ina nan a mahaukaciya ta kamar yadda kuka saba faɗa"
"waya isa yace miki mahaukaciya, ba mahaukaciya bace ke Daughter"
"Eh amma kuke kaini gurin likitocin mahaukata"
Alhaji Bulama yace "Daughter a bar wannan maganar, magana ce Maman ki tazo min da ita"
"ni uwata ta mutu, an kasheta bani da wata uwa, ta haifi dai wanda ta haifa"
Bulama ya girgiza kai yace "What ever dai, ta kawomin ƙorafi akan ki, kina fita lokacin da bata sani ba, ki koma bata sani ba, kuma kinsan babu tsaro haka kike yawo ga rayuwar ki a hatsari, kuma tayi koke akan wannan direban naki, bata jin daɗin yadda direban ki yake sintiri a sashenki, gaki budurwa ga ta da manyan yara mata, bekamata ya dinga sintiri kuna keɓewa dashi ba, daughter meyasa ba kya ɗaukarta kamar mahaifiya ne? "
Shiru Widad tayi tana jinjina kai, Yusuf kam gaba ɗaya ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya nutse, dan shi kansa baya jin daɗin yadda yake shiga inda Widad take, yana ganin rashin dacewar hakan.
Bulama yace " Daughter baki ce komai ba"
"so nake ka gama tukuna"
"Na gama feedback ɗinki nake jira"
Widad ta gyara zama tace "Ka gaya mata wanda ze iya zama a gidanmu a ƙarƙashin mulkina shikenan, wanda baze iya ba ƙofa a buɗe take ya ƙara gaba, tunda basu da zuciya dole su zauna su cigaba da zama, yadda ba ruwana dasu to sudena samun ido, idan zargin da takemin kenan, to ka gaya mata idan maza nake son kawowa bata isa ta hanani ba, tunda gidan mu ne, sannan ni bani da uwa, Uwata ta bar duniya an kasheta, bazan ƙara yadda da wani ba, ban yadda da kowa ba kuma bazan yarda da wani ba, i start loosing trust on you Bulama, bani da uwa an kashe uwata! Karta ƙara kiran kanta uwata, ni bani da uwa! Bana son kowa ya raɓeni, ban yadda da kowa ba wannan AƘIDATA ce"
Jikin ta ne ya fara rawa, wasu irin hawaye na zuba daga idon ta, da sauri Yusuf ya tashi suna rige rige da Bulama zuwa ga Widad, Numfashi take da ƙyar tana kuka, Yusuf yazo kanta da sauri yace
"Are you ok?" jinjina masa kai tayi
Bulama jiki a sanyaye yace
"daughter, ban faɗi wannan maganar dan in ɓata miki rai ba, Nayi ne dan in tunasar dake mahimmancin haƙuri, kuma koba komai matar mahaifinki ce sannan.. Ɗagawa Bulama hannu tayi ta miƙe ta nufi waje da sauri.
Bata tsaya ba seda taje mota, gaba ɗaya rayuwar Widad abun tausayi ce, tunda Yusuf yasan ta bata cikakken sati bata zubar da hawaye ba, Amma ina dangin mahaifinta kona mahaifiyar ta? "
A haka ya kaita gida, yana tuƙi kamar baya so, saboda yadda yake jin kukan ta me ban tausayi, kamar yadda ta saba indai sukaje guri suka dawo, kame tazo dashi a motar zata barshi, se Yusuf ya kawo mata.
Dan haka yana parking ta buɗe ta fice, ya ɗakko jakar da Wayar ta ya bita.
Sedai yana shiga Falon ya jiyo sautin kukan Widad cikin gurɓatcciyar hausar ta take faɗa
"danme zaki dinga zuwa kina kai ƙarata, bafa ki haifeni ba, keba uwata ce ba, kin sani meyasa kike shisshigi a al'amura na, idan baki dena min haka ba zan ɗau mataki mafi muni akanki, ki ƙyaleni inji da abunda nake ji, ki ƙyaleni inji da ƙunci da baƙin cikin dana ke ciki tsawon shekaru mana, danme zaki dinga min haka?"
