alert today, you can leave"
"amma ranki ya daɗe, wannan wayar ai tayi min girma, kuma..."
Ai ko kallon inda yake bata sake yiba ta miƙe ta nufi part ɗin ta.
Gaba ɗaya hankalin Hajiya Halima akan Yusuf yake, Yusuf ya fita daga falon, ganin bashi da wani aikin da zeyi ya sashi ya ƙudure tafiya gida, yana ta ƙara jinjina kyautar wayar da Widad ta bashi.
Yayiwa su Nura Sallama ya fice ba tare da ya gaya musu abunda Widad ta bashi ba, yana cikin tafiya kafin ya kai ƙarshen layin aka sha gaban sa da mota, tsayawa yayi cak yaga waye wannan.
Ramla ce ta fito daga motar tana masa wani irin kallo, ta kalle shi a yatsine tace "Nasan zakayi mamakin ganina anan, saboda bakamata mace kamarni ta tsaya tana ɓata yawunta akan talaka mutum maƙasƙanci kamar ka ba, sedai ita kasuwar buƙata idan ta taso tamkar guguwa take bata da shamaki, magana nake so muyi da kai me mahimmanci, wadda zata amfaneka, idan ba zaka damu ba ina so ka shiga mota muyi magana"
"talakan mutum maƙasƙanci a gurin ki, amma wataƙila me matsayi a gurin Allah be cancanci ya shiga motar mace me girman kai da tinƙaho ko ince tagumi da haɓar wani ba, bana buƙatar dukkan wani abun Amfani da ze taso daga gare ki komai mahimmancin sa kuwa, a gurin Allah nake nema dan haka ki bar abunki koma menene kuma komai amfaninsa"
"karkayiwa kanka gaggawa, ƙarshe kazo kana cizon yatsa, da da nasanin fatali da abunda ya tunkaro ka kayi masa shinge da riskarka saboda girman kai na banza, talakan mutum me dakakkiya zuciya irinka, zuciyarsa cike take buƙatar samun damarmaki, dama irin wadda kowa ke lalube a duhu ko a sarari, katsam se gashi ka sameta a sarari, Amma ka kasa ƙafa kai fatali da ita, me yasa kayi hakan? "
"lokaci abune me mahimmanci a gurina, ina bashi mahimmanci fiye da yadda kike tunani, zefi kyau ki taƙaita wannan dogon surutan naki marasa amfani, a cikin taƙaitattun kalmomi kimin bayani gwari gwari kamar yadda Uwargida Widad keyi, hakan zefi min sauƙi, kuma ze adana lokacin mu".
Wani kallon banza ta watsa masa sannan tace "ko Uwargida ko ubangida wannan kai ta shafa, ni daban ita daban, dama ta sameka amma ka watsar da ita a yadda kake gaka matashi har matashi, kai dai ba muni ba kuma ba nakasa ba, a wannan shekarun naka da ƙirar da Allah yayi maka kamata yayi ace kana wani ɗan ƙwalisa meji da kansa, katsam sega shi ka ƙare a direba, direban ma maƙasƙanci, kana tuƙa ƙaramar Yarinya tana cin zarafinka yadda taso, bata ganin gjrmanka da aikin da kake mata, da kasan maƙudan kuɗaɗen dake cikin Account ɗin nan da tabbas baka dawo gidan nan ba, dan da kai da talauci har gaban Abada, ba kaiba har 'ya'yan ka da jikokin ka ba zasuyi talauci ba, sedai kash garin yin gwaninta kayiwa kanka mugunta"
Yusuf yace "har yanzu jira nake ki faɗi abunda kike tafe dashi, na gaji da sauraren wannan salon maganar taki me tafiyar kura, kiyi gaba kiyi baya kamar kema baki yadda da kanki ba"
