Gwaggo ɗazu tana ta aiki a tsakar gida, yace mata "dan Allah Mama ko zamu samu ruwan ɗumi, mara lafiyar zata yi wanka, nikuma ko na sanyi ne na samu se inyi Amfani da shi"
Tayi murmushi tace "bakomai, na zuba ruwan tuwon dare dama, bari in ɗibar maka"
Yusuf yace "to nagode"
Ya tafi ɗakin su, ya ɗakko sabon bokiti, aka zuba ruwa aka sirka Yusuf ya koma ɗakin yace "An haɗa ruwan"
Ta tashi zaune ta fara kiciniyar cire rigar jikinta, sedai hannunta na hagu shine wanda aka harbeta, na dama kuma yana ciwo saboda duka da wahalar mota.
Yusuf ya juya mata baya da nufin ta kintsa ya kaita banɗakin.
"Zoka tayani cire wannan rigar na kasa cirewa....
(Akwa ƙura fa🚶 🚶 🚶 🚶 🚶)
Share, share and share please 🙏
Domin, gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 28_29
Gaba ɗaya dirircewa Yusuf yayi, se yayi kamar beji me tace ba, ganin yaƙi magana yasa itama tai shiru ta nemi guri ta kashingiɗa.
Yusuf ya waigo yace "Kin gama kintsawar ne?"
Kawai ya ganta a zaune.
"Ya haka kuma? Se ruwan ya huce?"
"Ban sani ba, ai kana jina ina magana kayi min shiru, nace kazo ka tayani in cire rigar nan, amma kayi kamar baka jiba"
Ikon Allah bata da lafiyar ma, an tsira da ƙyar bakinta be mutu ba, gashi da ƙyar take maganar.
Yusuf yace "bari inyiwa mutanen gidan magana, se suzo su cire miki"
"Wallahi babu matar da zata taɓani" tai maganar tana kuka
Seda Yusuf yayi shiru, sannan ya tako a hankali kan katifar da take, ya zagaya bayanta hannunsa rawa yake ya zuge zip ɗin doguwar rigar tata ƙasa.
Farar fatarta ta bayyana cikin wata baƙar vest, shiru yayi yana kallonta, ta janyo hijjabi ta mayar ta yunƙura zata miƙe tsaye amma jiri ya kwashe ta.
Yusuf yace "ki dena gaggawa, a halin da kike ciki ɗin nan, idan kika faɗi zaki ji ciwo fa"
Ya duba ya ɗakko soson wankanta dake cikin Akwatinta, sedai babu sabulu haka ya riƙota suka fito, Gwaggo na ganin haka ta taho da sauri da nufin ta taya Yusuf, Amma Widad ta maƙale hannunta, ta manne a jikin Yusuf tabi gwaggo da ido, gwaggo ta tsaya sororo tana kallonsu.
Yusuf yace "Mama karki damu, kiyi haƙuri haka halinta yake bata da yadda ne"
Matar dake gaban murhu ta juyo ta kallesu tace "yau nake ganin ikon Allah, wannan gwandamemiyar matar ce take ƙyuya se kace me shan Nono, taɓ amma lamari ya ɓaci, koda yake wannan kamar ma ba irin tamuce ta nan ƙasar ba"
Widad tabi matar gaban murhun da kallo, haƙoranta yellow shar ga haƙorannata wasu sunyi goyon kura, gata baƙa sosai ga fuskarta duk tsagu, gashi se ƙara baje hanci take.
Gwaggo tace "Haba Hari, ina ruwanki da ita irinku ne ke sawa adinga cewa Hausawa basu da kirki, yanzu da taji abunda kike faɗa ba"
Zatonsu duk Widad bata jin hausa, gwaggo ta kalli Yusuf tace "ga banɗakin can seka kaita"
Suna zuwa ƙofar banɗakin Widad tayi tiris taƙi gaba taƙi baya.
