PART1
Page 26_27
Gaba ɗaya Widad ko motsi ba tayi, Yusuf ya rungumeta sosai a jikinsa kamar wani ze ƙwace masa ita, zuciyar ta na bugawa amma numfashinta baya fita sosai, ga cikinta se ƙara yake saboda yunwa.
Anwar ya kai Nurat gida, suka yi Sallama, ta shige gida jikin ta na rawa ta tafi ɗakin mahaifiyar ta.
"ke ina kika fita kikaje ban sani ba?"
"Mummy akwai matsala fa"
Cike da rashin fahimta mahaifiyar ta tace "matsalar me?"
"Widad ta ɓata an sace ta"
Dafe ƙirji tayi tace "innalillahi wa inna ialaihi raji'un, waye ya gaya miki?"
"Mummy can naje fa, Daddynta yana Asibiti ma naje na duba shi ma"
Zaro ido tayi tace "ubanwa yace kije? Sekin jawa kanki faɗa a gurin mahaifinki ko? Tashi maza kije ki cire hijjabin nan ki huta"
Nurat ta kalli mahaifiyar ta tace "Mummy, Daddy ne fa yasa aka sace Widad"
"inji ubanwa? Rufen baki shashasha, in kika sake maganar nan yaji kema zeyi maganin ki"
"Mummy a matsayinki na uwa, ya zakiji idan ni aka sace, yakamata ki cire tsoro a ranki ki gayawa babana gaskiya, ranar da hakki ya tashi bashi kaɗai ze kama ba harmu"
Ta ƙare maganar tare da ficewa daga ɗakin gaba ɗaya
Kwata kwata duk bidirin da'ake Fahad beje yaga jikin Alhaji Nasir ba shima kuma Alhaji Nasir be tambaya ba, yana fama da kansa.
Mussaman Abbas daga inda yake aiki ya kira Umman Yusuf ya sanar da ita ɓatan ɗanta, dama ta kira wayar Yusuf harta gaji bata shiga.
Aikuwa ta kiɗime sosai ta tashi hankalin ta, ta shirya ta tafi gurin aikin Yusuf.
Ma'aikatan su kansu a kiɗime suke tun bayan da suka samu labarin ɓatan Yusuf, Suleman yayi duk yadda zeyi a basu damar bincike akam al'amarin amma daga sama aka hanasu, akace an riga an danƙa case ɗin a hannun wasu jam'ian tsaron.
Sosai Umman Yusuf tasa Abbas a gaba tana zabga kuka
"dan Allah ranka ya daɗe ina ɗana yake? Ku kuka sashi aikin nan ina kuka turamin shi shi kaɗai nake kallo inji daɗi, Yusuf ne kaɗai dani, dan Allah ku temaka ku nemomin Yusuf ɗina"
Cikin ƙwarin gwiwa Sulaiman yace "ki kwantar da hankalinki Umma, Insha Allah indai Yusuf ne zamuyi duk me yuwuwa muga mun kuɓutar dashi, an baza jami'an tsaro kuma ins me tabbatar miki ba abunda zasuyi masa dan bashi suke hari ba, yarinyar da yakewa aiki suke hari, dan ba suce abasu komai ba, yanzu haka mahaifin yarinyar yana kwance a asibiti, kuma bashi da magana seta Yusuf"
Suleiman ya dinga kwantar mata da hankali, amma abunka da ɗa d uwa ta saurari kalaman Suleiman ne kawai, amma bata ga alamar ana neman ɗan nata ba.
Umman Yusuf bacci ya ga gareta, balle cin Abinci banda kuka da Addu'a babu abunda take yi wa ɗan nata, dan yanzu a duniya idan ta rasa Yusuf ba.
Jikin Alhaji Nasir ƙara rikicewa yake saboda damuwa, Anwar yace wa Mahaifiyarsa "Mummy ya kamata ayi wani abu akan rashin lafiyar daddy, inze yuwu ayi visa a fita da shi, kullum jikinsa ƙara rikicewa yake babu sauƙi"
Hajiya Halima tace "ko bangon duniya za'a kai shi idan Allah yayi niyyar karɓar rayuwarsa ba yadda muka iya, anan ɗinma naga likitocin suna iya ƙoƙarin su, meye kuma se an kwashi jiki an tafi ƙasar waje dan ɓarnar kuɗi"
"Mummy ɓarnar kuɗi kuma? Koma ɓarnar kuɗin ne naga nasane ai, meye amfaninsu in baza'a nema masa lafiya ba"
"kaga Anwar ka kiyaye ni, kafini sanin abunda ya dace ne? Fita ka ban guri kafin in ɓata maka rai, sakarai kawai"
Fitowa yayi gwiwa a saɓule yana tunanin wannan halina Mummynsa.
