Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fara ƙwanƙwasawa "Lovely daughter, Dad ɗinki ne, ki buɗe ƙofa kinji, karkiwa kanki illa" Still Widad ba tayi responding ba, dan ko motsin ta basaji. Alhaji Bulama yace "Kuma babu wani abu daya haɗaku da ita? Kowani saɓani ko ayi mata wani abun?" Ramlah tace "waze nata wani abu kuwa? Ita wannan se an mata wani abu? Ai sedai tayi wa wanima,wataƙila haukan nata ne ya motsa" Alhaji Bulama yace "ku bani mukullin ɗakin ta, a buɗe ɗakin karta" Mummy tace "taɓ wake da mukullin ɗakin basarakiya, ita da bata yadda da kowa ba, wa zata bari ya mallaki mukullin ɗakin ta ba wanda yake da mukullin ta" Alhaji Bulama yace "to ko maza za'a kirawo su ɓalla ƙofar a gani" Ramlah tace "A'a karka jamana Jaraba, a ɓalla mata ƙofa ka samu a tashin hankali da masifarta, a kira Baban ta aji meze ce" Alhaji Bulama yace "Keba babanki bane Ramlah"? Cikin tsiwa Ramlah tace "Niba baba na bane, kullum bata da gori seba gidan ubanmu bane, dan haka ubanta ita ya haifa bani ba" Yau Yusuf ya makara dan se sha ɗaya ya tashi na safe, tunda ya koma bacci ƙarfe takwas na safe, dan haka a gurguje ya kintsa ya fito, yayi sa'a Umma bata nan ta fita, dan haka ya kulle gidan ya fita, ya nufi gidan su Widad. Yana zuwa suka gaisa dasu Nura sama sama,suna masa wani kallon banza Yusuf ya kalli Murtalah yace "Murtalah Madam ta fito kuwa? Ko tazo nema na naga yau na makara sosai" Murtalah yace "ina fa, tana can tun jiya taƙi buɗe ƙofa, ana can anata fama da ita, ba wanda yasan tana raye kota mutu, gashi babu wanda yake da mukullin ƙofar ta, ana tunanin ko ɓalla ƙofar za'ayi Zaro Ido Yusuf yayi ba tare da yace komai ba, ya tashi da sauri ba tare da tunani komai ba ya tun kari cikin gidan. Isa ya taɓe baji yace "kalli uban shisshigi, Allah yasa yana zuwa su Wulaƙanta shi su koro shi, banza me rawar kai kawai" Murtalah yace "Haba Isa, ka sawa Yusuf ido da yawa wallahi, gashi kullum ƙara samun matsayi yake a gidan nan fiye da kai" "dalla rabu dani, se kace baka ganin yadda aka fifita shi akanmu a gidan nan, danma mun samu mu Hajiya tana bayan mu, duk yadda muka so samun gindin zama a gurin yarinyar nan muka kasa, Amma shi daga zuwan sa ga yadda ya samu sake yake wani zaƙewa kamar gidan ubansa" Yusuf kuwa na shiga Babban falo ya gansu a zazzaune suna tattaunawa, Ya durƙusa ya gaishe su. Alhaji Bulama ne kawai ya amsa, se Amal da tace "Sannu da zuwa" Hajiya Halima tace "To Munafuki me ka shigo yi uban iya" Yusuf yace "Naji ance Madam bata fito daga ɗaki ba yau kwana biyu shine nace..... Cikin hantara Ramla tace "shine me, mezaka iya? Bama son munafunci malam jeka mungode, Anjima baban ta ze dawo, yasan yadda zeyi da ita uban shishshigi" Yusuf yace "Amma be kamata a barta har se ya dawo ba, babu wanda yasan halin da take ciki, ta rufe kanta a cikin ɗaki yakamata a duba halin da take ciki" Hajiya Halima tace "kai bana son rawar kai irin naku na matsiyata, ka fimu sanin abunda ya dace ne? Dalla ɓacemin daga nan" Alhaji Bulama yace "A'a Hajiya Halima, kika san Alaƙar dake tsakanin su?, ki ƙyale shi ya Jarraba mana