siyowa A'isha koko kafin ta fito daga wanka. Kafin ta kai ga miƙewa Ma'u ta shigo zagayen nasu bakinta ɗauke da sallama. Inna ta amsa mata, Ma'u ta ce. "Ina kwana Inna." Inna ta ce. "Lafiya ƙalau, mun tashi Ma'u ya Innar taki?" Ma'u ta ce. "Tana nan ƙalau." Tana ajiye kofin robar hannunta da wani ɗan k'ullin leda ta ce. "Gashi in ji Innata wai babu yawa." Inna ta kalli kayan sannan ta kalli Ma'u ta ce. "Kai, Ladidi bata gajiya da abun arzik'i dai, to ki ce mata na gode sosai kin ji Ma'u, Allah ya saka da Alkhairi." Ma'u tana murmushi ta ce. "Indo ce take wanka?" Inna ta ce. "Ita ce." Ma'u ta juya tana faɗin, "Bari na je nima na shirya kar ta riga ni." Inna ta ce. "To Ma'u ki ce mata na gode sosai." Ta ƙarashe zancen tare da sakin ajiyar zuciya tana yin hamdala ga Ubangiji a cikin zuciyarta. Ita kam babu abun da zata ce da Innar Ma'u akan irin taimakon su da take yi sai dai Allah ya saka mata da Alkhairin sa kawai. Kayan ta shiga dubawa ta ga kunun tsamiya ne a cikin kofin, k'ullin ledar kuma fanke ne. Dai-dai nan A'isha ta fito daga wankan, tana duban Inna ta ce. "Inna kamar murya Ma'u na ji da ina Wanka." Inna ta ce. "Ita ce ta shigo." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ba ta shirya ba ko? Salon ni na gama shirina ta makarar da Ni?" Inna ta ce. "Sai ta shirya ma kina nan kina shirita ke baki shirya ɗin ba, ga kunu da fanke nan Innarta ta aiko mana, idan kin biyawa ma'u makaranta sai ki yi mata godiya." A'isha ta yi murmushi ta ce. "Toh Inna, bari na wanke bakina na zo na ci."
Ƙarfe takwas da mintuna su A'isha suka fito daga ɓangaren su Ma'u dan tafiya makaranta. Suna sanye cikin uniform ɗinsu white and blue, wanda ya kasance fess da shi babu datti, duk da babu guga a jikinshi amma bai yamutse ba. Suna tafe A'isha tana ta yiwa Ma'u mitar ta makarar da su. Ma'u ta ce. "Kai Indo, yanzu ma fa idan mun je makarantar nan babu kowa, duk ba'a fara zuwa ba, kullum fa mu muke fara zuwa kin sani." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Wai bana ce miki bana son Indon nan da kike ce mun ba, ni sunana A'isha, ki daina ɓata mun suna, ehe." Ta ƙarashe zancen tana hararar Ma'u. Dariya Ma'u ta yi ta ce. "Ai na faɗa miki kema sai kin daina ce mun Ma'u kin koma ce mun Asma'u sannan nima zan daina ce miki Indo." A'isha ta ce. "To aike haka kowa yake ce miki dama, ni kuwa ke kaɗai kike ce mun Indo, wai Indo? Sai ka ce wata tsohuwa." Dariya kawai Ma'u ta yi bata ce komai ba. Dai_dai nan suka ƙaraso ƙofar gidan Mai_ gari, Ɗan_juma dake tsaye a cikin soron gidan da waya a hannunsa yana latsawa ya fito ya sha gaban su, dama ita yake jira ta zo wucewa. Wani uban tsaki A'isha ta ja ta kama hannun Ma'u da nufin su sauya hanya amma sai ta ji an fizgo hijabinta. Ta juyo a fusace tana ƙoƙarin k'wace hijabinta daga hannun Ɗan_juma ta ce. "Me ne haka?" Ɗan_juma ya ce. "Na lura yarinyar nan kullum ƙara raina ni kike yi saboda na ce