Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gurin yayinda ya bita da kallo. Da Yusuf ya koma gida yayiwa Umma bayanin tafiyar da zasu yi ya raka Widad, da farko taƙi yadda tace sam bata san zance ba. Yusuf yace "haba Umma, ya za'ayi nida na ɗau Alƙawarin Yiwa jama'a aiki aikin ya taso kice baza'ayi ba, bayan ke kike cewa inyi gaskiya a aikina? Kina so in bari a cutar da ita ne, ba zan iya jure in ga wani mummunan abu ya sameta ba" "nifa na kasa gane meke wakana tsakaninka da wannan uwar ɗakin, ka damu da ita dayawa" "ba wani abu da yake wakana Umman Yusuf, kawai dai mahaifinta na mutuntani ne sosai" "shikenan Yusuf, Allah ya bada sa'a zanyi kewarka zakayi kwanaki ba tare da Umma ba" Yusuf yace "nikaina ina tunanin hakan, Amma insha Allah ba abunda ze faru kwana biyar ne kawai tafiyar" "to Allah ya bada sa'a" Ya amsa da "Ameen" Haka nan Umman Yusuf take jin kamar akwai wani abu daze faru dalilin tafiyar nan, sedai ta kasa gane na daɗine ko akasin hakan. Rana bata ƙarya sedai uwar ɗiya taji kunya, Yusuf ya shirya jakarsa da kayansa da ze dinga sawa da ɗan sauran kayan buƙatarsa a traveling bag. Yaje gaban Ummansa yace "Umma na fito zan tafi, zan kwana a gidan gobe in Allah ya kaimu da Asuba zamu tafi" Umma ta riƙo hannun Yusuf tace "ka kula da kanka Yusuf, kai kaɗai ka ragemin, Allah yayi maka Albarka ya sadaka da dukkan Alkhairi, Allah yayi maganin maƙiyanka ya karemin kai.." Kasa ƙarasawa tayi ta fashe da kuka, gaba ɗaya jikin Yusuf yayi sanyi yace "Umma ko in fasa tafiyar nan?" Ta girgiza kai da sauri tace "A'a bakomai yi tafiyarka, ban san kayi nesa dani ba shiyasa naji ba daɗi" Haka sukayi Sallama ya tafi. A can gidansu Widad da yaje, yaje ya sameta a ɗakinta tana ta aikin kuka, magenta se kewayata take itama tana kuka gwanin ban tausayi. A sanyaye Yusuf yace "waike abun kuka baya miki wahala, kiyi ta azabtar da rayuwarki, kiyi haƙuri ki dena kuka koma meye yake damun ki Allah yana sane dake" Sallamar Alhaji Nasir ce ta katse Yusuf daga maganar da yake yi "Yusuf ka shirya ne?" "Eh ranka ya daɗe na shirya ni" "to shikenan ta haɗa nata kayan, bayan la'asar semu tafi can farm house" Yusuf yace "to shikenan ranka ya daɗe" Alhaji Nasir yace "daughter ki tashi ki haɗa kayan naki, ya kaiki gidan daddynki Bulama kuyi sallama" Cikin kuka Widad tace "bazan ƙara zuwa inda yake ba, baya sona yafi san ɗansa" Alhaji Nasir yace "Allah ya baki haƙuri tashi ki hada kayan, ko inyiwa Halima magana tasa a haɗa miki" "Ni ba wanda ze haɗamin, zanyi da kaina" Haka Widad taita daru san ranta, Daddy ya dena mata faɗa lallaɓata yake yanzu. ************************************ "Daddy wai yanzu shikenan an fasa ɗaura mana Auren?" Bulama yace "Eh, an ɗaga dai akwai buƙatar taga likita, har yanzu bata da lafiya" "Daddy wane irin likita kuma? Naga dai da hankalinta ba hauka take tuburan ba" "eh mahaifinta ne yacemin akwai buƙatar a barta ta ɗan huta, dan gaba ɗaya tana nema ta illata kanta, ta damu sosai bata son Auren nan, dan haka ma zata Wuce England ta huta" "wace irin maganace wannan, an samin rai kuma ace an fasa?" Mahaifiyar Fahad dake gefe, tunda