gan su, tun ina ƴar ƙarama ake mini gorin rashin asali, tun bana damuwa har na fara damuwa duk da ban san me hakan yake nufi ba, yanzu na gane me ake nufi da rashin asali, na fuskanci me kalmar SHEGIYA take nufi, kamar yadda na gano ba Baba Malam ne ya haife ni ba."
Cikin tsantsar mamaki da damuwa Inna take kallon A'isha, a shekarunta ba ta yi tunanin za ta iya gane waɗan nan abubuwan ba a yanzu, musamman da har yanzu ɗabi'un yara sun fi yawa a tattare da ita a kan na manya, cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Wa ya faɗa miki ba Malam ne ya haife ki ba? Na ce ki daina mini wannan zancen ko, don ba gaskiya ba ne, Malam shi ne mahaifinki." Cikin matsanancin kuka ta ce. "Ki daina ɓoye mini Inna, na riga na gane gaskiya, amma don Allah ko ba za ki kai ni na ga ƴan'uwanmu ba ki taimaka ki ba ni labarin su, da dalilin baro su da kika yi."
"Zan faɗa miki, amma ba yanzu ba, domin har yanzu ke yarinya ce, ƙwaƙwalwar ki ba za ta ɗauki labarin ba balle har ta ba ki damar fuskantar shi, amma da sharaɗin ba za ki kuma tambaya ta ba har sai lokacin da na ga ya dace na faɗa miki da kaina."
Gyaɗa mata kai kawai ta yi tare da kifa kanta a kan cinyarta ta cigaba da kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar duk mai sauraren shi.
Washegari da ciwon kai ta tashi, hakan ya sa Inna ta ce ta zauna kar ta je makaranta, ranar Monday idan ta kai ta sai ta sanar da Malaman ba ta da lafiya ne ya sa ba ta zo ba. Da Yamma Inna tana ramuwar baccin da ba ta yi ba daren jiya ta ji muryar Namiji yana magana a kanta.
A firgice ta tashi tare da rarumar hijabinta dake kusa da ita ta saka, Yawale ta gani ya ƙura mata ido yana bin ta da wani irin kallo. Haɗe rai ta yi cikin ɓacin rai ta ce. "Mene ne haka Yawale? Ya za ka shigo mini har ɗaki babu neman izini, a kan me?"
"Saboda gidanmu ne ina da ikon shiga duk inda na ga dama."
"Ko kai ka gina sashen nan ka ba ni haya ba ka hurumin faɗo mini har cikin ɗaki ba tare da neman izini ba, don haka kar ka ƙara yi mini irin wannan ba na so, idan kuma ba haka ba wallahi hukuma ce za ta raba mu!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya. Dariyar rainin hankali ya yi ya ce. "To hukumar ta raba mu mana Asabe?"
Tsaki Inna ta ja tana ƙara gyara hijabin jikinta ta ce. "Ka tashi ka fitar mini daga ɗaki Yawale." Gemunsa ya shafa cikin shigar duniyanci tare da faɗin. "Ba ke kika saka na shigo ba, don haka ba ki isa kin sa na fita ba, A'isha na zo kira dama, Tsoho makaho ne yake jiran ta a soro za su yi taɗi."
Kallon ba ka da hankali Inna ta yi masa ta ce. "Dama a kan wannan shirmen ka shigo mini har cikin ɗaki ina bacci? ban da, da wata manufar a ranka da ka shigo gidan ba ka ga A'ishan kwance a tsakar gida ba? Yawale ka ji tsoron Allah, ka tuna za ka mutu fa, duk abubuwan da kake yi Ubangiji yana kallon ka."
"Har kura ce za ta ce wa kare maye? Ke har kin isa ki yi mini wa'azi Asabe? Ke da kike tattare da abin kunya, SHEGIYA fa kika ajiye, ai ke kika cancanci wa'azi ba ni ba."