"Babu batun rashin yadda da kai sedai ina so muyi tarayya gurin temakon juna ne, ina son ka gayamin password ɗin Widad ne na banki, nayi maka Alƙawarin samun wani gwagwaɓan sakamako indai kayi abunda nace, hakan ze zama madadin wannan shiritar da kayi nayin wasarere da damar daka samu, kuma ze baka damar samun 'yantuwa daga wannan aikin dakake ƙarƙashin wannan Yarinyar me Baƙar Aƙida"
Wani irin kallo Yusuf yayi mata sannan yace
"dukda kasancewa ta talaka maƙasƙanci kamar yadda kuke kirana, Yusuf yafi ƙarfin karɓar abunda zaku bashi saboda wannan baƙin aikin da kuke so inyi, ku tara dukiya da guminku seku yi barazana da ita ko tinƙaho, Bana danasanin aiki na ƙarƙashin Widad, duk inda tayi faɗa ko tsiwa to tabbas an mata ba daidai bane, shiyasa komai tayi take birgeni, kasancewata meyi mata aiki be sa naji cewar ni maƙasƙanci bane, kasancewata me aiki a ƙarƙashinta na sani ƙara samun ilimin rayuwa, dan haka kece maƙasƙanciya da kika ƙallafa rai akan abunda ba naki ba, ni talaka ne me wadatar zuci, dukiyar Widad bata isa ta yanken talauci ba"
"haka kace ko, to shikenan zakaga abunda bijirewa buƙata ta ze haifar maka, ba dai shishshigewa wannan mahaukaciyar ka zaɓa ba, a haka zata ƙare a hauka, kuma death contract data gaya maka zaka ganshi dan kusancinka da ita tamkar kusancinka da mutuwar Kane, Akwai mutanen dake farautar mutane irin ka, wanda suka raɓeta, zasu cigaba da farautarka da bibiyar ka, zasu nemi wani abu a gurin ka, muddin ka gaza yi musu zaka ga abunda ze biyo ba, ka rubuta ka ajiye zaka ce na gaya maka, sakarai mara rabo kawai "
"Ke rabon ne yasa kike zaune a gidan mutane kina harin yin zamba cikin Aminci ai, dukda irin gata da sutura da akai muku"
Wani murmushi tayi me ciwo, badan Widad tana Wulaƙanta su a gaban Yusuf ba ya isa ya kalli idon ta ya gaya mata wannan maganganun, ta ɗaga ido ta kalle shi tace "ka faɗi abunda kake so a yanzu, amma ka saurari ƙalubalen dake fuskantar ka" ta shige ta kunna motarta ta bar gurin a guje.
SHARE PLEASE 🙏
Please pray for my Dad, he is sick
Ayshercool
07063065680
.
_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.
PART1
Page 11
Bin motar Yusuf yayi da kallo harta ƙure, sannan a sannu yaja ƙafar sa ya ci gaba da tafiya abubuwa daban daban na yawo a kwanyarsa.
Maimakon ya tafi gida seya tsaya yayi sallar azahar ya wuce gurin aiki, office ɗin Abbas ya tafi yaje ya tarar da shi yana tsaka da wani aiki, Abbas na ganin Yusuf yai murmushi suka gaisa sannan yace
"Yane mutmina? Akwai wani latest update ne?"
Yusuf ya ɗan ɓata rai yace "na baka abu kayi assisting ɗina kaƙi, seni nayi abuna bakomai nagode"
"wane abu kace inyi assisting ɗin naka naƙi?" Abbas ya tambaya
"Akan mahaifin yarinyar nan Nurat mana, Nace ka tayani bincike akansa amma ƙarshe ni nayi abina"
Dafe kai Abbas yayi yace "Sorry my man, wallahi aiki yayi min yawa na manta shaf"
"Shikenan amma ina tafe da Labari ne"
Abbas ya tattara hankalin sa yace "ina jinka, dama kamar kasan jiya Oga Suleiman yayi min maganarka"
Yusuf yace "Abbas ina kyautata zaton akwai sa hannun matar Mahaifin Widad a farmakin da'ake kai musu"
Abbas ya ture System ɗin gabanshi ya sake tattara hankalinsa yace "ta yaya kenan? Meka gano?"