suka fara magana ba tace komai ba se yanzu tace "kai Dalla Allah ya rufa maka Asiri kana nema ka tonawa kanka, Allah ya rabaka da Auren mara tarbiyya mahaukaciya" Fahad yace "Ni gaskiya ina sonta a haka, kuma nasan Anwar ne yaje ya kai gulma ta gurin Alhaji Nasir, shiyasa yace haka, ko yana so ko baya so se anyi auren nan dani mu zuba mu gani" Bulama na ƙoƙarin dakatar da Fahad, amma yaƙi tsayawa ya fice. Yana fita ya ɗau mota ya nufi unguwar su Widad, yana zuwa beyi wata wata ba ya nufi boys quarters inda Sashin Anwar yake, Anwar yana zaune yana kallon labarai Fahad ya shigo bako sallama. Anwar yace "Lafiya zaka shigomin ba sallama?" "dole ka tambayi lafiya mana, ai ban san haka kake ba, ban san ka iya munafunci ba se yau, saboda rashin son cigabana shine ka shiga ka fita aka ɗaga Aurena da Widad bayan ina can inata shiri" "kamar yaya kenan? Waye ya gaya maka ni na hana aurenku ko nace a ɗaga?" "Au kai tunaninka wanine ya gayamin, bayan da bakinka kazo ka faɗamin, kayi Nasara Amma kasani Aure yana nan daram tsakanina da ita kuma se nayi maganinka" Anwar yace "Yanzu Fahad akan Mace kakemin wannan cin mutuncin? Ina ɗan uwanka kuma abokinka?" "na maka ɗin, haifata kayi da ba zan maka ba?" "Ni bam rufe ido maci mutuncinka ba saboda cin amanar abota na amincewa da Auren Yarinyar da nake so, se kaine zakamin?" Fahad yace "Ai ban ma yi maka komai ba, kuma wallahi ko bangon duniya zata zan bita sena Aure ta" Anwar ya kashingiɗa a jikin kujera yace "Ashe dai haɗin da'akayi ita za'afi cuta, saboda naka haukan yafi nata fitowa" "Anwar ni kake cewa mahaukaci?" Banza Anwar yayi masa be kuma ce masa komai ba "zakaga ƙarshen rashin mutunci kuwa" "Ya ƙare akanka" Anwar ya bashi Amsa A fusace Fahad ya baro part ɗin Anwar yana huci, yana ƙoƙarin shiga motarsa Ramlah ta ƙaraso da sauri tana faɗin haba "Fahad yanzu har kazo gidan nan amma ka tafi ba tare da ka ganni ba" "Am sorry, zuwan gaggawa ne shiyasa yakike?" Ramlah tace "gaskiya ban yadda ba, kazo mu shiga ciki" "A'a Ramlah ina sauri ne, zamu haɗe insha Allah" Ya shige mota ya bar Ramlah a gurin. Da Yamma ƙarfe huɗu Yusuf ya shiga gidan, sedai yaga Hajiya Halima na masa wani irin mugun kallo, wanda be gane dalilin hakan ba, ko kulata beba ya wuce part ɗin Widad. Tana zaune a gefen gado tana shafa jikin magenta, tayi shiru kana kallonta zaka san ɗauke take da damuwa. Yusuf yace "Ya jiki kuma?" Wata uwar harara ta aika masa ta ɗauke kanta. Akwatunan ta data shirya manya guda biyu da ƙarama, abun har mamaki ya bawa Yusuf me zata yi da wannan uban kayan haka oho? Ya ɗauki trolleys ɗin ɗaya bayan ɗaya ya kaisu Mota. Alhaji Nasir ya fito cikin shirinsa tsaf, yaje ya fito da Gimbiyar 'yar tasa a falo yana shirin fitowa Hajiya Halima ta tarar da shi tace "Nifa Alhaji ban gane ba? Ina zaka ne haka ba bayani, naga har ana fita da akwatuna" Alhaji Nasir yace "eh zamu ɗan fita ne, ba zamu kwana a gida ba Lovely zataje Abuja ganin likita daga nan kuma zata wuce UK" "Amma shine baka gayamin ba se yanzu, sekace kana zaman gaba dani? Ace Widad zata tafi amma baka gayamin ba" Wata uwar harara Widad ta aikamata dashi