Miƙewa Inna ta yi ba ta kuma magana ba, don ta fuskanci neman magana kawai yake da ita. Ficewa ta yi ta bar masa ɗakin zuciyarta na mata wani irin zafi, ta gaji da cin zarafin mutanen gidan nan, rashin dajarar ta har ya kai ƙaton mutum ya shigo mata ɗaki ba excuse tana bacci ya gama ƙare mata kallo, Gaskiya dole ta san abin yi, ba za ta ɗauki wannan akuyancin da jahilcin ba, musamman da ta daɗe da gane ƙudirin Yawale a kanta.
"Ke A'isha tashi mu je tsoho makaho yana jiran ki, ko ba kya ji ne? Ƴar bantan Uba kawai."
Yawale da ya fito daga ɗaki ya faɗi haka cikin masifa.
Ko motsi A'isha ba ta yi ba, duk da tana jin shi sarai, Hararar shi Inna ta yi ta ce. "Babu fa inda za ta, Yawale tun wuri ina shawartarka da ka ruguje wannan maganar Auren mara ma'ana, ban da zalunci yarinyar da ko shekara goma sha biyar ba ta cika ba ita ake ƙoƙarin aurawa Tsohon da ko ni ba zan aure shi ba? Tsohon ma mara mutunci da rashin sanin darajar ɗan Adam, ya mayar da aure ba a bakin komai ba, waye bai san Auri saki yake ba kaf garin nan, wato yanzu an gane halinsa an daina ba shi Auren shi ne zai zo nan, ni kuma da ban san ciwon kaina ba sai na ɗauka na bayar, to wannan ɓatan basiran ba da ni za a yi ba."
"Duk rashin mutuncin shi amma ai yana da asali ko?"
"Wannan ku ta shafa ba ni ba."
Jinjina kai Yawale ya yi ya ce. "Kuma yarinya tunda tana zaune a cikin gidanmu tana cin arziƙin mu muna da ikon aurar da ita ga duk wanda muka so."
"Tunda wata tsiyar kuke tsinana mata ba, gata nan ga ka, ka daura mata Auran mu gani."
"To mu zuba mu gani, ni da ke ɗan halak ka fasa." Ya ƙarashe maganar tare da ficewa da sashen, Inna ta raka bayansa da harara.
Cikin jin daɗin yadda Inna ta yi wa Yawale tatas A'isha ta ce. "Gwara da kika yi masa haka, gobe ba zai dawo ba."
Sai dai maganar A'isha ba ta tabbata ba, don kullum sai Yawale ya zo kiran A'isha akan ta fita gurin tsoho makaho, Inna kuma ta murje idonta ta ce bai isa ba, ba za ta je ba. Tun mutanen gidan ba sa fuskantar abin da yake Faruwa har suka fara fuskanta, nan fa suka yi caa a kan Inna, suna cewa don ma sun samu Tsohon ya taimake su ya ce zai auri ƴar tata take ƙi? Har da masu cewa ba ƙaramin jihadi Tsoho makahon ya yi ba da ya ce zai auri A'isha. Ba ta kula su, ta dage da kaiwa Ubangiji kukanta, don zuciyarta cike take da fargaba da tsoro, sanin halin Yawale ta san dagaske yake zai aura wa A'ishaTsoho makaho, a haka har kwanaki goma suka shuɗe.
Da yamma Inna ta ɗauko A'isha daga makaranta, suna tafiya tana ba wa Inna labarin wani sabon Malami da aka kawo musu daga Kano.
"Yawwa ga su nan ma sun dawo."
Muryar Yawale ta doki dodon kunnansu da faɗin haka lokacin da suka shiga zauren gidansu. Su tsoro ma ya ba su, saboda yadda ya yi maganar a hanzarce.
"Sannun ku da zuwa, ina A'ishushuwan tawa?"
Tsoho makaho dake zaune a kan tabarma ya faɗi haka yana shafa tumbinsa.
Tsaki Inna ta ja cikin takaici ta kama hannun A'isha suka yi gaba.
