Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
koma ta kwanta, zuciyarta cike da son ganin Inna da sanin halin da take ciki. After ten minutes aka cire mata ruwan Ummi ta raka ta toilet. "Ga tap nan sai ki kunna ki tari ruwan tsarki." Ummi ta faɗa tana ƙoƙarin fita. "Ai bana gani." A'isha ta faɗa cikin sanyin murya. Cak Ummi ta tsaya cikin faɗuwar gaba, da mamaki ta ce. "Kamar ya ba kya yi?" "Makauniya ce ni." "Subhanallahi!" Ummi ta faɗa cikin tausayawa da mamaki tare da kama hannunta, kallon idon A'isha take tana ƙara girmama ƙudura irin ta Ubangiji, saboda babu yadda za a yi ka ga fararen daradaran idanuwa kamar su ka ce ba a gani da su, ko suna tattare da wani ciwon. Jiki a sanyaye ta tara mata ruwa ta ba ta tare da tsayar da ita a inda za ta yi fitsarin, fita ta yi ta ce in ta gama ta sanar mata tana bakin ƙofa tana jiran ta. Sosai Ummi ta kaɗu da jin Aisha makauniya ce, don farko ta ɗauka ma dalilin accident ɗin ne, kallon ta take cike da tausayawa, ta kasa ɗauke idonta daga kanta, gefe guda kuma a cikin zuciyarta cike take da zullumin yadda za ta ji idan ta samu labarin rasuwar Inna. Numfashi ta sauke ta ce. "Ya sunanki?" A'isha da zuciyarta ke ta bugawa ta ce. "A'isha." "Ayya, ashe ma Mamana ce ke, Yaya kuke da Innar taki?" "Babata ce." Gyaɗa kai Ummi ta yi, za ta kuma magana wayarta ta fara ringing. Ɗauka ta yi ta duba, ganin Abba ne ya sa ta ɗagawa. Magana suka yi ta sakanni ya katse kiran. After 5 minutes wata nurse ta shigo ta ba su takardar sallama da magunguna. Ajiyar zuciya A'isha ta sauke ta ce. "Gurin Innar za mu je ko?" "Eh, tana can gidanmu an kai ta, yanzu za mu je ki gan ta." Ummi ta ba ta amsa cikin dakiya. Shiru ta yi cikin mamakin kai Innar gidansu ita kuma tana asibiti. Abba yana bakin Motarsa a tsaye suka ƙarasa, baya Ummi ta buɗe ta shigar da A'isha ta mayar ta rufe. A nan take sanar masa A'isha makauniya ce, wadda ta rasu kuma mahaifiyarta ce. Ba ƙaramin shock ya shiga da jin hakan ba, wani irin tausayin A'isha da ƙaunar ta ya ji ya cika masa zuciya, har suka ƙarasa gida babu wanda ya yi magana a cikin Motar. Ummi na riƙe da hannunta suka shiga har part ɗin Abba inda gawar Inna take. Zaunar da ita ta yi a kan kujera sannan ta zauna ta kamo hannunta ta ce. "A'isha ke musulma ce ko?" Cikin mamakin tambayar ta ce. "Eh." "Good" Ummi ta faɗa tare da duban Abba dake tsaye yana kallon su. Numfashi ya sauke bai ce komai ba. A'isha da ita dai burinta ta ji muryar Innarta ko ta ji ta a kusa da ita ta ce. "Su waye ku? Ina innar tawa?" Abba ya ce. "Ni ne na buge ku da Mota, Innarki kuma yanzu za ki ji Inda take." Abba ya ƙarashe maganar tare da zama a kujerar dake fuskantar wadda suke. So yake ya faɗa mata Inna ta rasu amma ya rasa ta inda zai fara, don sosai A'isha take ba shi tausayi. Ƙarfin hali ya yi ya fara da yi mata nasiha akan yarda da ƙaddara mai ratsa jiki, hakan ya sanyaya wa A'isha jiki sosai, ta nutsu tana sauraren shi. Ganin nasihar ta shiga jikinta yadda yake so sai ya