wataƙila kiga ta buɗe ƙofar, kaga tashi kaje ko zata buɗe" Yusuf ya miƙe ya nufi hanyar ɗakin ta. Yana zuwa ƙofar ɗakin ba tare da ɓata lokaci ba, yasa hannu a aljihunsa ya ɗakko mukullayen motocin ta dake gurin sa, ya saka key ya buɗe ɗakin nata, da yake yasan mukullin ƙofarta ta falo da ta bedroom tunda tana aiko shi ɗakin. "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un!!!" Shine abunda Yusuf ya faɗa In an karanta ayi share please 🙏 07063065680 Ayshercool _*AƘIDA TA*_ PERFECT WRITERS ASSOCIATION (WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS) https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/ P. W. A *Story and written by* _*AISHA HUMAIRA (Daddy's girl)*_ The experience writer of *ABDUL JALAL* * WATA KISSAR.... (SAI MATA) * And now *AƘIDA TA * I dedicated this book to my Mum (Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in PART1 Page 9 _Asslam Alaikum warahmatullah_da _fari dai zanyi wata magana_ _tun page ɗin farko nayi bayani_, _nace ina da Jarrabawar ƙarshe_, _ina ƙoƙarin cika Alƙawari ne yasa na cigaba da kawo_ _littafin nan ɗaya ga watan October_ _nace bazan samu yin posting kullum ba_ _amma ina iya ƙoƙarina inga nayi duk dan faranta muku_ _amma wasu na ƙorafi hadda gayamin baƙar magana_ _dan bana posting kullum_ _littafin nan dai nina sa kaina_ _kuma nace free ne balle ace siya akayi nake jan rai_ _babu wanda nayiwa dole seya karanta_ kuma ban karɓi kuɗin kowa ba, _ni nake saka data in ɓata lokacina inyi typing sannan inyi posting_ _dan haka wanda baze iya haƙuri ba ze iya dena karantawa_ ba zanyi _typing kullum ba tunda ba siyarwa nayi be_ _Ni bana Wulaƙanta kowa nasan soyayya ce tasa ake karanta littafina _ _Masoya har kullum ina sake godiya da Comments ɗinku da Addu'oinku_ _zancigaba da ƙoƙarin faranta muku Insha Allah_ Widad ya hango zaune acan ƙarshen gado kamar Mahaukaciya tuburan, rigar jikin ta iya cinyar ta, gaba ɗaya gashin kanta a hargitse, ta sunkuyar da kanta jikin ta se rawa yake tana kuka, ta rufe ko ina babu haske a ɗakin, seda ya buɗe ɗakin sannan haske ya bayyana a ɗakin. Babban abunda ya bawa mutan gidan mamaki be wuce yadda akayi Yusuf ya mallaki mukullayen ɗakin Widad ba, alhalin su raɓar ɗakin nata ma basu isa suyi ba, balle samun mukullayen. Da sauri ya ƙarasa gaban gadon ta yana ambaton Subhanallah,tana ɗagowa taga Yusuf ta gigice ta fara ja da baya tana girgiza kai. Yusuf yace "Meya sameki haka? Ki kwantar da hankalin ki, Yusuf ne direban ki fa" Girgiza masa kai tayi tana kuka tace "Ni karka kasheni" "No ba kashe ki zanyi ba" Ɗaga kai tayi ta kalli su Alhaji Bulama dake tsaye suna kallon su, riƙo rigar Yusuf tayi kamar zata yagata tace "Suwaye wannan? kace su fita bana son ganin su, kace su fita su bar nan" ta faɗa cikin ɗaga murya da zubda hawaye. Yusuf ya zauna yace "Calm down, kinga fa wancan Dad ɗinki ne Alhaji Bulama, ga Mummy, ga Ramlah ga Amal, sune baki gane ba?" Alhaji Bulama ya tako yazo inda suke, ya miƙa hannu ze riƙo Widad. Wata irin ƙara ta saki, ta rirrƙe Yusuf tana ɓuya a bayan sa tana girgiza kai, cikin ƙaraji take cewa "Ni su fita, su fita su bar nan gurin, kasheni za suyi, kana kallo nima zasu kasheni, bana son ganin su ba wannan ne Daddyna ba kuma bashi ne Bulama ba" Yusuf yace "buɗe ido ki kalle su fa, ga Daddy Bulaman nan s tsaye a gaban ki" Girgiza kai tayi tace "bashi bane ba, na gaya maka bashi bane" Ta rungume Yusuf gam tana ci gaba da zubar da Hawaye. Yusuf a ransa yace "ta tabbata kenan Widad tana da taɓin hankali? In ba haka ba meze sa ta koma haka?" Alhaji Bulama yace "Karka damu dama tana yin hakan wani lokacin, ciwonta ne ya tashi" Ihun da take yi ne iya ƙarfinta, kai kace wadda ake yankawa, ba shiri suka bar ɗakin Amal wani irin baƙin kishi ne ya cunkushe zuciyarta, yadda Widad ta rungume Yusuf yafi komai yi mata ciwo. A hankali Yusuf yace "Kinga sun fita ba kashe ki za suyi ba, cikani ki ga wani abu" Girgiza masa kai tayi "tace ni A'a tsoro nake ji, kasheni za'ayi nima an kashe Ammi nima kasheni za'ayi" Yusuf ya girgiza mata kai cike da damuwa yace "Ai ina nan tare da ke, ba inda zani babu me taɓa ki idan ina nan insha Allah , ba wani abun tsoro fa" A hankali ta cika Yusuf tana sauke Ajiyar zuciya, hawaye na cigaba da bin fuskarta. Yusuf ya kalle ta yace "je kiyi brush se kici Abinci, ance tun jiya baki ci Abinci ba" Girgiza masa kai tayi Alamar A'a. "Idan baki abunda nace ba, zan tafi in barki anan suzo su tafi dake" A firgice ta kalle shi, ya jinjina mata kai alamar eh, rigarsa ta kuma riƙewa gam ya rakata banɗaki ta wanke baki, ta fito, tana ta binsa da kallo kamar taga wata halitta daban. Da yayi hanyar fita seta biyo shi tana sake rirriƙe shi, gaba ɗaya tausayinta ya kama shi, ya ɗauki bedsheet ɗin dake kan gadon ta ya ɗaura mata, ya ɗakko hula ya saka mata. Alhaji Bulama ya kalli Hajiya Halima yace "Nayi mamakin abunda ya tayar da ciwon Widad, na zata tuni ta warke?" Hajiya Halima ta taɓe baki tace "to ni ina zan sani, daga ita se ubanta se kuma kai suke sakawa a lamarin su, ta yaya zan san kota warke ko bata warke ba" "Amma abun da mamaki, Akwai buƙatar ta cigaba da ganin likitan ƙwaƙwalwa kenan?" "Wannan kuma ya rage shawararka kai da Mahaifinta, ni 'yar kallo ce ai tunda alamu sun nuna haukan yana nan tuburan" Bulama yace "Hajiya Halima ai ba kyace haka ba ɗa na kowane" "A'a wannan dai bata kowa bace, ta babanta ce kawi, ka dena wannan maganar nawa' ya'yan dai nawane, itama 'yar wasu ce" Ƙyalƙyalewa da dariya Alhaji Bulama yayi yace "Shikenan tunda haka kikace, ni dai na tafi, Munyi waya dashi Megida kafin inzo nan yace yana kan hanyar dawowa, zezo ya dubata idan jikin da sauƙi ya koma, idan kuma da yuwuwar a maida ita ga likitocin ƙwaƙwalwa shikenan, dan be gama abunda yake ba ze yanke ya dawo, kin san idan bata da lafiya baze iya komai ba, Allah ya bata lafiya" Hajiya Halima tace "Karma Allah yasa tayi lafiyar, Ita da ubanta ya shafa bani ba" Alhaji Bulama ya girgiza kai ya fice. Yusuf Ya kira Amal a waya, ta ɗaga tana tura baki, dan gaba ɗaya kishin Yusuf take, Yusuf yace "Amal dan Allah ki kawo Abu me ɗan ɗumi a bata taci, da alama tana jin yunwa sosai" "wallahi Yusuf ba dan kai ba ko zata