haɗe da tsaki tayi waje abunta, Yusuf ma be tsaya a gurin ba yabi bayan Widad a hanyar da zasu fita harabar gidan Amal tace "Allah ya raka taki gona, ma huta na kwana biyu kafin ki dawo, kai kuma ka dawo ka sameni" Daga Yusuf har Widad ba wanda ya tanka mata sukayi gaba, kamar kullum gaban motar ya buɗe mata ta shiga, shima ya zagaya ya shiga suna jiran fitowar Alhaji Nasir. Kusan mintuna sha biyar sannan ya fito shima ya shiga motar, Anwar ne ya fito ya ƙaraso da sauri yace "ina zakuje ne haka Daddy?" Alhaji Nasir yace "zamuje farm house ne, gobe in Allah ya kaimu Yusuf ze raka Lovely zataje ganin likita Abuja, idan ta gama zata koma England ta huta" Turus Anwar yayi yana kallon su, jiki a sanyaye yace "Shikenan, A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya" Ya juya ze koma BQ, da sauri Widad ta buɗe motar ta kira sunansa, ya tsaya ta ƙarasa da sauri inda yake ta kalle shi tace "Anwar lafiya kuwa?" Anwar ya ƙaƙalo murmushi yace "lafiya ƙalau Widad" "Amma naga mood ɗinka ya canza" "zanyi missing ɗinki ne" Ɗan tsayawa tayi tana kallon sa, jiki a sanyaye tace "Anwar haka kurum naji bana son tafiyar nan, ji nake kamar akwai abunda ze faru a tafiyar nan, dan Allah idan na tafi ka kularmin da Daddy dan Allah ji nake kamar wani abu ze sameshi idan na tafi " Tai maganar hawaye na bin fuskarta. Anwar yace "Widad akwai matsala ne?" Girgiza masa kai tayi tace "ni dai ka riƙemin Amana dan Allah" "shikenan karki damu, Insha Allah zan kula dashi, zakije ki dawo ki sameshi lafiya" Ta jinjina masa kai tayi murmushi tace "Nagode Anwar" Ta juya ta koma mota, shikam Yusuf wani takaici ne ya ƙule shi yadda taje ta tsaya tana magana da Anwar. Yusuf yaja motar suka nufi gidan gona, tunda ma'aikatan suka ga tare da Alhaji Nasir ne suka dinga tururuwar zuwa kwasar gaisuwa, dan ya daɗe beje gidan gonar ba, nan ya dinga musu fara'a ya zolayi wannan ya zolayi wancan yana musu kyautar kuɗi. Saleh ne ya shigo harabar gidan ya ƙaraso gaban Alhaji Nasir yana murmushi yace "Barka da sauka Alhajin Allah yaushe rabonka damu a gidan nan, sedai muji labarin kazo gari " Alhaji Nasir yace "Abubuwa ne sunyi yawa Saleh ya aikin, ya haƙuri damu?" Saleh yayi murmushi yace "Yallaɓai ai kuke haƙuri damu" "to Allah ya ƙara mana haƙuri da juna, zan maka transfer ɗin kuɗi aje ayo order Abinci gaba ɗaya ma'aikatan gidan nan Vip kowa yaci ya ƙoshi" "Allah ya temakeka Alhaji namu, Allah ya ƙara nisan kwana da Arziki me Amfani" Alhaji Nasir yace "Ameen Saleh, soja marmari daga nesa" Saleh yayi murmushi ya fita, yana fita ya samu wani guri ya laɓe ya ɗakko wayarsa ya daddana yasa a kunnensa "Oga sunzo, kuma da alama a gidan nan zasu kwana gaba ɗaya" "shikenan kasa mana ido akansu sosai, sannan ka lura da motar da zasu yi tafiyar a cikinta kasa tracker dan karsu tafi kafin su Dage suje" Saleh yace "shikenan as you wish, amma dan Allah karku saɓa Alƙawari" "karka damu kai dai kayi abunda muka ce" Alhaji Nasir ya turawa Seh kuɗi, yayo order Abincin ma'aikatan gidan nan kowa yaci yasha yana walwala, aka kaiwa Alhaji Nasir nasu, Alhaji Nasir ya haɗe nasa da na Yusuf yace suci