miƙe ya kama hannunta da kansa ya kai ta gaban gawar Inna ya zaunar. A raunane cikin sigar rarrashi ya ce. "Na san kin san dukkan mai rai mamaci ne, duk wanda yake rayuwa a doron duniya akwai ranar da dole sai ya koma ga mahaliccinsa. Ina mai ba ki haƙurin sanar miki cewar a hatsarin da muka yi Ubangiji ya karɓi ran Mahaifiyarki." Wani abu A'isha ta ji ya daki zuciyarta, tamkar an saka adda an datsa ta gida biyu, numfashinta ya ɗauke na wucen gadi, ta daina fahimtar komai, lokaci ɗaya kanta ya yi wani irin juya mata, daga zaunen da take ta yi baya luuu za ta faɗi. Da sauri Ummi ta yi kanta ta riƙe ta tana ambatar "innalillahi... Abbansu dauko ruwan sanyi a shafa mata, kamar fa ta suma." "Subhanallahi." Abba ya faɗa tare da miƙewa ya ɗauko ruwan a fridge ya miƙa wa Ummi. Da rawar jiki ta karɓa ta shafa mata a fuska. Gwauron numfashi ta sauke tare da zabura tana faɗin. "Inna! Inna! Kina ina? Wani mummunan mafarki na yi yanzu, wai mun je Kano an kaɗe mu kin mutu, na san ba gaskiya ba ne, ba za ki mutu ki bar ni ba, don Allah Inna ki yi magana na ji muryarki." Kallon Abba Ummi ta yi idanunta cike da ƙwalla ta ce. "Ina ganin mu bari yarinyar nan ta dawo cikin hayyacinta sai mu sanar mata yadda hankalinta zai ɗauka." "Mutuwa ba a shirya mata Dr, a duk lokacin da za mu faɗa mata sabuwa take a gurin ta, kuma dole sai ta sani, don haka babu amfanin ɓoye-ɓoye." "Hakane." Ummi ta faɗa tana gyara wa A'isha zamanta, wadda ke zaune tamkar mutum mutumi." Cikin sanyin murya ta fara magana. "Ba mafarki kike ba Mamana, Allah ya yi wa mahaifiyarki rasuwa, ga gawar ta nan a gabanki." Ummi ta ƙarashe maganar tare da ɗora hannun A'isha a kan gawar Inna. Kuka ta fashe da shi don zuwa yanzu ta tabbatar ba mafarki take ba, amma kuma zuciyarta ta kasa yarda Innarta ta rasu, Innalillahiwa'inna'ilaihirra'ji'un kawai take maimaitawa cikin sarƙewar harshe, numfashinta na fita a rarrabe tamkar zai bar gangar jikinta. Jikinta na kyarma ta buɗe bakinta cikin rawar murya ta ce. "Ya Ubangiji ka yi gaggawar farkar da ni daga wannan mummunan mafarkin da nake, na san ba gaskiya ba ne, na san Inna ba za ta taɓa mutuwa ta bar ni ba saboda ta san ba ni da kowa sai ita, don Allah su waye ku? Ku tashe ni daga wannan mummunan mafarkin da nake." Ta ƙarashe maganar tana laluben hannu Ummi. Rungume ta Ummi ta yi tana rarrashinta da ba ta baki, amma ba ta fahimta, babu abin da take ganewa. Da ƙyar ta iya amsa tambayar da Abba yake nanata mata ta daga ina suke? Ya buƙaci ta faɗa masa sunan gidansu dan a sanar da ahalinsu halin da ake ciki, sai ta ce masa ba su da kowa. Daga nan ba ta ƙara magana ba. Duk yadda Abba ya so ya samu wani information ɗin amma bai samu ba, har yamma ta yi ba akai Inna makwancinta ba. Alhaji Abubakar abokin Abba da ya dawo gidan a lokacin ya ce. "Ina ganin Alhaji Sa'id a tara jama'a kawai a yi wa matar nan Sallah akaita makwancinta, dare yana yi kuma mun san ba a son jinkirta kai mamaci." Numfashi Abba ya sauke ya ce. "Haka