Nan Yusuf ya gaya masa abubuwan da Su Hajiya Halima keyi, da kuma Yadda suka yi da Ramla"
Jinjina kai Abbas ya shiga yi yace "Lallai biri yayi kama da mutum, amma kaga Oga yana Abuja akan wani case, Amma idan hakane meye alaƙar iyalan Alhaji Nasir da Mahaifin Nurat?"
Yusuf yace "Abunda zan ɗora da bincike na akai kenan"
Waya ce ta fara ringing, Abbas da Yusuf suka shiga waige waigen wayar da take ringing ɗin, Abbas yace "kamar daga jikin ka ringing ɗin ke tashi fa"
Se yanzu Yusuf ya tuna an bashi sabuwar waya, hannu yasa ya ɗakko wayar ya ɗaga, suka gama magana Umma ce ta kira shi.
ssebayan Yusuf ya gama Abbas yace
"jar uba mutumina wannan latest phone ɗinfa? Miƙomin in ganta, yaushe ka siyi waya haka, kaida manyan wayoyi basu dame ka ba?"
Yusuf ya miƙa masa wayar yace "Widad ce ta aikeni na siyo mata wayoyi masu tsada guda biyu, ina kai mata ta bani wannan"
Abbas ya dinga jinjina kai yana jujjuya wayar yace "Lallai ka faso gari, amma kamata yayi ka siyar da ita kai sabgar gabanka da kuɗin"
"Idan kuma ta tambayeni wayar nace na siyar taji daɗin Yimin wulaƙanci ko?"
Abbas yace "A'a ba haka nake nufi ba, Ashe dai har yanzu halin nata na nan, ai kwanan nan Insha Allah zan ɓullo gurin naku"
"to nidai in kazo ka kula, karka sake ka gaya wa wani unguwar da nake, haka kurun sun matsa da son sanin daga inda nake zuwa, dan nima kaina ban yadda da mutanen gidan ba"
Abbas ya kwashe da dariya yace "ashe dai ta koya maka halin nata"
Alert ne ya shigo sabuwar wayar Yusuf dake hannun Abbas, zare ido Abbas yayi yace "Yusuf an turo maka kuɗi"
Yusuf yace "waye ze turomin kuɗi tsakiyar wata haka?"
"wallahi dagaske nake, dubu ɗari shida"
Miƙewa tsaye Yusuf yayi yace "ni a wa? Waze turomin kuɗi haka?tabbas anyi kuskuren lambar account"
Abbas yace "dakata, kuma ba uwaɗakinka bace?"
Shiru Yusuf yayi yace "to aini bata da Account number ɗina, sedai idan naje gobe in Allah ya kaimu in tambaye ta, Amma inma itace gaskiya kuskurene, Kaga Abbas se anjima akwai inda nake son zuwa"
Gaba ɗaya Yusuf ya ruɗe, mamaki ya cika zuciyarsa yafi tunanin ko Ramla ce, dan tana son ta siye shi yayi mata aikin data keso? Amma daga rabuwarsu ta ina zata samu Account number ɗinsa?.
***********************
A mugun fusace Ramla ta koma gida, tana zuwa bata tsaya ko ina bs se ɗakin mahaifiyar su, taje ta tarar da ita suna magana da Amal.
"Mummy akwai matsala fa"
"matsalar me?"
"Mummy this guy is very rude, we have to exact power over him, how dare will he look into my eyes and tells me that he won't do what i ask him to do?" ta ƙarasa maganar tana ta gauraya Numfashi.
"Kinga nutsu kiyi min bayani ya kukayi dashi?"
Ramla ta warware mata komai, Amal tace "da anyi shawara dani da baza'a tun kare shi ba saboda nasan ba zeyi ba, Mutum ne me kafiya da dagewa akan gaskiyar sa"
Cikin fushi Ramla tace "A beg shut up Malama, wayafi kafiya talakan banza mara amfani, ni ya tsaya ya kalli cikin idanuna ya cimin mutunci, shikenan dani yake zancen wallahi se nasa zaman garin nan ya gagare shi banza da kansa kamar lemo"
Amal tace "Wai kansa kamar lemo, kekuma naki fa"?
