to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
..........Kusan a tare Matan gurin suka saki shewa tare da faɗin. "Yau za mu yar da ƙwallon Mangoro mu huta da ƙuda." Innar Ma'u wadda ta bi Inna da kallon tausayi ta sauke numfashi tare da runtse idonta. A ranta tana faɗin, komai zai faru ba za ta taɓa bari Innar Ma'u ta bar gidan nan ba, saboda dalilai guda biyu. Dalili na farko ta san ba ta da inda zata je idan ta bar nan ɗin, dalili na biyu kuma alƙawarin da ta yiwa Malam mijinsu kafin ya rasu, na taimakon Inna da ba ta kariya a gidan bayan ransa. Fakar idonsu Iya ta yi ta fice daga ɓangaren cikin sauri ta aiki Ma'u ta je ta sanar da mai gari halin da ake ciki. Inna tana cikin ɗaki tana ta harhad'a kayayyakinsu cikin sauri saboda jarabar mitar da Iya ta azalzale ta da ita, A'isha dake kwance wadda duk maganganun da aka yi a cikin kunnanta cikin sanyin murya ta ce. "Inna wai haɗa kayan kike yi? Ina zamu je idan mun bar nan ɗin to? Ko gurin ƴan'uwanmu da kika ce mun muna da su za mu?" Inna ba ta tanka mata ba ta cigaba da abun da take yi, hakan yasa A'isha fashewa da kuka. Inna ta fara kai kayansu tsakar gida saboda cigaba da azalzalar ta da Iya ke yi mata akan ta yi sauri ta zo su tafi, su Hansai na ƙara zuga ta tare da yadawa Inna Habaici, sallamar da suka ji ana kwad'awa yasa su juyawa suna kallon mai sallamar, Malam Garba ne, ɗaya daga cikin bafadan garin. Inna ce kawai ta amsa masa sallamar. Cikin ɗaga murya Malam Garba ya ce. "Mai_gari yana son ganin Asabe da Iya Mari a fada yanzu_yanzu." Bai jira amsar kowa ba ya juya ya fita. Wulwulga idanuwa iya ta fara yi, ganin ba ta ga Innar Ma'u ba ta shiga tafa hannuwa tare da faɗin. "Innalillahiwa'inna'ilaihirra'un, yanzu Ladidi ƙara ta, ta kai gurin Mai_gari? Idan uwarta ce ai baza ta kai ta ba, to mu je gurin Mai_garin sai me? Bai dai isa yasa na janye abun da na yi niyya ba, ato." Wata k'ak'k'arfar ajiyar zuciya Inna ta sauke lokacin da ta ji sak'on Malam Garba, ko ba komai zuciyarta ta samu nutsuwa akan zullumin tunanin inda za su dosa in sun bar nan. Dama da hijabinta a jikinta, takalmi kawai ta zura bayan ta kamo hannun A'isha ta kulle ɗakinta suka rab'a ta gefen matan gidan suka fice, gaba-d'aya suka raka su da kallon banza zukatansu fal baƙin ciki, domin sun san Mai_gari ba zai bar Iya ta kori su A'isha ba.