ne, amma da na fi so mu sanar da ƴan'uwanta su zo su ga gawar akai ta tare da su." "To Alhaji Sa'id ina muka san inda suke? Ita yarinyar da suke tare amsa ɗaya take ba mu ba su da kowa, mu kai ta kawai daga baya idan yarinyar ta dawo cikin nutsuwar ta sai mu je a sanar musu, amma idan ba haka ba gawar nan sai ta kwana." Cikin gamsuwa Abba ya ce. "Shikenan, bari na saka a sanar a masallaci, sai a nemo mai wankan gawa ta mata, Allah ya gafarta mata." "Amin." Kasancewar Abba babban mutum ne ana sanarwa a masallaci mutane suka fara taruwa a ƙofar gidan, maƙwabta mata kuma suka shiga cikin gida. A'isha dai tana zaune tamkar mutum-mutumi, ba ta fahimtar komai da yake faruwa, magana ma in an yi ba ta ji saboda komai nata ya tsaya cak, wani irin numfashi take fitarwa da sauri da sauri. Ummi na kusa ita tana tofa mata addu'a. An yi wa Inna wanka an haɗa ta an saka a cikin makara, jiki a sanyaye Ummi ta kamo A'isha ta tsugunnar a gaban gawar ta ce. "Ki yi mata addu'a, za a kai ta gidanta na gaskiya." Cikin fitar hayyaci A'isha ta ce. "Me zan ce? Ya ake addu'ar? Don Allah kar ku raba ni da Innata, ku bar mini ita a haka ina son ta, zan rayu da ita ko ta mutun." Sai kuma ta kama girgiza kai tana faɗin. "Innata ba ta mutu ba, don Allah Inna ki tashi ki ce musu ba ki mutu ba, na san ba za ki tafi ki bar ni, ni kaɗai ba." Ta ƙarashe maganar tare da ɗora kanta a kan gawar ta ƙanƙame ta. Da ƙyar aka ɗaga ta daga kan gawar, don tamkar mai iskokai haka ta koma, maganar wata tsohuwa da ta shigo tana cewa. "Shikenan fa rayuwar, yanzu ita ta tafi saura mu, Allah ya ji ƙan ta ya kyauta namu zuwan." Ya sa A'isha sumewa a jikin Ummi da ta riƙe ta. Safa da marwa kawai take yi a cikin makeken parlour'nta wanda ya ƙawatu da kayan alatu. Shigowar Baby ya sa ta dakatawa tana mayar da numfashi. Da mamaki Baby take bin ta da kallo. "Mommy lafiya kuwa na gan ki a hargitse?" "Ina fa lafiya Baby? Ba ki ga abin da mahaifinku ya yi ba ne?" "Me ya yi Mommy?" Taune leɓe ta yi alamun abun ya daki zuciyarta ba kaɗan ba ta ce. "Anan gidan fa aka yi wa matsiyaciyar matar da ya kaɗe sutura aka yi mata Sallah, maimakon ya kai ta can danginta su yi mata, ko kuma cewa aka yi dan ka kaɗe mutum ka yi masa sutura a gidanka?" Cikin rashin damuwa Baby ta ce. "To mene abin damuwa Mom? Daga an kai ta ba shikenan ba." A tsawace Mommy ta ce. "Akwai abin damuwa babba ma kuwa, a yi wa gawar talaka sutura a cikin gidan da nake ki ce mene abin damuwa? Talaka fa! Kin san yadda na tsani talauci da talakawa kuwa? Yadda nake jin tsanar talaka a cikin raina wallahi da ina da hali ƙasar da nake ciki a zaune ma ba zai zauna ba!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Yadda A'isha ta faɗi babu numfashi a jikinta ya taɗa hankalin su Ummi, Family Doctor ɗinsu ta kira ya zo ya ba ta taimakon gaggawa. Har bayan isha'i A'isha ba ta farka daga allurar baccin da aka mata ba, sai wajen ɗaya na dare ta farka da wani irin ciwon kai da nauyin ƙirji, har lokacin ba ta gama dawowa cikin hayyacinta ba.......