da suka yi kaca-kaca ba ta fasa zuwa part ɗinsa ta kwana ba. Ba tare da ta ce masa komai ba ta tashi ta fita. Jikinta har rawa yake gurin nemo lambar Kaltum ta kira ta. Sai da ta yi mata kira uku sannan ta ɗaga cikin muryar bacci. A zaƙe Mommy ta ce. "Ina kika shiga ne haka?" Khaltum ta ce. "Bacci nake, me ya faru kike mini wannan kiran da sassafe?" Numfashi Mommy ta sauke ta ce. "Wata dama na ga mun samu akan barin yarinyar can daga gidan nan, za su je asibiti ne kuma Alhaji ya ce driver ya kai su, shi ne nake ganin ko mu haɗa baki da drivern ne ya ɓatar da ita?" Khaltum ta ce. "Wannan shawara ce mai kyau gaskiya, abin da za a yi ki fara kiran direban ku yi magana ki ce masa za ki ba shi lada mai tsoka, idan suna tafiya ya bi ta cikin layika ya ce mata saboda go slow, ni kuma zan turo waɗanda za su tare su, su sace yarinyar. Ki ce ya faɗa miki irin motar da za su hau da numbern ta"
Mommy ta ce. "Ta ina su waɗanda za ki turo ɗin za su san inda suke?" Khaltum ta ce. "Wanne asibitin za su je?" Mommy ta ce. "Na ji da Alhaji ya kira direban ya ce masa asibitin Makka dake b.u.k road." Khaltum ta ce. "Okay, za su jira shi a layin, zan turo miki address ɗin inda suka ce mini suke, sai ki faɗa masa ya bi ta gurin, zan kira su yanzu, na san ina faɗa musu za su tafi." Cikin matsanancin jin daɗi Mommy ta ce. "Da kyau khaltum, na rasa ma me zan ce miki saboda farinciki, kin gama mini komai da wannan tunanin naki, yarinyar nan mai siffar mayu ita kaɗai ce damuwata a yanzu." Khaltum ta ce. "Duk abin da zai saka ki farinciki a shirye nake na yi shi, ki kira direban tunda kin san waye, ni ma zan kira su yanzu." Mommy ta ce. "Shikenan sai kin ji ni."
Suna gama wayar Mommy ta aika aka kira mata ɗaya daga cikin direbobin gidan mai suna Buhari wanda Abba ya kira ya ce zai kai su A'isha Asibitin, bayanin aikin da take so ya mata ta faɗa masa tare da alƙawarin 500k cash bayan komai ya kammala. Da murna ya amince, don shi bai ga wahalar aikin ba, don dai bi ta cikin layika kawai ko a 100k zai yi balle 500k. kafin 7:30 su Mommy sun gama tsara komai yadda suke so.
Ummi tana kulle Bedroom ɗinta ta dubi A'isha dake kiciniyar saka hijabi ta ce. "Ki yi abu da jiki mana Nana, mun kusa yin latti fa, har takwas saura quarter fa yanzu. A'isha da take jin duk jikinta a sanyaye ba tare da ta san dalili ba ta ce. "Na rasa fuskar hijab ɗin ne." Ummi ta ce. "Sai fa da na saita miki zirawa kawai za ki yi amma kika tsaya wasa." Ta ƙarashe maganar tare karɓar hijab ɗin ta saka mata tare da kama hannunta suka nufi parking space. Buhari yana hango su ya washe baki tare da zira wayarsa da yake ƙara duba address ɗin inda za su haɗu da wanda za su ɗauke A'isha ya ce. "Sannu da fitowa Hajiya." Da fara'a Mommy ta ce. "Yawwa, an tashi lafiya?"