Iya ce duƙe gaban Mai_gari sai zazzare ido take tana sauraran nasihar da yake yi mata, Inna na gefenta a zauna kanta a ƙasa ita da A'isha. Bayan Mai_gari ya kai aya Iya ta fashe da kuka ta ce. "Ranka ya daɗe ba wai ban ji abun da ka faɗa mun ba ne, amma ina so a duba abun nan da idon basira, Matar nan fa tunda ta zo cikin garin nan ba mu taɓa ganin wani nata ko da kaza ya zo gurinta ba, haka ita ma ba ta taɓa zuwa gurin wani nata ba, ai kuwa ka san da akwai ayar tambaya, domin duk abun da ya koro bera daga rami to tabbas ya fi ramin zafi. Mu da ma tsoron mu ɗaya ne, kar ta janyo mata abun tirrr a cikin zuri'a." Mai_gari ya jinjina kai ya ce. "Iya Mari tun zuwan matan nan garin nan kuke jifan ta da kalmar Maita, kuma idan ban manta ba Marigayi Malam Yusuf har Sarkin Mayu ya taɓa ɗaukowa akan sanin Mayya ce Asaben ko ba Mayya ba, duk da shi ya san ba Mayyar ba ce, sai dan kawai ku ku tabbatar. Sarkin Mayun kuma ya tabbatar ba Mayyar ba ce, amma duk da haka har yau ba ku daina dangantata da Maitar ba, akan me? Yanzu tsakani da Allah idan ƙaddara ta kai naku wani gurin da ba'a san shi ba aka dinga yi masa abun da kuke yiwa wannan baiwar Allah zaku ji daɗi? Rayuwa ba haka take ba, ɗan_Adam Ubangiji ma da kansa ya daraja shi, bai kamata mu kuma yan'uwansa mu dinga wulak'anta shi ba, wannan ba dai_dai ba ne, ban taɓa zaton abun da kika yiwa wannan baiwar Allah daga gare ki ba Iya mari, da girmanki da hankalinki? Maganar Barin Asabe gida kuwa kar na kuma jin ta, indai ba ita ta so hakan da kanta ba, saboda Malam Isuhu shi ya gina gurin da take zaune, kuma ya ce ya bar mata halak_malak, ko bayan ransa ta cigaba da zama a cikinsa, dan haka kar na ƙara jin makamanciyar wannan maganar, duk wanda ya kuma zan kira a zo a kama shi tun daga Kano, a kulle shi a can a koya masa hankali." Mai_gari ya ƙarasa Maganar cikin kaushin murya. Cikin Iya fa ya kad'a jin ta ji an ce za'a kai mutum a kulle, cikin hanzari ta ce. "Insha Allahu ba za'a kuma ba ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana, wannan ɗin ma ɓacin rai ne ya saka." Inna ta share ƙwallar data tarar mata a ido cikin ladabi ta ce. "Godiya nake ranka ya daɗe, Allah ya ƙara girma." Mai_gari ya ce. "Amin Asabe, a cigaba da hak'uri, ita kuma wannan yarinya Allah ya ba ta lafiya." Inna ta amsa da Amin. Daga haka Mai_gari ya sallame su.
Su Inna na gaba Iya na bin su a baya tana mitar da girmanta tsofai_tsofai da ita an saka ta fitowa da hantsin nan, kamar ba ita ta zubar da girman nata ba. Sai tsinewa Inna take yi tare da zagin Mai_gari, dama duk maganganun da ta faɗa kurin kawai take yi, haka take yi kodayaushe, ana zuwa gaban Mai_gari kuma sai ka ji ta shiru kamar ba ita ce mai tijarar ba. Suna shiga gida direct ɓangaren Innar Ma'u ta shiga ta dinga zazzaga mata masifa da bala'i, akan kai ƙarar ta gurin Mai_gari da ta yi. Ita dai ba ta kula ta ba, tunda Allah yasa Mai_gari ya yiwa tufkar hanci shikenan. Bayan Iya ta gama yi mata tijarar ta tafi ta shiga ɓangaren su Inna ta tarar tana mayar da kayan da ta fiffito da shi, hak'uri ta shiga ba ta akan abun da ya faru, Inna ta yi murmushi wanda ya fi kuka ciwo ta ce. "Ni fa duk abun da su Iya suke mun bana ganin laifinsu ko kaɗan, domin da gaskiyar su tunda......" Da sauri Innar Ma'u ta katse ta, ta ce. "Na sha faɗa miki ki dainar faɗar haka, dan ba su san asalinki ba bai kamata su dinga yi miki kage da sharri ba, bayan wulak'anci da tozarci gami da tsangwama da kike fuskanta daga gurinsu, idan ba za su iya mu'amala dake ba sai su daina shiga cikin rayuwarki, ba wai su dinga yi miki irin wannan ɗiban albarkar ba." Inna ta ce. "Haka ne, Allah yasa mu dace." Innar Ma'u ta amsa mata da Amin, zuciyarta cike fal da tausayinta. Lokuta da dama tana son ta yiwa Inna tambayoyi a game da rayuwarta, tana son sanin wacece ita? Mene ne dalilin barowar ta cikin danginta ta zo nan tana rayuwa cikin k'unci da k'untata? Amma ganin duk tsawon shekarun da suka yi tare da Innan ko da wasa ba ta taɓa yi mata magana makamanciyar wannan ba yasa take dannewa ba ta tambayar ta_ta.
