Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wanda Mummy ta kasa"? Amal tace "Fahad zakiyiwa magana, dan Mummy taje har gidansu ta gayawa mahaifinsa amma yaƙi ɗaukar abun da mahimmanci, ke tunda kuna ɗasawa dashi kisa yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki Yayanmu" Ramlah tace "Anya kuwa? Fahad fa akwai lafiyar kafiya mussman yanzu da suke takun saƙa da yaya" Amal ta taɓe baki tace "ashema ba son naki yake ba tsakani da Allah tunda ze iya barinki cikin damuwa, Allah wadaran wannan soyayyar" "Amal ni kike cewa Allah wadaran?" "Na faɗa Allah ya wadaranta, dama wannan banzan Fahad ɗin me fuskar jakai kansa kawai ya sani, in ba soyayyar ƙarya ba, yayiwa mahaifinsa magana yasa baki a saki ɗan uwanmu mana, naga shima dai ɗan uwansa ne" Ramlah tace "Aikuwa Amal i will prove you wrong, zan nuna miki soyayyar mu ta gaskiya ce" Amal tace "in gani ƙas, ancewa kare ana biki a gidansu, ƙaryar banza burodi a lefe, ina amfanin soyayyar da baka da alfarma a gun wanda kake so" Ta tashi ta bar mata ɗakin, tana ci gaba da mita da tsaki. Nurat ta shirya cikin doguwar riga, tayi rolling ta ɗau wayarta da jakarta ta fito, ta leƙa ɗakin mamanta taga tana bacci, ta taho cikim sanɗa ta fito harabar gidan, da sauri sauri ta tafi bakin gate tace "zoka buɗemin ƙofa zan fita" Me gadi ya kalleta yace "ina zaki?" "ka aikeni ne? Ka buɗemin zan fita" Ya ɗan sosa kai yace "Madam, me gidan nan yace kar in kuskura in sake bari ki fita, muddin bashi ya bada umarnin hakan ba" A ɗan hasale tace "ka buɗemin ba nisa zanyi ba, yanzu zan dawo" Girgiza mata kai yayi yace "dan Allah kiyi haƙuri, wallahi zan fuskanci fushinsa muddin na bari kika fita" Juya tayi cikin gida, jiki ba ƙwari tana tunanin meye mafita, can wani abu ya faɗo mata, ta miƙe ta fito tace masa "kazo Mummy na kiranka" Ya miƙe ya biyo bayan Nurat, yana gaba tana binsa a baya, yana shiga falonsu cikin sanɗa ta dawo baya a hankali, tayi waje tana zuwa tasa mukulli ta buɗe gate ɗin tayi waje abunta. Gidansu Widad ta tafi, tana zuwa tayi sa'a ta tarar da Amal a babban falo tana karyawa, Amal na ganinta ta buɗe baki tace "Nurat yau kece a gidanmu haka? Abun mamaki" Nurat tayi murmushi tace "meye na mamakin kuma?" Amal tace "ni dai nasan koda zaki zo gidan nan saboda Widad zaki zo, kuma duk garin nan ba wanda be san anyi kidnapping ɗinsu ba, kuma dai amma baban ku besan kinzo ba" Nurat tayi murmushi tace "tabbas nasan an sace Widad da ɗan uwanta, sedai... Amal tace " ɗan uwanta kuma? Direbanta dai" Nurat tace "direba kuma kamar yaya direba?" Amal tace "kamar yadda na gaya miki, ita da Yusuf ne aka ɗauke su, Yusuf kuma direbanta ne" Nurat tayi shiru, sannan tace "Amma meye alaƙar dake tsakaninta da Yusuf?" Amal tace "Allah kaɗai yasani, Wallahi Nurat ina cikin matuƙar damuwa ɓatn nan nasu, mussman Yusuf idan nace zan nuna damuwar da nake ciki ma babu me saurarata a gidan nan, Amma duk rashin yardar Widad ta yadda da Yusuf fiye da tunaninki" "Amma Amal mezesa matashi kamar Yusuf ya ɓige da aikin direba a gidan