Gidan Bulama ya tafi, yaje ya tarar yana shirin fita, suka gaisa da Anwar, Anwar yace "Daddy gurinka nazo"
Bulama yace "gashi ina shirin fita ne, Amma meya faru?"
Anwar yace "Daddy dama cewa nayi meze hana a fita da Daddynmu waje a duba shi yadda ya kamata a can, naga kullum ciwon nasa gaba yake ba sauƙi"
Alhaji Bulama yace "Anwar kazo da magana me kyau, amma ka sani ko an fitar da Daula waje in har baze cire damuwa dake ransa ba, babu yadda za'ayi magunguna suyi masa aiki, haka likitoci suke ta faɗa"
"Amma da dai an jarraba, amma jikinsa yana bani tsoro"
Alhaji Bulama yayi shiru sannan yace "shikenan Anwar, zamu yi maganar da mahaifiyarka, zanga abunda ya dace ayi"
Anwar yayi masa godiya sannan ya tafi.
Alhaji Haruna ne zaune akan kujera, fuskar nan tasa babu alamar imani ya kalli wani matashi dake zaune yace
"doctor Sufyan, mun yaba da ƙoƙarin da kuke yi a Asibitinka akan Shahararren Attajirin da'ake ji dashi a faɗin ƙasar nan wato Alhaji Nasir Daula"
Doctor Sufyan yayi murmushi yace "Nagode ranka ya daɗe"
Alhaji Musa yace "Kasan meyasa muka kiraka?"
Sufyan ya girgiza kai alamar aa'
Alhaji Haruna ya gyara zama yace "Abunda muke so da kai shine, bama son Daula ya tashi"
Zare ido Sufyan yayi yace "kamar yaya?"
Alhaji Musa yace "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ba muna nufin ka kasheshi ba, A'a bama so ya tashi ya warke ta hanyar dena bashi magungunan da ya dace, kayi duk abunda zakayi masa wanda ze ƙara kwantar dashi, idan kayi haka akwai lada me tsoka da zamu baka"
Saleh dake gurin gaba ɗaya ya rikice yace "Amma Yallaɓai ba muyi haka daku ba, idan kuma ya rasa ransa fa?"
Alhaji Haruna yace "Saleh ka rufewa mutane baki, karka ɓatamin rai"
Ya maida hankalinsa kan doctor Sufyan yace "Yaya zakayi ko bazaka yi ba?"
Doctor Sufyan yace "Nifa na ɗau Alƙawarin bazan cutar da lafiyar kowa ba kafin in fara aiki, kuma Alhaji Nasir ya yadda dani, na daɗe ina duba shi lokaci ɗaya kuma se in....
" Kai dakata " Alhaji Musa ya dakawa Sufyan tsawa yace " karka kawo mana maganar banza malam, idan baka yi ba zamu nemi wani, kwata kwata aikin wata uku muke so kayi mana, za mu baka Naira miliyan goma, idan yayi maka kaɗan zamu ƙara maka"
Zare ido Sufyan yayi yace "miliyan Goma"
"ƙwarai kuwa, miliyan goma idan kuma kaƙi zamu saka wani amma ka tabattar da kaima ba zamu ƙyaleka ba"
Cikin hanzari Sufyan yace "zanyi ma, na amince zanyi insha Allah karka damu Alhaji"
Shiru Saleh yayi yana tunani, wato akan kuɗi mutanen yanzu duk alkhairinka sesu manta, idan baze manta ba dangin Sufyan ɗaiɗaiku ne Daula be kai aikin Hajji ba, Amma ya amince ze karɓi kuɗi ya cutar da Alhaji Nasir "
Da Sufyan ze tafi dubu ɗari biyar suka bashi wai ya zuba mai a mota.
Saleh yayi shiru abun duniya duk ya dameshi.
Su Alhaji Musa kuwa cigaba da ƙulle ƙullen sharrinsu suka yi.
Wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, suka tsagaita da dariyar da suke Ya ɗaga wayar yace
"Yaya me Adda, ya ake ciki ta faɗa maka kuwa?"
"Ina fa ta faɗa se wahalar damu take, ga taurin kai da tsiwar tsiya, sannan ta bada saƙo a baku"
Alhaji Musa a gigice yace "Kamar ya ta bada saƙo abamu ta sanmu ne?"
Me adda yace "ina nasan mata, cewa tayi mu cewa wanda suka sa a sace ta, ta tattaar duk wata hujja akan su, ko bayan an kashe ta asirinku ze tonu"
Wani gumine ya shiga tsatsafowa Alhaji Haruna yace "ƙarya take bata sanmu ba, a gidan uban wa ta sanmu balle ta tattara wata hujja a kanmu, yanzu kana ina ne?"
"ina cikin gari mana, naje Asibiti ne wani yarfi yarinyar nan ta min na kasa ko miƙewa tsaye, na ɗauka ma na tashi daga aiki"
Alhaji Musa yace "wani sakarci ne zesa ku baro su acan, maza ka koma ku gana mata Azaba iya Azaba seta faɗi inda takaddun suke, idan ta faɗi inda suke ku kashe su kawai"
Saleh yace "What akan me za'a kashe ta?"
Alhaji Musa be saurari Saleh ba ya cigaba da wayar sa.
Me Adda yace "gaskiya Oga kisan Yarinya kamar wannan ba kamar kashe sauran mutane bane, tsaf wannan cinnakun zasuyi ram damu"
Alhji Haruna yace "ba wanda ze kama ku, zancen nan da muke maka gaba ɗaya mun siye jami'an tsaro ba wani bincike da'ake akan ɓatan nata, dan haka ka gaggauta zuwa jibi idan bata faɗa ba ka tirsasa ta, ta gaya maka wasu hujjoji take dasu sannan ka kashe mana su"
Me Adda yace "angama Oga"
Alhaji Haruna ya sharce gumi yace "bala'i, Musa anya ba dagaske yarinyar nan ta gano mu ba, karfa muje dagaske take"
"Rabu da ita ƙarya take, da dagaske ta sanmu da tuni ta ɗau mataki akanmu, amma kasan bamu gayawa Munir da Bukar hukuncin da muka yanke ba?"
Alhaji Haruna yace "Suma idan mun gaya musu hukuncin da za susa ayi mata kenan a kashe ta kawai, karta ja mana masifa"
Alhaji Musa ya kalli Saleh yace "wai kai meye naka na saka baki dan munce a kashe ta, kabi a sannu fa wallahi kar kasa musa a haɗa da kai, kabi umarnin mu kawai"
Saleh yayi murmushi yace "Tausayin Daula ne ya kamani wallahi, karka damu bazan baku kunya ba insha Allah dani za'a kammala komai nima in samu rabona"
"daka temaki kanka" cewar Alhaji Haruna, yayin da cikkunansu suka ɗuri ruwa.
Yusuf yana nan zaune rungume da Widad, har duhu yayi gari ya waye, sam be bacci ba gani yake da yayi bacci Widad zata mutu, dan bugun zuciyar ta da yake ji shike tabattar masa tana da rai, dan wani lokacin har motsawa take.
A hankali Yusuf ya kwantar da ita, yayi taimama yayi sallar Asuba, shima gaba ɗaya jikinsa a sake yake babu ƙwari saboda azabar wahala, ga yunwa ga duka ga cizon sauro ga azabar sanyi dake gurin, amma gaba ɗaya yafi tausayawa Widad, lokaci lokaci yakan kwance hannun nata, ya goge jinin ya sake ɗaure mata, ga wani irin zazzafan zazzabi da ko sauka bayayi a jikinta.
A hankali Widad ta buɗe ido, sedai dishi dishi take gani bata gane komai, tana yi tana lumshe ido haka take kallon Yusuf.
Yusuf ya girgiza ta yace "Alhamdilillah, you are alive"
Bata iya amsa masa ba, sedai idonta ya sake rufewa
Yana rungume da ita, yayi shiru yana ta ambaton Allah, babu zato ba tsammani yaji ana ta sukuwa a saman roofing ɗin ɗakin, Yusuf ya ɗaga kai yana son gane meke faruwa haka? Cigaba da sukuwa akayi a gurin anata ƙoƙarin ɓare kwanon, can kuma se'aka dena, yaji anata ƙoƙarin buɗe ƙofar da suke ciki, waze gani Saleh ne ya shigo cikin ɗakin.