Masifa take sosai kamar zata shaƙe Hajiya Halima, Abun na Widad ya fara wuce gona da iri.
Yusuf yace "kina hayyacinki kuwa? Meyasa kike haka?, a haife ta haife ki, bekamata kidinga gaya mata wannan maganganun ba"
Ta juyo kan Yusuf cikin faɗa tace "Bana hayyacina, ni mahaukaciya ce, idan baka sani ba yau in gaya maka, bani da hankali har ƙasar waje ake kaini ganin likitan mahaukata, Amma baka san me nakeji a zuciya ta ba, An kashe mamana ban san kowa ba se ita, aka kashe ta ba wanda ya damu dani se Babana da Bulama, kowa kansa ya sani babu wanda ya damu da abunda Widad take ciki, kasan me nake ji a raina idan na tuna lokacin da aka kashe mahaifiyata? Wannan tabin baze bar zuciyata ba, a ƙyaleni inyi rayuwar da naga dama mana, "
Yusuf yayi ƙasa da murya yace
" is alright I feel your pain "
" you don't feel my pain, your mum is still alive but me... Kasa ƙarasawa tayi se sake fashewa da tayi da kuka, ta tafi part ɗinta da sauri, Yusuf kam kasa bin bayan ta yayi wannan karon, Hajiya Halima kam ƙamewa tayi ta zubawa sarautar Allah ido.
Yusuf ya juya ze fice Hajiya Halima tace "Ina zaka tsohon munafuki, zuwan ka gidan nan shiya hargitsa komai, da yarinyar nan duk rashin mutuncinta bata fiye magana ba, seda kazo kana hure mata kunne, to idan ma wani ne ya turoka to tabbas zanyi maganin ka, dan da zarar Alhaji ya dawo zansa ya sallameka, matsiyaci banza dana wofi kawai "
" Niba matsiyaci bane, Amma talaka ne me wadatar zuci, sannan kafin kisa a koreni da kaina nayi deciding yin resigning, zan bar aikin nan dan nima abunda yake faruwa ba daɗi yake min ba ko dan tsira da mutuncina, dole in bar aikin nan tunda bana shiga aljanna bane"
Fitowar Amal yai daidai da maganganun Yusuf da yace ze bar aikin, sakin ƙaramin plate ɗin hannun ta tayi, tabi bayan sa da sauri tana kiran sunan sa.
" Idan kika bar ƙofar falon nan da sunan bin bayan sa, zan sallamawa duniya ke in bar masa ke, tunda haka kike so"
Juyowa tayi tana kallon Mummy, ta juya da sauri part ɗinta tana kuka.
************************************
Abbas se juyi yake akan kujera yayi shiru, gaba ɗaya abun alherin da Yusuf ke samu a hannun Widad ya tsaya masa a zuciya, yaji meyasa yasa aka tura Yusuf aikin shi beje ba? Yayi gudun kar yaje a dinga masa wulaƙanci yasa aka tura Yusuf, yanzu gashi kuɗin data bashi Yayi Albashinsa uku, ga gefe ana biyan sa Albashinsa, Sallamar Sakina ce ta dawo da shi hayyacin sa, ya amsa mata sallamar ta kalle shi tace
"lafiya kuwa Yallaɓai?"
"lafiya ya bata amsa"
Ta ɗan taɓe baki tace
"dama zuwa nayi in tambaye ka, dan Allah meyasa Yusuf baya zama a office yanzu? Wane irin aiki ne aka bashi haka?"
Abbas dama a ƙule yake yana neman wanda ze gayawa matsalar sa, dan haka ya zayyane mata komai, ciki harda Aibata Yusuf, ba ƙaramin mamaki ne ya kamata ba, ganin duk headquarter nan babu wanda Yusuf yake sakin jiki dashi kamar Abbas, Amma ace Abbas ne da bakin sa yake faɗar wannan mahanga akan Yusuf, lallai ɗan Adam ba abun yarda bane.