masu kuɗi?" Amal tace "bake ba ni kaina ina wannan tambayar, amma kin san da wani aikin gwamnatin gara aiki a gida kamar wannan, dan ba Widad ba hatta me gidan nan ya yadda dashi sosai, Amma a yadda Yusuf ya haɗu kam, bekamata ace aikin direba yake ba, nayi masa zancen ya nemi wani aikin, amma yaƙi yarda, yafi ƙaunar kasancewa a ƙarƙashin wannan uwar izzar, tana hantararsa tana komai amma baya ganin laifinta" Shiru Nurat tayi kamar ba zata ce komai ba, can tayi ajiyar zuciya tace "Amal ya batun Yaya Anwar kuwa?" Amal tace "hamm, yana can Mummy tana ta fama anƙi sakinsa, wai har yanzu bincike ake akai" Nurat tace "wani station ɗinne?" "Suna state CID shida Likitan" Nurat tace "Allah ya fidda shi lafiya, Insha Allah zanje in ganshi" Amal tace "kai amma kuwa mungode sosai Nurat" Nurat tace "bakomai Amal, se anjima" Yusuf yayi baccinsa ya tashi, ya buɗe jakarsa ya ɗakko kayan tea daya bada sautu aka kawo masa, ya ɗora tea Widad tana tsakar gida suna hira da Hindu, da hansai. Yayinda Hanne se wani gyatsine fuska take yi, bata kallon ko inda Widad take, Widad data fita bata taɓa nuna tasan da halittar Hanne ba, abun da Hanne bata sani ba shine, mutanen da suka damu da itama ba kowa take iya shiga sabgarsa ba, balle wanda ya nuna be damu da ita ba. Yusuf ne ya fito tsakar gida, yaje ɗakin megari suka sake gaisawa ya zauna suka shiga hira. Widad na zaune kusa da gwaggo, tana dama koko tana kallon yadda take yi, Widad tace "Mama haɗa kokon nan ma ashe ba wahala, na iya haɗa custard shima zan iya wannan" Hansai tace "meye kuma kostan?" Widad tace "wani abune shima sha ake, kamar haka ake dama shi amma suna da ɗan banbanci da wannan, Ai zaki ban watarna nima inyi ko?" "taɓ za'a sha kwaɓa kuwa, yadda kike a sangarcen nan ba uwar da kika iya, mijinki na fama wallahi, ba uwar da kika iya se zance" Widad ta ɗaga ido ta kalli Hari tace "Mijinki ne yake fama da ƙazantarki ba nawa ba, kuma karki ƙara cemin sangartacciya" Gwaggo tace "yi haƙuri Amarya, ƙyaleta" Gwaggo ta fara rabon koko, ana zuba na kofin megari Widad tasa hannu ta ɗauka tace "wannan nake so, wannan kofin yafi kyau" Gwaggo ta ɗanyi shiru, Hansai tace "Amarya kofin megari nefa" Widad ta tura baki tace "toni ina son kofin, wannan nake so" Gwaggo tace "Hindu, jeki ki duba ƙasan gadona a cikin kwanukan Hanne ki ɗakkon sabon kofi irina Malam" Hanne tace "kai gwaggo kofin Auren nawa za'a ɗakko?" Gwaggo tace "eh kema ba Allah ne ya baki ba, a sai miki wani" Haka aka ɗakko sabon kofin silva, se ƙyalli yake da murfinsa aka zubawa Widad koko a ciki, Hanne ta dinga mita tana kumbura baki, ai Widad bata nuna tasan da zaman Hanne a gurin ba. Hanne na tsaka da masifar ne sega Yusuf ya fito daga ɗakin megari, ai nan da nan Hanne ta nutsu ta fara murmushi, Yusuf ya harari Widad dan yaji duk abunda ya faru, ita kuwa tayi kamar bata ganshi ba. Hanne ta durƙusa ta gaida Yusuf, Yusuf ya ɗan saki fuska ya amsa mata, yazo ya durƙusa ya gaida su gwaggo, duk faɗan da Hari keyi da Widad, tana matuƙar girmama Yusuf, dan suna ɗasawa