A gigice Yusuf yace "kaine? Da kai aka haɗa baki kenan aka mana haka?"
Saleh yace "baka da lokacin wannan tambayoyin, zuwa nayi na tseratar da ku, ka adana tambayoyinka, idan kun tsira seka yi su"
Hankalinsa ya kai kan hannun Widad dake sume yama zubar da jini, da sauri ya ƙaraso yace "meya sameta haka? Harbinta sukayi?"
Yusuf bece masa komai ba, sedai kallon tuhuma da yake ta binsa dashi.
Saleh yace "zaka iya tafiya kuwa?"
Yusuf ya jinjina masa kai alamar eh, "to taso maza"
Yusuf ya yunƙura ya miƙe, amma ƙafafunsa se rawa suke saboda dukan daya sha, ga uwa uba yunwar da yake ji.
Amma cikin jarumta, da sadaukarwa ya miƙe ya goya Widad a bayansa.
Suka fito daga gidan, Saleh ya maida gidan ya rufe, sannan ya ɓare saman roofing yayi hanya, sannan yayi musu jagora hannunsa ɗauke da compass dake nuna masa direction suka nausa cikin daji.
Yusuf ji yake kamar ze kifa, amma haka ya cigaba da tafiya, Saleh ya kalle shi yace "ko zaka sauketa in ta yaka?"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a karka damu"
Tafiya sukayi bata wasa ba, ƙafar Yusuf ko takalmi babu, ya dinga taka abubuwa danma ta cikin ciyayi suke kutsawa, haka suka dinga tafiyar cikin sauri, suna bi takan ciyayi dan kaucewa barin sawunsu yadda za'a gane hanyar da suka bi, daji ne har daji me sarƙaƙiyar tsiya, da manyan bishiyu.
Sunyi tafiya me nisan gaske sannan suka fito titi, sam Yusuf be san a ina suke bama, Saleh ya nunawa Yusuf mota yace "ya shiga"
Yusuf yayi turus ya kalli Saleh, a wahalce yace "wannan taimakon ma da kayi mana mungode, amma bazan hauba, Insha Allah zamu bar gurin nan".
"Yusuf, wallahi suka kamaku kashe ku zasuyi, da inada niyyar cutar daku da bazan ceceku ba"
Da ƙyar Yusuf ya yadda, ya hau motar, da alama Saleh ya gama shirya komai.
Shima Saleh haka yayi doguwar tafiya dasu a motar, tafiya kamar za'a bar duniya dazuka kawai suke ratsawa, tituna bakowa se su kaɗai, Shiru ne ya wanzu tsakaninsu har suka fara fita gari.
Wani ɗan madaidaicin Asibiti suka tarar a hanya, Saleh yayi parking Yasa Yusuf ya ɗakko Widad suka shiga Asibitin.
Kuɗi Saleh ya ajiyewa likitan, dan haka ba wani dogon bincike suka karɓi Widad, Amma Yusuf yaƙi zuwa ko'ina, a gabansa aka cirewa Widad bullet, akace se an tafi neman jini za'a ƙara mata.
Yusuf yace a ɗibi nashi, Saleh yace "baze yuwu a ɗebi naka ba, kaima a galabaice kake akwai buƙatar a duba ka"
Yusuf ya dage sedai a gwada jininsa in zeyi a ɗiba a sa mata.
Aka duba aka ga Yusuf ze iya bawa Widad jini, saboda rukunin jininsa ake cewa universal donor wato O-, sedai an samu jinin Yusuf da malaria, likitan yace
"baze yuwu asa mata jinin ba"
Shikuma Yusuf yace be yadda da kowa ba, jininsa za'a saka.
Saleh yace "kaga doctor, koma menene a jinin nasa saka mata, can taƙarke musu dan zamanmu anan akwai hatsari"
Aka bawa Yusuf Abinci, amma ya kasa ci se ɗan kaɗan saboda hankalinsa na kan Widad, ana ɗibar Jinin Yusuf jiri ya ɗebe shi ya yanke jiki ya faɗi, haka aka ɗauke shi aka bashi gado.
