Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ni kuma ban san ta yaya zan yi ba." Kama hannunta ya yi suka zauna akan dankalin dake ƙofar gidan ya ce. "Kafin nan, wa ya fito da ke nan?" Ta ce. "Da kaina na fito." Ya ce. "Amma Mama ba ta sani ba ko?" Ta ce. "Eh wanka take yi, ni kuma na gaji da zaman gida." Ya ce. "Ta yaya kika fitowa?" Ta ce "Ai na san hanya, kawai bi nake yi a hankali." Shiru ya yi yana kallon ta cike da tausawa na wasu sakanni sannan ya ce. "Me yasa idan kika gan ni ba kya gaishe ni?" Cikin shagwab'a ta ce. "Kai ma ai baka mun magana sai dai ka gaishe da Inna kawai." Ya ɗan lumshe ido ya buɗe ya ce. "To na daina, daga yau zan dinga yi miki magana, ai mun zama Friends ko?" A'isha ta ce. "Kai! ta yaya? Kai fa Namiji ne." Ya ce. "Eh duk da haka, ni dai kin zama ƙawata." Dariya A'isha ta yi ta ce. "Tab', so kake Inna ta zane ni ina abota da Namiji?" Ya ce. "Ai zan faɗa mata da kaina." A'ishah ta ce. "Wai kai ina ne gidanku?" Ya ce. "Gidan Sarki." A'isha ta ce. "Amma ya aka yi ban san ka ba tun daa? Inna ma haka." Ya ce. "Wasa nake miki, gidanmu ba'a nan garin yake ba, wani abu ne ya kawo ni garin nan akan karatuna." A'isha ta ce. "To a ina kuke?" Ya ce. "Kaduna State, kin san garin?" Girgiza masa kai ta yi ta ce. "Sarkin Ɗan'uwanku ne?" Ya ce. "Abokin Abbanmu ne." Ta ce. "Me kake yi a garin nan to?" Ya ce. "Gona nake zuwa da sassafe kullum ina duba abu." Ta ce. "Yaushe zaka tafi?" Ya ce. "Sai an ɗan daɗe." Dai-dai nan Inna ta lek'o dan duba A'isha, ajiyar zuciya ta sauke ta ce. "Sannu A'isha." A'isha ba ta ce komai ba dan ta san ta yi laifi, shi kuwa ƙasa ya yi da kansa ya gaishe da Inna, ta amsa cikin fara'a sannan ya tashi ya tafi, yana jin zuciyarsa cike da Nishad'i sanadiyyar kasancewar su da A'isha. Ita ma ji ta yi dama kar ya tafi ya zauna su yi ta hira, tunda su Ma'u suka tafi ba ta da abokin hira, ko a makaranta sai dai ta zauna ta yi shiru ita kaɗai. Jiki a sanyaye ta tashi Inna ta kama hannunta suka shige gida. A hankali a hankali Umar yake shiga jikinsu Inna, dan kullum sai ya zo har gida ya gaishe da Inna tare yi musu Alkhairi. Cikin lokaci kaɗan suka saba da shi sosai, Inna ta yaba da hankali da nutsuwarsa shi yasa ta saki jiki da shi, zuciya tana son mai kyautata mata, Umar sai ya zamowa A'isha tamkar madadin Ma'u, dan mayar da kanshi yake yaro kamarta su yi ta hira cikin barkwanci. Cikin wata guda ya fahimci irin rayuwar da suke yi a cikin garin ta matsin rayuwa da ƙyarar su da ake yi, tausayinsu ne ya ninku a cikin zuciyarsa, hakan yasa ya ɗauki damarar taimaka musu har sai inda ƙarfinsa ya ƙare. Tun daga kan kayan abinci da komai na buƙatar rayuwa ya siyo mai ɗan yawa musu ya kawo musu, Inna ta dinga yi masa faɗa tana cewa kayan sun yi yawa ita baza ta karɓa, daƙyar ya lallab'a ta, ta karɓa. Ai kuwa ya sha addu'oi da tarin godiya. Mutan gidan sai yawo suke yi da inna a cikin gari suna cewa daga yin baƙo daga birni Inna ta lashe masa kurwa kullum yana jikinsu yana yi musu uban hidima yana wahala da su. Sarki kuwa yana sane da duk abun da yake faruwa, hakan ma shi daɗi ya yi masa, ya dinga sakawa Umar