mutu ba zan kawo komai taci ba, kaima ɗin dai kawai zan kawo ne" "Yi haƙuri, Nagode sosai da kika min Alfarma" Amal ta shiga kitchen ta haɗa kayan tea, Mummy tace "Me zakiyi da tea ranar nan?" "Widad za'a bawa" ta bata amsa "ke meye naki a ciki to?" "Mummy wai so kike se duniya tasan halin da muke ciki ne? Kar hankali ya dawo kanmu, Ai se munayi muna ɓadda sahu" Mummy tai murmushi tace "daɗina dake wani lokacin akwai hankali, ɗakkomin Jakata a ɗaki" Amal taje ta ɗakko mata jaka ta dawo, sannan ta ɗau tray ɗin ta tafi part ɗin Widad. Yusuf ya miƙe da nufin karɓo kayan tea ɗin, Amma Widad ta riƙe rigar sa tabi bayan sa tana zare ido. Yusuf ya kalli Amal yace "dama Amal dagaske Widad nada taɓin hankali?" Amal tace "gashi kuwa kana gani tana yinsa tuburan" Cikin tsawa Widad tace "niba mahaukaciya bace, ka gaya musu niba mahaukaciya bace, su suka haɗani da hauka, su suke maida ni mahaukaciya, Amma niba mahaukaciya bace" Gaba ɗaya Yusuf ya rikice, yace "is Ok ai dama ke ba mahaukaciya bace, ki kwantar da hankalin ki" Amal ta kalli Widad tace "kina wannan tamɓelen kike cewa ke ba mahaukaciya bace? Kalli fa abunda kike yi mahaukaciya ce ke tuburan, dan me hankali baze abunda kike ba" Yusuf yace "Haba Amal, ya ana ƙoƙarin kwantar mata da hankali Amma kike tinzira ta" Amal ta zumɓura baki tace "kaga ni karɓi kayan nan, kalli yadda take wani riƙe ka aikin banza kawai" Widad ta shammace ta, tasa hannu ta kifar da farantin ruwan zafin, aikuwa ya zube a ƙafar Amal, Ihu Amal ta saki, wanda ya janyo hankalin Mahaifiyar ta da Ramlah suka taho da sauri. Idan ba gizo idon Yusuf yake masa ba, tabbas kamar ragowar ƙwayar magani ya gani a ƙasan kofin da'aka zuba tea ɗin, sedai kafin yayi wani yuƙuri Hajiya Halima taƙarsaso tana cewa "lafiya, meye haka?" Cikin kuka da azaba Amal tace "Mummy, Widad ta ƙonani da ruwan zafi, Mummy ƙafata" Mummy ta kalli inda Yusuf ke tsaye, Widad na riƙe da shi tace "To maye Jarababbe, ka lallaɓa ka Asirce ta ita da uban ta, shine ka koma da baya zaka illatamin 'ya ko? Wallahi ka kiyayeni, kuma kafin kasa kwaɓata tayi ruwa ni zanyi maganin ka, ke kuma" ta nuna Widad dake bayan Yusuf tace "dan Ubanki ba dai hauka ba, a haka zaki ƙare, Hauka yanzu kika fara shi, daga nan har ƙarshen rayuwar ki, keda hankali sedai ki ganshi a gurin wasu, wannan haukan haka zaki mutu kina yinsa" Widad ta Jijjiga Yusuf tace "kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, kuma wallahi idan ta kasheni itama sena kashe ta, gaba ɗayansu sune zasu kasheni, suna tace min mahaukaciya zasu kasheni, wallahi in baka hana su ba ni zan kashe su" Ramla tace "kaga Malam dalla cikata kazo ka bar gidan nan, tunda babu gadon ka a ciki, ba'a haɗa kuɗi da matsiyacin uban ka an gina ba" Wani irin kallo Widad takewa Ramla daga bayan Yusuf. Kallon da Widad kewa Ramla ne yasa taga kamar Widad ta dawo hankalin ta. Widad tace "idan ka tafi ka barni kasheni za suyi, kashe mutane suke yi fa" Mummy tace "uwarwa muka kashe miki? Mu bama kisa kumako bamu kashe ki ba mutanen da kike Wulaƙantawa suna nan suna bibiyar ki zasu kashe ki, Mahaukaciyar