yanzu zanje in dawo"
Ramlah ta rakashi har gaban motarsa, kallo ɗaya Yusuf yayi musu ya ɗauke kai, Fahad yace "Baby wai waye wannan ne?"
Yai maganar yana nuna Yusuf, yamutsa fuska tayi tace "Direban wannan sakaryar ce"
"yanzu wannan ne direba?"
"direba ne, sedai ya samu gindin zama fiye da duk wani me aiki a gidan nan, shiyasa har wani jin kansa yake"
"ku kuka ƙyaleshi baku saita masa zama ba"
"ni yanzu ba shine a gabana ba, kaje kayi sauri ka dawo kaci Abinci"
Suka yi sallama Fahad ya tafi, se bayan ƙarfe huɗu Yusuf yaga message ɗin Widad, ya miƙe ya shiga part ɗinta.
Yau dogon skirt ne a jikinta baƙi, da wata riga me dogon hannu ta ɗora ɗan ƙaramin veil akanta, tayi kyau sosai kayan sun zauna cif a jikinta sedai ana ganin duk wani shape na jikinta.
Tunda Yusuf ya shigo ba tayi magana ba, se sabgar gabanta take yi.
"Ya jikin magenki?" ya tambaye ta
Abunda Yusuf ya faɗa ne yasa ta ɗagowa da sauri tace "i think she got better now, she's able to play"
"Allah ya bata lafiya, na ɗauka mutuwa zata yi ashe da sauran kwananta a gaba"
Harar Yusuf tayi ta ɗau jakarta tayi waje, binta yake a hankali baya sauri yana tafiya kamsr kazar da ƙwai ya fashewa a ciki , ta juyo ta kalle shi tace "wannan wace irin tafiya ce kuma?"
"Nifa gaskiya Yunwa nake ji, tun safe ban kuma cin komai ba, kuma kince kar inje ko ina ban samu na fita naci Abinci ba"
Hararasa tayi tai gaba abunta, suna fitowa falo taga an shaƙe kan dining da Kulolin Abinci, wani murmushi tayi ta kalli Yusuf tace "jirani anan"
Ta juya ta koma part ɗinta, fitowa tayi hannunta ɗauke da magenta ta nufi dining.
Alama ta yiwa Yusuf da hannu yaje, ya nufi kan haɗaɗɗen dining ɗin da'aka shaƙe da kayan Abinci.
Tai masa alama da ya zauna, yaja kujera ya zauna tace "buɗe duk abunda kake so a gurin nan kaci"
Kallonta yay yace "Amma ranki ya daɗe, naga kamar baƙo aka shiryawa teburin
" bana son musu ko jayayya, umarni na baka ba shawararka nake nema ba" ta faɗa cikin faɗa da bada umarni.
Yusuf ya shiga buɗe Kulolin, Abinci ne kala kala kamar ba'asan zafin nema ba, yasan duk tsiya wanda aka shiryawa Abincin baze iya cinyewa ba.
Widad ta zuba kifi akan plate ta miƙawa magenta, Taja plate itama ta ɗiba ta zuba, dama Yusuf yunwa yake ji ga Abinci yayi daɗi nan ya dinga zurawa
(samun guri direba a dining 🤣🤣🤣)
Ramla ce ta fito itada Amal suna magana, me zasu gani Widad da mage ga direbanta suna cin Abincin da'aka shirya karɓar baƙon Ramla sannan baƙon Widad, Amal tayi saroro tana kallon Ramla.
A fusace Ramla ta ƙarasa dining ɗin kamarta fashe da kuka tace "Widad wane irin wulaƙanci ne wannan, ta yaya za'ayiwa baƙo girki ki zauna kina ci naga dai idan munyi Abinci ba ci kike ba, dan kawai ki muzgunamin kika yi haka? Saboda wulaƙanci kuma ace harda direbanki saboda tsabar tozarci"
Shidai Yusuf bece komai ba, Widad cikin ko in kula tace "Ramla me direban nan nawa yayi miki ne haka? Naga kuna takun saƙa sosai dashi, kina yawan manta wani abu Ramla, duk wanda yake aiki a ƙarƙashina matsayinsa ɗaya da duk wanda yake zaune a gidan nan ƙarƙashin kulawa ta, dan haka babu laifi dan na bashi Abinci ko?"
