Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ni a haka ba ni na yi kai ba..." "Ke! Rufe mini baki, me ya fito dake ma daga ɗaki?" Inna ta katse ta cikin tsawa. Kuka ta fashe da shi ta ce. "Toh Inna kullum sai ta zo ta dinga zagin ki kuma ba ki yi mata komai ba?" Ta yi maganar cikin tsantsar takaici. "Ki cigaba da magana, tunda ban isa in ce ki yi shiru ki yi ba." Ƙwafa iya ta yi ta juya ta fita tana cigaba da masifa. Duban A'isha Inna ta yi ta ce. "Kar ki kuma yi mini haka A'isha, ko sa'ar ki ce Iyan da za ki dinga mayar mata da magana?" A raunane ta ce. "Ki yi haƙuri ba zan kuma ba." "Shikenan, bari na haɗa miki ruwa ki yi wanka, dama yanzu nake shirin tashin ki." Ba ta ce komai ba ta samu guri ta zauna, zuciyarta cike da damuwar rashin jin Umar da masifar gidansu da ba ta ƙarewa. A sanyaye ta ce. "Ina wayar nan Inna? Bai kira ba ko?" Girgiza kai Inna ta yi cikin tausayawa ta ce. "Bai kira ba, ki yi haƙuri ki cire damuwar hakan daga ranki, addu'a ya kamata ki yi masa Allah ya sa yana lafiya." "Insha Allahu, ya ce akwai karatun Alkur'ani a cikin wayar, ki ɗauko ki kunna mini." "Ai ban san ta yadda zan kamo ba, amma bari anjima idan zan je shago siyayya, sai mu biya gurin mai chaji ya kunna miki." Kwana Uku A'isha ta yi tana jinin sannan ya ɗauke, kamar yadda Inna ta sanar mata alamar da za ta ji ta san ya ɗauke, tana ji ta sanar da ita, duk da an koya musu yadda ake wankan tsarki amma sai da Inna ta ƙara yi mata bita domin ta yi shi yadda ya kamata. A ranar Inna ta ƙirga kuɗaɗen da Umar ya ba ta ranar da zai tafi, dubu ɗari da goma ne, ta zazzari wasu sun yi amfani da su saura dubu ɗari da biyu. Cikin farinciki ta haɗa musu kayansu don tafiya asibitin Kano gobe a duba A'isha, dama jira take ta samu tsarki sai su tafi. "Wai Haulatu ba za ki bar kukan nan ba? Na ce ki kwantar da hankalinki in dai Umar ne zai zo da ƙafafun shi har inda muke, ina nan ina shiri akan hakan." Haulatu dake gunjin kuka ta ce. "Yaushe zai zo to? Tunda ya tafi kike ce mini haka, kuma yau an fi sati da tafiyar tasa bai dawo ba." Cikin lallami Uwa ta ce. "Gaggawar me kike ne? Ki bi komai a sannu ze zo ne ai." Zunɓura baki ta yi ta ce. "Gaskiya ni dai na gaji da jira, so nake kawai na gan shi ko na ji muyar shi, ki je gurin Sarki ki karɓo mana lambarsa, na san ba zai rasa ba." Shiru Uwa ta yi cikin nazari sannan ta ce. "A baya na je na karɓo lambar Mahaifiyarsa, yanzu kuma na koma na karɓo tasa? Ba zai yiwu ba gaskiya, kin san Sarki da saurin gane abu, dole zai fuskanci akwai abin da muke ƙullawa, sai dai mu je gurin su waccar makauniyar yarinyar, na san ba za su rasa ba." "Kina ganin za su ba mu kuma Uwa?" "Na san me zan ce musu da dole za su ba mu, tashi ki ɗauko mini gelena mu je yanzu-yanzu, da zafi-zafi ake dukan ƙarfe." Cikin farinciki Haulatu ta share hawayen fuskarta tare da miƙewa. A'isha tana zaune a tsakar gida ta yi tagumi tana tunanin Umar su Haulatu suka kwaɗa sallama. A sanyaye ta amsa musu. Haulatu dake bin ta da Kallon tsana ta ce. "Asaben ba ta nan ne?" Cikin jin haushin yadda Haulatu ta gatsa mata sunan Inna A'isha ta ce. "Me ya faru?" Kafin Haulatu ta kuma magana Inna ta fito daga bayan gidan da ta zaga, da fara'a take duban Uwa. "Ku ne a tafe? Sannun ku da zuwa, ku zauna mana, kwa tsaya a tsaye." Ta yi maganar tana ware musu tabarmar da A'isha take zauna. Bayan sun