Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani mummunan zare ido tare da sauke numfashi yana kuma maimaita sunan nata. Widad ta wuce mota Yusuf ya bita suka tafi, suna tafe tana ƙwafa tareda yin tsaki jefi2 kallon ta kawai Yusuf yake. Suka isa gida ta buɗe murfin motar ta fice abunta, Yusuf ya ɗebo kayan ya bita dasu, matar gidan tana falo tana kallo, Yusuf ya shigo yabi bayan Widad har ɗakinta ya ajiye mata kayan, ze juya ya ɗebo sauran tace "ɗan tsaya" Yusuf yaja ya tsaya tazo ta duba kayan, ta ɗakko wata Jaka da turaruka a ciki ta ajewa Yusuf, cike da iko da kashedi tace "daga yau karka ƙara saka wannan banzan turaren da kake sawa in zaka zo inda nake, ga wannan turarukan kar in kuma jin kasa wannan turaren dan yana samin tashin zuciya ina fatan ka gane?" jinjina mata kai yayi alamar Eh. Ya ɗau ledar turaruka ya fita ya kwaso mata sauran kayan ya kawo mata, yana zuwa ya tarar ta shiga wanka, dan haka ya haɗa da ledar turarukan da ta bashi, ya ajiye mata akan gadonta yai ficewarsa. Bayan Yusuf yayi sallar Azahar ya nemi guri ya zauna a inda suka saba zama da sauran ma'aikatan gidan, Isa mai gadi yace "Yusuf manyan ƙasa, gaskiya ka ciri tuta a gidan nan, ina jinjina maka" Yusuf yace "Mena yi na cancanci jinjina haka"? "Ahh irin yadda kake jure cin mutuncin wannan yarinyar mana, naga da alama kaman kai bata yi maka wulaƙsncin, amma dukda haka kana haƙuri wallahi yarinya se kace sheɗaniya, zuciyar ta babu Imani se miyagun Aƙidun turawa to aibtama ci uwar turawa wannan" Yusuf yace "kaga dakata Isa, kana gidan mahaifinta kana cin Arzikin su sannan kuma ka dinga zagin ta? Aiba'a haka a rayuwa, ni duk wannan abubuwan da kuke faɗa akan ta ni bana gani, danni ba ta yi min ba" Isa yace "ni na rasa me yasa kullum kake ƙoƙarin kare ta, da anyi magana ka hau kare ta, ina tausayawa ranar da zata maka mugun halin nata, naga yadda zaka yi ai" "kaga Isa abar wannan maganar dan Allah" Isa yace "shikenan tunda haka kace, nikam nace ina Sani kuwa? kwana biyu baya zuwa gidan nan ko a waya bana samun sa, nasan kai kuna haɗuwa tunda unguwar ku ɗaya" Yusuf yace "waye ya gaya maka unguwar mu ɗaya?" "Ai gani nayi ɗan uwanka ne shiya kawo ka gidan nan, dan haka nayi zaton unguwar ku ɗaya" Yusuf ya murmusa yace "A'a ba unguwar mu ɗaya ba" "to kai a wace unguwa kake? Ko ince inane ƙauyen ku? Dukda baka yi kama da 'yan karkara ba, ni mamaki ma nake yadda matashi kamar kai yake aikin direba" Yusuf yayi murmushi yace "Isa kenan, dama su' yan ƙauyen wata kamace dadu ta daban ne? meyasa ka damu da sanin unguwar da nake?, indai Sani ne zan nemo maka shi dukda ba unguwar mu ɗaya ba, zan kawo maka shi har nan yazo" Yusuf ya basar da zancen yaƙi gayawa Isa unguwar da yake. Duk wasu hikimomi Isa yabi, Amma Yusuf ya nuna masa ƙwarewa irin ta jami'in sirri ya basar da zancen ya shiga wani. Daga ƙarshe ma ya miƙe ya bar gurin, Isa yace "wannan anyi Jarababbe me taurin kan