tare, ba ƙaramin mamaki abun ya bawa Yusuf ba, ace babban mutum kamar Alhaji Nasir yace zeci Abinci kwano ɗaya da ma'aikacin 'yarsa lallai be ɗau duniya da zafi ba. Widad kam sam bata walwala, Ƙarewa ma ɗaki ta ɗaya ta samu ta shige tayi kwanciyar ta. Yusuf kam suka zauna da Alhaji Nasir suna ta hira, kamar ɗa da Uba yana bashi labarin tafiye tafiyen da yayi da ƙalubalen kasuwanci da kuma nasarorin daya samu. Can Alhaji Nasir ya nisa yace "kaga gidan nan shine gidana na asali, ina jin daɗin unguwar nan amma tun bayan rasuwar mahaifiyar Widad naga bata son zaman gidan, saboda ita na canza gida, nan kuma aka zuba dabbobi a wani ɓangaren saboda tama son dabbobi" Yusuf yace "Allah sarki, tabbas naga tana matuƙar son dabbobi kam" Alhaji Nasir yace "Yusuf dan Allah ka ƙara haƙuri da 'yata, na yaba sosai da ƙoƙarin ka Allah ya saka maka da Alkhairi, dan Allah idan ta gama ganin likitan, ranar da zata bar ƙasar nan dan Allah ka tabattar jirgunta ya tashi, da ni naso in kaita da kaina, amma akwai taron kasuwanci na shekara da nake halarta, idan har ban halarta ba akwai matsala ga dukiyata, wadda take gauraye data al'umma" Yusuf yace "dukiyar ka data al'umma kuma?" Alhaji Nasir yace "Eh mana, akwai hannun jarin mutane a cikin kasuwanci na, wanda ciki harda masu ƙaramin ƙarfi idan har ban halarci taron nan ba to tabbas dukiyoyin wasu zasu halaka" "Amma meyasa dukiyar wasu zasu halaka, dan baka halarci taron ba? ' Alhaji Nasir yayi murmushi yace " karka damu, idan Allah yasa kuka dawo zan gaya maka yanzu dare ya fara yi " Yusuf a ransa yace" to ko dai Alhaji Nasir yasan maƙiyansa ne? " A fili kuma yace "Amma yallaɓai kana ganin za' a samu Nasara idan taga wannan likitan?" "To abun duk lalabune a duhu Yusuf, bamu san inda zamu dace ba" Suna cikin maganar saƙo ya shigo wayar Alhaji Nasir, ya ɗakko wayar ya duba Jikin Alhaji Nasir ne ya kama rawa, a ɗan gigice yace "Amm.. Ammm Yusuf jeka ka kwanta dare yayi, saboda ku samu ku fita da wuri gobe in Allah ya kaimu, kabi wannan varrender akwai ɗaki yana kallonka acan zaka kwanta" Yana gama faɗin haka ya shige wani ɗaki ya rufe ƙofa, mamaki ne yakama Yusuf ya miƙe ya nufi inda Alhaji Nasir ya kwatanta masa ya shiga. Masha Allah, ɗakine tangameme babu abunda babu na jin daɗin rayuwa a ciki, gadon kansa abun kallo ne kamar ka sace ka gudu, hotunan Widad ne ko ina a ɗakin, Yusuf ya dinga ƙare musu kallo, idonsa ya sauke akan haɗaɗɗen hoton Widad. Tayi kyau sosai tayi murmushi cikin wata jar doguwar riga, ta baje gashin kanta kamar ba ita ba. Ya daɗe yana kallon hotunan dake jikin bango, sannan ya ajiye jakarsa, yana sake ƙarewa ɗakin kallo. Ya shiga banɗakin yayi alwala ya dawo yayi nafilfili yayi karatun Al'qur'ani da addu'oi sannan ya nemi guri ya kwanta. Wajen ƙarfe biyu na dare cikin bacci Yusuf yaji muryar Alhaji Nasir na rawa yana kiran sunan Yusuf, a gigice Yusuf ya farka ya tashi zaune. Alhaji Nasir ya kamo hannun Yusuf yace "taso Yusuf akwai matsala" "matsalar me Alhaji?" "Yusuf rayuwar Widad, ni idan tawa ta salwanta bakomai, bana son Widad ta rasa Ranta" Cike da mamaki haka Yusuf ya biyo bayan Alhaji