Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daze mun" "Kinga saurara, ni babu abunda zan iyayi akan wannan al'amarin, wannan babban case ne da yake buƙatar bincike, idan bashi da laifi zasu sake shi fa" Hajiya Halima tace "Shikenan nagode sosai da abunda kukayi min, wato na gama yi muku amfani, zaku watsamin ƙasa a ido, zaku ga abunda zanyi" Ta juya fuuu tayi waje kamar zata tashi sama, tana tafe tana banbami, ofishin Bulama ta tafi, ta tarar yana shirin fita, ya kalle ta yace "Halima lafiya kuwa?" "karka ƙara tambaya ta ko lafiya, lafiyar kenan kana nan hankalinka kwance, ni kuma nawa a tashe ko baccin kirki bana samu, na zama kamar mahaukaciya, ɗana yana can a tsare, kun nunamin halin ko in kula, kun nuna baku damu da halin da nake ciki ba" Bulama yace "Nikam Halima kina bani mamaki, ɗanki fa ɗana ne, nima nawa hankalin ba'a kwance yake ba, muna iya ƙoƙarin mu, amma abunda ake gayamana shine, ana zargin da sa hannun Anwar a wannan abu daya faru, kuma duniya ta kasa kunne taji wani mataki za'a ɗauka, me kike tsammani idan aka ji da sa hannuna aka saki Anwar? " " Kaga sauraramin dan Allah, bana son maganar banza data wofi, na sani ka sani Anwar baze iya aikata laifin da ake tuhumarsa ba" "A'a karki shedeshi, ba'a shedar ɗa a zamanin nan" "Bulama, na gama magana da kai, zanje inyi abunda ya dace kawai" Bulama yace "abunda ya dace kamar yaya?" "Ka zuba ido zaka gani, bar ganin kai ɗan uwanane zan iya yin komai akan ɗana, na gaya maka" Bulama yace "hmm kibi a sannu dai, kin san ido ya fara dawowa kanki yadda kike wadaƙa da wasu daga cikin kadarorin mijinki? Mutane sun san me kike aikatawa, ki sani tsalle ɗaya ke kai mutum rijiya, amma se yayi dubu be fito ba" Tsaki tayi, ta ɗau mukullin motarta tace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, nasan abunda nakeyi" Tai waje abunta, tana fita Bulama ya ɗau waya, ya danna yasa a kunnensa yayi shiru, can kuma yace "Yawwa kana jina da kyau, ina son ku ƙara tsananta tsaro da sa ido akan yaron nan Anwar, under no circumstances zaku bada belinsa, ku matsa se ya faɗi inda Daula yake, dan uwarsa ba abunda ba zata iya ba" Daga cam ɓangaren yace "Ok sir an gama Insha Allah" Bayan barin Hajiya Halima Office ɗin Alhaji Musa, su Alhaji Haruna suka dira, dukda haushinsu da Musa yake ji, amma ya maze ya sakar musu fuska yace "kun san yanzun nan wannan mahaukaciyar ta bar gurin nan" Alhaji Haruna yace "wa kenan?" "Hajiya Halima mana, tazo nan tana ta banbami, wai munƙi saka baki a sakar mata ɗa" Alhaji Munir yace "ƙyale wannan mahaukaciyar, ni wata shawara nazo mana da ita" Suka tattara masa hankalinsu, suna saurarensa "Abunda nake gani shine, mu samu lauyoyin Daula, mu siye su, su saka hannu su fitar mana da wasu daga kadororinsa, a sasu a kasuwa a karya su, sannan ayi takaddun ƙarya, muce muna binsa zunzurtun bashi" Alhaji Haruna yace "kayi magana mekyau, sedai abunda ka manta shine, lawayoyinsa basu san kan dukiyarsa kamar yadda wannan koɗaɗiyar 'yar ta sani ba, ta san komai tasan inda komai yake" Alhaji Munir yace "to tunda yanzu