masifa, ƙiri Ƙiri yaƙi gayamin, amma zaka ga tsiya, in kasan wata baka san wata ba, zan biyo maka ta inda koka ƙi Allah seka faɗa" Share please 🙏🙏🙏 Masoya masu Comment ina godiya, Allah ya bar ƙauna 😍 😍 😍 ku sani yanzu aka fara wasan, amma gaskiya idan ba'a Comment yadda nake so zan ɗau matakin da ya dace, dan Allah idan kin karanta idan kin san Tanks kawai zakice koki turamin sticker ki riƙe abun ki please 🙏🙏🙏 Domin sharhi, gyara ko shawara ƙofata a buɗe take, feel free to contact me, sedai in ban buɗe saƙon da wuri ba ayimin afuwa, ina godiya 😍 Ayshercool 07063065680 _*AƘIDATA*_ PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) * And now *AƘIDA TA * I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends ELEGANT ONLINE WRITER'S PART1 Page 6 Widad kam koda ta fito daga banɗaki, da jakar turarukan nan data bawa Yusuf ta fara yin arba akan gadon ta, ta ƙarasa a hankali ta duba, sune dai turarukan da ta bashi, "lallai wannan ɗan rainin hankali ne, ni zan bashi abu yazo ya ajiye min?" Fita tayi falo ba kowa dan haka ta wuce part ɗinsu Amal, tana zuwa ta tarar da su a kitchen suna ta girki suna hirarsu, Wai Ramlah zata yi baƙi, se hada hada suke da kaji da sauran kayan masarufi. Basu san da zuwan Widad ba se muryarta da suka ji cikin isa tace "Ramlah kije gate ki kiramin driver na yanzu" Cike da ɓacin rai, ba tare da Ramlah ta kalleta ba tace "to" Haka Ramlah ta fita tana ƙunƙuni ta nufi bakin gate. Tana zuwa ta tarar Yusuf ya siyo Abinci ze fara ci, Ramlah tazo kansa ta tsaya ta ƙare masa kallon up and down a wulaƙance, ta kalli gurasar gaban sa ta masu balango da nama ta kuma kallon sa ta taɓe baki ta ɗanyi tsaji taxe "kai kazo inji waccan yarinyar" Banza Yusuf yayi mata ya cigaba da ƙoƙarin cin Abincin sa. "Wai baka ji ne?" ta masa magana cikin tsawa. Nura direban Alhaji yace "Yusuf da kaifa take magana" Yusuf ya ɗago ya kalli Nura yace "yawwa Sunana ka ambata, meze hana ta kirani da Sunana dan me zata cemin kai, kuma ni ban san wata yarinya a gidan nan ba" Mamakine ya kama Ramlah, dama yana magana haka da wulaƙanci amma yake iya tsayawa Widad taci zarafin sa? Ba mamaki saboda kwaɗayin abun duniya kar a kore shi shiyasa yake shnaye wulaƙancin Widad, amma har ita wannan talakan ze buɗe baki ya gayawa magana a fusace tace "kai saurara bazan kira sunan naka ba, uban waye kai da zaka dinga tambayar ban san sunan ka bane? Kai a wa? Ka kiyaye ni wallahi bana son shirme idan kace zakamin rashin mutunci zaka ga abunda ze biyo baya, sannan idan kaga dama kaje, in baka ga dama ba karka je ka san sauran" Yusuf yayi kaman ba da shi take ba ya ci gaba da antaya gurasar sa. Ran Ramlah ne yai mugun ɓaci da ganin wannan rainin hankalin na Yusuf, ƙwafa tayi ta koma cikin gida. Nura yace "Yusuf dan me zakayiwa Ramlah haka? So kake kaja wa kanka a kore ka?" Yusuf yace "Nura kenan, to a korenin mana seme?" ya ci gaba da cin gurasar sa seda ya gama cin Abincin