Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta kama hannun A'isha zuwa part ɗin Abba. Yana zaune shi kaɗai a parlonsa yana karatun Alkur'ani suka shiga. Bayan ya kai aya ya amsa musu sallamar da suka yi. Ummi ta ce. "Barka da dare Abba." Ya ce. "Yawwa DR." Cikin ladabi ita ma A'isha ta gaishe shi, ya amsa cikin kulawa da fara'a. Bayan Ummi ta faɗa masa yadda suka yi a asibiti ya ce. "Masha Allahu, Ubangiji ya sa a yi aikin a sa'a, gobe idan Allah ya kai mu sai mu je a biya kuɗin." Ummi ta ce. "Allah ya nufa ya saka da Alkhairi." Abba ya amsa da "Amin." A'isha da ta rasa kalmomin da za ta yi amfani da su ta gode wa waɗannan mutanen masu karamci, mutunci da tausayi ta ce. "Na gode sosai Abba, Allah ya ji ƙan mahaifa ya saka da gidan Aljanna." Cikin murmushi ya ce. "Amin amin daughter, Allah ya yi miki albarka ya ba ki lafiya." Suka amsa da Amin gabaɗaya. Gyara zama Ummi ta yi ta ce. "Ɗazu principle ɗin su Muneefah ta kira ni wai ba ta da lafiya a je ɗauko ta." Abba ya ce. "Subhanallahi, Allah ya kai mu gobe sai Khalifa ya je ya ɗauko ta, Allah ya sa jikin ba tsanani ya yi ba sosai." Ummi ta ce. "Muneefah ce fa, za ta iya kwanciya ciwon ƙarya ma, ka san ta tsani makarantar nan kamar mutuwarta." Abba ya ce. "A'a fa, autata ba za ta yi haka ba." Ummi ta ce. "Toh shikenan Allah ya kai mu goben ka gani." Kafin Abba ya ƙara magana Safwan da Salma sun shigo, wadda ke tafiya cikin taƙama tamkar basarakiya. Kan dole ba don son ranta ba ta zauna a ƙasa. Ba yabo ba fallasa ta gaishe da Abba, Ummi kuwa kamar an mata dole. Abba yana duban Safwan ya ce. "Gobe za ka je Gomben ko?" Gyaɗa masa kai ya yi. Ummi ta yi murmurshi ta ce. "Za a je gaishe da Gwaggo kenan?" Ya ce. "Eh, tunda ta ce sai dai ni na je ita ba za ta zo ta mini sannu da zuwa ba." Ummi ta ce. "Gwaggo kenan, idan ka je ka gaishe ta da kyau." Ya ce "Za ta ji in sha Allah." Tunda Salma ta zauna idanunta na kan A'isha, ita ta manta da Yarinyar ma gabaɗaya sai yau da ta gan ta. Bayan sun fita ta biya part ɗin Mommy take tambayar ta wacece A'isha a gidan? Mommy ta ce. "Au Khaltum ba ta faɗa miki ba? Na ɗauka da kika je ai ta miki bayani." Salma ta ce. "ko ɗaya, ai ba mu taɓa zancen yarinyar da ita ba." Taɓe baki Mommy ta yi ta ce. "Wai daga Alhaji ya kaɗe su ita da uwarta uwar ta mutu shikenan ya ce zai riƙe ta saboda rashin sanin ciwon kai, mutum ce aljana ce mayya ce sai Allah." Salma ta ce. "Ban gane ba, wai yana nufin shikenan a gidan za ta cigaba da rayuwa?" Mommy ta ce. "Eh mana, na nusar da shi illar hakan amma ya ƙi ganewa, wai shi Sarkin taimako." Cikin haƙiƙancewa Salma ta ce. "Idan taimakon ta zai yi ya kai ta orphanage mana ko police station a yi cikiyar iyayenta idan ba ta san inda suke ba, ni fa farko da na gan ta I thought ƴar'uwar waccan matar ce, ashe ma tsinto aka yi daga sama a titi. To gaskiya ba zai yiyu ba, babu