Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta yin ba. Bayan an tashi daga karatun suna hanya suka gamu da su Hindu. Hindu da ƙawayenta suka sha gaban su A'isha. A'isha da ba gani take ba jin tsayuwar mutane a gabanta yasa ta ƙara riƙe hannun Ma'u sosai tare da faɗin. "Ma'u su waye?" Dan a tunaninta Ɗan'juma ne. Kafin Ma'u ta yi magana Hindu ta riga ta da faɗin. "Su Uwarki ne, Shegiya Mayyar yarinya kawai." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ba dai Uwata ba wall... ..." Ai ba ta ƙarasa ba Hindu ta wanke ta da mari." Waro ido Ma'u ta yi ta ce. "Kai Hindu akan me zaki......" Kafin ta ƙarasa wata ƙawar Hindu ta janye ta tare da wancakalar da ita a gefe, cikin masifa ta ce mata. "Kama gabanki ki tafi kar mu haɗa da ke, yau sai mun ci kazakazar shegiyar yarinyar nan, saboda a kanta Ɗan_Juma yake mana rashin mutunci da wulaqanci." A'isha dake hawaye hannunta riƙe da kuncinta ta fara laluben iska tana cewa. "Kar ki tafi ki barni Ma'u dan Allah." Hindu ta dungure mata kai ta ce. "Sai ta tafi ɗin dan kan Ubanki, yau sai dai ki dinga tafiya kina fad'uwa a hanya." A'isha ta saka kuka ta fara kiran sunan Ma'u, ita ma Ma'un hawaye ta fara tare da ƙoƙarin kamo A'isha, amma saboda rashin tausayi su Hindu suka kora Ma'u, suka kuma daki A'isha son ransu. A'isha Tana durkushe a gurin tana kuka mai ban tausayi bayan su Hindu sun tafi Ma'u ta dawo ta ɗaga ta, dan dama ƙin tafiya ta yi ta b'uya a bayan wani gida. Cikin sanyin murya ta ce. "Ki yi haquri A'isha, kuma wallahi ba su daki banza ba, sai na je na faɗawa Sarki abun da suka yi miki." A'isha dai ba ta ce komai ba har suka ƙarasa gida. Ma'u ce ta zayyanewa inna duk abun da ya faru, sosai ran Inna ya ɓaci, amma ba ta ce komai ba, rarrashin A'isha kawai ta yi. Innar Ma'u kuwa Ma'u tana cikin ba ta labari ko gamawa ba ta yi ba ta zari hijabinta tay gidan Sarki ta kai ƙara. Babu ɓata lokaci Sarki ya saka aka kira su Hindu da iyayensu mata, sannan aka kira Inna da A'isha da Ma'u. Gargad'i sosai Sarki ya yiwa su Hindu akan A'isha bayan Ma'u ta ƙara zayyana masa yanda aka yi, ya kuma saka suka ba ta hak'uri, ya ce duk ranar da ko kallon da bai gamsar da A'isha suka yi mata ba idan ya samu labari sai ya saka dogarai sun zane masa su, ya kuma cewa iyayensu su ƙara ja musu kunne akan babu ruwansu da Aisha, sannan ya bawa Inna da A'isha haquri, daga nan ya sallami kowa. Suna tafe a hanya Inna ta dubi Innar Ma'u ta ce. "Me yasa kika kawo ƙarar su, da kin bar su ai." Innar Ma'u ta ce. "Su daki yarinyar sannan kuma a k'yale su? Sun ci bulus kenan, gobe ma su samu lasisin ƙara dukan ta kenan, yanzu kuwa da aka yiwa tufkar hanci ba shikenan ba. Ai ni wallahi yanzun ma na so kin bari an daddaki ƴan banza, amma kika wani dinga bayar da hak'uri kina ke kin hak'ura kin yafe." Inna ta ce. "Gwara dai da ba'a dake sun ba, me cece ita duniyar? Ai komai ɗan hak'uri ne." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne, Allah yasa mu dace." Saboda kuka da dukan da A'isha ta ci yau da ciwon kai ta kwanta. Ranar Monday da safe Inna ta shirya A'isha cikin uniform suka tafi Makarantar su. Ta yi Sa'a suna shiga shi ma Malam Buba ya shigo, ganin Inna da A'isha ya gane mahaifiyarta ce, cikin girmamawa ya ce. "Sannunku da zuwa, Ina kwana Baaba?" Inna ta ce. "Lafiya ƙalau, ya ƙoƙari?" Malam Buba ya ce. "Alhamdulillah." Sannan ya dubi A'isha ya ce. "A'isha ba magana?" Murmurshi ta yi ta ce. "Ina kwana." Ya ce. "Lafiya ƙalau, ya jiki_jiki kuma? Asma'u ta ce kin sha jinya." A'isha ta ce. "Da sauƙi." Ya ce. "To Allah ya ƙara afuwa." Suka amsa da Amin, sannan ya ce da Inna su ƙarasa office ɗinsu bayan ta yi masa bayanin abun da yake tafe da ita. Bayan sun zauna Inna ta ce masa. "Dama akan maganar Jarrabawar da A'isha ta ce an zaɓe ta zata zana na zo, na ce ko za'a bari sai wata shekarar duba da lalurar da ta same ta, kafin nan insha Allahu an yi mata magani ta warke." Malam Buba ya ce. "Wai har yanzu ba ta gani? Na ɗauka ai idon ya buɗe." Inna ta ce. "Tukunna dai, muna nan muna ta addu'a." Malam Buba ya ce. "Subhanallahi, Sannu A'isha, Allah ya yaye miki." Inna ta ce. "Amin." Malam Buba ya ce. "To Baaba tunda ana saka rai idon zai buɗe ta zana jarrabawar a hakan kawai, zan yi mata registration da komai da sunanta da hotonta, akwai k'anwata Mairo sai ta zana mata, tunda jarrabawar ta rana ɗaya ce." Inna ta ce. "Kana ganin hakan zai yiyu?" Malam Buba ya ce. "Insha Allahu, ai nine exam officer, Ni nake yin komai na jarrabawar, shugaban makarantar ma bani da matsala da shi, ina yi masa magana zai yarda." Inna ta ce. "Toh shikenan Allah ya ba da sa'a, na gode sosai ɗana, Allah ya saka da Alkhairi." Malam Buba ya yi murmushi ya ce. "Babu komai Baaba, Allah ya ba ta lafiya ita kuma." Inna ta ce. "Amin." Malam Buba yana kallon A'isha ya ce. "Indodo kin daina magana ne? Na ji kin yi tsit kamar ba ke ce mai cika mana aji da surutu ba." Murmurshi A'isha ta yi, tare da saurin rufe fuskarta da hannunta. Inna ta ce. "Ko godiya ba ta iya ba." Cikin sanyin murya ta ce. "Mun gode Malam." Murmurshi kawai Malam Buba ya yi, haka kawai A'isha take burge shi, saboda nutsuwarta da hankalinta, ba shiru_shiru ba ce ita dan ba ta barin ta kwana, indai aka faɗa mata sai ta rama, amma ba ta da tsokana, in dai ka ji an yi faɗa da ita to tsokanarta aka yi. Yana jin tausayinta kuma a cikin ransa saboda tsangwamar da take fuskanta a gurin abokan karatunta. Abun da yake ƙara burge shi da ita tana da ƙoƙari dai_dai misali, indai an yi musu karatu tana fuskanta. Anan Inna ta bar ta bayan ta biya kuɗin jarrabawar da na passport ɗin da za'a yi mata. Yau A'isha murna fal ciki ta zo makaranta, duk da ba ta ganin komai amma dai ta ji daɗi, kuma babu wanda ya tsokane ta, saboda Malam Buba ne ya kai ta har aji ya kuma jawa yaran kunne akan kar wanda ya tsokane ta, duk wanda ya tsokane ta sai ya zane shi........ Rayuwa ta cigaba da tafiyar wa da su A'isha cikin godiyar Ubangiji, an zana common entrance ɗin har ma ta fito, A'isha da Ma'u duk sun ci makarantar sakandare dake cikin garin. Tare Kawunsu Ma'u ya yi musu komai kama daga kan uniform da su takalmi da jakar makaranta da littattafai. Har lokacin Inna ba ta gama tara kuɗin kai A'isha asibitin Kano ba saboda sha'anin rayuwa. Zuwa lokacin kowa na cikin garin ya san A'isha ta makance, labari ya gama baza ko'ina, Iya da Matan gidansu kullum cikin yiwa Inna gorin ƴarta ta makance amma ta kasa kai ta asibiti a yi mata magani saboda baƙin talauci, Inna dai ba ta kula su dan ba ta su