ina son ki ko?" Cikin tsiwa A'isha ta ce. "An raina ka ɗin, kuma ni ka sakar mun Hijab ɗina, dan ni ba ƴar iska ba ce da Namiji zai riƙe mun Hijabi." Ɗan_juma yana bin ta da wani shegen kallo ya ce, "Hmm yaro man kaza." Sannan ya yi wani murmushi ya sakar mata Hijabin. Da sauri Ma'u ta ja ta suka yi gaba, A'isha ta juyo ta ce masa. "Kuma Allah ya isa na." Sannan ta juya suka cigaba da tafiya. Murmushi Ɗan_juma ya ƙara saki yana bin bayan ta da kallo tare da lasar leb'ensa na ƙasa, zuciyarsa na ƙara tunzura shi akan mummunan k'udirinsa akan A'isha. A fili ya ce. "Ki jirayi ranar da zan fanshe dukkan wulaqanci da tsiwar da kike mun A'isha, Ni Ɗan_juma kaf cikin garin nan babu wanda ya isa ya taba ni ya zauna lafiya, balle kuma ke mara asali da galihu, wadda ko me na yi miki baki da wanda zai ɗaukar miki matakin komai." Yana gama faɗin haka ya juya ya shige cikin gida still fuskarsa ɗauke da murmurshin da shi kaɗai ya san ma'anarsa...........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*0️⃣3️⃣*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
.........Bayan Sun ɗan yi nesa da gidan Mai_gari Ma'u ta dubi A'isha wadda ke ta huci ta ce. "Kin ga A'isha ki daina yiwa Ɗan_Juma tsiwa, ni ina tsoron kar wataran ya yi miki shegen duka, kin san halinsa fa." Tsaki A'isha ta yi ta ce. "Tab'dijan, sai ka ce wata ƴarsa zan zauna ya dake Ni, wallahi ya yi kaɗan." Ma'u bata kuma magana ba har suka ƙarasa makarantar. Kamar yadda Ma'u ta faɗa babu wanda ya zo sai mai_gadi wanda shine yake buɗe Makarantar, su ne na farkon zuwa. Bayan sun shiga ajinsu suka ajiye jakunku nansu suka shiga sharar ajin, dama kullum su suke yin sharar. Sai da ƙarfe tara ta wuce sannan sauran yara suka fa zuzzuwa da Malaman Makarantar. A'isha suna zaune akan desk ita da Ma'u wata yarinya wadda baza ta wuce sa'ar su ba ta zo ta tsaya a gaban A'isha, cikin tsiwa da neman faɗa ta ce. "Matsa zan wuce in zauna." A'isha ta kalli Ma'u dake jikin bango sannan ta kalli yarinyar ta ce. "Ina kuma zaki shige Kandala? Bayan ga guri a nan?" Ta ƙarashe zancen tana nuna mata gefenta inda babu kowa. Kandala ta ce. "Inda kike zaki matsa mun in zauna mana." Kallon sama da ƙasa A'isha ta yi mata ta ce. "Sannu Inna." Daga haka ta ɗauke kanta bata kuma magana ba, dan ba ta san su yi faɗa, saboda kullum kafin ta fito daga gida sai Inna ta gargad'e ta akan ko an tsokane ta kar ta biyewa kowa balle su yi faɗa. Kandala da dama neman tsokana ne ya kawo ta, ta ce. "Kar ki matsa ɗin, banza kawai, shegiya Mayya." Da sauri Ma'u ta dube ta, ta ce. "Haba Kandala mene ne haka?" Hararar Ma'u Kandala ta yi ta ce. "Malama ban saka baki da ke ba, ke dama ai sun riga sun gama cinye kurwarku ke da Innarki, shi yasa komai ta yi ba kya ganin lefin ta." Miƙewa tsaye A'isha ta yi ta ce. "Kar ki ƙara ce mun Mayya ke Kandala." Cikin ɗaga murya Kandala ta ce. "An faɗa ɗin Mayya ce ke mara Uba, Shegiya sai