zauna ta kawo musu ruwa Uwa ta dube ta, ta ce. "Asabe lambar waya muka zo karɓa a gurin ku." Cikin mamaki Inna ta ce. "Lambar wayar wa?" "Ta Umar baƙon yaron da ya zauna a gidanmu, don mun san ba za ku rasa ba." Dam! Gaban A'isha ya yanke ya faɗi, da sauri ta ɗago kanta amma ba ta ce komai ba. "Ayya, ai kuwa ba mu da lambar shi, don kwana uku mun je gurin mai chaji akan ya duba mana cikin wayar da ya bar mana ko akwai lambar waya amma ya ce ma babu, daga ta kamfanin layi sai ta layin da yake cikin waya....." "Sai dai in ba za ku ba mu ba ne kawai, amma mun san kuna da ita." Haulatu ta katse Inna cikin rashin ɗa'a." Inna ba ta ce komai ba sai kallon yarinyar da take cikin mamaki. Ɓata fuska Uwa ta yi ta ce. "To ai shi ya ce mu zo mu karɓa a gurin ku, saboda yana so su dinga waya da Haulatu, da zai tafi kuma ya manta yana sauri bai ba ta ba, abin da ya sa ma muka zo saboda kar ya gaji da jiran kiran mu, ga rashin jin muryata da ba ya yi zai iya jefa shi cikin wani hali, kin san ba ƙaramin ƙaunar ta yake ba." "To sai ku jira idan ya gaji da rashin jin murya tata ya dawo garin ya ba ku lambar da kansa, ina ganin hakan zai fi kyau ko?" Inna ta faɗi haka cikin haɗe rai. "Ko ba ki faɗa ba ma zai dawo, tunda ya gani yana so, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu, yarinya ƴar dangi da asali zai aura ba baƙin haure ba." Ɗan murmushi kawai Inna ta yi ba ta ce komai ba. Zuciya babu daɗi su Uwa suka zira takalmansu suka fice. A'isha da ta yi mutuwar zaune cikin bugawar zuciya tun lokacin da Uwa ta ambaci soyayya tsakanin Umar da Haulatu ta ji wasu hawaye masu ɗumi sun shiga rige-rigen zuba akan kuncinta, ba tare da ta san dalili ba. Ita tana nan tana zaman jiran kiran shi ashe ba ta ita yake ba, ko tantanma ba ta yi wannan dalilin ne ya hana shi kiran ta. "Kada ki bari wannan zancen ƙanzon kuregen ya yi tasiri a zuciyarki, na san yanzu ƙaramin tunanin ki ya ba ki abin da ba shi ba ne." Inna ta faɗi haka cikin tausasa harshe. Ajiyar zuciya ta sauke ba don kalaman Inna sun gamsar ita ba, duk da ƙarancin shekarun ta amma kalaman Uwa ba ƙaramin dukan zuciyarta suka yi ba, ba ta san mene ne so ba balle kuma kishi, abin da ta sani kawai ta damu da Umar, a halin yanzu babu abin da take buƙata sama da ta ƙara jin muryarsa, ta ji shi a kusa da ita yana yi mata hira, ta ji daddaɗan ƙamshinsa gami da dariyarsa mai sa ta ji sanyi a cikin ranta. Gocewa ta yi ta kwanta a gurin saboda jin kanta ya fara juya mata. Wani irin haushin Haulatu ta ji ya cika mata zuciya, tsaki ta ja a fili ba tare da ta san ta yi hakan ba. Inna dake lura da yanayin da take ciki ta miƙe don cigaba da haɗa musu kayansu, don gobe asubanci za su yi zuwa Kano. Kamar a mafarki wayar da Umar ya bar musu ta fara ringing, wata irin zabura A'isha ta yi ta fara laluben wayar dake gefen ta, jikinta har rawa yake saboda tsabar zaƙuwa da zumuɗin jin muryarsa da take........