take ba. A'isha kuwa zuwa yanzu har ta saba da rashin ganin. Da farko da aka kai su A'isha makaranta ƙin karɓar ta aka yi, Malaman suka ce ai kamata ya yi a kai ta makarantar makafi ba wai nan ba, Malam Buba ne ya yi ruwa ya yi tsaki daƙyar aka samu aka ɗauki A'isha, shi ma dan ya yi musu dabara ne da cewa, an kai ta asibiti sun ɗora ta akan magani tana kan shan maganin ne, sai ta gama shan maganin za'a yi mata aiki wanda idon zai buɗe. Ma'u ce take yi mata rubutu idan ta gama nata, ita dai kawai in ta je makarantar zama ne nata da saurare. Sai kuma wata sabuwar matsala da A'isha take fuskanta a garin, ba ta isa ta fito waje ba sai yara sun yi mata ihun Makauniya sun cinye idon wasu ya dawo kansu. Yau Laraba, da daddare Inna ta ɗauko kuɗin da take tarawa na kai A'isha asibiti ta irga, ta ga kuɗin ya kai dubu shida da ƴan kai, zai isa su yi kuɗin Mota da kuma ɗan abun da take tunanin za'a buƙata a asibitin, dan haka ta yanke shawarar gobe za su je asibitin Kanon da yardar Allah......✍️ *By* *Zeey Kumurya* *💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖* _By_ _Zeey Kumurya_ *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *0️⃣8️⃣* I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm! BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE I'm selling MTN data with this cheap price MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month Airtel,9mobile and Glo also available. *Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* Whatsapp OR Call 08066268951 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_ _*infection*_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_ _07084653262_ ..........Washegari tun sassafe suka shirya, A'isha tana zaune tana karyawa, Inna kuma tana duban kuɗin da za su yi amfani da shi a inda ta ajiye jiya da daddare amma kuɗi ya ce ɗauke ni inda kika ajiye. A cikin wata jaka dama ta ajiye su, ta duba jakar ya fi sau goma ta zazzage ta amma ba ta ga kuɗin ba. Wasu guraren ta shiga dubawa ko ta manta ta canza musu guri ne, sai da ta birkice duka ɗakin amma ba ta gan su ba. A'isha da take sauraren b'uruntun da Inna take ta yi ta ce. "Inna wai me kike dubawa tun ɗazu?" Cikin damuwa Inna ta ce. "Kuɗin da zan kai ki asibitin A'isha, ban gan su ba." A'isha ta ce. "Ko dai kin manta inda kika ajiye ne?" Inna ta ce. "Amma ko mantawar na yi yanda na birkice ɗakin nan ya ci ace na gan su, sai dai in ba ya cikin ɗakin." A'isha ta ce. "Allah yasa dai ki gan su Inna." Inna ta ce. "Amin." Dai-dai nan innar Ma'u ta shigo zagayen nasu, bayan ta yi sallama sun amsa mata ta ɗaga labulen ɗakin tana faɗin. "Har yanzu ba ku tafi ba? Idan takwas ta wuce fa ba za ku samu ganin likita ba." Inna dake maimaita kalmar innalillahi a cikin zuciyarta ta dubi Innar Ma'u cikin sanyin murya ta ce. "Ladidi kuɗaɗen na nema na rasa." Innar Ma'u ta ce. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, kamar ya kin neme su kin rasa? A ina kika ajiye?" Inna ta ɗauko jakar da ta ajiye kuɗin ta ce. "A cikin jakar nan na saka, kuma ko kafin na yi bacci na duba na ga suna ciki, Jakar kuma a gabana ta kwana a k'ark'ashin shimfid'ata." Innar Ma'u ta ce. "Bari dai na shigo mu ƙara duba ɗakin sosai, ko wani gurin kika cilla su kika manta." Inna ba ta ce komai ba har Innar Ma'u ta ƙaraso cikin ɗakin ta fara dubawa. A'isha dake ta murna yau za'a kai ta asibiti a yi mata magani sai murnar ta koma ciki, kana kallon fuskarta ka san tana cikin damuwa. Sai da innar Ma'u ta ƙara duba ko'ina a cikin ɗakin amma babu kuɗin babu alamar su. Hankalin Inna fa ya yi matuƙar tashi, baiwar Allah har gumi ya fara tsatstsafowa a jikinta na rud'ani. Duban Innar Ma'u ta yi wadda ita ma take cike da tararrabin abun ta ce. "Kuɗin nan fa ba ya cikin ɗakin nan." Innar Ma'u ta ce. "An shigo an ɗauke su kenan?" Inna ta ce. "Amma da na yi matuƙar mamaki, saboda babu yanda za'a yi a ɗaga shimfid'ar da nake kwance har a zare jakar nan ban ji na farka ba." Innar Ma'u ta ce. "Hmmm, Asabe bar mutum kawai, maso abun ka ya fi ka dabara, amma ko tantanma bana yi in dai shigowa aka yi aka ɗauki kuɗin nan to da sandar nan da suke amfani da ita suka zo, wadda idan aka ajiye ko idonka biyu baza ka iya motsawa ba har sai sun gama ɗaukar abun da za su ɗauka sun ɗauke ta." Inna ta sauke numfashi tare da zama dab'as a ƙasa cikin raunin murya ta ce. "Allah kai ka san me kake nufi da wannan al'amari, kuma kai ka bani wannan kuɗin Allah ka ƙara bani wasu." Cikin tausayawa Innar Ma'u ta ce. "Amin ya Allah, insha Allahu Asabe kuɗin ki sai ya fito, Allah ya dawo miki da su, ya toni asirin duk wanda ya ɗauka." Kamar A'isha zata yi kuka ta ce. "Inna shikenan yanzu baza mu je asibitin ba an sace kuɗin?" Inna ta ce. "Ki yi hak'uri A'isha, haka Allah ya Ƙaddaro mana, babu yanda zamu yi." Tsugunnawa Innar Ma'u ta yi ta dafa kafadun A'isha cikin son kwantar mata da hankali ta ce. "Insha Allahu A'isha Ubangiji zai kawo hanyar da za'a kai ki asibiti, ki kwantar da hankalinki insha Allahu zaki warke." Gyaɗa mata kai kawai A'isha ta yi. miƙewa Innar Ma'u ta yi ta fice bayan ta ce musu tana zuwa. Hawaye ne yake ƙoƙarin zubowa daga idon Inna amma ta ƙi ba su damar hakan, wani irin zafi take ji a cikin zuciyarta, kuɗin da ta hana kanta ci, ta hana kanta sha, da goma da ishirin ta tara su kusan watanni goma amma wani mara imanin ya raba ta da su a dare ɗaya, ita yanzu ina ta ga hanyar da zata kuma samun wasu kuɗaɗen? Hawaye A'isha ta fara ta ce. "Yanzu shikenan Inna ni ban zan kuma gani ba tunda an sace kuɗin da zaki kai ni asibitin? Allah ya isanmu wallahi, ba mu yafe ba, Allah ya kumbura cikin duk wanda ya ɗaukar mana kuɗinmu." Inna ta ce. "In Allah ya yarda A'isha zaki warke." A'isha ta ce. "To Inna wa zai ƙara baki wani kuɗin ki kai Ni?" Inna ta ce. "Allah, shi ya bamu wannan ɗin kuma shi zai ƙara bamu wasu." Wunin yau gaba-d'aya cikin damuwa da rashin walwala A'isha da Inna suka yi su, dan Inna ko abinci kasa ci ta yi. Abun da yake bata mamaki game da ɗaukar kuɗin da aka yi, ita dai a iya saninta babu wanda ya san da batun kuɗin kaf cikin gidan balle kuma a waje, daga ita sai Innar Ma'u suka sani, kuma ta san Innar Ma'u baza ta yiwa kowa zancen kuɗin ba, tunda ba wani shiga sabgar matan gidan take yi sosai ba. Amma babu komai ta bar wa Allah, shi kaɗai ya san me yake nufi da hakan ta faru, fatanta Allah ya musanya musu da mafi Alkhairi. Innar Ma'u ta yi iyarka ƙoƙarinta wajen ganin ta samu kuɗi ta bawa Inna ta je asibiti a cikin satin amma hakan bai samu ba saboda halin