Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mutum ne wanda ba ya son ɓatawa kowa rai, ko da a cikin rashin sani ne, idan hakan ya faru ba ya jin kunya ko nauyin ya ba ka haƙuri don ka yafe masa, ko da kuwa kana ƙasan shi ne ya girme ka, ko kuma kana aiki a ƙarƙashinsa. A kodayaushe yana faɗa ba ya son mutuwa da alhakin kowa a kansa. Wannan tunanin ya ɗan sassauta zuciyar Mommy daga tsananin razanin da ta shiga lokaci ɗaya. Idanunta a kansa ta ce. "Son ya kake zuba abincin da kanka? Ka bari yanzu Atine za ta zo ta zuba muku." Ba tare da ya bari ba ya ce. "Na ga tana jin yunwa ne sosai shi ya sa nake zuba mata." "Ka bar shi na ce, tana matarka ita ba ta zuba maka ba sai kai za ka zuba mata?" Satar kallon Salma ya yi kamar mai jiran umarnin sai ta ce ya bari sannan zai bari, ɗauke kanta ta yi tana ƙeɓe fuska. Ba don ya so ba ya zauna still looking at her, so yake su haɗa ido ya rarrashe ta da idon amma ta ƙi. Mommy dake lura da su ta sauke numfashi mai tattare da ɗunbin takaici, da akwai matsala kenan? Don ta san wannan rawar jikin da Safwan yake yi ba na banza ba ne, dole sai da wani abun a ƙasa. "I'm sorry Dear, ki ci abincin please." Muryar Safwan da ya faɗi haka ƙasa-ƙasa ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi. Ganin yadda yake rawar jikin ɗebo abincin a spoon zai kai bakin Salma ya sa ta juyawa ta bar musu parlour'n cikin sauri tana haɗa hanya. Da kallo Salma ta bi ta tare da sakin wani shu'umin murmushi. Zarya Mommy ta shiga yi a parlour cikin tashin hankali, me yake shirin faruwa da ita ne? Salma ta asirce mata ɗanta ne ko yaya? Girgiza kai ta yi da sauri tare da faɗin. "Hakan ba zai taɓa faruwa ba, na san Kaltum ba za ta taɓa cin amanata ba ko ta bar Salma ta ci." 'Amma kuwa rawar jikin da Safwan yake akan Salman fa? Wadda a da ba ya mata' Zuciyarta ta faɗa mata haka. Hannunta ta ɗora a kan goshinta ta shiga bubbugawa. Tabbas ta ga wani abu mai kama da tsoro a tattare da ɗanta da yake yi wa Salma. Zama ta yi ɗabas a kan kujera tare da haɗiyar wani yawu mai ɗaci. Tunanin yadda Salma take masifar tsoron Safwan a da ta tuna, amma yau ba ta ga hakan ba ko kaɗan a tattare da ita, sai ma zallar fitsara da isa gami da gadara ta gani. Jijjiga kai ta yi cikin ƙanƙance ido ta ce. "Babu shakka idan har khaltum cin amanata ta yi sai na nuna mata asalin kalata, don ba zai yiyu in shafe shekaru ina gini lokaci ɗaya wata ta zo ta rusa mini shi ba, zan cigaba da saka ido a kansu har na gano bakin zaren." Ummi tana ƙoƙarin tashi ta ɗauko wa A'isha maganin ciwon kai da ta yi mata complain yana damun ta Ihsan ta shigo parlour'n kamar munafuka tana rarraba ido. Kallon da Ummi ta bi ta da shi ne ya sa ta shan jinin jikinta. Cike da tsoro ta ƙaraso ciki ta zauna kanta a ƙasa. "Daga ina kike?" Ummi ta tambaye ta a kaushashe. Cikin inda-inda ta ce. "Wani class mate ɗina ne a nan