albarka akan taimakon su inna da yake yi. Su A'isha sun yi jarrabawa a makaranta, amma ita ba ta yi ba tunda ba ta gani, an yi hutu, hutun kuma mai yawa kasancewar idan an dawo sabon aji za'a shiga. Tunda aka yi hutun kullum da safe sai Umar yake yiwa A'isha lesson da baki (Oral), kuma Alhamdulillah tana ganewa, dan har words ɗin English yake koya mata, da yamma kuma su yi karatun Alkur'ani da tarihin Annabawa, da karatun su fiqhu. Yau da safe wajen ƙarfe goma sha ɗaya na safe A'isha na zaune akan tabarma a tsakar gida tana aikin b'ab'b'ata fuska tare da turo baki gaba, saboda Inna ta yi mata faɗa akan barnar ruwan da ta yi mata da sunan zata yi mata wanke_wanke ba tare da ta saka ta ba, Umar ne ya shigo gidan cikin shirinsa na manyan kaya, ya yi kyau sosai ya fito a matashinsa na ɗan 25 years. Tun kafin ya ƙaraso cikin zagayen su Inna ƙamshinsa ya riga shi zuwa, cikin kamilalliyar muryarsa ya yi sallama. Suka amsa mata a tare. Cikin girmamawa ya tsugunna ya gaishe da Inna dake cikin madafi tare da yi mata sannu da aiki, ta amsa cikin fara'a sannan ya ƙarasa ya zauna a kusa da A'isha. A hankali ya ce. "Good Morning." Shiru ta yi masa. Yana kallon yanda ta cukule ta kumbura k'iris take jira ta fashe ya danne dariyar dake cin sa ya ce. "Yau babu magana ne Indo?" Kamar za ta yi kuka ta ce. "Ya Umar na ce ka daina ce mun Indon nan?" Ya ce. "To ai na fi son na kira shi da sunan ya fi mun daɗi." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni dai gaskiya bana so, sai ka ce wata tsohuwa?" Shiru ya yi yana kallon ta tare da sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa a hankali. After some seconds ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "To na daina HUMAIRAH." murmurshi ta yi ta ce. "Yawwa Yayana, ai gara Humairan da wani Indo." Murmurshi ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce. "Kin yi kyau sosai Bestie." A'isha ta ce. "Amma ban kai ka ba ko? Na san kai kyakkyawa ne." Ya ce. "Taɓ, a yi shiru dai kawai." Kallon sa ta yi ta ce. "Ina son na gan ka Ya Umar." Yanda ta yi maganar cikin raunin murya sai ta tsinkar masa da zuciya, a hankali ya ce. "Za ki ganni watarana soon Insha Allah." Ta ce. "Allah yasa." Lesson ɗin ya shiga yi mata bayan sun ɗan yi revision akan na jiya ya ƙara tuttuna mata abun da ta manta. Suna cikin karatun wayarsa ta yi ƙara alamar shigowar kira, ɗaukowa ya yi ya duba, ganin mahaifiyarsa ce ya daga ya kara a kunne tare da yin sallama. Daga can bayan ta amsa sallamar ta ce. "Ka kira ni ina part ɗin Abbanku, wayar kuma tana ɗaki sai yanzu da na dawo na gani." Ya ce. "Ok, an tashi lafiya Mom? Ya su Abban da Mufeedah?" Ta ce. "Suna nan lafiya ƙalau, da fatan kai ma haka?" Ya ce. "Alhamdulillah, sai dai kewar ku kawai da nake yi Mom." Mom ta ce. "Yaushe zaka dawo ne? Na ji Abbanku yana wai sai nan da 1 month." Ya ce. "Eh haka ne." Mom ta ce. "Uwar me zaka yi har na 3 months a wannan ƙauyen? Me yake damun ka ne Faruq?" Cikin kwantar da murya ya ce. "Mom ban gama abun da na je yi ba ne." A fusace ta ce. "Ai baza ka taɓa gamawa ba, ko aikin uban me ne ai zuwa yanzu ya ci ace in ma haddacewa ne ka