"Lafiya ƙalau" ya faɗa tare fitowa daga motar da nufin ya buɗe musu. Dakatar da shi Ummi ta yi da faɗin. "Bar shi Buhari." Risunawa ya yi cikin girmamawa ya ce. "Da kin bari na buɗe miki ranki ya daɗe." Kafin ya gama rufe baki har Ummi ta buɗe motar ta zira A'isha. Har za ta shiga sai kuma tuna ta ce masa. "Yawwa Buhari, idan mun dawo ni zan sauka a matan fada, ita kuma ka zarto da ita ka kai ta gidan Hajiya Zainab, nan maƙwabtanmu kusa da gidan da aka yi rasuwa. Ka ce mata in jini" Amsa mata ya yi tare da buɗe mazaunin direba ya shiga..........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*3️⃣1️⃣*
A hankali ya buɗe murfin Motarsa ya fito daga mazaunin direba. Ummi na ƙoƙarin rufe motar da suke ciki ta ji sassanyar muryarsa yana faɗin. "Ummi."
Dakatawa ta yi ganin ya nufo su, da fara'a ta ce. "Safwan, fita za ka yi ne?" A ladabce ya ce. "A'a, na ɗan fita ne ban jima da shigowa gidan ba, na zauna a cikin mota ne ina duba abu a waya." A gaggauce Ummi ta ce. "Ayya, mu ma nan asibitin za mu je yanzu, mun ma yi latti sosai." Yana gyara siririn white glass ɗin dake fuskarsa ya ce. "Wanne asibiti?"
"Makka."
Ɗan jim ya yi kamar mai nazari sannan ya ce. "Ki fito kawai na kai ku Ummi."
"A'a Safwan kar ka tashi kanka tsaye, ga Buhari nan zai kai mu, may be kana da wani uzurin kar na tsayar da kai."
"Babu komai Ummi, ku zo kawai mu je." Ya yi maganar tare da juyawa ya koma gurin motarsa.
Buhari dake sauraren su ya ji tamkar ya fasa ihu, addu'a ya shiga yi a ransa Allah ya sa kar Ummi ta amince. A'isha da ta yi lamo a jikin kujera tun lokacin da ta ji muryar Safwan ta sauke numfashi jin Ummi ta kama hannunta ta fito da ita. Cikin rawar baki Buhari ya ce. "Hajiya ku koma mana na kai ku, kar a wahalar da ƙaramin Alhaji, kin san bai fiya san tuƙi da kansa ba." Ummi ta ce. "Mun riga mun fito, kuma ai shi ya ga zai iya." Bin bayansu ya yi da kallo kamar mai shirin fashewa da kuka, takaici da baƙinciki suka hana shi ya ce musu Allah ya kiyaye kamar yadda suka saba kodayaushe idan sun ga wani a gidan zai fita.
Baya Ummi ta buɗe ta saka A'isha ita kuma ta shiga gaba. Buhari yana kallon su suka fice, ji yake kamar ya ruga da gudu ya je ya tsayar da Safwan ya roƙe shi ya bar shi ya kai su A'isha, 500k ɗin da aka masa alƙawari kawai yake tunani. Ya ga samu ya ga rashi. Sai a lokacin tunanin sanar da Mommy ya zo cikin kwanyarsa, cikin sauri ya rufe motar ya juya ya nufi part ɗinta.
Tana zaune a kan lallusar carpet na alfarma da ya kusa mamaye tsakiyar ɗakin tana karyawa Buhari ya fara knocking. Tsaki ta ja tare da faɗin. "Wannan daga ji wani matsiyacin ɗan ƙauyen ne, ai ta buga ƙofa ba jira kamar wanda aka yi wa sata." Ta ƙara jan tsaki sannan ta ɗaga murya ta kira Murja dake kitchen. Da sauri ta fito tana goge hannunta a jikin zaninta.
"Je ki ga waye yake mini wannan bugun haukan da farar safiyar nan." Ta faɗa a lalace. Amsa mata Murja ta yi ta nufi ƙofa. Baby dake saukowa daga kan steps cikin shirin tafiya school ta ja tsaki cikin yamutsa fuska ta ce. "Wai wanne mahaukacin ne a nan? An taho ana buɗewa amma ya ƙi daina cika wa mutune kunne." Rufe bakinta ya yi daidai da faɗowar Buhari parlour'n kamar wanda aka ingizo.
