sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
...........Daren yau Inna ba ta iya runtsawa ba saboda tunanin wannan lamura iri_iri da suke faruwa da su, Tunda Ubangiji ya kawo su cikin garin nan zuciyarta ba ta huta ba, kullum da sabon al'amarin da yake riskar su na tashin hankali, amma duk ciki babu abun da ya fi firgita ta da tsorata ta kamar wannan yunk'urin yiwa A'isha fyaɗen aka yi, imagine take inda hakan ya kasance wataƙila da tuni tana k'iyama, dan ta san tsaf zuciyarta za ta iya bugawa saboda baƙin ciki. Ga wani tashin hankalin da yake risko su a gaba, wato dawowar Ƴaƴan Iya Maza gida da k'annen Malam waɗanda suke kasuwanci a Lagos, a bakin matan gidan ta ji suna zancen dawowar tasu. Duk ba su fiya shiga harkar ta ba amma Iya na zuga su su yi mata wulaqanci da tijara, guda ɗaya ne mai suna Yunusa wanda shine autansu Malam yake yi mata mutunci a cikin Mazan gidan.....Lokuta da dama idan abu ya ishi Inna ta kan ji dama su tattara kayansu su bar garin, kamar yau da aka yi yunk'urin ɓata mata rayuwar ƴa, sai dai idan ta tuna ba ta da gurin zuwa idan ta bar nan ɗin yakan saka dole ta hak'ura su ci-gaba da zaman. Washegari A'isha ta tashi da zazzaɓi da ciwon kai da ciwon jiki duka. Wajen ƙarfe takwas na safe Inna ta siyo musu koko da k'osai a gurin matar da ita kaɗai take siyar musu a cikin garin, dan Inna ba ko ina take zuwa siyayya a siyar mata da abu ba. Amma saboda rashin kunya ita a lokacin da ta yi sana'o'inta sai a zo a siya, saboda araha take yi sosai a kayan nata. A lokacin innar Ma'u kan yi dariya ta ce. "Gaskiya halin mutane sai su, suna ƙin ka da gudun ka rab'e su amma saboda son banza idan kana siyar da abu da sauƙi sai a zo gurinka a siya, idan har ƙin na Allah ai ko kyauta ka kasa abu ba'a zo a ɗauka ba." Inna kan yi murmushi kawai idan ta faɗi haka.
Bayan Inna ta d'ibarwa A'isha abun karinta ta zauna a gabanta cikin kulawa ta ce. "A'isha daure ki tashi ki karya, kin ga babu komai a cikinki, jiya ma haka kika ƙi cin funkasau da na zo da shi." Cikin muryar marasa lafiya A'isha ta ce. "Inna ba zan iya ci ba, bakina ɗaci." Inna ta ce. "Daurewa za ki yi ki sha ko kokon ne." Girgiza kai A'isha ta yi tare da kawar da kai. Daƙyar Inna ta lallame ta, ta sha kokon kaɗan ta koma ta kwanta. Ganin haka Inna ta ce. "Bari na yi wanka sai na je na siyo miki maganin zazzaɓin idan masu chemist ɗin sun fito." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. Bayan Inna ta yi wanka ta gama kimtsa gidan ta karya sai ta nemi guri ta zauna, jin shiru_shiru A'isha ba ta ji Inna ta ce za ta tafi gidan Hajiya Talatu ba, ta daure cikin magana daƙyar ta ce mata. "Inna sai rana ta yi ba ki tafi gidan abincin sadakar ba?" Inna ta ce. "Ba zani ba A'isha tunda ba kya jin daɗi." A'isha ta ce. "Inna akan me? Ba sai in zauna ki je ki dawo ba?" Inna ta ce. "Zance ma kenan, ai ko nan da can ba zan ƙara tafiya in bar ki ba, tunda an fara farautar rayuwarki, hanyar lafiya a bi ta da shekara, da dai ma lafiyarki ƙalau ne sai in saka ki a gaba mu tafi tare." Cikin wauta A'isha ta ce. "Inna kashe ni suka so yi ko? Tunda sun kwantar da ni sun daddanne ni, ina jin ma da wuk'a a hannunsu yanka ni suka so yi." Inna ta ce. "Uhm." Kawai. Aisha ta ce. "Mugaye kawai, ina