"A'a, Asabe ya za ki ja ta ku tafi kuma? Kin san daɗewar da muka yi muna jiran ku kuwa? Ki zo magana Malam Tsoho ya zo mu yi fa." Ko waigowa Inna ba ta yi ba balle ya saka ran za ta tsaya. Giwa a saɓule ya ce. "Ka yi haƙuri Malam, haka nake ta fama da su, daga uwar har ƴar taurin kai gare su, amma bari na je na saka su fito." Murmushi tsoho makaho ya yi, cikin washe dafaffun haƙoransa ya ce. "Babu komai ka ƙyale su, rashin fahimta ne, da zarar mun fahimci juna komai zai wuce, wuyarta a ɗaura mana Auren a kawo ta gidana." Ya ƙarashe maganar yana lalubar sandarsa. Bayan ya miƙe ya zira hannu a aljihu ya zaro kuɗi ya miƙa wa Yawale, hannu na rawa ya karɓa tare da washe baki ya ce. "Malam ba ka gajiya da abin arziƙi, Allah ya saka da Alkhairi ya ji ƙan mahaifa."
"Amin, babu komai, ai ni ka gama yi mini komai tunda ka ba ni Auren yarinyar nan, don yadda na ji ana faɗar kyawun surarta na san zan mori kuɗina."
Cikin dariya Yawale ya ce. "Za kuwa ka mora, don yarinyar a dire take dumurmur, sai dai an kai mata ita za ka tabbatar da abin da nake faɗa." Murmurshi Tsoho ya yi ya ce. "Madalla, haka ake so, yanzu bari na wuce gida, anjima su Nalami za su kawo kayan lefen, su kuma masu jere za su iya zuwa gobe, an gama gyara gurin amaryar."
"Toh Allah ya kai mu, bari na kira maka Mamman ɗin ko?" Yawale ya faɗa tare da fita ƙofar gida, inda ɗan jagoran Tsoho yake zaune yake jiran shi.
Tunda suka shiga gida A'isha take kuka, cikin kwanakin nan ta mayar da shi sana'arta, gabaɗaya ta lalace ta yi baƙi saboda damuwa da saka a ranta, a kodayaushe cikin rarrashin ta Inna take da nuna mata wannan Auren ba mai yiyu ba ne, amma ta kasa yarda da hakan, saboda ta san in dai suna cikin gidan nan to babu abin da zai hana Yawale aiwatar da abin da ya yi niyya, dama da Sarki yana nan ne zai iya tsawatar masa, shi kaɗai ne suke da tabbacin zai hana shi kaf cikin garin ya hanu.
Da daddare kamar yadda Tsoho makaho ya faɗa sai ga kaya an kawo a cikin leda Viva, atamfa Leda guda biyu da shadda wanke kuɗinka guda ɗaya, pant da shimi bibbiyu, da takalmi soso guda ɗaya, sai ƙullin su powder da man shafawa a wata baƙar leda daban. Yadda aka zube kayan a tsakar gida matan gida na gani haka Inna ta tashi ta bar su a gurin cikin tsananin baƙin ciki, ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba da ganin kayan, don hakan ya tabbatar mata dagaske fa Yawale yake aurar da A'isha zai yi. A'isha kuwa tsabar kuka har shiɗewa ta dinga yi, yadda suka ga rana haka suka dare, don jikinta rikicewa ya yi da zazzaɓi mai zafi gami da ciwon kai.