Yusuf yace "muje mana seki shiga kiyi wankan"
Girgiza masa kai tayi tace "Ni wallahi tsoro nake ji bazan iya shiga ba" sam Widad gurin be mata kama da banɗaki ba, kamar wani gidan horo haka taga gurin.
"meye abun tsoron, zan jiraki anan gurin kiyi ki fito"
Riƙe shi tayi tsam tana girgiza kai tace "Ni na fasa wankan, bazan shiga nan ba"
Gwaggo tace "ɗan nan ya naga bata shiga ba, lafiya kuwa?"
Yusuf yace "wai tsoro take ji ba zata iya shiga ba"
Gwaggo tace "Allah sarki, ƙasashenku babu irin wannan banɗakin ko? Abun duk se haƙuri ai, akwai wani ɗaki da babu komai a ciki ta shiga tayi a ciki kawai"
Yusuf yace "mungode Mama"
"A'a bakomai"
Ta nuna musu ɗakin, duk yadda Yusuf ya tsani roƙo, haka ya karya billensa ya tambayi sabulun wanka, sedai Sabulun da suke wanka da shi irin sabulun nan ne kore na wanki me ƙarnin tsiya, Yusuf ya miƙawa Widad, tasa hannu ta karɓi sabulun ta kalli Yusuf kawai yaga Hawaye a idonta.
Tausayinta ya kama shi, amma ya basar kamar bega hawayen idonta ba, haka ta shiga ɗakin da siminti a ƙasan ɗakin, tayi wankan nan tsigar jikinta na tashi saboda yadda ruwan in ya zuba a ƙasa yake taɓata, ga tashin zuciya saboda ƙarnin sabulun, ba shiri ta ajiye sabulun tayi wankan a haja, sedai taji daɗin ruwan zafin sosai "
Ta fito tana kama bango, Yusuf ya riƙeta ya maida ita ɗaki, ya duba Akwatinta ya ɗakko kaya ya bata, ta saka itama tayi salla.
Saleh beje gida ba se bayan sha biyu na dare, yayi tunanin ko yaje yayi magana da doctor Safwan amma wata zuciyar ta hana shi, saboda yadda Safwan ya dinga rawar jiki da yaji batun kuɗi tsaf zeje ya gaya musu, yaje ya sameshi.
Gaba ɗaya tunaninsa ya koma kan yaze ƙwaci Alhaji Nasir a gurin wannan Azzaluman mutanen? Dan ba ƙaramin shiri suke dashi ba.
Me Adda suka koma inda suka ajiye su Widad, da niyyar ayita ta ƙare, suna zuwa suka buɗe gidan, suka shiga suka saka mukulli suka buɗe ɗakin suka ga wayam ba kowa a ciki, a kiɗime ɗayan yace "Me Adda bafa kowa a ɗakin nan"
Ƙarasawa yayi da sauri ya shiga ɗakin shima amma ba kowa a ciki, nan da nan suka gigice suka shiga lalauben su Widad.
Me Adda yace "Mutanen da ko iya takawa basayi, ta yaya zasu gudu? Duk matakan tsaron dake gurin nan ina sukabi suka fita?"
Cam ɗaya daga cikinsu ya ɗaga kai ya kalli Roofing ɗakin yace "me Adda kalli ta nan suka fice" yai maganar yana nuna musu saman roofing ɗakin
Me Adda a gigice yace "ya zama dole mu bazama neman su, amma ta yaya suka samu abu sukayi hanya har suka fita?"
Ɗaya daga cikinsu yace "Allah ne ya san yadda suka gudu"
Me Adda yace "bamu da lokacin ɓatawa, maza maza mubi sahun su yadda suke a galabaice ba lallai su iya tafiya me nisa ba"
Haka kuwa akayi suka rarraba kansu a cikin daji.
Saleh yaje duba Alhaji Nasir a Asibiti, ya tarar da Anwar a gurinsa, suka gaisa yayi masa ya me jiki, ya ɗan dubi Anwar yace
"Amma meyasa baza'a fita da Alhaji waje a nema masa magani ba?"
