Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hak'uri zan ci." Sallamar Umar ta katsewa Inna maganar da take son yi. Cikin fara'a ta amsa masa tare da yi masa maraba sannan ta bashi gurin zama. Bayan sun gaisa ta shige ɗaki ta bar su tare da A'isha. Idanunsa a kanta ya ce. "Humairah!" Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana jin wani abu da ya cika mata zuciya mara daɗi yana gushewa. Kanta a ƙasa ta ce. "Na'am." Matsowa ya yi kusa da ita so closely, cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce. "Me yasa kike kuka?" Kansa ta nuna masa da hannunta ba ta ce komai ba. Ya ce. "Me na yi?" Cikin sanyin murya ta ce. "Ba jiya ne ka ƙi dawowa ba." Numfashi ya sauke cikin damuwa ya ce. "I'm sorry, wani abu ne ya tsayar da ni." Gyaɗa masa kai ta yi a hankali. Cikin rarrashi ya ce. "To ki daina kukan tunda na zo yanzu, ki ci abinci kuma ko in tashi in tafi." Da sauri ta ce. "Zan ci, amma dan Allah Ya Umar karka ƙara ƙin dawowa, ka ga bani da abokin hira sai kai, ita Inna sai dai tay ta mun faɗa." Kasa magana ya yi saboda wani irin tausayinta da ya kanainaye masa zuciya, iya jiya kaɗai da bai dawo ba ta shiga cikin damuwa ina ga ya tafi gaba-d'aya? Yaya zata ji idan ya ce mata yau zai tafi baza ta ƙara ganin shi ba? Ta ina zai fara faɗa mata wannan maganar? Cikin nutsuwa ta fara cin abincin duk da ba wani daɗinsa take ji ba, dan dai ba ta son Umar ya ƙara tafiya ya bar ta ne. Kaɗan ta ci ta ce ta ƙoshi, bai matsa mata ba akan sai ta ƙara ci ba ya ƙyale ta. Inna ta fito za ta cigaba da ayyukanta Umar ya dube ta ya ce. "Mama yau da safen nan fa zan tafi gida." Shi kansa da ya yi maganar sai da ya ji wani iri, balle kuma Inna da ta sandare a guri ɗaya cikin mamaki. A'isha kuwa ji ta yi zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske. Cikin al'ajabi Inna ta ce. "Wanne gidan? Ba dai can garinku ba?" Cikin ƙoƙarin ganin ya b'oye damuwarsa ya ce. "Can Mama." Inna ta ce. "Ikon Allah, kuma shine Umar saboda Allah sai yau ɗin zaka faɗa mana?" Ya ce. "Mama tafiyar ce ta kama ni babu shiri, kiran gaggawa aka mun a gida." Inna ta ce. "Too, in ce dai lafiya?" Ya ce. "Lafiya ƙalau, akan harkar karatuna ne." Inna ta ce. "Allah Sarki, in ka tafi sai yaushe kuma?" Murmurshin yaƙe ya yi wanda ya fi kuka ciwo ya ce. "Zan dawo nan kusa Insha Allahu." Inna ta jinjina kai cikin tsananin mamakin abun ta juya ta koma ɗaki. A'isha da ta kame kamar status ta sauke numfashi ta ce. "Yaya Umar ina zaka tafi? Tafiya zaka yi ka barni?" Hannunta ya kamo ya ce. "Wa ya faɗa miki zan iya barin ki Humairah? Ina tare dake a kodayaushe." Ta k'wace hannunta cikin damuwa ta ce. "Gashi nan kacewa Inna zaka tafi gida yau." Ta fara hawaye ta ce. "Dan Allah Yaya Umar karka tafi ka barni, ka ga kai kaɗai ne abokina, idan ka tafi da wa zan dinga hira da karatu?" Runtse idonsa ya yi yana jin yanda zuciyarsa ke yi masa suya, ba zai iya jurarar ganin ta cikin damuwa ba, dan haka ya ce. "Shikenan na fasa tafiyar." Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta shiga share hawayen fuskarta, baiwar Allah, har cikin zuciyarta ta yarda ya fasa tafiyar. Haɗe_haɗen su Daddawa da kuka da lalle Inna ta haɗawa Umar cikin wani ƙaramin buhu a matsayin tsaraba ta fito masa dashi tsakar gida. Yana zaune suna hira da A'isha har 11 ta wuce, kasantuwar su tare sai ya sanyaya masa zuciya ya mantar da shi damuwar da yake ciki. Suna cikin hirar aka kira shi a waya, d'agawa ya yi ya ji muryar Ado driver, bayan sun gaisa ya sanar masa ya ƙaraso cikin garin Kumurya yana ƙofar gidan Sarki. Wata irin bugawa ya ji zuciyarsa ta yi, lokaci ɗaya ya ji mood ɗinsa ya sauya, shikenan dagaske dai tafiya zai yi ya bar A'ishansa. Ba tare da ya bari ta gane halin da yake ciki ba ya miƙe ya fita bayan ya ce mata yana zuwa zai je ya dawo...........✍️ _*Ku yi hak'uri da wannan ina cikin sha'anin biki ne, ko editing ban yi ba*_ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣6️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Yana zuwa ya tarar da Sarki da Ado driver zaune a soron gidan Sarki suna hira, an kawowa Ado driver ruwa da abinci. Zama ya yi suka gaisa da Ado driver cikin mutunta juna. Wajen ƙarfe sha biyu Umar ya koma gidansu A'isha, lokacin an gama zuba komai nasa a cikin Mota, sun yi sallama da su Sarki, tafiya kawai za su yi. A inda ya bar A'isha a nan ya tarar da ita a zaune ta yi tagumi, Inna na zaune a gefen ta ita ma duk jikinta a sanyaye. Bayan ya yi sallama sun amsa masa sai ya rasa mai zai ce, tsawon minti biyu yana tsaye ya dai daure cikin sanyin murya ya ce. "Mama za mu wuce." Inna ta miƙe ta ce. "To Allah ya kiyaye ya kai ku lafiya, ga kayan ba ka ɗiba ba kuma." Idanunsa akan A'isha ya ce. "Idan zan fita zan tafi da su, an gode sosai Allah ya saka da Alkhairi." Inna ta ce. "Mu ne da godiya Umar, ka yi mana abun da babu wanda ya taɓa yi mana kamar shi a cikin rayuwarmu, ka taimake mu a lokacin da muke tsananin buƙatar neman taimako, Allah Ubangiji ya biya ka, ya raba ka da iyayenka da duniya da mutanen cikinta lafiya, Allah ya saka maka da gidan Aljannah ya baka mace ta gari." Ya ce. "Ameen." Tare da zaro waya keypad daga cikin aljihunsa ya miƙawa Inna ya ce. "Mama ga ƙaramar wayata nan akwai sim a ciki, insha Allahu idan mun ƙarasa zan kira ku ta cikinta." Inna ta ƙi karɓa ta ce. "A'a Umar, ka cigaba da amfani da abar ka, ya za'a yi ka bani wayarka?" Umar ya ce. "Bana wani amfani da ita sosai ne, dan Allah ki karɓa Mama kar ki ce a'a, akwai memory a ciki mai ɗauke da karatun Alqur'ani, sai ki dinga kunnawa Humairah tana saurara." Inna ta ɗan yi jim sannan ta saka hannu ta karɓa tare da yi masa godiya. Ganin yanda hankalinsa gaba-d'aya yake kan A'isha sai ta shiga ɗaki ta ba su guri. Tsugunnawa ya yi a daf da ita ya kama hannunta ya ce. "I'm sorry Humairah, ban san me zance miki da zaki fahimce ni ba, amma wallahi ba dan son raina zan tafi in bar ki ba." Ya ƙara damk'e hannunta sosai a cikin nasa ya ce. "Gida zan tafi gurin ahalina, amma duk watannin da na shafe ban gan su ba kewar ki da na fara ta saka ba na murna da d'okin ganin su, Please Humairah dan Allah kar ki saka kanki a cikin damuwa saboda tafiyata, zan dawo gare ki insha Allahu, ko dan na cika alƙawarin da na ɗaukarwa kaina na nema miki lafiya." Wani irin yanayi