Washegari ta tashi jikin nata ya tsananta, hakan ya ƙara tayar da hankalin Inna, ga ba ta da kuɗin siyo mata magani, abun ya taru ya yi mata yawa, so take ta samu space ɗin da za ta yi tunanin mafita akan ganin auren nan bai yiyu ba, amma yanayin jikin A'isha ya sa ba ta da nutsuwar hakan.......✍️
*💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*2️⃣0️⃣*
_*Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Allah ya yiwa mahaifiyar ɗaya daga cikin member ta ƙungiyarmu Elegant rasuwa, MOMMYN MUS'AB, muna barar addu'ar ku a gare ta.*_
Haka suka yini ranar, ko ruwa A'isha ba ta kai bakinta ba, ita kanta Inna dauriya kawai take, amma jikin nata kamar mai cuta haka take jin shi. Da ruwa bokiti ɗayan da ta dauko ta tsakura ta dinga shafa wa A'isha a jikinta da tsumma, hakan ya rage zafin jikin nata, har ta samu bacci ya ɗauke ta. Sharar da ba ta samu nutsuwar yi tun safe ba ta shiga yi, duk da a galabaice take saboda yunwa dake ɗawainiya da ita. Tana farawa Hansai da sauran matan gidan suka yi sallama, ba yabo ba fallasa ta amsa musu. Cikin izgili Ramatu ta ce. "Asabe tun jiya muke jiran mu ga an shigo kayan gado don mu je mu yi jere amma shiru, shi ne muka ce bari mu zo mu ji ko kafinta ne ya yi tsiyar, idan ba zai samu yau ba mu bari sai gobe."
"Gaskiya kam, mu bari kawai sai goben, don tunda yarinyar ƴar gata ce ita ɗaya jal mun san ba ƙaramin kaya za a narka a ɗakinta ba, yanzu kuma yamma ta yi muna farawa dare zai yi."
Cewar Hansai tana wani murmushi.
Sarai Inna ta gane Habaici suke mata, murmushi ta yi ta ce. "To na gode da kulawa." Kallon juna suka shiga yi, cikin mamaki uwargidan Yawale ta ce. "To ai ba ki ce mana komai ba game da maganar kayan jeren, mu jira yau ɗin ko mu bari sai gobe."
"Allah ya kai mu lafiya."
Inna ta faɗa a taƙaice, cikin ƙoƙarin danne damuwar dake cikin ranta. Duk yadda suka so su ji Inna ta ce wani abu akan maganar jeren na za a yi ko ba za a yi ba amma ta ƙi ba su tabbaci. Haka suka tattara ƙafafuwansu suka koma, zuciyoyinsu cike da gulma da farincikin ganin su A'isha a cikin baƙin ciki. Fitar su babu jimawa wata yarinya ƴar ajinsu A'isha ta zo gidan sanye da uniform. Bayan sun gaisa Inna ta ce. "Atika lafiya dai ko?"
"Lafiya ƙalau, wani malaminmu ne ya ce na rako shi gurin A'isha, tare muke ma yana ƙofar gida."
"To, wani abu ya faru ne? Ko laifi ta masa?"
"Gaskiya dai ban sani ba."
"To bari na ɗauko hijabina mu je."
Yana tsaye jingine da bangon gidan yana kallon cikin soro suka fito, cikin girmamawa ya tsugunna har ƙasa ya gaishe da Inna. Da fara'a ta amsa masa duk da cikin ranta cike take da fargabar Allah ya sa ba wani abun A'isha ta yi ba. Shiru ta yi cikin sauraren abin da ya zo da shi. Cikin nutsuwa ya fara magana. "Na ga A'isha ba ta zo school ba yau, shi ne na ce bari na zo na ji ko lafiya?" Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta ce. "Ba ta jin daɗi ne, yau ta tashi da zazzaɓi." Cikin damuwa ya ce. "Allah Sarki, Allah ya ba ta lafiya, zazzaɓin bai yi zafi ba dai sosai ko?" Inna ta ce. "Sai godiyar Allah dai jikin nata."
"Subhanallahi, Allah ya ba ta lafiya, amma kun je asibiti ko?"
"Za mu dai je insha Allahu."
