kallon Daddynta zuwa wani sashin daban, tanajin ɓacin ran saboda wannan daƙiƙin talasurun Fahad ɗin yau Daddynta ke mata faɗa, ze gane bashi da wayo.
"dan haka whether you like it or not, i have took the final decision, ending of this month zuwa farkon wata na gaba zan ɗaura Auren ki da Fahad"
Zare ido Ramlah tayi, taji zuciyarta kamar zata faɗo.
Fahad ya wani gyara zama ya kalli Alhaji Nasir yace "sannan Daddy gaskiya yakamata ayi mata magana akan tasan yadda zata dinga gayamin magana, ta tauna ta kafin ta faɗeta dan sam bata da ɗa'a"
Miƙewa Widad tayi tsaye a fusace tace "Over my death Body Daddy, wallahi da in auri wannan mara amfanin gara in kashe kaina, kai ka isa ka kalli tsabar idona kace a koyamin yadda zan magana, waye kai"
"Widad!!!" mahaifinta ya kira sunanta tare da Miƙewa kamar ze kai mata duka.
Cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya shiga tsakanin Widad da mahaifinta ya girgiza kai yace "Yallaɓai ayi mata afuwa dan Allah, baka saba yi mata magana haka ba karka fara yanzu karkasa zuciyarta tayi rauni, kowa ya juya mata baya, ka sauraretaba zata rasa dalilinta na ƙinsa ba"
Alhaji Nasir yace "Amma Yusuf yakamata Widad tayi min haka a gaban mutane ta nuna ban isa ba?"
Girgiza kai Yusuf yayi yace "ba tayi haka dan Wulaƙanta kaba, ta tashi a environment ɗin da kowa yana da 'yancin faɗan abunda yake ra' ayinsa, karka ɗau hakan a matsayin ta Wulaƙanta ka, kayi haƙuri dan Allah kasan bata da lafiya"
Tuni hawaye ya wanke fuskar Widad ta kalli Daddynta karo na farko a rayuwar ta da yaƙi bin abunda takeso, hannayenta biyu ta haɗa tareda duƙar da kanta alamar neman afuwa, daga nan ta juya ɗakinta.
Alhaji Nasir ya nemi guri ya zauna, Bulama yace "lamarin daughter se haƙuri, Allah ya shirya mana"
Hajiya Halima ta gyatsine baki tace "wannan direban ne yake hure mata kunne take iskancin data ga dama, na rasa wace irin alaƙace tsakaninsu banda haka ana mata faɗa meye na tsoma baki? Kaima Yallaɓai harda kai da kake saka bare a al'amuran gidanka"
Alhaji Nasir yace "ba ruwan Yusuf, a irin taurin kai na Widad da irin haƙuri na Yusuf be isa ya hure mata kunne ba, sedai haƙurinsa ne yasa suke tare har yanzu, dan haka karki ƙara aibata shi ko ɗora masa laifi, kaimu Fahad zan shawo kan komai insha Allah"
Yusuf ya miƙe yayi musu sallama ya fice suka cigaba da tattaunawa.
Cakwakiyar gidan nan akwai sarƙaƙiya da ban mamaki, yana nan zaune ya dafe kai yayi shiru Bulama da Fahad suka fito zasu tafi, Bulama ya shiga motarsa direbansa ya ja suka tafi.
Fahad ya tako zuwa gaban Yusuf ya zauna yana fuskantar Yusuf yace
"kaine direban Widad ko?"
Yusuf yace
"Eh nine"
"Naga kamar matsayinka a gidan nan ya wuce matsayinka na zahiri, zan ja maka kunne ne idan har kana shishshigi da iyayi ka kiyayi Fahad, dan bana barin duk wani abu daze kawomin cikas, matsiyaci kawai kalli rigar wuyanka wai har kaine zaka shiga maganar da bata shafeka ba"
Yusuf yayi murmushi ya miƙawa Fahad hannu yace "Assalamu Alaikum warahmatullah"
Fahad ya kalleshi yace "ni zaka miƙowa hannu kace mu gaisa, kasan koni waye?"