yi ba iyawa kaɗai ba. Kawai kana son ka ɓatan rai ne Faruq, amma ka san ba son zamanka a ƙauyen nan nake ba, yanzu kafin ka dawo na san duk sai ka yi baƙi ka fita daga hayyacinka ka koma kalar ƴan garin." Umar ya ce. "Haba Mom dan Allah ki yi hak'uri, garin fa akwai daɗin zama, yanda kike tunaninsa ba haka yake ba, dan suna da abubuwan...." cikin hasala ta katse shi da faɗin. "Kai ka san wannan, ni dai abun da zan faɗa maka nan da 1 week ka haɗa kayanka za'a zo a ɗauke ka, zaman ƙauyen naka ya ishe ni haka. Ko ka gama abun da ka je yi ko ba ka gama ba is not my concern." Cikin damuwa ya ce. "Amma Mum......" A fusace ta ce. "Umarni nake baka Faruq, idan kuma ban Isa ba ne sai in ji......Ka je ka zauna a ƙauye for almost two months bai ishe ka ba sai ka ƙara wasu kwanakin, salon ka saba da ƴan garin har bayan ka dawo ka dinga mu'amala da su....To ba zai yiyu ba wallahi, wannan zaman ma da ka yi ba ƙaramin hak'uri na yi na danne zuciyata ba, dan dai babu yanda zan yi ne tunda Mahaifinka ya ce dole sai ka je. Sanin kanka ne ka san ni sarai bana son tarayya da TALAKA da duk wani abu da ya danganci TALAUCI, balle kuma TALAKAN ma na ƙauye!" K'wafa ta yi ta cigaba da magana cikin ɗacin rai da faɗin. "Kamar ni a ce ɗana ya tafi wani ƙauye yana rayuwa a can na tsawon watanni? this is too much shameful thing for me." Shiru Umar ya yi ya rasa me zai ce mata, tsaki ta ja tare da kashe wayarta............✍️ *FAUZARH ORGANIC SKINCARE* _PRESENT_ *5️⃣ DAY'S SKINCARE ONLINE TRAINING* *💗ABUBUWAN DA ZAN KOYAR💗* *da farko zanyi bayani akan ƙurajen fuska da abun da ke kawosu, da hanyar da za a bi wajen magance su* *WHITENING BLACK SOAP* *LIGHTENING BLACK SOAP* *NATURAL BLACK SOAP* *FACE AND BODY SOAP* *BODY CREAM* *SABULUN GYARAN AMARYA* Wannan training ɗin tamkar gara6asa ne🤩 da naira ɗari ukun ki kacal za ki koyi sana'a.👌 *Zamu fara training din 5 ga wannan watan ne insha Allah* *DUK GARIN DA KI KE ZAN SANAR DAKE INDA ZA KI SAMU KAYAN HADIN* *Domin neman karin bayani a tuntu👉🏼http://wa.me/+2347065012071* *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣2️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Cikin sanyin jiki Umar ya zare wayar daga kunnensa, A'isha da ta yi shiru tare da zuba masa ido kamar tana ganin sa ta ce. "Wa ya kira ka a wayar?" Numfashi ya sauke tare kallon cikin idonta ya ce. "Mamana ce." Ɓata fuska ta yi ta ce. "Shine ba ka ba ni mun gaisa da ita ba." Jinjina kai ya yi a ransa yana imagine masifar da Mom za ta cinye shi da ita idan ya ba ta suka yi magana da wani a garin nan da sunan sun saba da shi. Cikin sanyin murya ya ce. "Sorry, zan kira miki ita wani time ɗin." Murmurshi A'isha ta yi. "Toh na gode." Inna ce ta zo ta ajiye tuwo da miyar da ta gama dafawa a gaban Umar, sannan ta koma ta deb'o masa ruwa ta kawo masa. Cike da kunya ya yi mata godiya sannan ya ɗauraye hannunsa ya yi Bismillah ya fara cin tuwon cikin nutsuwa bayan Inna ta shige ɗaki. A'isha ta turo baki cikin ɗaga murya yanda Inna za ta jiyo ta, ta ce. "Inna ni baki kawo mun tuwon ba." Inna ta ce. "Sai kuma na tashi, yanzu ina hutawa ne, tunda kina ji ai na kawo