unguwar, muna chat ɗazu na ce masa ina unguwarsu, shi ne ya ce zai zo mu gaisa." Fuska babu walwala Ummi ta ce. "Shi ne ba za ki sanar mini ba kika fita a munafunce ko?" Shiru ta yi tare da yin ƙasa da kanta. A fusace Ummi ta ce. "I'm talking to you." "I'm sorry Ummi." "Sorry for yourself, kin fita ba da izinina ba sannan kin bar yarinya ita kaɗai a waje, kuma kin san ba gani take ba. Lefi biyu kenan." Ummi ta faɗa tare da yin ƙwafa. Kamar za ta yi kuka ta ce. "Don Allah ki yi haƙuri Ummi b...." Hararar da Ummi ta wulga mata ya sa ta haɗiye sauran maganarta. Ummi ba ta kuma magana ta miƙe ta haye sama. Ajiyar zuciya Ihsan ta sauke ta miƙe ta koma kusa da A'isha. Kallo ɗaya ta yi mata ta gane ta yi kuka, da damuwa ta ce. "Me ya faru Nana na ga kamar kin yi kuka?" Ɓata fuska ta yi ba ta ce mata komai ba, saboda haushin ta take ji tunda ita ce sanadiyyar faruwar komai. "Allah ya sa ba faɗuwa kika yi ba ko wani abu ne ya same ki?" Ihsan ta faɗa tana dudduba jikinta. Ganin yadda ta damu sai A'isha ta faɗa mata abin da ya faru in brief. Cikin takaici da ɓacin rai ta ce. "Kan Uba! Mari fa kika ce da shaƙa? Taɓɗijan! Da ma fa matar nan Mahaukaciya ce, Shegiya mai kama da fatalwa." Ta ƙarashe maganar tare da jan tsaki. Sai kuma ta sassauta murya ta ce. "Ki yi haƙuri Please Nana, na yi sanadin da aka taɓa lafiyar jikinki kina zaman-zamanki, wallahi ban san zan jima ba, da ba zan tafi na bar ki ba." Gyaɗa mata kai kawai ta yi tare da lumshe idonta, har yanzu wuyanta bai gama saki ba daga shaƙar da ta sha. Hankali kwance take cin abincinta, tana ci tana latsa wayarta, lokaci zuwa lokaci tana sakin murmushi alamun tana enjoying abin da take. Shi kuwa ya kasa cin abincin na kirki saboda ɓacin ran Khalifa da ya cika masa zuciya. Miƙewa ta yi tare da kara wayarta a kunnenta, tana goge bakinta da tissue ta ce. "Mine bari na shiga ciki na huta kafin ka gama." Da sauri ya miƙe ya ce. "I'm ok ni ma." Ɓata fuska ta yi tana kallon plate ɗin abincin nasa ta ce. "Ka zauna ka ƙara ci, wannan ai babu abin da ka ci." Zai kuma magana ta ɗaga masa hannu, cikin bayar da umarni ta ce. "Ka yi abin da na ce kawai, make sure ka cinye duka kafin ka hawo sama, and you already know idan ba ka cinye ba ma ka ce mini ka cinye zan gane." Gyaɗa mata kai ya yi yana murmushi ya ce. "Shikenan Lovely zan cinye." Hannu kawai ta watsa ta yi gaba. Da kallo ya bi ta har ta ɓacewa ganin shi. "Hello Mama ina jin ki yanzu, ban san kin ɗaga ba ɗazu, muna magana da Mine ne." Salma ta faɗa lokacin da take murɗa key ɗin ƙofar bedroom ɗinta ta rufe. Daga ɗaya ɓangaren Kaltum ta ce. "Okay Daughter, kun sauka lafiya? Ya hanya?" "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, Ina Daddy? Shi ne ko ya kira ni ya ji ya na sauka?" Ta yi maganar a shagwaɓe. "Yana nan ƙalau, kin san yana Abuja, wannan weekend ɗin bai dawo ba sai next week." "Allah