rayuwa. Haka A'isha ta cigaba da rayuwa cikin makanta, ga tsangwama da tsanar da suke fuskanta daga mutanen garin, babu abun da ya ragu sai ma ƙaruwa da ya yi. Yau ta kama ranar Talata, da safe k'anin Innar Ma'u dake Kano ya zo. Bayan sun gama gaisawa da ita sun sha hirar yaushe gamo ya gyara zama ya ce mata. "Yaya ni fa abun da ya kawo ni na zo ɗaukar ku ne ku koma can Kano da zama tunda Allah ya nufa na kammala ginina." Cikin mamaki innar Ma'u ta ce. "Mu koma can kamar ya? Ina kake nufi? Ba dai Kano ba?" Ya ce. "Can mana gidana, sai ku fara shiri jibi za mu wuce tare." Innar Ma'u ta ce. "Haba Muntari, ya za'a yi mu koma gidanka mu ɗora maka nauyi bayan wanda yake kanka? Kuma ita Rakiyan ai kamar zamu takura ta idan muka koma gidanka gaba-d'aya da zama." Muntari ya ce. "Babu wani nauyi Yaya, ni fa na ce ku koma kuma na san zan iya ne, Rukayya kuwa ba ki da matsala da ita, da na faɗa mata ma murna tay ta yi." Shiru kawai Innar Ma'u ta yi ba ta ce komai ba, amma ko kaɗan ba ta so komawarta Kano ta bar garin da aka haife ta a ciki ba, gashi kuma ba ta son barin su Inna, amma saboda kar Muntari ya ga ta gwale shi sai ta amince, ta dinga yi masa godiya tare da tarin addu'oi. Jiki a sanyaye Innar Ma'u ta shiga ta sanar da inna batun tafiyarsu. Inna ta ce. "Jibi_jibin nan kuma? Ikon Allah" Innar Ma'u ta ce. "Wallahi Nima na ga abun ya yi kusa sosai, yaushe na gama zaga ƴan'uwa da abokan arzik'i na yi musu sallama? ga gari na damuna wataran ma sai ruwa ya hana ka fita. Amma ya zan yi tunda Muntari ya dage." Inna ta yi murmushi ta ce. "Ai da gaskiyarsa, ya san in ya tafi baza ki koma da wuri ba, Allah ya kai mu Jibin ya sanya Alkhairi." Innar Ma'u ta ce. "Amin, amma ko kaɗan ban so barinmu garin nan ba ko dan ku Asabe." Inna ta ce. "To ya za'a yi? Haka Allah ya yi, kar ki saka komai a ranki na damuwa saboda ni, Ubangiji yana tare da mu ai." Innar Ma'u ta ce. "Haka ne kam." Inna ta ce. "Zan shigo anjima mu yi wata magana idan na gama abun da nake yi" innar Ma'u ta ce. "To sai kin zo."......... Kwana biyun nan zuciyoyinsu Inna babu daɗi saboda tashin da su Ma'u za su yi, ita kanta innar Ma'u ta shiga cikin damuwa, ga tunanin halin da za ta bar su Inna ga kuma kewarsu da za ta yi. A'isha ma sosai ta damu saboda rabuwa da Ma'unta, ita kaɗai ce ƙawarta duk cikin garin, idan ta tafi shikenan ba ta da kowa. Ranar Alhamis da safe wanda ya kama ranar tafiyar su Ma'u, Inna tana wankin uniform ɗin A'isha Hansai ta shigo zagayen nasu babu ko sallama, ta tsaya akan Inna cikin izgilanci ta ce. "Yau koma wasu sai kwanan baƙin ciki, wadda aka yi nasarar lashewa kurwa zata bar gari, sai mu ga kuma da wa za'a dinga yin mu'amala yanzu." Inna ta yi murmushi ta ɗago ta kalle ta ba ta ce komai ba. Hansai ta cigaba da yadawa Inna habaici cikin shewa, yau duk matan gidan zuciyarsu fari k'al suke jin ta, a ganinsu tunda innar Ma'u za ta bar gidan watan tagayyarar su Inna ya kama. Har ƙofar gida aka kawo Motar da su Ma'u za su tafi a cikinta, bayan an gama saka kayansu a ciki suna bakin Motar a tsaye matan gida duk sun fito yi musu rakiya. Inna tana tsaye hannunta riƙe da na A'isha wadda ke ta gunjin kuka ita da Ma'u, ita kanta innar dauriya kawai take yi amma yanda take jin zuciyarta kamar ta