masa amma ba ki yi magana ba." A'isha ta ce. "Ni ban ji sanda kika kawo masa ba." Inna ta ce. "Ai ba za ki ji ba dama." Murmurshi Umar ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce. "Zo in baki wannan a baki ki ci." Waro ido A'isha ta yi tare da buɗe baki za ta yi masa kwakwazo. Cikin saurin ya rufe mata baki da hannunsa kamar ya san me take shirin yi. Cikin rad'a ya ce. "Wasa nake miki ba baki zan yi ba." Ture hannunsa ta yi ta ce. "To sai ka ce wata yarinya zaka ba ni abinci a baki?" Bai ƙara magana ba saboda yanda kunya ta lullub'e shi, dan ya san daƙyar idan Inna ba ta ji abun da A'isha ta faɗa ba. Da ya gama cin abincin ba su cigaba da karatun ba, sallama ya yi musu ya tafi. Yana fita daga gidan ya ga su Ɗan_juma a ƙofar gidansu Hamza a zaune, suna haɗa ido da shi ya haɗe rai, ya yi wucewarsa. Wani wulak'antaccen kallo Ɗan_juma ya bi shi da shi sannan ya yi k'wafa ya ce. "Gayen nan yana shigar mun hanci da ƙudundune ba kaɗan ba wlh, ya sa Sarki ya mun iyaka da yarinyar can sannan shi kuma yana lallab'awa yana zuwa gurinta yana yaudarar su da ƴan canji yana yin abun da ya ga dama ita, To billahillazi baza ta saɓu ba, kafin ya bar garin nan sai na yi masa abun da har ya mutu ba zai manta da ni ba, da ni yake zancen." Hamza ya ce. "Kai Ɗan_juma yanzu duk izayar da muka sha akan yarinyar nan baza ka rabu da ita ba?" Ɗan_juma ya yi wata dariya ya ce. "Ai ni wahalar da suka ba mu ƙara mun yawan abun da nake ji a kanta suka yi ba su sani ba, ni fa tunda na had'iyi yawo akan wannan yarinyar sai na mayar da yawuna ko ta halin yaya." Hamza ya ce. "To Allah ya ba da sa'a." Da yamma Umar ya koma gidansu Inna, suna zaune a tsakar gida shi da Aisha, Inna kuma tana bakin rariya tana wanki. Umar da yake kallon A'isha ya ce mata. "Wai Humairah duk akan turaren ne aka ƙi mun magana tun ɗazu?" A'isha ta ce. "Tun yaushe na ce maka ina son ƙamshin ka kawo mun amma ka ƙi? Ai na san da budurwarka ce ta ce ka ba ta da tuni ka ba ta." Umar ya ce. "Haba Indodona kema fa zan baki, mantawa nake yi ne." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni ba ma na so yanzu." Umar ya ce. "Me yasa? Haba Bestie kar ki yi fushi da Yayanki mana, bari in tashi yanzu in ɗauko miki." Aisha ta ce. "Ni dai ba na so, ko ka kawo ba zan karɓa ba." Cikin marairaicewa ya ce. "Dan Allah ki yi hak'uri ni ne fa?" A hankali ta ce. "Kana son na hak'ura?" Ya ce. "Eh." Ta ce. "To sai ka roƙi Inna ta bar ni mun je bakin ruwa mu yi wasa." Umar ya ce. "Kin san ma ba za ta bar ki ba, last week ma haka kika yi ta rok'on ta, ta ƙi barin ki." A'isha ta ce "to ai tare zaka ce mata zamu je, za ta bari." Shiru Umar ya yi amma ya san Inna ba za ta bari ba. Kamar A'isha za ta yi  kuka ta ce. "Dan Allah Ya Umar?" Ya ce. "Shikenan let me try." Duk maganar da suke yi a ƙasa_ ƙasa suke yi dan kar Inna ta ji. Yana shafa kai ya ce. "Am.... Mama wai zaki bar A'isha ta je bakin ruwa ganin wasa?" Inna ta juyo ta ce. "Idan ta je da wanne idon za ta gani banda neman magana irin nata?"  