Nasir, suka tarar Widad na tsaye a falo tana kuka, gaba ɗaya Yusuf ya rikice yace "Alhaji meke faruwa ne" Jiki na tsuma Alhaji Nasir ya miƙawa Yusuf wayarsa "RANA BA TA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA, YAU ZAMU KAWO ƘARSHEN WASAN KURAR DA MUKE, KODAI KA YADDA KA BAMU ABUNDA MUKE BUƘATA KA HALARCI TARON KASUWANCI, KO KUMA KA HANAMU KA RASA RANKA DA NA 'YARKA, KOMU KASHE TA AGABANKA MU BAR MAKA MUGUN TABO, WATAƘILA HAKAN YASA KA BAMU ABUNDA MUKESO" Yusuf yace "to koma mene ka basu mana, saboda rayuwar ka da tata su tsira" "Yusuf ni kaina abunda suke so in basu ba nawa bane, nayiwa kaina Alƙawarin bawa meshi abunsa, dan haka bazan basau ba" Yusuf yace "to ko ka kira jami'an tsaro" "A' a Yusuf hakanma matsala ne, dan Allah ka ɗau Widad ku tafi maza ku tafi yanzu" Fashewa da kuka Widad tayi tace "Ni bazan tafi na barka ba Daddy, bana son wani abu ya same ka, Daddy bana son tafiya kai kaɗai ka ragemin" Dattijon yana zubar da hawaye yace "Widad bana son rayuwarki ta salwanta, nima ke kaɗaice dani, idan suka kama ki komai ya ɓaci, ki tabbatar kin miƙa amanar nan ga masu ita, karki yards ta salwanta ko a karon banza wasu su karɓa, maza ku tafi" Ƙanƙame mahaifinta tayi tana kuka tace "Daddy ba inda zanje, kome ze faru ya faru muna tare" Daddy da kansa yaja hannun Widad ya kaita mota, ya kalli Yusuf yace "Allah ya kiyaye ku Yusufa, na yarda da kai ka kularmin da Amana ta, ka kula da Widad kayi haƙuri da ita, karku sake ku dawo idan bani na kira ku ba, zaman Widad anan tana cikin hatsari mutanen nan dagaske suke" Haka Yusuf ya shiga motar yaja, Widad tana wani irin kuka me ban tausayi. Su kansu ma'aikatan sunyi mamakin fitar su Yusuf a wannan daren. Saleh ne ya samu Alhaji Nasir yace "Alhaji lafiya kuwa? Meke faruwane haka?" Daula yace "Wata 'yar ƙaramae matsala ce, Amma komai ze daidaita insha Allah" Alhaji Nasir ya koma cikin gidan yana safa da marwa ya rasa abunyi, wayarsa ya ɗakko ya kira Bulama a waya ya sanar dashi halin da yake ciki. Yusuf kam a besan inda ze nufa ba a wannan tsohon daren, gaba ɗaya sahu ya ɗauke se abunda ba'a rasa ba,gudu yake yana ratsa tituna ba tare da yasan inda ze dosa ba. Befi mintuna talatin ba sega Bulama yazo gidan a sukwane, suka haɗu da Alhaji Nasir a harabar gidan, Bulama a gigice yace "Daula ina Widad ɗin take yanzu?" A kiɗime Daddyn Widad yace "na haɗata da direbanta nace su tafi" "su tafi suje ina?" 'Bulama na rasa yadda zanyi ne, ina tsoron rayuwar Widad ta taɓu, nasan yaron baze cutar da ita ba" A fusace Bulama yace "kayi hauka ne Nasiru, kamar ya ka haɗata da direba? Kasan daga ina yake ko kuma ina ze kaita, memakon ka kira' yan sanda kawai seka haɗata da direba idan kuma bakinsa ɗaya da mutanen fa" Girgiza kai Alhaji Nasir yayi yace "bana tunanin haka Bulama kaina ya gana kullewa ne" Alhaji Bulama ya ɗau waya ya fara kiran 'yan sanda. Sosai Yusuf yake gudu akan titi, yayin da Widad ta dunƙule tana aikin kuka, Yusuf ya kasa cewa komai se tunanin ya zasu tsira, sedai babu zato yaci karo da wata mota anyi parking ɗinta a tsakiyar titi, wani irin parking na rashin mutunci yanda babu damar