Sarki Daddyna na yi kewar ku sosai Mama, na ɗauka zan tarar da ke a gida kin zo tarɓar ta." Kaltum ta ce. "Kin san na yi accident last week, Har yanzu ƙafata ba ta gama warkewa ba." "Ayya sannu, har na manta fa kin faɗa mini, ya ƙafar?" "Ta yi sauƙi. Ya kuka yi da surukar taki ne? Na san yanzu tana can zuciyarta ta kusa bugawa." Dariya Salma ta ƙyalƙyale da ita ta ce. "Ai in ma ba ta buga ɗin ba kenan, kin ga yadda ta ruɗe lokaci ɗaya? Daga ganin mood ɗinta ba ƙaramin shock ta shiga ba." Cikin dariya Kaltum ta ce. "Na sani dama, yadda take tinƙaho da alfahari da ɗan nan nata kamar a kanta aka fara haihuwa ko ita kaɗai ce mai ɗa namiji a duniya. Kaɗan ma ta fara gani, duk wulaƙanci da jan ran da ta yi mana kafin ki auri ɗanta duk sai mun fanshe shi a yanzu, dukiyar tasa ma da take taƙama da ita da sannu duk za ta zama tamu." Salma tana murmushin jin daɗi ta ce. "Gaskiya I'm lucky da samun ki a matsayin Uwa Mamata, ni fa yadda nake juya Ya Safwan kamar waina ya fi komai yi mini daɗi a yanzu. Duk wannan miskilancin da tsare gidan ya daina yi mini, yadda kika san zai mini sujjada fa don rawar jiki idan na ce ya mini abu." "Good ɗiyar arziƙi, da fatan kin faɗa masa zancen mota da gold ɗin da na ce ki ce ya siya miki." "Na faɗa masa, sarƙar ma gata nan a jakata na taho da ita, motar kuma ya ce ya yi order." "Da kyau shu'umar ƴa kamar uwarta." Salma ta yi dariya ta ce. "Ai kin san barewa ba za ta yi gudu ɗanta yay rarrafe ba." Sun daɗe suna wayar kafin su yi sallama bayan Salma ta tabbatar mata tana nan tafe anjima kaɗan. Tana cikin wanka ya shigo ɗakin, kayan jikinsa ya fara cirewa, yana ƙoƙarin shiga toilet ɗin ta fito tana goge jikinta da ƙaramin towel. Ba ta kalli inda yake ba ta nufi gurin mirror. "Lovely." Ya kira ta cikin kamilalliyar muryarsa. Juyowa ta yi tana kallon shi tana jin yadda son shi ke ƙara mamaye ko wane saƙo dake cikin zuciyarta. Takowa ya yi a hankali ya mannata da jikinsa tare da faɗin. "Me ya sa kika yi wanka ba ki jira ni ba?" Ɗan yamutsa fuska ta yi tare da raba jikinta da nasa ta ce. "Ina sauri ne zan fita." "Fita kuma?" Ya faɗa cikin mamaki. Gyaɗa masa kai ta yi tare da zama ta ɗauko wani tsadadden lotion ta fara shafawa a jikinta. A raunane ya ce. "Ina za ki?" "Gidan Mama." Ta ba shi amsa a taƙaice alamun ya fara takura mata. "Okay, lemme take shower sai na kai ki." "No need." Ta faɗa cikin haɗe rai. Sororo ya tsaya yana kallon ta, zai kuma magana ta ɗaga masa hannu tare da faɗin. "Tunda na ce bana buƙata ka ƙyale ni mana, ka fiya naci fa sometimes." "I'm sorry." Ya faɗa tare da shigewa toilet. Tsaki ta ja tare da tashi ta ƙarasa wardrobe ɗinta dake cike da kaya ta zaɓo wata doguwar riga mai bin jiki ta saka. Kafin ya fito daga wanka har ta kammala shiryawa ta fice daga ɗakin. Part ɗin Mommy ta je ta yi mata sallama tare da karɓar car key. Har ta juya za ta fita Mommy