A zahiri ta maze tace
"gaskiya kai yakamata ace kana samun wannan sha tara ta Arziki ba shi ba, yanzu kayi duk yadda zakai kasa a maye gurbin sa da kai, a karɓe aikin daga hannun sa, idan kana buƙatar taimakona ma zan maka, kasan mu mata akwai iya makirci"
Abbas ya washe baki yace
"ƙwarai kuwa, amma fa nagode sosai Sakina"
************************************
Har Yusuf ya kama hanyar gida, kawai ya ɗakko wayarsa ya kira Manager Hotel ɗin nan, ai kuwa wayar ta shiga, Yusuf ya tambaye shi idan yana son ganin sa ya zasu haɗu? Ya gayawa Yusuf inda zasu haɗu a gidan sa, beyi wata wata ba yaje har gidan nasa.
Da ganin manager Hotel ɗinma kaga ɗan duniya, suka gaisa da Yusuf, Yusuf yace "dama wata buƙata ce ke tafe dani, ina son ka nunamin mutanen da suka kama ɗaki a hotel ɗinku, tun daga farkon wannan watan"
Manager yace "Kai Malam, ni na zata ma wata harkar cigaba ka kawo, wannan abun da kake tambaya sirri ne bama fitar dashi, manyan mutane ke zuwa Hotel ɗinmu, ba zamuyi exposing ɗinsu ba dan duniya babu yarda"
"ze kasance sirri ne tsakanina da kai, kasa a bani babu wanda ze sani"
"Malam bazan iyaba, ka tashi ka tafi kawai"
"zan baka dubu ɗari biyar, zaka bani akan wannan farashin?"
(Abunda yasa Yusuf baya son nuna shi waye, ma'aikaci ne na sirri, no need asan shi waye)
Murmushi mutumin yayi yace "yanzu naji batu, Amma tsakani da Allah turoka akayi, kokuma ma'aikaci ne kai?"
Girgiza kai Yusuf yayi yace
"Dani ma'aikaci ne ko sisi bazan baka ba, sedai inyi amfani da ƙarfin aiki na, Matata nake zargi ina so in kamata red handed, kuma kona kamata bazan taɓa sako sunan ku a lamarin ba"
"Shikenan, Amma dan Allah ya zama sirri tsakaninmu"
"in Allah ya yarda babu meji, da gani se kai"
"shikenan muje se a baka"
Yusuf yace "No bana son yawan zuwa gurin bana son a ganni a gurin, ta Email ɗina nake so ka turamin, zan baka ɗaya bisa huɗu na kuɗin seka turomin zan baka sauran, bana saɓa Alƙawari dan haka kaima karka saɓa"
Haka ya amince da wannan yarjejeniyar.
*********************************
Saleh ne yake kaiwa yana komowa, Alhaji Bukar ya fito ya sa meshi, ya kalle shi ya yatsuna fuska yace "lafiya?"
A fusace Saleh yace "dole ka tambaye ni lafiya, me kasa akayiwa ɗan uwana? Ta yaya zanje in ganshi lafiya ƙalau kawai labari ya isheni wai bashi da lafiya"
Alhaji Bukar yace "dakata! Da ina son ganin bayan ɗan wanka da tun a shekarun baya gudun karya tona min Asiri da tuni ya bar duniya, zaman kotu daza'a koma bani da fargaba sam, inada ƙwararrun lawyoyi da na biya su wanda zasu tsayamin, dan haka ba abunda zesa in yiwa ɗanuwanka wani abu"
"Au haka ma zakece? Wato kai a wanke ka shikuma ya cigaba da zama a prison ko? Ga wannan mahaukaciyar Yarinyar taje ta sameni, tace muddin wani abu ya samu Bala ni zan maye gurbin sa, me kake tunani ne wai? Yarinyar nan tana da kuɗi zata iya aikata duk abunda taso"
Alhaji Bukar ya ɗan daki kafaɗar Saleh yace
"shiyasa nace kazo mu haɗa kai mu raba ta da dukiyar, mu mallaki gundurin dukiyar da muke ta farauta muga ta tsiya"
Saleh ya make hannun Bukar yace "Niba dukiyar tace a gabana ba, babu irin kyautatawar da mahaifinta be minba, ni dukiyar sa bata gabana, ni burina a wanke ɗan uwana a fito da shi daga kurkuku tunda bashi da laifi"
Wata uwar dariya Alhaji Bukar ya saki yace "ubanwa yace maka bashi da laifi? Lallai har yanzu kanka a kwano yake, ka ƙyaleshi ya girbi abunda ya shuka, kazo a haɗa kai a nemi Arziki".
