Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma sai ki daina karatu? Ko ba kya son ki zama likitar ne yanzu?" A'isha ta ɓata fuska ta ce. "To Inna da wa za mu dinga tafiya tare?" Inna ta ce. "Ni zan dinga kai ki in na ɗauko ki." A'isha ta ce. "To wa zai dinga mun rubutu? Idan an fita Sallah wa zai na kama hannuna mu je mu yi?" Shiru Inna ta yi tana kallon A'isha na wasu sakanni, daga baya ta ce. "Mu je makarantar dai sai mu ji yanda za'a yi." Washegari ba dan A'isha ta so ba ta shirya suka tafi Makarantar tare da Inna. Allah ya haɗa su da wata Malama mai kirki mai suna Malama Hajara, Inna ta yi mata bayanin abun da yake tafe da ita, ta kwantarwa da Inna hankali ta ce, insha Allahu zata na kula da A'isha yanda ya kamata, ko da ranar da ba za ta zo makarantar ba zata yi waya ta faɗa a kula da A'ishan. Inna ta yi mata godiya sosai sannan ta dawo gida. Cikin satin nan rayuwa ta fara yiwa su Inna tsanani, saboda yanzu ba ta sana'ar komai, sai aikin abincin sadakar nan, 500 kuwa a sati mai zata yiwa rai biyu, ga abubuwan da yawa, bayan abinci ga sabulun wanka da na wanki, ga man shafawa, ga omon wanke_wanke, ga siyan ruwan amfanin gida, ban da sauran abubuwan buƙata na yau da kullum. Jarin ayar da ɗan guntun kuɗin dake hannunta duk sun ƙare. Sai suka koma irin rayuwar daa, sai su farka ba su da ko ƙwayar hatsin da za su ci a cikinsu. Yau Alhamis, wanda ya kama sati biyu cif da tafiyar su Ma'u. Da rana A'isha ta gama shirin tafiya makaranta kasancewar ta yamma suke yi tunda su ƴan junior section ne. Jakar makarantarta ta laluba ta ɗauka, cikin sanyin murya ta ce. "Inna na gama mu tafi." Inna ta sauke tagumin da ta rafka ta ce. "Haka zaki je makarantar ba ki ci komai ba A'isha, da hak'ura kika yi na fita na dawo ko Allah zai sa in dace in samo miki wani abun ki ci, sai ki tafin." A'isha ta ce. "Toh Inna a ina zaki samu?" Inna ta ce. "Sabon Gari zan je gurin Hajiya mai k'uli_k'uli, idan da aiki in yi mata ta biya Ni, na san ma ba'a rasa aikin ba tunda gobe ne cin kasuwa za'a zo a sissiya." A'isha ta ce. "To mu je makarantar, idan kin samu sai ki kai mun can ɗin." Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Kin kawo shawara kuma, tashi mu je kar ki makara, daga can sai na wuce." Miƙewa A'isha ta yi, Inna ta kama hannunta suka fice. Tun bayan da Inna ta tafi ba jimawa A'isha take saka ran dawowarta, domin wata irin yunwa take ji ba kaɗan ba, ɗan kokon Naira goman da ta sha da safe shi kaɗai ne a cikinta. Har aka fita Sallar la'asar Inna ba ta zo ba, gashi yau Malama Hajara ba ta zo ba, sai wata yarinya ta roƙa ta fitar da ita waje ta yi ta Sallah ta dawo da ita. Bayan an dawo aji tana ta jin yara na ta ciye_ciye abunsu, suka bar ta da jin ƙamshi. Har aka tashi Inna ba ta zo ba, zuwa lokacin yunwa ta fara galabaitar da A'isha, dauriyar ta ƙare ta fara hawaye. Gashi yara duk sun tafi gida sai ita kaɗai a bakin aji a tsugunne. Wani Malami ne ya hango ta ya taho inda take, da mamaki yake duban ta ya ce. "Ke lafiya kike zaune anan ke ɗaya?" A'isha ta ce. "Innata nake jira ta zo ta ɗauke ni." Malamin ya ce. "Ayya