"dan Allah kuyi min shiru karku yi min faɗa anan, mafita ya kamata munema ba surutu ba, sannan Amal wallahi idan baki kiyayeni akan yaron nan ba sena saɓa miki fiye da tunanin ki wallahi, bazan taɓa aurawa maƙasaƙancin mutum ɗana ba, dan haka ki shiga hankalin ki, zaƙewar da kike masa tayi yawa "
Zumɓura baki Amal tayi ta bar ɗakin.
"Mummy inaga mubi Amal a hankali, tabbas son gayen nan take, Amma cikin hikima zata iya samo mana abunda muke so, ki dena yawan hantarar ta a kansa, karta zo ta bijire mana daga baya fa"
"Bazan bari alaƙar tasu tayi nisa ba, saboda yaron kalar mayaudaran mazane, yana da mu'amala me kyau, daɗin Soyayya ze iya sa Amal ta tona komai, kin san bata da hankali, Amma zan sanar dake mataki na gaba da zan ɗauka.
**************************
Safa da marwa yake yana kaiwa yana komowa a cikin wani matsakaicin Office, yana ta sake nanata maganganun da Oga ya gaya masa game da poisoning ɗin Bala a prison, wani mutum ne yayi Sallama a office ɗin yace
"Yallaɓai Hisham lafiya kake nemana?"
Hisham yayi ajiyar zuciya yace "Oga Bukar ne ya bada wani aiki, kuma muddin aka samu kuskure bamuyi ba ze halaka mu"
"Kamar Yaya? Wai shi meyasa be maida kisan kai komai ba saboda buƙatunsa? Wallahi nayi dana sanin sabga dashi"
"Kwantar da hankalin ka Bashir, mu lallaɓa muyi masa wannan aikin bisa Yarjejeniyar shine na ƙarshe, idan ya cigaba da takuramu, semu ma mu ɗana masa tarko"
Tsaki Bashir yayi yace "ina jinka, me kuma zamuyi masa?"
"yace so yake ayi poisoning ɗin Bala, yadda ze fara rashin lafiya, da an kai shi Asibiti kuma zesa a ƙarasa shi, saboda Balan yayi barazanar tona Musu Asiri, sun barshi a gidan yari tsawon shekaru takwas, sunƙi fitar da shi"
"wallahi Hashim mutanen nan basu da Imani, tsaf muma zasu iyayi mana abunda suka yi wa Bala, amma salin alin muyi abunda suke so, muna dafe kan madarar kawai zan ajiye aikin gidan nan in fece"
Hisham yace "shikenan but you have to focus"
Bashir ya jinjina kai ya fice daga office ɗin.
*********************************
Dogayen kaya ne a jikin Yusuf, yayi kyau sosai ya shiga falon da sallama, ba'a amsa ba kasancewar ba kowa a ciki, ɓangaren Widad ya nufa kansa tsaye, yaje ƙofara falonta ya tsaya, tare da yin knocking.
Ƙasa ƙasa ya jiyo muryar ta tace "Come in" da Sallama ya shiga falon, tana zaune tana shan tea, ya kalleta yace "barka da Safiya ranki ya daɗe" jinjina masa kai tayi ba tare da ta amsa ba, ta cigaba da abunda take ba tare da tace uffan ba.
Haka ya shuɗe tsayin wasu lokuta yana zaune yana jiranta, ga shan tea ɗin take kamar tana shan magani.
