ta faru zan saɓar wa mutum fiye da tuanain shi ko waye." Mommy da take kallon shi tamkar idanunta za su faɗo ƙasa ta ce. "Alhaji ban fuskance ka ba, me kake nufi?"
"Komai ma." Ya ba ta amsa fuskarsa babu alamun wasa.
"Taɓɗijan!" Ta faɗa cikin tsantsar ɓacin rai da kololuwar takaici, lokaci ɗaya kuma ta saki wani murmushi, idanunta a kan Ummi ta ce. "Shikenan, Allah ya taya mu riƙo." Ta ƙarashe maganar tana miƙewa ta fice daga parlour'n.
Maganganun Abba sun saka A'isha a wani irin yanayi da ta kasa tantance na baƙin ciki ne ko akasin haka. Yau ta ƙara yarda mutum ba ya sanin yadda rayuwarsa za ta kaya sai ya ga yadda Ubangiji ya yi da shi, ba ta taɓa tunanin za ta yi rayuwa a wani gurin da ba garin da ta buɗe ido ta gan ta a ciki ba, amma ƙaddarar dake cikin rayuwarta ta ƙara jeho ta nan gidan, ba ta san kuma me zai faru a zamanta a cikinsa ba. Numfashi ta sauke a sanyaye ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ƙara arziƙi, ya sa aljanna ce makoma." Cikin kulawa Abba ya ce. "Amin Manana, Allah ya yi miki albarka ya ba ki lafiya." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Duban Maamah ya yi ya ce. "Kama hannunta ku koma part ɗin Mamanku, ta kwanta ta ƙara hutawa, na ga har yanzu jikin nata da saura."
"To Abba." Maamah ta faɗa tare da miƙewa. Khalifa ma tashi ya yi ya fita. Parlour'n ya rage daga Ummi sai Abba.
Ummi ta gyara zama tare da fuskantar Abba ta ce. "Al'amarin yarinyar nan ba ƙaramin ɗaure mini kai ya yi ba Abbansu, na kasa imagine yadda mutane biyu kacal za su yi rayuwa ba tare da wani jininsu ba, in ba dai a gidan marayu suka tashi ba." Abba ya ce. "Babu abin mamaki DR, hakan ya sha faruwa, kuma a yadda yarinyar ta ba mu labari ai kin ji mahaifiyar tata ta ce mata akwai dalilin da ya sa ta yi nesa da danginta, sanar mata ne Allah bai nufa ta yi ba har ta rasu." Ummi ta ce. "Haka ne Allah ya kyauta. Bari na je na shirya maka abin shan ruwa kar lokaci ya ƙure." Abba ya ce. "Toh shikenan, da daddare ma yi maganar diyyar matar, ki ba ni shawarar yadda kike ganin za a yi."
"Allah ya kai mu." Ummi ta faɗa tare da miƙewa ta fice.
Tunda Mommy ta koma part ɗinta ta kasa tsaye ta kasa zaune, ba ta son talaka da duk wani abu da ya shafe shi, ba ta san alaƙa da shi. Gani take tamkar talaucin zai goga mata. Ƴan aiki ma abin da ya sa take yin su don ta nuna isar ta ne da nuna ta kai matsayin yin su, amma ban da haka ba da ko gatekeeper ba za ta yi ba a rayuwarta. A haka Baby ta dawo ta same ta, ganin yanayin da take ciki sai ta ji babu daɗi a cikin ranta, da damuwa ta ce. "Mommy me ya faru? Ni fa ba na son na gan ki cikin ɓacin rai."
"Mahaifinki kuma burinsa kenan ya gan ni a cikin damuwa kodayaushe, duk abin da zai yi babu ruwansa da ɓacin raina a kai, in dai ƴar gold ɗinsa za ta yi farinciki shikenan, tunda Alhaji ya auri kinibabbiyar matar can na yi ban kwana da kwanciyar hankali da farinciki a gidan nan."
"Yanzu me ya faru?"