Gyaɗa kai ya yi tare da yin shiru na wasu sakanni sannan ya ce. "Mama don Allah da gaske ne aurar da A'isha za ku yi?" Cikin raunin murya Inna ta ce. "Eh." Cikin damuwa sosai ya ce. "Amma saboda me? Na ga yarinya ce ƙarama, kuma tana da ƙoƙari a makaranta, da kun bar ta ko secondary school ta gama, kuma na ga ita ma kamar ba ta son auren, saboda jiya an fita break na gan ta ita kaɗai a class tana ta kuka, da na tambaye ta me ya faru shi ne take sanar mini an ce aure za a mata, ita kuma ba ta so." A sanyaye Inna ta ce. "Ni ma ba na so, an fi ƙarfi na ne kawai."
"Kamarya? Su waye suke son aurar da ita ɗin to?"
Ya tambaya a hanzarce.
"Kawunnanta ne."
"Ba ma mahaifinta ba?"
"Eh, shi Allah ya masa rasuwa."
Jinjina kai ya yi bai ce komai ba ya zaro kuɗi ya ajiye a gaban Inna ya yi mata Sallama ya tafi, Inna tana kiran shi akan ya zo ya ɗauki kuɗin amma bai tsaya ba. Da kallo ta bi shi tare da yi masa addu'a a cikin zuciyarta, ko tantanma ba ta yi shi ne sabon malamin da A'isha take labarin an kawo musu. Ɗaukar kuɗin ta yi ta koma gida. Bayan A'isha ta tashi Inna take labarta mata zuwan malamin. Murmushi ta yi cikin muryar marasa lafiya ta ce. "Shi ne wanda nake ba ki labari, sunansa Malam Faisal, yana da kirki sosai da tausayi." Inna ta ce. "Allah Sarki, Allah ya saka masa da Alkhairi, dubu biyar fa ya ba ni, dama ina ta tunanin abin da zamu ci da wanda zan kai ki asibiti gobe."
Bayan kwana uku A'isha ta ji sauƙi sosai, ta sha allurai da magunguna. A kwana ukun kullum Malam Faisal sai ya zo ya duba ta tare da yi musu Alkhairi, hakan ya janyo tarzoma tsakanin Inna da Yawale. Ya dinga masifa da faɗin kar ya ƙara ganin Faisal ya zo, tunda dai yarinya yanzu ɗaya take da matar aure don ya karɓi sadakinta, rana kawai suke jira a ɗaura Auren.
Yau Juma'a ranar da su Yawale suka saka ta ɗaurin Auren A'isha da tsoho makaho. Tun cikin dare A'isha take kuka har gari ya waye ba ta yi shiru ba. Inna da gabanta ke ta faɗuwa ta dube ta, ta ce. "Don Allah ki bar kukan nan haka, sai kanki ya yi ciwo ko kin janyo wa kanki wata cutar, dama ba ki gama farfaɗowa ba." Cikin sheshshek'a ta ce. "Ni ba na son Auren nan, don Allah Inna mu gudu mu bar garin nan." Hawaye Inna ta matse ta ce. "Tabbas in har Yawale bai janye maganar auren nan ba to kuwa lokaci ya yi da zan bar garin nan dole." Ajiyar zuciya A'isha ta sauke mai ƙarfi ta ce. "Mu tashi mu tafi Inna, kin san ma ba janyewa zai yi ba ma, kamar yadda ya faɗa ana saukowa daga masallaci za su ɗaur......"
"Wacce irin sabgar tsiya da bayar da kai ce wannan Asabe kike yi haka?"
Muryar Malam da ya shigo kamar an hankaɗo shi yana baza babbar riga ta karaɗe zagayen cikin amsa amo. Da mamaki Inna take duban shi cikin alamun tambaya. Cigaba da ya yi da magana cikin ɗaga murya. "Wanne irin abu ne wannan? Yau kusan sati da cewa a je a yi jere amma kin ƙi siyo kaya ki bayar har yau ranar ɗaurin Aure? Ko a ƙasa kike son su ci amarcin ne? Wannan ai halin matsiyata ne da nuna tsiya." Miƙewa Inna ta yi ba ta ce komai ba, don ba ta da lokacin ɓaɓatu da mutumin da take masa uzurin ciwon hauka, ko ƙara kallon inda yake ba ta yi ba ta shige ɗaki.