jin wannan mutumin mai ƙamshin nan ne ya gan su ya k'wace ni." Inna ta ce. "Kin fara jin sauƙi kenan tunda har kike wannan surutun." Shiru A'isha ta yi ba ta kuma magana ba, sai bayan kusan mintuna biyar ta ce. "Inna ki tafi gidan aikinki kawai, sai ki kulle ni a ɗaki ki je ki dawo." Inna ta ce. "Saboda gani kuntacciya ko? Baki da lafiyar zan kulle ki a ɗaki in tafi wani gurin, idan wani abun ya same ki fa?" A'isha ta turo baki ta ce. "To Inna idan ba ki je ba a ina za mu samu kuɗi? Kuma ni abincin sadakar nan kawai nake son ci yau." Shiru Inna ta yi tana kallon A'isha, tabbas maganganunta suna kan turbar gaskiya, dan ɗan kuɗin da ta samo jiya babu abun da zai yi musu a cikin sati guda, amma idan ta je aikin ta ƙara samowa za su ɗan rage. Miƙewa ta yi ta ce. "Bari na kai ki gidan Sahura mai k'osai ki zauna a can kafin na dawo, na san za ta kula da ke yanda ya kamata. Sai na yi sauri na kammala aikina na dawo da wuri."
Ƙarfe goma sha biyu na rana Matashin nan ya fito daga cikin gidan Sarki. Sanye yake cikin ƙananun kaya wanda suka matuƙar yi masa kyau, sai tashin daddaɗan ƙamshinsa yake yi. Cikin nutsuwarsa yake tafiya zuwa gidansu A'isha, a ƙofar gidan ya tsaya yana kalle_kalle ko Allah zai saka ya ga wani yaron ya aika shi ya yi masa magana da Inna. Cikin ikon Allah sai ga wani yaro ya fito daga cikin gidan. Kiransa ya yi sai kuma ya rasa wa zai ce ya kira masa, yana son ya tuno sunan da Inna ta kira A'isha da shi jiya amma ya kasa. Sai kawai ya cewa Yaron. "My friend Matar gidan zaka yi mun magana da ita idan tana nan." Yaron ya ce. "Wacce daga ciki? Dan matan gidan nan sun fi goma." Shiru ya ɗan yi na wasu sakanni sannan ya ce. "Ban san sunanta ba, amma fara ce mai ɗan jiki, tana da yarinya mai kyau, yarinyar kuma kamar ba ta gani." Yaron ya ce. "Oh wai Asabe Mayya kake nufi?" Cikin mamaki Matashin ya ce. "Mayya kuma?" Yaron ya ce. "Eh, ai Mayya ce, A'isha ma da ba ta gani ai idon wasu suka cinye aka dawo musu da abun kansu, da alama kai baƙo ne a cikin garin nan shi yasa baka sani ba." Kallon yaron kawai yake with more shocked bai ce komai ba, yanda yaron ya dage yana yi masa bayani sai ka ce wani babba. Murmurshi ya yi ya ce. "Yanzu dai tana nan ka yi mun magana da ita?" Yaron ya ce. "Tab', ai ba ma yi musu magana saboda kar su cinye mu, an hana mu gaskiya." Daga haka yaron ya yi gaba abin sa, bin sa ya yi da kallo maganganun yaron na yi masa yawo a cikin kai, musamman sunan A'ISHA da yaron ya ambata. Yana nan tsaye sai ga su Inna su karyo kwana ita da A'isha dake tafiya daƙyar. Ajiyar zuciya ya sauke ya ƙurawa A'isha ido gabansa na fad'uwa. Tunda Inna ta hango shi ta gane shi, A'isha da ba ta gani suna ƙarasowa kusa da shi ta ce. "Laa Inna na ji ƙamshin mutumin jiya." Inna ba ta ce mata komai ba, shi kam murmushi ya yi cikin girmamawa ya ce. "Sannu da zuwa Mama, Ina Yini?" Cikin fara'a Inna ta ce. "Yawwa, lafiya ƙalau, ka zo kenan? Allah yasa ba ka dad'e kana jira na ba." Kansa a ƙasa ya ce. "A'a ban jima da zuwa ba." Inna ta ce. "Bismillah mu shiga daga ciki to." Sai da suka shige sannan ya bi bayansu. Inna ta shimfid'a masa tabarma a tsakar gida ya zauna, duk da tsakar gidan ƙasa ne babu siminti amma Inna ta yayyafa masa ruwa ta share