ke ce mai ciwon idon nan ko?" Gyaɗa masa kai A'isha ta yi. Ya ce. "To yanzu zama zaki yi ki ta jiran ta kuma? Yamma ta yi ga garin hadari ya haɗo sosai, mu ma duk tafiya za mu yi, amma abun da za'a yi bari na saka a raka ki gida, ina ne gidan naku?" A'isha ta ce. "A Ƙofar fada ne." Malamin ya ce. "To mu je a raka ki, wannan hadarin ai ba zai yiyu ki zauna ke kaɗai anan ba, gashi ba gani kike ba." Sai da suka fita daga cikin makarantar yana riƙe da hannunta sannan ya samu wani yaro ya ce ya raka ta gidan Sarki, daga nan sai ta samu wani ya kai ta gida, tunda shi yaron bai san gidansu ba. Kafin su ƙarasa, garin ya ƙara duhu, an fara iska mai ƙarfi haɗe da yayyafi. Yaran sai jan A'isha yake, duk ta ƙara galabaita, tafiya kawai take yi amma jin ta take kamar zata faɗi. Yaron yana kai ta ƙofar gidan Sarki ya juya ya yi tafiyarsa, saboda zuwa lokacin ruwa ya fara ƙarfi. Ɗan_juma suna zaune a soro akan benci shi da Hamza da wani abokinsa suna karta, kamar a mafarki ya hango A'isha tsaye ta rakub'e a jikin bango, ƙura mata ido ya yi yana tuna when last da ya gan ta, ya jima bai gan ta ba gaskiya. Sai ya ga ta ƙara girma ta fara zama ƴar budurwa. A'isha tana shekaru goma sha uku a yanzu, amma saboda tana da garin jiki da ɗan tsayi idan ka gan ta zaka yi tunanin shekarun ta sun fi haka. Ruwan da ya fara dukanta ya saka uniform ɗin jikinta duk ya mammanne mata a jiki. Ɗan_juma ya ƙurawa ƙirjinta da ya ɗan fara tasawa da irgen dangi ido, nan fa shed'an ya fara buga masa ganga akan mummunan k'udirinsa akan A'isha. Wani murmushi ya yi tare da lasar leb'ensa ya ce da su Hamza. "Tsuntsu daga sama gashashshe." Bai jira cewar su ba ya miƙe ya fita ya janyo A'isha cikin zauren ta ƙarfin tsiya, bayan ya duba gabas da yamma kudu da arewa ya ga babu kowa a wajen. A'isha ta ƙanƙame Jakarta a jikinta cikin rudu ta ce. "Waye wannan? Me na yi maka? Ni ka cika ni? Mene ne haka?" Ɗan_juma ya cika ta yana murmurshin mugunta, abokansa da sai yanzu suka gane mai yake nufi suna taya shi murmurshin. Laluben Hanya A'isha ta fara yi cikin hawaye, jikinta gaba-d'aya rawa yake yi saboda tsabar tsoratar da ta yi da janyon tan da Ɗan_juma ya yi, gashi ba ta san ko wanene ba. Garin neman hanyar fita ta ƙume goshinta da garu, kuka ta saka tare da kiran sunan Inna. Cikin rashin Imani ɗan_juma ya fizgo ta tare da fizge jakar hannunta ya cillar a ƙasa, wani uban ihu A'isha ta ƙwala ta fara tittirjewa, amma saboda ruwan da ake yi mai ƙarfi ne yasa babu wanda zai jiyo ihun nata balle ya kawo mata ɗauki, cak Ɗan'juma ya ɗaga ta ya shige da ita wani ɗaki dake cikin zauren ya kullo ƙofa. Ihu sosai A'isha take yi tare da ƙoƙarin k'wace kanta daga hannun Ɗan'juma amma ta kasa. Mara masa baya su Hamza suka yi zuwa cikin ɗakin, a ƙasa Ɗan'juma ya jefar da ita sannan ya saka ƙafa ya take ƙafafuwanta da take haurin sa da su, da ido ya yiwa su Hamza alamar su danne masa A'isha. Hamza ya ƙaraso ya saka hannunsa ya toshe bakin A'isha da ƙarfi saboda da ihun kukan da take, ɗayan kuma ya daddanne mata hannayenta da iyakacin ƙarfinsa. Cikin tsantsar zalunci Ɗan'juma ya cire Hijabin jikinta ya cillar, yana wani irin murmushin zallar iskanci da duniyanci ya fara cire kayan jikinsa...........✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣9️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ .........Wani kyakkyawan Matashi ne ya fito daga cikin gidan Sarki hannunsa riƙe da umbrella. Sai da ya zo zaure sannan ya tsaya yana nannad'e umbrellar. Dai_dai nan Allah ya bawa A'isha sa'a ta gantsarawa Hamza cizo a tafin hannunsa, cikin sauri Hamza ya janye hannun nasa saboda azabar zafin da ya ji ya shiga yarfa hannun, hakan ya bawa A'isha da ta fara fita daga hayyacinta damar ƙwala ihu. Cak matashin ya tsaya a inda yake cikin mamakin abun da kunnuwansa suka jiyo masa, kalle_kalle ya fara yi dan idan ya ji dai_dai kamar a cikin zauren aka yi ihun. Wani ihun A'isha ta ƙara yi saboda marin da Ɗan_juma ya wanka mata, wanda ya yi tunb'ur haihuwar uwarsa. Kallon ƙofar ɗakin Ɗan_juma Matashin ya yi, haka kawai ya ji hankalinsa bai kwanta ba da ihun da yake jiyowa, lemar hannunsa ya ajiye cikin sauri ya nufi ɗakin ya buɗe ya shiga. Tozali ya yi da Ɗan_juma tsirara yana ƙoƙarin cirewa A'isha riga, ita kuma sai jujjuya kai take yi hawaye na shatata daga cikin idonta. Cikin kid'ima ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, mene haka? Me kuke shirin aikatawa?" Juyawa su Hamza suka yi suna kallon sa a rud'e. Banda Ɗan_juma da ya cigaba da abun da yake yi, dan tunda ya samu wannan damar yau ba zai so ta kufce masa ba, bai ga kuma uban da ya isa ya hana shi yin abun da ya yi niyya ba. Runtse ido Matashin ya yi ya buɗe cikin tsananin ɓacin rai ya ƙarasa inda suke ya daddage ya saukewa Ɗan_juma wani uban naushi a tsakiyar gadon bayansa, gantsarewa Ɗan_juma ya yi dan naushi ya shige shi ba kaɗan ba, wani naushin Matashin ya ƙara sakar masa wanda ya saka shi yin taga_taga ya faɗi a ƙasa yana faɗin. "Aushh.....!" Ganin haka su Hamza suka miƙe cikin hanzari da niyyar guduwa, Matashin wanda zuciyarsa ke wani irin tafarfasa saboda baƙin ciki ya cakumo su dukan su ya bazar da su a ƙasa, ya ba su nasu rabon naushin. Sai ga su gaba-d'ayansu duka a ƙasa suna sassauke numfarfashin wahala. Jikin Matashin gaba-d'aya tsuma yake yi, kyawawan fararen idanunsa sun kada sun yi jajur. A hankali ya ƙarasa ya tsaya yana kallon A'isha wadda tuni ta sume, cikin sauri ya dauko hijibinta ya zira mata sannan ya ciccib'e ta ya fice da ita daga cikin ɗakin, sai a lokacin ya lura da jakar makarantar ta dake yashe a ƙasa a cikin zauren. Girgiza kansa kawai ya yi ya nufi wata ƙofa dake pacing ɗin ɗakin Ɗan_juma ya buɗe da key ya shiga. Akan ƙatuwar katifar dake ɗakin ya shimfid'e A'isha, sannan ya fito ya ɗaukar mata Jakarta ya koma ɗakin, har lokacin ruwa ake yi bana wasa ba. Zama ya yi a gaban A'isha yana sassauke numfashi, ƙura mata ido ya yi cikin tsananin tausayinta na ƙoƙarin keta mata haddi da su Ɗan_juma suka yi, fuskarta ta yi jajur saboda kukan da ta sha, shatin hannun Ɗan_juma rud'u_rud'u akan fuskarta. Haka kawai ya ji gabansa ya yanke ya yi wata irin fad'uwa, kasa ɗauke idonsa ya yi daga fuskar