Yusuf ya iya wucewa, ga gefe jeji ne, yayi reverse ze juya kan motar wata motar tazo ta ƙara rufe bayan tasu Yusuf aka sasu a tsakiya. Wasu irin ƙarti ne suka fito daga motocin suka kewaye su Motarsu Widad, gaba ɗaya Widad ta rikice ganin suna tunkaro su, suna zuwa suka buɗe ƙofofin motar, suka sawa Yusuf bindinga aka suka ce Widad ta fito. Ko motsi ba tayi ba balle ta ɗaga kai ta kalle su, cikin tsawa ɗaya yace "ba magana ake miki ba" Sunkuyar da kai tayi taƙi motsawa, ɗaya yasa hannu ze fizgota aikuwa ta riƙe Yusuf gam tana kurma ihu "Yoseef karka bari su tafi dani" Yusuf ya riƙe hannun ta yace "me mu kayi muku kuke ƙoƙarin cin zarafin mu akan titi haka" "zaka rufe mana baki ko semun fasa kanka da bindiga, dalla ku fizgota ta ƙarfin tsiya suna ɓata mana lokaci" Ai Widad sekace Mayya ko ƙarfe ta riƙe Yusuf gam, wani gigitaccen mari ɗayan ya kwaɗawa Widad yana ƙoƙarin janyo ta, sedai ga mamakin Yusuf mutumin yana sauke hannun sa Widad ta rama marin, dukda a gigice take tace "karka ƙara gangancin marina, wallahi ka kuma dukana sena rama" "Ashar ya saki yace lallai wannan yarinyar akwai ƙarfin hali, yau zamuyi maganinki" Hannu ya kai ze shaƙota, amma Yusuf ya riƙe hannun mutumin yace "karka kuskura ka sake marinta" "Idan aka sake marinta me zakayi? Dan Allah oga ka bani dama in fasa kan gayen nan da bindiga" Shugabansu yace "babu kisan kai a wannan deal ɗin, ban sani ba ko zuwa gaba" Suka cigaba da jan Widad, Yusuf yaƙi sakin ta, baya son ya zafafa suyi mata illa gashi babu makami a jikinsa. Yace "idan kunga kun tafi da Widad to tabbas kun kasheni ne, amma ba inda zaku da ita" Ganin Yusuf na ɓata musu lokaci ga Widad na nema tasa asrinsu ya tonu, bakinta yaƙi rufuwa sunan Yusuf kawai take kira, haka suka haɗa da Yusuf suka sasu a tasu motar. Suka ƙulle hannayensu, sukayi daji dasu, ihu Widad ta cigaba dayi, gaba ɗaya ta manne a jikin Yusuf sosai tana cewa "ni ku ƙyalemu, besan komai akai ba, direba nane kawai ku ƙyalemu mu tafi" Yusuf yace "kiyi shiru karsu illataki" Ai be gama rufe bakinsa ba, suka sa ƙyalle suka rufe musu ido. Widad tasa haƙoranta ta riƙe rigar Yusuf, duk dan kar su raba ta da Yusuf, se haki take tana jin yadda zuciyar Yusuf ke bugawa, Yusuf kam ya yabawa jarumtar Widad yau. Shikansa Saleh da'aka haɗa baki dashi akayi aikin, ya rikice gaba ɗaya ya shiga damuwa mussman yadda yaga Alhaji Nasir na zubda Hawaye yana kaiwa yana komowa a harabar gidan, Alhaji Bulama nata rarrashinsa amma se kuka yake kamar ƙaramin yaro, zuwan 'yan sanda yayi dai dai da shigowar wani saƙon wayar Alhaji Nasir. "A ZATONKA KA FIMU WAYO NE, MUN KAMA' YARKA DA DIREBANKA SUNA HANNUNMU, SHAWARA TA RAGE NAKA, ZAMU CIGABA DA AZABTAR DASU, DAN HAKA SEKA KA ZAƁA KO RANSU KOKUMA ABUNDA MUKA NEMA A HANNUNKA" Yana gama karanta saƙon ya yanke jiki ya faɗi a gurin In an karanta ayi share please 🙏 🙏 🙏 Gyara, sharhi ko shawara Ayshercool 07063065680 _*AƘIDATA*_ PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) * And now *AƘIDA TA * I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends ELEGANT ONLINE WRITER'S PART1 Page 24_25 Gaba ɗaya ma'aikatan