ta ce. "Da kanki za ki yi driving har Gandu Salma? Ina Safwan ɗin?" "Yana kwance, wai ya gaji ba zai iya fita ba, ni kuma gaskiya na ƙagu na ga Mama, that is why zan tafi ni kaɗai." Gyaɗa mata kai kawai Mommy ta yi tana jin zuciyarta ta fara samun sassauci a game da fargabar tunanin ta shanye mata ɗa da ya hana ta sukuni tun ɗazu. Da alamun abun da ta zarga ba gaskiya ba ne, tunda ga shi Salman za ta gurin mahaifiyarta ya ƙi bin ta, kuma ta haƙura dole za ta tafi ita kaɗai. Da ta asirce shin ai za ta masa dole ta ce sai ya raka ta, kuma dole ya yin. Salma kuwa murmurshi ta yi ta juya ta fita. Ta san yanzu ta saka mata wasi-wasi a cikin ranta kamar yadda Mama ta ce mata ta dinga raba mata hankali biyu, yadda abin zai fi ɗaga mata hankali ta rasa tudun dafawa ta kasa samun mafita. Har zuwa lokacin da duk wani shirinsu zai kammala, lokacin da ɗan da take taƙama da shi ɗin ganin shi ma sai ya yi mata wahala..........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *3️⃣0️⃣* Maimakon ta yi hanyar da za ta kai ta Gandu kamar yadda ta ce sai ta yi cikin Nasarawa G.R.A. Tafiyar mintuna kaɗan ta kai ta bakin ƙofar gidan da ta nufa, bayan ta danna horn mai gadi ya buɗe mata gate ta tura hancin motarta ciki zuciyarta cike maɗaukakin farinciki. Mata ne su huɗu zaune a cikin wani ɗaki cikin shigar da ba ta da maraba da tsirara. Biyu daga cikinsu na kan gado sun ba je suna zuƙar shisha. Sauran kuma suna kwance a kan carpet ɗin gaban gadon suna kallo a system. Jin shigowar mota ya saka su ɗago kai a tare gabaɗayansu. Ɗaya daga cikinsu mai suna Ramcy ta ce. "Salma Baby an ƙaraso kenan?" Ta ƙarshe maganar tare da tashi ta ɗaga labulen window tana leƙen waje. Shigowar ta ya saka su fasa ihu gabaɗayansu tare da nufar ta cikin murna suka ruƙunƙume ta suna faɗin. "Welcome." Dariya ta yi cikin matuƙar jin daɗi ta ce. "My babies I missed you so much." "Kin ga yadda kika canza kika yi kyau kuwa?" Ramcy ta faɗa lokacin da take zaunar da ita a bakin gado. Murmushi ta yi cikin daɗin yabon ta da Ramcy ta yi ta ce. "Ba dole ba tunda ina tare da Mine." Fadeela tana zama a kusa da ita ta ce. "Okay, ko kewar mu ma ba ki yi ba kenan?" Kuncinta ta shafa ta ce. "Faɗar irin kewar ku da na yi ɓata baki ne my guys, kawai dai kun san yadda nake tsananin son Mine kasancewa tare da shi ba ƙaramin abin farinciki ba ne a gare ni." Ba su kuma mata magana akan Safwan ba suka cigaba da murnar ganin ta. Daga nan suka zarce da abin da suka saba aikatawa na neman junansu. Tunda ya fito bai gan ta a ɗakin ba ya san ta tafi, maimakon ya ji haushi akan abin da ta aikata na ƙin yi masa sallama sai ya ba ta uzurin may be sauri take ta je ta ga Mahaifiyarta. A gaggauce ya shirya ya fito ya shiga part ɗin Mommy. Tana zaune a downstairs Atine na mammatsa mata ƙafa ya shiga parlour'n bakinsa ɗauke da sallama. Cikin fara'a Mommy ta ɗaga kai