A'isha ta ce. "Dan Allah Inna ki bar ni, ni kullum ina gida ba na fita, ko me ake yi bana zuwa." Ta ƙarashe zancen idonta cike da hawaye, sai ta bawa Umar tausayi, ga kuma wani iri da ya ji a cikin ransa ganin tana hawaye, bai san lokacin da ya ce. "Mama ki bar ta dan Allah sai mu je tare." Inna ta ɗan yi jimmm sannan ta ce. "To shikenan amma kar ku kai Magriba." Umar ya ce. "Insha Allahu." Rawa A'isha ta kama yi daga zaunen da take cikin murna. Harararar ta inna ta yi ta ce. "Sai in fasa barin naki in baki nutsu ba." Nutsuwa ta yi tare da miƙewa, Umar yana murmurshi ya tashi ya ɗauko mata takalmanta ta saka ya ciro mata hijabinta dake kan igiya ta saka sannan ya kama hannunta suka fice bayan sun yiwa Inna sallama. Inna ta bi su da kallo tana ganin rashin dacewar riƙe hannun A'isha da Umar ya yi, da tana da hali wani yaron za ta kira ya kama hannun A'ishan a maimakon Umar ɗin, addu'ar Allah ya tsare ta yi musu sannan ta cigaba da wankinta.   Bakin ruwa wani ɗan ƙaramin ruwa ne a cikin garin dake bayan gidan Sarki, duk ranar asabar da yamma ƴan'mata da samari na taruwa a gurin a yi wasanni, har kid'a ake bugawa wasu su shiga su yi rawa, gefe guda kuma ga masu siyar da abubuwan siyarwa kala_kala. Yau ma kamar kullum an cika a gurin, wasu na tad'i wasu suna cikin ruwa suna wanka. Kallon abubuwan da suke faruwa Umar ya tsaya yana yi, dan duk zamansa a cikin garin bai taɓa zuwa gurin ba sai yau. A'isha dake cikin farinciki ta ce. "Ya Umar mu je mu shiga ruwa." Kallon ta ya yi ya ce. "Ruwa kuma Humairah? ke da ba gani kike ba sai kin je ya tafi dake?" Shagwab'e fuska ta yi ta ce. "Ruwan fa k'arami ne ba shi da zurfi, kuma ba shiga za mu yi ba ƙafafuwanmu kawai za mu saka a ciki." Bai ce komai ba ya ja ta zuwa bakin ruwan ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna. Fiye da rabin mutanen gurin kallon su suke yi, musamman ƴan'mata da ba ƙaramin tafiya da hankalinsu Umar ya yi ba. A hankali ya zarewa A'isha takalmin ƙafarta ta zira ƙafafuwan nata a cikin ruwa fuskarta ɗauke da murmurshin dake nuna tana cikin farinciki. Tana ta wasa da su a cikin ruwan shi kuma yana ta aikin kallon ta, cikin ransa yana yaba kyawun halittarta, babu abun da ya fi burge shi a tattare da ita kamar kalar fatarta da dara_daran idanunta. Lumshe idonsa ya yi yana jin yanda son ta yake ƙara mamaye ko'ina a cikin zuciyarsa. After 15 minutes ya ce mata su tashi su je su saya wani abun su ci, shago suka shiga ya siya mata choculate da drinks. Suna zaune a ɗan nesa da ruwan kaɗan A'isha tana shan choculate ɗinta ta ce. "Yaya Umar ka ga gurin akwai daɗin zama ko? Ina son zuwa tun daa Inna ce ba ta bari na." Umar ya ce. "Eh, dan gaskiya ina cin dariya tunda na zo gurin nan, musamman in naga an shiga filin rawa ana cashewa." Ya ƙarashe maganar cikin dariya. A'isha ta yi murmurshi ta ce. "Ko mu ma mu je mu yi ne?" Waro ido ya yi ya ce. "Ai ban iya ba, ni dai mu zauna a nan ki bani labari mai daɗi." A'isha ta ce. "Ni ba ni da labari, sai dai kai ka ba ni na ƴan'gidanku dama baka taɓa ba ni ba." Karɓar choculate ɗin hannunta ya yi ya ce. "Sai dai na baki na budurwata, kina so?" Ɓata fuska A'isha ta yi ta ce. "Bana so." Tare da ɗauke kanta gefe. Murmurshi Umar ya yi ya ce. "Shikenan ga