A'isha ta tsinci kanta a ciki wanda ba zai misaltu ba, duk saurin kukanta sai ta nemi ko d'igon hawaye ta rasa a idonta. A hankali ta kamo ɗayan hannunsa cikin magana daƙyar ta ce. "Dagaske tafiya zaka yi Yaya Umar? Ashe ba zan taɓa ganin ka ba a rayuwata? Dan Allah ka ce mun mafarki nake yi ba gaske ba ne zaka tafi ka bar ni." Kasa magana ya yi saboda yanda kalamanta suka gusar da guntun dauriyar da yake da ita. Cikin raunin murya ya ce. "Ki yi hak'uri, shine kawai abun da zan iya ce miki." Girgiza kai A'isha ta shiga yi ta fashe da wani marayan kuka mai karya zuciyar mai saurare, da sauri Inna ta fito daga ɗaki tana tambayar ba'asi. Hakan ya saka Umar zare hannunsa daga nata ya miƙe tsaye. K'afufuwansa A'isha ta rungume cikin matsanancin kuka ta ce. "Dan Allah Yaya Umar kar ka tafi ka bar ni!" Runtse idonsa ya yi cikin ƙoƙarin mayar da ƙwallar da ta tarar masa a ido, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi da k'una. Inna ce ta zo ta janye A'isha daga jikinsa, cikin rarrashi ta ce. "Mene haka A'isha? Wannan wanne irin kuka ne? So kike ki karya masa zuciya zai tafi ya ga ahalinsa ya fasa saboda ke? Ai dama ko mun daren dad'ewa kin san zai koma tunda ba'a nan yake ba." Kamar zai fashe da kukan shi ma ya zaro kuɗi ya ajiye a ƙasa yana duban Inna ya ce. "Mama dan Allah ki kai ta asibiti da wannan kuɗin a duba a ga abun da ya samu idanun nata, in ya so duk yanda ake ciki sai ki sanar mun ta waya." Inna ta ce. "A'a Umar ba za mu yi haka ba, gaskiya ba zan karɓi wannan kuɗin ba, d'awainiyar da ka yi da mu a baya ma ta isa, Allah ya saka da Alkhairi." Dafe kansa dake sara masa ya yi ya ce. "Dan girman Allah Mama ki yi hak'uri ki karɓa, idan kika ƙi karɓa ba zan ji daɗi ba." Inna ta ce. "Amma Umar......" Ya marairaice ya ce. "Dan Allah Mama." Inna ta ce. "Shikenan." Ta shiga yi masa godiya tare da kwararo masa tarin addu'oi. Idanunsa akan A'isha dake gunjin kuka ya ce. "Humairah zo ki ji." Inna ta zare ta daga jikinta ta ƙarasa ta ɗauki kayan da ta haɗa masa ganin ba ta su yake ba kar ya manta ta nufi ƙofar gida da su. Takawa ya yi zuwa inda Aisha take ya ɗago kanta yana kallon fuskarta dake jik'e da hawaye ya ce. "Please ki bar kukan nan Humairah, da kin san yadda nake ji a cikin zuciyata da ba za ki bar d'igon hawaye ya fito daga cikin idonki a gabana ba, na faɗa miki zan dawo nan kusa Insha Allahu." Tana sheshshek'a ta ce. "Ai na san ba dawowa zaka yi ba." Ya ce. "Zan dawo mana, amma idan kin daina kukan nan, idan baki daina ba ba zan dawo ba." Duk yanda kukan ke cin ta haka ta haɗiye shi ta daina jin abun da ya faɗa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗauko handkerchief ɗinsa ya shiga share mata hawaye. K'uri ta yi masa idanunta a cikin nasa saboda kafen ta da ya yi da ido, wani numfashi ya sauke mai zafi ya shafi saman idanunta ya ce. "Allah ya baki lafiya My Humairah." Ba ta ce komai ba dan tana buɗe baki kuka ne zai biyo baya. Kama hannunta ya yi suka fita waje cikin yanayin damuwa. A bakin Mota ya tsaya ya ɗan rank'wafa ya kai bakinsa dai_dai kunnenta ya ce. "SAI WATA RANA HUMAIRAH! I will miss you so much." Wani kuka A'isha