"Malam lafiya za ka shigo mana har cikin parlour ba tare da neman izini ba?" Baby ta faɗa a wulaƙance cikin daka tsawa tana jifan shi da wani shegen kallo. Ƙasa ya yi da kansa a ladabce ya ce. "Gurin Hajiya na zo." Mommy da take masa kallo mai cike da tarin tambayoyi ta ce. "Na san da zuwansa, bar shi ya ƙaraso." Cikin mamakin yadda ta yi magana ba hargagi kamar yadda ta saba yi wa ma'aikatan gidan Baby da Murja ke kallon ta, don hakan baƙon abu ne a gurinsu. Fita Baby ta yi bayan ta mata sallama, a ranta tana tambayar kanta abin da zai haɗa Mommy da Buhari. Murja ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta koma kitchen ta cigaba da abin da take.
"Ina sauraren ka Buhari, me ya dawo da kai?" Mommy ta faɗa cikin son jin abin da ke tafe da shi.
Numfashi ya sauke ya ce. "Ranki ya daɗe an samu matsala, don Alhaji ƙarami ne ya tafi ya kai su asibitin." Cikin rashin fahimta ta ce. "Ban fahimci me kake nufi ba, wanne Alhajin ƙaramin?"
"Na ki Hajiya." Buhari ya faɗa tare da ba ta labarin yadda aka yi.
A zabure Mommy ta miƙe ta wanka masa mari a kuncinsa dama da hagu. Dafewa ya yi cikin sauri tare da kallon ta, cikin masifa ta ce. "Wanne irin mara lissafi da hankali ne kai? Tun lokacin da ya zo yana musu maganar ba ka kira ni ba ko da a waya ne sai yanzu bayan sun tafi?" Ƙasa ya yi da kansa tare da yin ɗurƙuso kamar mai shirin yi mata sujjada ya ce. "Allah ya huci zuciyarki Hajjaju makkatu, ban yi tunanin za su shiga motar tasa ba ne." Jijjiga kai ta yi tana jin kamar abincin da ta ci zai dawo mata ta kai saboda tashin hankali, baƙicikinta biyu ne, wargazewar da shirinsu ya yi da kuma kai su Ummi asibiti da Safwan ya yafi. Rasa ma abin cewa ta yi saboda tsananin ɓacin rai. Juyawa ta yi ba tare da ta kuma magana ba ta nufi gurin wayarta don kiran Safwan ta sanar masa ya juye su Ummi ko a tsakiyar titi ne ya dawo gida. Ganin haka ya saka Buhari tashi ya fice hannunsa da dafe da kuncisa. A ransa yana Allah wadai da rashin wadatar zuci da kwaɗayi, don su suka janyo masa shan wannan tagwayen marukan a gurin matar da ba ta fi sa'arsa ba. Ga shi ya yi ba wan ba ƙanin.
Sai da suka hau titi Safwan ya dubi Ummi ya ce. "Ina kwana." Ummi ta ce. "Lafiya ƙalau, ya aiki?" Ya ce "Alhamdulillah."
"Yau ka je aikin kenan?
Ya ce. "A'a, ban koma ba sai this coming Monday in sha Allah, saƙo Mum ta aike ni na kai mata gidan wata friend ɗinta." Gyaɗa kai Ummi ta yi tare da juyawa baya ta kalli A'isha da ta tsit kamar ba ta Motar, ta ce. "Nana ba ki gaishe da Yayanku ba." Numfashi ta sauke cikin sanyin murya ta ce. "Ina kwana." Ya amsa da "Lafiya." A taƙaice. Ba ta kuma magana ta mayar da idanunta ta lumshe, ƙamshinsa da ya kama motar da sanyin ac na ratsa ta. A lokacin kiran Mommy ya shigo wayarsa, dubawa ya yi, ganin ita ce ya ƙi ɗauka don ya san kwanan zancen. Ita kuma sai kira take ba ƙaƙƙautawa. Ganin haka ya sa Ummi ta ce masa. "Ka ɗaga kiran da ake maka mana." Yana sauke numfashi ya ce. "Mommy ce, idan muka ƙarasa zan kira ta."