Cike da ɓacin rai Ramlah tace "Amma fa baƙo nayiwa, ta yaya zaki min haka? Ina laifin kice inda saura in zuba masa"
Widad tace "waini wannan baƙon gurina yazo ko gurinki?"
Ras gaban Ramla ya faɗi jin tambayar da Widad tayi mata,
"naga alamar gurinmu yazo nida ke, nasan kina tunanin me zakice masa ne, idan baki da abunda zaki gaya masa kice kinyi masa girki, 'yar masu gida tayi yadda take so dashi"
Hajiya Halima da ta fito ta riski rigimar tace "Amma Widad baki kyauta ba, ya za' ayi kidinga nuna direba yafi 'yan gida"
"Ni bana abu dan in kyauta dama, bana abu dan in birge kowa, muddin zan cigaba da saka doka ana watsi da ita nikuma zan cigaba da ɗaukar matakin daya dace, if i can recall a falon nan nayi kashedi akan a dinga bawa direbana Abinci, akayi fatali da dokar aka barshi da yunwa tun safe, nayi abunda ya dace ne, ga ragowa nan mun bari idan baƙon naki yana buƙata seya ci dan naga ƙirarsa ta mayuntace dama kamar baya ƙoshi"
Tai maganar tana kallon Ramla, tare da goge hannunta da tissue.
Da gudu Ramla ta bar falon tana kuka, ita kanta Amal ba taji daɗin abunda Widad tayi ba taji haushin hakan.
Yayi parking ɗin motarsa a harabar gidan ya fito daga motar, yana rufe motar tare da amsa waya, kamar an ce ya ɗaga kai ya hangota tana fitowa, fara ce sosai fari me ɗaukar ido, tana da matsakaicin tsayi sannan tana da shape me kyau.
Tabbas idan ba gizo idonsa ke masa ba wannan itace Yarinyar da Anwar yake kallo a hoto yana nuna masa, kenan itace Widad ɗin daza'a haɗa shi Aure da ita? '
Cigaba da Ƙarasowa Widad tayi, Yusuf na bayanta da jakarta a hannunsa, tana kallon Fahad suka zo zata wuce shi
"Widad Nasir Daula" Fahad ya kira sunanta.
Ta tsaya cak bata juyoba tace "Fahad Bulama"
"Amma kin san gurinki nazo kina kallona zaki wuce ki tafi"
A hankali ta juyo cike da izzarta ta ban mamaki, ta ƙare masa kallo sannan tace "banyi tsammanin kaine Fahad ɗinba ai, na ambaci sunan ne dan tabattar da kai ɗinne ko ba kaiba, dan abun da mamaki ace kaine Fahad ɗin, ina jinka faɗi abunda ke tafe da kai"
Fahad ya jinjina kai yace "tun ɗazu nake gidan nan ina jiranki, meze hana mu shiga daga ciki mu samu guri mu zauna se muyi magana"
"bani da wannan lokacin, yi maganar ka anan inajinka" ta faɗa tana kallon Idon Fahad.
Fahad be taɓa zaton haka Widad take ba, ta kai mace har mace sedai tana da girman kai da izza.