choculate ɗinki cigaba da sha." A'isha ta ce. "Na ƙoshi." Karyar da kai ya yi yana kallon ta kawai, ita kuwa sai ƙare haɗe rai take tana turo baki gaba. Cikin sanyin murya ya ce. "Wai me ya faru na ga kina ɓata rai?" Kamar zata yi kuka ta ce. "Babu komai." A hankali ya ce. "I'm sorry, bana son na gan ki a irin wannan yanayin." Sakin fuska A'isha ta yi jin yanayin da ya yi magana ta ce. "Shikenan Yayana, ka san me?" Ya ce. "A'a." Ta ce. "Yau so nake ka mun waƙa mai daɗi." Da mamaki ya ce. "Waƙa kuma?" Ta ce. "Eh." Ya ce. "Ai ban iya ba." Cikin shagwab'a ta ce. "Ni dai kamun ko in yi kuka." Sauke numfashi ya yi ya ce. "Shikenan zan miki, amma ban iya na Hausa ba dan bana jin su." A'isha ta ce. "To ka mun ko ma wacce ce." Ɗan jim ya yi sannan ya yi gyaran murya ya fara rere mata waƙar cikin daddaɗar muryarsa. "_*I'm in love with my Bestie and I don't know what to do.......*_ _*Sometimes I dey feel say She dey feel the same way I do.........*_ _*But she day call me brother I no dey bab that thing........*_ _*'Cause sometimes we dey act like lovers Wey we dey do more things........*_ _*My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie Eh........*_ _*If you dey hear this song just know sey somebody fall for you.*_ _*My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie, My Bestie Eh.......*_ _*I know sey I no for catch feelings but ebe too risky to loose you to another one oo.........*_ _*So somebody tell me wetin man for do*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you.*_ _*So somebody tell me wetin man for do*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you......*_ _*Is it my brain or my body? May be my heart no well.*_ _*Aw Bestie eh wherever you dey I say you for hear me today I don't care if I shy for your face........*_ _*So Bestie, you no dey wonder why The girls girls no dey come my way no more times your jealousy sef dey blow ma mind*_ _*But Edey give me whim so I dawg them all*_ _*Now as you then your guy Shon I hope say we go fit to go the next level.........*_ _*'Cause the feeling dey grow strong make we look sharp before we start to blame devil........*_ _*Somebody tell me wetin man for do*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you......*_ _*Somebody tell me wetin man for do*_ _*(Somebody tell me wetin man for do)*_ _*Cause I no wan lose wetin I get plus you*_ _*(I'm in love with my Bestie yeah).*_" A'isha dake sauraren sa ta lumshe ido jin ya yi shiru ta ce. "Amma wannan waƙar nan ta yi daɗi sosai, zaka dinga yi mun kullum?" Umar dake kallon ta ko ƙifta ido ba ya yi ya ce. "Why not? Zan dinga yi miki mana." Ta buɗe idonta ta ce. "Na gode sosai, yanzu mu je mu ƙara shiga cikin ruwa, daga nan sai mu tafi gida." Umar ya ce. "Magriba fa ta kusa, kuma Mama ta ce kar mu yi dare." Cikin marairaicewa ta ce. "Muna shiga fa za mu fito, kawai ɗan wasa zan yi da ƙafata a ciki." Umar ya ce. "Shikenan mu je." Ya kama hannunta suka tashi suka ƙarasa bakin ruwan suka zauna, kamar ɗazu ita kaɗai ta saka ƙafarta shi bai saka ba. A hankali ya kai ragowar choculate ɗin da ta rage bakinta, matsar

Chapter 8 of 20