Akayi treating ɗin raunkan jikin Yusuf, aka masa allaurai dan samun relief.
Aka sakawa Widad jinin Yusuf, tare da sauran Allurai, Yusuf na farfaɗowa ya fara tambayar ina Widad.
Likitan yace "wai dan Allah meye alaƙarsa da wannan yarinyar haka?"
Saleh yace "ƙanwarsa ce shiyasa ya damu da ita, 'yan fashi ne suka harbeta akan hanyar su ta tafiya, ita kaɗai yake da ita shiyasa"
Yusuf ya koma inda Widad take yasa ta a gaba, ya ƙura mata ido ko ƙyaftawa bayayi, tunda aka cire bullet ɗin nan har yanzu bata farka ba.
A hankali ta buɗe idonta, ta yunƙura zata miƙe Yusuf ya riƙeta yace "bi a hankali fa jikinki babu ƙwari"
Ta kalli Yusuf tace "A ina muke nan?"
"I think we are save now insha Allah, yanzu zamu koma gida" ya bata amsa
Saleh ya shigo ɗakin yace "waye yace maka zaku koma gida ne"?
Widad ta kalli Saleh ta ƙura masa ido, kamar taga baƙuwar halitta.
Yusuf yace "meyasa ba zamu koma gida ba yanzu?"
"saboda idan kuka koma, da kai da ita da mahafinta duk sesun kasheku"
Yusuf yace "meyasa?"
"Zan gaya maka komai, Amma daga nan mafaka zan baku, inda zaku ɓuya ba zasu san inda kuke ba na gama shirya komai daga nan tafiya kawai zamuyi"
Saleh ya miƙowa Yusuf wata babbar jarkar youghurt yace "gashi nan kuci nasan ba wani Abincin kirki a cikinu, sannan ka canza riga ita kuma a sama ta hijjabi"
Yusuf ya karɓi youghurt ɗin ya buɗe ya miƙa mata, amma ta ɗauke kai, Yusuf ya girgiza youghurt ɗin ya ɗaga kai ya sha, sannan ya sake miƙa mata.
Se a lokacin ta karɓa, ta dinga sha saboda azabar yunwar da take ji, sedai tana gama sha ta dinga amai saboda kwanakin da tayi babu Abinci a cikinta.
Saleh yace "Yusuf yakamata mu bar gurin nan da gaggawa in kaiku inda zaku fake, zamanmu anan hatsari ne na gaske"
Yusuf yace "Amma jikinta har yanzu bata da lafiya, ya za'ayi mu tafi a haka?"
Saleh yace "zamu karɓi magungunan da zaku cigaba da Amfani da shi, amma dole mu bar gurin nan"
Haka likitan ya tattara magungunan Yusuf dana Widad ya basu, suka hau mota Saleh ya cigaba da nausawa dasu seda suka sake shafe wata tafiyar, Widad kam magungunan data sha basu saketa ba dan haka duka tafiyar nan bacci take, seda sukazo wata mararraba sannan Saleh yayi parking, wata tsohuwar motace akori kura ('yar ƙurƙura) gaba ɗaya ta sha jiki ta fatattake, hatta fentin jikinta ya koɗe duk ta mole, anyi parking ɗintabakin hanya.
Wani mutum ne ya fito daga a kori kurar, suka gaisa da Saleh, Saleh ya bashi mukullin motar da suka je da ita, suka kwance lambar motar dake jiki da wata.
Saleh Ya kalli Yusuf yace "Yusuf ku fito wannan motar zamu hau mu ƙarasa"
Yusuf yace "nifa Saleh ban gane wannan abubuwan ba, kodai kaima kana da wani ƙudurin ne akanmu"
"Yusuf wallahi ba wani abu da nake shiryawa don in cutar daku, sedai ƙoƙarin ceton rayuwar ku"
Yusuf ya fito hannun sa ɗauke da Widad suka shiga 'yar ƙurƙuran nan, Saleh yaja motar.
(Yau Widad ce a cikin irin wannan motar🙄)
Tashin hankali ba' a samasa rana, duk wannan uwar tafiyar da suka sha Nafila ce akan wadda suke yi yanzu, wata irin ruɓaɓɓiyar hanya suka bi, banda ƙura babu abunda yake tashi wata irin lalatacciyar hanyace, duk kwazazzabai da turɓaya ga uban ramuka, wani ramin in suka shiga da ƙyar suke fita ga ƙurƙuran nan se wani irin ƙugi injinta yake yi, gashi sun matsu a motar, duk yayin da suka shiga rami haka suke bige kafaɗu da ƙarfen motar.