Bayan kwana biyu kamar yadda mai magani ya ce Inna ta cigaba da sakawa A'isha maganin, amma idon bai buɗe ba. Hankalin Inna fa ya yi matuƙar tashi, ta saka A'isha a gaba tana kuka mai ban tausayi. Innar Ma'u ta dinga tausar ta tana ce mata, watak'ila ciwon idon A'ishan bana maganin gida ba ne na asibiti ne, idan Allah ya taimaka ana kai ta asibitin sai ta ga an dace, da wannan kalaman zuciyar Inna ta ɗan yi sanyi. A'isha ma ta damu ba kaɗan ba, domin rashin gani ba ƙaramin jarabta ba ce, dan ma wani ikon Allah sai Ubangiji ya ɗoro mata hak'uri akan makantar da ta same ta lokaci ɗaya. Amma duk da haka kodayaushe cikin tambayar Inna take yaushe idonta zai buɗe? Ita dai a kai ta asibiti, wani lokacin har da kuka take yi. Washegari Monday tun sassafe Inna suka shirya suka tafi asibitin Rano ita da A'isha. Tana zuwa suka yanki kati sannan suka yi zaman jiran a kira su dan ganin likita. Sai wajen ƙarfe goma aka kira su, Inna ta kama hannun A'isha suka shiga office ɗin likitan. Bayan sun gaisa Inna ta yi masa sannu da aiki ya tambaye su abun da yake tafe da su. Inna ta yi masa bayanin duk abun da ya samu A'isha, shiru ya yi na wasu ƴan sakanni, da alama jinjina al'amarin yake yi a cikin ransa. Cikin nuna damuwa ya ce. "Ya Subhanallahi, zazzaɓin mai zafi ta yi ne sosai?" Inna ta ce. "Eh gaskiya ta ji jiki." Likitan ya jinjina kai sannan ta taso ya zo inda suke zaune ya dudduba jikin Aisha. Yana yi yana yi mata tambayoyi tana ba shi amsa, sosai yarinyar ta ba shi tausayi, ƴar ƙaramarta da ita a ce ta rasa ganin ta, duk da dai ana haifar waɗanda ba sa ganin ma, amma nata sai ya fi zama abun damuwa tunda ita already ta san daɗin ganin. Bayan ya koma ya zauna ya dubi Inna ya ce. "Baaba a gaskiya wannan matsalar ba za mu iya magance muku ita a wannan asibitin ba, kasancewar ba mu da k'wararrun likitocin ido, ɗan ciwon ido dai haka da ake fama da shi ko jan ido wannan duk mu na iya bayar da maganinsa, amma idan abun ya girmama, ko ciwon idon da dole sai an yi masa aiki to fa sai dai mu tura mutum can Kano ya je a yi masa, dan haka yanzu ke ma sai dai mu tura ki can asibitin Makkah." Da sauri Iya ta ce. "Asibitin Makkah kuma likita?" Likitan ya yi murmushi ganin Yanda Inna ta yi, ya ce. "Ba wai garin Makkah na cikin ƙasar Saudiyya ba, a'a, wani asibiti dake nan cikin jiharmu Kano mai wannan sunan, to insha Allahu matuƙar kun je can za'a dace." Inna ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Amma asibitin na kuɗi ne ko na Gwamnati?" Likita ya ce. "Private hospital ne, na kuɗi." Inna ta jinjina kai cikin damuwa ta ce. "A asibitin gwamnatin shi ba za a iya duba mata idon ba?" Likita ya ce. "Za'a iya, har aikin ma idan ta kama duk za'a iya yi mata, amma maganar gaskiya asibitin Makkah ya fi, idan da hali ku je can ɗin." Inna ta goge wani gumi da yake tsatstsafo mata a goshi ta ce. "To shikenan likita, na gode sosai Allah ya saka da Alkhairi, insha Allahu sai a je can ɗin." Likita ya ce. "To ba damuwa, Allah yasa a dace." Ya kalli A'isha ya ce. "Sannu kin ji, Allah ya ba ki lafiya." Suka amsa da Amin sannan Inna ta yi masa sallama suka fito. Bayan sun fito daga asibitin A'isha ta cewa Inna. "Inna ba zan ƙara gani ba ko? Shikenan na daina ganin ku na daina ganin komai da kowa?" Inna ta shafi kanta ta ce. "Zaki cigaba da gani insha Allahu A'isha, ke dai ki yi ta addu'a, kar ki gaza kin ji?" A'isha ta ce. "Toh."
