Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ke ma 'yata ce kamar su Khalifa, ki saki jikinki ki yi rayuwa kamar kowa a gidan nan kin ji?" Gyaɗa masa kai ta yi tare da yin ƙasa da kanta. Ganin har yanzu ba ta saki da jiki da zaman gidan ba Abba ya shiga yi mata nasiha, ya san mutuwar Inna har yanzu tana dukan ta. Shi ya sa yake son ta shiga school ko hakan zai rage mata damuwa. Bayan kwana uku aka yi sadakar bakwai ɗin Inna kamar yadda aka yi ta uku, har lokacin A'isha ba ta daina kukan mutuwar Inna ba, kulawa da ƙaunar da Ummi da Abba ke nuna mata ke rage mata damuwa, gami da ƙara saka mata nutsuwa akan zaman ta a gidan. Lokuta da dama za ta kwanta da sunan bacci, amma baccin za ta yi ba, tunanin Inna da yadda suka gudanar da rayuwarsu take cikin hawaye, hakan ya saka kullum take fama da matsanancin ciwon kai. Duk da ta samu hutu da cima mai kyau amma kullum ƙara rama take. Kwanaki bakwan nan da suka wuce jin ta take tamkar mai rayuwa cikin mafarki, ko ƙaƙa ta yi bacci ta farka sai ta ji tamkar za ta ji muryar Inna tana mata magana, ko za ta tashi su cigaba da rayuwa a gidansu. Sai dai ta tabbatar hakan ba zai taɓa faruwa ba, Inna ta riga ta tafi ba za ta dawo ba. Ta san mutuwa gaskiya ce, duk wani mai rai jiran ta yake. Da yamma tana zaune ita kaɗai a parlour tana tunanin da ta saba, Ummi na toilet tana wanka, Ya Maamah ta koma Abuja gidan mijinta, Gwaggo ma ta koma Gombe kwana biyu da suka wuce. Kasa daurewa ta yi duk da ba ta son Ummi ta gan ta tana kuka ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Cikin kukan take faɗin. "Allah ya ji ƙan ki Innata ya gafarta miki, rashin ki a cikin rayuwata daidai yake da na rasa farinciki na har abada. Ban taɓa tunanin ko da wasa akwai ranar da zan yi rayuwa babu ke ba." Ta ja majina tare da yin sheshshek'a ta ce. "Allah ya kai haske kabarinki." A haka Ummi ta zo ta tarar da ita tana gunjin kuka. Hankali a tashe Ummi ta ƙarasa kusa da ita ta zauna tana tambayar ta dalili kukanta, a tunaninta wani ne ya shigo ya yi mata wani abun. "Me ya faru? Ko wani ya shigo ya miki wani abun? Shi ya sa bana son kina zama ke kaɗai a guri." Girgiza kai ta yi cikin ƙoƙarin tsayar da kukan. Ajiyar zuciya Ummi ta sauke ta ce. "To me ya faru?" "Babu komai." Ta ba ta amsa tana goge hawayen fuskarta. "Ko garinku kike son zuwa?" Nan ma girgiza mata kai ta yi. Dafa kafaɗarta Ummi ta yi ta ce. "To ki yi haƙuri ki bar kukan nan haka kar ki jawo wa kanki wani ciwon, na san rashin mahaifiyarki ne yake damun ki, amma ba kuka ya kamata ki zauna kina yi ba idan kika tuno ta, addu'a za ki yi mata, Allah ya ji ƙan ta." Numfashi ta sauke tare da gyaɗa mata kai. Cikin tausayawa Ummi ta ce. "Mutuwar Uwa akwai ciwo da dukan rai, amma sai haƙuri babu yadda za mu yi. Idan zafin abun ya taso miki ki dinga kiran sunan Allah ko kina karatun Alkur'ani, za ki ji sauƙin abun insha Allahu." Cikin raunin murya ta ce. "Zan na yi insha Allah, na