"Yarinyar da ya kaɗe ita ce wai za ta cigaba da rayuwa a gidan nan, don tsabar wani hali da son cusa mini baƙin ciki ba ma a matsayin ƴar aiki za ta zauna ba, wai a ƴa kamar ku. Kuma na san duk wannan abun tsinanniyar can ce ta kitsa masa shi." Ɓata fuska Baby ta yi ta ce. "Gaskiya Abba ya fiya janyo mana abin jin kunya da ƙasƙanci, yarinyar fa ƴar ƙauye ce, ranar suna hirar da Abba Abubukar na ji suna faɗa." Cikin ninkin ɓacin rai Mommy ta ce. "Wallahi matuƙar ina numfashi yarinyar nan ba za ta yi rayuwa a cikin gidan nan ba, gidan ɗana ne ai ba na Uban wani ba, mu zuba mu gani."
"Ya kamata dai ki ɗau mataki kam, kawai a wani kawo mana ƴar ƙauye gida mu rayu da ita, impossible wallahi, ko masu aikin gidan ba da daga ƙauye suke ba. Abba ma dai ya fiya kwashe-kwashe, daga accident ya haɗa ku sai ka ce za ka riƙe ta ban da ɗorawa kai." Ba tare da Mommy ta damu da kalaman da Baby take danganta Abba da su na rashin ɗa'a ba ta ce. "Ki bar ni da shi, wannan karon daidai nake da su dukansu."
Da daddare A'isha tana shan fruits ɗin da Ummi ta matsa mata ta sha a bedroom, Khalifa ya shigo ɗakin. Ba tare da ɗago kanta ba ta amsa masa sallamar da ya yi. Walking slowly ya ƙaraso ya tsugunna a gabanta tare da saka hannunsa yana karkaɗawa a daf da idonta, gani yake kamar ta faɗa ne kawai amma tana gani, har yanzu mamakin jin wannan Black beauty ɗin makauniya ce bai bar shi ba. Kamar ta san me yake mata ta tsaya cak da shan fruits ɗin, yadda ƙamshinsa ya cika mata hanci ya sa ta gane yana kusa da ita. Murmushi ya yi ganin yadda ta yi da fuska ya ɗan ja baya tare da ajiye mata ledar hannunsa.
"Tsohuwa ga Ice cream nan na kawo miki, Allah ya sa kin iya sha?" Ya yi maganar cikin barkwanci. Yanayin yadda ya yi maganar sai ya tuno mata da Umar har ta ji gabanta ya faɗi, ko dan shi ma wani lokacin yana ce mata tsohuwa ne idan ya so tsokanar ta? Ko kuma don yana kawo mata ice cream ne? Zoben da ya ba ta, ta murza a hankali tare da yin ɗan murmushi ta ce. "Na gode." Murmushinta ya masa kyau sosai, har ya ji dama ta ƙara yi. Lumshe idonsa ya yi ya buɗe ya ce. "Don't mind beauty, Allah ya sa kar ya kashe miki wannan kyawawan haƙoran." Murmushi ta ƙara yi a karo na biyu ba ta ce komai ba, wanda tun kafin rayuwarsa Inna rabon da ta yi, sai yau da Khalifa ya sa ta yi ba tare da shirya ba. Don har yanzu zafi da ciwon mutuwar Inna yana nan danƙare a cikin zuciyarta. Khalifa zai kuma magana Ummi ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo. Tsare shi ta yi da ido ta ce. "What are you doing here?"
"Abu na kawo mata." Ya yi maganar cikin sauri yana shafa kai.
"To an gode." Ummi ta faɗa tare da nuna masa ƙofa alamun ya tashi ya fita. Mayar da dubanta ta yi kan A'isha ta ce. "NANA, taso mu je ku gaisa da Gwaggo Maman Abba." Da yake ɗazu ta ce da Nana za suna kiran ta sai ta gane da ita Ummi take, hakan ya sa ta yunƙura ta miƙe cikin rashin ƙwarin jiki, Ummi ta kama hannunta suka fita.