Ya kalli Yusuf yace "Amm ko zaka iya bamu guri, zamuyi magana"
"Ko da Bulama zanyi magana agabansa ake yi, dan haka cigaba da maganar ka" ta faɗa cikin isa
"Amma kin san Aure zamuyi, meyasa zaki dinga gayamin magana haka ba respect, har ki dinga kiran sunan mahaifina kai tsaye"
"Anƙi ayi respecting ɗin naka, Babana ma ina faɗar sunansa balle wani Bulama, kai a tunaninka kai namijin daze tunkareni a matsayin wadda ze aurane?, ɗan sake kallon kanka mana sannan ka kalli da wadda kake magana kasan niba ajinka bace, haka Bulaman be gaya maka yadda mukayi da shi bane? Bana soyayya ban yadda da ita ba kuna ba zanyi Aure ba, ana ƙoƙarin cusamin kaine kawai kuma bani da ra'ayin Auren namiji irinka, dama ka kai Namiji ne zan iya maleji, amma sam baka da ƙira da zatin da za'a kalleka a kiraka Namiji balle ace mijin Widad, ka sani koda ace Widad nada ra'ayin Aure bazan taɓa zaɓarka a matsayin miji ba, banga alamar nagarta da kamala a tare da kai ba, idan kana da zuciya kaje ka gayawa Babana Bulama baka son haɗin Auren nan, 'yar tasa bata sonka, in baka da ita kuma kace masa kana son Auren kaga yadda zamu ƙareta da kai "
Aiba Fahad ba hatta Yusuf jikinsa yayi sanyi da wannan mummunan cin zarafi da'akayi wa Fahad, koba komai ɗan uwansa ne namiji.
Gaba ɗaya Fahad kasa magana yayi, be taɓa tunanin haka Yarinyar nan take ba, duk wadda za'ayi sedai ayi amma seya auri Widad, sedai hakan yayi sanadiyyar ɓatawarsa da Anwar, ze tabbatarwa da Widad shi Namiji ne, Namijin ma irin wanda kowace mace keda burin samu, be tsaya ba ya shige motarsa ya fice.
Yusuf yana diving ya kalli Widad data cika tayi fam yace "Madam amma kamar abunda kikayi wa wannan bawan Allah be dace ba, bakya tunanin ya Alhaji zeji idan yaji labarin abunda kika yi, baki kyauta ba
"Yoseef!!!" karo na farko da Widad ta kira sunansa cike da gargaɗi, koda wasa bata taɓa attempting kiran sunansa ba, danshi be zaci tasan sunan nasa bama, sannan yadda ta faɗi sunan nasa yasha banban da yadda ake kiran sunan nasa, dukda Wasu lokutan hausa bata isheta ba, idan ta faɗi wani abun yasha banban da yadda ake faɗa.
"karka kusakura in dawo kanka, meyasa kake son shiga rayuwata, ban taɓa ganin mutumin da nake ɗagawa ƙafa kamar kai ba, shiumrun da nake maka Albarkacin mahaifina kakeci, kar in ƙara yin abu kace zaka yi challenging ɗina, duk abunda kaga nayi inada dalili karka ƙara challenging ɗina if not i will teach you a lesson you never forget "
Tai maganar a matuƙar fusace cike da gargaɗi.
" Allah ya huci zuciyarki, Allah ya baki haƙuri insha Allah ba zan sake ba"
Ya kaita gurin saloon kaman yadda ta buƙata.
Ramlah tayi kuka sosai akan wannan wulaƙanci da Widad tayi mata, seda idanunta sukayi jawur saboda kuka, ƙanwar bayanta dan kawai suna zaune a gidansu ake musu wannan wulaƙancin haka.
Mummy ta tako tazo gaban gadon Ramla ta zauna ta dafata tace "Am sorry daughter nasan....
"Mummy dan Allah ki ƙyaleni wallahi wannan karon sena ɗau mataki, haba abun ya isa haka wace irin rayuwace wannan muke a gidan nan se kace zamanin Bayi, wallahi sena ɗau matakin daya dace"
"A'a Ramla tynda kikaga na haƙura ban ɗau mataki ba kema haƙuri zakiyi, karki ja mana Asara goma da Ashirin, kin san taɓa wannan yarinyar dai dai yake da kawo ƙarshenmu a gidan nan"
"Niba ita zan taɓa ba, wannan sakaran zan nunawa kuskurensa, se yayi dana sanin zuwa gidan nan, zega abunda zan masa"
******************************
Alhaji Munir, Musa, Haruna se kuma Sale ne zaune a katafaren Falon suna tattaunawa, kana ganin fuskokinsu zaka san abunda suke tattaunawar yana da matuƙar mahimmanci a gurinsu.
Nurat ce ta shigo falon bakinta ɗauke da Sallama tana ɗauke da manyan kuloli a hannunta.