A matuƙar hasale ta janye wayar daga kunnenta ta mayar da akalar kiran ga Khaltum. Ringing ɗaya ta ɗaga tare da faɗin. "Su Caska sun kira ni, wai har yanzu ba su ƙarasa ba." Kamar Mommy za ta yi kuka ta ce. "Ai komai ya wargaje Khaltum, wai Safwan ne ya tafi kai su."
"What? Safwan kuma? A kan me? Ko uban ne ya ce ya kai su?" Cikin ɗunbun baƙin ciki Mommy ta ce. "Ina fa? A yadda Buhari driver ya ce mini wai shi ya ce su fito ya kai su da kansa, tun ba yau ba nake faɗa matar nan fa ta asirce mini ɗa, tun yana rarrafe idan na aika aka ɗauko mini shi daga gurinta sai ya ƙara rarrafawa ya koma, na rasa yaya zan yi matar nan ta bar mini ɗana." Khaltum ta ce. "Kar ki damu Saratu, Gobe zan je gurin na kan tudu, zan saka a yi musu farraƙu, wannan duk ba wata matsala ba ne. Damuwata yanzu wargajewar aikin nan wallahi. Amma kuma ai kin faɗa mini likitar da ta yi wa yarinyar gwaje-gwaje last time da suka je kin san ta ko? Ta kira ni ta faɗa miki." Mommy ta ce. "Eh, ƙanwar Hajiya Zubaida ƙawata ce, tunda suka je ta gan su take kira na a waya ba ta same ba, sai bayan kwana biyu take faɗa mini." Khaltum ta ce. "To ai ta kwana gidan sauƙi, me zai hana mu haɗa baki da ita a ƙara lalata idon yarinyar." Murmushi Mommy ta yi ta ce. "Maganar da muke yi da ita kenan, don ta sanar mini tana sane ta ce su dawo bayan sati ɗaya saboda su zo ranar dutinta, ita duk ɗaukar ta ma Yarinyar Mufeedah ce." Khaltum ta ce. "Ni ma farko da na ga Yarinyar ranar da na zo na ɗauka ita ce, saboda suna kama sosai." Haka kawai Mommy ta ji gabanta ya faɗi da ta hasaso fuskar A'isha a cikin ranta, don ba ƙarya aka yi ba suna yanayi da Mufeedah ƴar Ummi. Kalar da fatarsu da girman jikinsu ɗaya. Taɓe baki ta yi ta ce. "Su suka sani, yanzu dai zan kira Doctor Zulaihat ɗin, duk yadda muka yi da ita za ki ji." Khaltum ta ce. "Ina sauraren ki." Daga haka suka yi sallama. Zama Mommy ta yi a kan kujera tare da dafe kanta, ta rasa me ya sa A'isha ta tsaya mata a rai, ba iya ƙin ta da take mata na talauci ne kawai ya sa ba ta son zamanta a gidan ba, har na fargabar da take ziyartar ta a duk lokacin da ta tuna da yarinyar ba tare da ta son dalili ba, shi ya sa ta damu ta bar gidan, saboda ko ma mene ne idan ta tafi shikenan.