banza da ta wofi, Allah kaɗai yasan me sukeyi da harta yarda da shi haka, dalla kuzo mu tafi suje su ƙarata, Allah ya ƙara birkita ƙwaƙwalwar ki zauna a haka koma samu mu huta, in ƙwaƙwalwar ki ta birki ce ta Ubanki ma ta birkice kowa ya huta da iskancin ki" Ramla tace " Mummy watch your words fa, kina ta sakin layi mu tafi kema Amal Allah ya ƙara, maganinki kina ma wannan ɗan isakan direban shisshigi, gashi ai sun ƙonaki a banza nan gaba ma illataki zasuyi" Shiru Yusuf yayi yabi bayan su da kallo, gaba ɗaya tausayin Widad da Mahaifinta ya kama shi. Ya lallaɓa Widad ya bata youghurt da ƙyar ta sha, tana sha tana masa surutai na shirme, irin na masu taɓin hankali. "Menene dalilin samun taɓun hankalin Widad?" Yusuf ya tambayi kansa Kwanciya tayi a jikin sa tana lumshe ido alamar bacci take ji, ƙirjin Yusuf se bugun uku uku yake, Kasancewar ya keɓance da Widad, abunda be taɓa yi ba, a duk lokacin da yayi yunƙurin rabata da jikin sa seta saka ihu kamar ƙaramar yarinya. Yusuf yayi mamakin iri maganganun da Hajiya Halima da 'ya' yanta suka dinga faɗa akan Widad, koda yake ba abun mamaki bane, duba da Yadda Widad ɗin ke Wulaƙanta su, Amma me sukayi mata take musu haka? " Yusuf yayi Alwashin tone duk wani abubuwa da ake ɓoyewa, kuma ya ƙudurce a ransa zeyi duk me yuwuwa ya jure wulaƙancin Widad yaga ta ina ze temaki rayuwar ta. Yusuf yai shiru yayi zurfi a cikin tunani, yaji Widad tana ajiyar zuciya alamun tayi bacci, a hankali ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita ya lulluɓeta ya fita ya kulle ta a ɗakin yaje yai salla. Ana idar da Salla Isa yace " Yusuf ashe uwar ɗakinka ce babu lafiya? Ance taƙi buɗewa kowa ƙofa amma tana jin muryar ka ta buɗe, gaskiya kai ɗan baiwa ne, Amma naji ance haukan nata ne ya tashi ko?" Yusuf ji yayi kamar ya kwaɗawa Isa mari, Amma ya ƙyaleshi ba tare da yace masa komai ba. Ya koma ɗakin nata ya tarar bata farka daga baccin ba. Falon ta ya koma yana tunani, Ba zato ba tsammani yaji sallamar Mahaifin Widad a falon, Amsawa Yusuf yayi cikin girmamawa tare da risinawa. Alhaji Nasir a ɗan ruɗe yace "Sannu babban Mutum, ya me jikin kuma?" "Alhamdilillah, ta samu bacci" "Masha Allah" Yasa kai ya shiga bedroom ɗin, ya taka a hankali zuwa gaban gadon Widad ya zauna a gefen ta ya ɗagota, idon ta a rufe tana bacci, ya shafa kanta yace "Allah ya baki lafiya my daughter" ya kalli Yusuf yace "Nayi mamaki data iya yadda da kai, idan ciwon nan ya tayar mata bata yadda da kowa seni, ko Bulama wani lokacin muɗinma bata yadda damu gaba ɗaya se an mata allurai" Yusuf yace "Wane irin ciwo ne haka?" Alhaji Nasir ya ɗan na Numfashi cike da damuwa yace "Yusuf, nasan mutane da yawa suna mata kallon bata da kirki, wasu suna zargina da barin 'yata ta lalace, kawai ina kallon sune, ba tare da nace wa kowa komai ba, Yusuf Widad ita kaɗaice' yata dana mallaka, larurar nan ta same ta ne sakamakon kashe mahaifiyar ta akan idon ta" Zaro ido Yusuf yayi yace "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un" Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "ƙwarai kuwa, Akwai abunda ya