Zuwan Mommy parlour'n ba jimawa su ma suka shiga, tunda A'isha ta zo gidan ba ta taɓa ganin fuskarta ba, saboda duk kwanakin da suka yi a asibiti ba ta je ta duba ta ba, ɗazu kuma a parlour'n Abba ba ta ga fuskarta ta ba. Ummi na ƙoƙarin zaunar da A'isha a kan carpet Mommy ta kalle ta, wata mummunar faɗuwar gaba da razani ne suka yi mata dirar mikiya a lokaci guda, sanadiyyar kallon farko da ta yi wa fuskar A'isha a rayuwarta.........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2️⃣6️⃣*
Duk yadda ta so ta ɓoye razanin da zuciyarta ta shiga hakan bai yiyu ba, sai da asirin hakan ya fallasu a kan fuskarta. Gwaggo dake amsa gaisuwarta ganin yanayinta ta ce. "Saratu!" Ɗan zabura Mommy ta yi tare da sauke numfashi, cikin ƙoƙarin ɓoye halin da take ciki ta ce. "Na'am Gwaggo."
"Ina hankalinki ya tafi Ina miki magana kin yi shiru?"
Yatsina fuska ta yi ta ce. "Na tafi wani ɗan tunani ne, zan yi abu yanzu na manta ban yi ba, bari na je na dawo." Taɓe baki Gwaggo ta yi ta ce. "Ai ke ba kya rabo da uzuri kodayaushe, sai ka ce mara gaskiya daga kin zauna burum kin tashi kamar wadda aka tsikara." Kicin-kicin Mommy ta yi da fuska ba ta ce komai ba ta tashi ta fita. Girgiza kai Abba ya yi ya miƙe ya nufi dinning area don cin abinci. Gwaggo na duban A'isha ta ce. "Wannan ce yarinyar? Allah Sarki, Allah ya ji ƙan mahaifiyarki ya ba ki haƙurin rashi, taso ki zauna nan kusa da ni kin ji." Ya Maamah ce ta kama hannunta ta zaunar da ita a kusa da Gwaggo, kanta a ƙasa ta ce. "Ina yini?" Gwaggo ta amsa cikin kulawa tana ƙare mata kallo.
"Tubarakallah ga ta kyakkyawa Masha Allah, Allah albarkaci rayuwarki ƴar nan, Addata mai sunan Yayata."
Ummi tana murmushi ta ce. "Mai sunanta ce kam, ga shi da alamu za ta yi haƙurin masu sunan." Ya Maamah ta ce. "Taɓ, ba su da wani haƙuri sunan tsofaffin, A'isha ta mana yawa gaskiya, duk an baibaye mu da su, kowa A'isha A'isha." Gwaggo ta ce. "Ja'ira sunanki ne dai."
Sun daɗe suna hira cikin raha da barkwanci, sai da A'isha ta fara gyangyaɗi sannan Gwaggo ta ce akai ta, ta kwanta.
Yadda Mommy ta ga rana haka ta ga dare, ta rasa me ya sa ganin A'isha ya firgita ta, ta ji wata muguwar tsanar ta lokaci ɗaya ta cika mata zuciya. Hakan ya sa ta ƙara ƙaimi akan ƙudirinta na korar A'isha daga gidan.
Washegari da safe bayan Gwaggo ta gama karyawa ta ce tafiya za ta yi. Abba ya ce. "Haba Gwaggo daga zuwa kamar wadda ake kora? Kin zo da daddare kuma yau da safe ki ce za ki koma?" Gwaggo ta ce. "Ƙyale ni na tafi, dama ba zama na zo yi ba, jaje na zo maka, Allah ya kiyaye ya tsare gaba, ya raba mu da sharrin ƙarfe. Ina ni ina zama cikin surukai, gara na yi tafiyata." Ummi ta ce. "Ki bari ko kwana ɗaya ki ƙara mana don Allah." Gwaggo ta ce, "Toh shikenan tunda kun matsa, kira mini mai sunan Adda mu yi hira, ta yi ta zama a ɗaki tana tunani ita kaɗai babu daɗi, goben idan Allah ya kai mu sai na tafi." Abba ya ce. "Allah ya kai mu, Dr mu je na sauke ki a school ɗin ko?" Ummi ta miƙe tare da faɗin. "Toh, Gwaggo bari mu je, sai na dawo, zan saka Maamah ta kawo miki Nanan."