Yusuf ya gyara zama yace
"Ranki ya daɗe jiya naga an turomin kuɗi a account ɗina masu yawan gaske, ban sani ba koke ce, shine nace bari in tambaye ki"
"Kana expecting ɗin kuɗi daga gurin wani ne?" tai maganar tana ajiye cup ɗin hannunta
"A'a, bana yi" ya bata amsa
"Anyway salary ɗinka ne na 3 months da ban baka ba"
Zare ido Yusuf yayi yace
"Amma sunyi yawa fa, ya zanyi da wannan maƙudan kuɗaɗen?"
"Zaka iya zubarwa, wannan kai ta shafa"
"A'a Madam, banyi aikin da zan karɓi wannan kuɗaɗen ba, sun yi yawa ban san....
"Kai ɗan Yimin shiru mana, idan ban manta ba kafin in ɗauke ka aiki na gaya maka salary ɗinka, kasan sunyi yawa meyasa kace zaka yi aikin? A beg keep this aside follow me"
Tayi maganar tana miƙewa tsaye ta nufi bedroom ɗin ta, jiki ba ƙwari Yusuf yabi bayan ta.
Wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗakko wayar nan da tasa ya siyo, ta tako zuwa gaban Yusuf, sedai tana zuwa suka ji wani shock a tare, ƙamshin turaren da Yusuf yake yasha banban da wanda ta hana shi sakawa, amma muddin zata ji ƙamshi a jikin sa se wata kasala ta saukar mata.
Shikam Yusuf ƙirjin sa ne ya shiga bugawa da ƙarfi ba tare da yasan dalilin hakan ba.
Widad ta tattaro nutsuwar ta ta dube shi ta miƙa masa wayar, yasa hannu ya karɓa yana kallon ta, a hankali tace
"Yanzu misali a ce wannan wayar ranka ce, a ina zaka ɓoye ta?"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "zan mata kyakkyawan ɓoyewar da babu wanda ze san inda take se Allah"
"Good haka nake son ka ɓoye wannan wayar tamkar na baka ranka, duk kusancinka da mutum karka kuskura yasan da wannan wayar a tare da kai, karka yarda da kowa, wannan wayar tamkar na baka ranka ne!!! ka kula da ita"
A diririce Yusuf yace "Amma me yasa zan kula da ita haka? Ban gane tamkar kin bani raina ba"
Ɗan taɓe baki tayi ta juya tace "bashi da mahimmanci kaji wannan a yanzu, saboda sanin hakan a yanzu tamkar sake jefa rayuwar ka cikin hatsari ne, let me tell you something, don't trust anyone, i repeat myself don't trust anyone, jeka ƙarfe biyar zan fita yau"
Yusuf ya jinjina kai yace "Amma kuɗin nan da kika bani wallahi sunyi yawa"
Widad tace "You can go, na sallame ka"
Yusuf yace "Amma ban san yadda zanyi da wannan maƙudan kuɗin ba"
Ba tare da ta kula Yusuf ba ta shiga ƙoƙarin rage kayan jikin ta zata shiga wanka, ba shiri Yusuf ya juya da sauri ya bar ɗakin, yana mamakin wauta irin ta Widad.
*********************************
Alhaji Musa ne zaune a falon sa, 'yarsa Nurat na kujerar dake facing ɗinsa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunata.
"Wallahi Nurat na rasa me zan miki in huce, da tuni harkar nan ta kankama, amma kikayi mana wauta da hauka, idan abun da muke nema ya samu, se kinfini mora"
Murya na rawa da alama tana tsoron mahaifin nata tace
"dan Allah kayi haƙuri, nima wani ne yace ze saceni idan ban nuna masa inda take ba"
"waye shi ɗin?" ya tambaye ta a ɗan hasale
"Wallahi ban san waye ba, nima bata gayamin waye shi ba"
"Ni zan gano ko waye inyi maganin sa, yanzu dole ki samo wata hanyar abunda zaki yi ta sake zuwa gidan nan"
Saurin girgiza kai tayi tace "Ai kasan ba zata ƙara yadda dani ba, wallahi kome zanyi ba zata zo ba"
A fusace yace "tashi ki bar nan, komai a kasa dake se kinyi wauta, ni nasan abunda zanyi"
****************************
Album guda na hotunan Widad yake dasu a System ɗinsa, ji yake kamar ya janyo kwanakin da ze koma Nigeria, kallon hotunan ta kawai yake hakan ke ƙara samasa nishaɗi.