Wani balaraben doctor suka samu yau, ya duba A'isha ya ƙara yi mata text a idon sannan ya ce su jira shi. After 1 hour ya fito da result ɗin abin da ke damun idon ya ba su bayan ya yi wa Ummi bayanin yadda yake. Ya ƙara da ce mata aiki za a yi wa idanun, ya faɗa mata kuɗin aikin tare da ba ta takardar da za a biya kuɗin. Farinciki sosai Ummi ta yi, tare da addu'ar Allah ya sa a yi aikin cikin nasara. Safwan yana mota suka fito hannunta riƙe da na A'isha. Tana buɗe baya za ta saka A'isha ta ce. "Safwan I'm sorry, na tsayar da kai kana ta jira." Murmushi ya yi ya ce. "Haba Ummi, babu komai ai." Takardun hannunta ta miƙa masa ya karɓa ya duba, bayan Ummi ta shiga front seat ta ce. "Daɗina da Asibitin nan komai nasu babu ɓata lokaci, idan muka yi payment a gobe cikin satin nan ma za su iya yi mata aikin." kallon A'isha ya yi ta madubi, ba tare da ya ɗauke idonsa daga kanta ba ya ce. "Allah ya sa a yi a sa'a." Ummi ta ce. "Amin, ka kai mu gidan Ruƙayya kawai mu ajiye ta a can, sai mu wuce ka sauke ni a school." Gyaɗa mata kai ya yi tare da kunna motar.
Aunty Ruƙayya tana sharar parlour suka shiga da sallama. Amsa musu ta yi tare da faɗin. "Sannun ku da zuwa, tun ɗazu nake dakon zuwan ku, na san yau ce ranar dawowar ku asibiti." Ummi ta zauna tare da faɗin. "Kuma da ba za mu zo nan ɗin ba wucewa za mu yi."
"Saboda me?"
"Kawai, har na cewa driver ya kai ta gidan Hajiya Zainab ta zauna kafin na dawo daga school, da ke kwana biyu can nake kai ta idan zan fita."
Aunty Ruƙayya ta ce. "Da ba ki kyauta mini ba kuwa."
"Ina kwana Aunty." A'isha ta faɗa cikin sanyinta."
"Lafiya ƙalau Mamana, ya fuska?"
"Alhamdulillah."
Ummi ta ce. "Cikin satin nan za a yi aiki ma in sha Allah." Aunty Rukayya ta ce. "Masha Allah, Allah ya sa a yi a sa'a." Suka amsa da Amin. Ummi ta ba ta takardun ta duba tare da faɗa mata yadda suka yi da likitan. Aunty Ruƙayya ta ce. "Haka na san asibitin Makka ba su da wasa, kana zuwa ana duba ka za a saka maka ranar aiki idan ciwon na aiki ne, shi ya sa na yi mamaki da kika ce an ba ku har 1 week ku dawo karɓar result." Ummi ta ce. "Ni ma na yi mamaki, har Abbansu sai da na yi wa complain, ya ce to ya za mu yi tunda haka suka ce." Aunty Ruƙayya ta ce. "Haka ne." Miƙewa Ummi ta yi tana duban A'isha ta ce. "Zan wuce Nana, Khalifa ko driver za su zo su ɗauke ki." Gyaɗa mata kai ta yi a hankali ta ce. "Allah ya kiyaye." Ummi ta ce. "Amin." Tare da juyawa ta fita, Aunty Ruƙayya ta bi bayanta don yi mata rakiya. Ajiyar zuciya ta sauke tana jin yadda tsoron aikin da aka ce za a mata ya cika mata zuciya, gani take kamar ko an yi aikin idon ba zai buɗe ba. Amma tana addu'ar Allah ya sa a yi cikin nasara, ita ma ta cigaba da gani kamar kowa. Numfashi ta sauke tana tuno mutane masu ƙololuwar daraja a cikin rayuwarta, wanda suke fata da burin ganin ranar barin ta daga makanta. Inna ce farko, wadda Ubangiji ya rubuta ba za ta ga wannan ranar ba, sai Umar da ba za ta taɓa mantawa da shi a cikin rayuwarta ba, duk da abin da take ji a kansa a cikin zuciyarta kaso mai yawa ya ragu, amma duk da haka ba za ta manta da Alkhairinsa ba, sai Innar Ma'u da ita kanta Ma'un, su kuma ba ta san a ina za ta gan su ba.