✍️ _*Alhamdulillah, uzurin da ya riƙe ni yake hana ni posting akan lokaci na kammala shi, insha Allahu yanzu za kuna ji na kodayaushe, na gode.*_ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣4️⃣* Da ruwan ɗumi Ummi ta gogge mata jikinta tare da sauya mata kaya zuwa wata doguwar riga mara nauyi ta yarta MUNEEFAH dake boarding school. Ta haɗo mata tea mai kauri amma ta kasa sha, duk yadda Ummi ta yi da ita akan ta sha amma ta ƙi, sai haƙura ta yi ta ƙyale ta. Tun wannan farkawar ba ta kuma komawa bacci ba har garin Allah ya waye. Har yanzu zuciyarta ta kasa aminta Inna ta rasu, ta kasa yarda ta tafi ta bar duniya, ta kasa yarda ba za ta kuma ganin ta ba har abada a cikin zuciyarta. Damuwa da tashin hankali mara misaltuwa suka cika zuciyarta, so take ko ɗison hawaye ne ya zubo mata dan ta ji sauƙin abin da take ji a cikin zuciyarta, amma kukan ya ƙi zuwa. Sai a wannan lokacin ta gane ashe kuka ma Rahama ne. Ta yi addu'ar Ubangiji ya ɗauki ranta a wannan daren ita ma babu adadi, saboda ba ta san ina za ta saka kanta ba, ba ta san ta yaya za ta fara rayuwa ita kaɗai babu Inna ba, ba ta san ta yaya za ta kula da rayuwarta ba alhalin tana makauniya. Ina za ta ga danginta? Wa zai sada ta da su tunda babu Inna? Tunanikan da ta kwana tana yi kenan, hakan ya ƙara rurucewar ciwon jikinta, zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ta haɗe da zazzafan ciwon kai. Yadda ciwon ya galabaitar da ita ko ɗanyatsa ba ta iya motsawa. Hankalin Ummi ya ƙara tashi ganin yadda take rawar ɗari, numfashinta na fita da sauri da sauri. Addu'a suka haɗu suka ita da Abba suna tofa mata cikin ɗimauta da yanda jikin nata ya yi tsanani. Ana yin Sallar Asuba suka ɗauke ta zuwa asibiti. Suna zuwa aka karɓe ta tare da ba ta taimakon gaggawa. Ganin ta samu bacci Abba ya koma gida ya bar Ummi tare da ita. A main parlour ya ci karo da Khalifa. Cikin girmama ga gaishe shi, amsawa Abba ya yi cikin kulawa. "Ya jikin yarinyar?" "Da sauƙi Khalifa, na baro ta ma tana bacci." "Allah ya ƙara sauƙi, Yanzu Ya Maamah ta kira ni wai za ta biyo jirgin 8 ta zo, ta ce na maka jaje kafin ta ƙaraso, ta kira wayarka kai da Ummi ba ku ɗauka ba." Abba ya ce. "Allah ya sauke su lafiya sai sun ƙaraso." "Amin." Khalifa ya faɗa tare shigewa ɗakinsa. Abba yana shiga part ɗinsa ya tarar da Mommy Hakimce a kan kujera, yana ganin yadda fuskarta take murtuk ya san ba ƙalau ba, haɗe tasa ya yi shi ma don ya san neman fitina ne kawai ya kawo ta kamar kodayaushe. "Sannu Sa'id." Ta faɗa cikin rashin ladabi. Abba dake ƙoƙarin shiga ɗakinsa ya dakata ba tare da juyo ba. Ba ta damu ba ta ci gaba da magana cikin ɓacin rai. "Wai me kake nufi da barin yarinyar can a cikin gidan nan?" "Gidanki ko nawa?" Ya yi maganar a tsawace tare da juyowa. "Na ɗana ne." Ta ba shi amsa kai tsaye. "To idan kin isa ki saka ɗan naki ya zo ya fitar da ita daga gidan. Saratu ki kiyaye ni fa da wannan haukan banzan naki, kar ki kai ni bango na faɗa miki!" Ya