sa, Sannan ya miƙe ba tare da ya kuma cewa komai ba ya nufi cikin gidan. Yana zuwa ya tarar da hakimar ta ɗora kafarta akan centre table tana jiran isowar sa. Yusuf ya ƙaraso cikin girmamawa yace "gani ranki ya daɗe" Widad tace "se yanzu ka ga damar zuwa? Na tura a kira ka kace bazaka zo ba seka gama abunda kake?" Da confidence ɗin sa yace "bance ba zanzo ba ina cin Abinci ne lokacin" "ba tun ɗazu aka kaiwa ma'aikatan gidan nan Abinci ba?" "Aini ban sani ba munfita tare da ke, kuma ni ba'a taɓa Abinci ba" Tsuke Fuska Sosai Widad tayi tace "Ramlah kiramin larai" Ramlah ta juya ta tafi kiran larai, Widad ta kalli Yusuf a wulaƙance tace "me kake nufi da in baka abu ka ajiyemin kayi tafiyar ka? Me kake nufi da hakan? Harni zan baka abu saboda wulaƙanci da girman kai irin na talaka harni zaka gwadamin halin naku na talakawa na girman kan banza akan abunda baku dashi" Yusuf ya ɗanyi murmushi yace "ba girman kai bane Madam, bakomai ne yasa na ajiye ba face abunda kika bani yafi ƙarfin talaka kaman ni in saka, duk wanda yaji ƙamshin wannan rantsatsun turarukan to tabbas zan zama abun tuhuma ga al'umma, kiyi hakuri wannan turaren seke" Wani irin murmushi Widad tayi wanda ita kaɗai tasan ma'anar sa, sannan ta tsuke fuska tace "Amma fa ka iya rainin wayo sosai, shikenan amma idan na kuma jin tashin wannan banzan turaren a jikin ka kasan sauran" "Insha Allah bazan sake saka turaren da shugaba ba taso ba" Ramlah ce ta dawo tareda 'yar aiki larai na biye da ita, jikin larai se tsuma yake tazo gaban Widad ta durƙusa. "Larai Me yasa ake hana direba na Abinci?" Larai ta kalli Ramlah a ɗan dirirce sannan ta dawo da kallon ta kan Widad za tayi magana, Widad tace "Idan kikamin ƙarya sena hukunta ki" "Wallahi ranki ya daɗe Hajiya ce tace kar a sake a bashi Abinci, ba a cikin ma'aikatan gidan nan yake ba" Widad tace "hmmm tunda ita ta siyo ta kawo ko? Ke Ramlah kije ki gayawa mahaifiyarku, ko kare na ajiye a gidan nan ya zama dole a bashi duk abunda yake buƙata tunda lokacin da'ake tara dukiyar gidan nan bada gumin ta aka tara ba, sannan.... Yusuf katseta ta hanyar cewa "Amma uwa ɗakina ina ganin idan kika yi haka baki kyau ta ba, ki bari... "Shut up....., do you think am doing it because of you?, let me tell you something, ba nace a baka Abinci a gidan nan dan komai ba sedan kauce wa hatsarin dake tattare da hakan, karka manta YOU SIGN ON YOUR DEATH CONTRACT ya rage naka kula da rayuwar ka" Ta miƙe ta nufi part ɗinta cikin takunta na isa. Jiki a sanyaye Yusuf ya fice yana mamakin waime take nufi da wannan death contract ɗin ne? ********************** Manyan Mutane maza su uku, zaune a wani ƙaton falo, da ganinsu kasan suna da kuɗi saboda yanayin suturar jikin su, zaune suke suna tattaunawa fuskarsu ɗauke da damuwa Ɗaya yace "nifa Al'amarin nan ya fara isa ta, tsawon shekaru muna fama akan abu ɗaya, amma abu yaƙi ci yaƙi cinyewa nifa na fara karaya" "haba Alhaji