ta fashe da shi ta rungume shi, so take ta yi magana amma ta kasa. Hansai dake tsaye tana lek'en su ta tafa hannuwa tare da fasa salati ta yi cikin gida cikin gudu_gudu tana cewa. "Jama'a yau na ga abun da ya ishe ni bai ishi Allah ba, karuwanci har ƙofar gida a gaban Uwa da bainan nasi, Jama'a ku fito ku ga ikon Allah." Inna dake tsaye ta yi saurin ƙarasawa ta b'anb'are A'isha daga jikin Umar daƙyar ta yi cikin gida da ita ganin har an fara taruwa a gurin kamar wani babban abun ne ya faru. Umar ya bi su da kallo wasu hawaye masu ɗumi suka zubo akan kuncinsa, saurin goge su ya yi ya buɗe front seat cikin mawuyacin hali da k'uncin zuciya ya shiga ya zauna. Ado driver dake kallon sa ya girgiza kai cikin tausayawa ya kunna Motar. Umar ya ɗago kansa daƙyar ya yiwa gidansu A'isha kallon ƙarshe, har lokacin sautin kukanta bai gushe daga cikin zuciya da kunnensa ba, kuma ya san har abada ba zai taɓa gushewa ba. Lumshe idonsa ya yi a hankali lokacin da ya ji Ado driver ya ja Motar sun fara tafiya. "I loose her." Ya faɗi hakan a cikin zuciyarsa. Wunin yau gaba-d'aya cikin kuka A'isha ta yi shi, ba ta taɓa tsintar kanta a cikin damuwa da tashin hankalin zuci irin wannan ba a rayuwarta. Ko lokacin tafiyar su Ma'u ba ta ji abun da take ji ba yanzu a cikin zuciyarta. Ta kasa yardar wa kanta Yaya Umar ɗinta ya tafi, ta kasa yarda ba za ta gan shi anjima ba, ta kasa yarda idan ta tashi gobe da safe ba za ta gan shi ba, ta kasa yarda ya tafi ya bar ta, gani take duk k'arya ne ko kuma mafarki take yi zata farka. Inna ma duk jikinta babu daɗi haka take jin sa, ga tausayin A'isha ga kuma kewar Uwar da za su yi, dan sabo ba k'arya ba ne, ko dabba ce da kai kuka rabu sai ka ji babu daɗi na rashin ganin gilmawarta balle Mutumin ya nuna maka k'auna a lokacin da kowa yake gudun ka, ya ja ka a jiki ya nuna maka kai ma wani ne, kai ma mutum ne mai daraja kamar kowa. Ya fitar da kai daga cikin halin k'unci da matsi na rayuwa. Da Magriba A'isha tana kwance akan gado zazzaɓi mai zafi ya rufe ta Inna ta shigo ɗakin dan yin Sallah, kallon inda take ta yi ta ce. "Za ki iya ki yin Sallah kuwa?" Girgiza mata kai ta yi. Inna ta ce. "Allah ya ƙara sauƙi, bari na yi Sallah na baki magani ki sha, sai ki daure ki yi Sallar." Hawaye kawai A'isha take yi, wani irin zafi da ciwo take ji a ƙirjinta, ga ciwon kai da ciwon ciki da ya bijiro mata lokaci ɗaya, ga sanyin da take ji yana shiga cikin ƙasusuwan jikinta, ga idanuwanta dake mata zafi saboda kukan da ta sha, ta rasa ina ma za ta saka ranta ta ji daɗi. Ajiyar zuciya kawai take saukewa akai_akai. Bayan Inna ta idar da Sallah ta zo ta ɗaga ta, ta zaunar da ita tana yi mata sannu, ragowar wani yoghurt da Umar ya kawo mata ta ɗauko. Cikin lallami ta ce. "Ki sha wannan sai ki sha maganin." Kawar da kai ta yi ta ce. "Ba zan iya sha ba Inna, cikina ciwo yake mun." Inna ta ce. "Yunwa ce, yau fa kwata_kwata ba ki ci abinci ba, ki sha wannan ɗin zaki ji daɗi." Daƙyar Inna ta samu A'isha ta ɗan kurb'i yoghurt ɗin ta koma ta kwanta. Inna tana shafa kanta ta ce. "A kullum ina faɗa miki ki dinga hak'uri da rayuwa a duk yanda ta zo miki A'isha, ki yi hak'uri