Yana gama maganar ya wuce ya bar Saleh a gurin.
************************************
Yusuf yaita safa da Marwa yana duba wayar sa, ba zato Sega abunda ya nema an turo masa ta Email ɗinsa, message ɗin na shigowa Manager ya kira Yusuf, Yusuf yayi masa godiya sannan ya tura masa sauran kuɗin, wanda kuɗaɗen da Widad take bashi ne, dan wani lokacin idan ta bushi iska se yaga alert.
Yusuf ya tura message ɗin cikin System ɗinsa da sauran wayyoyinsa, nan Yafara aiki akan bayanan da aka turo masa, ba ƙaramin mamaki ne ya kamashi ba ganin mutanen da suka ka kama ɗakuna a wannan watan zuwa ranar da suka je Hotel ɗin tare da Widad, wanda ya kama ɗaki ranar da sukaje shida Widad yafi bashi mamaki, Abun tambayar anan shine 'ya akayi Widad tasan da zuwan mutumin gurin? Me Widad taje yi? Gurinwa taje?' me ta gani ya sata kuka? '
Yusuf zuciyarsa ɗaya baya jin Widad zata aikata wani mummunan aiki na alfasha, amma akwai wani ɓoyayyen abu da yakamata ace ya sani.
Kamar wanda aka mintsina ya miƙe ya shirya, ya duba agogonsa ƙarfe takwas na dare, haka ya fita ya tari abun hawa ya tafi unguwar su Nurat.
Unguwar tasu shiru, amma haske ko ina da yake rukunin Gidajen masu kuɗi ne, har ƙofar gidan aka kaishi aka sauke.
Ya sauka ya nufin gidan su Nurat, ya tsaya suka gaisa da megadin, Yusuf yace "Dan Allah gurin Nurat nazo"
Maigadin ya kalle shi yace "tasan da zuwanka ne?"
"A'a, bata sani ba, Amma ka gaya mata tayi baƙo"
Mai gadi ya kira Nurat a waya yasa a hansfreee ya gayamata tayi baƙo.
"Babu wanda zan haɗu dashi yau, dan haka ba zanga kowa ba"
Yusuf yace "kace mata Widad ce ta aiko ni"
Aida jin Widad ce tayo aiken Nurat ta rikice, tace "Kaishi guest room, ina zuwa"
Maigadin yayiwa Yusuf jagora, har wani katafaren Falo, Yusuf ya zauna yana jiran fitowarta.
Ko mintuna goma ba'ayi ba se gata ta fito, ta ƙaraso cikin falon da hanzari, sedai tana arba da Yusuf ta rikice ta buɗe baki zata yi ihu ta gudu, Cikin zafin nama Yusuf ya riƙeta tare da toshe mata baki.
"Meye haka kamar kinga wani aljani ko mugu? Kinga fa mutum ne ni"
Fizgewa tayi, ta shiga Ja da baya ta kwaɓe fuska zata yi kuka tace
"Nifa wallahi tun ranar da kuka bar nan, Widad bata ƙara zuwa gidan mu ba"
Gaba ɗaya Nurat ba tafi sa'ar Widad ba, sedai Widad tafi Nurat jiki sannan Izzarta da jin kanta yake sa ka ganta kamar Babba.