Anwar yace "Nayi duk me yuwuwa inga an fita da shi, amma Mummy da Alhaji Bulama sunce nan ma ana kula da shi"
Saleh yace "Abunda za'ayi yanzu shi ne, ka ɗauke shi ka canza masa Asibiti ba tare da ka sanar dasu ba, ko ba'a fita dashi waje ba a camza masa Asibiti, sedai kawai suga ka canza maaa Asibiti"
Anwar yace "Amma zasuji babu daɗi idan nayi hakan, suna ganin nanma ana ƙoƙari akansa amma inyi haka kamar ban kyauta ba"
"Anwar zamanku a Asibitin nan yaci ace jikinsa yana karɓar treatment yadda yakamata, amma har yanzu babu wani cigaba, mu canza masa wani Asibitin kawai"
Anwar yace "Kana ganin babu matsala idan muka yi hakan?"
"eh babu matsala, Amma karkace ni nace ka canza masa Asibiti"
Anwae yace "shikenan, ka kawo shawara me kyau insha Allah gobe in Allah ya kaimu da Safe, sedai suzo su tarar na canza masa Asibiti ni kaina rashin samun sauƙin nan nasa yana bani mamaki"
Doctor Sufyan ne yake ta zagaye acikin Office ɗinsa, yana tunanin me yakamata yayi akan batun su Alhaji Haruna, yana tuno irin halacci da kirkin Alhaji Daula, idan aka haɗa kai dashi aka cutar dashi to tabbas mesa Adalci ba, Amma wani mataki Alhaji Musa zasu ɗauka akansa idan har be abunda sukace ba?.
Fitowa yayi da sauri daga office ɗin nasa ya nufi ɗakin da Alhaji Nasir yake, yana zuwa shiga suka haɗu da Saleh, suka yi kallon kallo babu wanda ya cewa kowa komai suka wuce.
Ya shiga ɗakin da Sallama, Anwar ya amsa masa, doctor Sufyan yace "Anwar yame jikin kuwa?"
"Jiki sedai muce Alhamdilillah, amma doctor na fara karaya da yanayin jikin sa, babu wani cigaba fa gashi nayiwa su Mummy magana a fita dashi amma sunƙi amincewa, na rasa dalili"
Sufyan yace "ka kwantar da hankalinka Anwar, treatments ɗin dai da muke masa anan, shi za suyi masa a can, komai ze tafi dai dai ze warke in Allah ya yarda"
Anwar yace "Shikenan Allah yasa"
Haka Widad ta kwanta akan katifar, Yusuf ya ɗau bargo ɗaya ya koma bakin ƙofa ya shimfiɗa ya kwanta, shiru Widad ta kasa bacci, tana tunanin wai itace zata kwana a gurin nan, ga sauro se kururuwa yake mata a kunne, ga zafi ga jikinta da yake ciwo, ga rashin lafiya tana fama.
Ɓangaren Yusuf ma shiru Yayi yana saƙe saƙe, yana tunanin wani hali Ummansa take ciki, yasan duk inda take hankalin ta a tashe yake, dan tun tasowarsa be taɓa nesa da ita ba, wani ɓangare na zuciyar sa yana tunanin Alhaji Nasir yasan tabbas shima yana cikin damuwa, ko wani haki yake ciki Allah masani, ga zamansa da Widad a ɗaki ɗaya baze yuwu ba, tunda ba muharramarsa bace, gashi ba ta yadda da kowa se shi, ga wasu abubuwan se anyi mata saboda bata da lafiya, dole idan Saleh yazo yayi masa magana asama masa wani ɗakin, dan gudun afkawa tarkon sheɗan.
Yana nan kwancw sauro yana cizonsa, yana masa hada hada aka, ga cinnaka da yake ta gasa masa cizo a gurin nan, tunani yake Allah yasa kae cinnakan ya ciji Widad.
Katsam ya jiyo sheshsheƙar Widad tana kuka, da yayi kamar ya basar amma ya dinga jin kukan nata a zuciyar sa, tabbas yakamata a tausaya mata.