"To shikenan, sai kun dawo, Allah ya kiyaye ya tsare."
Suka amsa da Amin tare da ficewa.
Har Rana A'isha suna tare da Gwaggo tana yi mata nasiha, ta ji daɗin kasancewa da Gwaggo sosai, don tamkar wadda ta daɗe da sanin ta haka ta nuna mata, babu ƙyara ko tsangwama sai zallar ƙauna. A'isha tana kan dardumar da ta yi Sallar Azhar bayan ta idar, Gwaggo ta tura mata abinci gabanta tana faɗin. "Ƙara ci sai ki sha magani ki kwanta." A hankali ta ce. "Na ƙoshi fa." Haɓa Gwaggo ta riƙe ta ce. "Abincin da kika ci nawa yake ƴar nan? Ki ƙara." Ba ta kuma magana ta lalubi plate ɗin ta fara cin abincin kamar ba ta so. Gwaggo ta ce. "Ko ke fa, abinci ai shi ne mutum, ke kuma daga gani za ki gaddamar cin shi, sai an dinga tsayawa a kanki, zan sanar da Zaran ta dinga tsaye a kanki idan za ki abinci." Ita dai A'isha ba ta ce komai ba ta cigaba da cin abincinta, tunda ta zo Gwaggo take ba ta abubuwan ciye-ciye, da ya Maamah ta kawo musu abinci ta zuba mata ta ci, yanzu ma ta ƙara mata. Kaɗan ta ci ta ture ta ce ta ƙoshi. Gwaggo ta ɓallo magungunanta ta ba ta. Tana gama sha ta kwanta bacci ya ɗauke ta.
Gyara gurin da suka ci abincin Gwaggo ta yi ta kwanta ita ma dan ta rintsa. Shigowar Mommy ya sa ta tashi zaune tare da amsa sallamar da ta yi.
"Sannu da hutawa Gwaggo." Ta faɗa lokacin da take zama a kan carpet. Gwaggo ta ce. "Yawwa, ki ƙaraso bakin gado ki zauna mana Hajiyar birni, ai ba girmanki ba ne zaman ƙasa." Duk da ta san Magana Gwaggo ta faɗa mata sai ta yi murmurshi, cikin son ganin plan ɗinta na farko da ta tsara ya yiyu ta ce. "Kina sama ai ba na zauna ba Gwaggo, nan ɗin ma ya yi, Ina yini? Ba mu Gaisa ba ma." Gwaggo ta ce. "Lafiya ƙalau." Gyara zama Mommy ta yi ta ce. "Gwaggo wata magana na zo miki da ita, wadda nake fatan ki fahimce ni da idon basira, shi Alhaji na yi masa bayani ya ƙi ganewa." Gwaggo ta ce. "Ina jin ki." Mommy ta ce. "Yawwa, akan yarinyar nan ne dama."
"Wacce yarinya?"