shi tass, sai ƙamshin ƙasa ne ke tashi a cikinsa. Inna ba ta zauna ba sai da ta kawo masa ruwan randa mai sanyi gami da abincin da suka shigo da shi. Ruwan kawai ya sha ya yiwa Inna godiya sannan ya gyara zama ya ce. "Mama dama na zo ne akan abun da ya faru jiya, ban sani ba ko A'isha ta faɗa miki?" Inna ta sauke numfashi ta ce. "Ta sanar mun da komai." Ya ce. "Amma Mama ba ta gani me yasa ake barin ta take fita ita kaɗai?" Inna ta ce. "Ba ta zuwa ko'ina ita kaɗai wallahi, jiyan ma tsautsayi ne Allah ya kawo, amma insha Allah hakan ba za ta kuma faruwa ba." Ya ce. "Allah yasa, Allah ya kiyaye gaba." Inna ta ce. "Amin, Amin, na gode sosai fa Allah ya saka da Alkhairi." A hankali ya ce. "Amin." Yana satar kallon ɗakin Inna da A'isha ke ciki, wadda tunda ta ji muryarsa ta yi tsit kamar ruwa ya cinye ta. Inna ta ce. "A'isha ta faɗa mun kai ka k'wace ta daga hannun azzaluman ko?" Gyaɗa mata kai ya yi sannan cikin sanyin murya ya ba ta labarin abun da ya faru. With more shock and concern Inna ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, Ɗan_juma kuma? Yanzu duk bibiyar yarinyar nan da yake yi dama da wata mummunar manufa ne?" Matashin ya ce. "Ya daɗe yana bibiyar ta ne dama? Amma ba ku ɗauki mataki ba?" Inna ta ce. "Nunawa kawai yake yi yana son ta tun tana ƴar ƙanƙanuwarta, ashe son ba na Allah ba ne." Girgiza kai ya yi ganin yanda hankalin Inna ya tashi ya ce. "Ok, babu damuwa, insha Allah komai ya zo ƙarshe Mama, zan sanar da Baba Sarki duk abun da ya faru, na san kuma zai ɗauki mataki akan hakan." Inna ta ce. "To na gode sosai, Allah ya saka da Alkhairi." Miƙewa ya yi ya ce. "Bari na wuce Mama, na ga lokacin Sallah ya gabato." Inna ta ce. "Har zaka tafi ba, to ba ka ci abincin ba kuma." Murmusawa ya yi ya ce. "Alhamdulillah, na gode." Inna ta ce. "To ka gaida gida, Na gode sosai."
Bayan fitarsa Inna ta rafka tagumi tana tunani, ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba da ta ji Ɗan'juma ne ya yi ƙoƙarin ke ta haddin A'isha, ko kaɗan tunaninta bai taɓa kawo mata Ɗan'juman ne ba. Ta san da Ubangiji ya ba shi nasara akan A'isha shikenan ya ci bulus, domin babu matakin da za'a iya ɗauka a kansa. Duk da kasancewar Sarki adalin Mutum ne kuma yana iyakar ƙoƙarinsa wajen ganin ya bawa iyalansa tarbiyya ingantacciya, amma shi kansa Ɗan_juman ya gagare shi, domin mahaifiyarsa ba ƙaramin ɓata shi ta yi ba, duk abin da ya yi ita take ɗaure masa gindi, ta shagwab'a shi ba kaɗan ba saboda shi kaɗai ne ɗanta a duniya. Hakan yasa Sarki ya zuba musu ido kawai ya ce indai duniya ce za su gani, tunda ya yi iyakar ƙoƙarinsa akan ganin rayuwar Ɗan_juma ta saitu amma hakan ya gagara, sai dai duk da haka bai fasa bin sa da addu'ar shiriya ba. A'isha ce ta fito daga ɗaki cikin laluban haya ta zauna a tsakar gidan ta ce. "Inna wannan mutumin ya iya magana, maganarsa irin ta ƴan gayu a hankali, me yasa ba ki tambayar mana shi sunansa ba?" Inna ta ce. "Da kin sani ai kin fito kin tambaye shi da kanki, uwar magana kawai, ba ki da lafiyar ma ba za ki bar ni in ji da abun da yake damuna ba sai kin ishe ni da surutu." Turo baki A'isha ta yi ba ta kuma magana ba, cikin ranta kuwa cewa take yi, 'Dama tana gani ta ga wannan ɗan gayun mai daɗin ƙamshi ya yake.'