dashi. Hanne tace "yau ba wanke wanke ne ka kawo ayi?" Yusuf ya kalli inda Widad take, yaga ko a jikin ta, jujjuya kofin kokonta kawai take. Yusuf yace "A'a babu na wanke tun Asuba. Gwaggo tace "kaine kake wanke wanken? " Yusuf yayi murmushi yace "A'a Mama, wani lokacin ina rage mata aikine kawai" Gwaggo ta kalli Widad tace "Anya Ɗiyata?" Widad tace "Mena yi? Shine yake cewa zeyi fa, kuma idan nace zanyi se yace ban iya ba" Hanne tace "ka dinga barinsu, da safe se in haɗa in wanke, tunda bata iya ba" Hansai tace "ikon Allah, toke Hanne dole ne sekin wanke musu kwanukan?" Widad tace "Yoseef kaga sabon kofinmu, Mama ta bamu" Yusuf yace "Ahh mama mungode sosai Allah yasaka da alkhairi" Ya kalli Widad yace "let's go and have a breakfast" Ta miƙe tayi gaba, suna zuwa ɗaki yace "sannu kinji" Cikin rashin fahimta tace "aikin me nayi kakemin sannu?" "yanzu memakon kice in sai miki kofin kina so, kawai seki sa rigima ke se'an baki?" "ko zaka Ƙwace ka mayar ne?" Yusuf yace "A'a ni bance ba, na dafa shayi ne kuma gashi kin karɓo koko" Da sauri tace "dan Allah dagaske?" Bece mata komai ba, ya wuce ya sauke tukunyar tea ɗin, ya buɗe jakarsa ya ɗakko kayan tea ɗin ya haɗa mata shayi yasa mata madara, tana zaune tana kallonsa, ya ɗauka ya kai ya ɗanɗana yaji in beyi zafi da yawa ba sannan ya bata. Ta kalle shi tace "meye kuma seka sha zaka bani?" "Na duba ne inji in beyi zafi da yawa ba karki ƙone baki" "to shine zaka sa baki a jikin kofin, toni gaskiya da cokali zan sha tunda kasa baki, ko in canza kofi" Tsayawa yayi yana kallonta, taje ta ɗakko wani kofin ta juye a ciki, ta ɗau bredin ta gutsura ta koma gefe. Karon farko da taga fuskar Yusuf ta canza saboda abunda tayi, ta nuna ƙarara tana ƙyamarsa kenan. Tana kallon yadda ya ɗan ɓata fuska, ya kasa sakin jiki yaci Abincin ma, amma ta basar ta cigaba da cin bredinta, da a gidane ba yadda za'ayi taci bredi babu mahaɗi, amma yanzu se tura shi take kuma tana jin daɗinsa a haka. Ƙarshe Yusuf miƙewa yayi yaje yayo wanka, yazo ya fara shirin fita sedai yaƙi cewa uffan, be sake kula ta ba shirinsa kawai yake. Widad ta matsa inda yake tace "wai naga ka wani yi shiru, lafiya dai?" Girgiza mata kai yayi, ya cigaba da shirinsa "Amma naji kayi shiru haka? Nasan baka saba zama haka kayi tsit ba" Still shiru ya kuma yi mata, yana gyara kayansa dake cikin jakar matafiya. Ɗagowar da zeyi taga idonsa yayi jawur, gaba ɗaya se jikin ta yayi sanyi. "dan Allah meye ya same ka?" Raɓata yayi ze wuce ta sha gabansa tana kallonsa. Ze kuma kaucewa ta kuma shan gabansa, ba tayi tsammani ba Yusuf ya janyota ya haɗe bakinsa da nata. Mutsu Mutsu ta dingayi tana ƙoƙarin ƙwacewa, amma ta kasa ko ƙwaƙwaran motsi, saboda yafi ƙarfinta nesa ba kusa ba. A hankali ya cika ta, tayi baya da sauri tana rarraba ido, tare da sauke numfashi. Tofar da yawun bakin ta ta dingayi, tana goge bakinta tana kuka. Yusuf ya ƙaraso inda take, amma ta shiga ja da baya, riƙota yayi ya ƙura mata ido, take yayi mata wani irin kwarjini. Cikin sanyin jiki Yusuf yace "Widad da