gode." Ummi ta ce. "Mu je ɗaki ki kwanta ki huta kafin a kira Sallah, na san kanki ba zai kasa yi miki ciwo ba." Washegari kafin bakwai na safe sun gama shirin tafiya Asibiti. Abba ya shiga part ɗin Mommy don yi mata sallama, ya tarar da ita a kwance tana bacci. Tashin ta ya yi ta buɗe ido da ƙyar. "Zan fita." Abba ya faɗa a taƙaice, don har yanzu bai gama hucewa daga abin da take yi ba. Miƙa ta yi gami da hamma ta tashi zaune. Cikin muryar bacci ta ce. "Ina kuma za ka je da sassafen nan na gan ka cikin shiri?" "Za mu kai Nana asibiti ne?" Cikin rashin fahimta ta ce. "Wace ce kuma Nana da za ta fitar da kai da sassafen nan? Ko Baby ce babu lafiya ai sai haka." Abba ya ce. "Yarinyar da na kaɗe su nake nufi, kin san tana da matsalar ido." Taɓe baki ta yi ta ce. "Ina zan sani tunda ba a wurina take ba? Sai kun dawo to." "Yanzu ai kin sani." Ya faɗa tare da juyawa zai fice. Tsaki ta ja a ranta tana mitar akan wannan shirmen zai katse mata daddaɗan baccin da take ya ƙara mata ɓacin rai. Ya ji tsakin da ta yi, amma bai ce komai ba ya fice. Asibitin Makkah suka je, aka yi wa A'isha gwaje-gwaje a idon bayan an buɗe mata File. 1 week aka ba su, su dawo don karɓar sakamakon gwajin. Daga nan gidan Aunty Ruƙayya suka zarce dake gadon ƙaya, Ummi ta bar ta a can, ta ce idan ta dawo daga school za ta biyo ta ɗauke ta. Sai yamma Ummi ta baro school a gajiye, hakan ya sa ta wuce gida tun da ya fi kusa. A Polytechnic ta matan fada take lecturing, department of Pharmacy. Su kuma suna zaune a unguwar Railway ne. Tana ƙoƙarin shiga wanka Khalifa ya shigo ɗakin, zama ya yi a gefen gado ya ce. "Sai yanzu kika dawo? Na ji da muka yi waya kamar kina hanya." Ummi ta ce. "Eh yanzu na shigo, dama kiran da na yi maka Nana za ka je ka ɗauko a gidan Ruƙayya, na gaji sosai ba zan iya driving har Gadon ƙaya ba, kuma zan yi girki anjima." Khalifa ya ce. "Okay, amma gaskiya Ummi ya kamata ki ƙara samo mai aiki, aikin gidan nan ya miki yawa ke kaɗai, ga shi ke ba zama kike ba." Ummi ta ce. "Zan saka a nemo mini ko dan Nana ta samu mai kula da ita idan bana nan, ba na son yara ne wanda sai an shaƙu su yi aure, har yanzu ban daina kewar Lami ba, shi ya sa ko zan kuma mai aiki na fi son dattijuwa." Khalifa ya ce. "Gaskiya kam, bari na je na ɗauko ta kar Magriba ta yi, Kin ji su Yaya jibi za su dawo ko?" Ummi ta ce. "Ya faɗa mini, ɗazu da muka fita Abbanku yake ƙara sanar mini, Allah ya kai mu ya kawo su lafiya." Miƙewa Khalifa ya yi ya ce. "Amin, na tafi." Ummi ta ce. "Allah ya kiyaye ya tsare, sai kun dawo." Ya amsa da Amin tare da ficewa. A'isha tana parlour a zaune ita kaɗai Khalifa ya shigo. Juyar da kanta ta yi inda ta ji motsi, yadda ta ware daradaran idanunta ba za ka taɓa cewa makauniya ba ce. Ƙura mata ido ya yi cikin faɗuwar gaban da bai san dalilin ta ba. A hankali ya taka ya ƙarasa cikin parlour'n tare da yin sallama. Amsa masa ta yi cikin murmurshin jin daɗin zuwan shi. "Indodo." Ya