Zomo baki ta yi ta ce. "Wannan ta kwancen, ban san sunanta ba ne." Gwaggo ba ta kuma magana ba sai ido da ta zuba mata alamun tana sauraren ta. Hakan ya sa ta cigaba da magana da faɗin. "Akan riƙon ta da Alhaji ya ce zai yi ne, Gwaggo zamani fa ya canza, yanzu ba da ba ne mutane babu gaskiya a zuƙatansu, kar mu je mu ɗauko abin da zai zame mana alaƙaƙai a rayuwa, TSINTACCIYAR MAGE fa BA TA MAGE, ina tsoron kar mu je garin neman gira a rasa ido, saboda ɗan hakin da ka raina shi ke tsole maka ido." Gwaggo ta ce. "Ni duk wannan karin maganar da kika jero ban gane me kike nufi ba da inda kika dosa." Karyar da murya Mommy ta yi cikin ladabi ta ce. "Abin da nake nufi ki saka Alhaji ya mayar da Yarinyar nan inda ta fito su cigaba da riƙe ta. Idan ya so in ma ɗawainiyar ta zai ɗauka sai ya dinga kai kuɗi ana kula da ita, amma nan gidan ɗin ta bar shi kawai." Gwaggo ta ce "Mene hujjarki na son a mayar da ita?" Ƙara karyar da murya Mommy ta yi ta ce. "To Gwaggo mene amfanin riƙon nata? Yarinya ba ka san daga inda take ba kawai ka ce za ka riƙe ta, ba ka san mutum ce, aljana ce, mayya ce, wacce iri ce sai Allah." Shiru Gwaggo ta yi tana kallon Mommy kamar me nazari, a ranta kuwa mamakin halin Mommy da ba za ta taɓa canzawa take, ta yi zaton ta yi hankali ashe har yanzu ana jika. Numfashi ta sauke ta ce. "Maganar ki abar dubawa ce gaske, amma shi Sa'id ɗin kin masa duk wannan bayanin?" Cikin jin daɗin ganin Gwaggon ta karɓi maganarta ta ce. "Na masa, na nusar da shi iya yina amma ya toshe kunnuwansa ya ƙi saurare na, saboda ba maganar shafaffiya da mai ba ce, saboda duk abin da ta ce masa ba ya musu yake yi."
"A'a, kar kuma ki ce haka, ke ma kin san Sa'id tsayayyen mutum ne da ƙafafunsa, ba irin mutanen da ake juya su ba ne, duk abin da kika ga ya yi shi ya saka kansa."
"Uhm Gwaggo kenan, don ba a gidan kike ba ne shi ya sa, amma ƙiri-ƙiri Alhaji yake nuna mana banbanci, yau fa kina gani girkina ne amma shi ya kai ta gurin aiki, ga ƴaƴanta ga driver duk ba za su kai ta ba sai shi? Kuma ita ma ta iya tuƙin nan, idan mota ce ga su nan burjik a gidan sai ta zaɓi wadda za ta hau." Gwaggo ta ce. "To shi ne me don ya kai ta gurin aiki ranar girkinki? Ke sau nawa yake fita da ke ranar girkinta?" Ɓata fuska Mommy ta yi ta ce. "Shikenan Gwaggo a bar maganar, mu dawo kan wadda muke yi, don Allah ki yi masa magana ya mayar da yarinyar, ke kaɗai ce za ki faɗa masa ya bi." Taɓe baki Gwaggo ta yi ta ce. "Idan ya ƙi ba sai a bar shi ba tunda gidansa ne kuma shi ya ga zai iya."
"Gidansa kuma?" Mommy ta tambaya kamar Gwaggon ta yi ƙarya. Kama haɓa Gwaggo ta yi tana girgiza kai ta ce. "Eh gidansa na ce, ko ba nasa ba ne? Daga an yi magana ki dinga gidan ɗanki gidan ɗanki. Tunda ya ɗauka ya ba shi ba shikenan ba? Kuma ban da rashin kunya don SAFWAN ya ba wa mahaifinsa gida sai ya zama abin magana? Kafin ya girma ya samu arziƙin a gidan wa ya rayu? Wa ya biya masa kuɗin da ya yi karatu har wata ƙasar ya samu aikin da ya yi kuɗin? Duk ba mahaifin nasa ba ne? Kuma kar ki manta da ƙyar Sa'id ya yarda ya dawo gidan nan da zama, sai da na saka baki na ce ba a yi wa yara haka idan sun yi gwaninta, hakan yana kashe musu gwiwa, sannan fa ya amince. A yanzu Safwan ya ce ya bar masa gidansa yana da gidaje ba ma ɗaya ba da zai zauna. Amma kin bi kin ishi mutane da gida na ɗanki ne, kullum cikin yi wa kishiya gori kina cewa albarkacinki take ci tunda tana rayuwa a gidan ɗanki, daga an yi magana ki dinga ɗaga hanci ke a dole ga uwar attajiri. Ban da shirme ma irin naki ai wannan abin alfahari ne a gare ki ɗanki yana kyautata wa mahaifinsa, amma kin mayar da hakan abin gori da izgili."