fashe da kukan, ganin abun take tamkar a mafarki, kamar za'a ce wasa ne su Innar Ma'un sun fasa tafiya. Innar Ma'u ta rungume A'isha tana hawaye ta ce. "Ki yi shiru A'isha ki bar kukan nan haka, kin ga idanunki dama ba lafiya ce da shi ba, ai zamu na zuwa muna ganin ku, kuma za ku na kawo mana ziyara, na bawa Innarki Lambar Muntari, idan kun tashi zuwa sai ta kira shi ya ba ta adreshin inda muke, ki yi hak'uri kin ji." A'isha dai tamkar ƙara zuga ta innar Ma'u ta yi, maimakon ta yi shirun sai ma ƙara volume ɗin kukan ta yi. Janye ta Inna ta yi, ta dubi Innar Ma'u tana murmurshin da ya fi kuka ciwo ta ce. "Allah ya kiyaye hanya ya kai ku lafiya, Na gode sosai da irin taimakon da kika ba ni a zamantakewarmu, Allah ya saka da miki da mafaficin Alkhairin sa, tabbas ke wani bango ce a cikin rayuwarmu." Ba ta jira cewar Innar Ma'un ba saboda wani kuka dake neman kufce mata ta shafa kan Ma'u ta ce. "To Asma'u, Allah ya tsare sai mun zo ko kuma ku kun zo." Ma'u ta riƙe Inna ta ce. "Ni na fasa tafiyar anan zan zauna tare da A'ishata, ni ba zan iya tafiya in bar ta ba." Inna ta ce. "Haba Asma'u, kar ki ce haka kin ji yarinyar kirki na, ki yi hak'uri." Ma'u ta saki Inna ta rungume A'isha suka fashe da kuka mai ban tausayi, hakan ya karya zuciyar innar Ma'u ta fara hawaye sosai ita ma, abun tausayi. Sabo da shak'uwa ba k'arya ba ne, tunda su A'isha suka taso tare suke yin komai da Ma'u, yau rana tsaka kuma Ubangiji ya raba su, abun da babu wanda ya yi tunanin faruwarsa nan kusa. Sosai suka bawa wasu daga cikin mutanen gari tausayi, shi kanshi Muntari dake tsaye yana kallon su sai da ya ji kamar ya fasa tafiya da su Ma'un, Malam ƙarami kuwa Mutumin Inna shi ma sai kuka yake yi. Dauriyar Inna ta ƙare, hawaye masu ɗumi ne suka shiga kwaranyowa daga cikin idonta, cikin matuƙar sanyin jiki ta d'agawa su Inna hannu sannan ta ɗaga ƙafafuwanta daƙyar ta yi cikin gida da sauri. Matan gidan suka bi ta da kallo suna sakin murmurshin mugunta. Daƙyar aka iya raba Ma'u da A'isha, ƴar Innar Ma'u ta shigar da A'isha gida Ma'u kuma aka tusa ta cikin Mota. Kuka sosai A'isha ta yi a yau, ko makaranta ba ta je ba, sai bayan Azhar bayan Inna ta saka ta, ta yi Sallah bacci ya ɗauke ta. Ita kanta Inna ta ci kukanta ta gode Allah. Sai yamma A'isha ta farka daga baccin, ta tashi da ciwon kai saboda kukan da ta sha. Tana farkawa abun da ta fara cewa shine. "Shikenan su Ma'u sun tafi sun bar mu, yanzu ba mu da kowa, ba ni da mai kama hannuna mu je makaranta, ba ni da mai yi mun rubutu." Inna ta ce. "Mu na da Allah A'isha, kuma shi zai yi mana maganin komai ya ba mu yanda za mu yi." Sosai kewar su Ma'u take damun su Inna, gashi ita ba waya ba bare ta kira lambar Muntari su yi magana da su ko sa ɗan ji daɗi. Duniyar duk sai ta yi musu wani iri babu daɗi. Gaba-d'aya A'isha ta daina walwala, komai cikin sanyin jiki take yin sa, ta rage yawan magana, kamar ba ita ce a daa idan ta fara yiwa Inna surutu sai ta ce ta rufe mata baki ba. Satin da su Ma'u suka tafi gaba-d'aya ƙin zuwa makaranta ta yi, Inna ba ta takura mata ba akan hakan ta bar ta, ta huta. Ranar Lahadi da daddare suna cin tuwon masarar da Inna ta yi musu Inna ta cewa A'isha. "A'isha ki daure gobe ki koma makaranta, dan babu Ma'u

Chapter 5 of 20