A'isha, lokaci ɗaya bugun zuciyarsa ya sauya, ta fara bugawa da sauri_sauri. Daƙyar ya yi ta maza ya janye idonsa daga kan A'isha ya miƙe ya nufi ledar pure water ɗin dake ɗakin ya dauko ɗaya ya bula ya shiga shafawa a fuskar A'isha zuwa wuyanta, tsawon mintuna biyu yana hakan sannan ya ji ta ja wani gauron numfashi, lokaci ɗaya kuma ta yi yunk'urin miƙewa jikinta na wani irin k'yarma tana kiran sunan Inna, tare da ƙoƙarin kai hannu tana dukan iska alamar son k'watar kai. Cikin tausayawa ya riƙe hannunta, so cool ya ce. "Sorry." A'isha ta fizge hannunta tare da ja baya ta fashe da kuka ta ce. "Su waye ku? Me yasa kuke son cutar da ni? Me na yi muku?" Ta ƙarashe maganar tare da tashi zaune. Lumshe ido ya yi ya buɗe saboda a yanzu A'isha ta buɗe idonta wanda ke cike da zallar firgici da tsoro, kallon idanun nata kuwa ya ƙara masa saurin bugun zuciyarsa gami da faduwar gaban da ta fi ta ɗazu. Cikin rarrashi ya ce mata. "Ki kwantar hankalinki, because by now ba kya hannun masu son cutar da ke, Ubangiji ya kub'utar da ke." A'isha ta ƙara volume ɗin kukunta ta ce. "Waye kai? Ni ka kai ni gurin Innata." Tana yin maganar ne cikin tsananin tsoro da firgicin da yake tabbatar da a cikin razani take, sai dunk'ule jikinta take yi guri guda. Bai kuma cewa komai ba ya miƙe ya fita ya lek'a waje ya ga har lokacin ruwa aka yi, amma an fara ɗaukewa. Tsayawa ya yi yana kallon ɗakin Ɗan_juma, zuciyarsa cike mamakin sa ba ɗan kaɗan ba, bai taɓa tunanin hakan daga Ɗan_juma ba, fyaɗe fa? Har su uku akan ƙanƙanuwar yarinya, wannan wanne irin zalunci ne haka? Ya manta rabon da ya yi tozali da abun da ya tayar masa da hankali kamar wannan. Yana nan tsaye har ruwan ya ɗauke ya koma sai yayyafi kaɗan_kaɗan saboda gabatowar lokacin Sallar Magriba. Juyawa ya yi ya koma cikin ɗakin, a tsakar ɗakin ya tarar da A'isha tana laluben hanya cikin kuka, riƙe ta ya yi ya ce. "Sorry, ruwa ake yi ne sai yanzu ya ɗauke, mu je in raka ki gidan." Wata k'ak'k'arfar ajiyar zuciya A'isha ta sauke tare da kallon fuskarsa kamar mai iya ganin sa, haka kawai ta ji zuciyarta ta ɗan nutsu da shi, murmushi ya sakar mata sannan ya cika ta ya ɗaukar mata Jakarta ya nuna mata ƙofa ya ce. "Mu je ko?" A'isha dake jin duk jikinta na yi mata wani irin ciwo ga juwa dake ɗiban ta, ta kai hannu ta lalubi bango ta dafa, cikin muryarta da ta ci kuka ta ƙoshi ta ce. "Ba na gani, sai dai a riƙe mun hannuna." Cak ya tsaya yana kallon ta cikin shock yana maimaita abun da ta faɗa a cikin zuciyarsa, ba ta gani? What she meant? Ita makauniya ce ko me? Ya faɗi haka a cikin zuciyarsa. Numfashi ya sauke a hankali ya ce. "Ok." Sannan ya kama hannunta suka fice daga ɗakin, ko rufe dakin bai yi ba suka yi waje. Suna fita ana fara kiran Sallah, Allah ya haɗa su da wasu yara suka nuna masa gidansu A'isha daga nan, kamar yadda ta ce masa ya tambayi wani ya nuna masa da ya tambaye ta ina ne gidansu. Tunda bayan da Inna ta kai A'isha makaranta ta wuce Sabon gari kamar yadda ta ce, tana zuwa ta tarar lokacin za'a fara aikin k'uli_k'ulin, zama ta yi aka fara aikin da ita. Ba su gama aikin da wuri