zuciya zatamin adalci to da ban iya jure duk wulaƙancin da kikemin a baya ba, saboda Yusuf baya Jura wulaƙanci dan shima mutum ne kamar kowa, sedai kash zuciya ta ta fara son abunda tasan yayi mata nisa har abada, wanda be dace da ita ba, zuciyata ta saɓa Alƙawarin da mukayi da ita nayin ban kwana da soyayya har Abada, hakan shine kawai mafita ga irin rayuwar da Yusuf ya tsinci kansa a ciki, Amma ko warkewa banba daga cikin zugi da raɗaɗin da zuciyata ke ciki ba, ƙaddara ta haɗani dake, kuma zuciyata ta shiga begen ki, Auren nan da mukayi har cikin zuciyata nake som Auren nan, sedai nasan dole wataran zamu rabu saboda bamu gina Auren akan tirbar soyayya ba, dan Allah Widad ni bance sekin soni ba, saboda nasan hakan baya cikin tsarin rayuwar ki, kuma tamkar ƙasƙancine a gareki Auren mutumin dabe kaiki a komai ba, nasan yanzu ma kutsen ƙaddara ne ya haɗamu zama inuwa ɗaya dake, ko baki soni ba dan Allah kidena nunamin ƙyama kinji Gimbiya, yi haƙuri na saki kuka" yai maganar yana ƙoƙarin goge mata hawaye Fizgewa tayi tace "Dalla ni cikani in wuce, the must useless word i hate in my life Love, kaima ka shiga sahun imagination da shirme kenan, ban guri ni zan wuce" Ta ture shi tayi gaba abunta, ta ɗakko brush da toothpaste ta tafi sake wanke baki, duk dan Yusuf yayi kissing ɗinta. Jiki a sanyaye ya ƙarasa shiryawa, ya fito ze fita ko kallon inda yake ba tayi ba, ganin ba kowa a tsakar gidan se Hanne yasa yazo gabanta yace "Zan tafi" "Jirani inzo in zama mota seka hau ka tafi" Ya girgiza kai yace "nasan kina jin haushina, kiyi haƙuri" Banza tayi masa ta cigaba da abunda take, Hanne tace "Adawo lafiya Allah ya tsare" Yusuf yayi murmushi yace "Allah yasa nagode" Har yayi gaba ya waigo ya kalle ta, suka haɗa ido ya ɗan lumshe ido yace "I love you My queen" Wata uwar harara tayi masa ta miƙe ta bar tsakar gidan. Nurat tana zaune a reception, da ƙyar aka bari taga Anwar, fuskarsa duk ta ɗaga yayi wani iri, a gigice tace "Yaya Anwar me kayi aka kama ka haka?" Anwar yace "wallahi Nurat ban saniba, wai ana tuhumata da haɗin bakina akan sace Daddy, kuma wallahi ban san komai ba, na gyara masa jiki na bashi abinci, likita yace inje in karɓo wani magani, ina komawa se cemin yayi wai ya shiga ɗakin amma be ganshi ba" Nurat tace "kamar yaya, ta yaya za'a sace mutum a Asibiti mutumin dako motsin kirki baya iyayi" Anwar yace "wallahi bam sani ba Nurat, ni yanzu ba kamanin da'akayine damuwa ta ba, sanin inda Alhaji Nasir yake shine babbar damuwa ta, ba shi da lafiya waye ya sace shi? Waze kula dashi? Waze bashi magani na rasa wacce irin masifa ce tasa ake bibiyarsa haka" Shiru Nurat tayi tana zancen zuci 'Anya kuwa babu sa hannun mahaifina a sace Alhaji Nasir?' Ta ɗago ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar baka yi laifi ba dan baka banga dalilin da zesa a kama ka ba, dan haka ka kwantar da hankalinka, akwai wani cousin brother ɗina, barrister Abdallah zan masa magana ya shiga cikin case ɗin" Anwar yace "bakya ganin akwai matsala? Kar a sashi a matsala fa, sunce