Haruna, akan me zaka karaya haka? Ai ba gudu ba ja da baya, se burinmu ya cika se mun samu abunda muke nema, abun baƙin cikin yarinyar nan muguwar gaddamammiya ce, wani irin mugun Aƙida ne da ita tamkar tasan abunda muke nema, sam bata da wani mutum data aminta da shi ya shiga jikin ta balle mu samu abunda muke so" Alhaji Haruna yace "kai bari kawai Alhaji Musa, Yarinya kaman ba jinsin mutane ba, duk na kusa da ita ba wanda bamu bi ba amma bamu samu abunda muke buƙata ba, Kalli yadda shirin mu na jiya ya wargaje. "Hmmm bari kawai kaga jiya yadda ta wulakanta Jamil a harabar Store ɗin nan, ina zaune a mota na ɗauka zeyi ƙoƙari ta bashi lambar wayarta amma ta fasa wayar ta ƙare masa zagi a gaban mutane" Alhaji Haruna ya girgiza kai "yanzu meye abunyi ko mu kashe yarinyar nan mu huta mu kama Nasir daula ta ƙarfin tsiya mu samu abun nan" Alhaji Munir yace "kul Haruna, in baka iya kama ɓarawo ba shi seya kama ka, wannan ai wauta ne, kasan yarinyar nan a gurin sa ta gaji wannan taurin kan, idan muka kashe ta tamkar mun kashe Nasiru Daula ne, kuma kasan akwai hatsari sace shahararren mutum kaman Nasiru a ƙasar nan, dan haka ita yarinyar ya kamata mu ci gaba da farauta " Alhaji Musa yace " to sace ta zamuyi ko yaya? Duk hanyoyin da ya kamata mubi munbi amma abu ya gagara, idan muka bari ta koma ƙasar waje aikin mu ze kuma komawa baya ne" "to sace ta zamuyi ko kuwa?" Alhaji Munir yace "A'a a yanzu ba sace ta ya kamata mu yi ba, zamu ci gaba da bin diddigin ta, kun san sace wannan yarinyar se anyi kyakykyawan shiri" Alhaji Musa yace "Anya Alhaji Bulama be san komai akan abun nan ba? naga amintaccen Nasiru Daula ne ko zamu gayyato shi cikin mu?" "Taɓɗijan ashe tamkar mu fita mu tonawa kanmu asiri ne, kome zamuyi kar mu shigo da bare cikin mu, zamu ci gaba da yin zagon ƙasa ne a sirri har mu samu abunda muke so" Haka suka ci gaba da tattauna wa a tsakanin su. ********************** Yusuf na bakin gate ya bada hankalin sa akan wayar sa, Amal ta fito yana ganin ta yai murmushi tace "Sannu da hutawa" "Yawwa ranki ya daɗe ya gidan?" "lafiya ƙalau, Widad na nemanka" "to shikenan muje" ya tashi ya bita har part ɗin Widad, suna shiga Widad ta tsira musu ido, ta sauke idon ta akan Amal ta ƙura mata ido ko ƙyaftawa ba tayi, Sum sum Amal ta fita ta basu guri, zuciyar ta ɗauke da zazzafan kishin barin Yusuf daga shi se Widad a ɗaki. Widad ta ƙare Yusuf kallo kaman bata sanshi ba kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai, dogon wando ne a jikin ta da vest ko kunya ba taji a irin shigar data keyi Widad tace "zan fita anjima ƙarfe huɗu zanje gurin birthday, ƙarfe huɗu, in kaga dama ka tafi yawon ka" Ya jinjina mata kai yace "Insha Allah zan kiyaye lokacin" daga nan ya fice. Ƙarfe huɗu saura kwata akayi sallar la'asar, Yusuf ya gabatar da sallar la'asar, sannan ya shiga cikin gidan. Yana zuwa ya tarar da Alhaji Nasir da iyalan gidan, gefen sa ga trolley alamun