ba, dalilin da ya saka kenan ba ta koma makarantar su A'isha ba, yin aikin kawai take yi amma hankalinta gaba-d'aya yana gurin A'isha. Lokacin da suka gama aikin haɗarin nan ya haɗo sosai, amma haka Inna ta taho gida saboda hankalinta gaba-d'aya yana kan A'isha, har fad'uwa ta ji gabanta yana yi ba tare da ta san dalili ba. Sai dai tun kafin ta ƙarasa gida aka fara ruwan, duk da haka ta so zuwa ta ɗauko A'isha a ruwan, amma saboda yanda ruwan ya yi ƙarfi yasa dole ta hak'ura ta wuce gida ba dan ta so ba. Tunda ta koma gidan sai ta kasa tsaye ta kasa zaune, haka kawai ta ji zuciyarta ta kasa nutsuwa, ga gabanta da yake ta fad'uwa. Addu'a ta dinga yi akan Ubangiji yasa a ɗauke ruwan ta je ta gano halin da ƴarta take ciki. Ana fara tsagaita ruwan kuwa ta ɗauki buhu ta lullub'a a kanta ta nufi makarantar su A'isha, tana zuwa ta tarar babu kowa makarantar ma a kulle take. Hankalinta a matuƙar tashe ta dawo gida zuciyarta cike da tarin tambayoyi akan inda A'isha take. Tana shiga soron gidan su ma su A'isha suna shiga. Juyowa ta yi jin takun tafiya a bayanta, da sauri ta dawo baya cikin zak'uwa ta ce. "A'isha!" Jin muryar Inna yasa A'isha ta fara kuka tare da janye hannunta daga cikin na Matashin. Inna ta rungume ta tare da sakin ajiyar zuciya. Cikin kuka A'isha ta ce. "Inna ina kika tafi ba ki zo kin ɗauke ni ba?" Inna ta ce. "Ban dawo da wuri ba ne A'isha, da fatan babu abun da ya same ki? Ruwa bai dake ki ba ko? Na ji jikinki da lema, ina takalmanki?" A'isha ba ta iya bawa Inna amsa ba sai kuka kawai take yi. A rud'e Inna ta ce. "Me ya faru dake ne A'isha? Me aka yi miki kike wannan kukan?" Ta ƙarashe maganar tare da ɗago ta daga jikinta. Matashin dai kawai kallon su yake yi cikin tausayawa, yanda A'isha take ƙanƙame Inna yasa ya gane har lokacin a cikin firgici take. A hankali ya ɗan risina ya cewa Inna "Ina Yini?" Inna da ta manta ma A'isha tare suke da wani ta ɗago ta dube shi ta ce. "Lafiya ƙalau." Kallon shi Inna ta dinga yi ko kiftawa babu gabanta na fad'uwa, ƙasa ya yi da kansa ya miƙawa Inna jakar A'isha. Inna da duk zaton ta sabon Malami ne shi aka kawo a makarantarsu A'isha dan ko kusa bai yi kala da ƴan garin ba ta sauke ajiyar zuciya, cikin sanyin murya ta ce. "Mun gode sosai Bawan Allah, Allah ya saka da Alkhairi." Shafa kansa ya yi ya ce. "Babu komai Mama, bari na wuce na ji an shiga Sallah, akwai maganar da nake son mu yi dake idan babu damuwa sai na dawo gobe da safe mu yi in Allah ya kai mu." Inna ta da kasa ɗauke idonta daga kansa ta ce. "Babu damuwa ɗan nan, Allah ya kai mu goben lafiya." Ya amsa da Ameen, sannan ya yi mata sallama ya tafi, har ya fice daga soron Inna ta kasa ɗauke idonta daga kansa, kallon sa take yi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. Kama hannun A'isha ta yi wadda ke kuka har lokacin suka shige cikin gida, abun mamaki suna shiga Inna ta ga Ramatu ta bar bakin zauren da sauri ta shige cikin ɓangarensu har tana tuntub'e, ko tantanma Inna ba ta yi leken su take yi ta ga me suke yi a zauren jin muryar Namiji. Girgiza kai kawai Inna ta yi ta wuce. Tambayar duniya