tana kallon shi tare amsa masa. Ƙarasawa ya yi ya zauna a kusa da ita. Kallon Atine ta yi cikin isa ta ce. "Ke tashi ki fita." Cikin girmamawa ta miƙe jiki na rawa ta fice bayan ta gaishe da Safwan. Kansa Mommy ta shafa tana murmushi ta ce. "Yanzu Abbanka ya kira ni ya tambaye ni ka sauka lafiya, ya kira sim ɗinka na Nigeria ba ya tafiya." Lumshe idonsa ya yi ya buɗe ya ce. "Ban saka sims ɗin a cikin waya ba ne har yanzu." Mommy ta ce. "Haka na ce masa." Ya numfasa ya ce. "Bari na je masallaci Mom." "Toh shikenan, idan ka dawo ina son magana da kai." Gyaɗa mata kai ya yi tare da tashi ya fice. Ganin ba a fara kiran Sallah ba ya nufi part ɗin Ummi. A'isha na zaune ita kaɗai tana cin abincin da Ummin ta tilasta mata kamar ba ta so ya shigo. Ƙarar Tv da yadda ya yi sallama a hankali ya sa ba ta ji shigowar shi ba. Kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke kansa ya nufi bedroom ɗin Ummi. Tana haɗa kaya a wardrobe ya shiga bakinsa ɗauke da Sallama. Ba tare da ta bar abin da take ta amsa masa ba yabo ba fallasa. "Sannu da aiki Ummi." Ya faɗa yana zama a kan carpet ɗin dake gaban gado. "Yawwa." Ta amsa masa still tana cigaba da shirya kayanta. Ganin yanayinta ya san fushi take da shi akan abin da ya faru. Cikin murmushi ya ce. "Zuwa fa na yi mu yi hirar yaushe gamo Ummina." Ummi ta ce. "To Bismillah mu yi mana, ya hanya? Da fatan kun dawo lafiya?" Cikin jin daɗin yadda ta saki fuska ya ce. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, da fatan mun same ku lafiya?" "Alhamdulillah, ai na ɗauka ƴar gold ɗin ba za ta bar ka, ka zo ka gaishe ni ba." Ya gane Salma take nufi, don haka ya yi shiru bai ce komai ba. Girgiza kai kawai ta yi ta zauna suka cigaba da gaisawa. Tana son Safwan sosai don duk abin da za ta yi ba ta banbanta shi da su Khalifa. Shi ma kuma haka, duk abin da ya yi wa mahaifiyarsa na kyautatawa to sai ya yi wa Ummi. Wannan dalilin yake ƙara yawaitar tsanar Ummi a cikin ran Mommy, Ta yi iya yinta don ta ga ta raba su amma Ubangiji bai ba ta nasara ba. Dole ta haƙura, amma duk da haka ko part ɗin Ummi ya je idan ta samu labari sai ta yi masa sababi ranar. Hakan ba ya hana shi ya ƙara zuwa ko ya yi mata abin Alkhairi. Sai da aka fara kiran Sallah sannan ya yi wa Ummi sallama ya tafi masallaci. Lokacin da ya fito A'isha ta gama cin abincin ta kwanta. Bai kalli inda take ba ya fice abinsa. Abba na dawowa Mommy ta tare shi da ƙorafin Khalifa ya mari Salma, da yake ta karɓi girki yau. Da mamaki Abban ya ce. "Mari kuma? A kan me?" "Wa ya san masa Alhaji? Yaron nan fa dama can ba mutunci gare shi ba." Abba ya ce. "Gaskiya akwai abin da ya faru, haka kawai Khalifa ba zai mari matar yayansa ba, amma bari na kira shi a waya na ji ba'asin zancen." Cikin takaici Mommy ta ce. "Kamar ya sai ka kira shi ka ji ba'asin zance? Akwai ba'asin da ya wuce wanda na faɗa maka? Ko kuma