Wannan kwaraf kwaraf ɗin ne yasa Widad ta farka, a hankali ta kalli Yusuf tace
"A ina muke?"
Yusuf yace "Sannu ya jikin naki?"
Bata bashi amsa ba ta kuma cewa "A ina muke ne?"
"Mun kuɓuta ne, Saleh ze bamu mafaka"
Ɗan lumshe ido tayi sannan tace "Na gaji jikina ciwo yake, hannuna zafi kaina ze fashe, Wayyo Allah Daddy na"
Yusuf yace "kiyi haƙuri insha Allah komai ze daidaita, zakiji sauƙi mun taho da magunguna"
Shiru tayi ta sake kwantar da jikinta a ƙirjin Yusuf, hawaye na bin gefen idonta.
Tun Yusuf yana sa ran tafiyar ta ƙare har yayi shiru ya zubawa sarautar Allah ido.
A hankali Yusuf ya fara ganin gidaje tsilla tsilla a gurin, gine gine na tsurar ƙasa haka Gidajen suke, wasuma ko katanga babu a haka suke, yayi mamakin wannan irin ƙasurgumin ƙauye haka da yadda mutane ke rayuwa a cikinsa, suka baro duk bakin hanya suka shigo wannan surƙuƙin guri sukayi ginin Gidaje.
A hankali suna cigaba da tafiya, yaga ƙauyene sosai me ɗauke da gidaje da mutane a ciki, sedai sunyi hannun riga da duk wani abun more rayuwa da jin daɗi, kama daga Makaranta, Asibiti, ko wani abu me kama da borehole tunda suka shiga ƙauyen Yusuf be ganshi ba.
A ƙofar wani babban gidan ƙasa, an shafawa ƙofar gidan farar ƙasa, alama dai mamallakin gidan yana riƙe da wata sarauta ne a ƙauyen.
Saleh yace "Yusuf ina zuwa"
Ya sauka daga motar ya shiga cikin gidan, Yusuf yana ta ƙarewa gurin kallo yana tunanin anya Widad zata iya rayuwa a cikin gurin nan?
A hankali yaji tace "Ka yadda da Saleh, kana da tabbacin shima ba cutar damu zeba?"
"Ko ban yadda dashi ba, Allah baze bashi damae cutar damu ba, nidai fatana inga kinji sauƙi gaba ɗaya"
Ajiyar zuciya tayi, tai shiru ba tace komai ba can Saleh ya fito shida wani dattijon Mutum, kansa ɗauke sa rawani.
Suka ƙaraso gaban akori kurar, dattijon yace "sannu dai ɗan samari"
Yusuf yace yawwa Baba, barka da yamma
"Yawwa barka" mutumin ya kalli Saleh yace "sune wannan?"
"Eh sune wanda na gaya maka, ina son su zauna a gidanka na wani lokaci, kafin komai ya lafa su koma"
"Amma kana ganin babu wata matsala Saleh, nifa bana son abunda zezo ya ɗagawa Al'ummar garina hankali, kasan ku mutan binni se a hankali"
Saleh yace "Haba dai, wane irin matsala taimako zakayi, baka ga yadda suke a galabaice ba, babu wata matsala insha Allah"
"Shikenan, shigo dasu se a kaisu ɗakin daka gyara musun"
Yanzu ma Widad ba zata iya tafiya ba, Yusuf ne ya ɗauke ta zuwa cikin gidan.
Duk da rabi tana hayyacin ta rabi bata hayyacin ta, tana mamakin mutane ne ke rayuwa a wannan gidan, roofing gidan kansa na Azarane, ta dinga kallon roofing tana tunanin menene wannan?
Yayin da wasu ɗakunan roofing danga ne.
Tunda suka shigo gidan, mutan gidan maza da mata suka fito suka yi cirko cirko kamar zakaru suna binsu Yusuf da kallo kamar sunga baƙin halitta.