ƙarashe maganar cikin ɗaga murya mai haɗe da tsawa. Ba ta ce komai ba ganin yadda ya ɗauki zafi, ƙwafa ya yi ya shige ɗaki cikin ransa yana mamakin wacce irin zuciya ce da Saratu, ana girma ana hankali da tunanin lahira amma ita ƙara haukacewa take da son duniya. Da harara Mommy ta raka shi, tsanar Ummi na ƙara cika mata zuciya, don ta san duk wannan abun ita take kitsa shi. Ƙwafa ta yi ta miƙe tana ƙissima matakin da za ta ɗauka a cikin ranta. Ƙarfe takwas da mintuna Khalifa ya ɗauko Ya Maamah daga airport, direct asibitin ya wuce da ita. Da kwatancen da Abba ya yi masa suka ƙarasa har ɗakin da suke. Ummi tana waya suka shiga da sallama. Bayan ta gama ta amsa musu tare da faɗin. "Sannun ku da zuwa, I'm sorry Ina waya ne da can school Ina sanar musu ba zan samu zuwa ba yau, kin sauka lafiya Maamah?" "Lafiya ƙalau Ummi, ashe abin da ya faru kenan? Allah ya kiyaye gaba" Ummi ta ce. "Amin, abun ba daɗin ji, amma babu yadda za mu yi tunda Ubangiji ya ƙaddaro." Ya Maamah ta ce. "Haka ne, wannan ce yarinyar?" Ta ƙarasa maganar tare da tashi ta koma gaban gadon da A'isha take. "Ita ce, wadda ta rasun kuma Mahaifiyarta ce, ƙarin abun tausayi ashe makauniya ce." Da sauri Khalifa da ya ƙura wa A'isha ido ya ce. "Wace makauniyar?" Ummi ta ce. "Yarinyar." "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'ji'un, Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya." Ya Maamah ta faɗa cikin tausayawa. Ummi ta amsa da "Amin." Khalifa kam kasa magana ya yi saboda tsananin mamaki da tausayi. Idanun Ya Maamah a kan A'isha ta ce. "Ba a samu ƴan'uwansun ba har yanzu?" "Ba a samu ba, ita yarinyar da aka tambaye ta ma cewa ta dinga yi ba su da kowa, amma ta faɗi daga inda suke, wani gari ne a cikin Kanon nan Kumurya." Da mamaki Khalifa ya ce. "Ai kuwa ina jin sunan garin nan, amma na rasa a inda na san shi." Ummi ta ce. "Abbanku ya ce babu nisa, tun jiya ma ya so su je, amma yanayin jikin yarinyar ya sa ya ce a bari ta samu lafiya sai su tafi har ita." Jinjina kai Ya Maamah ta yi, ita kam ta kasa daina kallon A'isha, lokaci ɗaya tausayi da ƙaunar ta suka cika mata zuciya. Wajen ƙarfe tara Aunty Ruƙayya ƙanwar Ummi ta zo asibitin ita ƴaƴanta, a kallon farko da ta yi wa A'isha ta ji gabanta ya faɗi ba tare da ta san dalili ba, ba ta ɗauki hakan da wata manufar ba ta zauna aka cigaba da jajanta al'amarin. Sai bayan Azhar A'isha ta farka, Alhamdulillah ta farko cikin hayyacinta. Ummi ta haɗa mata tea ta rarrashe ta, ta sha kaɗan da ƙyar. Ba jimawa ta ƙara komawa bacci, saboda Allurar da aka mata ba ta gama sakar ta ba. Bayan kwana uku Jikin A'isha ya yi sauƙi sosai, ta daina koke-koken da take yi. Sai dai ba ta magana kwata-kwata, duk abin da aka ce mata sai dai ta gyaɗa kai. Kulawar da su Ummi suke ba ta ya sa ta fara samun nutsuwa a cikin ranta. Ga Abba kodayaushe idan ya zo asibitin cikin yi mata nasiha akan yarda da ƙaddara yake, hakan ya sa ta fara dangana da rashin Inna, amma da zarar ta tuno ba ta kowa a duniya a halin