"haka Addini na ya koyamin, ban saniba ko zama a cikin turawa yasa ka manta hakan, rigar wuyana zata iya fin taka daraja in har da gumin halak na sameta, sannan nafi kowa sanin ko kai waye, ɗan adam ne da'aka samar daga Najasa wanda ƙarshena ni da kake kira matsiyaci da kai da kake ganin kanka wani ƙarshen mu ɗaya wato turɓaya kuma Abincin tsutsa, kana fuffukar ban san waye kaiba, kamar ba'a gabana mace ta keta ka ba ta Wulaƙanta ka, wulaƙanci mafi ƙasƙanci shine yadda ake cusa mata kai tana cewa bata sonka "
Galala Fahad yayi yana kallon Yusuf, sam be zaci Yusuf ya iya yanka baƙaƙen magnganu haka ba, Yusuf ya miƙe yace " ka kiyaye gaba, dan idan baki yasan me ze faɗa be san abunda za'a mayar masa ba, bana shkkar kowa se Mahaliccina, kana gayamin abunda beminba zan rama, ni yanzu damuwata be wuce yadda a dalilinka aka samun uwar ɗakina a damuwa ba, damuwarta tafi komai tsayawa a zuciyata"
************************************
"Akan me za'a ayi maka transfer bayan bamu sallami wannan mutanen ba? Waima waye yayi maka transfer ne haka ba shiri? Aknme za'a ɗauke ka daga garin nan?"
Abbas yayi ajiyar zuciya yace " wallahi ranka ya daɗe ban san yadda hakan ta faru ba, Suleiman ya cemin daga sama transfer ɗin tazo, abun baƙin ciki aka maye gurbina dana bari da Yusuf, ni ina kyautata zaton shine yaje yasa akamin transfer dan ya gaji muƙamina, kuma da yake munafiki ne ya zo yana nuna damuwarsa akan transfer ɗin da'akayi min"
Saleh ya numfasa yace "Abbas tabbas akwai babbar matsala wannan transfe da'akayi maka ba tare da samun binciken da Yusuf yayi ba, a ɗan ganin da nayi masa beyi kama da mugun mutum ba yana da nutsuwa, dan haka bashi da hannu a cikin transfer ɗin da'akayi maka, ni babban burina in samu binciken da yayi a hannuna in sallami wancan mutanen kafin su shiga target ɗinsu na biyu kuma na ƙarshe akan Widad, wanda target ne me hatsarin gaske"
Abbas yace "nifa takaicina shikenan yanzu ba zan samu kuɗaɗen nan ba? Gaskiya na ƙallafa rai amma karka damu Yallaɓai, dukda zan bar garin nan dole a samu binciken da Yusuf yayi"
Saleh yace "don't stress yourself i know what to do"
"Amma kana ganin rashin bada file ɗin akan kari zesa kaima ka shiga cikin matsala?"
"babu wata matsala am also planning something, karka damu ni zan tafi duk yadda ake ciki zamuyi waya"
Daga nan suka yi sallama.
Sam Yusuf ya dena ganin Widad, hakan yasashi shiga damuwa sosai, hakan yaso ya shafi aikin da yake yi, ya damu sosai yaga halin da take ciki, bashi da hujjar shiga cikin gidan tunda ba nemansa akayiba.
Mutanen gidan dama ba wanda yake saurarar Yusuf, dan haka haka yake zuwa ya wuni ya tafi zuciyarsa cike da son sanin halin da take ciki.
Yusuf yana zaune yana tunanin yadda zega Widad dan yasan koba'a gaya masa ba Widad tana cikin damuwa.
Fitowar Alhaji Nasir dasu Hajiya Halima ne ya dawo da Yusuf daga tunanin da yake yi, Fuskar Alhaji Nasir akwai damuwa amma ya danne damuwar tasa yana ta fara'a.
Yayiwa Yusuf alama da yazo, Yusuf ya taso yazo, Alhaji Nasir yace "Babban Yaya, airport za muje zamu ɗakko ɗana Anwar, ya kammala karatun sa"
Yusuf yayi murmushi yace "Masha Allah, shima Yayan uwa ɗakina ne?"