faɗa cikin tsokana. Murmushi ta ƙara yi tare da faɗin. "Ina yini?" Yana zama a kusa da ita ya ce. "Lafiya ƙalau, ya na gan ki ke kaɗai, ina Aunty da su Ihsan?" "Suna ciki." Ta ba shi amsa cikin sanyin murya. Zai kuma magana Aunty Ruƙayya ta fito daga kitchen, da mamaki ta ce. "A'a, Babana yaushe ka zo?" "Yanzun nan, Ina yini?" "Lafiya ƙalau, ya aiki?" "Alhamdulillah." "Ka zo tafiya da ita ne?" Ya ce. "Eh, Ummi ce ta ce na zo na ɗauko ta." Aunty Ruƙayya ta ce. "Ai na ɗauka za ta bar ta kwanar mana biyu a nan, Kodayake gobe Friday ba jimawa za ta yi ba a school." Khalifa ya ce. "Ai ummi ba za ta iya barin wannan tsohuwar ta kwana a wani gurin ba, ji take da ita kamar ɗanyen ƙwai." Aunty Ruƙayya ta ce. "Ta ma fi ƙwai ko Mamana?" Murmushi kawai A'isha ta yi ba ta ce komai ba. Daidai lokacin Ihsan ta fito daga ɗaki, da fara'a sosai ta dubi Khalifa ta ce. "Mun yi fushi Ya Khalifa gaskiya." "Me kuma na yi?" Ya tambaya cikin marairaicewa. Ta ce. "Yaushe rabon ka da gidan nan, sai yau da ƴar gidanku ta zo muka gan ka." Ya ce. "A yi haƙuri tuba nake." Dariya ta yi tare da gaishe shi. Ko 10 minutes ba su ƙara ba Khalifa ya ce za su tafi kar dare ya yi, kayan cosmetics da turaruka Aunty Ruƙayya ta ba wa A'isha, ta yi mata godiya sannan Ihsan ta kama hannunta suka fita ta raka su bakin Motor. Sai da Khalifa ya tsaya a hanya ya yi wa A'isha shopping kafin su je gida. Hankalin Mommy ya yi kan shirye-shiryen tarɓar ɗanta da Matarsa wadda ta kasance ƴa ga Kaltum ƙanwarta. Shi ya sa ta ajiye batun A'isha a gefe ba don ta haƙura ba. Yadda ake toye-toye da abubuwa sai ka yi zaton shugaban ƙasa ne zai dawo. Kasancewar shi ma'abocin tsafta da son ta ya sa tun saura kwana biyu su sauka masu aiki suke bautar gyaran part ɗinsa dake gidan, tamkar za su sauya masa halitta saboda ƙalƙala. Yau tun safe Ihsan ta zo da yake weekend ne babu school, A'isha ta ji daɗin zuwan ta sosai, saboda ita ma kamar su Ummi take babu ruwanta, ga faran-faran da son jama'a. Bayan Sallar la'asar Ummi tana bedroom tana azkar, Khalifa kuma ya tafi airport ɗauko su Safwan. Hannun A'isha Ihsan ta kama ta ce. "Zo mu fita compound mu shaƙata." A'isha ta ce. "Wacce irin shaƙatawa kuma?" "Ke dai ki zo mu je." Ihsan ta faɗa tare da jan ta suka fice. Suna zaune a kan kujerun roba wayar Ihsan ta yi ringing, dubawa ta yi ta miƙe ta ce. "Bari na ɗan leƙa waje na dawo, wani guy ne ya zo za mu gaisa, yanzu zan dawo." Gyaɗa mata kai kawai Aisha ta yi, ɗaga kiran ta yi tare da barin wajen. Buɗe makeken gate ɗin gidan tare da shigowar wata rantsatstsiyar mota, ya saka Mommy dake tsaye a gaban window sakin murmushin farinciki dawowar ɗanta Namiji tilo a duniya, wanda take gani da jin duk duniya tamkar babu ɗan da ya kai shi. Sakin labule ta yi ta koma ta zauna tana jiran shigowar shi. Bayan Khalifa ya yi parking Safwan ya sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idonsa ya buɗe. A hankali ya buɗe