"Ni fa ban ce komai ba Gwaggo."
"Za ma ki ce ne, ai ba yau na fara sanin halinki ba." Gwaggo ta faɗa a harzuƙe. Cike da haushin maganganun Gwaggo Mommy ta tashi ta fice daga ɗakin fuuu. Gwaggo ta raka ta da harara tana faɗin. "Ka ga mace har mace, wuya da kunne da hannu sun sha zinare kamar mai hankali, amma tunanin ta na marasa lissafi ne." Ta ja tsaki tare da faɗin. "Allah ya shirya."
A fusace Mommy ta ƙarasa part ɗinta, ɗaya daga cikin masu aikinta tana mopping kawai ta ji ta ɗauke ta da mari. Dafe kuncinta ta yi cikin gigita tare da tsugunnawa ƙasa ta shiga ba ta haƙuri, duk da ba ta san lefin da ta yi ba.
"Don matsiyacin Ubanki Uwar me kika tsaya yi har yanzu ba ki gama mopping ɗin ba? Me ya sa ku matsiyata komai za ku yi sai kun nuna ƙaranta da tsiya?"
Jikin yarinyar na rawa tana hawaye ta ce. "Ki yi haƙuri don Allah Hajiy....."
"Dalla rufe mini ruɓaɓɓen bakin nan kafin na fasa shi." Mommy ta katse ta cikin tsawa tare da hamɓarin ta. Saurin ja baya ta yi tana haɗe hannayenta alamun roƙo. Ƙwafa Mommy ta yi tare da faɗin. "Ban da ƙaddara me zai haɗa ka zama guri ɗaya da talaka? Shi da duk inda yake naso yake kamar funfuna." Ta ƙarashe maganar tare da hayewa upstairs. Ajiyar zuciya mai aikin ta sauke ta cigaba da abin da take cikin sauri, jikinta har rawa yake saboda tsoron kar ta sakko ta tarar da ita ta ƙara yi mata wata sabuwar tijarar.
Mommy na tsaye a bedroom ɗinta da waya kare kunnanta, after some seconds ta ce. "Kina ji na Kaltum, na je gurin tsohuwar can na faɗa mata kamar yadda kika ce, amma matar nan ta ƙi amincewa, sai ma wasu maganganu da ta bi ni da su, kin san shegiyar tsohuwa ce mai kankanbar tsiya. Da farko fa kamar ta amince, amma ina taɓo wadda suka fi k'auna ta canza akala" Daga ɗaya ɓangaren Kaltum ta ce. "Duk ki ƙyale ƴan abu ta kazar uba Saratu, ki ba ni 1 hour gani nan zuwa gidan, wallahi shirin da zan zo da shi sai yarinyar nan ta bar gidan, kin san halina idan na ce zan yi abu sai na yi." Ajiyar zuciya Mommy ta sauke, sanin hatsabibanci da ƙwarewa a shaiɗananci na ƙanwar tata ya sa ta yi amanna da zancenta, ta saka a ranta kawai matsalarta ta kau, indai barin A'isha daga gidan ne tamkar an yi an gama. Murmushi ta saki tare da faɗin. "Sai kin zo ɗin.".........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2️⃣7️⃣*
Har Ummi ta dawo Gwaggo ba ta daina mitar halin Mommy ba, bayan ta zauna ta dubi Gwaggo cikin mamaki tana ajiye jakarta ta ce. "Lafiya Gwaggo? Ke da wa?"
"NI da Saratu mana, wa zai taɓa ni a gidan nan ban da ita da ba ta girma."