in suka gama bincike za'a sakeni" "babu wata matsala insha Allah, ka kwantar da hankalinka, Insha Allah zak bar gurin nan" Anwar yace "Nagode sosai Ƙanwata, Allah yasaka miki da alkhairi" Nurat tace "you deserve it dear" ta ɗau jakarta tayi waje. Ramlah ce zaune a motar Fahad, ta murtuke fuska yana ta surutu amma tayi shiru, kallonta yayi yace "beb, ya inata magana amma kinyi shiru, lafiya kuwa?" "Fahad yanzu ace brother na yana ɗaure, amma koka jajantamin talk less of kace zaka kai masa ziyara" Fahad yace "ni inje state CID no i can't tarnish my image" "Amma fa kaima ɗan uwanka nae" "Yeah really, you are right dear but zuwa gurin nan se masu manyan crimes da manyan terrors, kuma kinga daddy na sanannen mutum ne, ace anga mutum kamar ni a irin wannan gurin is not fair at all, it will tarnish our family image" Ramlah tace 'but your dad can bale him out, so you don't care about my feelings, ɗan uwana yana rufe kaikuma abunda ya dameka daban ko? " "Ai na miki bayani, ban san me kike so ayi ba kuma" "ina son ka saka baki, Daddynka yayi magana a sake shi" "Amma Ramlah kin san ba abune me sauƙi yin hakan ba ko, yaynki an haɗa baki dashi an sace Daula, me zesa Daddy yasa baki" A fusace Ramlah tace "shut up Fahad, ta yaya Anwar ze hakan, tare kukayi school room ɗinku ɗaya, you know what he can do and what he cannot do, dan haka ina jiran kaje kayi magana da mahaifinka a fito da shi, that's the only way you can prove to me that you loves me" Tana gama maganar tayi waje ta bar motar, ɗan taɓe baki yayi ya kunna motarsa yayi tafiyarsa. Yau da Yusuf ya dawo a ɗaki ya tarar da widad, kamar tana cikin damuwa ya kalle ta yace "Na dawo" Jinjina masa kai kawai tayi, amma ta kasa magana, se ya zata tun abunda ya faru da safe ne yasa take jin haushinsa. "Meke damun kine? Ko har yanzu fushin kike dani?" A kasale tace "Bakomai fa" Haka ya fita yaje yayi wanka ya dawo ya sameta a inda ya barta, yau dambun tsaki Hansai ta girka ta aiko musu, amma taƙi sakin jiki taci, ya kaɗa ya raya amma tace lafiyarta ƙalau, sedai ya lura buni buni seta tafi toilet ta dawo. "Gimbiya ko cikin kine ya ɓaci?" Girgiza masa kai tayi tare da kwanciya, haka taita yi har washegari gaba ɗaya kamar bata da sukuni, kuma taƙi gaya masa abunda yake damun ta, haka ya fita ya barta ya ɗauka dai fushi kawai take, Da Azahar ya dawo sedai ya tarar da tun Abincin safe bata kuma cin komai ba. Yaje gabanta ya durƙusa yana ƙare mata kallo yace "dan Allah idan fushi kike dani kiyi haƙuri, kin sani a damuwa fa" "Nifa ba fushi nake ba, ka ƙyaleni kawai" "baki da lafiya ne?" "lafiya ta ƙalau" "but you look so much restless" Shiru tayi bata ce uffan ba, ya miƙe yana duba kwanuka yaga abunda aka kawao, se yaga tana ta dube duben abun shimfiɗar dake kan katifarta. Yana zuwa ya ɗagata cak daga kan katifar, meze gani jini ne a jikin ta, ya ɓata mata jiki da katifar. A gigice yace "Subhanallah, Widad meya same ki haka?" Take ta fashe da kuka tace "Period yazo min tun jiya bani da pad" Cike da damuwa yace "shikenan is