motar ya fito yana kallon harabar gidansu da ya shafe watanni ba a cikinsa ba. After some seconds ya buɗe bayan Motar tare da ja baya. Wata farar matashiyar mace siririya ce ta fito tana yamutsa fuska tare da kare fuskarta da hannunta. Yanayin shigar jikinta ba za ka ce matar aure ba ce idan ba faɗa maka aka yi ba. Kanta ta ɗora a kan kafaɗarsa, cikin marairaicewa ta ce. "I'm so tired mine." Gefen fuskarta ya shafa cikin kulawa ya ce. "Sorry." A taƙaice. Ba ta ce komai ba ta bar jikinsa jin wayarta dake hannunta na ringing. Picking ta yi tare da nuna masa hanya alamun ya yi gaba za ta taho. Bai ce komai ba ya juya ya fara tafiya cikin nutsuwa, a ransa yana mamakin daga saukar su har ta saka sim ɗinta na Nigeria an fara kiran ta. Khalifa dake kallon su ya taɓe baki tare da buɗe murfin motar ya fito shi ma. A'isha ta fara gajiya da jiran Ihsan, ga iska sai ƙadawa take sanyin la'asar yana ratsa ta. Ganin iskar na takura ta ya sa ta miƙe ta fara tafiya a hankali cikin laluben hanya. Ba zato ta ji ta yi karo da wani abu, taga-taga ta yi za ta faɗi ya yi saurin ruƙo ta yana yatsina fuska, ko kaɗan bai lura da mutum yana tahowa ba saboda ba ta gabansa take ba ta gefen shi take. Ita kuwa Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi jin ba ta kai ƙasa ba, siririn tsaki ya ja ya zare ta daga jikinsa tare da yin gaba ba tare da kuma kallon inda take ba. Tsayawa ta yi cak ta kasa cigaba da tafiya, saboda tsoron kar ta kuma karo da wani abun. Mamakin wanda suka yi karo da shi ne ya cika mata zuciya, su yi karo da mutum amma ya ƙi magana sai ka ce kurma. Ta san ba Ya Khalifa ba ne ko Abba, don in su ne ba za su taɓa wucewa su bar ta ba, kuma ƙamshin da ta ji a jikin mutumin ba irin nasu ba ne, ba ta taɓa jin irin ƙamshin ba tunda ta zo gidan sai yau. Lumshe ido ta yi saboda yadda daɗin ƙamshin yake ratsa ta, duk da ya bar gurin amma ƙamshinsa bai daina ratsa ƙofofin hancinta ba. Jin ƙarar taku ya sa ta sakin ajiyar zuciya, a tunaninta Ihsan ce ta dawo, tana shirin yin magana ta ji an wanke ta da wani gigitaccen mari, ba ta gama fita daga ɗimuwar marin ba ta ji an damƙi wuyanta tare da lailayo mata narkekiyar ashariya gami da faɗin. "Dabbar ina ce ke da za ki bari ki yi karo da mijina har ki gogi jikinsa? wallahi sai na kashe ki tunda kika haɗa jiki da mijina!" Ta ƙarashe maganar cikin ƙaraji.........✍️ *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣8️⃣* Khalifa da ya tsaya yana magana da ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ya yi saurin ƙarasowa inda suke yana faɗin. "Salma! Mene haka? Ba ki da hankali ne za ki mata irin wannan shaƙar?" Ya ƙarashe maganar cikin fusata tare da ƙoƙarin ɓanɓare hannunta daga wuyan A'isha, amma ta ƙi sakin ta sai ma ƙara cakumar ta take cikin bala'i. Marin da Khalifa ya sauke mata ne ya sa ta sakin A'isha ba shiri tare da dafe kuncinta da take jin tamkar ba ya jikinta, saboda tsabar zaraɗaɗi da zafin