Hankalin Inna a tashe suka dawo gida, babbar damuwarta rashin kuɗi da rashin hanyar samun sa, domin ta san maganar zuwa asibitin Kano dole sai ta tanadi kuɗi masu kauri, musamman da likitan ya sako maganar aikin ido, ta san kuɗin aiki ba ƙaramin kuɗi ba ne, ita kam zata iya cewa ba ta taɓa riskar kanta a cikin tashin hankali irin wannan ba, wani irin tausayin A'isha ne yake ƙara mamaye mata zuciya game da wannan ƙaddarar da Ubangiji ya ɗoro mata, sai dai ba ta ƙasa a gwiwa gurin kaiwa Ubangiji kukanta a kodayaushe akan ya yayewa A'isha wannan makanta. Bayan ta gama zayyanewa innar Ma'u abun da ya faru a asibitin ta ƙara da cewa. "Babban tashin hankalina inda zan samu kuɗin da zan kai yarinyar nan Kano a duba ta, mu da ko abun da za mu ci ma gagarar mu yake yi." Innar Ma'u ta sauke numfashi ta ce. "Ubangiji shine zai kawo mana mafita Asabe, insha Allahu Allah zai warware." Inna ta ce. "Ni yanzu sana'ar da zan kama nake tunani, na rasa me zan siyar a garin nan wanda zan dinga samun k'wandala da ficika." Innar Ma'u ta ce. "Tun kwanaki nake son na yi miki magana akan aikin abincin sadakar da muke yi a gidan Hajiya Talatu duk ranar juma'a, wannan fargabar ciwon A'ishan da muke ciki ne yasa na sha'afa. Ɗaya daga cikin wanda muke yin aikin tare ce ɗanta ya ɗauke ta ya mayar da ita can Kano gidansa, to kuma har yanzu ba'a samu madadinta ba, zan yiwa Hajiyar magana idan mun je wannan satin, idan Allah ya saka da rabonki sai ki maye gurbin waccan ɗin, aikin 500 ne kullum kuna gamawa za'a sallame ku, sannan kuma za'a baku abinci sosai wanda zai ishe ku, ku ci daga rana har dare." Cikin jin daɗi Inna ta ce. "Amma na gode sosai Ladidi, Allah ya saka da Alkhairi yasa ta ɗauke ni." Innar Ma'u ta ce. "Insha Allahu zata ɗauke ki, dan ba ta da matsala matar, ga ta da ihsani." Inna ta ce, "Allah yasa a dace." Innar Ma'u ta ce, "Amin Amin, ga wata shawara kuma, zan cewa mutane ina yin Nik'an kayan miya namu na gargajiya na dutse da muke yi, idan an kawo mun sai in baki kina yi ki karb'i kuɗin kya rage wasu abubuwan da shi. Tunda idan ke kika ce kina yi ba za'a na kawo miki ba." Inna ta ce. "Na gode, na gode sosai Ladidi, Ubangiji ya taimake ki kamar yadda kike taimako na, ba dan dake ba a cikin gidan nan da ban san yanda zan yi ba." Innar Ma'u ta ce. "Kin wuce haka a gurina Asabe, yanda nake jin ki a cikin zuciyata tamkar ƴar'uwata ta jini, dan haka babu godiya a tsakaninmu, fatanmu kawai Ubangiji ya dafa mana akan dukkan al'amuran rayuwarmu." Inna ta ce. "Amin."