Ɗakin baƙiƙirin da duhu, ko tafin hannu ba'a iya gani saboda duhu, haka yaja jikinsa cikin lalube yaje gefen katifar ta yace "uwa ɗakina kukan me kike?"
Maimakon tayi magana seta sake fashewa da kuka, Yusuf yace "Am sorry, i feel your pain kiyi haƙuri ki karɓi hakan a matsayin ƙaddarar mu, yakamata ki gode Allah da yasa muka tsira daga hannun mutanen nan, kuma insha Allah zamu koma gida ki dena kuka, kiyi bacci zaki ji daɗin jikin ki"
"I can't sleep, sauro ya dameni zafi nake ji, kuma ina tunanin Daddy na"
Tai maganar tana sake fashewa da kuka.
"kiyi hakuri, Insha Allah Daddy yana nan lafiya, komai ze wuce kamar be faru ba, ki dena kuka kinga baki da lafiya"
Ajiyar zuciya kawai tayi, ta lumshe idinta tana jin yadda zuciyarta ke raɗaɗi.
Da Asuba yayi Alwala yazo ya tada Salla, bacci take dan sam bata samu bacci ba da daddare, seda ya idar sannan ya tashe ta ya kaita tayi alwala tazo ta tada salla.
Da gari ya fara haske me gari da kansa yayi sallama a ƙofar ɗakin su Yusuf, Yusuf ya fita ya durƙusa ya gaishe shi.
Ya amsa cikin mutuntawa yace "Ya me jikin kuwa?"
Yusuf yace "Jikinta da sauƙi Alhamdilillah"
"Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa ya bata lafiya, karkaji komai ku saki jikinku duk abunda kuke buƙata kuyi magana insha Allah baze gagara ba"
Yusuf yace "Masha Allah, mungode sosai da wannan karamcin naku"
"Karka damu, ai shi ɗa na kowa ne"
Wajejen ƙarfe tara na Safe aka aiko yaro ya kawowa Su Yusuf Koko me zafi da ɗumamen tuwo, Yusuf ya karɓa yace sun gode.
Ya kalli Widad dake zaune tayi shiru, gwanin ban tausayi yace "ga Abinci an kawo, ki daure kici se Kisha magani"
Kallon kwanon tuwon tayi, sannan ta kalli kwanon da'aka zubo kokon, har ɗan gara kwanon kokon, amma na tuwon dai se a hankali ga warin daddawar nan ji tayi kamar tayi amai, miyar nan baƙa wuluk ga uban tuwo a ido in ka kalli Tuwon nan kasan ze azabar tauri.
Ta kalli kokon tana tunanin ta ina zata sha abun sha a cikin kwano, ta kalli Yusuf tace "janye min wannan baƙin Abincin kar inyi amai"
Kallonta yayi da mamaki, tuwon ne bata sani ba ko kuma tsabar rainin hankali ne? Ta miƙa hannu ta ɗau kwanon kokon, ta dinga juya kwanon sannan ta kai bakin ta, karɓa ɗaya tayi ta dire kwanon ta yamutsa fuska kamar zata yi kuka.
Yusuf yace "ya dai?"
"Ba daɗi" ta bashi amsa
"to ai badan daɗi zaki sha ba, kinga nan ba kamar gida bane da zakici abunda kike so, ki daure kisha"
Banza tayi masa taƙi kallonsa, ya ɗau kwanon ya zuƙi kokon, kokon dawane kuma gasarar tayi tsami dan ta ɗan fara wari ma, gashi babu ko ɗigon sugar a ciki.
Yusuf yace "kinga babu wani Abincin da zan baki, idan baki sha ba babu wani Abincin da zaki samu kici, ki daure ki ɗauke numfashi kawai kisha"
Da ƙyar ya lallaɓata ta sha kokon nan shima kaɗan ta sha tace ita ta ƙoshi, sannan ya bata magungunanta.