yanzu kuma ba ta san inda rayuwarta za ta kaya mata ba sai hankalinta ya yi mugun tashi. An yi wa Inna Addu'ar uku da safe a masallaci gami da abubuwan toye-toye na sadaka. Kafin Azhar aka sallami A'isha. Da yamma bayan ta yi wanka ta rama sallolin da suke kanta Ummi ta kama hannunta suka je parlour'n Abba. Suna zaune da shi da Khalifa suka shiga, tunda suka shigo Khalifa ya ƙura mata ido cikin wani irin yanayi. Yadda take tafiya da yin komai a sanyaye shi yake ƙara masa tausayin ta a cikin ransa. A kan carpet Ummi ta zaunar da ita. Cikin sanyin muryar da ta dashe ta ce. "Ina Yini." Abba ya amsa mata cikin kulawa sannan ya ɗora da faɗin. "Yaya jikin naki? Ina fata yanzu kin daina jin jirin da nauyin ƙirjin?" Ɗaga masa kai ta yi a sanyaye. "Ciwon kan fa?" "Shi ma ya daina sai kaɗan-ƙadan." Ta faɗa kamar mai koyon magana. Cikin jin daɗi Abba ya ce. "Masha Allahu, Allah ya ƙara lafiya." Gabaɗaya suka amsa da Amin. Gyara zama Abba ya yi tare da fuskantar ta sosai ya ce. "Yau kwana uku da rasuwar mahaifiyarki, kuma har yanzu cikin danginku babu wanda ya sani, na so a ce mun je garin naku tun ranar da al'amarin ya faru don mu sanar musu, amma saboda rashin sanin Ina za mu tunkara idan mun je ya sa muka dakata har ki samu lafiya ki yi mana jagora. Kuma yanzu nake son mu tafi, ba na son a ƙara kwanaki ba mu je ba, saboda sanin yanzu duk wani makusancinku hankalisa a tashe yake da rashin sanin inda kuke." Hawaye masu ɗumi ne suka sauka a kan kuncinta, cikin rawar murya ta ce. "Ba mu da kowa, ko an mun je garin ban san wurin wanda zan kai ku ba." Shiru Abba ya yi yana nazari akan maganar ta, a hankali ya sauke numfashi ya ce. "Ina mahaifinki?" "Ya rasu." Ta ba shi amsa cikin kuka. Girgiza kai Ummi ta yi ta ce. "Yi haƙuri ki bar kukan haka ki yi mana yadda za mu gane, saboda babu yadda za a yi a ce kuna rayuwa ku biyu babu dangi, ina ƴan'uwan mahaifinki da na mahaifiyar taki?" Cikin sheshshek'a ta ce. "Duk ban san su ba, ban san inda suke ba, Innata kawai na sani." "Kuma ba ta faɗa miki inda suke?" Abba ya tambaye ta cikin mamaki. Gyaɗa masa kai ta yi. Ummi ta ce. "Ikon Allah, ku kaɗai kuke zaune a gidanku kenan?" Girgiza mata kai ta yi alamar a'a. Abba ya ce. "Allah ya kyauta, amma na kasa gane kan wannan al'amarin." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke tare da share hawayen fuskarta ta fara ba su labarin rayuwarsu da irin wahalar da suka sha, don ta sauƙaƙa musu tambayoyin da suke mata. Bayan ta gama ta ɗora da faɗin. "Don Allah kar ku mayar da ni gurinsu, wallahi kashe ni ne kawai ba za su yi ba saboda ba sa san mu, ku bar ni kawai na tafi wani gurin." Ta ƙarashe maganar cikin gunjin kuka. Cikin matuƙar tausayawa Ummi ta rungume ta tare da faɗin. "Ki kwantar da hankalinki Mamana, babu mai mayar da ke gurinsu kin ji?