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣8️⃣* Ta yi nasarar lalubo wayar ta riƙe a hannunta, ajiyar zuciya ta saki mai ƙarfi tare da faɗin. "Inna ana kira ki zo ki ɗaga kar ta katse." Karɓar wayar Inna ta yi da niyyar ɗagawa, kafin ta ɗaga wayar ta saka Battery shutdown ta ɗauke. "Yawwa, ba ni in kin ɗaga." A'isha ta faɗi haka tana yawo da hannunta a cikin iska tamkar za ta cafki babu. A sanyaye Inna ta ce. "Ban kai ga ɗagawa ba ta mutu, ina ji chaji ne ya ƙare." A gigice A'isha ta ce. "Innalillahi! kunna dai mu gani ko batir ɗin ne ya goce." Inna ba ta yi musu ba ta kunna wayar, ƙara mutuwa wayar ta yi alamun dai babu chajin. Cikin damuwa na ganin samu da rashi A'isha ta miƙe tana faɗin. "Bari na kai ta wurin chaji." "Idan kina ganin hanya ba, mene haka ne wai A'isha kike yi? Duk kin bi kin gigice saboda an kira waya, shi ne ma ko ba shi ba ne wanda kike ta ƙulafucin kiran nasa oho? Kin ga A'isha ki raba kan ki da abin da ya fi ƙarfin ki, ki cire damuwar yaron nan daga ranki." Komawa ta yi ta zauna tare da saka kuka, cikin raunin murya ta ce. "Inna shi kaɗai ne fa wanda ya so mu a cikin garin nan bayan Innar Ma'u, shi ne abokin hirata, tunda ya tafi na koma halin zaman kaɗaici, idan na damu da kiran shi laifi ne? Idan kuma laifi ne ki yi haƙuri na daina." Wani irin sanyi jikin Inna ya yi, tausayin A'isha ya cika mata zuciya. Tabbas idan kana cikin hali na ƙunci da kaɗaici ka samu mai ɗebe maka kewa, lokaci ɗaya kuma ya tafi dole ka damu. Cikin kwantar da murya ta ce. "Ko kaɗan abin da kika yi ba laifi ba ne, kawai dai ina so ki rage damuwar da kika saka a ranki ne, kawo wayar yanzu na kai ta gurin caji, kar a kuma kira a ji a kashe." Share hawayen fuskarta ta yi ta miƙa mata wayar. Sai bayan isha'i Inna ta je karɓo wayar, ta cewa mai cajin ya kunna ya duba gurin kira ya kira mata lambar da aka kira. Bayan ya duba ya ce. "Babu lamba ko ɗaya a gurin kira fa." Da mamaki Inna ta ce. "An kira fa tana ta ringing, kafin a ɗaga ta mutu babu chaji." "Shi ya sa ba za a ga kiran ba, ai indai aka kira ba a ɗaga ba har waya ta mutu a haka to kiran ba zai nuna ba." "Yanzu kenan ba za a ga lambar da aka kira ba?" "Eh." Ya ba ta amsa a tak'aice. Zuciyar Inna babu daɗi ta karɓi wayar bayan ta biya shi kuɗin cajin ta koma gida. Ihu ne kawai A'isha ba ta yi ba da Inna ta sanar mata ba a ga lambar da aka kira ba, amma ta sha kuka mara sauti. Washegari tun asubar fari suka shirya don tafiya, sai dai a karo na biyu Inna ta nemi kuɗi sama da ƙasa ta rasa, ga shi ba ta ko ficika da ya yi saura, gabaɗaya kuɗaɗen hannunta ta haɗe guri ɗaya ta ajiye a tare. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Inna ko dai aljanu ne suka makarantar da ni? Ba sa son a mini magani shi ya sa duk sanda muka shirya da niyyar tafiya asibiti suke sace kuɗin." A'isha ta faɗi haka cikin matsanancin kuka. Kasa magana Inna ta yi, saboda abun ba ƙaramin dukan zuciyarta gami da ɗaure mata kai ya yi ba. Sunayen Allah kawai take ambata a cikin zuciyarta, wannan wanne irin bala'i ne da jarabta? Waye yake musu wannan satar rainin hankalin? Ta tambayi kanta tare da ɗaga hannu cikin hawaye ta ce. "Allah kai ne sarki, kai ka san me kake nufi da wannan yarinya, Allah duk wanda yake zaluntar mu Allah ka saka mana, ka toni asirin duk wanda yake daukar kuɗin nan, ka ba wa wannan baiwa taka lafiya." Kuka sosai A'isha ta wuni tana yi ranar, rarrashin ta Inna ta dinga yi tare da yi mata nasiha akan Ubangiji yana sane da su, su cigaba da addu'a kawai ita ce mafita. Rayuwa ta koma musu tamkar ta da kafin zuwan Umar, rayuwar rashi da ƙunci da fuskantar ƙyara da tsana daga mutanen gida da na gari. Kullum Inna a tafe take yawon nema musu abin da za su ci, rayuwa dai ta tsananta a gare su. Yau ta kama Monday, da safe suna cin gayen dafaffen