Yusuf yace "Inaga yakamata inyi musu magana, idan da hali a bani ɗakin da zan dinga kwana, kinga be dace mudinga kwana a ɗaki ɗaya nida ke ba, sannan dole kiyi haƙuri su ɗan dinga temaka miki ko gurin wankan ne da canza kaya, nida nake miki be dace ba, tunda ba muharrama tace keba"
Da sauri ta kalle shi tace "Nikaɗai zan dinga kwana a ɗakin nan? Ni gaskiya bazan iya ba"
"to se a samu a yaran gidan wasu su dinga ta yaki kwana"
Ai tuni ta fara kuka tace "Ni wallahi ba wanda nasani a gurin nan ba zaka tafi ka barni a ɗakin nan ba, kuma wallahi niba zasu dinga taɓani ba, wannan matar me haƙora tsoro take bani, in ba haka ba kawai ka maida ni gida"
Yusuf ya ƙara kwantar da murya yace "Widad mufa musulmi ne, mun san illar zaman mu a guri ɗaya, bekamata yadda nake kula dake ba bayan ga 'yan uwanki mata a gidan nan ba"
"to ni ka maida ni gida mana, kkme ze faru ya faru amma wallahi ba inda zaka tafi ka barni".
"so kike mu koma gida wani abu
ya sameki?
" Idan ba zamu koma gida ba, to bazaka bar ɗakin nan ba, in ba haka ba ni zan tafi gidan nikaɗai "
"Amma kin san zamana dake a ɗaki ɗaya ya saɓawa shari'ar musulunci?"
Shiru tayi bata ce komai ba, Yusuf yace "kiyi haƙuri, mutan gidan nan suna da kirki kuma duk mutane ne, babu wanda ze cutar dake, kiyi haƙuri zanje in samu me garin muyi magana"
Riƙo rigar Yusuf tayi ta fashe da kuka tace "Wallahi bazan dinga zama a ɗakin nan nikaɗai ba, sedai duk inda zaka in bika"
Shiru yayi yana Kallonta, kuka take sosai har cikin ranta, tabbas yasan halinta da ƙyanƙyami da rashin yadda, ba zata yadda ta zauna da kowa a ɗaki ɗaya ba in bashi ba, kuma gashi hakan ya haramta.
Jiki a sanyaye yace "shikenan is ok kidena kuka, idan har kina son mu cigaba da zama tare a ɗakin nan inyi jinyarki bisa shari'a mafita ɗaya ce, kuma mafitar nasan me tsaurin gaske ce a gurinki ba lallai ki yadda ba"
Widad ta ɗago idonta tace "Meye mafitar?"
Yusuf yace " Sedai ki amince muyi Aure zuwa lokacin da zaki warke, mu koma gida semu rabu"
Gaban Widad ne ya faɗi ta tsaya tana masa wani irin kallo
Duk yadda me Adda yake tunanin lamarin ya wuce tunaninsa, dan babu wata alama ko sheda da zata nuna maka inda su Yusuf sukabi, suka yi sintiri da neman duniya a dajin nan basu sami su Yusuf ba, me Adda yace "gaskiya ina mamakin guduwar mutanen nan, tabbas akwai munafiki a cikinmu, wanda ya kuɓutar dasu banda haka yaza'ayi mutanen da ko tashi basa iyawa ace sun gudu?"
"Oga nima dai nayi wannan tunanin, dan tabbas maganar ka haka take, da saka hannun wani a kuɓutar tasu"
Me Adda yace "Ni yanzu tunanina yadda zanwa wannan mutanen bayanin sun ɓata, dan wallahi babu lallai su ƙyalemu"
"To Oga ko muma sanfewa za muyi muyi ta kanmu"
Me Adda yace "ƙwarai kuwa, Amma zamu fara kiransu mu gaya musu su san meya dace suyi, sannan muma muyi ta kanmu da ba mutunci mutanen nan suka cika ba"
Suleiman shike zuwa ya rarrashi Maman Yusuf, dan ko Abinci bata iya ci, sedai wataran inzeje yayi mata Nasiha ya sai wani abun ya kai mata.