marin da ya ratsa ta. "Ni ka mara Khalifa?" Ta tambaya cikin tsantsar mamaki da ɓacin rai, idanunta cike da ƙwallar takaici. Khalifa bai kula ta ba ya riƙo A'isha dake numfarfashi gami da hawaye. "Are You okay?" Ya tambaye ta a ruɗe ta cikin damuwar halin da take ciki. Ganin yadda take kuka ya ƙara ɗaga masa hankali. Daidai lokacin Ummi da ta fito parlour ba ta ga sun ba ta duba ko'ina duk ba ta gan su ba ta fito compound ɗin. Hango su a tsaye Khalifa na riƙe da A'isha ya sa ta ɗaga murya ta ce. "Khalifa Lafiya? Me yake faruwa?" Numfashi ya sauke mai zafi yana jifan Salma da wani mugun kallo wadda ta yi suman tsaye, a kufule ya ce. "Shaƙe ta ya yi tana ƙoƙarin kashe ta." "Subhanallahi, shaƙa kuma kamar ya? Akan me?" Ummi ta tambaya a ɗimauce tare da ƙarasowa ta janye A'isha tana faɗin. "Me ya faru ne wai? Ina Ihsan ɗin?" A'isha za ta yi magana amma ta kasa saboda kukan da take, har yanzu jikinta bai daina rawar firgici ba, don ba ƙaramar shaƙa ta sha ba. Khalifa da yake jin tamkar ya rufe Salma da duka ya juya ya bar wajen, saboda idan ya cigaba da tsayawa yana kallon ta zai iya yi mata abin da ya fi mari. "Wallahi sai ka yi nadamar mari na da ka yi, zan nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne." Salma ta faɗa a zuciye tare da wucewa ta nufi ciki a matuƙar fusace. Da kallo kawai Ummi ta bi ta ta kama hannun A'isha suka shiga ciki. Direct part ɗinsu ta wuce a maimakon na Mommy da ta yi niyya, Upstairs ta haye ta buɗe bedroom ɗinsu ta shiga, zuciyarta har wani huci take saboda zafin da take ji a cikinta, an daɗe ba a yi mata abin da ya yi ƙoluluwar ɓata mata ran da Khalifa ya yi ba yau. "Ni zai mara yana ƙanin mijina akan wata SHEGIYA? Wacece ita da har wani mahaluƙi zai kai hannunsa jikina saboda ita?" Ta yi maganar cikin ɗaga murya tare da cillar da wayarta kan gado ta fara kai kawo a cikin ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin tare da wanzuwar ƙamshinsa a cikinsa ya sa ta juyawa cikin sauri ta fuskanci shi. Ƙura mata ido ya yi cikin faɗuwar gaba saboda ganin yanayinta, a duniya idan akwai abin da yake gudu da tsoron faruwar shi to ɓacin ran matarsa abar ƙaunar shi ne. Cikin damuwar da ta kasa ɓuya a ransa ta bayyana a fuskarsa ya ce. "Lovely what happened to you? Wa ya taɓa mini ke?" Ya ƙarshe maganar tare da ƙoƙarin riƙe ta. "Don't touch me!" Ta faɗa cikin tsawa. Tsayawa ya yi cak tare da runtse idonsa, don ba ƙaramin ratsa shi tsawar ta yi ba. Cikin kakkausar murya ta ce. "Ƙaninka ya mare ni saboda na mari wata aba da ba ta kai in saka ta a jerin mutane ba, ka je ka rama mini yanzu-yanzu ba sai ya lokaci ya ƙure ba, don da zafi-zafi ake dukan ƙarfe." Cikin ɓacin rai ya ce. "What? Khalifa ne ya mare ki ko wa?" "Kana da wani ƙanin ne bayan shi?" Ta tambaye shi cikin tarar numfashi. Bai ce komai ba ya juya ya fice da sauri cikin ɓacin rai. Ajiyar zuciya ta sauke ta zauna a bakin gado, sai yanzu ta ji ta fara hucewa