Yusuf yace "Haba Nur, nifa ba wani abu zanyi miki ba kawai tambayoyi zan miki in tafi"
Girgiza kai ta shiga yi tana kiran sunan Daddy a hankali.
"Daddyn yana nan ne?" ya tambaye ta
Ta girgiza masa kai alamar A'a
"to ki nutsu ki zauna, hira za muyi in tafi"
A hankali ta zauna, tana rarraba ido dan a tsorace take da Yusuf, dan ba zata manta randa Yusuf ya shaƙeta ba, har yayi barazanar sace taba.
Yusuf yace "Calm down dear, hira zamuyi kawai in tafi"
Ganin taƙi sakin jikin ta yasa Yusuf ya miƙe ya zaro komai na Aljihunsa, dan ya tabattar mata da babu wani makami a tare dashi.
Ya kalleta yana ɗan nazarin ta sannan yace
"ko ki tambaye ni ina Widad ko? Tun ranar da ta bar nan baki sake neman ta ba"
"Na kirata bata ɗaga wayata ne, nasan bazata sake yarda dani ba"
"Waye yace miki ba zata sake yarda dake ba? She's very simple and kind, but why do you attempt to kidnapped her?"
Kamar Nurat zatayi kuka tace "bafa laifi na bane, Daddy ne"
Yusuf ya ɗan ƙara matsowa yace "Amma me tayi wa Daddy haka da zesa a saceta?" yai maganar yana kallon idon Nurat, Yarinya ce dan haka yake binta a sannu cikin hikima
Ɗan shiru tayi sannan tace "Nifa ban sani ba"
"Haba me sunan manya, Haske maganin duhu, baki kama da maƙaryata ba, ni ya akayi ma kika san Widad har kuke hulɗa bayan bata son mutane?"
"Nifa ba wani hulɗa mukeyi sosai ba, da tun ina ƙarama, gidan su na U. K yana kusa da namu daga baya suka dawo Nigeria shine... Sekuma tayi shiru tana satar kallon Yusuf.
"Shine me? "
"Dad ɗina sunyi faɗa da Daddynta akan Siyasa, shikenan abunda nasani, Amma dan Allah karka gayamata Daddy nane yasa ayi kidnapping ɗinta idan ta sani, zata sa a kai Daddy na prison ne"
"bazan gaya mata ba, ai kin gayamin gaskiya, amma naga Daddynta ɗan kasuwa ne ba Siyasa ba me zesa suyi faɗa da Daddynki akan siyasa"
"to ainima bakomai na sani ba, muna yara lokacin Amma tabbas sunyi faɗa ne shine yake son ya rama akan Widad, amma ni ban san me yake so yayi mata ba"
Yusuf yace "shikenan nagane, gaskiya you are so kind dear, Insha Allah bazan bari taji ba, Amma dan Allah karki bari a cutar da ita, kinga marainiya ce ita abun tausayi, ke kina da Mum da Dad ɗinki ita kuma she's orphan"
Jinjina masa kai kawai tayi.
Yusuf yace "Bani wayarki in sami ki lambata, se mudinga gaisawa ni daga yau nayi ƙawa, ni zan maye miki gurbin ƙawancen ki da Widad"
Kallon sa tayi ta ɗanyi murmushi yadda yake magana ya burgeta, bashi da hayaniya, ya iya tsara magana daki daki, se yanzu ta gane ranar da yayi mata wannan barazanar ne ya koma kamar wani mugu amma ba haka yake ba, ta miƙa masa wayar sannan tace
"Amma ni ban sanka a Family ɗinsu ba, waye kai a gurin ta?"
Yusuf yayi murmushi yace
"i don't belong to her family, but a very important person attached to her destiny"
Kallon sa tayi cike da rashin fahimta za tayi magana ya kashe mata ido ɗaya, gaba ɗaya seta sunkuyar da kai ta kasa maganar, ya daɗe yana daddana wayarta, ita kuma ta kasa cewa komai.