Alhaji Nasir yayi murmushi yace "Yusufa kenan, ai uwaɗakin ka bata da wa ba ƙani, Amma Anwar ma ɗana ne tunda na riƙe shi"
Yusuf yace "ba da ita zamuje bane? Naga ita bata fito ba?" Yusuf yayi maganar cike da son sanin halinda Widad take ciki.
"Kasan tana fushi dani ne, ta dena zuwa inda nake ma, na ɗan ƙyaleta ne ta huta, har seta gane mahimmancin maganata"
Har Yusuf zeyi magana, Hajiya Halima tace "Kaga ka ishemu da surutu, muyi mu tafi kar jirginsu ya sauka yazo yana faman jira"
Alhaji Nasir yace "Bimin shi a hankali Halima, Yaya nane a girmama shi ko dan sunan nasa"
Nura yana gefe ji yake kaman ya shaƙe Yusuf, ba'a taɓa ma'aikacin da Alhaji Nasir ke nunawa soyayya kamae Yusuf ba dukda mutum ne me girmama na ƙasanshi, tsabar abu yanzu Alhaji Nasir be fiye damuwa da Nura yaja shi a mota ba sedai Yusuf.
Gaban Mota Amal ta shige, yayin da su kuma suka shiga baya, Suna tafe a mota iyalan suna hira kamar ba abunda ke damunsu, Alhaji Nasir yana dauriya ne kawai, yayin da Yusuf ko uffan yakasa cewa hankalin sa na kan Widad.
Koda suka je airport sunyi A ƙalla mintuna talatin, sannan wanda suka zo dominsan jirginsu ya sauka, matashin kamarsa ɗaya sak da Amal, kana kallonsa kasan ɗan uwansu ne, da gudu sukaje suka rungume shi cike da farinciki, ya ƙaraso gaban Alhaji Nasir ya durƙusa ya gaishe shi.
Bayan sun gaisa ya kalli Yusuf ya miƙa masa hannu sukayi musabaha, da alama Anwar shi a nutse yake ba kamar 'yan uwansa ba, daga nan suka nufi hanyar gida, suna tafe kamar zasu fasa motar da hayaniya da shewa.
Har sukaje gida hirarsu kawai suke, amma alamu sun nuna Alhaji Nasir biye musu kawai yake, sun Sakkowa sukayi cikin gida yayinda aka bar Yusuf da kwaso akwatunan Anwar.
Suna shiga falo kawai Yusuf yaga Widad a zaune tana shan ruwan roba, sedai idanunta a kumbure suke, alamar kodai bata bacci kokuma kuka take yi, gaba ɗaya Yusuf yaji babu daɗi.
Anwar yace "Masha Allah, little queen ta girma Amma Daddy sha ka fashe ka bata dan yayi wuri ace tayi wannan girman"
Daddy yayi murmushi yace "gata nan tambaye ta, in da ragiwar sha ka fashe ɗin kaima ta sammaka"
Ba tsammani Yusuf yaga Widad ta ɗanyi murmushi, yayin da Hajiya Halima ta tsuke fuska tace "kaga muje ka wataa ruwa ka nemi Abinci"
Anwar yace "bari Mummy in gama ganin lovely ɗin Daddyn ta inji dalilin da yasa ba tazo taroni ba"
Yai maganar yana ƙarasawa inda Widad take ya zauna, Alhaji Nasir kam part ɗinsa ya wuce yana murmushi saboda Anwar akwai barkwanci.
Ramla cikin tsawa ta cewa Yusuf "dalla malam ka ajiye kayan na ki fita, uban sa ido kawai"
"Karki kuma yi masa tsawa, na kuma gayamiki ba zamanki yake ba, idan kika ƙara hukuncin daze biyo baya ka iya ɓatawa kowa rai" Widad tayi maganar ba tare da kallon Ramla ba.