Lokacin da Safwan ya koma gida Mommy ba ta nuna masa ɓacin ranta ba a kan kai su Ummi asibiti da ya yi, saboda tsananin so da ji da shi ɗin da take ya sa ba ta iya yi masa faɗa. Sai dai tay ta zagin Ummi a gabansa tana cewa ba ƙaunar shi take ba, lunbu-lunbu take masa take jan shi a jiki, cikin ranta kuma tana da wani mugun nufin a kansa. Shi dai ba ya tanka mata idan tana maganganunta.
Salma na tsaye a gaban mirror tana kwalliya, wayarta dake kan mudubin ta fara ruri. Ɗauka ta yi ganin Fadeela ce tare da faɗin. "Ba dai har kun shirya ba?" Fadeela ta ce. "Tun yaushe? Ke kaɗai muke jira." Cikin fariya ta ce. "No ku wuce kawai ba sai kun jira ni ba, Mine ne zai kawo ni." Baƙi Fadeela ta taɓe ta ce. "Ok." Tare da katse kiran.
Ihsan tana koya A'isha karatun Alkur'ani a baranda Safwan ya shigo gidan. Tun kafin ya ƙaraso inda suke ƙamshinsa ya ziyarce su. Da sauri A'isha da ta san me ƙamshin ta ɗago kanta duk da gani take ba. Sallamarsa cikin kaushin murya ta saka Ihsan ɗagowa ta dube shi, cikin girmamawa ta ce. "Sannu da zuwa."
"Yawwa." Ya amsa idanunsa a kan wayarsa dake hannunsa. Miƙewa Ihsan ta yi tana faɗin. "Yayanku ya zo daukar ki, bari na sanar da Mami." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi tare da yin ƙasa da kanta. Kamar mai tsoron magana ta ce. "Ina yini?" Duk da ya san da shi take amma ko ɗagowa bai yi ba balle ya amsa. Ɓata fuska ta yi don ta tsani ta yi wa mutum magana ya ƙi amsawa, yadda ƙamshinsa ya cika mata hanci ta san yana kusa da itan da idan ta yi magana zai ji. Dawowar Ihsan da Aunty Ruƙayya ya sa ta sakin ajiyar zuciya, don duk jin ta take a takure kasancewar su kaɗai a guri ɗaya.
"Safwan kai ta kuma tasowa?" Cewar Aunty Ruƙayya tana duban shi.
Murmushi ya yi ya ce. "Ina yini?" Ta ce. "Lafiya ƙalau." Tare da mayar da duban ta ga Ihsan ta ce. "Kama hannunta ki raka su mota, kin ɗauko mata saƙonta dai ko?" Ihsan ta ce. "Eh gasu nan." Ta kama hannun A'isha da ta miƙe tsaye. Aunty ta ce. "To Mamana, ku gaida gida."
"Zai ji in sha Allahu, na gode Aunty."
Tunda Ihsan ta saka ta a mota ta sunkuyar da kanta ba ta ɗago ba, shi kuwa dama ko kallon inda take bai yi ba, driving ɗinsa kawai yake. Lokaci zuwa lokaci yana duba wayarsa da kira ke shigowa ba ƙaƙƙautawa.