Seda ya gama abunda yake sannan ya miƙo mata wayar yace
"Nagode sosai ƙawata, Allah ya bar zumunci, ni zan koma naji daɗin kasancewa dake da wannan hirar da mukayi"
Murmushi tayi tareda sunkuyar da kai tace "baka gayamin sunan ka bafa"
"Sunana Abokin Nurat, Just call me Aboki or any name you like, good night Nur"
Ya ƙarasa maganar tare da nufar hanyar fita yana addu'a Allah ya shiga lamarin sa akan wannan aiki me hatsarin gaske da yake yi, yasa hanyar da ya ɗakko ta zama mafita ga al'amuran.
Yayinda Nurat ta rakashi da ido har ya fice
Nurat tana komawa cikin gida Maman ta tace
"Ke lafiya kuwa? Waye wannan yazo kika daɗe haka?"
"Abokina ne yazo muka gaisa" tai maganar cike da basarwa ta shige ɗakin ta tana tunanin Yusuf
(Masha Allah, daga wannan posting bana tunanin zan kuma wani posting se Allah ya kaimu ranar Asabar insha Allah, gobe in Allah ya yadda zan fara jarrabawar ƙarshe ta makaranta, ku sani a addu'oinku please 🙏 🙏 🙏
Dana kammala exams insha Allah zanyi ƙoƙari ku dinga samun update akan lokaci, comments ɗinku zesa kudinga samun update kullum, idan kun shirya yanzu aka fara wasan, ba'a fara komai ba thank you for being with me 😍 😍 😍)
Domin gyara sharhi ko shawara, feel free to contact me
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in
PART1
Page 14
ELEGANT ONLINE WRITER'S
Sosai Yusuf yake ƙara samun haske akan lamarin binciken da yake yi, Sam babu specific lokacin da Widad take bawa Yusuf albashi, duk lokacin da ta bushi Iska sedai yaga alert ɗin kuɗi, kuma kuɗi masu yawa, sannan be isa yayi magana ba.
Yana ta tattara bayananan daze gabatar a gurin aiki na sakamakon binciken da yake yi.
Tunda Yusuf ya tafi Nurat take tunanin, ko ta gayawa Mahaifiyarta yadda suka yi da Yusuf, wata zuciyar ta gargaɗe ta akan hakan.
********************************
Gaba ɗaya Widad ta takura kanta, sam ko Babban falo bata fitowa, tana iya sashin ta daga ita se magenta, duk da haka Yusuf kullum se yaje koda baze ganta ba kuwa.
Lambar wani abokinsa likita ya dubo a wayarsa ya kirashi, se da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka.
"Yusuf kana da kirki kuwa? Ace ka ɓata ko neman mutane baka yi?"
Yusuf yace "Amma ka tsaya mu fara gaisawa, sarkin ƙorafi"
Nan suka gaisa suka taɓa hirar yaushe rabo, sannan Yusuf yace "dama doctor Hamza ina da wata 'yar tambaya ne, dukda nasan tambayar da zan maka ba a fannin daka karanta kenan ba, amma na sanka da shige shige"
Hamza yace "shikenan ina jinka, Allah yasa nasan amsar tambayar taka, in babu amsar ma se'a nemo"
'Masha Allah, dan Allah Hamza wace irin larurar ƙwaƙwalwa ce take sa mutum ya dinga gudun mutane? "
Doctor Hamza yace
"Anthropophobia kenan, is a mental disorder, masu irin wannan larurar suna jin tsoron taron mutane, idan abun ya tsananta ma ko ahalinsu basa son su raɓe su, sedai wasu tsirari daga mutane, basu fiye son taron jama'a ba, ko shiga cikin mutane basa so"
Yusuf yayi ajiyar zuciya yace "to me yake haddasa ciwon"
Hamza yace "eh to, abun da yake haddassa wannan larurar ga wasu, idan an taɓa cin amanarsu, mussaman wanda suka yadda da shi, ko kuma wani abu da ya taɓa faruwa dasu mara daɗi a rayuwarsu, wasu kuma hormones ne suke haddasa musu excessive fear ya danganta dai, zakaga wataran suna lafiya ƙalau ga wanda ciwon be tsananta a gare su ba, amma idan ya tashi zaka ga basa son haɗa ido da mutane, basa son suga ana kallonsu, kosu kasa bacci, ko yawan ciwon kai, bugun zuciyar su ya canza, wasu numfashinsu har ɗaukewa yake, ko su dinga karkarwa in sunga baƙo, ko wanda basu yadda dashi ba, ko kuma su dinga wrong perception akan abubuwa, ko su dinga ganin duk wanda ya raɓesu ze cutar da sune"
"Ok magana, nagode sosai Hamza amma meye maganin ciwon?"