ok, kwantar da hankalinki" Yasa hannu ya naɗe bedsheets ɗin, ya ɗora ruwa yayi ɗumi ya haɗa mata ruwa, ya rakata banɗaki, ya dawo ya haɗa abun shimfiɗar da kayan data cire ya zubasu a bokiti. Tayi wankan ta fito ta dawo ɗakin, har yanzu bata dena kuka ba, Yusuf yace "jeki zauna bari inje gurin Mama inga inda wani taimako da zata bamu" "Idan na zauna ɓata gurin zanyi" Yusuf yace "bakomai zauna, idan ya ɓaci zan gyara" Ya zaunar da ita ya fita da sauri. Yana fita tsakar gida Hanne ta kalle shi tayi murmushi tace "kana buƙatar wani abune?" Yusuf yace "gwaggo zaki kira min dan Allah" Tace "to" Ta tashi ta shiga ɗakin gwaggo, gwaggo ta fito ta kalli Yusuf tace "lafiya dai malam Yusuf?" Cike da kunya, Yusuf yayi mata bayani, Gwaggo tace "to mudai yaranmu da tsimmane suke amfani, ban sani ba ko zata iya amfani da shi" Yusuf yace "bakomai Gwaggo, zata iya insha Allah" Gwaggo ta shiga ɗaki ta ɗakko sabon turmin Atamfa, da sabuwar reza, da ƙyar Gwaggo ta iya shiga ɗakin nasu saboda kunya. Widad na zaune da towel se vest a jikinta, Gwaggo tace "Sannu Amarya ya jiki?" Widad tace "lafiya ƙalau" Tasa reza ta yanka Sabuwar Atamfa ta gwadawa Widad yadda zata yi. Widad tayi shiru taƙi cewa uffan, Yusuf yace "Mama nagode sosai da taimakonki, Allah ya saka da alkhairi" Gwaggo tace "bakomai Malam Yusufa" Gwaggo ta fita, tana fita Hari tace "Yaya wai Wudas ɗince bata da lafiya?" Gwaggo tace "Eh" "meya same ta?" Gwaggo bata amsa mata ba, Hanne tace "waini Gwaggo meye na yanka sabuwar Atamfarki, wallahi kin fiye zaƙewa akan wannan fitsararriyar" Gwaggo a fusace tace "wallahi kika kuma magana sena kwaɗa miki mari, ina kallon ki duk abunda kike yi, ɗa na kowa ne, meye dan na yanka Atamfa? Abum duniya fararre ƙararre" Haushi Hanne taji, dan da wuya kaga Gwaggo tana faɗa se an ɓata mata rai sosai, Amma yau akan wannan koɗaɗɗiyar tana ta mata masifa. Yusuf ya kalli Widad yace "gimbiyata nasan baki saba amfani da irin wannan ba, amma kiyi haƙuri gidanmu babu mata nikaɗai ne shiyasa nima ban san kan wannan abubuwan ba, da tuntuni nasa an nemo miki abunda zaki yi amfani dashi" Da ƙyar Yusuf ya lallaɓata ta saka ƙyallen nan, sam she's not comfortable with this thing, gaba ɗaya ta takure kanta, Yusuf yana kallonta ta kwanta ta zauna gaba ɗaya ta kasa zama. Ya kwashi kayan data ɓata yaje ya wanke su tsaf, taga ya dawo ɗaki yana goge hannu ta kalleshi tace "wai me kayi?" "kayanki na wanke" "Kayan jinin?" "Eh mana, nasan idan na bar miki ba zaki iya wankewa ba" Shiru tayi ta bishi da kallo, tuno abunda ya faru da safe tayi, yadda tay masa wulaƙanci amma har ya manta yana tarairayarta, yasa hannu a kayanta na jini ya wanke. Ganin da yayi ta kasa zaune ta kasa tsaye yace "Gimbiyata meya ke damunki yanzu?" "ƙafafuna ne kamar ba nawa ba, babu daɗi marata ma ciwo takemin" Yazo ya zauna a kusa da ita, ya kamo ƙafafunta ya ɗora akan cinyarsa yana matsa mata a hankali, lumshe ido ta dinga yi. Ta ɗauke ƙafafunta daga kan cinyarsa, ta ɗora kanta sannan ta miƙa masa hannunta, tana masa nuni daya ja mata