dankalin hausa Inna ta dubi A'isha ta ce. "Ya kamata ki koma makaranta yau, kin ga ni yanzu ba zama nake ba, kuma duk inda na je hankalina ba a kwance yake ba, saboda ina fargabar kar wani abun ya same ki na bar ki ke kaɗai a gida, na dinga tafiya da ke kuma duk inda za ni ba mai yiyuwa ba ne, amma idan kina makarantar sai na fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali." A sanyaye ta ce. "Shikenan Inna zan koma yau insha Allahu, amma fa kullum na je sai Form master ɗinmu ya ce mini har yanzu lokacin da za a mini aikin idon bai yi ba?" "Ki shirya sai mu je tare na roƙi alfarmar su bar ki ki cigaba da zuwa kafin Allah ya hore a kai ki asibitin." "To, Allah ya sa su yarda." "Amin." Kamar yadda Inna ta faɗa tare suka je makarantar, ta samu malamin su A'isha ta yi masa bayanin matsalar da aka samu na sace musu kuɗi, cikin tausayawa ya ce babu komai ta cigaba da zuwa, abin da ya sa suka damu har suke magana saboda A'ishan tana da ƙoƙari, kuma rashin ganin da ba ta yi zai iya sawa ƙoƙarin nata ya ragu, tunda ba ta rubutu ba ta ganin abin da aka koya musu. Godiya Inna ta yi masa ta dawo gida. Tunda ta shigo layin su ta san da akwai wani baƙon al'amarin da yake faruwa a gidansu, ganin mutan gidan kusan dukan su a waje, ga wata ƙaramar Mota fake a ƙofar gidan yara sun yanyame ta. Ƙarasowar ta gurin ya yi daidai da boɗo murfin motar da Yawale yayan Malam ya yi ya fito, karaf suka haɗa ido da Inna, wanda hakan ya haifar mata da faɗuwar gaba. Haɗe fuska ta yi sosai ta wuce cikin gidan ba tare da ta bari sun haɗa ido da kowa a gurin ba, yayinda shi kuma ya bi ta da wani irin kallo, sauran matan gidan kuma suka raka ta da harara. Tana ji yo su zagayensu ana ta murnar dawowar su bayan sun shigo cikin gidan, anata ɓangaren kuma fargaba ce fal ranta, na rashin sanin da wanne kalar cin mutunci mazan gidan suka dawo musu da shi wannan karon ba. Har A'isha ta dawo ba ta fita ba, tana zaune tana ta tunane-tunane, Sallah ce kawai ke tashin ta. "Inna sannu da gida." A'isha ta faɗa bayan ta yi sallama tare da laluben gurin zama ta zauna. Numfashi Inna ta sauke tare da janye tagumin da ta yi ta ce. "Yawwa, har kun taso?" "Eh, me ya sa yau ba ki je kin ɗauko ni ba?" "Wallahi shaf na sha'afa ne A'isha, ban ma san lokacin ya yi ba, wa ya dawo da ke?" "Wani malaminmu ne, ya ga duk za a tafi a bar ni, shi ne ya ce bari ya rako ni." "To an gode Allah ya saka da Alkhairi, ki je ki cire uniform ɗin kar ya yi datti, kin san ba mu da omo." "To, ina abincina yunwa nake ji." Ta yi maganar cikin marairaice fuska. Cikin damuwa Inna ta ce "Ba mu da komai na ci a gidan nan, kuma ban san inda za mu samo ba, tun ɗazu nake tunani amma na rasa ina zan je." "Yau ma haka za mu kwana ba mu ci komai ba?" "To ya za mu yi? Sai dai mu yi ta addu'a Allah ya kawo mana mafita." Cikin karaya A'isha ta ce. "Inna me zai hana mu siyar da wayar da Yaya Umar ya ba mu, mu siya abinci da kuɗin, tunda babu abin da muke da ita, shi bai kira ba mu ma ba ma kiran kowa." Shiru Inna ta yi cikin nazari, a ranta tana mamakin kaifin basira da hankali da A'isha ta yi bayan tafiyar Umar, ta koma so silent, kamar ba ita ce wadda ba ta zama guri ɗaya ba a da, ta daina sangarta da abubuwan yara. Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Kin kawo shawara, amma kuma kar sai mun siyar ya yi ta neman mu ba ya samu." "Ba ma zai kira ba." Ta yi maganar cikin jin zafin rashin kiran nasa a cikin ranta, zuwa yanzu ta fitar da rai daga tsammanin kiran shi ko dawowar shi kamar yadda ya ce mata, ta ba wa zuciyarta haƙuri tare da ƙoƙarin cire shi daga cikinta, gami da ɗaukar ƙudirin mantawa da shi gabaɗaya a cikin rayuwarta, duk da ta san yiyuwar hakan na da matuƙar wahala, amma tana addu'a da fatan hakan ta kasance. Shawarar A'isha Inna ta bi, ba tare da jinkiri ba ta je ta siyar da wayar, bayan Magriba kuma ta tattara wasu daga cikin takalman A'isha masu tsada da agoguna da Umar ya siya mata ta kai gidan wata dillaliya dake nan ƙofar fadan wadda ke siyan tsoffi kaya ta sayar. Da wannan kuɗin ta yo musu sayayyar kayan abinci da sauran abubuwan amfani wanda za su musu kwanaki. Bayan kwana uku da daddare suna zaune a tsakar gida A'isha tana muraja'ar Alkur'ani, ɗaya daga cikin ƴanmatan gidan ta faɗo musu zagaye babu ko sallama, cikin fitsara ta dubi Inna ta ce. "Asabe ki zo ke da makauniyar ƴarki yanzu in ji babanmu." Kafin su ba ta amsa ta juya ta fita. Cikin tsantsar ɓaci rai A'isha ta ce. "Ba za mu je ɗin ba." Inna dake danne nata ɓacin ran ta ce. "Mu je mu ji neman me yake mana." "Ni dai gaskiya ba za ni ba, kin san fa Baba Yawale ba ya ƙaunar mu, in mun je ma na san zagi da cin mutuncin mu kawai zai yi kamar yadda ya saba." "Mu dai je A'isha, kin san na fi ki ƙin son haɗuwa da mutumin nan, amma saboda gudun magana da fitina mu je ɗin mu ji kiran me yake mana." "Amma Inna...." "Ki tashi mu tafi kawai, ba na son jan maganar nan taki." Ba ta kuma magana ba ta tashi kamar za ta yi kuka ta zira takalmi Inna ta kama hannunta suka tafi. Sashen matansa suka je, suka tarar da su zaune har da Iya. (Yawale Yayan Malam mijin Su Inna ne, Babansu ɗaya, ɗan Iya ne shi, duk mazan gidan a yanzu shi ne Babba.) Bayan sun yi sallama suka nemi guri suka zauna duk da ba wanda ya amsa musu sallamar, cikin ladabi Inna ta gaishe da Iya, ba tare da ta amsa ba ta fara magana cikin masifa. "Sannu Asabe, yanzu tsabar mugun hali da tsiya a ce ɗannan ya dawo har ya yi kwana uku amma ke da ƴarki ku kasa zuwa yi masa sannu da zuwa?" Shiru Inna ta yi ba ta ce komai ba, A'isha kuwa dama ɗauke kanta ta yi kamar ba ta gurin, sai turo baki gaba take." "Ai ban isa ba Iya, kina ganin yanzu ma sun shigo ko arziƙin gaisuwa ban samu daga gare su ba." Yawale ya faɗi haka yana jifan da Inna da mugun kallo. Wani kallo Inna ta watsa masa, amma still ba ta yi magana ba. Hangame baki Iya ta yi ta ce. "Iyee, samun guri, lallai Asabe, muna magana kin mana shiru, wato ga yan iska marasa aikin yi ko?" "Ai su ɗin ne." A'isha ta faɗa ƙasa-ƙasa. Hararar ta Inna ta yi don ta ji ta sarai, ba yabo ba fallasa ta ce. "To Iya ku yi haƙuri." Ƙwafa Iya ta yi tare da jan tsaki. Cikin gadara Yawale ya ce. "Na dawo na samu wani labari da sam bai yi daɗi ba Asabe, wato har yanzu ba za ku daina bin mutane kuna ci musu sassan jiki ba ko?" Kafin Inna ta yi magana A'isha ta fashe da kuka tare da faɗin. "Mu ba ma cin mutane, kuma......" Marin da Iya ta wanka mata ya sa ta yin shiru tare da dafe ƙuncinta, da sauri Inna ta kalli Iya, duk haƙuri da kawaicinta amma kana kallon fuskarta ka san yau an kai ta bango, don ɓacin rai ne kwance a cikinta. "Ko za ki rama mata ne da kike kallo na haka?" Iya ta faɗi haka kamar za ta kai mata marin ita ma. Ɗaya daga cikin