saboda sanin babu abin da zai hana Safwan rama marin da Khalifa ya mata, ko da kuwa a gaban Ummi da Abba ne, ko da yana sauke hannunsa daga fuskar Khalifa za su ba shi nasa marin, shi dai tunda ta ce ya je ya rama mata sai ya yi. Ummi tana zaune a kan kujera A'isha na jikinta tana rarrashin ta bayan ta faɗa mata abin da ya faru da ƙyar cikin kuka ya shigo cikin parlour'n tamkar an cillo shi yana kiran sunan Khalifa. Ɗago kai ta yi ta kalle shi, ganin yadda yake huci ta haɗe rai ta ce. "Khalifa ba ya nan, sai ni uwarsa idan za ka rama mara marin a kaina, tunda kai ma uwarka ya mara." Kallon ta ya yi kamar zai magana sai kuma ya fasa ya juya ya fice daga parlour'n. Tsaki Ummi ta yi cikin takaici, a ranta tana masa addu'ar Ubangiji ya kawo ranar da zai bar wannan rayuwar ta raƙumi da akala da Salma ke jan shi. A'isha kuwa cak ta tsayar da kukanta tare da ƙara ƙanƙame Ummi, ba ta san waye ya shigo ba, ba ta taɓa jin muryarsa ba tunda ta zo gidan, amma yadda ya shigo yana kiran sunan Khalifa cikin ƙaraji da masifa ya sa tsoron shi ya dirar mata a zuciya lokaci ɗaya. Mommy da ta ga gilmawar su ta window ta miƙe cikin sauri ta nufi part ɗin nasu, Upstairs ta hau don ta san suna can, ganin ba sa parlour ta nufi bedroom ɗin Salma ta shiga. "Lafiya na ga my son ya wuce a firgice? Ke ma kamar wadda ranta ke ɓace." Mommy ta faɗa cikin mamaki ganin yanayin Salma. A shagwaɓe ta ba ta labarin duk abin da ya faru. Ashariya Mommy ta lailayo ta narka ta ce. "Khalifan ne ya mare ki? Yana cikin hankalinsa kuwa? Ko ya fara shaye-shaye ne?" Taɓe baki Ta yi cikin ƙara jin zafin abun a cikin ranta ta ce. "Wa ya san masa, amma wallahi bai mari banza ba, bayan Mine ya rama mini sai na kuma ɗaukar mummunan mataki a kan shi, sai ya gane kurensa, zai san da ni yake zancen." Mommy ta ce. "Gaskiya wannan yarinyar annoba ce, babu Alkhairi kwata-kwata a tattare da ita, daga saukar ku har ta yi sanadin abin da ya ɓata muku rai?" Ƙwafa Salma ta yi cikin ɗacin rai, har yanzu ba ta daina ganin lokacin da A'isha suka yi karo da Safwan a idonta ba. Runtse idonta ta yi jin kamar an saka mashi an soki zuciyarta, a yadda zuciyarta take tafarfasa lokacin da ta shaƙe A'isha ba don Khalifa ba da za ta iya kashe ta har lahira. Duk da ransa a ɓace yake amma a nutse yake tafiya, da sallama ya shiga bedroom ɗin amma ba su amsa masa ba, sai ido da suka zuba masa suna jiran jin irin matakin da ya ɗauka akan Khalifa. Sanin halin miskilancinsa ba lallai ya yi magana ba ya sa Mommy ta ce. "Da fatan ka masa dukan mutuwa dai?" Idanunsa a kan Salma da ta tsare shi da ido ya ce. "Ban same shi ba." "Uwarsa ta ɓoye shi kenan." Mommy ta faɗa a harzuƙe. Bai ce komai ba ya ƙarasa ya zauna a kusa da Salma tare da ƙoƙarin kama hannunta. Wani kallo ta wurga masa tare da miƙewa tsaye ta ce. "Babu abin da za ka ce mini Safwan, ai komai ya faru lefin ka ne, yarinyar ta rungume ka amma ka kasa ɗaukar mataki a kanta, sai