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da ƙara fashewa da kuka, kewar Inna da zafin mutuwar ta na ƙara cika mata zuciya. Numfashi mai zafi Khalifa ya fesar cikin takaicin jahilcin wasu mutanen, daga mutane sun zo garinku cin arziƙi don ba ku san su ba sai su zama abin muzantawa da ƙyara a gurinku? Saboda rashin ilimi. Abba da yake jin kamar ya zubar wa A'isha hawaye saboda tausayi ya ce. "Allah ya ji ƙan mahaifiyarki, ya inganta rayuwarki har ki zamo abar alfahari. Ki daina kukan nan haka kar ciwon ki ya dawo." Jinjina masa kai ta yi amma ta san ba za ta iya tsayar da hawayen dake fita daga idonta ba a yanzu. "A'isha!" Abba ya kira ta cikin taushin murya. Ɗagowa ta yi daga jikin Ummi ta amsa masa a raunane. "Na'am." "Kin tabbata labarin da kika ba mu gaskiya ne?" "Gaskiya ne Abba, idan ba ka yarda ba ka je garin ma ka tambaya za a faɗa maka." Gyaɗa kai ya yi cikin gamsuwa sannan ya dubi Khalifa ya ce. "Je ka kirawo mini Maamah da Baby da Saratu." Cikin ladabi ya amsa tare da miƙewa ya bar parlour'n........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣5️⃣* Mommy na zaune a parlour tana waya da ƙanwarta Khalifa ya shiga, ganin tana waya ya nemi guri ya zauna yana jiran ta gama. Hararar ƙasan ido ta wurga masa sannan ta ce. "Ina zuwa Kaltum zan kira ki." Ta ƙarashe maganar tare da zare wayar daga kunnenta ta katse kiran. "Abba ne ya ce ki same shi a parlour'nsa yanzu ke da Baby." Khalifa ya faɗa a taƙaice, bai jira amsar ta ba ya tashi ya fita. Da wani mugun kallo ta raka shi, bayan ya fita ta ja tsaki tare da duban ɗaya daga cikin masu aikinta dake duƙe a gefe cikin jiran umarni, ta ce. "Ke! miƙo mini takalmin nan." Jikinta har rawa yake gurin amsawa tare da cika umarnin da ta ba ta cikin sakanni ƙalilan. Miƙewa Mommy ta yi ta nufi ƙofa cikin takun ƙasaita, da sauri mai aikin ta wuce gabanta ta buɗe mata ƙofa ta fita. Ba tare da sallama ba ta shiga parlour'n Abba ta zauna tana bin kowa da kallon ƙasƙanci, musamman Ummi da take jin tamkar ta shaƙe ta saboda tsana. Ba ta taɓa ganin A'isha ba tun da ta zo gidan, yanzu ma ba ta ga fuskarta ba kasancewar ta sunkuyar da kanta ƙasa. Taɓe baki ta yi ta dubi Abba ta ce. "Ga ni Alhaji an ce kana kira na." "Na gan ki ai." Abba ya ba ta amsa da irin sigar da ta yi magana. "To ina jin ka." Girgiza kai kawai Abba ya yi ya ce. "Ina Baby?" "Ta je gidan Bahijja." Ta ba shi amsa cikin tarar numfashinsa. "Kuma shi ne har yanzu ba ta dawo ba ga Magriba ta kawo kai?" Ɓata fuska Mommy ta yi ta ce. "Mun yi waya ta ce mini ta taho." Bai bi ta kan maganar tata ba ya yi gyaran murya ya ce. "Masha Allah, mafi yawa daga ahalin gidan nan duk kun hallara, Safwan, Baby da Muneefah ne kawai babu." Ya numfasa idanunsa a kan A'isha ya ce. "Dalilin da ya sa na tara ku a nan shi ne don na sanar da ku wani abu mai mahimmanci da na zartar a cikin raina wanda duk ya shafe mu. Wannan Yarinya A'isha da tsautsayin accident ya haɗa mu za ta cigaba da zama a gidan har illa Masha Allah, a matsayin 'ya tamkar ƴaƴan cikina. Don haka ina gargaɗin ku akan kar na ji kar na gani wani a cikinku ya yi mata wani abu na muzanci ko wulaƙanci, idan hakan

Chapter 15 of 20