Bayan an sauko daga Masallacin Juma'a Sarki ya gama gaggaisawa da Jama'a Matashin nan ya same shi ya zayyane masa duk abun da ya faru jiya Na ƙoƙarin cutar da A'isha da su Ɗan_juma suka yi. Sosai ran Sarki ya ɓaci, cikin takaici ya ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, wannan Mata Asabe ita da ƴarta suna ganin tashin hankali da taskun rayuwa kala_kala a cikin garin nan, daga wannan sai wannan, ba don Allah ya kawo ka ba UMAR da tuni wannan shashashan yaron sun ɓata mata rayuwar yarinya. Allah ya biya ka bisa wannan ceto da ka yi, shi kuma Ɗan_juma da sauran abokanan shashancin nasa zan ɗauki mataki mai tsauri a kansu Insha Allahu, a yau ba gobe ba." Godiya Umar ya yi masa ya tashi zuciyarsa cike da son sanin abubuwan tashin hankalin da Sarki ya ce suna samun su Inna, ya rasa me yasa zuciyarsa ta damu da al'amarin waɗan nan bayin Allah, daga juya zuwa yau kaɗai tausayinsu ya cika masa zuciya, sai kuma wani abu daban da yake ji a cikin ransa bayan tausayin da bai san mene ba a game da A'isha...........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*1️⃣1️⃣*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
..........Daga Masallaci direct cikin gida Sarki ya wuce sashen Matarsa ta uku wato mahaifiyar Ɗan_juma. A lokacin Ɗan_juma yana kwance ya yi matashi da cinyarta tana lallab'a shi akan ya ci abinci, shi kuma sai taɓara yake zuba mata. Muryar Sarki suka tsinkaya a kausashe yana faɗin. "Rabi! Rabi! Yaron nan yana ciki?" Dan ɓata fuska Rabi ta yi tana duban da Sarki ta ce. "Ranka ya daɗe lafiya kake mun wannan kiran haka murya a sama?" Sarki ya ce. "Ban sani ba." Sannan ya dubi Ɗan_juma ya ce. "Kai! taso." Tashi zaune Ɗan_juma ya yi yana b'ab'b'ata fuska. Cikin tsawa Sarki ya ce masa. "Ba da kai nake ba ne? Ka zauna kana kallo na." Miƙewa tsaye Rabi ta yi ta ce. "Wai me ya faru ne Yallabai na ga kamar ranka a b'ace? kuma sai magana kake yi cikin hargagi, wato an zigo ka akan Shalele an maka masa wani sharrin ko?" Wani kallo ya wurga mata bai ce komai ba ya tasa Ɗan_juma a gaba suka fice ya bar ta tsaye baki buɗe. Da dogarai guda biyu Sarki ya haɗa Ɗan_juma da su ya ce. "Ka je ka raka su duk inda za'a samu sauran abokanan shashancin naka da kuka yi yunk'urin yiwa Yarinyar mutane fyaɗe jiya." Wani murmushi Ɗan_juma ya yi irin idon't care ɗin nan sannan ya yi gaba, dogaran suka bi shi a baya.