Gaba ɗaya suka bita da ido, kanta a ƙasa ta ƙaraso cikin falon ta durƙusa tana gaishesu, Amsawa sukayi gaba ɗaya Alhaji Munir yace "wai yanzu Nurat ce ta girma haka, gaskiya babu zumunci yakamata ace yaran nan suna zumunci suna a tsakaninsu"
Alhaji Haruna yace "gaskiya kam danni banda yanzu ma ban santa ba"
Nan sukayi ta surutunsu, yayin da Saleh yake gefe yaƙi cewa komai, Nurat ta gana hada hadar kawo musu Abinci ta juya bar falon.
"Wai kai Saleh bazaka saki jiki damu bane? Akwai fa riba a harƙallar nan" cewar Alhaji Musa
"Niba ribar ce a gabana ba ɗan uwana ne a gabana, yana gadon Asibiti kunsa an bashi guba ku kuma kuna nan kuna cin Abinci"
Alhaji Haruna yace "to kuka kake so muyi? Wallahi idan asirinmu ya tonu dagamu harshi sedai wasu bamu ba danme zamu bari ya fallasamu"
"shikenan a rayuwa kenan kowa kansa ya sani"
"ƙwarai kuwa ka bari harƙallar nan ta faɗa, idan ta faɗa ka samu kasanka seka fiddashi"
Alhaji Musa yace "Wasan yana dab da zuwa ƙarshe indai abunda muka tsara ya tafi daidai"
Alhaji Haruna yace "ƙwarai kuwa"
Suka maida kai suka cigaba da hirarsu yayin da Saleh gaba ɗaya abun duniya ya dameshi.
***********************************
Gaba ɗaya a sukwane Fahad ya koma gida, se huci yake kamar wani fusataccen kumurci, a falo ya tarar da mahaifiyarsa da ƙannensa, yazo ze wuxe fuuu Hajiya Sarah ta miƙe da sauri tace "lafiya kuwa Fahad?"
Ya daki kujera yace "harni za'a kalla ace ban kai namiji ba? Me take taƙama dashi ne haka? Ni Fahad Bulama har akwai Yarinyar da zata kalleni taci zarafina, dan kawai tana da kuɗi, toni na ganta kuma ina sonta sannan zan nuna mata ni cikakken namiji wanda mata je rububin samu!!! Meta taka da harta ke wannan izgilin da cin zarafi ga mutane? "
"kuɗi yaro wanda hausawa kance masu gidan rana, tabbas Widad ko ba ran Mahaifinta tana da kuɗin da zata taka wanda taso, kar ka manta da bazarsu muke rawa Fahad, ina son saka alkhairi ne da alkhairi shiyasa nake ƙoƙarin haɗaka Aure da ita, karka kusakura inji kayi mata wani abu wanda ze ɓata ranta kona mahaifinta, bazaka taɓa gujewa wannan Auren ba"
Alhaji Bulama ne tsaye a ƙafar benen dake falon, yana wannan maganar
" dan tana da kuɗi, kuɗin banza kuɗin wofi, akanta aka fara arziki? Aiko da ance a gujewa Auren bazan guje masa ba ina sonta tayi min, amma wallahi na aure ta she must pay for what she did, kai kafin in Aureta ma zan Wulaƙanta ta wulaƙanci mafi muni wallahi ni za'ayiwa cin zarafi irin wannan bata isa ba Wallahi "
Ya juya ya bar falon a matuƙar fusace
Hajiya Sarah cikin masifa tace " Alhaji seda nace maka bana son wannan haɗin, kawai ka kaimin yaro ana Wulaƙanta shi daga dawowarsa yaje gurinta zata ci zarafinsa haka, yarinya babu tarbiyya babu ta ido, na gaji da wannan abu"
"maza ki ziga shi, wallahi duk wanda yayi yunƙurin kawowa auren nan cikas zega matakin da zan ɗauka, sannan kija masa kunne, wallahi idan yayi yunƙurin yi mata wani abu ta ɗaureshi wallahi ba zan sa baki a sake shi ba, kinji na gaya miki ku bar komai a hannuna nasan matakin da zan ɗauka"
Yai maganar tare da barin falon ya koma benensa
Yusuf kam tunda aka masa warning yaja bakinsa ya tsuke har sukaje suka dawo be kuma cewa komai ba, amma yana jinsa a ƙoshe saboda garar da ya kwasa yau.