me?" Sauran ƴan aji suka tattaso suka ƙaraso gurin dan bawa idonsu abinci, Kandala ta dube su ta ce a bugawa A'isha gangar Shegiya Mayya. Nan fa yara suka fara buga desk da jarkokin ruwansu suna yiwa A'isha ihun Mayya da SHEGIYA cikin waƙa. Komawa A'isha ta yi ta zauna tare da toshe kunnuwanta da hannayenta saboda yanda ihun da suke yi yake shigar mata har cikin kai. Wasu Hawaye masu zafi suka fara zuba akan kuncinta, kusan kullum idan ta zo makarantar sai an yi mata wannan ihun aka, duk da yanda ko an tsokane ta bata kula mutum saboda gudun hakan, amma ba sa ƙyale ta Yaran. Cikin tausayawa Ma'u ta rungumo ta jikinta tana bata haquri. Shigowar wani Malami ce tasa yaran suka yi tsit bayan ya daka musu tsawa tare da buga ƙofa. A fusace ya ce. "Kowa ya nemi guri ya zauna." Bayan sun zauna ya dube su ya ce. "Ihun Uban me kuke mana a aji? Duk kun cika mana makaranta da hayaniyarku." Ma'u ce ta ce. "Malam Kandala ce ta ce su yiwa A'isha ihun Mayya da SHEGIYA." Sai a lokacin Malam Buba ya dubi A'isha wadda ke kuka sosai ya ce. "Ina Kandalar take? Ta miƙe tsaye." Kandala ta miƙe tana cuccuna baki gaba kamar bakin tulu, Malam ya ce ta fito gaban allo ta yi kneel down ta rufe ido, sauran Yaran ma ya saka su yin haka amma su kowa a inda yake zaune, ban da A'isha da Ma'u. Sannan ya rarrashi A'isha ya bata baki ta yi shiru ta bar kukan da take yi. Gaban allo ya koma ya ce. "Dama abun da ya kawo ni na zo ne in sanar muku za'a ɗauki mutum uku masu ƙoƙari a cikin ajin nan wanda za su zana common entrance tare da ƴan aji Shida." Kasancewar su A'isha a Primary 5 suke. Nan fa yara suka fara murna kowa yana fatan a ɗauke shi. Malam Buba ya karanto sunan Yara Ukun ciki har da A'isha. Wannan abun ya yayewa A'isha damuwar ihun da ƴan ajin suka yi mata, sai su gata suna ta tsalle da murna ita da Ma'u.
Bayan an tashi daga makaranta sun koma gida A'isha ta tarar Inna bata nan, ko uniform bata cire ba ta fara duban abinci ko Inna ta girka ta ajiye mata amma bata ga komai ba. Zama ta yi a tsakar gida tana jiran dawowar Inna, sai dai har Ma'u ta biyo mata zuwa gidan Malama karatu Inna bata dawo ba, haka ta tashi ta shiga ɗaki ta canza kaya suka tafi karatun yunwa na ƙwaƙular hanjin cikinta. Sai Yamma suka dawo, zuwa lokacin yunwa ta fara galabaitar da A'isha. Inna tana wankin kayan sakawarsu A'isha ta shigo da sallama can ƙasan mak'oshi. Inna ta amsa mata tare da bin ta da kallo. A'isha ta turo baki ta ce. "Inna Ina kika je? Na dawo na tarar ba kya nan." Inna ta ce. "Sabon Gari na je." Ba ta jira cewar A'ishan ba ta tsame hannunta daga cikin ruwan wankin ta shiga ɗaki ta ɗaukowa A'isha k'uli_k'uli mai gishiri da awara ta bata. Da murna A'isha ta karɓa ta ce. "Inna yau yunwa ta kusa kashe ni fa." Inna ta ce. "Tunda bata kashe kin ba sai ki yiwa Allah godiya." Bayan A'isha ta gama cin awarar da k'uli_k'ulin ta sha ruwa ta dubi Inna ta ce. "Inna Ina son in tambaye ki