Yauma bayan Azahar da ya taso daga gurin aiki gidan su Yusuf yaje, yatarar da Umman Yusuf akan dadduma taci kuka ta ƙoshi, idanunta duk sunyi jawur.
Suka gaisa Suleiman yace "Umma har yanzu baki dena kukan ba? Ki sani wannan carbin da kike ja kina masa Addu'a yafi wannan kukan da kike yi, dan Allah ki kwantar da hankalinki, kar wani ciwon ya shige ki"
Umman Yusuf tace "To Suleiman dangana ta zama dole, yau da gawar Yusuf na gani seta fiyemin kwanciyar hankali akan ɓatansa, ban san a ina yake ba, yaci Abinci? Yayi wanka? Me yake ciki? Yana samun Abincin da yake so duk ban sani ba, Allah ne kawai ya barwa kansa sani, dole in shiga damuwa inyi kuka"
Suleiman yace "hakane Umma, amma ki kwantar da hankalinki, muna nan muna bincike akan mu gano inda Yusuf yake, very soon zakiji labari me daɗi, kuma kisawa zuciyarki addu'ar nan da kike tana isa ga Yusuf insha Allah muna sa ran jin labari me daɗi akan Yusuf"
Umman Yusuf tace "Nagode Suleiman, Allah ya saka da alkhairi tunda abun nan ya faru kai kaɗai kake zuwa inda nake ka rarrashenin, Nagode Allah yayi Albarka"
Suleiman yace "Ameen Umma, kin san mahaifin yarinyar ma yana can a gadon Asibiti, sedai fatan Allah ya bayyanasu"
Umma ta amsa da Ameen.
Nurat ta kuma satar jiki, mahaifiyarta bata sani ba ta tafi Asibiti duba jikin Baban Widad, koda taje Anwar kawai ta gani a gurinsa, sedai abun mamaki har yana zaune yana cin Abinci da kansa.
Nurat tace "Alhamdilillah lafiya ta fara samuwa, ya ƙarfin jiki kuwa Daddy?"
Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, yau gani a zaune ina cin Abinci ma"
Nurat tace "Alhamdilillah"
Ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar ina kwana"
Anwar yace "lafiya ƙalau, ya mutan gidan?"
"duk suna lafiya Alhamdilillah, Amma ina su Anty Ramlah ne?"
Ɗan kame kame Anwar ya fara yace "kin san da yake tunda Daddy ya kwanta itama taƙi lafiya, tana can tana jinya su Amal ke kula da ita"
Nurat tace "Allah sarki, Allah ya sawwake naje in duba ta"
Saleh ne yayi sallama ya shigo, yana ganin Daula a zaune yace "Alhamdilillah Alhajin Allah, kaine a zaune haka kake cin Abinci?"
Daula yayi murmushi yace "Alhamdilillah, tambayi Anwar da kaina na tashi na zauna, sedai bana jin daɗin Abincin sam tunanin 'ya' yana nake, ban san a halinda suke ciki ba"
Saleh yace "Insha Allah suna lafiya, kuma da yardar Allah za'a gansu"
Nurat tayi shiru zuciyarta gaba ɗaya ta tsinke, tausayin Daddyn Widad ya kamata, ji take tamkar ta gaya masa abunda ke faruwa, Amma idan ta faɗa da wani suna za'a kirata, kuma meye hujjarta na cewa da hannun mahaifinta a sace Widad tunda ita kaɗai taji abunda suka faɗa, Mahaifinta yana zaune da nasa iyalin cikin kwanciyar hankali, amma ya jefa rayuwar wannan iyalan cikin fargaba da damuwa.