gidan su kayo kan Alhaji Nasir, sedai jikinsa kamar babu rai, 'yan sanda suka ƙaraso cikin gidan aka kwashi Alhaji Nasir a daren zuwa Asibiti. Widad kam gajiya tayi da zaman motar, saboda tafiya suke bata wasa ba cikin wani irin azababben gudu, jin tafiyar taƙi ƙarewa ne yasa Widad fara mustu mutsu, tun tana mutsu mutsun har bacci ya kwashe ta, a firgice ta farka ta kurma wani uban ihu tana kiran "wayyo Allah na Yoseef, karka tafi ka barni" Yusuf yace "Widad ina nan, muna tare har yanzu Allah ze fitarmu insha Allah, ki dena shouting karsu miki wani abun" Me tuƙa motar yace gara dai kaja mata kunnen. Memakon tayi shiru ta cigaba da ihu tana "ku ƙyalemu mu tafi, yoseef na gaji da zaman nan hannuna igiyar nan ta dameni, bayana ciwo na gaji bayana ze karye" Wata hoda su watsawa Widad, wanda hakan yasa ta baccin dole, ba Widad ba har Yusuf gaba ɗaya bacci ya kwashe su. Ana kai Alhaji Nasir Asibiti, aka kwantar da shi aka dinga masa allurai da ƙarin ruwa, ga oxygen ansa masa domin temakawa numfashinsa dake barazanar ɗaukewa. Likitoci suka duƙufa akansa, suna bashi dukkanin taimakon da zasu iya, ga jininsa ya hau fiye da kima suna ta ƙoƙari jininsa ya sauka. Yusuf ne ya fara farkawa jin motar ta tsaya, aka buɗe motar suka kwance musu ido, mamakine ya kama Yusuf, tun cikin dare suke tafiyar nan amma da'aka kwance musu ido yaga yanayin garin kamar Azahar ta gota, daji ne sosai ciyayi sun lulluɓe ko ina, gaba ɗaya Yusuf baya gane inane gabas ko yamma ya kasa gane ta ina suka zo nan gurin. Widad kam sam bata hayyacinta, ta farka amma se tangaɗi take haka suka sasu a gaba zuwa wani gini. Yusuf yayi mamakin yadda aka shigo cikin wannan uban dajin akayi ginin gida, suka buɗe gidan suka shiga dasu Yusuf. Gaba ɗaya gurin kango ne, kuma ga dukkanin alamu an samar dashi ne mussman saboda wannan aikin, saboda gurin sabon gini ne harda ragowar kayan aikin ginin. Wani ɗaki suka kai su Widad suka ajiye, akan tsurar tabarma suka kawo musu ruwan pure water guda biyu suka ajiye musu suka maida ƙofa suka rufesu a ciki. Yusuf ya ɗau ruwa ɗaya ya fasa ya bawa Widad, aikuwa nan da na ta zuƙeshi da alama tana jin ƙishirwar sosai, ga ko salla ba suyi ba haka ya zuba mata ruwa tayi alwala, ɗan ragowar shima yayi ba tare da sun san inane gabas ba haka suka gabatar da salla. Shiru Widad tayi, gaba ɗaya jikinta ciwo yake ga wata uwar yunwa da take ji, gashi har yanzu jikinta babu ƙwari saboda hodar da suka watsa mata. Ta kalli Yusuf da yayi shiru ya sunkuyar da kai, gaba ɗaya tausayinsa yakamata duk a dalilin ta wannan masifar ta faɗa masa. Kifewa tayi a gurin, hakan yasa Yusuf ɗagowa da sauri yana kiran sunan ta, cikin kasala tace "Yunwa nake ji" A hankali yace "kiyi haƙuri kinji, Insha Allah zamu bar gurin nan, kuma zaki ci Abinci" Ba tace komai ba ta maida kanta ta kwanta, wani irin sanyi na ratsa ta, miƙewa Yusuf yayi yana zagaye ɗakin harda ban ɗaki sedai an rufe ko ina babu hanyar tsira. Zagaye ɗakin ya shiga yi yana sake tunanin menene mafita, ya kalli inda Widad ke kwancw ta takure sosai gwanin ban tausayi. Haka suka wanzu babu me cewa komai tsawon

Chapter 22 of 35