Bayan Magriba Inna sun fito za su tafi chemist suka haɗu da Umar, yana tsaye a ƙofar gidan Sarki yana latsa wayarsa. K'ansa a ƙasa ya gaishe da Inna, ta amsa cikin fara'a. Yana kallon A'isha ta ƙasan ido ya ce. "Unguwa za ku ne Mama?" Inna ta ce. "A'a, nan chemist zan kai A'isha ba ta jin daɗi ne." Cikin tausayawa ya ce. "Subhanallahi, amma dai jikin nata da sauƙi ko?" Inna ta ce. "Alhamdulillah." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, sai kun dawo......Sannu A'isha, Allah ya ƙara sauƙi." A ƙasan mak'oshi ta amsa masa, shi ko ji ma sosai bai yi ba. Har sun yi gaba zuciyarsa ta ba shi umarnin ya bi su ba tare da shi kansa ya san dalili ba. Bayan sun je mai chemist ɗin ya duba A'isha ya ce allura zai yi mata ta kwana uku 600. Shiru Inna ta yi tana tunanin gaba-d'aya kuɗin hannunta bai fi 800 ba, amma ya za ta yi? haka ta ce a yi mata. Jin haka A'isha ta fara hawaye tare da lafewa a jikin Inna, dan ba ta k'aunar allura ko kaɗan a rayuwarta. Umar ne ya yi sallama a cikin chemist ɗin, su Inna suka amsa masa, da mamaki Inna take duban sa amma ba ta ce komai ba. Bayan Mai chemist ɗin ya gama haɗa allurar ya dubi A'isha ya ce. "Bismillah ku shigo a yi mata." Kuka A'isha ta fashe da shi ta ce. "Ni dai Inna dan Allah kar a mun allura." Inna ba ta kula ta ba ta ja ta suka shiga, daƙyar ta bari aka yi mata allurar, sai gunjin kuka take yi. Inna za ta biya kuɗin ta tsinkayi muryar Umar yana tambayar mai chemist ɗin nawa ne kuɗin, ta juyo ta dube shi ta ce. "Haba Ɗana, ka bar shi ma zan biya ai." Murmurshi ya yi bai ce komai ba ya zaro kuɗi a aljihunsa ya bayar bayan mai chemist ya faɗa masa adadin kuɗin, ko kaɗan Inna ba ta so haka ba, ba ta so ta saka shi wahala ba, godiya ta yi masa sosai sannan ta fita za ta siyo abu ta cewa A'isha ta jira ta anan ta je ta dawo. Bayan fitar Inna ya zauna a kusa da A'isha akan benci ya ce. "Kukan ya isa haka me tsoron allura." Turo baki A'isha ta yi ba ta ce komai ba ta shiga share hawaye." Murmurshi ya yi ya ce. "Ya jikin naki?" A hankali ta ce. "Da sauƙi." Ya ce. "Allah ya ƙara sauƙi, da fatan kina cin abinci dai ko?" Girgiza masa kai A'isha ta yi ta ce. "Bakina ɗaci, bana son cin komai." Ya ce. "Ba kya so ki warke kenan a daina yi miki alllura?" Ta ce. "Ina so." Ya ce. "To ki dinga cin abinci kin ji Indo?" Ta ce. "Toh." Tare da ɗan ɓata fuska na Indon da ya kira ta da shi. Dai_dai nan Inna ta dawo ta yi masa sallama suka wuce gida. Suna shiga gida suka tarar da Matan gidan da yaran gidan tsaitsaye a bakin ɓangarensu. Da mamaki Inna ta tsaya tana kallon su, Iya ta tako ta tsaya a gabanta tana mitsi_mitsi da ido ta ce. "Yanzu Asabe rayuwar da kika ɗaukarwa kanki kenan ta bin maza ke da ƴarki?" Inna ta yi shiru kawai tana kallon ta cikin mamaki. Iya ta ce. "Kya yi shiru ki tsare ni da ido mana, to wallahi ki saurara ki ji ba zai yiwu ba, baki isa ba, ba'a gidan nan ba, baza ki dinga kawo mana maza kuna iskanci har cikin gida ba." Ramatu ta karɓe zancen da faɗin. "Jiya fa ana cikin tsakiyar zuga ruwan nan amma na gan su a soro cikin duhu ita da shi da ƴar, abun kunyar ma yaro ne qarami ɗan cikinta, ɗazu kuma har cikin