ki cire damuwar tafiyar yaron nan daga cikin ranki, kar wani ciwon ya kama ki." Cikin rawar murya ta ce. "Shikenan fa ba mu da kowa a cikin garin nan, yanzu za'a cigaba da zaginmu da yi mana rashin mutunci tunda mai tare manan ya tafi." Inna ta ce. "Muna da Allah, a lokacin da su Ma'u suka tafi haka kike ce, bayan tafiyarsu babu jimawa kuma sai Allah ya aiko mana da Umar, to yanzun ma shi zai taimake mu ya ba mu yanda zamu yi, ki daure zuciyarki ki cire komai na damuwa daga cikinta, ko zaki samu ki ɗan yi bacci zuciyarki ta huta." Lumshe ido kawai ta yi, amma ta san yau duk iya satar bacci ba zai ɗauke ta ba, dan ba ta da nutsuwar yin sa ko kaɗan. Washegari ta tashi jikin nata da ɗan sauƙi, ta kuma daure iya iyayinta dan ganin ba ta yi kuka ba, saboda kar ta tayarwa da Inna hankali. Tun safe Matan gidan suke zarga a ɓangarensu suna yada musu maganganu da habaici akan tafiyar Umar, daga mai shigowa da shewa sai mai shigowa tana gud'a. Inna dai ko kallon inda suke ba ta yi, balle kuma A'isha da ta ji zaman garin gaba-d'aya ya ƙara fice mata a rai. Jiya wajen goma na dare haka Iya ta zo ta ƙarewa Inna zagi tass akan kwakwazon da Hansai ta yi na A'isha ta rungume Umar, har sha biyun dare ba ta bar Inna ta huta ba...... Kusan sati A'isha ta yi tana jinya kafin ta samu sauƙi, bayan ta sha allurai har da ƙarin ruwa. Ta ji sauƙin zazzaɓin da ciwon kai, ciwon cikin ne dai ya ƙi yi mata sauƙi, dan cikin dare haka za ta tashi ta kasa bacci tai ta juye_juye tana hawaye, sai Inna ta yi mata tofi a ruwa ta ba ta, ta sha sannan yake lafa mata. Yau da yamma A'isha tana kwance a tsakar gida idanunta a lumshe amma ba bacci take yi ba, tunanin Umar take yi da moment ɗinsu da suka gudana masu tsayawa mutum a zuci, lokuta da dama sai ƙamshinsa yay ta mata gizo a cikin hancinta, ta ji kamar yana kusa da ita za ta ji daddaɗar muryarsa. A hankali ta saka hannu ta share hawayen da ya zubo mata, sannan ta juyar da kanta inda take jiyo sautin muryar Inna tana karatun Alkur'ani, cikin muryar marasa lafiya mai cike da damuwa ta ce. "Inna har yau bai kira ba ko?" Inna ba ta amsa mata ba sai da ta kai ƙarshen aya, ta dube ta cikin rashin jin daɗi ta ce. "Ke da wayar kodayaushe take hannunki da ita kike kwana kike komai ai inda ya kira zaki ji." A'isha ta ce. "Ki kai wurin Abba mai caji anjima ya duba dai, ko an kira gani ne baki yi ba." Inna ta ce. "Amma ai da za'a ji ƙarar kiran ko?" A'isha ta ce. "To ki kai a duba lambobin cikin wayar a kira, na san baza'a rasa tasa ba, idan ma babu sai mu cewa wanda mu kira dan Allah ya turo mana lambarsa muna son kiran sa ne." Inna ta ce. "Toh." A'isha ta lalubo wayar da kodayaushe tana kusa da ita tana jiran tsammanin kiran Umar a cikinta, amma har yau sati guda da tafiyarsa bai kira ba, abun da yake ƙara ɗaga mata hankali kenan, ta kasa samun nutsuwar zuci. Daddanna wayar ta shiga yi ba tare da ta san inda take dannawar ba. Inna ta ce. "Ki ajiye wayar kar ki shiga wani gurin da za ta samu matsala kuma." Ba ta ce komai ba ta ajiye wayar. Duk maganganun da ta yi cikin dauriya ta yi su, dan ba ƙaramin ciwo cikinta yake yi mata ba, lokaci ɗaya ta ji ya yi mata wata irin murd'awa, da sauri ta tashi zaune tana salati hannayenta duka akan cikin nata. A kid'ime Inna ta yi kanta ta riƙe ta tare da tambayar ta lafiya? Babu bakin amsawa saboda aman da ta ji ya taso mata, a hanzarce ta miƙe da nufin ta ƙarasa bakin rariya, sai dai bai fi taku uku ta yi ba ta tsugunna ta fara kelaya aman, Inna dake bin inda ta tashi da kallo ganin abun dake gurin ta ɗago ta kalle ta cikin wani irin yanayi..........