"gaskiya babu wani sahihin maganin ciwon gaskiya, rehabilitation ne a dinga kwantar musu da hankali tare da ƙoƙarin canza musu tunani daga mummuna zuwa kyakkyawa, dan wasu in damuwar tayi musu yawa suna fara shaye2, ko dinga wasu tunani wanda ya saɓa da abunda yake a zahiri, ayi ƙoƙarin samar da wani abu daze dinga ɗebe musu kewa, koya ɗauke musu hankali daga damuwarsu, in kaga an basu magani mafi akasari sedai a basu magani akan sauran matsala, kamar bugun zuciyar, ko daidaituwar hormones ɗin ko makamancin hakan...
Shiru Yusuf yayi yana tunani, meye alaƙar ƙwayar daya gani a ƙasan kofin shayin da za'a bawa Widad da ciwon nata, Doctor Hamza Yana cikin yiwa Yusuf bayanin ne ya hango Widad ta fito, tana nufo inda yake zaune, gaba ɗaya fuskarta a haɗe kamar kullum, yauma shigar tata da ta saba ita tayi, jikin nan a tsuke a cikin ƙananan kaya.
Da sauri Yusuf yace "shikenan nagode sosai doctor, nagane Allah ya saka da alkhairi" ya katse wayar
Ya shiga wani tunanin, "to wace irin Allura akewa Widad haka? Amal tace masa ana mata wata Allura, ga kuma abunda likita yace"
Ta ƙaraso ta kalle shi a yamutse tace
"ɗakko mota, zamu airport ne yanzu"
Ya kalle ta yace
"me zamuje yi a Airport?"
"ban sani ba" ta bashi amsa
Ƙasa yai da idonsa yayi mata wani irin kallo sannan ya miƙe yai gaba, gaba ɗaya kasa gane kalar kallon tayi meya ke nufi da haka?
Ya ɗakko mota ya kunna suka fara tafiya, suna tafiya yana satar kallonta yana tunanin, me zeyi wa Widad wanda ze temaka gurin canza tunanin ta mara kyau zuwa me kyau, kamar yadda doctor Hamza ya gaya masa.
Yana cikin tunanin wayarsa ta fara ringing, sedai lambar ba suna, kuma yana tsoron ya ɗaga yaje a cikin abokan aikinsa ne, wani yayi masa kwaɓa, sekuma ya tuna halinta, yanzu yana ƙin ɗaga wayar zata masa wata fassarar, haka ya basar ya ɗaga wayar yasa a kunnen sa tare da yin sallama.
Siririyar muryar mace ce ta amsa tace
"Aboki ya kake?" se yanzu ya gane muryar Nurat, murmushi yayi yace "lafiya ƙalau, light ya kike?"
Wani murmushi ne ya suɓuce mata tace "lafiya ƙalau friend, dama cewa nayi bari in kiraka mu gaisa"
"Amma gaskiya kin kyauta Light, ina fatan kina lafiya ba kya cikin kowace irin damuwa? Kin san damuwa da yawan haɗe rai yana sa mutum ɓacin rai da saurin tsufa, kuma duk kyansa ya koma kamar wani abun tsoro"
Da sauri Widad ta juyo ta kalle shi, amma ya basar ya cigaba da wayar, yayin da Nurat tayi murmushi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 35