faru da Widad, wanda tun daga lokacin take gudun mutane, ta haɗu da larurar ƙwaƙwalwa, dukda partially ne larurar tata da farko, Amma daga depression ya zarce mata ta samu Arthropophobia, larurar ƙwaƙwalwa me sa mutum ya dinga jin tsoron mutane, ba mutane ba wani lokacin idan tana cikin larurar ko haske bata so, muna ta magani Sedai har yanzu na gaza samun abunda zesa ta farinciki, kana gani ko fara'ar kirki ba tayi, na yanke shawarar in mata Aure amma tace bata so, dan Allah Yusuf na san kana haƙuri haka nan naji ka kwantamin, dan Allah ka tayani Addu'a, Allah ya bawa 'yata lafiya, ita kaɗai nake da ita, ba uwa ba uba" Gaba ɗaya tausayin Alhaji Nasir da' yar sa suka cika shi, Yusuf ya numfasa yace "Insha Allah Alhaji, Amma ba kayi...... "Yallaɓai ya akayi harka shigo ban sani ba? muna can part ɗina muna fafutukar a kira likita yazo ya duba ta, gaba ɗaya yau kwana mukayi ba muyi bacci ba saboda yadda jikin Widad ya rikice, ko Abinci ba wanda ya iya ci yanzu ma mun shiga muyi salla ne ka dawo ban sani ba" Hajiya Halima ke wannan maganar cike da salon bariki da Kissa. Alhaji Nasir yace "Allah sarki, nasan kina ƙoƙari akan Yarinyar nan, Allah ya saka miki da Alkhairi, ina su Baby Amal ɗinne ko basu san na dawo ba?" "Amal ma bata jin daɗi, Ramla kuma salla take, ina jiran Widad ta farka ne a bata Abinci, mun samu da ƙyar tayi bacci" Yusuf kam bin Hajiya Halima yayi da kallo, yana mamakin wannan iya salon barikanci nata, gaba ɗaya ta juye kamar tana cikin damuwar gaske. Yusuf yace "Bari inje gida Alhaji tunda ka dawo" "Shikenan Yusuf ka gaida gida, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi" "A'a bakomai Yallaɓai" Yusuf yasa kai ya fice, Hajiya Halima tabi bayan sa da harara. Kan Yusuf ya ƙara ɗaurewa da maganganun da Alhaji Nasir ya gaya masa, yana daf da fita kawai yaga Ramla ta sha gaban sa. Tsayawa yayi yana kallon ta, ta kalle shi cikin Isa tace "Bani mukullayen Motar Widad dana ɗakin ta dake gurin ka" Yusuf ya tsuke Fuska yace "ɗan bani hanya zan wuce mana" "Ni kake kallo kakewa wannan gadarar haka? Zaka bani ko sena maka rashin mutunci?" "bake kika bani ba, ba kuma ke nakewa aiki ba, dan haka babu ruwan ki dani" "Kai kalli tsabar Idona, karka kuskura kace zakayi Jayayya dani, naga se wani shisshigi kake kana cusa kai a gurin waccan Mahaukaciyar da ita da Ubanta, to bari kaji in gaya maka, idan ma wani abu kake kwaɗayin samu wallahi ba zaka samu ba, Kuma hauka yanzu Widad ta fara shi daga nan har ƙarshen Rayuwar ta, ba zata sake moruwa ba, gara ka cire wa kanka ƙwalamar wannan daular da dukiyar, yadda kazo a talaka haka zaka koma a matsiyaci, idan kaga dama kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa, shawara ta ƙarshe da zan iya baka itace, ka gaggauta Ajiye aikin nan ka ƙara gaba ya fiye maka Alkhairi akan wasa da rayuwar ka" Murmushi Yusuf yayi ya dubi Ramla yace "in kinga na bar aiki a gidan nan wanda nakewa aikin ne suka sallameni, kina wani iƙrarin dukiya, dukiya nawace taki a dukiyar nan? Ki kiyayi Yusuf, matsi da takura babu wanda Yusuf be gani ba a rayuwar sa, dan haka