Anwar yace "Ramla baki kyauta ba, babu daɗi abunda kikayi fa"
A fusace Mummy tace "dalla tashi ka wuce ciki, ina magana harda neman guri ka zauna"
Anwar ya miƙe yace "Widad idan na fito zanzo mu gaisa sosai ki bani sirrin wannan girman naki"
"No need Anwar, yanzu ma mun gaisa yawan shiga harkata ka iya baka matsala da kai da Ahalinka, ina taya ka murnar kammala karatunka, Allah yasa al'umma su amfana"
Tai maganar tana miƙa masa hannu suka gaisa, from no where Yusuf yaji wani takaici ya tokare masa zuciya ganin abunda ya faru.
Mummy ta tasa ahalinta suka shige sashinta, aka bar Yusuf da Widad a falon har ya juya ze fita ya bar falon ya waiwayo, ba zato suka haɗa ido tai saurin ɗauke nata idon daga nasa, a hankali ya dawo ya kalleta yace "Madam ko baki da lafiya ne?"
Girgiza masa kai tayi tace "jirani a waje gani nan zamu fita" ya jinjina mata kai ya fita.
Cike da damuwa Anwar yace "Mumsy meyasa bakya son Widad ne? Me tayi mikine haka?"
Ramla tace "yanzu daka dawo idonka ze gane maka ai"
"kar in sake magana ki samun baki, in bahaka ba sena tattakaki na gaya miki"
Ya maida hankalinsa kan Hajiya Halima yace "Rayuwar ta abun tausayi ce, tana buƙatar kulawa meyw a ciki dan ki haɗemu gaba ɗaya kin nuna mata kamar ke kika haifeta"
Amal tace "Taɓɗijan lallai baka san yarinyar nan da taurin kai kamar arnan farko ba, ba mutunci a lamuranta balle tausasawa bata ganin kowa da gashi waye za janyo ta a jiki?"
"Amla yaushe kika koma hakane? Gaba ɗaya kun zama fitsararru"
"karka ƙara ce musu fitsararru na gaya maka, bazan riƙe yarinyar da zata nemi ta halakani da baƙinciki ba, bata da tarbiyya sam bata da ɗa'a, shikansa mahaifin nata bata ƙyaleshi ba, weekends ɗin nan Fahad yazo ganin ta za'a haɗasu Aure da shi da ubansa ta haɗa ta wanke su da rashin mutunci tsaf, ubanta ya kirata yayi mata faɗa nan ma ta sake kunyata shi a gaban mutane ta hanyar nuna masa be isa ba"
Cike da ɗimuwa Anwar yace "wait ji nayi kamar kince za'a haɗata Aurw da Fahad, wani Fahad ɗin wai?"
"Fahad ɗin Bulama mana" ta bashi amsa
A diririce yace "Mummy ta yaya haka zata farune? Ita tace tana sonshi? A zatona ai Ramla yake so"
Amla tace "Ramla yake so, amma babansa da Babanta sukayi ƙarfa ƙarfa sukace zasu aura masa ita, tayi masa rashin mutunci amma yace ba gudu ba ja da baya seya aure ta"
Anwar yace "Impossible wallahi sedai ayi biyu babu, Fahad yafi kowa sanin yadda nake son yarinyar nan danme zemin haka? Na tabbata da nine bazan masa haka ba, wallahi indai da raina Fahad be isa ba, sedai zumuncin namu ya watse"
"haka nima indai da raina baka isa ka aureta ba, sedai ka canza wata uwar bani ba, dan da hankalina ɗana baze auri dangin mahaukata gadon rashin tarbiyya ba"
Bin mahaifiyar tasa yayi da ido, tare da mamakin wannan magana data fito daga bakinta, be kuma cewa komai ba ya fice cikin hanzari.
Wata katafariyar ma'aikata sukaje, Yusuf yayi mamakin haɗuwa gami da tsaruwar ma'aikatar kamar ba'a ƙasa Nigeria ba, Widad ta dinga ratsawa Yusuf na binta kamar inuwa haka suka isa wani makeken Office.
Kai tsaye ba neman izina ta bankaɗa ofishin ta shiga, Bulama ne zaune da ɗansa Fahad suna dudsuba wasu file, Widad ta kallesu tana huci kamar mayuwanciyar Mesa.
