusuf yace "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"
"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace "Yi haƙuri Umma, bana son ɗaga miki hankali ne"
"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa
"Eh banji ciwo me yawa ba"
Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta ɗakko masa first aid box ɗinsa ya ɗau magani ya sha, ya koma ya kwanta.
Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"
"Ina gida bana jin daɗi ne"
"Subhanallah, meya sameka?"
"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa
"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama
**************************
Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"
"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta ɗanyi tsaki sannan tace "shigo"
Ya shiga falon ya durƙusa yace
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"
"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"
"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faɗamin kanka tsaye meke tafe da kai"
Isa ya gyara zama yace "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai buƙatar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita, basu dawo ba se ƙarfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa
"da idanu na naga suna rungume juna, Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin ɗakin kwanan ta, Allah kaɗai yasan me suke yi, gaki da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 35