ƙaramar barazana irin taki ba zata hanani Aiki na ba, ni babu ruwana da rayuwar da kuke a cikin gidan nan ni aikina kawai nasani, ban guri in wuce ko in hankaɗeki" Galala tabi Yusuf da kallo, da ma akwai Yadda yake mata magana cikin Izza shima, Me yasa ba yayiwa Widad da take Wulaƙanta shi, lallai maganar Mummy gaskiya ce, ya kamata ayi maganin Yusuf. Yusuf fa kai ya sake ɗaukar wuta, abun da ya faru yau, ya ƙara tabbatarwa Yusuf akwai wani mugun nufi a zuciyar Hajiya Halima da 'ya' yanta. Umman Yusuf ta lura da yanayin Yusuf ko iya sakewa yaci Abinci ba yayi, Umma ta kalle shi tace "Yusuf wai meke damunka ne haka? Naga gaba ɗaya kwanan nan na kasa gane kanka, Allah yasa ba wani abun aka kuma yi maka ba?" "Umma ni a rayuwa ta wani irin ƙalubale ne ban gani ba? Aini lamarin rayuwa ta na miƙawa Allah, aikin da aka bani ne me matuƙar rikitarwa" Nan ya kwashe komai ya gayawa Umman sa, Umms tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace "lallai wannan lamarine me sarƙaƙiya, nidai fatana ka kula da kanka Yusuf, kayi taka tsan tsan ka cigaba da Addu'a, Amma waye yazo ya nemi da a dinga bawa ita Yarinyar kariya?" Shiruu Yusuf yayi sannan ya girgiza kai yace "Wallahi Umma ban sani ba" "Ta yaya za'a bawa mutum kariya ba tare da sanin sa ba? Kaima kamar baka san aikin naka ba?" "Umma nasan aiki na, Amma nima umarnin manya na nake bi, wataƙila be kamata in sani bane" "Hakane amma kayi taka tsan tsan, naji tausayin yarinyar nan, Amma ni jikina yana bani wani abu game da aikin nan da aka saka, Amma kasa gane ko menene, ina dai yi maka addu'a a duk inda kake Yusuf, ni dai fatana ka kula da kyau" "Insha Allah Umma na" Haka suka cigaba da taɓa hirarrakin su na ɗa da uwa. Sosai tunani ya auri Yusuf, maganar Umma tana bisa hanya, waye wannan da ya nemi a bawa Widad kariya a ɓoye, dole akwai wata a ƙasa. ******************* Washegari da safe, Yusuf ya koma gidan su Widad, bayan sun gaisa da su Nura, Yusuf yace "Nura ya jikin uwa ɗakina kuwa?" Nura yace "ta yaya zamu sani? Kaine dama aka ɗauka mutum a gidan nan, da kai ake komai mu ina zamu san wani abu? Ai kaine mutum a cikin mu" Yusuf yayi Murmushi ya samu guri ya zauna. Murtalah ya ƙaraso inda Yusuf yake yana faɗin "Malam Yusuf, ɗazu Alhaji ya leƙo yana tambayar ko kazo, dama yace in kazo a shiga da kai ɓangaren sa" Yusuf yace "shikenan babu laifi, muje" Murtalah yayi gaba Yusuf ya bishi a baya, Sam Yusuf be taɓa sanin da wannan ɓangaren a cikin gidan ba, gjda se kace ba'a duniya ba, Yusuf ya buɗe ido yana bawa idonsa Abinci. Suna shiga Ƙaton falon, Murtalah yace "to ni na tsaya daga nan, dan bani da ikon ƙarasawa ciki, seka fito" Seda Yusuf ya gama waige2 sannan ya kalli ƙatuwar ƙofar dake cikin falon, a hankali ya taka yaje ƙofar ɗakin ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Alhaji Nasir ne ya amsa tare da cewa "Shigo" Yusuf ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, Alhaji Nasir ne zaune Widad ta ɗora kanta akan cinyar sa, idonta biyu tana ta jujjuya ƙwayar idon ta, gefe kuma Alhaji Bulama ne zaune a kusa da Alhaji Nasir.

Chapter 9 of 35