tafiya zeyi. Yusuf yace "barka da rana Yallaɓai" Alhaji Nasir yace "Yawwa Yusuf ya aikin, ya haƙuri da Daughter"? Murmushi Yusuf yayi yace "ai mune take haƙuri damu, Aiki kuma Alhamdilillah, mungode Allah" Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "tafiya ta kamani zani Paris, se shagwaba take wai bazan tafi ba, Yusuf ga amana ta nan, na bar amanar daughter na a hannun ka, har inje in dawo kar a bari tayi kuka, idan tana buƙatar wani abun akula ayi mata dan Allah" Widad da sauri ta kalli mahaifin ta sannan ta kalli Yusuf a wulaƙance tace "Allah ya kiyaye Ina da komai da nake buƙata, dan haka bana buƙatar taimako daga gurin kowa balle talaka kaman direba na" Gaba ɗaya suka ɗauke wuta, shi kansa Alhaji beji daɗin abunda Widad ɗin ta faɗa ba. Yusuf kuwa yai murmushi yace "indai wannan Amanar ce Alhaji na yadda na karɓa, Insha Allah zaka je lafiya ka dawo ka tarar da ita, Allah ya bani ikon kula da ita" Alhaji Nasir yace "Ai dama nasani duk me sunan Yaya na mutumin kirki ne, ban taɓa ganin Yusuf wanda ba shi da kirki ba, Allah yayi wa Rayuwar ka Albarka" Yusuf ya amsa da Ameen Ita kuwa Maman su Ramla tamkar ta haɗiye zuciya, wai direba ake bawa amanar 'yar masu gida, tunda ita cinye ta zata yi ai dole a ce direba ya kula da ita, shikenan direba ya kula da ita in yasan wata ai be san wata ba. Ba ƙaramin haushi take ji yadda Alhaji Nasir ke nuna wa Yusuf kulawa ba. Yusuf ya ɗaukar wa Alhaji Nasir trolley ɗin sa suka fito harabar gidan, Nura ya taho jiki na rawa ya buɗewa Alhaji Nasir bayan mota ya shiga. Ramlah ce ta taho da nufin itama ta shiga motar ayi rakiyar Alhaji Nasir da ita. Widad ta kalli Ramlah tace "ba gurin ki a motar nan, dan bama buƙatar rakiyar ki" ta kalli Yusuf tace "shiga gaban motar" . Nura ya tsaya ya kalli Widad ya kalli Yusuf, Yusuf ma saroro yayi yana kallon Widad, Waidad tace "ba kaji ba? ko sena maimaita" Yusuf ya buɗe gaban mota ya zauna, yayin da ita da mahaifin ta suka shiga baya suka zauna. Nura ya ja mota suka tafi, Ramlah ta rasa me zata yi ne, Mummy tace "yi haƙuri ƙyalesu, in sun san wata basu san wata ba" Haka ta rarrashi Ramlah suka wuce cikin gida. Jefi2 Alhaji Nasir da Widad suke hira, yayin da Yusuf da Nura suka yi shiru kowa da abunda yake saƙawa a ransa Suna cikin tafiyar ne, Alhaji Nasir yace "daughter na dan Allah ina sake roƙon ki, karki watsamin ƙasa a ido, idan fahad ya dawo ku daidaita, ina son ganin ki cikin farin ciki ne daughter bana son irin wannan rayuwar takura kan da kike yi" Banza tayi da Daddyn, seda aka ja lokaci sannan tace "Daddy na fara tunanin ka dena sona, idan har kana tunanin yi mun aure ne ze sani farinciki, to tabbas zaka sake jefani ne cikin wata damuwar, kafi kowa sanin meye buri na, Aure ze zama tamkar barrier ne a cimma buri na" "Daughter yanzu abun nan baze wuce a gurin ki ba? Ba zamuyi haƙuri ba mu barwa Allah, ba zamu yadda komai ya faru damu muƙaddari ne daga Allah ba?" "Daddy