Video call ya kira Mummy, Hajiya Halima na ganinsa tayi murmushi tace
"'yan makaranta, lokaci ya kusa ko?"
Anwar yace "Eh Mummy se missing ɗinku nake, ina su Ramla ne"
"Suna nan gasu a kusa dani"
"shine ba zasuzo mu gaisa ba, dama ba nemana suke ba"
Amal tace "waze kira ka a kwashe masa kuɗi"
Haka suka dinga video call suna hira da 'yan uwan sa, can yace "Mummy wai ina Widad ne? Naji ance tana Nigeria kuma tunda nake kira bana ganin ta"
Tsaki Mummy tayi tace "Ban sani ba, ita ta haifeka koni? Idan bani kske nema ba shikenan, kullum baka da zance sena wanne banzar yarinyar?"
"yi haƙuri Mumsy, Yadda mahaifinta ya riƙemu ai senake ganin kamar babu laifi dan na tambayi inda take"
Ramla tace "Brother dan Allah karka ɓatawa mutane rai, waya ke maganar wannan mahaukaciyar"
Anwar yace "ni a ganina, Widad rashin me janta a jiki da kuma depression yasa condition ɗinta ya zama complicated, amma...
Cikin tsawa Hajiya Halima tace " Rufemin baki dan uban ka, kaga ka kiyaye ni ko in ɓata maka rai, in baka son ɓacin raina karka sake Yimin zancen yarinyar nan, ko dan kai kana can baka san irin zaman da muke a gidan nan ba"
Ramla tace "ina ze sani, muna nan ta mayar damu kamar bayi, cin kashi kala kala, ana Wulaƙanta mu muda mahaifiyar mu amma kana neman ta"
Anwar yace "Amma Mummy....
A fusace tace "ke Amal katse min kiran nan, shashashan banza kawai"
Amal ta katse kiran.
Anwar ya turawa Amal message
"Amal ɗan turomin lambar Widad"
Ta masa reply da "Taɓɗijan wa kake tunanin ze samu lambar wannan? Duk yadda kake tunanin abun ya wuce haka, ba ruwan ta damu fa"
Jujjuya message ɗin ya dinga yi, babban abunda yake bashi takaici be wuce duk lokacin da ya kira Mummy, ya tambayi ina Widad seta balbaleshi da masifa, duk wanda ya tambaya ya bashi lambar ta kowa se yace bashi da ita, ya rasa meye dalilin hakan.
Yana wannan tunanin Fahad ya shigo ɗakin da sallama, ya kalli Anwar yace "Man what's wrong ne? Nayi sallama baka amsa ba"
Ɗan guntun tsaki Anwar yayi yace "Fahad, ni gaba ɗaya na kasa gane kan lamuran nan dake faruwa, duk lokacin da zamuyi waya da Mummy, idan har zan tambayi Widad se taita faɗa, babban abunda yake bani mamaki shine, wai ace duk gidanmu babu me lambar Widad balle ya bani"
Fahad yace
"Widad Widad Widad, kai dai baka da zance se wannan Yarinyar, please don't kill yourself mana, Nifa yadda kake bani labarin ta sam bata Yimin ba, nifa tun tana ƙarama yadda take wannan Share mutanen haushi take bani, kuma gashi da bakin ka ka gayamin tana da taɓun hankali "
Anwar yace " shut up please, tunda ba zaka bani shawara ba ka ƙyaleni, baka san yadda nake ji akan ta ba, kai kana soyayya amma kamar baka san meye son ba, Ni anya ma in baka Ramla zaka iya riƙe ta kuwa? "
Fahad yayi murmushi yace
"Anwar kenan, aini Soyayya ta da Ramla tana sona ina sonta, amma kai banda wahala babu abunda kake yi"
"Kai kaga wahala, ni bangan ta ba, Ni na ƙagu kamar in janyo lokaci in koma gida, gashi seka rigani komawa Nigeria"
"Allah ya baka lafiya Anwar, dan ga dukkanin alamu ta shafa maka haukan"
Shiru Anwar yayi ya miƙe ya bar ɗakin, dan Fahad ya fara baƙanta masa rai.