yadda za a yi mu yi rayuwa da wata bare a gida ɗaya, dole a san abin yi yarinyar nan ta bar gidan nan." Mommy ta ce. "Ƙoƙarin da nake ta yi kenan." Salma ta ce. "Better, don ba zan yarda Mijina yana ganin wata mace ba bayan siblings ɗinsa ba." Mommy ta bi ta da kallo kawai ba ta ce komai ba. Washegari da safe A'isha na zaune ita kaɗai a parlour tana karyawa Khalifa ya shigo. Bayan ya yi sallama ya zauna a kusa da ita. Cikin sanyinta ta ce. "Ina kwana?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, 2 days ba mu haɗu ba ko cikiya ta ba kya yi ko?" Ta ce. "Na tambayi Ummi ta ce kana gurin aiki." Cikin murmushi ya ce. "Dagaske?" Ta gyaɗa masa kai. Ya ce. "Ya jikin naki? I hope dai yanzu kin warware?" Ta ce. "Eh Alhamdulillah." Ya ce. "Ina Ummi?" Ta ce. "Tana kitchen." Miƙewa ya yi ya shiga kitchen ɗin. Bayan sun gaisa Ummi ta ce. "Abba ya faɗa maka za ka je ka ɗauko Muneefah ko?" Ya ce. "Eh, amma sai na je office na yi abu daga nan zan wuce." Ummi ta ce. "Toh shikenan Allah ya kiyaye." Ya amsa da Amin sannan ya dawo parlour'n. Ummi ta biyo shi da breakfast ɗinsa. Bayan ya gama ci ya dubi A'isha ya ce. "Zan fita, me kike son na taho miki da shi?" Shiru ta yi kamar mai nazari. Ya ce "Yau fa sai kin faɗa mini duk zamiyar ki." Murmushi ta yi ta ce. "Komai ma, amma abin zaƙi." Ya ce. "Shikenan shazumama, sai na dawo." "Allah ya tsare." Ta faɗa idonta a kan direction ɗin inda take jiyo muryarsa. Kafin 8 sun je asibitin, Abba ya biya kuɗin aikin, ba a saka ranar aikin da nisa ba, Monday za a yi mata da safe. Tunda suka dawo gida A'isha take kwance a ɗaki, ta rasa me ya sa tsoro mai tsanani ya kamata akan aikin. Misalin ƙarfe ɗaya Ummi tana kitchen tana girki Muneefah ta shigo parlour'n da gudu tana ƙwala wa Ummi kira, ta manta da wani langwaɓewa na pretending ɗin cuta da take. Ganin babu kowa a parlour'n ta nufi kitchen ta rungume Ummi ta baya. Ummi ta ce. "Mene haka? Bana son shashancin nan naki fa?" A shagwaɓe ta ce. "Kai Ummi, duk murnar ganin ki ce fa." Ummi ta ce. "To patient, cutar kenan?" Murmushi ta yi ta ce. "Ina ganin ki na warke Ummita." "Allah ya shirye ki Muneefah, da kin yi haƙuri ma jibi za a yi hutu." Ɓata fuska ta yi ta ce. "Ni fa bana son boarding school ɗin nan ko kaɗan, Abba yana dawowa zan faɗa masa a mayar da ni Day." Ummi ta ce. "Zan fi kowa murna da hakan, dama aikin gidan nan ya mini yawa, in kina nan kuwa sai dai na miƙe ƙafa." Ta ce. "Toh shikenan, bari na ƙarasa na ga ɗakina, na yi kewar shi." A'isha tana kwance ta ji an shigo ɗakin, Muneefah ba ta lura da ita ba har ta ajiye trolley ɗinta. Sai da fara cire kayan jikinta ta lura da A'isha. Da mamaki ta ce. "Ihsan ko Mufeedah?" Miƙewa zaune A'isha ta yi don ta fahimci autar Ummi da ake yawan zancen ta ce ta dawo. "Sannu da zuwa." Muneefah ta ce. "Yawwa." Tare da juyawa ta fice daga ɗakin da sauri. Gurin Ummi