bazan taɓa mantawa ba, kuma bazan yafe ba sena cika buri na, kuma ka dena min batun Auren nan bana so, bazan iya zama a ƙarƙashin wani ba inyi masa biyayya ko waye shi, ku ƙyaleni da zancen Auren nan please bana so" Ta mirror Yusuf yake ganin Widad yadda Hawaye ya wanke mata fuska, ta rintse ido tana magana cikin kuka. Alhaji Nasir ya rungume ta a jikin, sa cikin sigar rarrashi yace "Am sorry my dear, i don't mean to hurt you, nasan tamkar na fama miki wani ciwo ne dake cin zuciyar ki, amma kiyi haƙuri ina ƙoƙarin wanke miki wannan damuwar ne, ina son komai ya wuce kema ki fuskanci rayuwar ki" "No Daddy i can't, ta yaya zan manta da abunda ya faru, Daddy bazan ƙara yadda da kowa ba, yin aure na tamkar ƙara kusanto da maƙiya jikin mune, ni bazan yadda da kowa ba balle a sake cutar dani a karo na biyu ba, Daddy i repeat my self bana son kowa a kusa dani, bana so" sosai kukan nata yake ƙara ƙarfi harda sheshsheƙa. "yi haƙuri daughter na, Amma ina sa ran Insha Allah zakiyi alfahari da auren fahad, yana da kirki sosai ɗan uwanki ne, tunda jinin Alhaji Bulama ne, bana tunanin akwai wata cutarwa da Alhaji Bulama ze mana" Haka nan Yusuf yaji ta bashi tausayi, duk abunda zesa Widad ta sauke wannan izzarta ta, ta dinga irin wannan kukan lallai ba abune ƙarami ba. Har suka je airport Widad kuka take, har kyawawan idanuwan ta sunyi ja, haka suka yi Sallama da mahaifin ta. Alhaji Nasir ya dubi Yusuf yace "Yaya na a kulamin da amana ta" A fusace Widad tace "Daddy karka ƙara cewa ka bar amana ta a hannun wani , ka barni a hannun Allah zaka je ka dawo ka tarar dani lafiya Insha Allah, amma zuwa yanzu yaci ace kayi darasin da bazaka ƙara bawa mutum yadda da Amana ba, narasa me yasa Daddy ka kasa fahimta ta" Alhaji Nasir yai murmushi ya riƙo hannayen ta yai mata raɗa a kunnen ta, sannan a fili yace "ina da surprise a gare ki idan na dawo, ku koma karku yi dare my lovely" Haka Widad suka juya zuwa mota, yanzu ma Nura ne ke jan Motar Widad tace "yi parking anan" Nura ya tsaida motar, tace masa "gaya masa inda farm house yake" Nura ya gane abunda take nufi, dan haka yaiwa Yusuf kwatancen inda tace. Daga nan ta ɗaga idon ta wanda suka jiƙe da hawaye tacewa Nura "fita ka bar motar nan ka hau ta haya ka koma gida, Kaikuma ka karɓi tuƙin mu tafi" Nura yace "Amma ranki ya daɗe motar Alhaji ce kuma.... "motar Alhaji ta ubanka ce? Ko ta Ubana?" ta jefo masa tambayar "A'a amma ban fito da kuɗi ba" "Idan ka bari na sake magana, zan ɓata maka rai fiye da tunanin ka, fita daga motar nan nace, idan ba tare muka haɗa kuɗi muka siya ba" Haka Nura ya fice daga motar, Yusuf ya karɓi tuƙin. Yusuf ya dinga bin kwatancen da Nura yayi masa, har sukaje gidan gonar Widad bata dena kuka ba, Sam Yusuf yaji beji daɗin yadda take kukan ba, gashi ita ba'a iya mata balle ya rarrashe ta Wani irin tangamemen gida ne har yaso yafi gidan da su Widad ke Rayuwa a ciki girma, Yusuf ya fara tunanin