Tsaki Salma ta ja karo na babu adadi ta dubi Baby da za su fita tare ta ce. "Wai ina Mine ya shiga ne? Ina ta kiran shi ya ƙi ɗauka, kuma ya san zai kai ni unguwa yanzu, na faɗa masa fa." Baby ta ce. "May be driving yake shi ya sa bai ɗaga ba." A fusace ta ce. "Amma ai ko parking sai ya yi ya ɗaga kira na, idan mun gama wayar ya cigaba." Kallon mamaki Baby ta mata, a ranta tana faɗin. "Sannu Mommy." Amma a fili ba ta yi magana ba, sanin halin masifar Salman sai ta huce a kanta. Ganin har biyar ta wuce bai dawo ba bai kuma ɗaga kiran ta ba ya sa ta miƙewa a ƙufule ta nufi parking space da nufin ta tafi kawai a motarta, ta gaji da jira, kuma ta san zuwa yanzu an kusa gama birthday ɗin da za ta. Amma fa ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, saboda ta gama cin burin Safwan ne zai kai ta, ya buɗe mata mota a gaban ƙawayenta, ta nuna musu yanzu a tafin hannunta yake. Tana ƙarasawa parking space ɗin motarsa na shigowa, ko bari ya gama parking ba ta yi ba ta nufi inda suke a fusace tare da saka hannu ta kama murfin motar na front seat.........✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
*_Zeey Kumurya_*
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*3️⃣2️⃣*
"Aunty Salma." Baby dake bin ta a baya ta kira sunanta.
Tsayawa ta yi tare da juyawa ba tare da ta buɗe motar ba.
"Mene ne?" Ta faɗa a zafafe.
Baby ta ce. "Stain na ga kin yi, kuma na san ba ki sani ba." Cikin takaici ta ce. "What?" Tare da fara dudduba jikinta. Tsaki ta ja ganin yadda jikinta ya ɓaci da jini ta gurin zama. Kamar za ta fashe da kuka ta juya ta koma ciki, bin bayanta Baby ta yi don ita ta yanke ta ma fasa fitar.
Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ya sauke wadda ta sa A'isha ɗagowa da sauri ta kalli saitin da yake kamar mai ganin shi. Ƙura mata ido ya yi na wasu sakanni sannan ya sauke numfashi, lokaci ɗaya kuma ya haɗe rai. Jan motar ya yi ya ƙarasa har kusa da part ɗin su Ummi. Ba tare ya yi magana ya fita ya buɗe ɓarin da take. Duk da bai yi magana ba amma motsin buɗe ƙofar ya sa ta yunƙurawa ta fito tana laluben hanya da hannunta. Mayar da ƙofar ya yi ya rufe. A hankali ta ce. "Na gode." Ko kallon ta bai yi ba ya koma cikin motar ya bar ta da zullumin yadda za ta iya shiga ciki. Daidai lokacin Lubna ƴar Hajiya Zainab ta fito daga ciki. Da mamaki ta ce. "Nana dana ina na gan ki ke kaɗai?" Cikin jin daɗi ta ce. "Ba ni kaɗai ba ce, yanzu aka sauke ni." Kallon motar Lubna ta yi ta ƙaraso ta kama hannunta suka shiga ciki. Da mamaki Ummi ke Kallon su har suka zauna. Tana duban A'isha ta ce "Wa ya dawo da ke? Yanzu nake ƙoƙarin kiran Khalifa na ce masa ya biya ya ɗauko ki." A'isha ta ce. "Wanda ya kai mu ne." Cikin ɗaurewar kai Ummi ta ce. "Safwan?" Gyaɗa mata kai ta yi.
Ummi ta ce. "Ikon Allah, to an gode masa."
Tana saka wani kayan ya shiga ɗakin. Murya ƙasa-ƙasa ya yi sallama. Wani kallo ta wurga masa mai haɗe da harara, ba tare da ta amsa masa sallamar ba ta ce. "Ina ka je?" Cikin danne tsoron da yake ransa ya ce. "Abba ne ya aike ni, kafin na ƙarasa inda zan je muka samu accident na buge wasu." Ɗauke idonta ta yi daga kansa ta ce. "Daga nan kuma sai yaya?"
"Hospital na kai su aka yi musu duk abin da ya dace, lokacin da kikkira wayar tana mota na bar ta a ciki." Cikin gamsuwa ta ce. "Amma da ka kai su Hospital ɗinka yaranka sun kula da su ai, tunda ka san you keep me waiting."
"I'm sorry." Ya faɗa cikin sauke ajiyar zuciya tare da hugging ɗinta.
Da daddare Ummi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 20