gida ta shigo da shi." Wata ƴar budurwa mai siffar fitsararru ta amshe zancen da faɗin. "Iya yanzu ma fa tare na gan su da shi, kuma ba ku gan shi ba kyakkyawa ɗan birni, duk yanda aka yi wani abun nasu na Mayu ta yi masa ta asirce zuciyarsa, ban da haka ya zai yi ya kula su." Jan hannun A'isha Inna ta yi suka shige ciki zuciyarta na mata k'una, abun mutanen gidan nan ya daina ba ta mamaki sai dai tsoro, wani lokacin kuma uzuri take musu, kamar dai yau da haukansu ya ba su su yi mata k'azafi. Suna shiga ɗaki A'isha da ta haɗe rai sosai ta ce. "Su ƴan gidan nan kullum masifa_masifa, su ta yi mana masifa, Inna dan Allah mu bar musu gidan mu tafi gurin ƴan'uwanmu da kika ce muna da su, Allah na gaji da zaman gidan nan." Kama hannun A'isha Inna ta yi ta ce. "Na fi ki son mu bar gidan nan A'isha, ƙaddara ce ta saka har yanzu muke zaune a cikinsa, babu yadda zamu yi ne. Na sha ki faɗa miki ki kasance mai hak'uri akodayaushe a duk halin da kika tsinci kanki a rayuwa, duk wannan abubuwan da suke faruwa watarana za su wuce su zamo labari, komai lokaci ne a rayuwa." Cikin sanyin jiki A'isha ta gyaɗa mata kai. Suna nan zaune sai ga yaro ya shigo da leda wai a bawa A'isha in ji wani. Inna ta ce gaskiya ba su ake nufi ba sai dai in yaron ɓatan kai ya yi, amma yaron ya ce su aka ce masa, kwatantawa Inna Umar ya yi, lokaci ɗaya Inna ta gane shine, godiya ta ce yaron ya yi masa sannan ta karb'i ledar cikin mamakin wannan hidimar da yake yi musu. Dafaffiyar indomie ce da k'wai sai yoghurt mai sanyi na jarka. Tunda A'isha ta shak'i ƙamshin abincin yawonta ya tsinke, ai kuwa zagewa ta yi ta ci abincinta ta kora da yoghurt ɗinta, ta ma manta da wani ɗacin baki. Washegari Sarki ya aiko aka kira masa Inna ya ba ta hak'uri akan abun da su Ɗan_juma suka yi, sannan ya tabbatar mata da hakan ba za ta kuma faruwa ba Insha Allahu, dan yanzu haka ma su Ɗan_juman an kulle su an saka musu mari, kuma ana ba su horo mai tsanani. A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, kullum Umar sai ya haɗu da su Inna idan A'isha zata je makaranta ko kuma idan ta dawo, suna gaisawa sosai da Inna amma A'isha ba ta yi masa magana, shi ma kuma sai dai ya kalle ta kawai. Inna har ta gaji da yi mata faɗan ƙin gaishen shi da take yi.
Yau ya kama ranar Juma'a, sati biyu da haɗuwarsu A'isha da Umar. Da yamma Inna tana wanka A'isha ta lallab'a ta fita ƙofar gida ta tsaya tana kallon hanya kamar mai ganin masu wucewa, Umar yana bakin masallaci ya hango ta, da yake masallacin opposite ɗin layinsu Aisha yake. Cikin mamakin yanda ta iya fitowa ya miƙe ya ƙarasa ƙofar gidan nasu. Tana can duniyar tunani ba ta ma san ya ƙaraso ba, key ɗin ɗakinsa ya ɗauko a aljihunsa ya shiga karkad'awa a wajen kunnanta. Ɗan zabura ta yi fuskarta na nuna alamun tsoro ta ja baya. A hankali ya ce. "I'm sorry na tsora ta ki ko?" Ajiyar zuciya ta sauke ba ta ce komai ba sai ɓata fuska da ta yi. Murmusawa ya yi ya ce. "Tunanin me kike har na zo nan ba ki sani ba?" Canzawa fuskarta ta yi ta koma kalar damuwa, cikin sanyin murya ta ce. "Jarrabawa za mu fara ranar Monday,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 20