anya wannan gidan gona ne? Horn Yayi aka buɗe masa wani jibgegen gate me matuƙar nauyi ya shiga da Motar cikin gidan. Ma'aikatan gidan ne suka dinga tahowa cikin matuƙar sauri inda motar su Widad take, Kallon gurin Yusuf yake yi, dabbobi kala kala a ɓangarori daban daban wanda idon sa yake iya gani, gefe kuma gida ne sosai ginanne a ciki, cikin zafin Nama ta fito daga motar tana ta Hawaye, cikin girmamawa ma'aikatan ke zubewa suna gaishe ta, babu wanda ya samu Arziƙin kallo balle ta kula shi. Cikin matuƙar sauri ta nufi ɓangaren da yake gida ne a cikin gurin, Yusuf ya bita shima cikin sauri, binsu ma'aikatan suka yi da kallo mussman Yusuf, Wani irin murgujejen kare ne fari da baƙi a jikin sa ya nufo inda Widad take yana wani irin gurnani gami da sufa. Durƙusawa tayi ƙasa Karen yazo yana zagaye Widad yana shanshana jikin ta, shafa gashin karen tayi tana kuka tace "I miss you Miz" Karen ya kwantar da kansa a jikin Widad yana zaro harshe, ko tsoron sa bataji balle ƙyama. Haka karen yai lamo a jikin ta tareda ƙurawa Yusuf ido, ita kuma tana cigaba da kuka, can kuma ta shafa kan karen tace "Excuse me Miz, I will see you later" Ta miƙe zata yi gaba Yusuf ya bita, Karen nan ya bishi yana masa wani irin haushi da gurnani yana zubar da yawu, Yusuf a ransa yace "Wane irin jarababben kare ne wannan se kace zaki?" Widad ta juyo ta kalli karen tace "don't Worry, I trust him Miz" Daga nan ta miƙe ta ci gaba da tafiya, Aikuwa tana faɗar hakan karen ya dena bin Yusuf. Sunyi doguwar tafiya sosai a cikin gidan, dabbobi daban daban wasu daka gansu kasan sun sha banban da kalar namu na Nigeria. Gida ne sosai a ciki ginanne me matukar kyau, ya tsaru sosai sedai da alama babu mutane a ciki. Wani ɗaki Widad ta nufa ya bita, suna shiga ɗakin Widad ta ƙara sautin Kukan ta, wani katafaren gado ta nufa ta zube a gaban gadon ta ci gaba da rera kukan ta, daga jin yadda take fidda sautin kukan kasan kuka ne me taɓa zuciya. Yusuf se binta yake da ido cikin tausayawa halin da take ciki, amma bashi da damar yayi mata magana ko ya rarrashe ta dan bata son shisshigi, yanzu zata masa rashin mutunci. Ba tare da ta kalli Yusuf ba, a hankali tace "Excuse me please" Yusuf ya jinjina kai ya fice ya tsaya a wajen ɗakin, kusan mintuna talatin yana tsaye yana jiran ta. Fitowa tayi ɗauke da wata shigar ta daban, kamar ba ita ba, shigar jikin ta ba kace musulma ce ba. Kallon ta Yusuf ya tsaya yanayi duk wani ilahirin surar jikin ta seda ta bayyana, Farar fatar ta se ɗaukar ido take. "let's go" shine abunda ta cewa Yusuf, haka yabi bayan ta zuwa inda motar su take, nan ma ma'aikatan ne suka kuma biyo ta suna mata Fatan Alkhairi, gaban motar ta buɗe ta ɗebo kuɗi bandir bandir ta basu, ta shige motar Yusuf yaja motar. Wani ƙaramin kati ta miƙawa Yusuf, kwatancen inda gurin partyn yake ne, shi sam ya manta tace ze kai ta gurin birthday ne, ga yamma tayi sosai, se dai bashi da

Chapter 6 of 35