Da yamma Ɗan_juma suna zaune akan wani dakali ɗan nesa da gidansu shi da wasu abokanansa guda biyu suna hira sai ga wani abokin nasu wanda gidansu yake jikin nasu A'isha shi ma ya zo. Bayan sun gaisa ya dubi Ɗan_juma ya ce. "Ɗan_juma ɗan Sarki jikan Sarki kuma Sarkin gobe da yardar Allah, yau ina tafe da wani labari mai daɗin gaske." Ɗan_juma ya yi murmurshin jin daɗin kirakin da Hamza ya yi masa ya ce. "Shaƙa mun cikin gaggawa, ni kuma in shaƙa maka tukuici mai nauyin gaske." Hamza ya ce. "Labari ne akan Yarinyar can daka ƙwallafa rai a kanta, yau kwana huɗu kenan da wayar garin da aka yi ba ta gani, a tak'aice dai ta zama marainiya." Cikin mamaki Ɗan_juma ya ce. "Kar dai ka ce mun A'isha?" Hamza ya ce. "Ita fa." Wani yalwataccen murmushi Ɗan_juma ya saki ya ce. "Kaii, amma na ji daɗin wannan labari Hamzeze, saboda zai samar mun da hanya mafi sauƙi ta cikar burina akan A'isha, ka ga watarana idan uwar ta_ta ta tafi yawon nemo musu na cin ƙanzo sai mu zagaya mu farmata, mu yi mu gama mu ƙara mai ba tare da ta san mu ba ne, tunda ba ta gani balle ta gane su waye. Sakamakon wannan labari da ka kawo mun Hamza, kai ne na biyu a yin wannan harka bayan na gama." Hamza ya fashe da dariya suka tafa shi da Ɗan_juma wanda shi ma yake dariyar, sauran abokan nasa su ma suka taya su, domin sun san da su za'a yi wannan harkar...........✍️
*By*
*Zeey Kumurya*
*💖 KOMAI NISAN DARE.....! 💖*
_By_
_Zeey Kumurya_
*ELEGANT ONLINE WRITER'S*
*0️⃣7️⃣*
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 08066268951
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_
.........Cikin ikon Allah rayuwa ta fara warware wa su Inna, domin kuwa kamar yadda innar Ma'u ta faɗa ta yiwa Hajiya Talatu magana kuma ta ɗauki Inna, duk ranar juma'a tana samun 500 ɗinta sannan kuma ga abinci wanda za su ci su ƙoshi a ranar har dare, har washegari ma yake kai musu su d'umama su yi karin kumallo da shi. Ƴar Innar Ma'u ta fari ta kawo mata ɗanta mai suna Yusuf, ana kiransa da Malam ƙarami, ya dawo hannun Innar Ma'un gaba-d'aya da zama. Shine Innar Ma'u ta cewa Inna ta dinga yin aya mai sugar da Mai gishiri sai ya dinga fitar mata da ita idan ya dawo daga makaranta. Inna ta yi Na'am da wannan shawarar, ba tare da jinjiri ba ta siyo ayar ta fara soyawa. Alhamdulillah ana ciniki sosai, dan duk mutanen gari ɗaukar su Innar Ma'u ce take yi, ga kuma Nik'an kayan miyan shi ma ana kawowa ba laifi, Dai_dai gwargwado Inna sun samu rufin asiri, cikin abun da bai fi sati biyu ba ta biya Innar Ma'u duka bashin da take bin ta, sannan ta fara bankin ajiyar kuɗin kai A'isha asibitin Kano.