Inna ta yiwa A'isha akan me ya faru bayan sun zauna amma A'ishan ta ƙi faɗa mata, sai kuka kawai take yi. Gajiya ta yi ta kama yi mata faɗa, cikin takaici ta ce. "Wanne irin iskanci ne wannan A'isha? ina miki magana kin mayar da ni wata gantalalliya, sai kukan banza da kika sani a gaba kina yi, ki faɗa mun me ya samu fuskarki na ga kamar shatin hannu? Ina takalmanki kuma suke?" A'isha ta share hawayen fuskarta ta bawa Inna labarin duk abun da ya faru. Cikin tsananin tashin hankali Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, su waye waɗan nan azzaluman?" A'isha ta ce. "Ban san su ba nima." Inna ta fara hawaye ta ce. "Hasbunallu'wa ni'imalwakil, Allah ka shiga tsakanin mu da waɗan nan azzaluman da ba mu san ko su waye ba, Allah ka saka mana, Ubangiji karka ba su ikon cutar da wannan baiwa taka ko nan gaba. Allah na gode maka da ka kub'utar da ita. Wannan wanne irin abu ne, daga wannan sai wannan." A'isha ta ce. "Inna waye ya kawo ni gida? Ni ban gane muryarsa ba." Inna ta ce. "Ni ma ban san shi ba A'isha, da alama baƙo ne a cikin garin nan." A'isha ta shinshina jikinta ta ce. "Ɗan gayu ne ko Inna? Na ji yana ta ƙamshi mai daɗi, ni ma kin ji kayana suna yin ƙamshin ya shafa mun." Inna ta bi ta da kallo tana jinjina sha'anin k'uruciya, ban da haka ita da aka so yi mata fyaɗe har ta soma manta abun cikin ƴan mintuna ta fara sakin ranta. Kwanciya ta yi a jikin Inna cikin raunin murya ta ce. "Kaina ciwo, duk jikina ma haka musamman ƙafata da suka tattaka mun." Inna ta ce. "Allah ya saka miki, bari na ɗora miki ruwan zafi ki yi wanka sai ki ji daɗin jikinki, idan kika ci abinci kuma sai ki sha magani ki kwanta." A ɓangaren Matashin nan, yana fita cikin sauri ya nufi gidan Sarki dan yin alwala, a zaure ya tarar da su Ɗan_juma wanda suka iya tashi daƙyar suka fito. Wani mugun kallo ya watsa musu ya shige ɗakinsa. Hamza ya sauke numfashi ya dubi Ɗan_juma wanda ya bi bayan Matashin da wata muguwar harara ya ce. "Wai waye wannan ɗin ne Ɗan_juma da ya bazar da mu?" Harara Ɗan_juma ya banka masa ya ce. "Ban sani ba, ragwayen banza kawai, kuna gani yana auna mun naushi amma kuka kasa yi masa komai kuna kuku biyu sai ma ƙoƙarin guduwa kuka yi." Hamza ya ce. "Mu fa ba ragwanta ce ta saka muka yi yunk'urin guduwa ba, tsoron muke kar asirinmu ya tonu ya je ya faɗawa Sarki a hukunta mu." Ɗayan ya ce. "Ai har yanzu ma a cikin tsoron muke, tunda ba mu sani ba ko zai faɗa ɗin." Tsaki Ɗan_juma ya yi ya ce. "Wannan kuma ku ta shafa, dan ni ko a jikina, amma wallahi Wannan garan bai daki banza ba, sai na ɗauki fansar abun da ya mun." K'wafa ya yi ya fice daga zauren fuuuu kamar zai tashi sama, su Hamza suka mara masa baya. Daren yau gaba-d'aya Matashin nan da tunanin su A'isha ya yi shi manne a cikin zuciyarsa, ya rasa tausayi ne ko mene ne ya mamaye masa zuciya akan A'isha a gani ɗaya tak da ya taɓa yi mata yau a cikin rayuwarsa, hakan ya yi matuƙar ɗaure masa kai da ba shi mamaki ba kaɗan ba.....✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣0️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar

Chapter 6 of 20