wani abu." Inna ta ce. "Ina jin ki." A'isha ta ce. "Dan Allah Inna da gaske Baba Malam ba shine Babana ba? Kuma ba mu da asali?" Haɗe rai Inna ta yi ta ce. "Ba na ce kar ki ƙara mun wannan tambayar ba A'isha?" Cikin raunin murya A'isha ta ce. "Inna ki yi haquri kin faɗa mun, amma Inna ke baki da qani ne ko Yaya ko k'anwa kamar Innar Ma'u? Kin ga ita suna zuwa Kano gurin ƙaninta, kuma suna zuwa Sanda gidan Inna larai k'anwarta, amma mu ba ma zuwa gidan kowa." A'isha ta ƙarasa Maganar cikin raunin murya. Shiru Inna ta yi gabanta na fad'uwa, a ranta tana faɗin. Tun yanzu A'isha ta fara tambayar ta wani nasu? ina ga ta ƙara girma da wayo ta san me duniya take ciki? Tabbas dole ta yiwa tufkar hanci tun yanzu, ta kuma san me zata faɗawa A'isha wanda zai kwantar mata da hankali. Ganin Inna ta yi shiru cikin raunin murya A'isha ta kuma cewa. "Dan Allah Inna mu ma muna zuwa gurin ƴan'uwanmu a daina ce mana marasa asali." Sosai tausayin A'isha ya cika zuciyar Inna, ta san dole abun ya dame ta duk da kasancewarta yarinya, ko dan yanda mutanen gari suke muzanta_ta akodayaushe. Tasowa Inna ta yi ta dawo gaban A'isha cikin sanyin murya ta ce. "A'isha! INSHA ALLAHU watarana zamu je gurin ƴan'uwanmu mu ma kamar kowa, kin ji?" Hawaye A'isha ta fara ta ce. "Yaushe Inna? Mu je gobe mana." Inna ta girgiza kanta ta ce. "Inda suke ne da nisa A'isha, sai na tara mana kuɗin Mota, Nima ina son mu je ɗin, amma mun kusa zuwa insha Allahu." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Inna ta ce. "Jiya da kika je ɗiban ruwa me aka yi miki kika dawo da kuka?" A'isha ta ce. "Ce mun aka yi MAYYA SHEGIYA a gurin, yau ma a makaranta an mun ihun haka a aji." Kama hannunta Inna ta yi cikin lallami ta ce. "Ki yi haquri A'isha, duk abun nan da ake yi miki ni na jawo miki, amma insha Allahu komai zai wuce, duk wannan abubuwan da ake yi mana sai sun zamo tarihi, watarana komai zai wuce da yardar Allah, KOMAI NISAN DARE gari zai waye A'isha, ki ƙara hakuri." A'isha ta ce. "Shikenan Innata." Inna ta ce. "Yawwa A'ishana, share hawayen naki ki tashi ki dauraye mana kwanikan can kafin a kira Sallah." A'isha ta miƙe ta ce. "Toh." Inna ta bi ta da kallon tausayi kafin ta miƙe ita ma.
Daren Yau Inna bata rintsa ba, tunanika kala_kala ta kwana tana yi. Na farko tana tunanin yanda rayuwarsu zata kasance nan gaba a halin da suke ciki, na ƙyara da nuna musu tsana ƙarara da mutanen gari ke yi. Na biyu kuma halin babu da suke ciki, dan yau ma gidan wata mata da suke mutunci ta je a can unguwar Sabon gari ta taya ta aikin k'uli_k'ulin da Matar take yi na siyarwa, shine ta samu matar ta bata k'ulin da ɗan Kuɗi wanda a cikinsa ta siyowa A'isha awarar da ta bata ta ci, ita kuma a gidan matar ta ci abinci. Washegari da zazzaɓi da ciwon kai A'isha ta tashi, sai Inna ta danganta hakan da kukan data ce mata ta yi ne a makaranta da kuma zaman da ta yi da yunwa bata ci abinci ba Jiya.