Se bayan isha'i ya baro gidansu Widad, yanata sauri ya koma gida
Ba zato kawai yaga an saka masa wuƙa a saitin Ƙirjinsa, tasayawa yayi cak ba tare da yayi yunƙurin guduwa ba.
Kamar waccan ranar mutanen da suka tareshi ne suka sake tareshi.
"munzone dan mu cigaba da jadadda maka har yanzu muna bibiyarka, muna jiran karɓar wannan abun daga hannunka muna nan muna cigaba da sa maka ido da duk wani motsinka"
"Wai wani abune wannan kuke son karɓa? Ku gayamin in karɓo in baku ku ƙyaleni"
"An gaya maka bamu da lissafi ne? Ba zamu gaya maka menene ba, amma da zarar ka samu abun zamu sani, kuma zamu biyoka mu karɓa"
Suka koma cikin motarsu suka tafi, sedai sunyi ganganci dan tuni Yusuf ya ɗauke lambar motar akansa.
Yau yaci sa'a basu dake shiba suka tafi suka barshi, gida ya tafi yana tunanin meye wannan abun da'aka damu se an karɓa a gurin Widad.
A haka har ya ƙarasa gida, Seda ya zauna sukayi hira da Ummansa dukda abubuwa sun cunkushewa ƙwaƙwalwarsa.
Ya gama cin Abinci ya tafi ɗakinsa, dole zeyi tracking ɗin lambar motar nan ya gano motar waye.
Da ya koma gida Ummansa taita mita akan daren da yake kaiwa a waje, yaita bata haƙuri yana rarrashinta sannan ya tafi ɗakinsa, ya nutsa a duniyar tunani sosai wayarsa ta fara ringing.
Lambar Sakina ce kamar kar ya ɗaga, sekuma ya ɗaga yasa a kunnensa tare da sallama.
"Yusuf baka yi bacci ba?"
"Eh banyi ba" ya bata amsa a taƙaice
"dama magana nake so muyi"
"Amma kinsan dare yayi ko?"
"eh nasani, maganar tana da mahimmanci ne a gareka"
Yusuf yace "to ina jinki"
"Yusuf akwai buƙatar ka dinga taka tsantsan da wasu abubuwan, akwai mutanen da suke nuna suna tare da kai amma a bayan idonka suna cin dunduniyarka, ba kowane mutum ne aboki na gaskiya ba"
Yusuf yace "nifa bana son irin wannan ƙananan maganganun, ni ina zaune da kowa lafiya"
"ba ƙananan maganganu bane ba, ka dai yi a hankali sannan karka yadda wani yasan sakamakon binciken da kake komai kusancinka dashi in ba yallaɓai ba shawara ce yakamata ka kula"
"Shikenan nagode" Yusuf ya faɗa cike da ƙosawa, shi sam baya san abunda ze haɗa shi da Sakina baya son mace mara kamin kai sam.
Amma nazarin maganganun ta ya shiga yi, wayarsa ce ta sake ɗaukar ringing har yayi tsaki ze kashe wayar yaga lambar Alhaji Nasir.
Cikin ladabi ya ɗaga wayar suka gaisa da Baban Widad, Alhaji Nasir yace "Yusuf meyefaru ɗazu da Fahad yazo gurin Daughter"
. Cikin kame kame Yusuf yace "Amm.. Yallaɓai yazo sun gaisa"
"Yusuf karka kareta, ka gayamin gaskiya me tayi masa? Wace irin karɓa tayi masa?"