"daughter lafiya kuwa?" Bulama ya tambayeta.
"Dole ka tambayi lafiya mana tunda kayi nasarar cusawa mahaifina ra'ayinka wansa yake barazana ga ratuwata, be taɓa fushi dani kamar wannan karon ba yana kallon hawaye akan fuskata amma ya kasa share min hawayen, ya barni tsawon kwanaki ina fama da ƙuncin zuciya "
Bulama yace " Calm down daughter, wannan fa duk ba abun zafi bane, ke kika kambama abun kika maida shi babba, meye laifin Fahad dan an Aure shi? Kuma daba'a aure a haifeki? "
" kai baka ga laifin ɗanka ba ni na gani, bashi da nagartar daze iya zama miji a gare ni, na tsane shi bana sonsa kuma bazan aure shi ba, sannan ka gaggauta zuwa ka janye wannan maganar daga gurin mahaifina ya dena fushi dani, fushinsa yana daga abunda ke jefa zuciyata cikin tashin hankali, be taɓa fushibdanibba se a dalikin wannan gurguwar shawarar taka, bazanyi aure ba ka janye wannan maganar idan ba haka ba Wallahi sena baka mamaki daga kai har ɗan naka"
"Ke jahila!" Fahad ya faɗa tare da yunƙurin kai mata mari, ganin yadda take wa mahaifinsa shouting, sedai ba zato yaji an riƙe hannunsa anyi gefe dashi.
"karka kuskura koda wasa ka kuma yunƙurin ɗaga hannu akanta, koda mafarki kake kaga hakan zata faru kayi duk me yuwuwa kaga ka farka da baccin dan mummunan mafarkine balle a gaske, sannan kasan da kalmomin da zakayi amfani gurin yi mata magana"
Yusuf yayi maganar cikin fushi da harzuƙa, wani irin kwarjini Yusuf yayiwa Fahad, dan a doke tsaf Yusuf ze bazar dashi a gurin.
Bulama yace "ɗan samari kamar kana zaƙewa fa wasu lokutan"
Yusuf ya saki hannun Fahad cikin ladabi yace "bahaka bane ranka ya dade, nayi ƙoƙarin hana faruwar tsamin alaƙar daze biyo baya idan har Alhaji Nasir yaji ɗanka ya dakar masa 'ya me"
Bulama yace "koda baka yi hakan ba ni zan ɗau mataki Yusuf, bazan bari hakan ta faru ba sam"
Widad tace "naso ka bari ya dakeni, in sa a nuna masa shi ba komai bane, in nunawa duniya da bazata yake rawa, duk wannan fuffukar da yake da sena nuna masa in ba Widad babu shi, kuma Auren nan dole a fasashi, nazo ne dama dan in muku gargaɗi na ƙarshe a janye maganar nan kafin rugujewar duk wata alaƙa dake tsakaninka da mahaifina"
Sosai Fahad ya dinga huci, a gabansa yarinya ƙarama take cim zarafin mahaifinsa.
Bayan fitarsu Widad, Bulama yayi shiru yana tunani, Fahad yace "Daddy wannan wace irin dabbar yarinya ce me kyan ɗan maciji, bata da tarbiyya bata da ta ido Sam, ta dubi mutum kamar kai ta dinga gaya masa wannan maganganun, kana kallonta kuma Daddy"
Bulama yayi ajiyar zuciya yace "daka sake ka daki yarinyar nan da tabbas yanzu wani zancen ake ba wannan ba, koda wasa karka kuskura kayi gangancin cewar zaka dake ta, ta wuce yadda kake tunani, tabbas ba dan inajin nauyin Daula ba da se an fasa Auren nan, dan ina ganin ƙiyayyarka a idonta wanda har hakan yake son ya shafeni"
Fahad ya daki teburi yace "Nikuma ina sonta a hakan, zan Aure ta koda zata kashe kanta sena Aureta na wulaƙantata na nuna mata ita bakomai bace zanga wanda ze Nasara tsakanin ni da ita"
Bulama ya girgiza kai yace "Fahad kenan kai kana tunanin zaka iya Wulaƙanta ta idan ka Aureta, dole kayi haƙuri da duk abunda zata aikata maka, zamuyi mata aurene dan samun nutsuwar ta ba dan a muzguna mata ba, shiyasa tun da fari bamu nemi wani bare sekai"
Gajeren tsaki Fahad yayi yaja kujera ya zauna tare da dafe kansa.