"Wato ga mahaukaci ina magana kin mini shiru kin shige ɗaki ko? To wallahi ko me za ki yi sai an ɗaura auren nan yau, sai dai baƙin ciki ya kashe ki." Ya ƙarashe maganar tare da wurga wa A'isha wani mugun kallo. Hamɓarin ta ya yi da ƙafa ya juya ya fita. Yana tafe yana cigaba da banbanmin faɗa shi kaɗai, gidan tsoho Makaho zai je ya ba shi haƙuri akan rashin zuwa jeren, ya kuma tabbatar masa zai tursasa Asabe dole ta bayar a siyo ko da katifa ne, don tsohon ya ce masa ba zai angonce a dandaryar ƙasa ba. Jiniyar da ya ji ya sa shi tsayawa a ƙofar gida yana kallon Motar police dake tahowa.
Officer gashi nan ma."
Faisal dake fitowa daga cikin Motar ya faɗa tare da nuna Yawale. Zaro ido ya yi cikin tsoro ya ce. "Kai ɗan samari me na yi kake nuna ni?"
"Idan muka je office za ka ji, shiga Mota mu ƙarasa."
Cewar wani police cikin haɗe rai.
Yawale zai kuma magana aka daka masa tsawa, dole ya shiga Motar ƙirjinsa na dukan uku-uku, sai rantse-rantse yake akan bai aikata laifin komai ba, Auren ƴa ma zai yi yau. Bayan tafiyar su ba jimawa labari ya karaɗe unguwa da gidansu A'isha ƴan doka sun zo sun tafi da Yawale a Mota.
Bayan sun ƙarasa station wani ɗansanda ya dubi Yawale tare da nuna Faisal da hannu ya ce. "Wannan Malamin su wata yarinya ne A'isha dake gidanku, ya kawo ƙarar ka akan kana shirin yi mata Auren dole saboda mahaifinta ya rasu, haka ne ko ba haka ba ne?" Gumi ne ya shiga tsatstsafo wa Yawale, cikin rarraba idanu ya ce. "Ranka ya daɗe ba Auren dole ba ne, tana so yarinyar, ita ta kawo mijin ma da kanta." Wani mugun kallo Faisal ya wurga masa bai ce komai ba.
"Mahaifiyar yarinyar da bakinta ta shaida wa Faisal ba sa son Auren, sanadin maganar auren har ciwo yarinyar ta kwanta, amma tunda ka ce haka mu je gidan mu zanta da su mu ji gaskiyar al'amari, wallahi idan suka tabbatar mana Auren dole ne sai ka yi kwanan cell, saboda wahalar da shari'a da ka yi."
"A yi haƙuri ranka ya daɗe zan faɗi gaskiya, wallahi ba sa so, amma ka mini rai kar ka kulle ni."
Yawale ya faɗa cikin tashin hankali.
"Shikenan ka wanke kanka, yanzu za mu je mu taho da uwar yarinyar a yi yarjejeniya akan ba za ka ƙara shiga cikin rayuwarsu ba, sannan kuma maganar Auren nan an rushe ta."
"Faɗa taka cikawa tawa, duk abin da ka ce haka za a yi ranka ya daɗe."
Inna tana cikin haɗa kaya wata mace ta je ta tafi da su, cike da zullumi da fargaba suka je, amma da suka ji dalilin kiran sai farin ciki ya lulluɓe su. Bayan ƙara tattaunawa aka yi musu iyaka da Yawale, kowa ya yi signing aka ce su tafi. Yawale kamar zai zura da gudu saboda saurin da yake zubawa don ya yi ya bar gurin, sakamakon kaɗawar da cikinsa ya yi yana buƙatar zagayawa masai. Tsabar farinciki Inna har da ƙwalla, ji take tamkar an yaye mata dukkan damuwarta. A'isha kuwa tamkar ta taka rawa haka take ji don murna.