"da alama dai beyi mata bane, ta ɗan dai nuna masa bata sonsa ne"
"Yusuf karka fara ƙarya saboda ka kare uwar ɗakinka, Bulama ya tabattar min da wulaƙanci tayiwa Fahad, kuma nasani zata aikata na kiraka ne dan in tabattar, saboda zan ɗau mataki na ƙarshe daya dace da ita, duk abunda nake dan gyaran rayuwar ta nake amma ta kasa ganewa, dan haka zan ɗau matakin da bata taɓa zata ba akanta wanda ze kasance hukunci na ƙarshe da zan yanke akanta "
Domin gyara sharhi ko shawara, feel free to contact me
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 19_20
Gaba ɗaya Yusuf ya dirircei yace "Amm... Amma Yallaɓai wani mataki zaka ɗauka haka akanta, ina fatan ba wanda ze mata tsauri bane?"
"Yusuf kenan, ka damu da al'amarin Widad haka nan naji na yadda da kai, shiyasa har nake saka a cikin abunda ya shafi rayuwar mu, na yanke shawarar tsayar da ranar Aurenta a ƙarshen wannan watan zuwa farkon wata me kamawa"
"Amma yallaɓai baka ganin hakan ze sake jefa rayuwarta cikin hatsari, duba da yadda babu Aure a tsarin Rayuwar ta?"
"Yusuf, Widad fa mutum ce kuma lafiyayyiya tana ƙin Aurene saboda wasu dalilanta da suke masu rauni a gurina, bana so in mutu in barta cikin kaɗaici, nasan Bulama baze taɓa barin ɗansa ya Wulaƙanta Widad ba ko bayan raina, dan Allah ka cigaba da yimana addu'a, Amma insha Allah ko ba taso zan ɗaura mata aure karo na farko a rayuwata da zan ɓata mata rai, amma ina fatan hakan ya zama alkhairi a gareta, Insha Allah gobe zuwa jibi zan dawk"
"shikenan Yallaɓai, Allah ya tabattar da alkhairi ya dawo da kai lafiya"
"Ameen Yusufa nagode sosai"
Tunda sukayi Sallama da mahaifin Widad abun duniya ya damu Yusuf, ji yake matakin da mahaifin Widad ke shirin ɗauka tamkar ƙarasa rugurguza rayuwar uwar ɗakinsa ne gaba ɗaya, matakin yayi tsauri sosai, haka nan yaji wani irin matsanancin kishi na taso masa game da Widad ɗin.
Dafe kansa yayi tare da faɗin "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, Allah ka tsareni da sake faɗawa hatsarin Soyayya, Allah yasa tausayinta kawai nake ji, tabbas idan na fara son Widad zan shiga matsala fiye da wadda nasha a baya"
Bacci kam se Ɓarawo ne ya kama Yusuf.
Kwana biyu a tsakani Yusuf yana zuwa gidansu Widad amma ba wani aiki da yake yi, kuma sam baya ganinta.
Abubuwa sun ƙara cakuɗewa Yusuf, tunani kala kala a zuciyarsa amma zuciyarsa tafi fargaba akan hukuncin da Daddy ya yanke ɗauka akan Widad.
Ya ɗakko wayarsa yana ɗan duddubawa kawai yaga message ya shigo wayarsa, anyiwa ma'aikata canjin gurin aiki ciki harda Abbas, an maida Abbas aiki a kudancin Nigeria, abun ya ɗaurewa Yusuf kai sosai, mafi akasari anfi yin wa mutum wannan canjin aikin ne, kodai dan wani mahimmin bincike, ko ƙarin girma kokuma dan hukunci ga wani laifi da ya aikata, sedai shi a ganinsa babu ɗaya da Abbas yayi wanda zesa ayi masa wannan transfer.
Ba shiri Yusuf ya bar gidansu Widad ya tafi gurin aikinsu, kai tsaye ofishin Oga Suleiman ya wuce, gaje suka gaisa Suleiman yace "Yusuf naga aikin daka turomin, kayi ƙoƙari sosai Yusuf sannan ina taya ka murna da sabon muƙaminka"
Yusuf cikin rashin fahimta yace "Yallaɓai nida ban fahimci abun nan ba, me Abbas yayi za'a ɗauke shi daga gurin nan akaishi wata uwa duniya?"