ba ita babu ubanta aise muyi yadda zamuyi mu kwashi rabonmu, ko so kuke se wannan mahaukaciyar matar tasa ta ƙarar da komai ita da' ya'yanta? A ɓoye fa se saida kadarorinsa sukeyi, haka zamu zauna mu zuba ido." Alhaji Musa ya nisa yace "duk naji ta bakin ku, kuma kowa yazo da magana me kyau, zamu jarraba lawyoyin suma, danni yanzu kuɗin tsayawa takara nake nema" Kallonsa sukayi gaba ɗaya sukace "kamar ya tsayawa takara?" "kamar yadda na gaya muku, bazan zauna bani ga tsuntsu bani da tarko ba" Alhaji Haruna yace "hala ka manta da baƙin fentin da kake da shi, a dalilin Daula?" "ina fa na manta, sedai a ƙasar nan indai kana da kuɗi ba abunda baze yuwu ba" "Amma baka ganin hakan, ya saɓa da Yarjejeniyar mu, idan kayi haka kamar ka zame daga cikinmu ne, kuma me zaka cewa Bukar?" "Bukar ubanane, ko haifata yayi? Ba gudu ba ja da baya, ina tare da ku amma tabbas zanyi takara" Gaba ɗaya Yusuf ya fara jin kunyar mutanen da yake ja salla, musamman idan ya tuna abunda Widad tayi a gaban su, tunda su hakan kamar baƙon al'amarine a gare su, haka nan ya ɗan dinga basarwa, sukayi sallar magariba da isha'i suna ta sake duba shi. Widad jin shiru Yusuf be shigo ba, yasa ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan gidan Hansai tace masa "kaga ɗan jeka waje ka cewa Yoseef in jini nace, baze dawo ba se sauron ya sake cizonsa yazo ya kwantamin?" Gwaggo dake alwala tace "A'a kul kaje ka faɗi haka, kace tace 'dan Allah ya shigo gida, kar sauro ya kuma cizonsa'" Widad tace "to ai kusan abunda na faɗa kika maimaita" Gwaggo tace "A'a ke naki umarni da kashedi kika yi, aishi miji abun lallaɓawane da tattalawa, ki kalli yadda kika damu da bashi da lafiya, ki dinga masa magana da girmamawa kinji Amarya, yana da kirki mijinki, kema ki dinga tausasa harshen ki a kansa" Widad tace "To Hajiya Mama" Gwaggo tace "ni a Hajiya, to me rai baya fidda rai da rahama, amma abun da wuya" "Insha Allah indai da rai da rabo, zaki je saudi Arabia in dai Allah be ɗau rayuwar wani daga cikin mu ba, idan muka koma gida lafiya zaki je ƙasa me tsarki" Tsaki Hanne tayi tace "san a sani, ji wata ƙarya kuma da son nuna iyawa, karma kisa rai ana gayamiki gaibu" "Ke! Ki kiyayeni, dake muke taɗin, ina ruwan ki Hanne ki kiyayeni fa" Widad ta juya kawai ta koma ɗaki, ta ɗakko ƙaramar fitilarsu ta kunna, batirin ma ya fara sanyi. Ta zauna tayi shiru tana tunani, sallamar Yusuf ce tasa ta ɗago ta amsa masa, yaje kusa da ita ya zauna, daya kalleta se tausayinta ya kama shi yace "gani naji ance kina nemana" "shine tun la'asar kaƙi dawowa, se sauro ya kuma cizonka ko?" "Ai na warke, Alhamdilillah" "dan ka warke shine se kaje, ka kuma kwaso wani zazzaɓin, kazo ka ɗagamin hankali" "Insha Allah na warware ai, ance jinina ma yayi ƙasa, dole in dinga cin ganyayyaki" "Sannu kaji jiki ai" "Gaskiya muje ki dawomin da jinina dana baki" "wai jininsa, jinin naka ma duk malaria ya ƙara samun zazzaɓi, zan biya ka jinin ka harda riba ma" Dariya Yusuf yayi yace "ni iya nawa nake so, bana son naki danni bana son jinin me taurin kai" "kai kai, nice me