✍️ *Ban yi edit ba* *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *1️⃣7️⃣* ..........Sosai ta yi aman, hakan ya ƙara galabaitar da ita. Taimaka mata Inna ta yi ta wanke fuskarta ta cire kayan jikinta ta sauye wani ta koma ta kwanta tana numfarfashi. Inna tana gyara mata kwanciya ta ce. "Sannu, bari na je chemist na karɓo miki magani da audiga." Ɗaga mata kai ta yi duk da ba ta fahimci audugar me take nufi ba. Murɗawar cikin nata ya yi mata sauƙi, hakan ya sa take ta sauke ajiyar, wani irin abu take ji yana fita daga jikinta wanda ya kasance baƙo a gurinta, tunani ta dinga yi akan hakan amma ba ta fahimci komai ba har Inna ta je ta dawo. Bayan ta yi wanka Inna ta ba ta pant ɗin da ta saka mata pad a jiki kamar yadda Nurse ɗin dake zaune a chemist ɗin ta yi mata bayani. Cikin mamaki A'isha ta ce. "Inna mene wannan na ji shi a jikin wandon?" "Auduga ce, wadda za kina amfani da ita har jinin al'adar da kika fara ya ɗauke, ai kin san mene ne shi ko?" Gabanta ne ya faɗi, jikinta ya yi wani irin sanyi ƙalau, ta san me jinin haila yake nufi, Malamar da suke zuwa gurin ta karatu ta yi musu bayani a kan shi sosai, ba tare da ta san dalili ba ta ji hawaye ya zubo mata. "Ki saka wandon kar ki kuma ɓaci mana." Cikin tsananin jin kunyar Inna ta fashe da kuka tare da saka wandon. Umarni inna ta ba ta akan ta zauna za su yi magana, ba ta yi musu ba ta zauna tana sharar hawaye. Cikin nasiha Inna ta ce. "Mene na kukan kuma? Abin da ba kanki farau ba, duk macen da kika gani a duniya tana yin jinin al'ada in dai ta kai munzalin farawa, wanda ba sa yi kuma yawanci ciwo ne, a yanda aka ce ma zai yi wahala su haihu in ba wani ikon Allah ba." Ita dai ba ta ce komai ba sai kukanta ta cigaba da yi. Nasiha sosai Inna ta yi mata akan yanzu girma ya hau kanta, an fara rubuta mata zunubi da lada kamar kowa, don haka ta ji tsoron Allah a duk inda take tare da tsare mutuncinta, ita dai ba ta tanka ba, kunya da yanayin da take ciki ya hana ta magana. Bayan ta ci abinci ta sha magani ta kwanta bacci. Hayaniyar Iya da ta shigo tana yi wa inna tijarar da ta saba ce ya tashe ta daga baccin, lokacin har an yi Sallar Isha'i. Tsaki ta ja tare da tashi ta fito tsakar gida cikin lalaben hanya. Duk da yanda take jin rashin ƙwarin jikinta da cikinta da ya ɗaure mata, amma ta daure ta cewa Iya. "Wai don Allah Iya me muke tsare miki ne a gidan nan da kullum kike zuwa ki ishe mu da masifa?" A ƙufule Iya ta ce. "Ban sani ba, wato wuyanki ya yi kauri ko? Yar mitsitsiya dake amma har za ki faɗa mini wannan maganar? Ki ji da rashin ganin da ba kya yi mana, masu idon ma sun yi shiru sai ke makauniya ce mai bakin magana." "Ai Allah ne ya yi

Chapter 11 of 20