zan maka ƙarya ne?" "A gabanki aka yi marin ne?" A shaƙe ta ce. "A'a." Abba ya ce. "To kuma, ko shaidar zur za ki bayar?" A ƙufule ta ce. "Amma ka san shi ma dai ba zai faɗi gaskiya ba ko? Kansa kawai zai kare" "Idan ma ya yi ƙaryar zan gane." Abba ya faɗa tare da kara wayarsa a kunnensa. Khalifa yana parlour'n Ummi a lokacin yana tambayar A'isha yaya take jin jikinta a yanzu. A hankali ta ce masa. "Kaina da wuyana ne suke mini ciwo." Taune lips ɗinsa ya yi yana ƙara jin zafin Salma a ransa ya ce. "Sorry, kin sha magani?" Ta ce. "Eh Ummi ta ba ni." Cike da kulawa ya ce. "Ko kina son cin wani abu na siyo miki." Ta girgiza masa kai alamar a'a. "Ki faɗa mini dai, me kike son ci zan siyo miki ko mene ne Nana." Yadda ya yi maganar cikin wani irin yanayi sai ta ji tamkar Umar, ta rasa me ya sa kalamansa da muryarsa suke mata shige da na Umar sometimes. Numfashi ta sauke ta ce. "Babu komai fa, bacci kawai nake son yi." Ya ce. "Mu je na raka ki ɗaki ki kwanta to." "Ummi ta ce na bari a yi Sallar Isha'i sai na yi baccin." Ta ba shi amsa cikin jin daɗin yadda yake nuna damuwa a kanta. Fitowar Ummi daga kitchen ya saka shi fasa faɗar abin da ya yi niyya. "Ka je Abbanka na kiran ka, ya kira ka ba ka ɗauka ba." Da to ya amsa mata tare da miƙewa ya fice ba tare da ya bari sun haɗa ido ba. Mommy na zaune har lokacin tana cika tana batsewa ya shiga, Abba da suke gaisawa da Safwan ya dube shi tare da amsa sallamar da ya yi. "Sannu da zuwa Abba." Ya faɗa lokacin da yake zama. Abba ya ce. "Yawwa." Duban Safwan ya yi ya gaishe shi tare da yi masa sannu da zuwa, a maimakon ya sai harara ya wurga masa. Tambayar shi Abba ya yi akan abin da ya faru ya faɗa masa duk abin da idanunsa suka gane masa cikin nutsuwa. Jinjina kai Abba ya yi cikin gamsuwa ya ce. "Me ya sa ka mare ta? Duk da ka girme ta ai Yaya take a gurinka yanzu." Khalifa ya ce. "Wallahi Abba ban je inda suke da niyyar taɓa jikinta ba, na yi na yi ta sake ta ne ta ƙi, ban ma san lokacin da zuciya ta ɗeɓe ni na mare tan ba." Ƙwafa Mommy ta yi tana hararar shi ba ta ce komai ba. Safwan kuwa danne zuciyarsa kawai yake don a gaban Abba ne, amma da sai ya rama wa Salma marinta, kuma idan ya tashi ba ɗaya zai masa ba, sai ya ninka marin sau uku. "To ka ja masa kunne Abba, kar ya ƙara gigin kai hannunsa jikin matata." Safwan ya faɗa a fusace. Abba ya ce. "Ita ma ka ja mata kunne akan ta dinga bin komai a sannu, ba wai abu bai kai ya kawo ba ta hau dokin zuciya, don watarana zai kai ta ga da na sani." Cikin jin haushin maganarsa Mommy ta ce. "Alhaji kana nuna masa abin da ya yi fa daidai ne, Salma ce ke da laifi kenan?" Abba ya ce. "Eh." Ganin yadda ya yi maganar fuska a haɗe ya sa ba ta kuma magana ba, amma a ranta ta ƙudurce Khalifa bai mari banza ba, za ta ɗauki mataki da kanta. Duk da Abba ya ce ya kashe maganar kar wanda ya ƙara taso ta. Salma tana mayar