yatsun, haka Yusuf ya riƙe yatsun ta yana matsawa a hankali, babu daɗewa kuwa bacci yayi gaba da ita. Seda Nurat ta tinkaro komawa gida sannan gabanta ya shiga faɗuwa, dan se yanzu ma ta tuna taɓargazar da tayi. Kanta tsaye tana ta Addu'a ta fara buga gate ɗin, me gadi yazo ya buɗe mata bece mata uffan ba, ta shiga cikin gidan, sedai me a harabar gidan idonta ya sauka a cikin na mahaifinta yana zaune yana kallonta. SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!! (Ina ma'abota karatun littafin AƘIDATA, a fari nace zan bada littafin kyauta ba tare da ko sisi ba, amin Afuwa wani dalili zesa zan saida book2 and 3,dukda nima ba hakan naso ba, gaba ɗaya kyauta nayi niyya bada littafina, Amma dalilin me ƙarfi zesa in saida ƙarashen in na gama book1 ina fatan zaku fahimceni) Domin gyara, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 _*AƘIDATA*_ PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA _ (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) * And now *AƘIDA TA * I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends NOT EDITED ELEGANT ONLINE WRITER'S PART1 Page 40_41 Gaban Nurat ne ya shiga bugawa da sauri da sauri, ta shiga zazzare ido be kula ta ba bece mata komai ba, tazo ta tsaya tana kallon sa, taga harta wuce bece mata uffan ba. Ta shiga ɗaki ta nemi guri ta zauna, tayi shiru tana tunanin yadda zata samu Anwar ya kuɓuta, babu zato taji an murɗa ƙofar ɗakin nata. Mahaifinta ne ya shigo yana rarraba ido, gadan gadan yayo kanta yana faɗin "gidan ubanwa kika je?" Miƙewa tayi a gigice ta shiga ja da baya tana faɗin "babu inda naje Daddy" "ƙarya kike munafuka, harni zan saka doka ki sa ƙafa kiyi fatali da ita? Uwarki ta ɗaure miki gindin kiyi rashin mutunci ko? Ni da Daula waye ya haifeki?" "Daddy niba gurinsa na je ba, Ai an ɗauke shi daga Asibiti" Sekuma yayi sak, "Ubanwa waye ya gaya miki?" "wallahi Daddy a gari naji" "to gidan ubanwa kikaje? Zaki gayamin ko sena yanka ki a gidan nan?" Girgiza kai take, takasa magana ya cakumo wuyanta yana zazzare ido, kakari ta dinga yi tana kuka tace "Wallahi Daddy ba inda naje, kawai gajiya nayi da zaman gidan na fita, dan Allah kayi haƙuri" "se naci ubanki yadda idan na sake saka doka ba zaki takamin ba" Cikin kuka Nurat tace "Wayyo Allah Mummy, ki temakeni karya kasheni" Maimakon ya saketa sake shaƙeta yayi, yana kuma zaro mata ido kamar tsohon maye. Kakarin Nurat ne yasa mahaifiyar ta, ta sallame salar da take, a guje ta rugo ɗakin Nurat, ta tarar ya shaƙe Nurat kamar ya kama sa'ansa ko kuma wani shahararren Ɓarawo. "Kayi haukane, ka cikamin 'yata ita kaɗai ce dani, kana gani duk yaranmu mutuwa suke, ita kaɗai Allah ya barmin ka ƙyalemin' yata" Juyowa yayi a fusace ya mangare mahaifiyar Nurat yace "itama ɗin gara in aikata inda waɗancn suka tafi, muddin zata dinga takemin doka, tasan a duniya bani da maƙiyi sama da Daula, danme zata dinga zuwa inda yake, akan me?" Yai maganar tare da wurgi da Nurat, wadda tuni ta fara fita a hayyacinta, dan daya jefar da ita ko motsi

Chapter 31 of 35