"Na gode, na gode sosai ɗana da wannan taimakon naka, Allah ya biya ka ya fi mu yabawa." Murmushi ya yi idanunsa a kan A'isha ya ce. "Ba komai Mama, Allah ya kiyaye gaba." Kan A'isha a ƙasa ta ce. "Mun gode sosai Sir." Still yana murmushi ya ce. "Babu komai A'i." Ya rasa me ya sa tun ranar farko da ya fara ganin ta tausayin ta ya cika masa zuciya, ko don makauniya ce ita? Babur ya samu suka hau ya biya kuɗin aka mayar da su gida.
Labarin fasa auren A'isha da tsoho ranar shi ya yi ta yawo a cikin garin, kowa na tofa albarkacin bakinsa. Iya da sauran mutanen gidan kuwa baƙinciki da takaici kamar su kashe su, suka dinga cewa kamar yadda Inna ta lashe kurwar Umar haka ta lashe ta Faisal, shi ya sa ya tsaya musu har aka fasa Auren. Bangaren Tsoho da Yawale kuwa faɗa ne ya kaure, tsoho ya ce sai ya biya shi duk kuɗaɗen da ya dinga ba shi akan auren, Yawale kuma ya ce ya cinye ba zai biya ba, ai ba shi ya ce ba shi ba. Rigima har gaban wazirin Sarki, da ƙyar aka yiwa tufkar hanci da cewa Yawale ya biya rabin kuɗin da Tsoho ya ba shi, sun raba asara kenan.
A ranar Iya ta zo ta ɗauke kayan lefen da aka kawo, wanda ya yi ta walagigi a tsakar gida, don tun ranar da aka kawo Inna ba ta ɗauke su daga gurin da aka ajiye su ba. Da yamma ganin Inna ba ta da niyyar ta ce su tafi ya sa cikin karaya A'isha ta ce masa. "Inna ba za mu tafin ba ne? Kar dare ya yi fa."
"Tunda an fasa auren maganar barin mu garin nan ta rushe ita ma."
"Amma Inna...."
Ɗaga mata hannu ta yi tare da faɗin. "Ki bi abin da na ce kawai, tunda kika ga na ƙi barin garin nan akwai dalili, amma na san watarana dole mu bar shi, lokaci kawai nake jira." A'isha ba ta kuma magana ba, amma cikin ranta ba ta so hakan ba, don zaman garin gabaɗaya ya fice mata aka, duk da a nan ta buɗi ido ta gan ta.
Washegari kamar daga sama sai ga Innar Ma'u ta sauka a garin da safe. Tsabar murna rasa inda Inna za ta saka ta, ta yi. Bayan sun gaisa Inna ta kawo mata ruwa da abinci ta ce. "A'isha haka kika ƙara girma? Yanzu ai kin fi Ma'u komai da komai." Cikin murmushi Inna ta ce. "Ni ma har mamakin girman da take nake yi, lokaci ɗaya kuma ta yi wannan girman, don ma ta yi ciwo kwana biyu ta yi rama, kafin ta yi ciwon ai ta fi haka." Innar Ma'u ta ce. "Masha Allahu, haka ake so. Ya fuska? Har yanzu idon dai bai buɗe ba?" A raunane Inna ta ce. "Muna nan muna ta addu'a dai."
"To Allah ya amsa, ya ba ta lafiya."
"Amin."
A'isha ta ce "Inna me ya sa ba ki zo da Ma'u ba?"
"Tana tahfiz ne, amma ita ma ta so mu zo tare, makarantar ce suna da tsauri ba sa son fashi, amma idan suka yi hutu ko ita kaɗai ce zan sako ta a Mota ta zo ta kwanar muku biyu."
"Allah ya kai mu."
Bayan sun taɓa hira Innar Ma'u ta tashi ta shiga cikin gidan don su gaggaisa da sauran matan gidan, saboda a ranar za ta koma Kano. Kafin ta tafi take sanar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 20