da rigarta Fadeela ta fito daga toilet tana faɗin. "Wai da gaske Salma tafiya za ki yi?" Ta ce. "Eh mana." "Duk missing ɗin namu da kika ce kin yi iya baki ne kenan? I thought a nan za ki kwana?" Tana taje gashin dokin dake kanta ta ce. "Gidan Mama za ni." Rukky dake kwance a kan gado tana sauraren su ta ce. "Sai yaushe kuma? Ko mu zo gidanki gobe?" Tsayawa ta yi da tazar da take cikin waro ido ta ce. "What? Gidana fa kika ce, kar ma ku soma, don Mine yana nan, kuma kun fi kowa sanin bana barin a zo mini gida idan yana nan, saboda bana ƙaunar duk wani abu da zai haɗa shi da wata mace komai ƙanƙantar shi." Dariya Ramcy ta yi ta ce. "Me a kai kenan? Idan kin ɓoye shi a gida a gurin aikinsa fa? Likita ne fa shi, likitan ma na mata, ai babu wanda zai kai shi hulɗa da mata kala-kala ma." Salma ta yi murmushi tare da faɗin. "Wannan na san aikinsa kawai yake ba ya bi ta kansu, ke koma yana bi sai dai ya gani ya ƙyale, don ba aura zai yi ba, saboda babu macen da ta isa na haɗa miji da ita duk duniyar nan. Safwan nawa ne ni kaɗai, don ni kaɗai aka halicce shi." Fadeela ta ce. "Easy bab, ba a kuri a kan namiji." "Ni na yi na kuma yi, ku zuba ido ku yi kallo, ko mutuwa na yi Safwan ba zai so wata mace ba, balle kuma ina raye." Ta ƙarashe maganar tare da ɗaukar jakarta ta juya ta fice bayan ta ɗaga musu hannu. Da kallo suka bi ta da shi. Haleemah ba ta tanka musu ba tun ɗazu ta ce. "Iska na wahalar da mai kayan kara, wato ita har ta manta baƙar wahalar da ta sha kafin ya yarda ya aure ta?" Rukky ta ce. "Har aka yi auran fa baya son ta, yanzu ma soyayyar duk ta asiri ce." Taɓe baki Fadeela ta yi ta ce. "Zai karye ne watarana, mu ga ƙarshen jijjigi da kai da ɗagawar auren mai kuɗi, kyakkywa da ake mana." *5 days later* Yau ta kama ranar komawa asibiti karɓar sakamakon gwajin da aka yi wa A'isha. Sai a cikin kwanakin nan da suka wuce Mommy ta san A'isha makauniya ce, ranar da ta ji labarin ba ƙaramin bala'i ta yi ba, ta ce sai dai Abba ya zaɓa ko ita ko A'ishan. Don ba za ta iya zama da ita a gida ɗaya ba, ga talauci ga rashin asali sannan kuma ga makanta. Da farko Abba bai kula ta ba, sai da ta ishe shi ya ga idan bai tsawatar mata ba, ba za ta bar shi ya yi sukuni ba sannan ya ce mata ya zaɓi A'isha, ta je ta yi duk abin da za ta yi. Ƙaramin hauka ta yi da jin furucin nasa saboda ba ta taɓa zaton zai iya kallon cikin idonta ya faɗa mata haka ba. Ko Ummi bai taɓa cewa ya zaɓa a kanta ba sai wata TSINTACCIYA mara asali? Ranar kasa rintsawa ta yi saboda baƙin ciki. Tsanar A'isha mai tsanani ta ƙara cika mata zuciya. Cikin daren jiya Allah ya yi wa wani maƙocinsu rasuwa, hakan ya sa Abba da sassafe ya kira Ummi ya ce mata idan sun shirya driver zai kai su asibitin, shi zai zauna a yi jana'iza da shi. Lokacin da suke wayar Mommy tana kwance a gadonsa, da yake ita ce da girki. Duk da faɗan

Chapter 18 of 20