Kallonsa take yana tuƙi fuskarsa ɗauke da ɓacin rai, tunani take a duk lokacin da yaga wani na shirin cin zarafinta ko ɓata mata rai se yayi duk me yuwa ya hana faruwar hakan, a duk lokacin da take cikin damuwa zataga damuwa a fuskarsa, wanda ko ɓata masa rai tayi be fiye nuna damuwa haka ba.
Ajiyar zuciya ta sauke seda Yusuf ya juyo ya kalleta yace "lafiya kuwa?"
Ta jinjina masa kai alamar eh, haka suka koma gida ranta a matuƙar ɓace.
Anwar suka gani a harabar gidan, ya ƙaraso da sauri inda take yace "Widad ina kika jene? Tun ɗazu nake dubaki a gidan nan ban ganki ba" yai maganar cike da damuwa.
Widad tace "Anwar bana son daga dawowarka ka fara shiga cikin matsalolin gidan nan, zaka fuskanci fushin mahaifiyarka idan haraka cigaba da shiga harkata, am sorry amma kayi harkokinka inyi nawa please"
Ze sake yin magana tayi gaba ta shige ta barshi a gurin, ya kalli Yusuf yace "ɗan uwa dan Allah meke wakana a gidan nan ne? Ni gaba ɗaya abubuwan mamaki suke bani"
Yusuf yace "gaskiya nima ban sani ba, tunda nima banfi watanni huɗu da fara aiki a gidan nan ba, bakomai nasani ba, sedai damuwa na damunta sakamakon Auren da za'ayi mata, bata fiye son a shiga harkar ta ba idan tana cikin damuwa shine kawai abunda nasani"
"dan Allah wai dama maganar Auren nan dagaske ne?"
"Eh gaskene" Yusuf ya bashi amsa
"Impossible" Anwar ya faɗa da ɗan ƙarfi
"Ni Fahad zeyi wa haka? Saboda cin amana da wulaƙanci" Anwar ya girgiza kai ya koma cikin gida fuskarsa ɗauke da ɓacin rai.
Washegari da safe Yusuf ya shirya ya fita, seda ya fara biyawa gidan Abbas amma ya tarar baya nan, kamar yaje office amma ya fasa ya wuce gidansu Widad.
"Yusuf gimbiyar masu gida da kanta ta fito nemanka, da alama ka makara fa"
Yusuf yace "wani abune ya ɗan tsareni, bari inje in ganta"
Murtalah yace "tana lambu ita da tsuntsayenta da ƙanwarta wato kyanwarta"
Yusuf yayi murmushi ya nufi lambun, kamar yadda Murtalah ya gaya masa tana lambun ita da magenta Roux, magana takewa magen nata kamar da mutum take magana tana cewa
"Roux har yanzu Daddy yana fushi dani, gaba ɗaya duniya tamin zafi, ba wanda ya goyi bayana ko ya tausayawa halin da nake ciki, ba zan iyayiwa Daddy biyayya in Auri Fahad ba, ji nake kamar zuciyata zata tsaya saboda ɓacin rai, amma dole in san hujjar da zan gabatarwa Daddy da zesa a fasa Auren nan, am so much disturbed Roux"
Tana maganar tana shafa jikin magen, yayinda magen tayi luf a jikin Widad kamar tasan me take gaya mata, lokuta da dama Yusuf yana jin Widad tana hira da Mage, hirar da be taɓa jin tana yi da ɗan adam cikin mutuntawa da nutsuwa haka ba.
Ji tayi kamar ana kallonta ta ɗaga kai suka haɗa ido da Yusuf, ta tsuke fuska tace "baka iya Sallama bane?"
"Ai idan nayi sallama bakya amsawa" ya bata amsa
"Se yanzu kaga damar zuwa ko?"