Wani ɗakine a can ƙarshen gidan, Saleh yasa mukulli ya buɗe ƙofar katakon dake ɗakin ya shiga yacewa Yusuf "bismillah"
Ba lefi ɗakin yana da girma amma ba sosai ba, yana da taga guda ɗaya wadda akayi ta da katako da kuma langa langa, ɗakin ginin ƙasa ne tsura, sedai anyiwa ƙasan floor, aka shimfiɗa buhu a ƙasa sannan aka kawo tabarma duk aka shimfiɗa.
Akwai matsaikaciyar katifa a shimfiɗe a ƙasa, da bargo guda biyu se fula guda ɗaya duk sababbi.
Gefe ga tulu, da wani ƙaramin kwandon kwanuka da 'yan kwanuka a ciki, gefe ga sababbun bokitai guda biyu, da sabuwar buta.
Akan katifar Yusuf ya kwantar da Widad, da duk inda ya motsa ta ciwo yake mata.
Dattijon yace "wannan bata da lafiya ne haka?"
Saleh yace "Eh bata da lafiya, a hannun masu garkuwa fa na karɓo su, na maka bayanin komai, dan Allah Baba a kula dasu, duk abunda suke buƙata ayi musu"
"Shikenan, indai nine baka da matsala, ko baka kawo kowa ya zauna a gidan nan ba, gidan nan na jama'a ne, Allah ya basu lafiya"
Ya juya ya fita, yana kora yaran da suka yi dandazo a ƙofar ɗakin suna leƙen su Widad.
Idon Yusuf ne ya sauka akan akwatunan Widad data shirya domin tafiyar da zasuyi, da traveling bag ɗinsa da suka bari a motar da'aka sace su.
Yusuf ya zare ido yace "Nifa Saleh ina buƙatar kamin bayanin abubuwa, ya akayi ka samu jakunkunan mu na tafiya? Ya akayi kasan idan muke kaje ka tseratar damu?"
Saleh yace "Nasan zakayi mamaki, kuma dole ku tambaya, Amma yanzu ina sauri saboda zan koma kano kar su gane wani abu a ƙasa su fara zargina, duk yadda aka shirya sace ku dani akayi shi, Tun bayan sace ku ni kuma na fara shirin yadda zaku tsira, amma ka sani koda wasa karka kuskura kayi gangancin barin ƙauyen nan in bani na fita daku ba, dan wallahi suka ganku sekun kasheku"
Yusuf yace "wai tsaya, wai inane nan ma tukuna?"
"Nan wani ƙauye ne a cikin garin Bauchi, Zan dinga zuwa ina duba ku, a waccan jakar na ajiye muku abubuwan da ba'a rasa ba da zaku buƙata kafin ku saba da irin rayuwar da suke yi, ga kuma kayanku can dana kawo nan, nan gidan ƙanin kakana ne dan haka insha Allah baku da wata matsala, idan ma dawo za kaji komai "
Saleh ya fita tsakar gida ya kalli wata dattijuwa yace "Gwaggo dan Allah Amana nan, a kula da baƙin nan dan manyane duk abunda suke buƙata ayi musu"
Gwaggo tace "Lallai kam, baƙin suna da girma a gurinka, tunda sanadinsu gashi kana leƙo mu"
Wata mata a tsakar gidan tace "Eh aimu da yake cinyesu zamuyi shiyasa ba'a bamu amanar baƙin ba se ita"
Saleh yace "Aifa kedai halinki yana nan bazaki canza ba" yayi gaba abunsa, ya tafi gurin me gari suka sake tattaunawa sannan ya tafi.
Haka Saleh ya tafi ya bar su Yusuf a cikin wannan ƙasurgumin ƙauye.
A hankali Widad tayi juyi, ta ƙarewa ɗakin da take ciki kallo, wai anan zata zauna ita da suka zo sam bata zaci wai nan mutane ne ke rayuwa a cikin gurin ba se yanzu.
Yusuf yaje yayo Alwala, yazo ya tada salla sedai duk inda yayi se mutanen gidan su bishi da kallo.
Widad ta cire hijjabin jikinta, jikinta se faman ƙaiƙayi yake mata, Yusuf ya idar da salla zeyi magana ta riga shi ta hanyar cewa "zanyi wanka"
Ɗan zare ido yayi yace "to shikenan, bari inwa mutan gidan magana"
Ya fito tsakar gidan, yaga wadda Saleh ya kira da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 35