matan Yawale ta ce. "Ai sai ta aikata, kin san su mayu ba kunya gare su ba, mu dai muna ta li'ilafi, aniyar mutum ta bi shi, kuma naman jikinmu ɗaci gare shi ba ciyuwa za mu yi ba, ato." Wani abu mai ɗaci ne ya zo ya tokare wuyan Inna, magana take so ta yi amma ɓacin rai ya hana ta, rungume A'isha dake kuka kawai ta yi tare da ɗan bubbuga bayanta alamar rarrashi. Cikin karkaɗa ƙafa da muzurai Yawale ya ce. "Abin da ya sa na aika a kira ku ba komai ba ne sai don na sanar da ku cewa na karɓi kuɗin baikon A'isha daga hannun Tsoho Makawo ɗazu da yamma, mun kuma tsayar da ranar ɗaurin Aure ni da shi sati biyu masu zuwa, ranar juma'a bayan an sakko daga masallaci za a ɗaura auren, don haka sai ku fara shiri." Ya yi maganar cikin sigar bayar da umarni.........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣9️⃣* Cikin rashin fahimta Inna ta ɗago kai ta dube shi ta ce. "Ban gane ba Yaya? Wacce A'ishan kake nufin ka karɓi kuɗin Auren ta?" "A'isha nawa muke da su a gidan nan da kike da iko da su wanda zan saka a kira ki don na sanar miki batun auren su? Wannan dai makauniyar dake gabanki ita nake nufi." "Tabɗijan! Tatsuniya ma kenan, to wallahi ba zan aurar da ƴata ba a yanzu, kuma babu wanda ya isa...." "Ke Asabe saurara!" Iya ta katse ta cikin tsawa sannan ta cigaba da magana. "Don ma kin samu Tsoho makahon ya taimake ku ya ce zai aure ta shi ne za ki yi wa mutane iskanci? Ƴar taki Shegiya mara asali za ki yi wa mutane firfita a kan ta? To wallahi wannan auren tamkar an yi an gama." Cikin bushewar zuci da tsantsar ɓacin rai Inna ta ce. "Ni kuma babu wanda ya isa ya aurar mini da ƴa ko wanene." Ta ƙarashe maganar tare da kama hannun A'isha suka miƙe, wadda kukan da take na marin da Iya ta yi mata ya sa ba ta fahimtar abun da suke cewa. Wata dariya Yawale ya yi ya ce. "Me za ki iya in an aurar miki da ƴar? Wa kike da shi? Ƙarƙari ki ce za ki kai ƙara gurin Sarki ko? To Sarkin baya nan ya tafi umra, sai mu ga wa zai tsaya miki." "Allah, shi ne zai mini katangar ƙarfe da duk wani mummunan ƙudirin ku a kan mu." Inna ta faɗa a fusace, yau kam sun kai ta bango, duk haƙuri da kawaicin da take musu a yanzu ta ji ba za ta iya ba. "Ni kuma in dai sunana Yawale sai an yi auren A'isha makauniya da Tsoho makaho." Sai a yanzu A'isha ta fahimci abin da ake magana akai, da wannan kalaman na Yawale. Wata irin bugawa zuciyarta ta yi, ƙara volume ɗin kukanta ta yi cikin rawar murya ta ce. "Inna me na ji Baba Yawale yana cewa? Ni za a yiwa Aure?" Hawayen fuskarta Inna ta fara share mata tare da faɗin. "Ki kwantar da hankali, in dai ina raye babu wanda ya isa ya miki Auran dole, tunda babu wanda ya haifar mini ke." Ba ta jira sauraren tijarar Iya da Matan Yawale suke taya ta ba, ta ja A'isha suka fice daga ɓangaren. "Inna don Allah mu bar garin nan, mu bar musu gidansu, kin san tunda Baba Yawale ya dawo rashin mutuncin da ake mana sai ya ƙaru." A'isha ta faɗi haka cikin kuka. Girgiza kai Inna ta yi cikin ɗacin rai ta ce. "Na fi ki gajiya da zaman gidan nan A'isha, dan dai babu yadda zan yi ne, kuma ina tunanin idan mun bar nan ba mu san ina za mu ba, ba mu san da waɗanda Allah zai ƙara haɗa mu ba." "Ƴan'uwanmu mana, ko da gaske ba mu da su?" "Muna da su, amma wani babban dalili ya sa ba zan koma gare su ba." "Wanne dalili ne? Don Allah Inna ko sau ɗaya ne ki kai ni na

Chapter 12 of 20