Yau juma'a, da yamma Inna suna ɓangaren su Innar Ma'u suna Nik'an kayan miyan wani biki da za'a yi anan unguwar ita da Innar Ma'un. A'isha da Ma'u suna gefe Ma'u tana ba ta labarin abubuwan da suke faruwa a makaranta. A'isha ta dubi saitin da take jin muryar su Inna ta ce. "Inna kin ji, Malam Buba kullum sai ya zo aji yana nema na, wai za'a mun passport ɗin zana jarabawar komen." Inna ta ce. "Me cece haka ita abun da zaki zana ɗin?" A'isha ta ce. "Jarrabar shiga Sakandire ce." Inna ta ce. "A'a, ba aji biyar kuke ba? Ina sai an zo aji Shida ake zanawa?" A'isha ta ce. "Ai zaɓar mu aka yi mumu uku a ajinmu aka ce zamu zana." Inna ta ce. "Toh, dama ana yin haka?" Innar Ma'u ta ce. "Eh mana, ƴar gidan gaji ma ai a aji biyar ta gama firamare, ita ma zaɓar su aka yi, masu ƙoƙari suke zaɓa ai." Inna ta ce. "Tab'dijan, to ke da ba lafiya ba ina kika ga ta wani zana jarrabawa? kawai ki bari sai wata shekarar, kafin nan kin samu lafiya da yardar Allah, sai ku zana tare da Ma'u." A'isha ta ɓata fuska ta ce. "Ni dai Inna dan Allah ki bari in zana, an ce ma akai kuɗin jarrabawar 600 ko Ma'u?" Ma'u ta ce. "Eh, kullum sai ya ce in faɗa miki ma." Inna ta ce. "To da wanne idon zaki yi rubutun jarrabawar? Ki haqura kawai ki bari sai wata shekarar, sai ku zana tare da Ma'u." Innar Ma'u ta ce. "Ai ita ma Ma'un wannan shekarar zata zana, Kawunta ya ce ta isa shiga Sakandiren, Ranar Litinin zan bata kuɗin insha Allahu ta kai, tunda sun ce duk mai so zai iya biyan kuɗi ya zana." Inna ta ce. "To ai A'isha ita matsalar ba ta gani, amma sai mu je makarantar ranar Litinin ɗin mu ji ya za'a yi." Jin abun da Inna ta ce sai A'isha ta fara murna, dama ta gaji da zaman gidan, dan ko zaure Inna ba ta barin ta, ta je, sai dai in zata fita ne Innar Ma'u ba ta nan take tafiya da ita duk inda zata, idan kuma innar Ma'u tana nan sai ta bar ta a gurin ta. Washegari A'isha ta takurawa Inna sai ta je gidan Malama karatu, ita ta gaji da zaman gida har da kukanta. Inna ta ce to ta saka hijabinta Ma'u ta kama hannunta su tafi, Allah ya kiyaye. Zuciyar A'isha cike da zumud'i suka tafi. Idan ba sani ka yi ba ko an faɗa maka baza ka ce A'isha makauniya ba ce, domin idanunta a buɗe suke kuma babu alamar mara sa lafiya ne, ga ta tsaf fess da ita, Inna tana tsaftace ta yanda ya kamata, dan Inna akwai tsafta. Suna zuwa gidan Malama yara suka fara tsokanar A'isha suna cewa. "Ta zama makauniya!! Ta zama makauniya!!" Dama abun da Inna take gudu kenan shi yasa ba ta barin A'isha ta fita ko nan da can ba tare da ita ba. Ita kuwa A'isha ba ta kula su ba, guri kawai ta nema ta yi zamanta, Ma'u ce ma take yi musu magana. Sai da Malama ta fito ta tsawatar musu sannan suka bari. Hak'uri ta dinga bawa A'isha cikin tausayawa, sosai yarinyar take ba ta tausayi tun a daa, ga kuma jarrabawar da Ubangiji ya ƙara ɗora mata. Ko kaɗan abun da yaran suka yi bai damu A'isha ba, duk da ta ji zuciyarta ta karye kamar za ta yi kuka, amma dai ta daure ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 20