"Nima ban san meyasa hakan ta faru ba, sedai daga sama ne akayi wannan transfer sannan ka samu ƙarin matsayi"
Yusuf ya dafe kai yace "Yallaɓai babu yadda za'ayi a bar Abbas a gurin nan ne? Bekamata a raba shi da iyalinsa ba zuwa wata uwa duniya ba, ni dai banji daɗin hakan ba, zanyi kewar abokina kuma ɗan uwana"
Suleiman ya jinjina sauƙin kai irin na Yusuf yace "ya za'ayi se haƙuri haka sha'anin aiki yake"
Jiki a sanyaye Yusuf ya baro office ɗin Suleiman ya nufi na Abbas, se sarawa Yusuf ake ana masa murna amma shi sam hankalinsa yana kan wannan transfer da'akayiwa Abbas.
Da sallama ya shiga Office ɗin ya tarar da Abbas yana ta tattara kayansa dake Office ɗin.
"Abbas ya akayi haka? Me yasa akayi maka transfer haka ta gaggawa?"
Abbas yace "nima ban sani ba Yusuf, jiya aka sanar dani kuma akace lallai gobe in Allah ya kaimu in tafi"
"yanzu babu wani abu da zamu iyayi a fasa wannan transfer ɗin?"
"Yusuf nayi duk ƙoƙarin da zanyi amma abun ya gagara"
Gaba ɗaya Yusuf ya rasa abunda yake masa daɗi, dan har cikin ransa yake jin rabuwa da Abbas ɗin, dan yana jin Abbas tamkar wani ɗan uwansa.
Wayar Yusuf ce ta fara ringing, ya ɗakkota daga aljihunsa ya ɗaga.
"Yusuf mai gida ya dawo yanzun nan, yace a kiraka"
"Shikenan gani nan zuwa"
Yusuf ya kashe wayar yace "Abbas zanzo gida insha Allah, zan ganka muyi sallama"
Abbas yace "Yusuf na ta yaka murna, an ƙara maka matsayi"
Yusuf yace "Abbas sam bana murna da wannan ƙarin matsayin, ni tafiyarka ce damuwa ta, bari inje wannan kiran zan nemeka Insha Allah"
Sukayi musabiha, Yusuf ya juya ya fita, Abbas ya raka bayan Yusuf da harara tare da yin ƙwafa.
Tun daga harabar gidan Yusuf yaga manyan motoci da alama bayan dawowar maigidan anyi baƙi a gidan.
Kansa tsaye ya nufi cikin gidan, a falon ya tarar da Alhaji Nasir, Bulama, Fahad Hajiya Halima da iyalanta.
Yusuf ya ƙaraso yana gaishesu, Alhaji Nasir yace "ƙaraso kusa dani Yayana, nace a kiraka aka cemin ka fita ne"
Yusuf yace "eh naje wani uzuri ne"
Fahad se wani hararar Yusuf yake, shiko Yusuf ya basar kamar be gani ba.
Tsit falon yayi na wani lokaci, Yusuf ya rasa dalilin hakan, yana ɗaga kai yaga gimbiyar ta fito daga ƙofar part ɗinta, da alamu wannan zaman fitowarta ake jira, seda ta tsaya ta ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya sannan ta ƙaraso cikin takunta na isa, ta samu kujera ɗaya ta zauna ba tare da ta kula kowa ba.
Alhaji Nasir yace "daughter"
"Na'am Daddy"
"waye wannan?" ya nuna mata Bulama
"Alhaji Bulama"
"kin san matsayinsa a gurina?"
"Just a long time business partner to you"
"he is more than that to me, kuma kin sani danme zan baki umarni kiyi fatali dashi? Duk abunda mukeyi munayi ne dan rayuwarki, danme zaki ciwa Fahad mutunci? A gaban Yusuf komai ya faru, daughter nasan duk abunda kike yi, ina ƙyale ki ne saboda nasan halinda kike ciki na maraici, amma kina zarce ƙa'ida wasu lokutan, daughter farincikin ki muke fata shiyasa muke son aurar dake"
Gaba ɗaya Widad ta ɗauke kai daga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 35