Tana cikin tunanin Daddy yace "Nurat, ki koma gida kinji ko, nagode sosai Allah yayi miki Albarka"
Nurat tace "Ameen Daddy"
Ta miƙe tsaye ta fita, Anwar yabi bayanta suka fita, suna fita harabar ta tsaya ta kalli Anwar tace "Yaya Anwar wai meyasa baza'a fita da Daddy waje ba, tunda yana da kuɗin nan ba babu ba? Kana kallon da yadda yake numfashi fa"
Anwar yace "Wallahi Nurat, nayi iya yina amma su Mummy sunƙi Amincewa, wai anan ma ana kula dashi, Jiya Saleh ya bani shawarar ko Asibiti in canza masa basu sani ba, sedai kawai suga an canza amma ina tunanin abunda ze biyo ba idan nayi hakan"
Nurat tayi ajiyar zuciya tace "ya batun taron kasuwanci da'ake yi duk ƙarshen shekara da ma'aikata da 'yan kasuwa kuwa?"
Anwar yace "Ana nan za' ayi jibi insha Allah"
Nurat tace "babu wanda ze wakilci Daddyn Widad kenan?"
"Nurat ana ta lafiyarsa wake ta wani taron kasuwanci"
"Amma idan da kara, tunda shike jagorantar taron ayi wani abu akai, tunda yana kwance ba lafiya"
"Ayi wani abu kamar me kenan?"
Nurat tace "A ɗaga taron zuwa wani lokacin"
Anwar yace "kina ganin su saura mahalarta taron zasu yarda da haka?"
"Yaya Anwar, ƙaddara bata wuce kan kowa ba, dan haka babu laifi idan munyi wani abu akai"
Anwar ya gyara tsaiwa yace "to gurin wa zamuje ayi mana wannan Alfarmar?"
Nurat tace "karka damu ina da hanya, duk yadda ake ciki zan kiraka amma wannan maganar da gani se kai, karka gayawa kowa"
"insha Allah babu wanda zan gayawa, Allah ya saka da alkhairi da wannan taimako da zakiyi"
"Babu komai yaya, yiwa kaine inda kara ai bekamata ayi taron nan Daddy na kwance ba"
A ranta kuwa cewa tayi "daka san Abunda ake shirya yi a gurin taron nan, da kaima ka nemawa Alhaji Daula mafita '
Saleh ya kalli Alhaji Daula yace
" Yanzu idan nace maka na san inda Widad take zaka yadda? "
Daula yayi murmushi yace " daka san inda Widad take da baka ƙyaleni ina fama haka ba"
Saleh yace "Hakane, jikina yana bani Su Widad sun kuɓuta, sedai kasan su dawo cikin garin nan hatsari ne?"
Daula yayi shiru yace "Tabbas, dan mutanen nan basu da imani, Allah kaɗai yasan halin da suke ciki, ina cikin damuwa sosai Saleh"
Saleh yace "Insha Allah nan ba da daɗewa ba zanzo maka da Labari me daɗi a kansu"
"kamar yaya kenan?"
"Kai dai ka kwantar da hankinka Alhajin Allah, kasan retired solder neni, nasan techniques na abubuwa da dama, dan haka ina daf da gano su"
Riƙo hannun Saleh yayi yace "Dan Allah Saleh dagaske kake? Gaba ɗay....
Farinciki yasa Daula kasa cigaba da magana, sema tari daya sarƙeshi.
Saleh yace" ka kwantar da hankalinka, Amma wannan maganar iyani da kaine, ban yadda wani yaji ba, ko Bulama karka sake ka gayawa "
" Insha Allah bazan gayawa kowa ba, Nagode Saleh "
Yusuf ya cigaba da kallon Widad da take masa wani irin kallo, zame hannun ta yayi daga jikin rigarsa yace
" Shikenan tunda baki amince ba, na manta baki da babban maƙiyi kamar Aure, kuma Aure ma kamar Auren maƙasƙancin mutum irin direbanki, bani da wani zaɓi na zama dake inba Aure mukayi ba, kuma niba abunda ze haɗa ni dake har mu gama zamanmu anan mu koma gida, tunda baki amince ba shikenan "
Ya ƙarasa maganar tare da miƙewa ya nufi hanyar fita, jiki a sanyaye Widad tace
"Na Amince!"
Share, share and Share please 🙏🙏🙏
Domin gyara sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 35