Ummi ta sauke numfashi ba ta ce komai ba. Gwaggo ta ce. "Wai zuwa ta yi tana faɗa mini na cewa Alhaji Sa'id ya mayar da mai sunan Adda ƙauyen da take, wai kar a je watarana mun yi mata rana ta yi mana dare. Ko a kanta yarintar take oho?" Ya Maamah da ta shigo ɗakin ta tsinci zancen ta ce. "Mommy ko?" Gwaggo ta ce. "Ita fa." Girgiza kai Ya Maamah ta yi tana zama a kusa da Gwaggo ta ce. "Ban san me ya sa ba ta son wani ya raɓi gidan nan da sunan cin arziƙi ba, ita dai kullum kar talaka ya raɓe ta ya goga mata tsiya, zancen ta kenan." Tsaki Gwaggo ta yi ta ce. "Tsiya ta wuce tata? Ita ba ta duba abin faɗar da suke da shi sai na wani, tunda ubansu ya gudu ya bar su suna ƙanana wa ya ƙara jin labarin inda yake? Ya tafi ya bar uwarsu da wahala sai abincin siyarwa ta kama a bakin tasha don ta rufa musu asiri, su ma suka tashi a haka yan tuwo-tuwo, har daf da Sa'id zai aure ta ba daina fita tasha siyar da abinci ba. Amma yanzu saboda ɗanta ya yi arziƙi duk ta bi ta ishi mutane da jaraba." Ummi ta ce. "Ki yi haƙuri Gwaggo, ki bar maganar nan, kuma don Allah kar sanarwa da Abbansu ta zo miki da wannan batun, kin san shi da saurin hawa, yanzu sai ya je su yi ta rigima." Gwaggo ta ce. "Ni ban san irinki ba Zara'u, matar nan ba ta ƙaunar ki amma ke kodayaushe ba kya son ki ga ta ɓaci a idon mijinku." Ummi ta ce. "Ita ma Allah ya ganar da ita, ta gane abin da take yi ba daidai ba ne." Ya Maamah ta ce. "Hmm." Kawai.
Kaltum ba ta samu zuwa ba, ta taho a hanya ta samu accident, sai asibiti ta wuce. Hankali a tashe Mommy ta tafi asibitin da suke bayan ta kira ta sanar mata. Ta je ta tarar ba ta yi wani rauni sosai ba, a ranar aka yi mata treatment aka sallame ta.
Da daddare bayan Abba ya gama buɗa baki ya saka Ummi ta kawo masa A'isha part ɗinsa, bayan ta gaishe shi ya amsa cikin kulawa sannan ya gyara zama ya ce. "Mamana a ina kika tsaya da karatu ne?" A hankali ta ce. "J.s. 3." Gyaɗa kai ya yi ya ce. "A haka ba kya ganin kike zuwa makarantar ko?"
"Eh." Ta ba shi amsa cikin ladabi.
"Masha Allahu, idan Allah ya kai mu bayan bakwan mahaifiyarki za mu je asibiti a duba idon naki, idan Ubangiji ya ba mu sa'a kin warke sai ki cigaba da karatunki." Duk son ta da karatu da son ta warke daga makanta sai ta ji ba ta yi wani farinciki ba da kalaman Abba, saboda ɗaci da zafin da zuciyarta take ciki na rashin Inna, wanda kullum kewar ta da zafin mutuwar ta yake ƙaruwa a cikin ranta. Tana ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta cika mata ido ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ƙara girma ya ji ƙan mahaifa." Cikin jin daɗin Addu'ar ta ya ce. "Amin ya ALLAH, Allah ya miki albarka ya inganta rayuwarki. Zan saka a samo malamar Addini ta dinga yi miki ƙarin Ƙur'ani da littafai, saboda Ummin taku ba ta zama tana fita aiki, da sai ta dinga miki." Godiya ta ƙara yi masa cikin raunin murya, don sosai Alkhairin Abba ya karyar mata da zuciya, taso a ce Inna tana raye su ga wannan ranar tare, ranar da wani zai nuna musu ƙauna duk ya kasance mai arziƙi da wadata. Abba ya ce. "Babu komai,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 20