Widad tana ta shirin fita, wayarta ta fara ringing, hannu tasa ta ɗau wayar tasa a kunnen ta, shiru ta ɗanyi tace
"Ok, thank you very much, send the address via my email" ta ajiye wayar tana ci gaba da shiryawa.
Maimakon ta fito seta tsaya ta saman bene tana duba lokaci, Yusuf ta hango ya fito da Mota yana ta gogewa dukda a wanke take, abun da ta fuskanta da Yusuf mutum ne meson tsafta sosai, baya son datti sam.
Message ne ya shigo wayar Yusuf ya ɗaga ya duba.
"Ba'a wannan motar zamu fita ba, ka fita waje ka jirani"
Mamaki ne ya kama Yusuf, tabbas Wannan message ɗin daga Widad ne, 'Amma yaushe ta samu lamba ta?' ya tambayi kansa, basarwa yayi ya mayar da motar, yana fita wajen gate yaga wata mota, ba dai me tsada bace dan kamar ma ta ɗanji jiki.
Guri ya samu ya tsaya yana jiran fitowar ta.
Seda yayi kusan mintuna talatin kamar ance ya ɗaga kai ya kalli gate, ganin Widad ne yasa ƙirjin Yusuf bugawa da ƙarfi.
Wani arnen black leg jeans ne a jikin ta, da wata tied pitted blue body hook, tayi stocking ta saka beilt, ɗan ƙaramin baƙin veil ta ɗaure gashin kanta, dukda ƙasan gashin nata ya fito.
Google glass ne a fuskar ta baƙi, ga takalmi me matuƙar tsini, se 'yar ƙaramar jakarta, gaba ɗaya bazaka ce idan Widad ta buɗe baki zata yi hausa ba, duk wani shape da surar jikin ta ya fito.
Tabbas da Yusuf nada damar Mayar da Widad ta canza kaya da tabbas zeyi, dan haka kurum yaji takaicin fitar Widad a haka.
Ƙarasowa tayi ta miƙawa Yusuf key ba tare da tace komai ba, jiji a sanyaye ya karɓa, ya buɗe mata motar ta shiga ya rufe ya zaga mazaunin direba ya zauna, gaba ɗaya ƙamshin turaren da take ya cika motar, ya kalle ta yace
"Ina zamu je?" shiru tayi na ɗan wani lokaci sannan ta miƙa masa wayarta, yasa hannu ya karɓa ya duba.
Adress ɗin inda ze kaita ne, ya ɗago ya kalleta zeyi magana, amma yaga ta ƙara yi masa kwarjini, dan haka ya bata wayar ta ya kunna motar.
Yana cikin tuƙi wayarsa ta fara ringing, Umman Yusuf ne a jikin screen ɗin wayar, ya ɗaga wayar yasa a hansfree ya ajiye ta yace
"Umman Yusuf"
"Ɗan gidan Umman sa, yau zaka dawo da wuri ne, an kawomin wani kifi tun daga Yobe, nayi maka farfesu ka dawo da wuri karya huce, ko kuma in cinye abuna"
Duk da ransa a dagule yake wanda ya rasa dalilin hakan, Amma seda ya maze yace
"Umman Yusuf, ai bazaki iya ci baki ajiye min ba, zan siyo gurasa yai akwai dinner me kyau"
Hirarsa yake yi da maman sa hankali kwance, se shagwaɓa yake yi kamar yaro ƙarami, Widad kuwa ƙura masa ido tayi ko ƙiftawa ba tayi, dukda ta cikin Glas ɗin idonta take kallon sa amma yadda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 35