taurin kai? Zaka ga taurin kai' Kwanciya yayi a kafaɗarta yace " dan Allah a sake rungumeni mana, i need your body warm " Ture shi tayi tace 'kaje kaji ɗumin bargo mana" Cikin kwantar da kai yace "A' a ni gaskiya naki nake so, ai naga yau ke kika rungumeni, idan muka koma gida sena gayawa Ummana, nima ince kina rungumeni" Widad tace "ai kai ka fara bani ba, ka koyamin abunda ban iya ba" Dariya Yusuf yayi yace "nayi mamakin yadda kika damu da rashin lafiya ta My queen" "A cikin AƘIDATA babu butulci, bana manta alkhairi, bazan taɓa manta wahalar daka sha saboda rayuwa ta ba, idan na nuna halin ko in kula ga kafiyarka to tabbas banwa kaina adalci ba, dukda ana faɗin bani da kirki, banj da mutunci amma bana manta alkhairi" Yusuf yace "waye yace miki baki da kirki, kina da kirki uwaɗakina" "Hmm yoseef kenan, ka dena kareni danka burgeni, amma nasan bani da kirki kamar yadda da yawa mutane ke faɗa" "ba kareki nake dan na burgeki ba, ina faɗa miki gaskiya ne kawai, amma kince bakya manta alkhairi, amma meyasa bakwa jituwa da Saleh, dukda irin taimakonmi da yayi?" "saboda bana yafiya ga mutane ma'abota fuska biyu, da fari mahaifina ya yarda da shi da ɗam uwansa, amma ya koma ɓangaren maƙiyanmu, yanzu ya kuma dawowa ɓangaren mu, wani tabbaci muke dashi na muma baze sake juya mana baya ba? Duk yardar da nayiwa mutum, duk girman Alkhairin da yayumin, muddin yaci amanata koya min ƙarya to tabbas ze shafe dukkan alkhairansa a idona, bana yafewa mayaudari da maƙaryaci ko me fuska biyu, wannan itace AƘIDATA!!! TOFA! Alhamdilillah nan na kawo ƙarshen kashi na ɗaya a littafin AƘIDATA, Ɗanɗano daga Littafi na biyu (idanunta sunyi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyaf da kanta ta shafi ciknta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi prison, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don in ganta tawa, amma maƙiyana sun na ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine...............) Karku bari a baku labari, saƙar labarin mukayi a na farko, tufaka da warwarar gami da cakwakiyar suna littafi na biyu dana uku, anan gwaramar take SHINE MEYE LABARIN YUSUF? MEYE LABARIN WIDAD? WAYE MAMALLAKIN ABUNDA AKE NEMA A HANNUN WIDAD? MEYE ABUNDA AKE NEMAN? WAYE YA SACE DAULA? SHIN ZASU BARO ƘAUYEN NAN? ZASU KOMA GIDA DA WANNAN AUREN? YA ZATA KAYA TSAKANIN WANNAN MANYAN ALHAZAI? YA WIDAD ZATA YI IDAN TA GANE YUSUF JAMI'IN TSARO NE YA MATA ƘARYA? Akwai cakwakiya me tarin yawa karku bari a baku labari, ga masu buƙatar siya Normal group duka littafi biyun ₦300 Idan kuma ɗaya zaki siya ₦200 VIP ₦ 500 Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700 Account Number Aisha Adam 0009450228 Ja'iz Bank Ko katin MTN banda VTU please A turo evidence of payment ta 07063065680 Zan fara posting ɗin littafi na biyu dana uku, ranar 20 ga watan October Masu neman complete zasu sameshi ranar biyar ga watan November insha Allah Domin gyara, sharhi ko shawara Ayshercool. 07063065680 Nagode da ƙaunar da kuka nunamin An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 35 of 35