Ƙarfe Bakwai na safe Inna ta fita ta siyo mata koko da k'osai ta dawo. Tabarma ta shimfid'a a tsakar gida ta ɗauko A'isha ta kwantar da ita a kai. Inna tana taɓa goshinta ta ce. "Jikinki ya yi zafi sosai A'isha, tashi ki sha kokon nan ko yaya ne, anjima sai in siyo miki magani ki sha." Girgiza kai A'isha ta yi tare da lumshe idanunta. Inna ta ce. "Daurewa zaki yi ki ɗan kurb'a, ai ba zai yiyu ki zauna baki saka komai a cikinki ba." A'isha tana taune lips ɗinta ta miƙe daƙyar ta zauna ta jingina bayanta da jikin bango. Inna tana zuba mata sugar a cikin kokon ta ce, "Sannu, Allah ya sauwak'e." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. A baki Inna ta bata kokon ta yi kurb'a ɗaya ta kau da kai, Inna ta ce ta daure dai ta ƙara sha. Tana ƙara kurb'a sai kakarin amai, kafin ta yunk'ura ta miƙe har ta fara aman a gurin. Inna ta riƙe ta tana jera mata sannu cikin tausayawa. Bayan ta gama Inna ta dauraye mata fuska da baki ta cire mata rigar jikinta da ta ɓaci da amai. Cikin Muryar marasa lafiya A'isha ta ce. "Inna ki mayar da ni ɗaki ki lullub'e ni sanyi nake ji sosai." Inna ta ce. "Toh." Sannan ta kama ta, ta kai ta ɗakin ta kwantar da ita, cikin ikon Allah sai bacci ya ɗauke ta. Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta fito tsakar gida ta fara ɗan ayyukan gida, jikinta duk ya yi sanyi da yanda ta ga jikin A'ishan. Da Ma'u ta biyo mata makaranta Inna ta sanar da Ma'un baza ta samu damar zuwa ba, bata jin daɗi, Ma'u ta shiga ɗaki ta duba ta sannan ta yi mata addu'ar samun sauƙi cikin tausayawa.
Wajen ƙarfe goma na safe har lokacin A'isha tana ɗaki tana bacci, Inna kuma tana tsakar gida tana karyawa aka yi sallama a zagayen nasu. Inna ta amsa tare da duban Matar da ta shigo, duk da ba ta taɓa san ta ba amma ta tarb'e ta cikin fara'a tare da bata gurin zama. Bayan sun gaisa Matar ta ce. "Na san baki gane ni ba ko?" Inna ta ce. "Gaskiya, dan zan iya cewa ma ban taɓa ganin fuskarki ba." Matar ta yi murmushi ta ce. "Haka ne, Nima ban taɓa ganinki ba sai yau, kuma na zo gurinki ne da wata samuwa da nake fatan zaki karɓe ta hannu bibbiyu." Inna ta ce. "Samuwa kuma? Wacce iri?" Matar ta gyara zama ta ce. "Da farko dai Sunana Hajiya Kareema, Ni mazauniyar ƙasar Saudiyya ce a can nake kasuwanci na." Inna ta jinjina kai tana ƙara bin matar da kallo, a ranta tana mamakin dalilin zuwanta gurin ta. Matar ta cigaba da magana da faɗin. "Shekaran jiya na zo nan gurin Ramatu abokiyar zamanki, sai yarinyarki A'isha ta shiga zagayen su, anan na gan ta, dalilin zuwana ma gurinki a yanzu saboda ita ne." Inna ta ce. "To, Allah yasa ba wani abun ta yi miki ba?" Hajiya kareema ta girgiza kai tana bin zagayen su Inna da kallo sannan ta ce. "Na zo ne in tallata miki wata hanya ta samuwa kamar yadda na faɗa miki tun farko, duba da yanayin talauci da k'uncin rayuwa da kuke ciki na ji ina son in taimake ku." Inna ta ce. "Taimako kuma wanne iri?" Hajiya Kareema ta tauna cingum ƙas_ƙas sannan ta ce. "Yarinyarki A'isha zaki bani in tafi da ita Saudiyya komawar nan da zan yi ta nemar muku kuɗi a can, cikin ƙanƙani lokaci zaki ga kakarku ta yanke saƙa kun yi bankwana da talauci, zaku samu kuɗi sosai wanda zai isa ku bar wannan ƙauyen ku fita duk inda kuke so a cikin birni ku gina gidanku na zamani, ku ji daɗin rayuwarku. Musamman ma da ya kasance A'isha kyakkyawa ce gata da ɗan dumurmur ɗin jiki za'a amfana da ita sosai" Ta ƙarashe zancen tare da sakin wani irin murmushi............✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*0️⃣4️⃣*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
..........Baki buɗe Inna ta shiga bin Hajiya Kareema da wani irin kallo mai kama da na baki da hankali, kafin ta daure zuciyarta ta ce. "Ban gane ba Hajiya? Ƴar tawa guda ɗaya tal zan baki ki tafi ita da Saudiyya? Ban san ki ba ban taɓa ganin ki ba, ban kuma san daga inda kike ba." Hajiya Kareema ta yi murmushi ta ce. "Ai ba haka sakaka zaki bani ita na tafi da ita ba, komai a rubuce za'a yi shi da shaidu da saka hannun hukuma, kuma ƴaƴana suna cikin garin nan da zama zan kai ki har inda suke ki gani, balle ki ce zan gudar miki da ƴa ne." Inna ta ɓata fuska ta ce. "To ita A'isha ƴar ƙanƙanuwa da ita neman kuɗin me zata iya yi?" Hajiya Kareema ta ce. "Sana'a mana, ga sana'o'i nan kala_kala a ƙasar Saudiyya na samun kuɗi." Murmurshin takaici Inna ta yi ta ce. "Amma a sana'ar ne na ji kin yi maganar ko dan kyan A'isha za'a amfana da ita, wacce irin sana'a ce da take da haɗi da kyau ko wani yanayin halittar jikin Mutum?" Hajiya Kareema ta ɗan taɓe baki ta ce. "Aa, ai a komai na duniya an fi son abu mai kyau Ko? Ko abu take saidawa sai a siyi nata ai kafin a siyi na munana, ni haka nake nufi ba wani abun ba." Murmurshin takaici Inna ta ƙara yi ta ce. "Haba Hajiya, ba fa Yarinyar goye ba ce ni ko kuma wadda aka haifa yau da ban san takan duniya ba, karki ganni haka a ƙauye ki yi tunanin ban san me nake yi ba, na san sarai me kuke yi a Saudiyyan idan kun je." Hajiya Kareema ta ɓata fuska ta ce. "A'a Tsohuwa karki yi mun wata fassarar daban, samuwa ce fa kawai na zo miki da ita." Inna ta haɗe rai sosai ta ce. "To na gode, amma ba zan iya ba, ƴar tawa guda ɗaya tal a duniya zan tura ta yawon aikatau wata ƙasar? To bazan iya ba gaskiya." Hajiya Kareema tana yi mata wani shegen kallo ta ce. "Taimakon ki na zo yi fa ba wani abu ba, in kuma fitar dake daga wannan k'angin talaucin da kike ciki." Inna ta ce. "Allah ne zai fitar da ni, kuma Ni ban ce ina neman taimakon kowa ba bayan na Ubangiji na." Hajiya Kareema ta miƙe ta saɓi Jakarta ta ce. "Ai dama an ce kare bai gaji arzik'i ba, sai da aka mun bayanin halinki amma na dage sai na zo, ni uwar son gwaninta." Inna ba ta kuma yi mata magana ba. Ta zira takalminta sannan ta ɗauko wani ɗan kati daga cikin Jakarta ta ajiye a gaban Inna ta ce. "Gashi nan, idan kin yi shawara daga baya in kin ga kina da interest akan abun da na zo miki da shi sai ki neme ni, ga Numbern wayana nan a jikin katin, kya kira ni." Daga haka ta juya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 20