"Umma na taya aiki shiyasa banzo da wuri ba"
"shikenan, zamu fita yau ƙarfe tara"
"Amma ai tara ta wuce yanzu, sedai ta gobe in Allah ya kaimu"
"tara na dare" ta bashi amsa
"tara na dare kuma? Ina zamuje haka da daddare? Kuma mu dawo yaushe? "
Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "hmmm akwai ka da ƙwarin gwiwa, ƙarfin hali bin ƙwaƙwƙwafi da sa ido sekace ɗan Sanda ko wani jami'in sirri, za kayi kyau da Aikin ɗan sanda ko kuma fannin shari'a"
Wani abune ya tsarga tun daga kan Yusuf har yatsunsa na ƙafa.......
(INA BUƘATAR JIN SHARHINKU FANS, ME KUKE TUNANI NE AKAN WANNAN TURKA TURKA, INGA COMMENTS ƊINKU KO IN KOMA POSTING DA TSALLAKEN KWANA ƊAYA)
Share and share please
domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680
_*AƘIDATA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_
The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *
I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum
Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
ELEGANT ONLINE WRITER'S
PART1
Page 20_21
Widad ta cigaba da cewa "da aikin shari'a zakayi zeyi wuya a iya kada kai, yakamata Alhaji Nasir yayiwa yayansa wani abu, yakamata ya nema maka makaranta ko dai horarwa akan aikin tsaro kokuma a nema maka aikin shari'a" ta ƙarasa maganar da wani ɗan guntun murmushi
Yusuf ya daskare ya kasa ko motsa ɗan yatsansa 'Widad ta gano shine kokuwa?'
"Jeka in lokacin yayi kazo mu tafi"
Kasa motsawa Yusuf yayi, ya tasaya yana kallon Widad, ta ɗago ta kalle shi tace "ya dai naga ka tsaya? Meyafaru?"
Girgiza kai yayi ya juya ze fita, beji takuma cewa komai ba.
Tunani ne ya shiga zarya a zuciyarsa, kodai Widad tasan waye shine? Amma ya tuna da sharaɗinta bata yafewa wanda yayi mata ƙarya, a rashin yarda nan tata tabbas da tasan waye shi da tuni tayi maganinsa ta ɗau mataki akansa.
A hankali ya furta "Ubangiji Allah ka shiga lamarina, Allah yasa har in kammala aikin nan yarinyar nan ba zata ganoni ba"
*****************************
"Amma ni tabbas ba'ayimin Adalci a wannan lamarin ba, nida ɗan uwana ku kusan halaka shi sannan ace bazan ganshi ba, wannan wane irin zalunci ne"
"zaka iya kiransa da duka abunda kaga dama, amma tabbas ba zaka ganshi ba, zamu ci gaba da ajiye shi a ɓoyayyen guri har se sakamakon binciken nan yazo hannun mu"
Saleh yace "binciken nan bani na yake yi ba, kun san hukumar da sukeyi meze sa ku cigaba da azabtar min da ɗan uwa"
"saboda shi kaɗai ne hujjar daze fallasa komai a kotu, kuma yana nan shirin tona mana Asiri dan haka gara muyi maganinsa"
Cike da damuwa Saleh yace "to ai wanda yake ƙoƙarin samo min sakamakon anyi masa transfer ya kuke so inyi, ni ko ganinsa inyi shikenan"
Alhaji Musa yace "baja da wannan damar Saleh, kayi abunda muka ce kawai"
A fusace Saleh ya miƙe ya bar gurin zuciyarsa na masa zugi, tabbas su Alhaji Musa masifa ne a rayuwarsa da ɗan uwansa.
Anwar a cikin ɓacin rai yaje ya samu Fahad a gida, Fahad na ganinsa yace "Ohh God, Anwar ai namanta gaba ɗaya jiya zaka dawo am so sorry brother"
Jiki a sanyaye Anwar ya kalli Fahad yace "Am disappointed Fahad, dole kace ka manta jiya zan dawo, yanzu Fahad yarinyar dana daɗe ina mafarkin aura ita zaka aura?"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 35