ta koma tana faɗin. "Ummi wace ce waccan a ɗakina mai kama da ni?" Ummi ta ce. "Yar'uwarki ce." Cikin jin daɗi ta ce. "A gidan nan take?" Ummi ta ce. "Eh." Da murna ta ce "Na samu abokiyar hira, Allah ya sa kar ta tafi, mu yi ta zama tare." Ta ƙarashe maganar tare da juya cikin sauri ta koma ɗakin. Bayan ta zauna a kusa da A'isha ta ce. "Ya sunanki?" "A'isha." "Sunan Maman Ummi da Abba da Ya Maamah." A'isha ta yi murmurshi kawai. Muneefah ta ce. "Ni kuma sunana Khadija, sunan ƙanwar Ummi ne shi ya sa ake ce mini Muneefah." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Ba ta damu ba ta cigaba da magana. "Kina da kyau Masha Allah, ga kalar fatarki ma mai kyau, ana ganin kyan tawa amma taki ta fi, idanunki ma masu kyau irin na Yayanmu, ai kin san shi ko?" Girgiza mata kai A'isha ta yi alamun a'a. Da mamaki ta ce. "Kuma Ya Khalifa ya ce mini ya dawo, shi ne babban Yayanmu, duk ya fi kowa kyau a gidan nan, Likita ne, yana da Hospital ɗinsa na kansa a bayan layin nan mai suna *S.S.GIƊAƊO*, sunansa da sunan Abba ya haɗa *Safwan Sa'id Giɗaɗo*." Ta taɓe baki sannan ta ce. "Amma matarsa sai ta dinga cewa S.S ɗin wai sunanta da nasa ya haɗa, wai Salma and Safwan, ko daɗi ma babu." Murmushi kawai A'isha ta yi, a ranta tana mamakin surutu irin na Muneefah, daga ji ita ma babu ruwanta. Ummi ce ta shigo ɗakin tana faɗin. "Kina nan kina cika ta da surutu ko?" Ta ce. "Hira fa muke yi Ummi." "Ya yi kyau, ki kama hannunta ku je toilet ku yi alwala, idan kun yi sallar sai ku fito ku ci abinci, ki yi mata a hankali kuma saboda ba ta gani." Waro ido Muneefah ta yi ta ce. "Makauniya ce?" Ummi ta ce. "Ban sani ba, ki yi abin da na ce kawai." Cikin mamaki da tausayawa ta kama hannun A'isha tana faɗin. "I'm sorry sis, ban sani ba." Da yamma Ummi ta dawo daga gidan rasuwa ta shiga ɗakin Muneefah ta tarar da ita tana shirya kaya a wardrobe. Daga bakin ƙofa ta ce. "Ina Nana na gan ki ke kaɗai?" "Tana parlour a kwance." Ummi ta ce. "Wanne parlour'n?" "Parlour'n ƙasa." Ummi ta ce. "To ni ban gan ta ba, mu je ki nunan inda take." Babu musu ta miƙe suka fita. Ganin ba ta parlour'n a ruɗe Muneefah ta ce. "A nan fa na bar ta na shiga ɗaki yanzun nan." Wani kallo Ummi ta wurga mata ba ta ce komai ba ta shiga duddubawa. Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba, duk inda suke tunanin za su ga A'isha sun duba ba su gan ta ba. Hankali a tashe Ummi ta fita ta duba compound da bayan gidan amma ba ta gan ta ba. A ruɗe ta nufi gurin masu gadi ta tambaye su ko sun ga fitar A'isha? Suka ce mata ba su gani ba, kuma tunda ta fita har ta dawo babu wanda ya shigo gidan ko ya fita.........✍️ *Anan na kawo ƙarshen littafin KOMAI NISAN DARE part one, kamar yadda na faɗa kuma part two na kuɗi ne, mai so ya tuntube ni a 09047871750, sai na ji ku masoya.* An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 20 of 20