kawai ka tafi ka bar ta, maimakon ka ture Shegiya ka yar da ita ta faɗi ka tattake cikinta? Amma ka ƙi saboda ba ka kishin kanka bare...." A tsawace Mommy ta katse ta faɗin. "Ya isa haka Salma, kin san bana son wannan tsiwar taki da rashin ɗa'ar da kike masa ko? Sai ka ce ba mijinki ba." Kuka ta fashe da shi tare da faɗin. "Amma Mom rungume shi fa wata ta yi a gabana, don na nuna ɓacin raina laifi ne? Mijina ne fa, kuma kin san ina tsananin kishin shi." "Shikenan ya isa, mu je ƙasa ku ci abinci sai ku yi wanka ku huta, kar ki saka damuwar wasu sakarai a cikin ranki ki ɓata mood ɗinki, ki bar komai a hannuna za ki ga matakin da zan ɗauka." Mommy ta faɗi haka tare da juyawa ta fice. Da sauri Safwan ya miƙe ya janyo Salma jikinsa, kukan nan da take ji yake tamkar ana watsa masa garwashi a cikin ransa, yadda kukan yake taɓa ransa ba ya jin zai iya ƙara sakanni bai rarrashe ta ba, ko da a gaban Mommy ne kuwa. A ruɗe ya ce "Please stop crying My one, kin san babu abin da tsana a rayuwata sama da zubar hawayenki." Ƙara fashewa da kukan ta yi cikin son ta ƙara ɗaga masa ta ce. "Dole na yi kuka Mine, wata ce fa ta taɓa jikinka a gaban idona." Numfashi ya sauke mai zafi yana jin da zai ƙara ido huɗu da yarinyar sai na lahira ya fi ta jin daɗi, saboda sanadin zubar hawayen sanyin idaniyarsa da ta yi. Cikin rikicin da kukan nata ya ƙara saka zuciyarsa ya ce. "Taɓa jikina da ta yi ba ya nufin wani ba ne Lovely, kin fi kowa sanin ni naki ne ke kaɗai, wallahi duk macen da na gani kallon Namiji kamata nake mata, ke kaɗai idanuna suke gani a cikin mata, don Allah ki daina mini asarar hawayenki akan wata kucaka, Please Lovely kar zuciyata ta tarwatse." Ganin yadda ya rikice sai ta ɗan saki fuskarta tare da ƙara lafewa a jikinsa. Da ƙyar ya rarrashe ta, ta haƙura suka sauka ƙasa don cin abinci. Sai lallaɓa ta yake tamkar ɗanyen ƙwai, ita kuma tana ta ƙara botsarewa. Bayan ya ja mata ɗaya daga cikin kujerun dinning ta zauna ya ce. "Let me serve you dear, me kike son ci?" Yadda ya yi maganar tamkar bawa da Uwargijiyarsa ya sa Mommy da ta dawo parlour'n tsayawa cak cikin bugawar zuciya. 'Me take shirin gani haka? Ɗanta Safwan tsayayyen mutum da ba ya ɗaukar wargi tamkar mahaifinsa shi yake shirin zama mijin ta ce ko ma ya zaman?' Ta faɗi haka a ranta cikin tashin hankalin ganin irin kallon zallar rainin da Salma take bin shi da shi. "Impossible!" Ta furta cikin sauke numfashi gumin firgici na tsatstsafowa a jikinta........✍️ *Rashin comment ya sa ba ni da karsashin yin dogon typing, idan kun gyara ni ma zan ƙara.* *💖 KOMAI NISAN DARE......!*💖 *_Zeey Kumurya_* *ELEGANT ONLINE WRITER'S* *2️⃣9️⃣* Jijjiga kai ta yi ta ƙarasa dinning area ɗin cikin ƙoƙarin ɓoye halin da take ciki. Fatanta da addu'arta Allah ya sa kar zarginta ya zama gaskiya, tana fatan a ce laifi Safwan ɗin ya yi wa Salma shi ya sanya yake mata haka don ta yafe masa. Saboda sanin da ta yi masa

Chapter 17 of 20